Showing 51001 words to 54000 words out of 82682 words

Chapter 18 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4327

ya yake sha suka hadu suka bada wani kanshi me dadi a dolen ta ta lumshe ido...
Kallon ta yake yi can yace zaki raka ni wani waje?


Ido ta zaro tace Ni?


Yes ke!


Gaskiya ba... Hannun shi ya daura a kan lips din ta yace karki ce ba zaki ba plssss! Yanda yace plss din ya bata daria sbd yayi kamar karamin yaro kuma bata taba zaton ze iya roqonta ba...
Shiru tayi bata ce komai ba


Yace I promise to do whatever u want ba zan miki abun da ba kya so ba I just want to spend a little time with u... Just do this for me yau kadai!


Be kamata ace ta bishi ba sbd ba muharramin ta bane amma a zuciyar bata jin wani tsoro dan tasan shi in yace ba zai yi abu ba bayayi... Ajiyar zuciya ta saki sannan tace na yarda...


Yess! Thank u Baby se wani irin dadi yake ji..
Ita dai Janan gani take kamar a film wai yau ita Dr. Godwin the mighty yake ce ma thanks...


Key din motar shi ya dakko yace let's go!
Waje ya fita ta bishi yace can I hold ur hand?
Wani harara ta watsa mishi tare da fadin No!
Daria yayi yace "am just kidding kin san dai ba zan miki abun da ba kya so ba...




Sabuwar motar shi BMW fara sol tasha tinted ya nufa tare da danna mabudin suna karasowa ya bude mata gaban mota seda ta zauna sannan ya koma ya shiga shima..
Da mugun gudu ya figi motar har Janan na buge kai
seda suka hau kan titi sannan yace ki daura belt din ki.. Babu musu ta daura sbd tasan in dai ya cigaba da kalan tukin nan nashi ta dinga bugewa kenan..
Wakan *Despacito* ya saka ya kure volume da sauri Janan ta toshe kunnen ta da karfi tace wayyo ear drum dina zai toshe
A hankali ya rage volume din..
Tace gwara haka dai




Hotel 17 taga ya sa hancin motar shi da sauri ta kalle shi tana neman karin bayani, ya gane me take nufi yace mata "chill babu abunda ze faru kin san am nt a bad person just watch nd see!


Parking space yaje ya ajiye motar shi sannan ya kira wani numb yace "hey! Mun karaso fa.
Bata ji me aka ce ba yace OK but anything that happens to her ke zan kama nd also do whatever she want bana so a bata mata rai! Hope u understand! Ya sake cewa better..




Fitowa yayi sannan ya bude mata itama ta fito suka fara tafiya suna zuwa daidai wani lungu yace ki bi nan za ki ga wata me qiba ki bita.


Kamar ya in bi wacce ban sani ba?
Be kulata ba ya juya abin shi bata da wani zabi face tayi abunda yace dan taga alaman miskilancin nashi ya motso..


Cike da tsoro ta bi lungun bata ga kowa ba ji tayi an dafa mata kafada sallati ta fara yi amma ta kasa juyo wa sbd tsaban tsoro......










RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [10/4, 8:20 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ❀♠β™₯♣❀♠β™₯♣♠❀β™₯♣♠β™₯❀♠♣♠❀β™₯♣♠β™₯♣♠β™₯♣♠❀β™₯ *MATAR DOCTOR* β™₯♣♠β™₯♣❀♠♣β™₯❀♣β™₯♣♠β™₯♣❀β™₯♣♠❀β™₯♣♠










RukkyBae 😏😏😏








*Na sadaukar da wannan shafin ga duk wata writer Ubangiji Allah ya kara Basira, hakuri da juriya....* *one love*πŸ™ŒπŸ»
*Alherin Allah ya kai muku a duk inda ku ke*










****9⃣9⃣****












Miyau ta hadiye da kyar sannan ta juyo, wata mata ta gani kafin tayi magana matar tace "sunana Suhailat nice wacce Doc yace kizo waje na"
Kai Janan ta daga tare da fadin OK
Suhailat tace "in bazaki damu ba muje ko!
Ba musu Janan ta bita....


