Showing 60001 words to 63000 words out of 82682 words

Chapter 21 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4820

magana ba...


Dr. Magaji na kiran shi amma be juyo ba ya fice da saurin gaske,
tafiya yake yi amma be san inda yake sa kafar shi ba da uku_uku, bibbiyu yake tsallake steps din a haka ya kai wajen da ya ajiye motar shi ya zura hannu a aljihu be ji key din shi ba, se lokacin ya tuno ya baro shi a kan table din office din shi dazu daya shiga da dan karfi ya naushi hannun shi yana fadin "damn it"


Hanyan gate ya nufa dan ba zai iya komawa ya dakko mukullin ba yana fitowa ya tsaida me adaidaita........












_Rukkybae_😏😏😏
[11/19/2017, 11:00 AM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/18, 5:27 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ❀β™₯♣♠β™₯♣β™₯♠♣β™₯♣♠β™₯♣♠β™₯β™₯♣♣♦♣β™₯♦♣♠♣β™₯♣♠β™₯ *MATAR DOCTOR* ♠♣β™₯♣♣β™₯β™₯β™₯♣β™₯♣β™₯♣♠β™₯♣♠♣β™₯♣♠♣β™₯♣








_Rukkybae_😏😏😏








🌐HAJOW🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE*✍🏻✍🏻




1⃣0⃣6⃣






Yana tsaida me adaidaitan ya shiga ba tare da tanbayan kudi ba balle ya fada mishi inda za su..


Mai adaidata yace "ina muka dosa ne?


Mitchwwwww yaja tsaki yace muje mana dole se na fadi in da zaka kai ni? In ba zaka je ba In sauka na hau wani"


Ah me ze hana in kaika? Kawai da kar muje ne ka kasa biya na kudin dana fada maka"


A dan hasale yace "kai kudi ya dama dilla ka wuce muje bana son raini, kai da gani na na maka kalan wanda ze kasa biyan kudi?


Me adaidaita yace "oho! Wannan kai ka jiwo" Ya ja suka fara tafiya.. Can ya danna radio aiko dai dai an sa wakan *JIRGIN SO* yana yi yana bin wakan harda kara volume..


Haushi kaman ya kashe Dr. Godwin dan shi wakan ma ji yake tana kara dagula mishi lissafi..
Masifa ya fara ma dan adaidaita "ka cire wakan ko ka rage kuma ka kara sauri kana tuki kamar dan koyo"


Kai ni fa wallahi zan sauke ka ka cika korafi ni da abu na zaka zo kana bani ka'ida kamar wani ubana? Toh baka isa ka fada min yanda zan yi ba ka san shekarata nawa ina wannan sana'ar zaka zo kana wani surutu? Yasin da yanzu zan baka ba zaka iya tukawa ba se dai ku kife kai da adaidaitan"


Banza Dr. Godwin yayi da shi dan abun da ke damun shi yafi wannan shirmen! Da hannu ya dinga nuna mishi har suka kai, a dai dai kofar gidan suka tsaya ya sakko yace "ka jira ni yanzu zan dawo"


Alqur'an ka bani kudi na dan ba zan yarda ka tafi ka ki dawowa ba" Ya kashe adaidaitan tare da zare key din ya fito...


Abun ma yaso ya ba Dr. Godwin din daria amma se ya basar yayi wucewar shi,


Mai adaidaita ya kalle shi yaga kayan dake jikin shi se ya shafa gemu yace "da alama yana dan da kudi amma dai mutum ba abun yarda bane bari dai in ga iya gudun ruwan shi.......


Shiko Dr. Godwin a hankali yake tafiya yana dosar kofan gidan amma ji yake kamar yana tafiya akan kaya, a haka har ya karasa yana zuwa yaga kofar a kulle da katon padlock, buga kofan ya fara yi da duk iya karfin shi yi yake yana karawa.. Da sauri mai adaidaitan ya karaso tare da fadin "Ba ka ganin kofan a rufe take da kwado? Da alama babu kowa ka gane mana"


Wani yaro ne ya fito daga gidan dake kusa da na su Janan din, har ya wuce se kuma ya dawo, gaishe su yayi sannan yace lafiya dai ko?


