Showing 27001 words to 30000 words out of 82682 words

Chapter 10 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4340

shirya tana dawowa parlor taga duk basu fito karya wa ba a gurguje ta dan tsakuri dankalin sbd bata da appetite ta dau jakar ta zata fita kenan Ummiey ta fito tace "har kin shirya ne 'yar albarka"
Janan tace "eh Ummiey bana so in kara yin latti ne ga breakfast nan na hada muku se na dawo"
Ummiey tace naji kamar muryarki ta canza ko mura kike yi ne?
"Eh Ummiey ruwan daya dake ni jiya ne amma ga ruwan shayi nan zan tafi dashi asibiti"
"Torm Allah ya tsare a dawo lfya"
Da sauri ta fita karfe 7 daidai me napep ya sauke ta a bakin asibitin tana shiga Dr.Godwin ya shigo da motar shi yi tayi kamar bata ganshi ba tayi wuce warta yana kallo ta kauda kai parking lot ya nufa inda aka tanadarwa likitoci ya ajiye motar sannan ya fito yana sanye da riga me gajeren hannu na versace da black pencil trousers da bakin hightop shoes ba karamin kyau yayi ba da sauri ya dau brief case dinshi yabi bayan ta duk saurin ta seda ya kamota daidai wajen hawa steps yace "kina ta sauri gashi na kamoki kuma idan kika bari na riga ki shiga office yau ma latti zaki tafi gida" ya kashe mata ido daya
Zata yi magana kenan wani atishawa me karfi yazo mata harda guntun hawaye... ta bashi tausayi amma ya basar yace "karki sa mun mura kin san dai communicable disease ne koh?
Baki ta murguda mishi sanna tayi saurin wuce wa..
Murmushi yayi yace "ji dan bakin har ta iya murguda shi" da sauri da sauri ya hau steps din daga nesa ya hangota ta tsaye tana magana da wasu mutane guda biyu da alama kwatance take musu kara sauri yayi ya raba ta dayan gefen ya wuce batama lura dashi ba tana gama musu kwatance kawai ta hangi Dr.Godwin har ya shige salati tayi dan ta san dole se ya aikata abun da yace... jiki a salube ta bude kofar ta shiga kanta a kasa a hankali ta karasa wajen shi tace "Good morning"
Yace "se yanzu kika ganni da zaki gaishe ni? Torm hv a seat dan yau keda tafiya se 7pm kuma ko kin riqo ni bazan yi changing mind dina ba"
wani irin zaro ido tayi hade da toshe bakin ta ji take kamar ta fashe da kuka amma a ranta tace "wallahi bazan roke ka ba in ya gaji dole ka barni in tafi kuma nasan abin da zan maka" da wannan tunanin ta samu guri ta zauna... messenger na shigowa Dr.Godwin yace "yau patients 4 kawai zan duba sbd zan shiga theater room karfe 9......
yana cikin duba patient din farko Ruth da Jessica suka shigo tare da gaishe shi ko kallon su be yi ba bare ya amsa musu.. Janan ta kawo iya wuya wato ita ya raina su da suka zo latti be ce musu komai ba tana dagowa suka hada ido da shi kasa tayi da idon ta hade da hararan shi yanda ba zai gani bah..
ya duba mutane uku saura na karshe.. mata da miji ne suka shigo tare da yarinyar da bazata fi 5yrs ba tunda Janan taga yarinyar taji ta shiga ranta se kallon ta take yi a ranta tace "very cute baby" itama yarinyar tunda suka shigo take kallon Janan gani kawai suka yi ta kwace hannun ta tafi wajen Janan da gudu kallon juna sukayi ita da mijin ta sannan suka karasa wajen Dr.Godwin.. wajen zama ya nuna musu suka zauna sannan suka fara mishi bayani kamar haka "yarinyar mu kullum tana complain cewa kirjin ta yana ciwo jiya daya tashin mata se take nuna mana daidai setin zuciar ta mu kuma bamu san me hakan yake nufi ba shiyasa muka kawo ta nan"
Dr.Godwin ya kalli setin su Janan yaga se hira suke yi da yarinyar yana kallo Janan na barewa yarinyar chocolate da kanshi ya tashi yaje wajen su hannun shi a aljihu yace "cutie zo muje"
Kafada ta maqe alaman bazata ba ganin ya miqo hannu ze dauke ta ta kankame Janan tana fadin "Anty kin gan shi ze dauke ni kuma allura ze min ni dai bazani ba"
Maman ta ce ta zo tace "Baby Hanayya kizo ba allura ze miki ba"
"No Mummy nidai bazan je ba"
Baban ta ma yace "babu abinda ze miki kuma in kika je zan saya miki chocolate kinji"
Yarinyar tace "aa Daddy nidai ina jin tsoro kuma gashi Anty ma ta bani chocolate" ganin taki yarda ne yasa Janan tace "my baby baki so in zama frnd dinki ko?
Tace "pls Anty ina"
"Torm in dai kina so in zama ki tashi Doctor ya duba ki kuma bazai miki allura ba in kuma yayi miki zan rama miki"
''Yawwa my Anty promise! Ta miko mata hannu alamar su kulla alkawari Janan ta miqa mata suka kulla sannan Janan ta riqe mata hannu suka karasa gaban gadon
Sosai Dr.Godwin ya duba ta yace ma Janan "ki kai ta dakin x-ray a duba ta kuma kiyi sauri cuz yanzu 20mins to 9... suna zuwa dakin x-ray akwai mutane wajen wata nurse ta nufa tayi mata bayani tunda urgent ne yasa nurse din ta ba mutanen hakuri akayiwa Hanayya.... basufi minti 10 ba aka gama komai suka koma office din Dr.Godwin suna zuwa ya duba result din sanna ya ce musu "yarinyar ku tana fama da cardiovascular disease"
Mijin ne yayi saurin cewa "Doctor pls kayi mana bayani yanda zamu fahimta bamu san me kake nufi ba"
Tunanin yanda zasu dauki abun yayi sannan ya nunfasa yace.......