Cikin wani daki me kyau suka shiga Suhailat ta nuna mata kujera tace pls sit ina zuwa... Bayan mintuna 3 ta fito,
wani guri kebabbe tace ma Janan ta shigo
kallon ta kawai take yi, wata dogon riga fara da baka me kyan gaske ta miqa ma Janan din tace ki saka Ina zuwa..


Tsayawa tayi tana mamakin me hakan yake nufi seda tayi kusan secs 30 kafin ta tashi ta saka kayan full length mirror din dake wajen ta juya tana kallon kanta, mamaki take yi yanda kayan suka zauna a jikin ta cass kamar an gwada ta daga sama ya kamata daga kasa kuma ya bude yana dan jan kasa kadan yanada dogon hannu se belt daga baya
tana cikin kallon kanta matar ta dawo tana fadin "wow! So perfect.. U look super cute! Murmushi Janan tayi tace thanks


Inda Janan din ta zauna da farko nan suka koma...


Suhailat ta fito dauke da wani purple & pink jaka ta ajiye a kusa da Janan sannan ta bude fridge ta dakko mata drink..


Jakar ta bude se ga kayan makeup ashe makeup kit ne..
Seda Janan din tasha juice din sannan Suhailat tace kiyi hakuri zan kara miki artificial beauty akan natural beauty din ki! Janan dai bata ce komai ba illa shirun da tayi dan ita gaba daya kanta ya kwance bata san plan din Dr. Godwin ba..


Cikin minti 40 ta gama mata makeup din..
Ya Salaammm! Fadin irin kyan da tayi bata lokaci ne a takaice dai shi looks extra ordinary beautiful...
Gashin kanta Suhailat ta gyara tayi mishi style ta yi parking din shi a tsakiya, bakin veil ta dakko tayi mata rolling irin na Larabawa


Takalmi hill ta dakko ta miqa mata, Janan na cikin sawa sega kira ya shigo wayan Suhailat da sauri ta dauka tana fadin sorry Doc. Yanzu zan kawo maka ita ka bani 3 minutes"
be ce komai ba ya kashe wayan.
Janan ta kalle ta tace Miss Suhailat pls why all this? What r u guys planning?


Suhailat tace "ki bari Dr da kanshi ze miki bayani ni dai ga iya abunda ya sani kenan kiyi sauri kisa takalmin yana jiran ki...
Janan ji tayi kamar tayi kuka amma haka ta daure ta gama sa takalmin... Suhailat tace Tubarakallah Ma shaa Allah! Ki gode ma Allah gaskiya u r a real definition of beauty, Bari in dauke ki hoto...
Haka ta dinga mata hotuna sannan tayi musu selfie sunyi kyau sosai!
Wajen mirror din ta sake kai Janan tace just take a look at ur self"
ita kanta gani take kamar ba ita ba sbd gaba daya ta canza ta zama kamar wata Amarya a ranta ta gode ma Allah da wannan baiwar da yayi mata...


Hannun ta Suhailat ta riqe suka fito tare, wani guri ta nuna mata tace can zaki shiga ni ga iya inda aka bani izini tsayawa"
Janan tace gaskiya am scared ba zan iya zuwa ni kadai ba


No karki ji tsoro zan tsaya a nan har se kin shiga zan wuce"


Babu yanda ta iya haka ta fara tafiya tana yi tana waigen Suhailat seda ta kai kofan shiga sannan Suhailat ta daga mata hannu ta juya...