Eh lafiya ba lau ba, na kawo wannan mutumin ne se naga yana ta buga kofan gidan nan kuma da alama babu kowa dan na ganshi a rufe da kwado..


Ayya! Ai basa nan sun tashi daga gidan''


Dr. Godwin yace "sun tashi? Yaushe? Ina suka koma? Zaka iya raka ni inda suka koma?


Gaskiya ban san inda suka koma ba dan lokacin da suka zo yima yan gidan mu sallama bana nan ina makaranta,


Toh yanzu kai baka san komai ba akan labarin su? Ya kara tanbayan yaron


Gaskiya ba ni da labari amma na san ba zaka rasa lambar su ba ka kira se suyi maka kwatancen in da suka koma ina ga haka ze fi..


Se a lokacin ya dan ji sanyi daya tuno yana da lambar ta koma mene ne zai zo da sauki, yasa hannu a aljihu ya ciro kudi hannun shi a dunqule ya mika ma yaron, kin karba yayi yace "ni Dan Allah nayi maka ba dan komai ba"


Eh na sani kuma sbd Allah ka karba ba dan ni ba, da kyar yasa hannu ya karba tare da godia ya wuce..


Komawa su kayi me adaidaita ya shiga suka fara tafiya, tun da suka shiga Dr. Godwin ya jingina kan shi a jikin kujera ya lumshe ido,wayar shi ya ciro ya fara dialing numb din Janan amma taki zuwa ya kira yafi so a kirga amma taki shiga, ji yayi kamar ya cillar da wayan se kuma ya ajiye ta a gefe zuciyar shi na tafasa sosai komai ya birkice mishi ya rasa me ke mishi dadi a duniya...




"Kayi hakuri ka bar ma Allah komai naga ka damu da yawa amma ina so ka sani duk abunda ke damun ka ka yi Addu'a Allah ze amsa maka kuma ze tausaya makamaka, sannan shi da ya saka ka a wannan halin shi ze cire ka!


Kai kawai yake gyadawa yana mamakin mai adaidaitan dan be yi zaton yana da tunani ba kuma yaji dadi a ranshi dan ko ba komai ya dan ji radadin dake zuciyar shi ta fara dan ragewa, be ce mishi komai ba se dai yana bin shi da kallo


Dai dai kofar asibitin ya tsaya Dr. Godwin ya fito tare da ciro dubu 5 ya mika mishi, ido ya zaro waje yace "ai kudin ka basu kai haka ba dari biyar ce itama dan sbd drop ka dauka amma da na dau pasinja ba zai kai haka ba!


Eh na sani kuma ni na baka sbd naji dadin shawaran daka bani sannan ni Dan Allah na baka, ko ba komai yanda naji dadi kaima zaka ji dadi!


Cikin sanyin jiki yasa hannu ya karba tare da mishi godia, hadi da fadin kayi hakuri da duk abun da nayi maka, nayi maka haka ne sbd yanda tsoron Allah yayi karanci a zuciyar mutane wasu ma sun fi so suci hakkin mutun ya bar su da Allah..


No ba komai karka damu ai hakkin ka ne dole ne kabi duk wata hanya da zaka kare abun ka, se anjima... Ya zuya ya shiga asibitin, me adaidaita ya tafi yana me farin ciki tare da jinjina ma wannan mutumi...


Yana shiga office ya rufe ta ciki dan kwata kwata yau baya jin ze iya duba kowa hannu yasa a aljihu dan ya ciro waya ya kara trying ko zai samu wayar ta shiga se yaji wayam!


Oh My God! Na manta da shi a Napep! Yasa hannu ya bugi goshin shi, I loose It! Shikenan I loose her number and pics! Shi ba ma wayar ta dame shi ba lambar ta ce ya dame shi dan yana ji ze iya siyan irin wayar guda goma ba tare da yaji komai ba amma shi ba wannan bane matsalar shi ba..




