Showing 36001 words to 39000 words out of 82682 words
shiga dake theatre room zaki haihu ana bukatan kudi.. Be tambayeni nawa bane yace in shigo mota muje... Wani super market muka je ya siyo min waenan kayan dana kawo miki.. Har bakin gate din asibitin nan ya ajiye ni sannan ya bude brief case dinshi ya ciro 100k wai inyi manaji sbd babu kudi dayawa a hannun shi kuma in ina bukatar wani abu in kira shi...
Kinji yanda akayi na samu kudin.. seda na shigo asibitin sannan naga waya ta babu chargy"
Hamdala tayi tare da kara gode ma Allah sannan tayi ma Muhammad addua'a.. Amma bata ce komai ba akan Kawu..
Janan ce ta katse su da fadin "bari ayi alluran sbd ki samu bacci" bata jira komai ba ta mata.. Mituna kadan bacci ya dauke ta.. Mutumin da Janan suka fito yana ta mata godia.. kudi ya dakko ya bata wa na abubuwan data siya amma taki karba sbd ita duk sun bata tausayi kuma sun fita bukata sannan ita Dan Allah tayi musu badan su biyata ba..
Seda yaje yaga yaran shi yayi musu huduba da addua'a sannan suka tafi Office din Dr.Godwin yayi mishi godia ya fita ita kuma Janan ta zauna har time din tashi yayi Dr Godwin bace komai ba ta dau jakarta ta fita be hana ta ba....
❤❣❣❣❣❤❣❣
_ina so inyi anfani da wannan daman wajen ba dukkanin masoya na hakuri na rashin jina kwana biyu wannan ya faru ne sakamakon rashin samun lokacin da banyi_ _Makaranta yasha kaina_ _amma in shaa Allah zaku dinga jina a duk sanda na samu chance_
_ina sanku fiye da yanda kuke so na_😘😘😍
_Pls ku sani cikin addua'an ku_
*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [1/29, 11:58 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❤❣: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣⚜❤⚜❤⚜❣⚜
_Wannan page din na sadukar dashi ga dukkan masoya na ina son ku fiye da tunanin ku_😘😍😍
*_Rukky Bae_*😏😏😏
8⃣6⃣
_2 days later_
Yau ya kama Friday bayan Janan ta dawo daga asibiti Dr.Imran ya kirata yake sanar da ita ranan Lahadi magabatan shi zasu zo ayi maganan aure sbd haka ta fada ma su Ummiey... Cike da mamaki da jin kunya tace "Nurul-qalbee Allah ina jin kunya bazan iya fada mu su ba"
"Haba Angel wa kike so ya fada mu su tor?
"Ka fada ma Big Bro ko ka fada ma Bro Saleem plsss"
"Tor shikenan tunda haka kike so in mun gama waya zan kira Khaleel din in fada mishi"
Hira sosai suka yi kafin yayi hanging call din sannan ya kira Khaleel sun gaisa sosai tare da barkwanci irin na abokai nan yake shaida masa abunda ya fada ma Janan..
Farincin ciki sosai yayi da Janan zata samu miji kaman Imran...
Yana dawowa gida ya sanar da Ummiey ita kuma ta fada wa Abbiey....
A ranan Abbiey ya kira ya fada ma dangin shi na Makarfi sannan ya fada ma yan uwan Ummiey dake Gombe kowa se fatan alkhairi da sa albarka yake...
_Sunday_
Tun asuba Ummiey da dangi suke aikin tarban baki sosai suka gyara gidan se kamshin turaren wuta yake hade da kamshin girke girke kala kala...
Janan na tashi tayi wanka ta dau hijab da jakanta tayi ma Ummiey Sallama ta tafi gidan su Zee sbd bazata iya zama a gidan ba..