*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/26, 6:42 AM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋: ❤⚜❣⚜❤⚜❤⚜❣⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❣⚜❣








*_Rukky Bae_*😏😏😏






*_Dedicated this page to all the group members of_*
🆑🅰 *_SSIC LADIES_*








7⃣6⃣








Dr.Godwin yace "abun da nake nufi da 'yar ku tana fama da cardiovascular disease shine tana fama da ciwon zucia"
A tare iyayen suka hada baki wajen cewa "ciwon zucia kuma Doctor! Innalillahi wainna ilaihirraji'un" ita kanta Janan abun ya girgiza ta sbd bata taba ji ance karamin yaro ko yarinya na ciwon zucia...
Ganin sun shiga rudani yasa Dr.Godwin cewa "cool down ba wani abun tada hankali bane domin shi ciwon zucia yana cikin jerin ciwukan da ake inheriting dinshi watakila wani a cikin family'n ku yana fama da same sickness amma in dai zaku kiyaye rules nd regulations tor komai ze dawo normal but in dai baku kiyaye ba dole ne se an mata operation domin bugun zuciar ta ya daidaita...
Baban yace "tor Doctor mene ne rules nd regulations din?
Dr.Godwin yace "firstly! a guji duk abun da ze bata mata rai sannan duk abun da take so a bata in kuma babu se ayi mata dabara tunda yarinyace a bata wani abun kuma ku lura da duk abun da take ci zan muku prescribing drugs kuje pharmacy ku siya ku tabbatar kun bi ka'idan magungunan ina tabbatar muku da cewa ur baby will be healthy kar kuyi skipping bata drugs din ko da once ne sbd in kuka tsallake za a iya samun matsala.... a nan ya sake basu appointment nan da 1 month su dawo a sake duba ta.........
Bayan ya gama musu bayani suka mishi godia sannan suka fito domin tafiya har a lokacin Baby Hanayya tana tare da Janan har bakin mota ta raka su da kyar da wayau Hanayya ta yarda ta shiga mota bayan Janan ta hada ta da chocolates masu yawa.... se da sukayi exchanging digit da Maman Hanayya sannan Janan ta daga musu hannu har suka wuce....


Tana komawa office din taga baya zaune a kujerar shi se su Jessica da suke ta lbr kasakasa ita da Ruth waje itama ta samu ta zauna se ga Dr.Godwin ya fito daga inner room na cikin office din sanye da kayan shiga theater yana gyara hand gloves dinshi.. gaba dayan su duk suka miqe suna shirin binshi theater room da sauri ya dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu kuma yayi haka ne sbd Janan dake fama da mura dan baya so ta wahala sannan baya so su Ruth su tayashi aiki domin rawan kansu yayi yawa.. ko waigowa be sake yi ba ya bar office din..
Janan taji dadin hakan jakarta ta bude ta dakko karamin flask dinta ta zuba ruwan tea tama su Jessica tayi suka ce basu sha a hankali take shan abunta su kuma su Ruth suna hira tana kammalawa ta dauki wayar ta ta fara buga game din _My Talking Tom_ a cikin hiran su Ruth ne taji sun sanyo maganan Dr.Godwin inda Jessica ke cewa "hmm Ruth kin san yanda nake son _young surgeon_ din nan? Ba karamin burge ni yake ba he is unique nd different ya iya daukan wanka kuma gashi so charming i luv his style kin san me yafi burge ni dashi? He is very neat ga class gashi baya san hayaniya he is jst d perfect Mr.right 4 me cuz he is damn handsome...
Wani irin harara Ruth ta watsa mata tace "hey! hey!! hey!! Hang it there Miss! Naji kina ta wani surutun banza ne ni yanda nake son shi kamar raina lokacin da aka ce min he is d must handsome guy a asibitin nan naji ya burge ni dana ji cewa he is d first _youngest general surgeon_ a hospital din nan tunda aka gina shi yasa na fara zuwa church ba dare ba rana in fara aiki as a nurse kuma tare dashi at last God answered my prayers na samu aiki...
The first day i set my eyes on him i knw d guy is damn hot kuma a lokacin naji am completely in love with him.. in kika lura bana barin kitson attachment dina ya wuce 2 weeks nake sake sabo nd always fixing my nails nd applying heavy makeups in banda abinki ai na fiki komai babu abinda ze yi dake kuma ni na fara son shi sbd haka u better take back ur words na cewa u love him badan ke frnd dita bace dana miki abunda bazaki manta dan kinyi kuskuren fada min cewa kina sonshi domin in dai am still alive bazan bari wata ta kwace mun shi ba cuz he is *Mine* mine alone!