Mintuna 30 bayan haka kawai me adaidaita yaji waya na kara a bayan sit,
Laaa! Mutumin nan ya manta wayar shi!
Juyawa yayi ya koma hanyar Asibitin! Yana zuwa ya shiga nan ya samu me gadi yayi mishi kwatancen Dr. Godwin


Kwatancen office din shi yayi ma mai adaidaitan, yana zuwa ya sake tambaya aka kara nuna mishi, har kofan ya karasa yayi knocking, tsaki Dr. Godwin yaja, baya jin ze iya bari azo a dame shi.. Kara knocking aka yi


cike da jin haushi ya mike ya bude kofan, yana fadin "What the... Sauran kalman ya makale a wuyan shi ganin me adaidaitan a tsaye yana washe mishi hakora!


Ya dai? Ya tambaye shi


Wayar ka ce na ji tana kara shine nace bari na kowa maka kada hankalin ka ya tashi dan na san kana ta nema!


Murmushi yayi ya mika hannu ya karba yana fadin Na.. Go.. De! Abun da be saba ba kenan amma yau ya fada sbd hallacin da yayi mishi... gaskiya da za a dinga samun matasa irin ka da an huta da sace sace ka burge ni kwarai! Ina zuwa" Ya shiga ciki, drawer ya bude ya rubuta mishi cheque na dubu 100, yana fitowa ya mika mishi yace "kada kayi min godia kaje kai ma in ka samu hali ka taimaki wani" yana gama fadin haka ya rufe office din shi... Me adaidaita ya wuce jiki a sanyaye harda dan hawayen shi na farin ciki ......






Bayan Sati daya!






Dr. Magaji tsaye a kan shi yana magiya "Haba Surgeon G! Ya zaka mana haka? Kazo muje dakin theater ka gama ba wani dadewa za kayi ba appendix ne plsss!! Ya hade hannayen shi biyu waje daya!


Nifa bana cikin walwalan da zan iya yin komai ba kawai ku bari nxt time"


Eh duk da haka muje abun yayi chronic dan any moment frm now ze iya fashewa..


Ohhhh no! Kana so a kara samun matsala kenan? Sau 3 ina yin operation amma daga in manta almakashi se in mata sirinji, kaima a gaban ka aka dawo dasu kuka cire ni kam bazan iya ba!










_Rukkybae_😏😏😏
[11/19/2017, 11:17 AM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/18, 9:25 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ♣β™₯♠❀β™₯♣♠❀β™₯♣β™₯♠❀♣β™₯♠❀♣β™₯♠❀♣β™₯♠♣β™₯♠❀β™₯♣ *MATAR DOCTOR* ♣♠♠❀♠β™₯♣❀♠♣β™₯♠❀β™₯♣❀♠β™₯♣❀♠β™₯♣♠










_Rukkybae_😏😏😏




*HAJOW*🌐
_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_✍🏻✍🏻








1⃣0⃣7⃣










Zaka iya! Na sani zaka yi, ni nafi yarda da aikin ka, hankali na yafi kwanciya da aikin ka, ban taba rokon ka wani abu ba amma yau na roke! Yau kadai...


Huh! Sabo da kai kadai zan yi!


Yesss! Thank u!


Tare suka tafi dakin theater, cikin kwarewa yake aikin har ya gama, kafin ya dinke se da yasa Dr. Magaji ya duba mishi kada yayi mantuwa


Murmushi yayi yace "job well-done Surgeon G"






Yau kusan kwana 4 kenan kullum ya kwanta se yayi mafarkin Janan tana kuka, ya rasa wannan wani irin mafarki ne! Haka ya kasa komawa bacci ya zauna! Hotunan ta dake wayan shi ya fara kallo yana shafa fuskan ta a haka har bacci ya kwashe shi!




Tun bayan da yayi last theater din nan be kara zuwa asibitin ba dan shi yanzu baya iya komai, komai yake yi se yaga fuskan Janan, be taba zaton son ta ya kai har haka ba, dai dai setin zuciyar shi ya dafa yana fadin "ke kadai nake so, ke kadai zuciya ta ta aminta da ita, ba zan kara son ko wace 'ya mace ba a duniyanan, ko wani bugu na zuciya ta da ke take yi, na so ki jiya, ina son ki yau kuma zan so ki har abada! Hawaye yaji suna kwaranya daga idon shi, a hankali ya shafo hawayen yana fadin "nayi kuka a kan son ki,
Na so ace na baki labari na wanda ze faranta miki rai! A ina zan ganki? Yaushe zan sake ganin ki? Ya rushe da wani irin kuka me ban tausayi! Na yarda soyayya halittace sannan bata da magani!