Karfe 2 daidai Baban Imran da yan uwa da abokanan arziqi suka zo gidan su Janan.. A parlor'n baki aka musu mausaki... Bayan adduo'i da gaisuwa suka gabatar da abunda ya kawo su aka tattauna suka tsaida lokacin aure nan da watanni shida masu zuwa suka bada komai da ake bukata harda sadaki aka rufe taro da addua'a suka ci suka sha kowa ya tafi yana san barka da yaba hali irin ta zuri'ar su Janan
Su kansu yan gidan su Janan din sun yaba da kokari tare da halin dattako irin na zuri'ar su Imran..
Se yamma Janan ta dawo gida cike da jin kunya.. Tana shigo yan uwa suka fara mata barka da zuwa suna tayata farin ciki se fadi suke "Allah ya sa Albarka Amaryar wata 6 masu zuwa"
Da gudu ta wuce dakin ta harda sa key ta zauna a tsakiyan gado tana maida nunfashi amma can kasar zuciar ta wani farin ciki ne mara misaltuwa....
Sallan Magrib tayi bata tashi daga kan sallayar ba ta cigaba da Dhikiri tana jira a kira sallan Isha'i ta gabatar...
Ummiey ce ta shigo dauke da food flask da plate a hunnun ta ta ajiye mata a kan stool na dakin tace "ga abincin ki na san yau bazaki sake fitowa ba sbd kunya karki mata ki kwanta da wuri gobe Monday karki makara...seda safe"
tana gama fadar haka ta juya ta bar dakin...
Janan na idar da sallah ta ci abincin ta sannan ta wuce bayi tayi wanka tasa kayan bacci tana hawa gado wayarta ta fara ringing murmushi tayi amma ji take kamar kar ta dauka sbd shi kanshi Imran din yau wani irin kunyar shi take ji da kyar dai ta dage ta daga tare da sallama cikin siririyar muryarta... Cike da zumudi da farin ciki Imran ya amsa tare da fadin "My Angel, my Amarya ykk? Ya gida? Ya komai da kowa? Ya aiki? Ya...
Janan cikin daria tace "ya..ya din ya isa haka mana yau gaisuwar naga har wani sabon ta ta akayi tor komai da kowa lfya lau Alhamdulillah"
Imran yace "torh Mata's nayi shiru haka amma gaskiya yau ina ciki farin ciki mara misaltuwa"
"Ohhh har na zama Matar taka kenan?
"ai ni gani nake tamkar kin zama mallaki na har na kosa lokacin yazo a kawo min ke daki na.. Ranan ban san wani irin farin ciki zanyi ba"
"Hmmm Nurul-qalbee kenan inda rai da lfya wata 8 kamar gobe ne ai"
Cikin sauri ya katse ta da fadin "a haba Malama ki dena kara min lokaci wata 6 ne ni inda so samu ne a maida shi wata 3 bari inje in samu Daddy in fada mishi gaskiya a matso da bikin ko in ce ke kika ce a dawo dashi wata 3"
Cikin zaro ido tace "haba Nurul-qalbee yaushe na fadi haka pls karka fada kafin ace bani da kunya"
"Tor naji na daina amma duk sanda kika kara cewa wata 8 tor sena fada kin ce a dawo dashi wata 3"
Seda dare yadan fara sannan yayi musu addua'a suka shafa...
Yace "ki kwanta se kinyi bacci zan kashe"
Batayi musu ba ta kwanta seda yaji alaman numfashin ta na sauka a hankali sannan yace "ki kwana lfya Angel Allah ya kare min ke daga sharrin shedan"
Bata amsa ba sbd baccin ta yayi nisa....
