Showing 33001 words to 36000 words out of 82682 words

Chapter 12 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4341

zaton matar zata farka yanzu ba....






*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/28, 8:40 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❀⚜❣⚜❀ *MATAR DOCTOR*_⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜








*_Rukky Bae_*😏😏😏






_Dedicated this page to my lovely sisters_
_Firdausi Zubairu_
_Maryam Zubairu_
_Fateemah Zubairu_
_Safiyya Zubairu_
_Asma'u Zubairu_
_I really love nd cherish u guys_😍😍😍😘😘😘









8⃣2⃣






Salati Janan ta dinga yi sbd batayi zaton matar zata farka yanzu ba.. Da sauri ta karasa gaban gadon ta zauna a gefe tana shafa kan matar a hankali tare da tofa mata adduo'i cikin kankanin lokaci bacci me nauyi ya dauke matar wani wawan ajiyar zucia Janan ta saki sannan ta tashi taje ta dakko yaran gashi ba a zo da gadon saka yara ba ko kaya babu a jikin su se zanin asibiti da aka rufe su dashi se kuka suke yi abun gwanin ban tausayi.. Wani empty gado ta daurasu wanda yake nesa kadan dana matar duk sun jigata sbd kukan da suka sha se faman tsotsan hannu suke yi cike da tausayi Janan ta bar dakin ta koma office din Dr.Godwin duk da tana cike da fargaba sbd matar zata iya farkawa kuma tana bukatar alluran bacci in ta farka se kuma alluran jijiya sbd rage mata yunwa.. Cikin nutsuwa ta bude kofar ko knocking batayi ba sbd tunanin daya cika mata zucia.. Kamshin turaren Dr.Godwin ne ya alamtar mata tana cikin office dinshi


Tana dagowa suka yi ido hudu dashi da sauri ta kauda kanta ita ta rasa dalilin dayasa bata iya hada ido dashi kuma yana mata kwarjini sosai..
Wajen zamanta ta koma ta dauki jakarta sbd tana zaton akwai wasu yan kudi a ciki kuma zasu ishe ta siyan ma yaran kaya.. Gefen table din Dr.Godwin ta tsaya amma ta kasa magana sbd bata san ta ina zata soma ba..
A hankali ya dago yana kallon ta se yaga ta bashi tausayi yau kadai har ta rame ta fita daga hayyacin ta kamar itace bata da lfya... Ji tayi a jikin ta yana kallon ta da sauri ta dago suka sake hada ido amma wannan karan bata dauke ido ba itama ta shagaltu da kallon shi seda taji alaman hawaye na kokarin sakkowa daga idonta cikin azama ta dauke idonta amma kafin nan har hawayen su zubo.. Farin hanky ya mika mata yace "ki share hawayen ki cuz ganin su yana daga min hankali"
Cike da mamakin kalman daya fito daga bakin shi ta karbin hanky din tana kallon shi.. Shi kanshi be san ya fadi hakan ba sedai har cikin zuciar shi hawayen ta yana damun shi kuma he mean what he said... Ganin taki magana yasa shi cewa "me ya faru ko kina son wani abu ne?
Kai ta daga amma bata ce komai ba
Yace " me kike so tor?
"Ehhmm.. Dama...dama ina so ne in dan fita zan siyo abu ne shine nake so ka bani izini pls don't say no cuz fitan is very very important plssss" ta hade hannayen ta waje daya..
Yayi niyyar ya hanata amma yanda take pleading ta kashe mishi jiki badan yaso ba yace "u can go"
Godia ta tsaya mishi ya daga mata hannu alamar baya so


Gudu gudu sauri sauri ta bar office din... A bakin gate din asibitin ta samu adaidaita kasuwa ta fadi mishi zata ba bata lokaci ya dauke ta.. Siyayya daidai gwargwado tayi wanda matar da yaran zasu bukata sannan ta dawo asibitin...