Wayan shi dake gefe ta fara ringing Dr. Magaji ne ke kiran shi tun jiya amma ya kasa dauka dan be san me zai ce ba har kiran ya katse, wani kiran ya kara shigowa seda ya seta muryan shi sannan ya dauka!


"Surgeon G lafiya dai ko? Yau kwanan ka nawa rabon ka da zuwa asibiti? Ga patients se zuwa suke yi ta ko ina"


"Bana jin dadi ne, but gobe zan yi kokari in zo"


Ya Allah! Meke damun ka? Bari inna tashi daga office zan biyo in duba ka"


No karka damu na warke ai, gobe dai kuyi expecting zuwa na!


Suka ajiye waya!





Washe gari




Yau patients 5 yayi ma operation duk ya gaji!


Ba tare da shawaran kowa ba ya rubutu takardan barin aiki! Da kanshi ya kai Ministry,, suka ce nan da kwana biyu ze ji daga gare su...






Cikin shirin shi ya tafi Ministry dan yau kwana biyu ya cika kuma sun kira shi!
Wani conference hall aka gyayyace shi da ya shiga! Yana shiga yaga mutane da yawa a zazzaune be damu ba kuma be tsorata ba dan tsoro ba ya da muhalli a zuciyar shi! Wata kujera aka nuna mishi ya zauna!
Wani mutumi ya mike yana fadin "Sunana Kabeer Sulaiman ina daya daga cikin members na wannan Ministry din, mun ga takardan daka kawo, kuma munyi bincike a kanka sosai mun gano kana da matukar anfani a wannan asibitin domin kana daya daga cikin wanda muke alfahiri da shi kuma Garin nan ke alfahiri da shi, but unfortunately ka turo mana da abunda ban zaton za mu iya barin ka subuce mana, se dai ba muda ikon hanaka abunda kake so amma muna so muji dalilan ka"


sannan ya zauna..


Dr. Godwin yana zaune yayi gyaran murya kafin ya fara magana "Sunana Godwin Williams Albert, General Surgery DOCTOR a Barau Dikko Special Hospital, dalilai na ba masu karfi bane amma na zabi ajiye aiki na sbd bani da natsuwar aiwatar da aikin, sannan kusan ko da yaushe ina shiga theater cikin tunani wanda ya ke haddasa min mantuwa da abubuwa masu kaifi a cikin patients, bana so wani ko wata su rasa ransu ta dalili na shiyasa kawai na zabi barin aikin!


Me yasa ba zaka dauki hutu ba ka zabi ka bar aikin? Wani daga cikin su ya tambaye shi..


Saboda matsalar babbace kuma bana tunanin zan fita daga ita nan kusa!


Shin ko za mu iya sanin mece ce matsalar?


Gaskiya aa sbd wannan personal problem dina ne!


Munji bayanin ka kuma zamu sa maka hannu dan ka bar aiki amma se ka yi mana wani aiki wanda daga shi in dai baka kuskure ba zamu barka ka tafi kuma ba zamu taba mantawa da kai ba amma in ka kuskure ba zaka ajiye aiki ba kuma zamu kai maganar zuwa kotu dan lokacin da zamu dauke ka aiki se da ka yi rantsuwa za kayi aiki a ko wani yanayi kuma a ko wani hali!


Ku fadi abunda kuke so ina jin ku!


Projector a kunna a jikin bango, nan kowa ya kai duban shi jikin bangon, wata matashiyar yarinya ce kwance fuskarta kacakaca abun ba kyan gani, nan waje ya kaceme da hayaniya kowa da abunda yake fada!