Rufe ido ta yi gam sannan ta tura kofan ta shiga.. Duhu ta gani a ciki kamar ta koma se kuma ta daure ta cigaba da tafiya seda ta kai tsakiya sannan taga haske ya mamaye gurin daga baya ta jiyo muryar Dr. Godwin yana wakan happy birthday...
Da sauri ta waiga tana kallon shi cike da mamaki, a hankali ya tako yazo daidai gaban ta yace
"kinyi mamaki ko? Today is 14th Feb ur birthday nd also my birthday"


Se a lokacin ta tuno yau birthday dinta kwata kwata ta manta da wani abu wai shi birthday




Hannu tasa ta rufe bakin ta Cikin jin dadi tace "ya akayi kasan birth date dina?


Sbd nima birthday dina ne shiyasa yau kika ganni so excited duk da bana celebrating se dai su Momma suyi dan ni bana son hayaniya amma yau tunda na samu birthday mate shiyasa na hada mana at least yau am happy kuma zai zama history cewa I celebrated my birthday once in my life with u kuma na saki farin ciki...


Kallon shi kawai take yi amma she is totally speechless. A ranta tace shiyasa yake ta faraa harda sa kaftan ashe yau birthday din shi ...
Ganin bata da niyyan magana yasa ya raba ta gefen ta seda yazo gefen kunnen ta yace "kinyi kyau sosai u look like a princess ya wuce sannan yace muje ko!
ba musu tabi bayan shi steps kamar guda 3 suka hau sannan suka iso wani waje rufe da curtain hannu yasa yaja curtain din gafe!
Ohhh My God!! 😍 gurin zagaye yake da decoration black nd white se table aka daura katon cake akai da wasu manyan drinks da flowers red se kujeru guda 2 a gefe akwai haske sosai a wajen ga wani sanyi me ratsa jiki se dan karami swimming pool daga gefe, wajen ya hadu iya haduwa..
Kallon ta yayi yace kina son wajen ko be yi miki ba?


Tace "I love it yayi min kyau sosai"


Duk kyan wajen be kai kyan ki ba..
Ita dai shiru tayi, gaban cake din yaje ya yanko yace "ahh" alaman ta bude baki
Ido ta zaro waje kamar ya I should open my mouth!?


Yace "Yes ki bude nace"
kafada ta maqe kamar karamar yarinya..


"Ki bude ko in matse miki bakin"


Ka manta kayi alkawari ba zaka yi min komai ba kuma kace duk abunda nake so za kayi min ?


Naji bazan miki ba ai wannan ba komai bane..
Ita dai taki yarda haka ya hakura ya kyale ta....


Sunci sun sha ya dauke ta hotuna sun kusa 50 duk wani motsi a idon shi take yi kuma se ya dauka haka suka gama komai duk da hankalin ta yana gida amma yau ta daure har sun ta taba hira..
A cikin hiran su take ce mishi can I ask u a question?


Yace yea go ahead u are free to ask me anything..


Tace "anything fa kace koda baka son magana akan abun kayi alkawari zaka fada min?


Yace eh zan fada miki


Ajiyar zuciya tayi kafin tace "me yasa baka taimako kuma baka so a ambaci taimako?


Lebe ya cije tare da runtse idon shi zuciyar shi ta fara tafarfasa kwata kwata ya kasa magana sbd be taba tunanin zata mishi wannan tambayar ba...














RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [10/6, 9:43 AM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀β™₯♣β™₯♣❀β™₯♣β™₯❀♣β™₯ *MATAR DOCTOR* ♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀β™₯♣❀β™₯♣❀♣β™₯






*Innalillahi wainnailaihirrajiun! Allah ka sa mu cika da kyau da Imani. Mutawar Samari, Yammata da Yara kanana yana daga min hankali gaba daya yanzu a ko Ina mutuwa ake yi Allah kaji tausayin mu ka ji qan mu* 😭😭😭









1⃣0⃣0⃣












Ajiyar zuciya ya sake kafin yace "nayi miki alkawari zan fada miki in ba dan haka ba babu wanda ze san lbrn nan wannan lbrn daga family na babu wanda ya san shi se ke yanzu da zan fada miki kuma inna gama kema akwai tambayoyin da zan miki kin yarda?


