Showing 24001 words to 27000 words out of 94974 words
hakan be dameshi ba saboda yasanta wata rana inta riga su tashi tana zuwa part din Ammi ko Hajiya babba , tashin anty amarya ya yi akan taje ta yi sallah shi ze tafi masallaci saboda sun kusan makara ma , mikewa ta yi tana sallati lokacin da taga Asrah bata bed din girgiza kai ta yi kawai ta mike tashiga toilet ta dauro alwala uncle Hameed kuma yafice yasan su Abbie suna jiran shi suje masallaci duk suna main falon gaba dayansu su ka wuce masallaci .
Bayan sun dawo ma sukaci gaba da barci se 10:00am sukayi wanka suka fito saboda ayi breakfast, duk suna kan dinning gaba daya ahalin gidan banda mutum biyu Asrah da Tajuddeen,shima be jima ba yafito yazo ya zauna ,yau tsaban ruwan munafurci umma khareema da bata cin abinci a dinning dan taga reaction din anty amarya yasa ta fito ita kadai se murmushi take .
Ba su fara cin abinci ba anty amarya ta zuba ido tana jiran taga fitowar Asrah amma shiru bama ita kadai ba duk wani dake gurin ita suke jira Abbu ne ya ce " nikam Abida Asrah bata farka bane " murmushi anty amarya ta yi ta ce" ai tama rigamu farkawa tana part din Ammi ne " ɗago kai dasauri Ammi ta yi ta ce" gaskiya yau banga idon Asrah ba kwata_kwata batazo min ba sede ko In ta kaiwa Hajiya babba ziyara " yar dariya sukayi . Kallonsu gabaki daya Hajiya babba ta yi ta ce" no rabona da Asrah tun daren jiya da muka rabu a dinning batazo part dina ba " cak lokaci daya murmushin dake kwance akan fuskar anty amarya ya dauke ta ce " gaba dayanku kunce Asrah batazo wajanku ba to ina take kenan " ganin tana kokarin ta da hankalinta ne yasa Abbie ya ce" kwantar da hankalinki Abida kinsan Asrah fa yanzu haka tana wani gurin ! Abbas,Hafiz , Ahmed ku je ku dubomin Asrah" cike da bin umarni suka mike suka rabu suka fara dubata a cikin gidan .
Su Kuma suna dinning sunyi shuru suna jiran dawuwan su Ahmad da haryanzu basu dawo ba ,anty amarya de hankalinta ya kasa kwanciya kawai so takeyi taji ance mata anga Asrah, haka Tajuddeen ma yarasa gane wa kanshi tunda yatashi yakejin zuciyarshi na yawan tsinkewa .
Bayan kamar 30mint suka dawo suna haki domin zagaye Bishara house kadai in akace kayi an haɗaka da babban aiki Hafiz ne ya ce" Abbie ko Ina mun duba acikin gidan nan lungu da saƙo amma bamu ga Asrah ba hatta masu aiki mun tambaya sunce basu ganta ba suma"
Duk tashi tsaye sukayi a matukar tashin hankali jin abinda Hafiz ya faɗa , daura hannu aka anty amarya ta yi ta ce" nashiga uku na, ina Asrah tashiga? " jawota Hajiya babba ta yi ta riketa tana " karki damu za'a ganta kinsan gidan nan da girman gaske duk yanda akayi tana ta wani gurin " ba shiri daga manya har yaran suka watsu aka fara neman Asrah , babu irin nemanta da ba'a yi ba amma shuru babu ko alamar ta acikin gidan kusan awa daya ana nemanta .
Dawuwa falo duk sukayi akayi cirko_cirko kiran jami'an tsaron gidan Abbu ya yi ya ce musu ko sunga wani bakon fuska, suka ce mishi sude karfe uku na dare suka tashi kuma basuga wata alamar kan cewa an shigo gidan ba .
