Showing 6001 words to 9000 words out of 94974 words

Chapter 3 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8652

By




MRS🌹ISHAM🌹
( Yar lelen Jarumai)






*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹






📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️






Page 04




" Se tajuju ya aureni ! se munyi aure ! and we love each other" kalmomin da tadinga faɗa kenan tana kuka , tun suna mata dariya har suka koma lallashinta ƙin sauraransu ta yi , ta ci gaba da kukanta jikinta har rawa yakeyi lokaci daya ta haɗa zufa saboda kuka , daukanta Hajiya babba ta yi ta daurata akan cinyarta tana lallashinta amma sam taki shiru.
Abbie, Abbu , uncle Hameed suna zaune suna tattaunawa suka ji ihun kukan Asrah dafe goshi uncle Hameed ya yi. murmushi Abbie ya yi ya ce" to yanzu kuma wa ya taɓo wannan rigimammiyar " ya faɗa yana mikewa yar dariya sukayi su ma suname bin bayanshi , su iklas dasu Abbas duk suna part din Hajiya babba gaba dayansu , yaran matan sun duƙufa suna homework Hafiz na gyara musu in basuyi dede ba , saghar tun da suka shigo be kula kowa ba ɗan har iya zuwa lokacin fushi yakeyi ,yakoma gefe aranshi kuwa yana aiyana irin mugun dukan dazewa Asrah aduk lokacin da Tajuddeen yatafi U.S.A , idan ya tuna Tajuddeen zeyi nesa dasu ne yake jin ranshi nayi mishi sanyi ɗan hakan ne ze bashi damar cin zalin Asrah yanda yaga dama.
Kukan Asrah suka faraji da rigimarta kallon juna Abbas da Ahmad sukayi sukasa dariya , Ahmad ya ce" tabb dijam ! Yau anya zamu yi bacci kuwa? gaskiya Asrah akwai shegen rigima " " ni wallahi kukan yara dagamin hankali yakeyi , Allah de yasa Tajuddeen na gida , ɗan kuwa inde baya nan banajin akwai wanda zesa yarinyar nan ta yi shuru" cewar Abbas .
Dogon tsaki saghar yaja ahassale ya ce " wannan iskancin da yarinyar nan takeyi guri ta samu ,aikin banza " ya mike yabar musu part din,girgiza kai kawai Hafiz ya yi bece komai ba.


" zoya,parsa,umaisha,rameesa kuzo muje gurin Asrah kunji tana kuka ko " cewar iklas da ta mike tana jiran sauran yan uwan nata su tashi suje, mikewa sukayi su ma suna kokarin tafiya, daka musu tsawa sahil ya yi ya ce" common ku zauna babu inda zakuje, ta yi kukan jini ma ina ruwanku " duk tsilli_tsilli sukayi da ido kamar wasu marasa gaskiya, basu zauna ba kuma basu tafi ba . sake daka musu tsawa ya yi yana kokarin mikewa suka zura aguje sukayi part din Tajuddeen ɗan saboda suna kyautata zaton Asrah na can.
Kwafa sahil ya yi ya ce" zamu haɗu ai duk senayi maganin ku " Abbas, Ahmad,Hafiz de basu ce musu komai ba karshema tashi sukayi suka bi bayansu parsa zuwa part din Tajuddeen din.