Ta amsa da in shaa Allah in dai na san amsa tambayan zan fada maka"






Wannan al'amarin ya faru ne tun Ina shekara 10....




Kwance muku ni, Momma da Dad a wani kongo bayan na dawo daga dako na samu naira 100 da kudin na siyo mana Gari da ruwa ko sugar babu balle gyada ko kuli kuli...


Ruwa ake sosai kayan jikin mu kwata kwata basa kare mu daga jin sanyi dan duk a yace suke, Momma ce ta fara wani irin nishi nan da nan muka tashi dama ba wani baccin arziki muke ba, Dad ya riqo ta yana fadin abunne? Shiru kawai tayi tana yarfe yarfen hannu amma ta kasa magana da sauri nima na matsa kusa Ina yi mata sannu! Dad yace in je wajen wani mutum wanda gidan shi ke kallon kongo yazo ya taimaka mana mu kai Momma asibiti


Da gudu na fita duk da ana ruwa naje kofar gidan mutumin Ina ta kwankwasawa amma ba a bude ba seda na juya zan tafi sannan naji ana budewa, gaishe shi nayi sannan na fada mishi abunda ake ciki se ya ce gaskiya bazai iya ba sbd bacci yake ji sannan yanzu be shirya fitowa da mota ba se dai in je wani wajen, rokon shi na dinga yi amma be kula ni ba ja kofar shi ya rufe,
jiki a sanyaye na koma dan in fadawa Dad naje na tarar da Momma ta suma a wajen da gudu na karasa Ina jijjiga ta amma bata motsa ba ban tsaya jiran komai ba na koma gidan wannan mutumin seda na dade sannan ya Kuma zuwa ya bude yana ganina ya fara min fada harda zagi ban damu ba na duka kasa Ina mishi magiya kawai naji ya wanke mun fuska da mari yana fadin kai wani irin yaro ne? Wannan wani irin naci ne? Idan ka kara zuwa kofar gida na sena sa an kulle ku kaida iyayen ka"
ya hankada ni gefe cikin cabalbali..


Haka na dinga zuwa gida gida Ina rokon mutane amma babu wanda ya taimaka mana har safiya Ina ta yawo ruwa yayi min duka sosai se diga nake yi dama ga kayan ba suda kauri faduwar da nayi suka kara yagewa


Ba wani kwarin gwiwa a tare da ni na koma wajen su Ina zuwa naga Momma nata wani irin jijjjga Dad yana goge mata zufa kuka na fara yi Ina kara fada mishi na rasa yanda zanyi ban samu me kaimu ba shiru yayi shima kukan yake yi yama kasa magana... Ganin be ce komai ba yasa wata dabara ta fado mun na sake fita da gudu,
bakin titi naje na nemo me a daidai ta sahu ban tsaya tayi dashi ba, muka je muka dakko ta se wani asibiti na gwamnati jmuna zuwa ko ta kan me adaidaita bamu bi ba da gudu Dad ya dauke ta aka muka shiga asibitin.. Likita ne ya fito yana fadin kun bude mata file a asibitin nan?

Dad yace aa


Likita yace toh kuyi maza ku bude mata file sannan ku je ku biya kudin aikin da zaa yi mata za ku biya dubu hamsin"


Dad ya fara roqon Likita akan ya rage mana kudin sannan ayi mata aikin kafin ya nemo kudin"


Likita yace mu bama haka a asibiti


Dad yace ka taimake mu karta mutu"


In baka da shi ka dauke ta ku tafi amma mu ba a taimako a asibiti sbd ba wajen taimako bane, nan da minti 30 in baka kawo kudin ba ku bar asibitin nan babu dole se ku wani zo kuna a taimaka muku
yana gama fadin haka yayi tafiyar shi..


