Showing 39001 words to 42000 words out of 82682 words

Chapter 14 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4329

tayar da kura.. Imran yayi saurin mika mata ruwan goran dake hannun shi na mata sannu..
Se da tarin ya lafa mata sannan yace tazo su wuce ya kai ta gida lokaci yana kurewa ga shi akwai walima a gidan.. Ba musu ta bishi suka fara tafiya duk an watse saura mutane yan kadan...


Mintuna 30 ya kai su gidan su Janan daga can nesa kadan da gidan yayi parking ji yake kamar kar ta sauka amma ba yanda ze yi.. Handle din kofan ta bude har ta fitar da kafa daya waje yace "oops! Naso in manta. Hannu ya miqa ya dakko wasu manyan ledoji guda 4 yace "Angel ga nawa gift din Allah ya sanya ma karatun ki albarka"


Tace "Ameen nagode Nurul-qalbee" ..


Ya cigaba "Allah ya mallaka min ke a matsayin mata uwa ga 'ya'yana"


Shiru tayi kanta a kasa bata amsa ba..


Yace "Angel baki amsa ba"


Da sauri ta dauki ledojin ko sallama bata mishi ba sbd kunya..


Murmushi yayi yana girgiza kai shi gaba daya mamakin irin kunyarta yake.. Yana murmushi yayi reverse ya bar layin..


Tana shiga gida ta fara neman Ummiey bata ganta ba... Nan ta fara kiranta "Ummiey! Ummiey!!
Muryan ta daga baya tace "oh ni wannan kira kamar makauniya ko ance miki na bata ne kike min irin kiran nan"
Dariya Janan tayi tace "tor ba na shigo bane ban ganki ba se neman ki nake yi'


Ummiey tace "gani ai yanzu kin ganni"
Hannun ta Janan taja suka wuce dakin Ummiey.. Nan ta mika mata ledojin da Imran ya bata..
Kallon ta Ummiey tayi tace "wannan daga ina kuma?


Janan ta fara inda inda "Am.. am.. Yanzu ya bani wai gift din sauka..


Murmushi Ummiey tayi dan ta gano wanda ya ba Janan din.. "Tor Allah ya saka da alkhairi"


Kayan Ummiey ta fito dasu nan suka ga atamfofi leda daya se cosmetics leda daya takalma da Hijjab leda daya se ledan karshe tarkacen chocolates da sweets..


Albarka Ummiey ta sama Imran sannan tace ma Janan "tashi ga kayayya kin ki a cikin wardrobe an karbo daga dinki ki shirya mutane sun taru" tana gama fadan haka ta bar dakin ita kuma Janan ta shiga bayi ta watsa ruwa... A gurguje ta shirya bata wani bata lokaci ba wajen kwalliya dama batayi, kwalli, powder sai lip balm kawai tashafa se dauri me kyau da tayi... Ba karamin kyau tayi ba.. Tana fitowo mutane suka fara fadin "Tubarakallah Ma shaa Allah"......




An ci ansha sannan anyi rabon souvenirs sosai tamkar ana biki haka Janan tayi ta canza kaya ana ta hotuna...




Alhamdulillah taro ya tashi lfya gwanin ban sha'awa ga tarin gifts da mutane keta kawowa harda sisters din Imran sun zo da nasu kyaututtukan se yaba Janan suke farat daya ta shiga ran su.... Se yamma mutane suka fara watsewa harda Maman Hanayya..


Bayan Sallan Magrib Janan da Ummiey zaune a parlor wani yaro yayi sallama suka amsa.. Wata karamar jan jaka ya miqa ma Janan tare da fadin "gashi wai in kawo miki inji wani a waje"


"Wani a waje kuma?? Janan ta fada cike da mamaki..


Yaron yace "eh a mota yazo yana bani kuma ya wuce"


Ummiey tace "ko dai Imran ne? Ki kira shi kiji"

Yaron bema tsaya jira a kira ba ya wuce abin shi


Tana kokarin kiran shi se ga kiran nashi ya shigo "bayan sun gaisa se take mishi godia da hidima..


