Showing 42001 words to 45000 words out of 94974 words

Chapter 15 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8664

maganar yana murmushi tsinkayar muryar Sabriyah ya yi tana cewa "Fu'ad Allah sarki wanda kukazo afafa dashi yaron hotel din nan de an kashe shi."nan take ya sauya fuska zuwa na mutanen kirki me cike da jimami ya juyo da sauri ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun Umar din!?"ya faɗa da alamun tashin hankali a tattare dashi ya mike da sauri yabar dakin jikinshi na rawa.


Bin bayanshi sukayi da kallo cike da jimami Asmita ta ce "Allah sarki ji yanda hankalin Fu'ad ya tashi" Sabriyah ta ce "eh ai dole hankalinshi ya tashi,kinsan Umar din yaron shine!shi yake mishi hidima a hotel din nan" haka suka dinga jimanta mutuwar Umar din.




Ba'a yi wani dogon bincike dangane da mutuwar Umar ba saboda Lagos oriental hotel,babban hotel ne a Lagos yana daya daga cikin hotel din da ake ji dashi.idan aka fara bincike kuma ze jawo hankalin al'umma hakan yasa aka kashe maganar kawai dama bashi da wani gata yaron.


Bayan sati daya shakuwa sosai ya shiga tsakanin Fu'ad da Sabriyah and Asmita saboda yanda yake kulawa dasu komai yi musu ya keyi kamar wani ɗan uwansu,ya hana su komawa afafa ya ce su bari in ya tashi tafiya shi da kanshi ze kai su, a yayinda yake kwana a falo Sabriyah da Asmita kuma suna kwana a bedroom,har zuwa wannan lokacin be nemi Sabriyah da wata mu'amala ta banza ba, saboda kamar yadda ya faɗa mata son tsakani da Allah yake mata.


Asmita ta yi wani saurayi acikin hotel din ya dawo daga Indonesiya ya sauka a hotel din a ranar ya hadu da Asmita sosai suke soyayya har waya ya siya ya bata,hakan yasa Fu'ad ma ya siyawa Sabriyah waya Samsung Galaxy S20.




Sabriyah da Fu'ad se Asmita ne zaune a falon hotel din Sabriyah ta ce "nikam Fu'ad ba kace nan da sati daya zaka tafi bane!?,ni Wallahi na gaji da zama a hotel din nan kawani killace mutane haba."dariya shi da Asmita sukayi ya ce"kai Sabriyah kina da matsala yanzu ke hakan be fi miki ba?,akan gantalin da kukeyi afafa!?"harara ta watsa mishi cikin ɓacin rai ta ce "ba gantali mukeyi ba,a haka muka taso kuma ni bani da wajan da yafi mini wannan gidan"tana gama maganar tabar falon domin maganar da Fu'ad ya faɗa ya bata mata rai,kallon juna Asmita da Fu'ad suka yi cike da mamaki domin sude acikin wannan maganar ba su ga abin ɓacin rai ba,bin bayan sukayi domin ba ta hakuri.






THE UNITED STATE OF AMERICA


MILITARY HEADQUARTER.






Manya_manyan sojoji ne masu muƙami a zaune acikin wani keɓebben dakin bincike su biyar kuma dukkanninsu turawa ne daga General, brigadier general,major general, surgeon general, colonel general duk suna zaune da alama akwai wanda suke jira domin su ci gaba da tattaunawar da zasu yi ɗago kai general ya yi cikin harshen turanci ya ce"anya lieutenant general ze samu zuwa kuwa!?"colonel general yana duba wasu files da sukayi ƙura ya ce "tabbas lieutenant general ze zo saboda,burinshi shine criminals su shiga hannunshi su sha azaba,ba ya wasa da abinda ya kasan ce me mahimmanci,kar ku manta shifa sojan ƙasa da ƙasa ne dole ne ma yazo saboda rayuwanka al'ummar ko wata ƙasa yanada alhakin kare su"jinjina kai sauran sojojin sukayi.


bude kofa wata kyakkyawar baturiya ta yi jikinta sanye da kakin uniform din sojaji ga bindiga a gefen kugunta, tana shigowa ta ƙame sannan ta sara musu.