*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [2/3, 11:03 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❤❣: [2/3, 7:40 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❤❣: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❤⚜❣⚜❤⚜❤⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣
_in remembrance of our lovely sist *Khadeeja Zubairu Aliyu*_.. _We love u but Allah loves u more_...... _it's been long u left us but we can never erase u in our memories_
_May Allah 4gv u nd may u be among the dwellers of Jannatul Firdaus_.... _Ameen_
_Allah says in d Holy Qur'an_: *_Every soul shall taste death_* *Qur'an 3 verse 185*
_we all r waiting 4 our time_
_Ya Rabb!! 4gv us all nd take away our souls whenever u r happy with us_
*_Rukky Bae_*😏😏😏
8⃣7⃣
_Monday_
Da wurwuri Janan ta shirya ta wuce asibiti sbd bata so Dr.Godwin ya riga ta ko ya fara tsareta da sleepy eyes din shi.. Cikin kankanin lokaci ta shigo asibitin ta ko ci sa'a ta riga duk yan officr din su zuwa amma abun haushi a rufe kofar take ko da tai ma masu kula da wajen magana se cewa sukayi "ai yanzu da key din office Dr.G yake tafia"
Cike da jin haushi ta zauna akan kujeran da patients suke zama.....
Yau Dr.Godwin cikin mulki da miskilanci ya shigo asibitin as usual yana sanye da suit da bakin glasses tunda ya shigo be cewa kowa komai har Janan dake zaune be kalle ta ba ganin haka ya sa ita ma taki gaida shi tayi kamar bata ganshi ba.. Ta cikin glasses dinshi ya kalleta a ran shi yace "wow! She looks so cute! Yau ta riga kowa zuwa abun is surprising ko dai dama da gangan take zuwa latti? Anyways, ita ta san dalilin zuwa da wuri yau"
Ya bude office din yayi shigewan shi ciki... Itama ta bi bayan shi...
Can daga baya su Ruth suka shigo a tare yau kayan aikin nasu da gani sabo suka dinka ya matse su ga kirjin su a waje fuska tasha heavy make-up sunyi fixing nails da eyelashes se yanga suke kamar baza su taka kasa ba... Table din Dr.Godwin suka nufa harda dan rankwafawa suna gaida shi kamar ance ya dago idon shi ya ajiye a kansu cikin sauri ya cire glasses dinshi, Jessica harda wani kara jijjiga jiki duk a tunanin ta ganin daya musu ne ya sa shi cire glasses dan ya gansu da kyau.... Cikin tsawa yace "what d hell is this? R u girls insane? Wani irin dressing ne haka? Zaku zo asibiti nd u r dressing shabbily? Party zaku je ko club? Ku kalli kan ku! U r looking so disgusting! Daga yau in kuka kara dressing haka u will see d other side of me" ya buga tsaki "mitchwwwww will u get out of my sight u bunch of idiots?
Jiki na rawa suka koma wajen zaman su duk sun razana da yanda yayi musu..
Janan na daga gefe se faman daria kasa kasa take yi a ranta tace "daidan ku kenan"
Cike da bacin rai Dr.Godwin ya mike idon shi sun kada sunyi jazir ya bar office din don yau su Ruth sun kai shi bango
Seda yayi kusan minti 30 sannan ya dawo cikin office din yana chewing gum yana zama wani cardiologist (likitan zucia) Dr.Bichi ya shigo da sauri yace "Surgeon G pls muna neman taimakon ka an kawo mana patient yanzu tana emergency room kuma akwai bukatan yi mata operation... Cikin azama Dr.Godwin ya miqe tare da fadin bani secs 10 in canza kaya na... Inner room na office din ya shiga ciki seconds 15 se gashi sanye da kayan aiki yace "muje ko?
Dr.Bichi yace "we need a nurse wacce zata taimaka mana".. Da sauri Ruth da Jessica suka tashi wani kallo Dr.Godwin ya watsa musu yace "ko a mafarki kar kuyi zaton zaku bi ni theater room da wannan kayan, ku zauna kuyi gadin office dama shine daidai daku....
Ke!! Ki biyo ni in kin ga dama" yana gama fadan haka ya fita abin shi
Dr.Bichi yace ma Janan "muje time yana wuce wa"
Ba dan taso ba ta bisu dan ke! din da Dr.Godwin yace mata ya bata haushi...