Albarka ta sama Imran sannan tace ma Janan "tashi ga kayayya kin ki a cikin wardrobe an karbo daga dinki ki shirya mutane sun taru" tana gama fadan haka ta bar dakin ita kuma Janan ta shiga bayi ta watsa ruwa... A gurguje ta shirya bata wani bata lokaci ba wajen kwalliya dama batayi kwalli, powder sai lip balm kawai tashafa se dauri me kyau da datayi... Ba karamin kyau tayi ba.. Tana fitowo mutane suka fara fadin "Tubarakallah Ma shaa Allah"......




An ci ansha sannan anyi rabon souvenirs sosai tamkar ana biki haka Janan tayi ta canza kaya ana ta hotuna




Alhamdulillah taro ya tashi lfya gwanin ban sha'awa ga tarin gifts da mutane keta kawowa harda sisters din Imran sun zo da nasu kyaututtukan se yaba Janan suke farat daya ta shiga ran su....


Bayan Sallan Magrib Janan da Ummiey zaune a parlor wani yaro yayi sallama suka amsa.. Wata karamar jan jaka ya miqa ma Janan tare da fadin "gashi wai in kawo miki inji wani a waje"


"Wani a waje kuma?? Janan ta fada cike da mamaki..


Yaron yace "eh a mota yazo yana bani kuma ya wuce"


Ummiey tace "ko dai Imran ne? Ki kira shi kiji"


Tana kokarin kiran shi se ga kiran nashi ya shigo "bayan sun gaisa se take mishi godia da hidima....


Yace "haba Angel ki dena gode min.. Naso in zo se kuma aiki ya rike ni tunda na bar wajen ki ina asibiti har yanzu ban dawo gida ba ma"


Shiru tayi hakan ya tabbatar mata ba shi bane ya kawo mata sako yanzu.. Katseta yayi daga shirun "Angel zan kiraki anjima I love u".. Dinggg ya katse wayar...


"Ummiey bashi ya aiko da sakon ba"


Ummiey tace "Tor bude ki ga mene ne a ciki"


Envelop ta gani tana bude wa taga bandir din 500 ( dubu Hamsin) abun ya bata mamaki gashi bata san wanda ya aiko mata da shi ba.. Tashi tayi zata miqa ma Ummiey kudin wani farin soft tissue paper ya fado kasa.. Dauka tayi anyi rubutu da bakin biro yayi kyau sosai kamar anyi typing da computer..


Ga abun da aka rubuta kamar haka.....










*_Rukky Bae_*😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β£β£β£β£β£β£β£πŸ”±βšœβ£β€πŸ”±βšœπŸ”±β€β€β€β€ *MATAR DOCTOR* β€β£β£β€β€β£β£β£β£β€β€β€β€β£β€πŸ”±






_*RukkyBae*_😏😏




_Bismillahirrahmanirraheem_


_Yabo da godia sun tabbata ga Ubangijin halittu baki daya_!




Da farko dai karfin in cigaba da rubuta wannan littafi mai farin jini se na fara da baku hakuri Masoyana kuma mabiya wannan littafi! Dalilin Jina shiru ya faru ne sakamakon sace min wayar da aka yi a makaranta.. Nasan cewa kun jini shiru na lokaci mai tsawo wanda har wasu sun fara tunanin ko na daina rubuta *MATAR DOCTOR* ne wasu kuma suka dinga fadin wai basira ce ta kare min shiyasa na kasa cigaba da rubutun☺☺... Wannan shine farkon novel din dana fara rubutawa kuma Bayan shi akwai wanda da izinin Allah zan rubuta wanda nake kyautata zaton se yafi nishadantar daku fiye da *MATAR DOCTOR*! In shaa Allah....


Ina so ku kara min hakuri akan yanda kuke min tun baya kuma ku cigaba da bani kwarin gwiwa tare da tayani da addu'a..
Ina godia a gare ku mai tarin yawa kuma ku sani RukkyBae na son ku fiye da yanda kuke sonaβ£πŸ’‹ Naga Kiran ku da sakonnin ku masu tarin yawa. Allah ya bar zumunci ya bar mu tare....




Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan.....


Shin ko waye wannan saurayi ko ince mutumin??