shigowa dakin binciken ya yi cike da jarumta irin na manya_manyan sojoji,yana sanye da army trouser wato wandon sojoji,yayinda yake sanye da riga armless na sojaji yaɗan matse shi,ya nada wata irin sura me matukar razanarwa, rikitarwa da kuma jan hankali haɗe da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne me farfadar kirji a bude yake,ga six packs din shi baro_baro ya cika vest din kana ganin zanen kirjinsa ya fito a ta cikin vest din da ya sa'ka,idan ka kalli damtsen hannunshi kuwa se ka tsorata,kana gani kasan yanada matukar karfin gaske kamar dan wrestling haka surarsa take mutum ne me ji da karfi.
Idan muka je wajan cikin sa kuwa a shafe yake babu alamar yana cin abinci saboda yanda wajen ya yi flat.
Launin fatarsa kuwa fari ne sol irin wannan farin larabawa saboda shidin jinin shuwa Arab ne bugu da ƙari kakar mahaifiyarsa ta kasance baturiya.
A wajan kyau kuwa sede muce tubarakallah Masha Allah domin Allah ya yi masa baiwar kyau me matukar razanarwa da kuma kayatarwa,ko na miji da suke jinsi daya se ya zuzutawa kyawunsa ɓalle mace. bugu da ƙari dogo ne ga murɗaɗɗen,ƙarfaffa duk abinda mace za ta bukata a jikin namiji Allah ya wadatasa da shi.sumar kansa kuwa yana ɗauke da wata irin aski me suna faded hair cut gefe da gefen kan an rage wannan ƙayitatciyar sumar, se ya zamana tsakiyar kan ne ke dauke da suma me matuƙar yawa da tafiya da hankali, sumar baƙine sosai yana kwance se sheki da daukan ido da yake yi,irin gashin larabawa. askin kanshi ma kadai abin kallo ne,hatta gaban goshinsa akwai suma a kwance,gashin jagirarsa kuwa tamkar an zanasa yana cike har suna kokarin hadewa waje daya,idan muka koma kan idanunsa kuwa sun kasance manya masu daukan hankali yana dauke da dogayen eyelashes, Allah ya ba shi kyawawan idanu masu girma da ga su so sexy da kuma tsoratarwa,farare tass da su me dauke da kwayar ido golding color masu shining kamar an kunna haske da kuma daukan ido.yana da dogon hanci me kyau da tsayi kamar pencil ga red libs din shi da suka kasance dan karami kamar ya shafa jan baki.fuskar shi na kewaye da wani irin kwantatciyar saje, da ya yi wa fuskarsa ado.
Hannunsa na hagu na sanye da wrist watch kirar Breguet wanda kudinsa yakai kimanin N=950000 dubu ɗari tara da hamsin.yayinda hannun dama shi ke dauke da wani bangule fashion designer ne silver color ya yi masa kyau sosai.


Zama ya yi akan daya daga cikin kujerun ya miƙa musu hannu suka gaisa ba tare da ya yi musu magana ba,nan suka fara tattaunawa akan abinda ya tara su a wajen.
"The Italian Mafia gangs sune abinda muka maida hankali akai suna da matukar hatsari, musamman boss din su da bamu san ya kamanin shi yake ba hatta su yan kungiyar ba su san wanene shugaban su, saboda ya kasance me wayo,basira da kuma basaja shisa har yau ba'a yi nasarar kama shi ba,su din yan ta'adda ne masu matukar hatsari.amma daga zaran an kama shugaban nasu to game din su yazo karshe,se wasa yakeyi da hankali hukuma domin yasan neman shi mukeyi ruwa a jallo!"duk wannan jawabin general din su ne yake yin su,su kuma sun kasa kunne suna saurarar shi.
Ci gaba da magana ya yi cikin harshen turanci"a cikin kwanakin nan mun samu update kan cewa yana Cameron so ya kamata kafin ya yi wani kokarin cutar da mutane ya kamata ya shigo hannun mu." "No!he is not in Cameron"ya yi maganar calmly yana kallon gefe duk zuba mishi ido sukayi,major general ne ya ce "how do you know that?"basarwa ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba. General ne ya ce"*LIEUTENANT GENERAL TAJUDDEEN* ka sanar da mu yanda akayi kasan baya Cameron"juyawa ya yi ya kalli major marry Johnson ta hannun damarshi ita ce duk inda zeje take tsaron shi wato sakatariyar shi kenan,cikin zafin nama tafito da wani ɗan karamin converter a aljihunta ta miƙa mishi sannan taje ta haɗa slide show ta koma ta tsaya.
Mikewa ya yi, ya taka izuwa inda slide show din ya ke yayi connecting din sa da converter nan take bangaren da yake ya koma kamar akwai tv awajan hoton katoton map ne ya bayyana.
Facing din su ya yi ya soma magana kamar ba yaso"last week anyi updating dina kan cewa shugaban Italian Mafia yana Cameron but dana sake bincike se na fahimci ya yi hakan ne ɗan ya juyar da tunanin mu akan inda ze je"jinjina kai sukayi sannan colonel general ya ce"to inde ba ya Cameron to yana ina!?" "He is in Nigeria!yaje Nigeria ne ɗan akwai wani mission din shi da yakeso ya yi accomplish amma bazan taɓa bashi wannan damar ba ni da kaina zan kamo shi in mishi hukunci mafi girma da azaba"tafa mishi sukayi suna yabawa kaifin basirarsa da kuma naciya akan aikinsa bugu da ƙari yana da ƙwaƙwalwa wacce take da kusan karfin computer yana da saurin nazartan abu da kuma hasasowa, gaskiya Allah ya yi wa lieutenant general Tajuddeen baiwa.