Emergency room suka nufa nan taga baby Hanayya ce jini na fita ta baki da hanci Dr.Godwin na kanta yana yan gwaje gwaje suna shigo yace "mu wuce theater room yanzu yanzu"
Sallati kawai Janan keyi nan da nan idon ta ya ciko da kwalla tausayin yarinyar ya kamata.... Suna shiga dakin theatre suka fara aikin su Janan haka ta dinga yi kamar kwai ya fashe mata a ciki.. Duk abun da take yi idon Dr.Godwin na kanta se yaga sun kusa hada ido ze kawar da kai gefe...
Sun dau awa har 4 cikin dakin theatre kafin suka fito duk sun jike da zufa cikin sauri iyayen suka yo kan su suna tambayan jikin yarinyar su... Be ce musu komai ba ya wuce zuwa office din shi Janan na binshi a baya suna jerowa tare da Maman Hanayya...
Suna shiga suka zazzauna ya fara musu bayani kamar haka "abunda ke damun ta shine dai ciwon zucian dana fada muku gwaje gwaje ya nuna cewa bugun zuciar ta is nt normal yana bugawa fiye da yanda ya kamata sakamakon haka se ya haifar mata da taruwan jini a cikin zuciar domin jinin baya circulating ya daskare waje daya har ya kumbura zuciar sannan jinin daya rasa hanyar wuce wa se ya tunkudo mata ta baki da hanci amma yanzu an gama operation lfya sedai mu jira ta farfado muga yanda jikin yake"
Ajiyan zucia suka sauke duk tausayin Hanayya ya kama su...
Bayan awa hudu ta farfado Alhamdulillah sedai bazata ci komai ba sbd ana mata karin ruwa da jini se sun kare tukunna......
*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [2/5, 8:51 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❤❣: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜ *_MATAR DOCTOR_*⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜
_Dedicated this page to my one nd only Bro. Even though u will nt read this novel but u deserve a dedication from me. U r more than a Brother to me u r part of my life_
_I love u so much_ *_Abdurrasheed Zubairu Aliyu_*
_# MY STRAWBERRY_# a special name 4 u❤❣❤
*_Rukky Bae_*😏😏😏
8⃣8⃣
_Bayan wata 1 da sati 3_
Haka asibitin Barau Dikko ya zama talk of d town domin aiki tukuru akeyi a cikin sa gashi likitoci da Nurses sun san aikin su yanzu Janan ta dena kuka in za ayi ma mutum operation sedai har yanzu in taga za ayi se tausayi ya kamata..
Dr.Godwin yayi kaurin suna domin kusan ko ina an san _'Surgeon G' d youngest must chamming nd active Doctor_...
*************
Shirye shirye ya kan kama sbd saukan su Janan ya matso saura sati daya.. Sun raba kati ma Nurses waenda suke mutunci har da Dr.Magaji basu mance da shi ba sun kai ma.. Amma Janan ta hana Dr.Godwin katin dan a ganin ta babu anfanin bashi...
Cikin lokacin nan aka sallami patients din da aka ma operation domin jikin su yayi kyau sosai.. Kuma Maman Hanayya tayi alkwarin zuwa wajen daukan Janan
Ana gobe sauka su Janan suka karbo kayan su gun tela ita da Eesher sun yi kitso se kuma jan lalle da aka masu se yamma likis suka dawo Eesher ta wuce gidan su..
Yan uwan Ummiey na Gombe har sun zazzo maza da mata se kuma dangin Abbiey na Makarfi suma haka zuka ciko mota suka zo se aiki ake yi ...