_*CONTINUATION*_
(CIGABA)




*** 8⃣9⃣****






Wannan page din naku ne Masoyana πŸ˜„β£β€πŸ˜˜πŸ˜πŸ’‹






A hankali ta karasa gaban motar sannan tayi sallama.. Cikin hanzari ya dago suka hada ido, Dr. Godwin ta gani da sauri taja baya tana runtse ido, bude motar yayi ya fito hade da sanya hannayen sa biyu cikin aljihun wandon shi yana kare mata kallo kafin yace


"Monster kika gani ne da kika wani tsorata? Ko kuma nayi kama da dodo ne? A tare ya jero mata waennan tambayoyin.


Maimakon ta bashi amsa se ta jefa mishi tata tambayar da fadin "Kai ka aika min da sako?


Harara ya watsa mata sannan yace "amma dai kin san na tsani inyi tambaya instead of a bani amsa se a sake min wata tambayar ko?
Yi tayi kamar bata ji shi ba, jin shirun yayi yawa ya sake fadin


"anyway congrats kuma ba don halinki nazo ba kawai naga dama ne"


Murmushin takaici tayi tana mamakin girman kai irin nashi kafin ta miqa mishi envelope din tace "gashi bana so ka barshi" ta ajiye a saman motan ta juya zata daga kafa kenan ya take bayan takalmin ta tayi gaba zata fadi yayi saurin riqe gefen hijjab dinta, da sauri ta qabe mishi hannu cike da masifa tace


"miye haka kuma?
Gira daya ya daga yace
"ban sani ba, ni bana kyauta a dawo min dashi in karba sbd haka zoki dauka in kinga dama ki sa a dustbin I don't care amma baki isa in amsa ba kuma naji ana fada a addinin ku ba a maida hannun kyauta baya so yanzu the decision is urs in kinga zaki karba oho in ma bazaki amsa ba duk ke kika jiyo stubborn girl"


Komawa tayi ta dauka ta murguda mishi baki tace kasakasa "se iyayin tsiya ko ana kyauta dole ne ban sani ba kuma bani bace stubborn girl"


"me kike cewa? Ya tambayeta


Tace "ban ce komai ba",
ya jita sarai amma so yake ta sake maimatawa


"yaushe zaki dawo asibiti? Ya sake tambayanta


"Upper week" ta bashi amsa


"Baki isa ba goben nan zaki dawo aiki kuma it's a command"


Wani kallon uku saura kwata tayi mishi,


"hope ba dani kike ba''


"'Da kai nake yi kuma ba zan zo goben ba"


"Ni kike fada ma haka


Batayi zaton yaji mai tace ba
Ai da gudu tayi kofar gida seda taga tasa kafa daya a ciki hannu daya a kugu daya a jikin side na gate din sannan ta juyo ta murguda baki tace "Yes!


Cikin zafin nama ya biyota ta juya zata shige ciki warwaron ta mai chain ya maqale a jikin gate din ba shiri ta dawo baya tana kokarin cirewa amma ta kasa gashi ya matse mata hannu kuma ga Dr. Godwin ya nufota ta san in ya kamata ta gama yawo, a hankali ya cigaba da matsowa tun kafin ya karaso ta fara bashi hakuri, abun yaso bashi daria amma ya dake, hannun rigarshi ya fara nadewa kamar mai shirin dambe, tana ganin haka ta rufe ido tana jiran saukan mari, ji tayi kamar ana hura mata iska a hannu da sauri ta bude ido akan hannun nata, Dr. Godwin ta gani ya sa bakin shi yana kokarin cire mata ya kusa minti daya yana kokarin cire mata yana gama cirewa maimakon ya dago sai ya manna mata peck a hannu tare da cizon ta da sauri ta cire hannun tana yarfewa be gama dagowa ba tace
"ban gode ba"
ta shige gida da sauri ko waigowa bata sake yi ba, girgiza kai yayi yana daria ya koma ya tada mota amma be dena daria ba yana tuno yanayin ta da yanda take murguda baki komai tayi burge shi take yi a haka har ya kai gida cikin farin ciki da kewar Janan yana tuno hannun ta me laushi.....