Zama Dad yayi tare da dafe kai ya rasa ta inda ze fara..


Nima haka na zauna Ina ta kuka..


Kamar an mintsili Dad ya tashi ya fita ba tare da yace komai ba,
be dade da fita ba se ga me adaidaita ya shigo yana cewa mun barshi a waje bamu bashi kudi shiru nayi sbd ban san me zan ce mishi ba rashin mutunci ya fara mun mutane se kallon mu suke yi yace in baka bani kudina ba zan je in dakko wanda zasu amsan min kudin


rokon shi na fara yi Ina ce mishi ba muda komai ya yi hakuri ya taimaka mana ko kallo na be yi ba ya fita.....




Bayan kamar minti 10 se gashi ya dawo tare da dan Sanda nan aka ce nayi karami ba zaa iya kulle ni ba Ina Baba na?
Nace baya nan ya fita nemo kudin da zaa biya a ma Mama na operation"


Mai adaidaita yace Oga kawai a tafi dashi in Baban ya dawo be ganshi ba dole ya kawo kanshi sbd a sake mishi Yaron shi"


Babu musu Dan sandan nan ya iza keyata ya tafi dani Ina kuka amma babu wanda ya kalle ni balle ya taimaka min"






Bayan awa 2 se ga Dad ya zo waje na ban san Ina ya samu kudi ba yaba yan Sanda sannan aka abude ni duk na sha wahala sbd wari da zarnin cell ga wani dan shaye shaye da yake ciki ya dinga duka na babu wanda ya hana shi...


Lallashi na Dad ya fara yi ni dai hankali na yana kan Momma nan na tambaye shi Ina take?


Yace min kar in damu tana nan lfya kuma ta haifi baby girl"
doki da murna yasa na manta halin da nake ciki...


Wani gida me kyan gaske muka shiga se dai ba wani babba bane gidan amma ya yi kyau ko Ina an kwata shi.... Wani daki muka shiga nan naga Momma kwance tana bacci akan Gado ga Baby a gefe ita ma cikin gadon ta... Mamaki na dinga yi nace Dad gidan waye wannan?
Yace namu ne Son muje in nuna maka Dakin ka...




Tun daga lokacin rayuwar mu ta canza muka koma rayuwar jin dadi sakamakon wani babban alamari daya faru wanda bazan iya fada miki ba watakila se nan gaba..... Kuma yau kinji dalilin da yasa bana taimako kuma bana so a furta min kalmar taimakotaimako!




Janan wacce tunda ya fara bata lbrn take kuka tare da tausayawa rayuwar shi ta baya.. Wani irin ajiyar zuciya tayi sannan tace "gaskiya kunyi facing hardship a rayuwar ku amma.....


Dakatar da ita yayi yana fadin mu bar maganan.. Kamar yanda nace miki akwai tambayoyin da zan miki kin shirya in tambaye ke?


Kai ta daga alamar eh"


Yace......












RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [10/7, 2:40 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ♣❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣❀♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯ *MATAR DOCTOR* ♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣β™₯♣♣








_RukkyBae_😏😏😏








_Mata mune iyayen giji tarbiyyar Yara na hannun mu! Mene ne anfanin exposing jikin mu? Me yake kara mana? Wace riba muke samu akan haka? Mutuncin mu yafi komai! Dame muka fi matan da suka gabata kafin mu? Shin se mun bayyana baiwar da Allah yayi mana kafin mu samu masu son mu? Mace ta gari itace me kare darajar da Ubangiji yayi mata.... ALLAH ka yafe mana ka bamu ikon kare mutuncin kan mu Ameen!_




_Tunatarwa ce_πŸ‘ŒπŸ»








1⃣0⃣1⃣










Yace Ina so ki fada min mene ne musulunci? Da duk abunda kika sani game da musulunci sannan Ina so ki fada min abunda ke sa mutum ya zama cikakken Musulmi kuma Ina so ki fada min akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login