" Ohhh no! wa ya taba Asrah ne haka, meyafaru yar lelen Abbie" Abbie ne ya yi magana a yayinda yake sa hannu yadauketa akan cinyar Hajiya babba suka zauna akan manyan kujerun da ke zagaye a falon.
Rarrashin ta Abbie yakeyi ko zasu samu ta yi shuru amma ina ,kamar ana zugata ga har kanta yafara daukan zafi , uncle Hameed ne ya kalli anty amarya ya ce " nikam Abida wa ya taɓo wannan rigimammiyar" dariya anty amarya ta yi ta ce" ita da Hajiya babba ne , ce mata ta yi bazata aura mata Tajuddeen ba shine ta ke wannan kukan " dukkansu dariya sukayi harda su Abbas da su ma suka shigo, ga su parsa atsaye sunyi carko_carko duk jikinsu ya yi sanyi sosai ganin irin kukan da yar uwarsu Asrah keyi , ɗan kuwa ba karamin so sukeyi mata ba shisa kullum se sunje wajanta duk da ita bata wani shaƙu dasu ba ,saboda ba kasafe take zama a cikinsu ba.
" Haba Hajiya babba ! kinsan halinta inde akan Tajuddeen ne tofa seta hanamu bacci agidan nan " cewar Abbu fuskarshi dauke da murmushi .


Shigowa cikin falon ya yi idonshi akan Asrah da ke zaune akan cinyar Abbie tana kukanta , sake tsuke kyakkyawar fuskarshi ya yi babu annuri a fuskar, ko kallonsu beyi ba yakarasa tsakiyar falon ya tsaya , tunda ya fito , cak kukan nata ya tsaya kamar anyi ruwa an dauke tafara dariya kamar ba ita ce take wannan kukan ba da kururuwa , hannu ya mika mata ya ce" let's go Asrah" cikin hanzari ta sauƙo akan cinyar Abbie ta riƙo hannun nashi hade da rungume shi, duk zuba musu ido sukayi babu wanda ya ce mishi uffan , ɗan sun san wani inya mishi magana acikinsu ze iya basu amsar da bazeyi musu daɗi ba , domin Tajuddeen inda kunya yabi ma be biba , riko hannunta ya yi yajata zuwa part din shi suka barsu afalon.


Ajiyar zuciya Ammi ta yi kawai taname bin bayan Tajuddeen da Asrah da kallo, kallon Abbie ta yi taga shima ita yake kallo, alama yamata da ido ,ta kwantar da hankalinta, gyada mishi kai ta yi sannan ta mike ta bar falon ta nufi nata part din ,hadaddiyar bedroom dinta tashiga na alfarma dayasha dukiya, zama ta yi akan gado. wasu abubuwan da suka faru shekaru sha takwas abaya ne yake dawo mata acikin kwakwalwar ta , bedside table takai idonta ,yar karamar hoton enlargement ne me kyau ita ce acikin hoton da wani kyakkyawan yaro ajikin hoton sa hannu ta yi ta dauki hoton , shafawa ta yi hawaye na fita a idonta " am sorry my Tajuddeen, ɗana ka yafemin ninasan me laifi ce agareka amma ban cancanci haka daga gunka ba, wallahi bantaba jin bana sonka ba kawai ,abinda ya faru sharrin shaidan ne " ta faɗa tana kuka ta rungume hoton a kirjinta , haka ta kwanta da hoton rike ahannunta , shigowa bedroom din Abbie ya yi yabiyo bayanta domin yasan inde tashiga daki setayi kuka hakan ya rigada ya zame ma ta jiki, tana jin motsi , da sauri tasa hannu ta goge hawayen fuskanta, zama Abbie ya yi a kusa da ita yasa hannu ya ɗagota ta zauna , ganin idonta ya yi ja ne yasa ya ce " sarauniyata kuka kika yi ?" girgiza mishi kai ta yi" ah ah kuka kika yi mana ga idonki ya yi ja ! nasan abinda yake damunki nikaina abun na damuna, wallahi nafara zargin kode sihiri akayi wa wannan yaron , da nayiwa malam baba gana magana ya ce babu sihiri ajikinshi . bansan meye matsalar shi ba "
Kwantar da kanta Ammi ta yi akan kafaɗar Abbie ta yi shuru tana sauraranshi.
Cikin tsigar lallashi ya ce" sarauniya ta , ki kwantar da hankalinki in sha Allah zanyi iya kokarina inga Tajuddeen yadawo kamar kowa " bata fuska ta yi domin ji ta yi ranta yafara ɓaci ta ɗago ta kalleshi ta ce " ka fa riga da kasan matsalar kasan wacece ta shiga tsakanina da ɗana, amma narasa wani daliline ya hanaka yarda da hakan" murmushi Abbie ya yi ya cire glass din idonshi sannan ya ce" bansan meye matsalarku da Hajiya khareema ba , ko da yaushe ita kuke kallo amatsayin me laifi , bayan ita tsakani da Allah take son Tajuddeen. babu mugun nufi aranta amma kun ka sa fahimtar hakan ! to gaskiya banason irin haka " yagama maganar shi yana me janyeta daga jikinshi sannan yafita yabar dakin nata babu walwala atare dashi .
Ammi kam bakin ciki da bacin rai ne ya hanata magana se ma bin bayanshi da takeyi da kallo harya bacewa ganinta .ta rasa dalilin da yasa Abbie kwata_kwata ya tsani akawo mishi aibin Hajiya khareema, kallon mutumiyar arziki yakeyi mata ,domin duk inda makira algunguma take tofa inde akasamu Hajiya khareema magana ya ƙare.
Kwafa Ammi ta yi azuciyarta tafurta " ina sha Allah sena kwato ɗana da mijina daga sharrinki khareema".