Tana shiga gida seda ta dan tsaya ta kalli hannun ta ga shaidan hakoran san a jiki dan guntun tsaki taja tace mugu sannan ta shiga parlor ta fadama Ummiey Dr. Godwin ne ya bata a matsayin gift! Murmushi Ummiey tayi hade da godia tana fadin "ai kudin sunyi yawa"


Janan ta ce wallahi nima da kyar na karba gashi ki ajiye a wajen ki babu abunda zan yi da su"
Aa ki rike a wajen ki ko da abunda za kiyi dasu koda a asibiti ne ki taimakawa gajiyayyu


Toh Ummiey tace sannan tayi hanyar dakin ta har ta kusa shiga Ummiey tace yaushe yace ki koma bakin aiki?
"'Wai gobe" ta ba ta amsa


"Haba dai gobe ai ya kamata ki dan huta gajia kafin ki koma"


A tou ai ba inda zani tayi shigawar daki....










*_RukkyBae_*😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❣❣❀❣❀❣❀❣❀❣❀❣❣❀❣❀❣❀ *MATAR DOCTOR*πŸ–€β™£β™ β™₯♠♣β™₯♠♣β™₯β™ β™₯♣β™₯β™ β™₯♣♠β™₯♣






Rukkybae😏😏😏




This page is urs my CUPCAKE .. Ina sonki fiye da yanda nake son kaina cuz ke ce Best Frnd dina kuma abokiyar shawarata.. Muna fada amma ba wanda ya isa ya shiga tsakanin mu.. I can't imagine life without u Safiyya Zubairu Aliyu (Sophie_Luv) I love you more than chocolate Big Sisβ™₯πŸ’‹ my partner in Gulma πŸ˜‚πŸ€£








***9⃣0⃣***






Tunda Janan ta shiga daki tayi sallah ta watsa ruwa zata kwanta kenan sega kiran Imran ya shigo sun dade suna waya daga bisani sukayi sallama ba don sun gaji ba se dan ya bar ta tayi bacci...






Washe Gari tunda ta koma bacci da asuba ba ita ta tashi ba se karfe 10 na safe shima ringing din wayar ta ta tashe ta, ta janyo cikin bacci ido rufe ta dauka sallama bisa tsarinta tayi tana da fadin waye pls a dan shagwabe
Jin muryar baccin ta da kuma yar shagwaban ta ya sa shi ajiyar zucia yana fadin ohh wato bacci ma kike yi kin ma manta nace yau ki dawo wajen aiki ko?
Nan take idon ta ya wartsake ta yaye bargon jikin ta tare da duro da duk kafafunta kasa tana sake murza idanuwa cikin jin haushi yace "how dare u ina miki magana kinyi shiru kuma kina Jina!
Sorry tace irin na ko a jiki na din nan, mitchwww yaja tsaki "oya ki shirya yanzu ki taho,
kamar za tayi kuka tace "ka bar in dan huta Allah yau bazan iya zuwa ba cuz am extremely tired kuma jiki na is weak ko nazo nasan ba zan iya aikin komai ba help me plss! Yanda tayi maganan ta kashe mishi jiki amma se ya basar yace "point of correction Miss whatever u call ur self I don't help kuma bazan taba taimako ba"
Kayi hakuri naji bazan sake neman taimakon ka ba amma ka bari ko da nan da 4 days ne se in dawo"
What! Are u insane? Ni kike ba ma command? Kuma da kike cewa in baki 4 days idan supervisors suka zo daga Ministry of Health me kike so in fada musu? Kin san dai bana taimako kuma bana karya sbd haka daga kanki bazan fara ba, na baki nan da 2hrs ki taho asibiti!
Be jira amsarta ba ya kashe wayan shi,
Cikin ranta tace masifaffen Likita kawai wallahi ba inda zani se gobe in Allah ya kaimu in kaga dama ka tsire ni karshen hukunci kenan....