Ana cikin haka kenan wata me aiki da ita take shara agidan ta shigo da gudu har kamar zata faɗi murya na rawa ta ce" ranka ya dade naga wani takun sawu da ban yarda dashi ba " tashi sukayi gaba daya suka bita tundaga bakin ainihin main part din gidan har zuwa cikin compound akwai sawun tafiya kusan na mutane hudu kuma sawun takalmin ranbut ne da alama akwai inda suka taka laka basu sani ba hakan yasa shatin takalminsu ya bayyana hakan ne ya tabbatar musu da har cikin gida aka shigo aka dauke Asrah amma babban abinda yafi daure musu kai shine wani irin bacci sukayi haka da har aka shigo aka dauke Asrah babu wanda yasani.
Duk suna cikin tashin hankali da baze iya faɗuwa a baki ba musamman ma anty amarya da takejin jikinta ya yi mata nauyi sosai ga kuma zuciyarta da se tafarfasa yakeyi kamar ana watsa mata garwashin wuta akai daurewa kawai takeyi amma harta su ɗin ganin su takeyi bibbiyu.
Few hours latter
Manya_manyan jami'an tsaro masu mukami gaba da an hallara a Bishara house se bincike akeyi lokaci daya cikin Umma da Ammuh yafara kaɗa ƙugi ,alama ummah tayiwa Ammuh akan taje ta samu ta binne wannan layan da boka mauzau ya bayar saboda dakatar da binciken. part dinta tashiga ta bude locker data ajiye layar aciki kamar wasa taga wayam bakomai aciki nemanshi tashiga yi sama ko ƙasa amma babu shi babu dalilinshi hankalinta ya tashi tarasa ina ta boye zaman yan bori ta yi akasa tama ka sa fita daga dakin .(abinda ya faru shine bayan gari ya waye duk suna dinning zasu yi breakfast kaltume ta shigo part din Ammuh saboda ta yi aikinta na yau da kullum da ta saba tana cikin yin shara kawai idonta ya sauka akan laya yashe a ƙasa kwata_kwata ranta be yarda dashi domin tasan mugun halin Ammuh tana tsoron karta cutar da bayin Allah hakan ne yasa ta daukeshi da sauri tasaka a hularta ta fita a part din ta shiga kitchen ta dauki kalanzir da ashana ta fito backyard ta duba lungu da saƙo taga babu kowa.ta fito da layar ta ƙona shi ƙumurus bata bar wajan ba se da ta tabbatar da wutar ya mutu ta share wajan gudun kar ayi zargin wani abu, se a sannan ne hankalinta ya samu kwanciya.)
Bayan anty amarya Tajuddeen yafi kowa shiga tsantsan madarar tashin hankali gaba daya ya fita a hayyacinsa idon nan ya yi ja sosai hatta eyeballs din shi da suka kasance golding in color seda suka canza kala.domin duk duniya in aka cire Allah da Manzonsa tofa Asrah ce mutum ta farko da yake matuƙar haukar so,yafi sonta sama da son da yake yiwa kanshi.
ji ya yi gaba daya komai baya mishi dadi zufa ne yake zubo mishi ta ko ina ya ma rasa ina ze tsoma ranshi har yanzu yama ka sa yarda da wai ansace Asrah bata gidan daga zaran yarufe idonshi ganinta yakeyi ta nayi mishi gizo runtse idon ya yi kawai.
Yau Bishara house ba lafiya su Zoya suna part din ya Abbas suna kuka , su Abbas din kuma suna main part inda ake ta bincike, Hajiya babba da Ammi suna part din anty amarya suna lallashinta da bata baki kancewa in Sha Allah za'a ga Asrah. Itade jin su kawai takeyi amma tunaninta yatafi wata duniya. dede da hawaye babu a idonta dama in tashin hankali yakai tashin hankali hawaye ma kanshi nemanshi zakayi karasa inbanda girgiza kai babu abinda anty amarya takeyi se kukan zuci da takeyi ta ciki.