Shigowa bedroom dinshi sukayi yana rike da yan dugui_dugui din hannunta, yanda yafita yabar Hajiya khareema ahaka yadawo yasameta sede wannan karon yanayinta babu yabo babu fallasa, zaunar da ita ya yi akan gadon ,tun kafin yakai da zama akan gadon,zazzakar Muryar Asrah kamar wanda aka barbaɗawa suga ya dira musu akunne tana faɗin" my tajuju ai zamuyi aure ko" bece mata kala ba face gyada mata kai da ya yi, dan tun ahanya ta cikashi da surutu hade da bashi labarin abinda yahadata da Hajiya babba cike da yarinta gwarancinta. nan ne ya gane asalin musabbabin kukan nata da yajiyo , har cikin ranshi yaji dadin yanda Asrah take matukar kaunar shi da har yakai in ance bazata aureshi ba kokuma baya sonta take kuka kamar wacce taci duka , duk dakuma kananun shekarunta, shisaka yake jin duk fa ɗin duniyar nan bashi da mata sama da Asrah domin son dayake mata tun tana cikin mahaifiyarta yakamu da sonta , hakan yasa yasanyawa ranshi duk dadi duk wuya yana tare da ita baze taba barinta ba .
muguwar kallo Hajiya khareema take bin Asrah dashi domin yanda ta tsani yarinyar ma aranta to bazata iya faɗa ba domin tsanan yawuce misali , duk wata hanya dazatabi wajan ganin ta ka war da Asrah tagama shirya komai kawai lokaci take jira tarusa farin cikin anty amarya da uncle Hameed da sauran mutanen cikin gidan.mikewa ta yi ta ce" my son nafarajin bacci bari inje in kwanta sannan zanbawa parsa abincinka ta kawo maka " lumshe mata idanunshi dasuka kasance masu daukar hankali ya yi. kan nan tafice a part din nashi tana tafiya tana sake_sake na ganin bayan Asrah in bahaka ba kuwa zata bata mata aikinta ne.


Dawo da kallonshi ya yi kanta yaga ta dauki headphone dinshi tasa akunne , kokari takeyi wajan ganin ta kunna ƙida amma takasa , girgiza kai ya yi dan yasan yanzu zatace seya kunna mata ,aikuwa hakan ce ta kasance datayi iya yinta ta ka sa budewa ta miko mishi " tajuju play a song for me" karba ya yi ya ajiyeshi ya ce" not now , ke bakyajin bacci ne karfe 9 fah " turbune fuska ta yi zata mishi kuka ya ce" karma ki fara ɗan drygon zan kira miki " nan take tayi shuru kamar ba ita ba ,saboda tana matukar tsoron wannan karen nashi da yasa mishi suna drygon hakan yasa cikin tsoro_tsoro ta ce" tajuju ka kaini wajan mommyna zanyi bacci" ta yi maganar tana hawa bayanshi . har part din su yakaita abakin bedroom din anty amarya ya ajiye ta da gudu ta shige ciki ɗan gani takeyi kamar ze iya kiran karen.