Bayi ta shiga tayi wanka ta wanke bakin ta sannan ta fito ta sa fitted gown na atamfa tayi kyau kayan sun mata kyau. Palor ta fito taga duk kowa ya tashi har sunyi brkfst ita kadai ya rage, se da ta gaida kowa sannan ta wuce kitchen ta zubo pankasau da kunun gyada ta dawo ta fara ci seda ta koshi sannan ta maida kayan kitchen ta wanko hannu ta dawo ta zauna aka cigaba da hira inda yan Makarfi suka ce gobe da rana za su tafi su kuma yan Gombe suka ce suma gobe zasu tafi amma da bayan sallan asubahi sbd garin nasu da nisa...


Seda aka kara gyara gidan sannan kowa ya samu natsuwa..
Da yamma Imran ya kirata yace ze zo bayan sallan Isha'i ya gaida baki kafin su tafi, toh kawai tace amma bata san yanda zata fada musu ba, dabara ce ta fado mata ta tura ma Ummiey text, Ummiey na gani tayi murmushi sannan ta fada musu surukin su zai zo gaishe su.


Kamar yanda yayi alkwari se gashi yazo Khaleel ne ya shigo dashi sbd Janan tace ba zata iya ba.
Cikin ladabi ya gaishe su nanfa daki ya kacame da gaishe gaishe aka cika gaban shi da kayan ciye ciye da shayeshaye ya dan ci ko ba laifi kuma ya saki jiki an dan taba hira da zai tafi ya ajiye musu kudi tare da yi musu Allah ya kiyaye hanya.. Haka ya tafi ba tare da yaga Angel din tashi se dai a waya suka yi magana.


Washe Gari ba da wuri ta tafi asibiti ba sbd Imran dinta yace ta jira shi yau shi da kanshi zai kai ta, se wajajen 8:30am yazo ta fada ma Ummiey kafin ta wuce ta same shi sanye da half jampa kalar coffee brown haka hula da takalmin shi duk kalar coffee brown din ce yayi kyau sosai.. Janan na ganin shi ta saki murmushi sbd Imran jarumin namiji ne ga nagarta da kamala seda ta gaishe shi ya amsa sannan ya bude mata gaban mota seda ta zauna ya rufe kafin shima ya koma mazaunin sa ya shiga suka fara tafiya tace "My King kayi kyau sosai" Murmushi yayi yace Angel kin fini yin kyau kayan asibitin nan kamar dan ke ake yi su kuma banda abin ki namiji ai bashi da wani kyau mata ne aka sani masu kyau.
Haka dai ka fada amma akwaio kyawawa a maza kuma kaima kana cikin su domin kai cikakken Namiji ne kuma daya tamkar da dubu. Yaji dadi sosai kuma ya kara tabbatar daya samu mace ta gari, haka sukayi ta hira har ya kaita kofan asibiti yace Angel yau karki sai komai zan kawo miki lunch kinji,
"Haba Mijina kar... Shhhh ya katseta bana son jin komai kuma fa kin kira ni da Mijin ki karki manta hakkin miji ne ya ciyar da matar shi sbd haka bana son kice komai.. Shikenan Nurulqalb nagode, kallon ta yayi da wani irin salo sannan yace ni ba godia nake so ba
Toh me kake so? Ta tambaye shi
Kin fini sanin abunda nake so, hannun biyu ta rufe fuska dasu sannan tace Ina son ka
Daria yayi yace nima Ina son ki amma wannan kunyar ya kamata ace kin rage shi ko sai munyi aure tukunna zaki de ne? Da sauri ta wuce tana daria ba tare data bashi amsa ba se dai ta dago mishi hanni..
Ina sonki Angel ya fada a hankali tukunna yaja motar shi ya wuce


Tun tsayuwar su Dr. Godwin na kallon su ta saman window ji yake zuciyar shi na wani irin daci kamar ya sauka yaje ya janyo ta ganin yanda take ma wani murmushi be ga wucewar ta ba sbd ya lula duniyar tunani se ji yayi kamar mutum ya bude kofa yana juyowa daidai ta rufe kofar ta juyo suka hada wani kallo yayi mata wanda ita ma bata san nufin shi ba.. Kamar ba za tayi magana ba a hankali tace "Morning! Be kulata ba har ta gaji da tsayuwa taje tayi zaman ta..


Kallon ta kawai yake yi kan shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login