Dakin da aka kwantar da matar ta wuce tana zuwa ta tarar da yaran har sunyi bacci sbd wahala ga fuskar su duk jirwayen hawaye... Drawer'n gefen gadon ta ajiye kayan shayi da madaran yaran da ta siyo.. Pharmacy din dake cikin asibitin ta tafi ta karbo alluran bacci dana jijiya ta dawo tana shigowa dakin daidai nan yaran sun farka... Hannuta ta mika ta dauki daya ta bata ruwa da madara sannan ta dauki dayar itama ta bata a tare suka saki gyatsa ita kuma Janan tayi murmushin farin ciki..
Wata tsohuwa dake asibitin wanda Janan ke kira da _'Innata'_ ta roke ta akan tayi ma yaran wanka babu musu ta karbe su sbd tana son Janan...


Bayan minti 30 se gashi an shigo da yaran pess sun sha wanka kayan da Janan ta siyo musu me kalan pink nd white aka sa musu nan yara suka fito gwanin ban shaawa dari biyar ta ba Inna amma taki karba tace "haba 'yata sbd na miki abune zaki bani kudi? Ai kinfi karfin haka daga wajena"
Janan tace "aa Innata ba dan kinyi min abu bane kyauta ce na baki kuma dan Allah ka ki ki karba"
Badan taso ba ta karba hade da yima Janan godia
Janan tace "nice da godia Innata"
A haka tsohuwar ta bar dakin cike da farinciki... Janan na cikin yi musu wasa taji matar na fadin "La'ilahaillah Muhammadurrasulullah (SAW)"
Janan ta tashi taje wajen ta har ta gama bude ido tana shafa cikin ta tace "Baiwar Allah na haihu ne? Ina abun da na haifa ko ta mutu ne?
Janan tace "eh kin haihu kuma bata mutu ba"
"Tor ina take in ganta?
Janan ta koma wajen gadon ta dakko daya ta mika mata ta sake komawa ta dakko dayar cike da mamaki matar tace "wannan kuma fa?
Janan tace "duka yaranki ne"
Kina nufin 'yan biyu na haifa?
Janan tace "eh 'yan biyu ne kuma duka mata"
"Alhamdulillah ina Baban su yake?
Shiru Janan tayi seda matar ta sake tambayar ta sannan tace "yaje memo cikon kudin asibiti ya dawo"
Cike da tashin hankali matar ta fashe da kuka tana fadin "da kyar ze dawo ba zai taba dawowa ba"
Janan tace "me kika ce?












*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [1/6, 7:50 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❀ *_MATAR DOCTOR_*⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜








*_Rukky Bae_*😏😏😏








_Dedicated this page to ol d grp members of_
_MATAN ALJANNAH_


_Thanks 4 ur support❀❣ especially Ummu Adnan_








8⃣4⃣








Maganar da Janan tayi yasa Dr.Godwin rufe laptop dinshi da karfi yana huci wanda shi kanshi be san yana yi ba lokaci daya idon shi ya kada yayi ja....


Imran daga bangaren shi yace "I love u so much my Angel"
Cikin shagwaba Janan tace "ni dai ban yarda ba I love u more"
Imran yace "aa Angel babu yanda zaayi sanki yafi nawa dan dai baki san yanda nake sonki bane shiyasa kike fadan haka"


"Naji kafi sona yaushe zaka zo tor? Kasan dai nayi missing dinka ko"


"Am so sorry my Angel kina raina aiki yayi yawa ne but in shaa Allah cikin week din nan zan zo in ga cute face dinki da murmushin ki me faranta raina kuma I missed u more"


Janan tace "shikenan my love se ka zo take care of ur self for me"
Seda Dr.Imran ya kara jadadda irin son da yake mata kafin sukayi sallama...
Rungeme wayan tayi a kirjin ta ta ce "I really love u Nurul-qalbee"


Karan rufe laptop din Dr.Godwin ne ya dawo da ita daga yanayin data fada a firgice ta dago suna hada ido taga idon yayi ja ga wani abu dake yawo a cikin kwayar idon shi wanda bata gane me hakan ke nufi ba se wani irin kallo yake binta dashi
Yana yin shi ya tsoratar da ita da sauri ta sunkuyar da kanta kasa...