Washe gari 6:00am


Yawan comments dinku yawan read more din da zan muku ah to.
Se mun haɗu gobe in Allah yakai da rai da lafiya.








Comments,share and like




🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




Page 05




*_ story & written_*

By




*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)


*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*








🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️





Page 05




Duk yaran gidan sun tashi daga bacci tunda sukayi sallah asuba basu koma bacci ba , iyayensu sun koma bacci amma su basu koma ba , kaltume tana shiryasu dan ganin kar suyi letting a makaranta, amma gaba daya sun ƙi natsuwa se raba mata hankali gida biyu sukeyi musamman ma umaisha tafisu rashin ji , dakyar da suɗin goshi ta samu ta kammala shiryasu ta kwashe su dukkansu biyar din suka wuce dinning table.


Kitchen kaltume ta shiga ta Samu me girkin gidan fatime ta gama shirya musu breakfast dinsu , gaisawa sukayi cikin mutunta juna kafin suka fito atare rike da food flask din abinci suka jera a dinning . Kallon fatime kaltume ta yi ta ce" fatime naga yan mazan basu fito ba ko za ki je ki taso su karsuyi letting" ba don ran fatime yaso ba ta gyada mata kai, ta nufi part din yaran mazan tana tunani iri_iri aranta, domin tasan halinsu wasu daga cikinsu ma dakyar insun tashi daga baccin, part din twins tafara shiga ta yi Knocking daga ciki aka amsa da" Yes come in " turo kofar ta yi ta tsaya daga bakin kofa.


Dukkansu biyu sun shirya sahil ya kammala necktie yake sawa. shikuma salim takalmin makaranta yake sawa batare da sun ɗaga kai sun kalleta ba suka hada baki wajan faɗin" fatime ya akayi ?" Mamaki ne yau yakamata ganin yau sune akazo aka samu sun shirya suda kullum se sunyi letting kafin su tashi jinjina kai ta yi aranta ta ce" ahh lallai yau sahil da salim sunyi abin kai " afili kuwa ta ce" dama nazo in tasheku ne ,kuzo kuyi breakfast". " okay" salim ya furta suka ci gaba da shirin da sukeyi .
Fita tayi anasu part din ta shiga na Saghar , Jawan da Sudais , su kam ma a falo ta samesu sunfito hannunsu rike da school bag gaisheta sukayi ,ta amsa tarike haɓa kafin ta ce " dama ku zanje in taso kuzo kuyi breakfast saboda karkuyi letting " murmushi kawai suka mata , suka wuce ta .
Daga karshe part din Tajuddeen ta nufa tana tunani yau kuma wani irin wulakanci zeyi mata , sadaƙarwa ta yi kawai ta shiga part din kai tsaye ta wuce bedroom dinshi knocking ta yi taji ji shuru babu amsa , hakan yasa ta sake gwadawa duk da tasan abune mawuyaci Tajuddeen yabude. haka tai ta gwadawa kusan mintin ta goma a tsaye awajan cire rai ta yi da ze bude ta juya tafara tafiya ta ji , yabude kofar dawuwa ta yi ta tsaya kanta akasa domin kuwa dukda Tajuddeen beda wasu Shekaru bata iya kallon fuskarshi tunda tazo gidan saboda yana da matukar gwarjini ga wannan golding eyes din nashi da in ya tsare mutum dasu tofa se ka sha jinin jikinka.
Yana sanye da kayan bacci fuskar nan yaci murr ga idonshi da har lokacin akwai alamun bacci acikinta yawatsa mata harara dashi, cikin daga murya da rashin nuna ko In kula ya ce" meyafaru kikazo kina dokamin kofa da wannan safiyar ?" Hadiye wani yawu ta yi muryanta yafara rawa dakyar ta iya furta dama nazo in tasheka ne ! ka shirya zuwa makaranta kuma angama breakfast kai kadai suke jira " wani banza kallo yabita dashi ranshi yayi matukar ɓaci " daga yau se yau karda ki kuskura insake ganinki a part dina da sunan kinzo tashi na daga bacci , sannan wa'yanda suka turoki ki tasheni din kije kice musu bazanje makarantar ba" ya yi mata maganar cike da gargadi da izza da rashin kunya sannan yana kammala faɗa mata abinda ze faɗa ya rufe kofar da karfi kamar ze ɓalle ta , ya koma ciki yana tsaki yana rike kanshi dan ji ya yi kamar ze faɗi , ɗan duk sanda a ka tashe shi daga bacci tofa se ciwon kai ya ziyarce shi.