Jessica ta tsaya kallon Ruth ta kasa cewa komai cuz she is totally speechless a ranta tana jinjina ma Ruth dan tasan in dai tana son abu to zata iya komai akan abun.... cike da sanyi gwiwa tace ma Ruth "kin san dai shi so ba kai kake sama kanka ba nd u won't knw when u r falling in se dai kawai kaga kana son mutum so don't try to force me akan abunda bazan iya ba kuma it might be possible ya soni cuz dukkan mu be ce yana son kowa a cikin mu ba we r all trying to win his heart!
Wani irin zafi maganan yayi ma Ruth ji take kamar ta rufe Jessica da duka amma se ta fara kwantar ma da kanta hankali ido ta rufe a ranta tana cewa "control Ruth control karkiyi misbehaving karki tsaya cacan baki kawai ki nuna mata action show her u can do it show her u can easily win his heart...hka tayi ta lallaba kanta a hankali ta bude ido ta kalli Jessica tace "gaskiyar ki ne yanzu mu bar wannan maganan kowa taje yayi trying luck din ta.........
Baki bude Janan ta tsaya kallon ikon Allah sbd taga haukan nasu yayi yawa no wonder in suka ganshi suke wani rawan jiki.. haushin su da taikaici ya kamata dan ta tsani taga mace tana ma namiji rawan kai ita bata ma ga wani abun burgewa a wajen Dr.Godwin ba ji tayi zaman office din ya gundure ta tana duba agogonta taga daya saura... jakarta ta dauka ta fita a office din ba tare data tankasu ba... daidai ta kusa karasawa kofar theater room Dr.Godwin ya fito yana share zufa da hanky.. kamar ance dago! kawai ya hango Janan ta kusa karasowa, jikin bango ya jingina yana jiranta... cikin tafiyar ta a hankali kanta a kasa ta zo zata gifta shi taji ance......










*_pls am sorry cuz zaku jini shiru na dan wani lokaci sbd fama da nake yi da ciwon ido amma In shaa Allah dana samu sauki zan cigaban muku da wannan littafin_*
*_ina barar addu'ar ku_*..... *_taku har kullum_*






*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/5, 12:34 AM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣⚜❤⚜❤⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜






*_Alhamdulillah am getting better nw... thank u guys 4 d prayers Jazakumullah bi khayr_* ❤❣❣❤❣❤❤❣




_Dedicated this page to_
_Khairat Dabai_
_Little Eesher_
_Fateema M.Sabo_
_nd ol d grp members of_
_GYARA SHINE MACE_