Jessica da Ruth da suke zaune a gefe suka kalli juna Jessica ta matsa da kanta wajen kunnen Ruth tace "me kika fahimta daga kallon da Doctor yake ma Janan?


Ruth tace "yafi kama da yana jin haushi ko kuma yana kishi"


Jessica tace "noo baki gane ba kallon tsana yake mata.. Baki ga yanda yake kallon ta bane"


Ruth tace "kuma fa haka ne.. Indai kallon hatred yake mata we r safe"
Jessica zata sake magana suka ji Dr.Godwin yayi banging kofar ya fita


juyawa suka yi suna kallon Janan suka ga ko a jikin ta tana ma buga buga talking Tom ( _Hahahaha My Momma's best game_ πŸ˜‚)


_15 mints later_


Dr.Godwin ya dawo cikin office din har yanzu be dawo daidai ba wasu files ya dauka da bakin glasses dinshi ya daura lab coat akan kayan shi yace "follow me"
Jessica da Ruth suka tashi jiki na rawa Janan ko game dinta ta cigaba da bugawa..


Har ya juya ze fara tafiya se yayi tunani in ya barta ita kadai zata iya cigaba da wayan kuma zatayi tunanin ko yana kishin ta ne ko yaji haushin wayar da tayi dazu da wani.. Yace "hey u! I don't need to repeat my self"
Ya juya yayi tafiyar shi su Jessica suka bishi kamar jela..
Tsaki kadan taja sannan ta bi bayan su
Daki daki suka bi suka duba marasa lfya daya bayan daya se wani shan kamshi Dr.Godwin yake yi.. Dakin da aka kwantar da matar nan suka shiga ya dudduba patients suna zuwa kan matar nan Dr.Godwin ya nufi kofa da niyyar fita da sauri Janan ta sha gaban shi tace "Doc.baka duba waccan patient din ba yanzu ta tashi"
Yace "and so what? Bazan iya dubata ba na gaji I need to rest"


Kwalla ne ya ciko idon kamar zata yi kuka cike da mamaki Dr.Godwin ke kallon ta a ranshi yace _"ohh my God! Wannan ta cika shagwaba abun kuka baya mata wuya maybe yanzu in na ki duba patient din nan ta zauna tayi ta kuka dan naga alaman tausayin ta yayi yawa_"


Gadon matar ya nufa yafara duddubata nan yaga komai yayi operation din da aka mata was perfectly OK da alama zeyi saurin warkewa dan bata da kan jiki...
Matar tace "Doctor kishi nakeji zan sha ruwa"


Yace "no bazaki sha ruwa ba yanzu se kin kwana biyu bayan kin fidda iska shine zaki iya fara shan ruwan lipton da fruits da dai abu me ruwa ruwa"
Kallon Janan yayi yace "akwai alluran da za ayi mata na jijiya sbd haka ke se kiyi mata cuz nu bazan iya ba"
Hanyar kofa ya nufa gab da ze fita mijin matar ya shigo rike da kaya niki niki dukkan su suka maida kallon su kan shi suna mamakin dawowar shi a wannan lokaci










*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [1/1, 11:07 AM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜ *_MATAR DOCTOR_*❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜








*_Rukky Bae_*😏😏😏






_Dedicated this page to my lovely sis who is more than a frnd to me_❣
_Hauwa Slim Small_❀❣