Washe gari tun asuba ta tashi ta fara shi ga wani nishadi da farin ciki daya ke ratsa duk jikin ta ko abinci ta kasa ci sbd doki kayan saukan su fari kal tasa tana sa socks wayar ta ta fara ringing ko bata duba ba tasan Imran ne bayan sun gaisa yake mata fatan alkhairi da kuma addua'a basu dade suna waya ba suka yi sallama sbd kar ta makara.. Tana ajiye wayar taji alaman sako ya shigo kamar kar ta duba se kuma ta dau wayar ta zauna bakin gado tare da bude msg din.. Ga abinda sakon ya kunsa
*_Congratulations on ur graduation.. I wish u all d best Baby girl_*
Ta karanta text din yafi so a kirga tana mamakin wanda ya turo mata wannan sakon harda ce mata Baby girl ko dai mistake ne ta fada a ranta ganin tunani ba zai mata anfani ba ya sa ta tashi ta karasa shirin ta.....
***********
Daya bayan daya aka kira su suka fara karatu wajen a cike yake da jama'a maza da mata Aisha na cikin yan farko da suka fara karatu can daga baya aka kira Janan Pharouk Makarfi kowa yayi shiru nan ta fara karatu da muryan ta me zaqin gaske cikin suratul Bakrah shafin karshe cikin qira'ar Sheikh Sudais.. Yanda take karatun ya sanyaya zukatan masu sauraro dayawa seda suka zubda hawaye domin dadin karatun ta ita kanta karfin hali take yi amma ji take kamar ta fashe da kuka.. Tana kaiwa karshe wajen ya kaure da kabbara...
Seda aka gama da yan sanawiyya sannan aka dawo kan mahaddata nan fa aka kowa ya fito yayi nashi karatu Janan aka sake kira ta fito tayi karatu cikin suratul Ahzab da sautin Sheikh Shureim nan fa ta nuna kwarewar ta domin tana son kira'ar kuma ta iya sosai...
An basu kyaututtuka da yawa domin Janan ta karbi kyauta kusan guda 5 ciki harda wacce tafi kowa ladabi da kuma tsafta... Sunyi hotuna sosai se faman kukan rabuwa suke da juna... Dr.Magaji da iyalin shi sun zo harda kyauta suka ma Eesher da Janan.. Mmn Hanayya ma tazo kuma ta fada ma Janan har gida zata biya se yamma Baban Hanayya ze zo ya dauke su
Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan.....
Shin ko waye wannan saurayi ko ince mutumin??
_Godia da jin jina gare ku masoya na ngd da adduo'in ku Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci_
_Allah ya biya muku bukatun ku na alkhairi_
_Sai kun sake jina_😉😉
*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [3/4, 4:10 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❤❣: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤❣⚜❤ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣⚜❤⚜❣⚜❣⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣
*_Few days to my birthday in shaa Allah_*💃👯♂👯♂👯💃👯👯💃💃
*_Rukky Bae_*😏😏😏
_Dedicated this page to My pretty nd Maman Abulkhyry_😘😘
_Thanks 4 ur support_
8⃣9⃣
Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan....
A hankali ta fara takawa zuwa gaban motar gab da zata karasa taji daga baya ance "Angel ina zaki je?
Da sauri ta waigo don jin an kirata da Angel... Imran ta gani a tsaye sanye da sky blue caftan.. Murmushi tayi mashi tace "Nurul-qalbee ashe kazo.. Ban ganka ba se yanzu"
Yace "Haba ni na isa in zo yanzu? Saukan Angel guda! Tun kafin ayi nisa da karatu nazo sbd kar nai missing karatun ki"
Murmushi tayi seda fararen hakoranta suka bayyana..
Mai daukan hoto ne yazo wuce wa, da sauri Imran ya kira shi yace "zo ka dauke mu nida Angel dina"
Karasowa yayi ya dinga daukan su hotuna kala kala
Tari Janan ta fara yi sbd kuran da yake tashi wajen duk ya kaure da kura.. Hango motar nan suka yi tayi nisa wanda ke ciki se gudu yake kamar ze tashi sama duk ya