7⃣7⃣








Ji tayi ance "ina zaki je?
A razane ta juyo dan ta tsorata sbd batayi tunani akwai mutum ba.. ganin Dr.Godwin ne yasa ta dan bata rai sannan tace "lokacin salla yayi"
"Ohhh kin fito bada izini na ba koh? Dama kin san akwai laifi akan ki yanzu kin karama kanki wani... saura kije ki dade...
Bata bashi amsa ba ta juya har ta fara tafiya se ta tuna da suit din shi baya ta dawo ta ciro a jakar ta cikin wata farar leda me kyau ta miqa mishi amma bata ce komai ba se ma kau da kanta gefe da tayi ganin bata da niyyar magana yasa shima ya yi kamar be ganta ba se ma ciro wayar shi daya yi ya fara dannawa irin shima yayi banza da ita.... hannun ta ne ya fara sagewa jin be amsa ledar ba yasa ta juyo tana kallon shi gani tayi yana danna waya kamar be san tana wajen ba gashi ya hada rai kamar be taba daria ba.. cike da jin haushi tace "gashi mana"
Yi yayi kamar be ji ba se da ta kara magana yace "ohh dama ashe kina da baki?miye wannan"
"Suit dinka ne na jiya da baka amsa ba na dawo maka dashi"
"Ko dai kika tafi dashi kika hana ni hala kina so ne in bar miki ban sani ba tor tunda se yanzu kike kawo wa ki riqe na bar miki"
Tace a ranta "lallai ma guy din nan yace wani abu ita me ma zatayi da suit din"...
Ce mishi tayi "ni bana so cuz ba abun da zanyi dashi"
Yace "ohh! Kina fada mun indirectly wannan is too cheap 4 u tor karki damu zan zabo miki wanda yafi kowanne tsada in kawo miki though ni bana sa kaya me arha se dai designers me arha a ciki shine 50k" ya wani kashe mata ido daya...
Zata yi magana yayi sauri katsata ta hanyar daura yatsa akan leban shi yace "shhhhh say no more ki tafi kiyi salla kuma in kika fi 20mins ni da ke ne" be jira ta sake magana ba ya wuce abun shi...
Haushi ya kamata kamar ta pashe tana tafe tana mita a ranta "shi wannan guy din ban san meke damun shi ba komai se ya wani tsaya yana iyayi ni ina ruwana da tsadan kayan shi ya cika miskilanci a haka waencan marasa aikin yin suke wani sonshi har suke so suyi fada" mitchwwwww taja tsaki... haka ta kai wajen da aka kebe nayi salla tayi alwala ta shiga seda tayi nafila tadan jira sannan liman ya tayar bayan an idar ta tsaya tayi adkhar sannan ta fito tana sa takalman ta taji muryan Zee tana cewa "yar halas yanzu muke maganan ki kwana biyu bamu hadu ba ikon Allah ashe rabon zamu hadu ne yasa da muka fito daga massalaci muka tsaya anan" cike da jin dadin ganin su Janan ta wani rungume su tace kawayen albarka wallahi kwana biyu nayi kewar ku kuna raina
Eesher tace "ku akwai latest fa dama nace se mun hadu duka zan fadi muku"
bayan masallacin suka koma suka zazzauna Eesher ta fito da wafer sticks da bounty chocolate ta miqa musu duk sun kosa ta fada masu ganin tayi shiru yasa Janan cewa "hohoho! haba kiyi magana mana kin tsaya yanga se kace kin gammu da hula"
Zee tayi carap tace "gane mun hanya wai makaho yaso tsegumi" daria suka yi sbd maganar ta basu daria..
Seda Aisha tayi gyaran murya kafin tace "kun san me yake faruwa ne" a tare suka hada baki wajen cewa "aa se kin fada"
"Bazan fada ba kuyi guessing"
"Mitchwwww kefa yar rainin seti ce in bazaki fada ba ki barshi baza a yi guessing din ba" cewar Zee
Aisha ta kyalkyale da daria sannan gace "tor iya tsiwa karki tsiwance ni ...dama Pharouk ne ya aiko magabatan shi har anyi maganan komai yanzu an tsaida rana nan da wata biyar kunga bayan saukan" mu da wata uku tunda yanzu saura 2months saukan
A tare suka wani rungume ta cike da jin dadi...
tace "ni ku sake ni kar ku karya ni wannan irin matsa da kuka mun"
Janan tace "aww daga abun arziki se ki fara korafi Allah dai ya kaimu musha biki abu namu" Zee ta karasa da fadin "wai akace maganin a kwabe mu" suka tafa
Aisha tace "kuma dai kuyi kuyi ku fito da mazajen aure musha biki"
Janan tace "tor rasa kunya kar kiga munyi shiru ki raina mu nima My Dr.Imran yazo ya nemi izini gun Abbiey kuma ya tabbatar mun very soon ze aiko in shaa Allah"
Zee tace "hehhehe kice tuwo na mai na za ayi gaskiya muna da sha bukunkuna"
Aisha tace "Allah ya nuna mana lokacin ke kuma Zee ya muke ciki yaushe ne naki bikin?
"Hmm kanku ake ji ni dallah karku dame ni" inji Zee
Janan da Aisha suka kalli juna suka tuntsire da daria dan sun san halin Zee kwatakwata bata kula samari.....
Sunyi hira sosai har suka tuno daya daga cikin babbar kawar su wato Fateema M.Sabo wacce tana Bauchi tana shan karatu suna waya sosai da ita...
Janan tace "aiko in shaa Allah zamuje mu gaida Innar M.Sabo kafin ta dawo huta maybe ma tana nan za ayi sauka da bikin ki Eesher tunda sun kusa hutu
Allah ya kaimana ran" suka amsa da Ameen...
Kamar ance Janan ta duba agogon ta aiko taga karfe daya da minti 45 ido ta zaro waje ganin taci mintuna sun kai 45

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login