8⃣3⃣








Janan tace "me kika ce"
Kasa maimaitawa matar tayi sbd kukan daya ci karfin ta.. Kallon ta kawai Janan take cike da mamaki...
Ita gaba daya ma ta rasa me zatayi can dai ta nisa ta fara lallashin matar kamar haka "haba baiwar Allah be kamata ki zauna kina kuka ba godia ya kamata kiyi ma Allah daya sauke ki lfya har ga yaran ki biyu kuma a cikin yanayin nan be kamata kina kuka ba sbd baki gama samun sauki ba.. Kamata yayi ace kina bacci yanzu"
Matar tace cikin kuka hawaye wani na bin wani "hmm Nurse bazaki gane abun da nake fada ba ni na san se dai wani iko na Allah mijina ze dawo dan bashi da kudi sannan be san inda ze samo ba" ta sake fashewa da wani matsanancin kuka
Ganin haka yasa Janan mikewa ta karasa kusa da ita ta dakko alluran bacci zatayi mata da sauri matar ta dakatar da ita da fadin "Nurse ba se kinyi min allura ba ki barni inyi kukan ko zan ji dadi a cikin raina"
Janan tace "kiyi hakuri ki sani ke musulmace kuma duk abun da ke faruwa daku muqaddari ne daga Allah kuma jarabawa ce sbd haka ki cire damuwa a cikin ranki ki bada goyon baya wajen neman lfyar ki" da kyar da ban baki Janan ta samu tayi mata allura cikin dan lokaci kadan bacci ya dauke ta sassanyar ajiyar zucia Janan ta saki sannan ta dauki yaran daya bayan daya ta maida su gadon data dakko su se bacci suke yi ta fita harta fara tafiya se can wani tunani yazo mata _"anya zan ba yaran nan su kadai bayan Maman su tana bacci kuma babu wacce zata kula dasu yanda satan jarirai ya zama ruwan dare_ .. _Dayawa daga cikin mutane suka zama babu tsoron Allah a cikin ransu_! _kai!! gaskiya bazai yiwu ba gwara in kaisu dakin kula da jarirai in ba nanny daya ta kulan min dasu tunda se bayan awa biyu Maman su zata farka ni kuma ba lallai bane in dawo ta farka maybe akwai aikin da zan ma Doctor_.... Da wannan shawaran ta koma ta dakko su tare da feeder dinsu in case ko zasu farka su nemi abinci..
Bata sha wahala ba wajen samun nanny din dazata kula dasu kafin ta dawo zuwa anjima..


Office din Dr.Godwin ta koma.. Knocking tayi aka bata izini ta shiga bata kalli kowa ba taje ta zauna su Jessica se hararanta suke ita batama san sunayi ba se a lokacin ta ciro wayar ta a jaka nan taga har 5 missed calls daga Dr.Imran din ta murmushi kadan ta sake tanaso ta kirashi amma tasan Dr.Godwin bazai barta ta fita ba tana cikin tunani wayar ta fara ringing cikin wakan _Ashquii_ kallon gefen Dr.Godwin tayi taga se faman danna laptop yake yi.. Tana so ta dauka amma bata so ta kasa sakewa.. maganar shi ce ta katse da fadin "pick up d call karan yana damu na"


Tace "zan iya fita na amsa sbd kar na dame ku?


Yace "no ki amsa a nan as u can see babu wanda keda time din jin abun da zaki ce cuz we r all busy"
Kamar jira take da sauri ta dauka tare da fadin "Amincin Allah ya tabbata a gareka Nurul-qalbee"


"Kema Aminci da Rahmar Allah su tabbata a gareki my pretty Angel" ya fada daga daya bangaren...


Nan fa suka fara zuba soyayya gaba daya Janan ta manta a inda take da waenda take tare dasu kalaman soyayya kawai take zuba ma Imran..


Tunda ta fara waya Dr.Godwin ya kasa cigaba da aikin shi sedai kawai ya kafe screen din laptop da ido ji yayi zuciar shi na zafi tana bugawa da sauri da sauri... Mamakin kanshi yake yi a ranshi yace _"what d hell is wrong with me_? _meyasa nake damuwa da yarinyar nan_? _meyasa nake jin wani babban alamari a kanta_?
Shi kanshi ya rasa amsan wadannan tambayoyin can wata zuciar tace _"ko dai kana son ta ne_?
A hankali ya furta "no! Bazai yiwu ba no!

Wata magana Janan ta furta cikin shagwaba wanda yasa Dr.Godwin rudewa tare da da rufe laptop din da karfi yana huci wanda shi kanshi be san yana yi ba lokaci daya idon shi ya kasa yayi ja.....