Abinka da masu hannu da shuni akasar Nigeria nan take duk wani hanyar shiga da fita dake cikin Maiduguri anrufe. babu me shiga babu me fita nan take aka fara yaɗa hotunan Asrah a kafafen sada zumunta ana cikiyarta da alkawarin duk wanda ya samota za'a bashi kyautar naira millon goma .
Kamar wasa tun safe ake neman Asrah har karfe sha daya na dare shuru babu ita babu alamarta gaba dayansu babu wanda ya iya sawa cikin shi wani abu duk basa cikin nutsuwar su.
Washe gari ma akayi neman duniyar nan anyi kuma har lokacin ba'a bude Maiduguri ba , gaba daya kasar Nigeriya ansa tsaro ana nemanta amma shuru ba'a yi nasara ba , acan kuwa gida yanda suka ga rana haka sukaga dare kananan yaran ne kawai sukayi bacci se wa'yanda sukasa aka dauketa din.
Duk suna zaune afalo sunyi tagumi sunyi jugum_jugum har yar rama seda sukayi hankalinsu atashe anty amarya kam rabonta da magana tun jiya sede ta yi ta binsu da ido.
Abbie ne yacewa uncle Hameed yakaita daki ta kwanta inta ci abinci.
Riko hannunta ya yi yadagata suka fara tafiya ji ya yi ta tsaya kallonta ya yi yaga tazuba mishi ido ga jinin dake fita a hancinta sekuma tasa hannu a setin zuciyarta idanunta yafara rufewa da sauri uncle Hameed ya rungumota jikinshi ya yi dede da daukewar da numfashinta ya yi cak rai ya yi halinsa .
Innalillahi wa'innailaihi rajuun 🥺🥺🥺
Se mun haɗu gobe in mai duka ya kaimu da rai da lafiya.
Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.
Comment,like and share 🖋️🖋️
Share , comment and like
https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹
Page 11
*_ story & written_*
By
*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)
*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️
Page 11
Cikin kiɗima da tashin hankali duk suka rufu akanta suna kiran sunanta "Abida! Abida! Abida" amma ina ta yi nisan da bazataji kira ba domin kuwa babu alamar rai ajikinta, Hajiya babba ce ta sunkuya agabanta ta daura kanta asetin zuciyar anty amarya bugawa da karfi ta ji yake yi da sauri ta kalli uncle Hameed ta ce"ayi gaggawan kaita asibi......"kafin ma ta iddasa maganar ta uncle Hameed ya suri anty amarya ya yi waje da ita a hannu , driver's kusan hudu ne suka rufa mishi baya daga cikinsu ne yabude mishi back set ya sakata aciki driver yaja motar suka wuce asibiti, su Abbie dasu Ammi duk bin bayansu sukayi hankalin Ammi ya yi kololuwar tashi ganin halin da kanwarta take ciki wanda ita kadaice tarage mata afadin duniya.
After one hour
Doctor ne yafito daga dakin da akayi admitting din anty amarya ya ce" she's out of danger now sede kubita a hankali kar adinga bata mata rai , ta kamu da ciwon zuciya na farat daya , zuciyarta ze iya bugawa idan har yaci gaba da fuskantar kunci da tashin hankali kuma dole ku dinga kasancewa tare da ita gudun kar a barta ita daya ta faɗa tunani . Kudinga tayata hira domin dauke mata kewa Allah yabata lafiya" duk jikinsu ya mutu jin anty amarya ta kamu da ciwon zuciya dama tana cikin damuwar rashin haihuwa ga kuma yarta daya tilo data mallaka aduniya ansace ta.