Jikin fatime a sanyaye takoma falo taje ta samesu duk suna zaune a dinning table suna zaman jiran Tajuddeen dukda sun san mawuyacin abune yafito tunda yariga da ya yi pepper tare da yan ss3 ya dena zuwa makarantar, jiran admission dinshi kawai yakeyi , dukda sun san ba lallai yafito ba amma basu da ikon cin abinci harse ance baze fito ba , domin wannan shine dokar gidan basa cin abinci a ware , Jawan ne ya ce " fatime yaya Tajuddeen din ya ce baze je ba ko ?" gyada mishi kai ta yi , tun daga nan be sake cewa komai ba ya ja plate din omelette din gabanshi yafara ci.
Salim ne ya ce " hmm dama ai bro Tajuddeen ba lallai ya fito ba tunda shi yanzu ya rena kowa agidan " dakatawa da cin omelette din dayakeyi Jawan ya yi ya kalli salim ya ce" babu ruwanka da rayuwar dan uwana ka ji da abinda yake gabanka, banason reni yaya Tajuddeen ba sa'anka bane " tsaki salim ya yi be kula Jawan ba , sudais ne ya kalli salim ya ce" salim karka sake irin haka , wannan rashin kunya ne " tunda akayi haka babu wanda sake cewa komai harsuka karisa cin abinci , fita sukayi izuwa packing space , motaci uku suka shiga se escort din da suka bi bayansu zuwa makarantar.


Tajuddeen ba shi ya tashi daga bacci ba har 10:00am toilet yafada ya yi wanka yafito ya shirya cikin ƙananan kaya riga da wando saman rigar yadaura rigar sanyi me hula, hular yarufe mishi rabin fuskar shi, sannan ya yadauki headphone dinshi ya toshe kunnenshi dashi . Kafin yafito kai tsaye dinning ya wuce.
duk a dinning din yasamesu wasu sun gama cin abinci wasu kuma suna kan ci , se hira sukeyi gwanin burgewa ,Hajiya khareema na sashinta bata fito ba.
Jan kujera ya yi ya zauna batare da ya kallesu ba balle su sa ran ze gaishesu, kallon fatime dake tsaye akanshi ya yi murya kamar wanda aka tilastawa dole ya yi magana, ya ce " in banida rabon abinci ne yau kifadamin in tashi in tafi " ya faɗa yana me tsareta da wa'yannan mayun golding eyes din nashi da se ƙyalli sukeyi kamar wa'yanda aka kunna kwan fitila, hannun fatime na rawa tafara bubbude food flask din da suke wajan domin ya zaba wanda zeci , gama bude gaba daya food flask din dake kan dinning ta yi tana jiran yazaba wanda ze ci ,dan gudun kartasa mishi wanda ba shi yake da niyyar ci ba ta yi laifi . ganin ta budesu bata zuba mishi bane yasa yagane me take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login