*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [January-10-2017 10:09 AM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜






_Na sadaukar da wannan page din ga duk mai suna Rukayya_😜 _I love y'all_❣








8⃣5⃣








Mijin matar ne ya shigo rike da kaya niki niki dukkan su suka maida kallon su kan shi suna mamakin dawowar shi a wannan lokacin..
Kallon shi Dr.Godwin yayi sannan ya fita abun shi..


Wajen matar shi ya nufa cikin sauri ya rungume ta yama manta da cewa an mata operation..
"Alhamdulillah! Allah nagode maka! Allah nagode maka"
Cikin farin ciki ya mike ya nufi wajen Janan yace "nagode da haliccin da kika mun kuma nasan babu abun da zan iya biyan ki dashi.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi ya biya miki dukkan bukatun ki na alkhairi ya baki miji na nagari"


"Ameen" Janan ta amsa..


Yace ina "Doctor yake ba yanzu na ganshi ba"


"Eh yanzu ya fita maybe ya koma office ne"


Gefen gadon ta koma ta saka hand gloves sannan ta dau allura...


Dayan side na gadon ya zauna yana kallon matar shi nan yaga tana hawaye cikin kidimewa yace "Rahma me ya faru kike kuka?


Hannun shi ta kamo tana shashshekan kuka tace "a ina ka samu kudi? Waya baka? Allah yasa ba bashi ka ciyo ba.. Na dauka bazaka dawo ba har ina tunanin ko ka tafi kenan Nurse nata kiran wayan ka a kashe nace mata bazaka taba dawowa ba.. Ka fada min yanda aka yi ka samu kudi"
Ka sani in dai haram ne kada ka ciyar damu dashi ko kayi mana wani abu dashi domin Manzo Allah (SAW) ya bamu lbrn wani mutumi a cikin hadisin shi inda yake cewa _"wani matafiyi ne ya daga hannu yana cewa Ya Ubangiji_! _Ya Ubangiji_! _Amma abin cin shi na haram ne kuma abin shanshi na haram ne sannan tufafin shi na haram ne kuma da haram aka ciyar dashi tun yana yaro tor taya Allah ze amsa mishi"_


"Dan Allah kar ka aikata abun da kasan Allah ya haramta"...


Rungumeta yayi yace " madalla da mace irin ki.. Sunan ki ya dace dake domin ke Rahmace a gare ni .. Allah yayi miki albarka"..


"Tor ai har yanzu baka fada min inda ka samu kudin ba"


"Zan fada miki amma ina abun da kika haifa me aka samu?

"yan biyu ne duka mata kuma Nurse zata nuna maka su amma kafin nan ka fada min inda akayi ka samu kudin"
Sujjada yayi tare da daga hannu sama yayi ma Allah godia.. Gefen gadon ya sake komawa ya zauna ya ce "bayan fitana daga asibitin nan naje gidan Kawu Halliru na fada mishi halin da ake ciki amma kirikiri yace shi ba yada kudi bare ya bani na tashi zan tafi kenan sega danshi Sageeru ya je yana tambayan shi wai pocket money dinshi ya kare a take ya ciro 20k ya bashi ko nagode be ceba ya wuce.. Wai dan wulakancin Kawu se yake ce min "kasan yara in suka tambaya abu ba'a basu ba zasu iya shiga wani hali bance mai komai ba na fito... Gaba daya na rasa inda zan samo kudin har na fara tunanin in saida kayan sawan mu, ina cikin tafiya zan karasa gida naji horn daga bayana amma ban juya ba sbd tunani yayi min yawa
Kamar daga sama naji ana kiran sunana da sauri na juya Ina waigewaige nan naga Muhammad pry sch frnd dina ya fito daga mota.. cikin mamakin yanda akayi ya gane ni na juyo muka gaisa yake tambayana iyali nace suna lfya.. Kallona yayi yace da alama wani abu yana damun na.. Shiru nayi ya dafa ni yace kar in boye mishi komai nan na fada mishi kina asibiti an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login