Dakyar suka iya amsawa doctor da ameen sannan suka shiga ciki tana kwance tana baccin wahala gaba daya ta tane sosai ta yi fayau kamar ba jini ajikinta bacci takeyi amma hawaye ne yake fitowa daga idanunta zama kusa da ita uncle Hameed ya yi hawaye na zubowa daga idonshi tausayin kansu ne ya kamashi da kuma tausayin matar shi na irin halin da take ciki sun yi rashin babban farin cikinsu da in sun kalleta suke jin sanyi da kwanciyar hankali a tare dasu.ita kadai suka mallaka a duniyar nan ga shi to mara imani sun dauketa. Abbie ne ya tsaya kusa da uncle Hameed ya dafa kafardar shi cikin sassauto da murya ya ce "in sha Allah za'a ganta"
kiran waya ne yashigo wayar Abbu dubawa ya yi yaga DPO ne da sauri ya yi picking , a dayan bangaren aka fara magana"ranka shi dade !a iya binciken mu mungano bawai aikin enemies bane , daga shekaran jiya zuwa jiya ansace yara ƙanana mata sama da goma , daya a Damaturu uku a pataskum , uku a biu sekuma hudu a nan Maiduguri harda yar gidanka itace cikon na goma din kuma binciken mu ya nuna mana yaran nan da masu garkuwar basa cikin garin Maiduguri amma duk inda suka shiga zamu nemosu in Allah ya yarda"Abbu dake tsaye ne yasamu guri ya zauna zufa na tsatsafo mishi be iya cewa DPO komai ba kawai ya kashe wayar kallon shi Abbie da uncle Hameed sukayi dasu Hajiya babba ganin reaction dinshi tambayanshi suka shigayi , "babu komai" ya ce musu jan hannunshi Abbie ya yi sukayi waje nan Abbu ya kwashe duk yanda sukayi da DPO yafaɗa mishi.shi kanshi Abbie jin yara har goma aka sace hankalinshi yatashi sosai , waya yadaga ya kira gomna sukayi magana sosai sannan ya kashe.
Yau kwanan anty amarya biyu a asibiti , kuma har izuwa yanzu ana binciken neman yara mata goma da aka sace amma shuru babu su babu alamar su kamar ba sacesu akayi ba makwamusan sunada matukar basira sosai basu bar alama ko sheda ƙwalli daya ba wanda za'a kamasu ,har suka isa inda zasu isa cike da basira babu wanda yaci nasarar kamasu saboda ba haka suka zauna ba harda tsafi a lamarin kwamushen su shisa ba'a taba kamasu.
Bayan an sallame su sun dawo gida ana kulawa sosai da anty amarya kullum Tajuddeen na tare da ita duk da rashin son yin magananshi ga kuma abinda ya hadu mishi na rashin Asrah hakan ne yasa ya dauwa kanshi alkawarin cewa inya zama babban soja shida kanshi ze nemo Asrah aduk duniyar da take sannan ya kashe duk wanda yake da sa hannu a saceta ,gaba daya ya zama kamar wanda beda lafiya ji ya yi ma zama acikin gidan batare da itaba ya ishe shi hakan yasa ya gama shiryawa gobe ze bar kasar kuma ya fadawa Ammi akan ta faɗa wa Abbie , yanzu ma yazo wajen anty amarya ne yana tayata zama dukda akwai mutane atare da ita saboda inba bacci ba ba'a barinta ita kadai tadena magana sosai tadena shiga cikin mutane komai dinta ya canza , su Saghar duk suna tare da ita haka anty Sameera da anty Sakeena suma kusan kullum se sunzo gidan . Haka de gidan yakoma kamar gidan zaman makoki.