Nan Kabeer ya jiyo da duban shi wajen Dr. Godwin yace "Hanan sunan ta yarinyar Mataimakin Gwamnan garin nan, sun sami plane crash ne wanda haka yayi sanadiyar kwashewar fatan fuskar ta, yanzu haka tana Egypt nan da 3days zasu dawo sbd sun ki karban ta a duk kasar da suka je, mu kuma mun san muna da kai kuma u can do It shine mu kayi convincing Baban ta a kawo ta nan garin kai zaka yi aikin!


Sosai hankalin Dr. Godwin ya tashi dan shi be taba irin wannan aikin ba duk da ya san ze iya amma abun yayi worse, ga kuma halin da yake ciki!












_Rukkybae_😏😏😏
[11/24/2017, 4:07 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❀♣β™₯♠♣β™₯♣♠♣β™₯♣♠♣β™₯♣♠♣β™₯♣♠β™₯β™₯♣♠♣β™₯♣♠β™₯♣ *MATAR DOCTOR* ♠♣β™₯♣♠β™₯β™₯♣♠♣β™₯β™₯♣♣♠β™₯β™₯♣♠β™₯β™₯♣♠β™₯








_Rukkybae_😏😏😏










*_HAJOW_*🌐🌐
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_*✍🏻✍🏻✍🏻








1⃣0⃣8⃣








Kabeer yace "kai muke jira muji ta bakin ka Dr. Godwin!
Se a lokacin hankalin shi ya dawo jikin shi! Ajiyar zuciya yayi sannan yace "na ji bayanin ku kuma na gani dan haka plastic surgery za ayi mata amma ta ya ze yiwu ba muda kayan aiki ingantattu? In fact ba muda kayan da za muyi anfani da su wajen yin aikin!


"wannan ba matsala bace kar ka damu za a samo su in dai zaka iya!


Nan dai taro ya watse da alkawarin za a bashi kwangilar siyo kayan online tunda babu lokacin da zai iya zuwa siyowa da kan shi..










Yau kwanakin ukun suka cika komai a ake bukata sun iso tun jiya nan da awa daya za su karaso a fara aikin... Dr. Godwin yau yayi kokarin seta kanshi ko dan ya ba su mamaki..


Saukowan su kenan daga jirgi ko gida ba su wuce ba suka kamo hanyar asibitin.. Tun kafin su karaso har an sakko da wani sabon gadon mara lfya wanda duk yana cikin kayan...


Sabuwar motar ambulance ce ta shigo cikin asibitin, tana tsayawa Dr. Godwin ya taka a hankali har ya karasa bakin motar
Hannu yasa ya bude kofar, a lullube take tun daga kanta har kafa, a hankali ya dan bude fuskarta wani irin zabura yayi yana fadin "Ohhhh My God! Tare da zare ido, ganin yanda fuskarta take har tafi munin gani akan na hoton da aka nuna mishi, cikin sanyin jiki yayi ma Nurses alama su matso da gadon, cikin hanzari suka karaso, Maman ta da Baban ta suka fito daga wata jeep suka tsaya dai dai bakin kofar motan da take, hawaye ne ke fita daga idon Maman tace "kuyi a hankali jikin ta babu kaya kuma akwai raunuka idan kuka yi mata da karfi fatan da ze iya sabulewa!


Ajiyar zuciya Dr. Godwin ya sauke,


kamar kwai haka suka dakko ta suka daura akan gadon sannan suka tura ta, Dr. Godwin da iyayen ta suna bin su a baya har suka kai kofar wani daki inda aka tanada sbd yi mata operation din!


Daki na musamman aka kai Iyayen nata don jira!


Dr. Godwin ya kira Dr. Magaji sbd yafi so yayi aikin da wani a kusa da shi duk da ba fannin Dr. Magaji din bane, Nurses 4 ne suke ciki dan taya su... Seda ya tuno Janan din shi a ran shi yace "da yanzu kina gefe na kina tayani, koda baki taya ni ba inna kalle ki zan samu courage duk da na san da kina nan kuka zaki dinga yi dan na san water melon eyes gare ki! Ya yi murmushi...


Motsi ya dinga yi da bakin shi kaman yana addua'a sannan ya matsa kusa da ita


Cikin dauri ya fara aikin duk da zuciyar shi tana dokawa shi kan shi Dr. Magaji jikin shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login