Washe gari misalin ƙarfe goma na safe Tajuddeen ya gama duk wani shirin da zeyi na tafiya kowa an hallara a falo saboda rakashi airport ,fitowa ya yi sanye da wandon sojoji da bakar riga me hula ya rufe fuskarshi dashi falon ya shiga ya zauna kusa da Hajiya khareema (Ammuh) nan suka fara mishi addu'ar samun nasara akan karatunshi, tashi ya yi yaje gaban anty amarya ya tsuguna ya rike hannunta yana kallon cikin idonta ya ce"Anty amarya nayi miki alkawari da hannuna zan dawo da Asrah cikin wannan gida,ko min daren dadewa ina me tabbatar miki da zamuga juna , ki yarda dani " shafa kanshi anty amarya ta yi tana yar murmushi ta ce "na yarda dakai Tajuddeen nasan duk inda Asrah din ka take zaka dawo mana da ita in Sha Allah , zan zuba idanu domin inga wannan rana idan har Allah ya aramin tsawon kwana , Allah yabaka Sa'a akan karatunka" murmushi kawai ya yi ya mike ,Abbie ya zubawa Tajuddeen ido yanaso yaga ko ze mishi magana ko bazeyi ba , kallon Abbie Tajuddeen ya yi ya taka zuwa inda suke tsaya batare da ya ce musu komai ba da fa kafaɗar shi Abbie ya yi yana murmushi ya ce" nasan zaka sani alfahari arayuwata da kowa in ya ganka zece wannan ɗan Mubarak Bishara ne I have trust in you" murmushi kawai ya yi.
Ammi na zaune ta yi shuru ji tayi dama ace kar ya tafi."Ammi" ya kira sunanta murya akarye dagowa ta yi ta kalleshi mika mata hannu ya yi, ta rike ya dagota tsaye sannan suka rungume juna kusan minti biyu , addu'a sosai Ammi ta yi mishi saketa ya yi yaje ya rungumi Hajiya khareema se goge hawaye takeyi " son zanyi kewarka sosai" " me too Ammuh na "murmushi Hajiya khareema ta yi ta ce"ka kulamin da kanka sosai domin na damu da kai da kuma rayuwarka!"gyada mata kai ya yi.
Hajiya babba ma sosai ta yi mishi addu'ar samun nasara arayuwa ya amsa mata.
Fitowa sukayi su Abbas ne dasu Abbie ne suka rakashi airport, fita ya yi a motar yana kokarin nufan wajen jirgi, bin bayanshi Abbas da su Hafiz sukayi riko riganshi Abbas ya yi, juyowa Tajuddeen ya yi ya fuskance su " Tajuddeen mudinma fushin da kakeyi damu na ba gaira ba dalili dashi zaka tafi azuciyarka ba zaka rungumi yan uwanka ka musu bankwana ba?"buɗe musu hannu ya yi dukkansu suka rungumeshi can ƙasan makoshinsa ya ce"zanyi missing naku" suma suka ce "muma haka amma duk end of month zamu dinga kawo maka visit in Sha Allah" haka suka rabu akan idonsu ya shiga cikin jirgi after few minutes jirgin yatashi. Ajiyar zuciya sukayi suka koma motar yau zasu ji gidan wani iri ba Asrah ba Tajuddeen.
Haka rayuwar gidan yaci gaba da kasance babu wani walwala sosai atare dasu, yau sati biyu kenan da dauke Asrah kuma haryanzu anata bincike amma shuru sede muyi addu'a muce Allah ya bayyana su.
Lokacin da Fu'ad Abubakar Daula ya samu labarin an sace Asrah kamar zeyi hauka, bori da faɗe_faɗe babu irin wadan beyiwa mahaifin shi ba Abubakar Daula kan cewa lallai se yasa an samo mishi Asrah din shi ko kuma shi ya bazama duniya ya nemota dakyar Abubakar Daula ya shawo kan Fu'ad ya nutsu gaba daya ya tarwatsa bedroom din shi ya jijjima kanshi ciwo Abubakar Daula ne ya ce "Fu'ad karka damu zan sa a nemo maka Asrah amma ba yanzu ba, se bayan komai ya lafa tukun dan banaso ayi tunanin akwai hannunmu acikin saceta da akayi saboda kowa yasan irin gaban dake tsakanin mu da su just calm down"ya faɗa yana dafa shi,zubewa akan guiwowin shi Fu'ad ya yi rai a matukar ɓaci batare da ya ɗago kai ya kalli Abubakar Daula ba ya ce"dad leave my room bana san ganinka just leave me alone"