"LTG.Taj wannan case din yana hannunka ko ta wani hali muna bukatar shugaban Italian Mafia ko a ma ce ko a raye,all the best."cewar general,gyada musu kai ya yi sannan ya karbi sun glass din shi a hannun major Marry ya saka fita ya yi daga dakin binciken, major Marry na biye dashi abaya,sojoji birjik na gani ko ta ina duk inda ya wuce se an sara mishi sannan kuma su biyoshi a baya nan na fahimci nan din HEADQUARTER sojoji ne wa'yanda suke biyosu kuma duk sojojin sa ne,bude mishi motar akayi ya shiga sannan major Marry ma ta shiga. motocin da suka kai guda goma ne suka fita a cikin headquarter din domin zuwa gidan LTG.Taj.




Yana cikin mota kira ya shigo wayarsa dake rike a hannun major Marry dubawa ta yi cikin harshen turanci ta ce "Ammi is calling you LTG."miƙa mata hannu ya yi ya karbi wayarsa kirar iphone 15 pro max wanda kudinsa yakai 2.5million, ganin video call Ammi ke kiransa yasa ya yi picking.








Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.




Comment,like and share 🖋️🖋️


🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹




Page 16




*Story & written*


By




MRS🌹ISHAM🌹
( Yar lelen Jarumai)






*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹






📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️




Page 16


Cire sun glass din idonsa ya yi ya zubawa kyakkyawar fuskar Ammi ido, murmushi ta yi ganin shi acikin motar ne ya tabbatar da baya gida.


Slowly ya ce "Ammi kuna lafiya?"


"Lafiya klau Taj,yaushe zaka shigo Nigeria ne kam nagaji da zuwa ganinka,rabonka da gida yau shekaru goma kenan ka ƙi dawuwa!"ta yi maganar tana tsare shi da idanu.


Ba ze iya faɗa mata kan cewa yanzu haka ma yana shirin shigowa Nigeria ba ,saboda in suka san da zuwansa to zasu dame sa bazasu barshi ya yi abinda ya kawo shi ba.hakan yasa ya ce mata


"Very soon Ammi"sun danyi hira balaifi daga bisani suka yi sallama,ya yi dede da isowar su makeken gidansa dake cikin babban birnin Green bye Wisconsin.


Wa'yannan manyan samudawan ne suka bude mishi motar, major Marry ce ta fito ta tsaya, seda ya kusa mintuna uku sannan ya fito duk sara mishi sukayi. be bi takansu ba yawuce direct cikin haɗeɗen gidansa.
Babban gida ne me kyau da tsari komai na jikin gidan glass ne kama daga windows,kofofi,da kuma wasu bangaren jikin gidan glass ne,daga ta waje painting gidan light brown ne amma daga zaran mutum ya shiga cikin gidan , nan ne ze san anyi wasa da kuɗaɗe acikin wannan gida kamar ba'a so, painting ciki White color ne,falo yana da girman gaske ga manyan kujerun da suke ciki suma farare hatta carpet, chandelier light se kawo wuta kala_kala sukeyi,ga makeken tv dake manne a jikin ginin kamar tare aka gina gidan dashi,gefe daya na kuma wani wajene da aka tanadeshi dan shan dumi, idan ana sanyi wajan duk gilashi ne amma shi da kanshi ze kunna wuta ya bawa falon warm weather,iya haɗuwa falon ya haɗu,ga matattakalar bene dake falon wanda in mutum ya hau ze sadashi izuwa wajan lifter. anan zaka samu damar zuwa bangarori da suke dauke da wasu ɓangaren daban acikin gidan,suma wannan bangaren sun gaji da haɗuwa dan zan iya cewa ya mafi downstairs tsaruwa da hafewa.gidan LTG.Taj ya hadu ta ko ina innace zan tsaya zayyane muku irin kyawun gidan to fa ko page daya be ze ishemu ba.
Ya na shigowa falo ya cire armless vest din dake jikinsa ya rike a hannunsa ya haura stairs domin ya sada shi da lifter da ze kai shi part din shi.bayan lifter ya tsaya bedroom din shi ya shiga ajiye vest din ya yi akan gado sannan ya nufi toilet ya yi wanka ya fito daure da guntuwar towel daure a kugunsa nan ne nasake ganin ainihin zubin halittar jikinsa, farfadar kirjisa na dauke da wasu kwancecciyar suma mai laushin gaske sun yi luf_luf akan fatar kirjinsa haka daga abinda ya yi cinyar sa har izuwa ƙafafuwan sa akwai wayan nan kananun sumar nasu jan hankali, remote control ya dauka ya ɗanna nan take wani bangare daga cikin dakin ya bude ko ta ina gilashi ne ,a wajan shiga ciki ya yi,dakin kayan sawan sa ne kawai aciki komai wani irin nau'in kaya bangaren sa daban haka zalika bangaren uniform din shi ma daban,three quarter na company Dior designer black color yasa ka,ba tare da yasa riga ba ya fito daga dakin ya dawo bedroom din shi ya kwanta akan gadonsa.




Nigeria




Sauri_sauri ya ke tafiya saboda baze iya gudu ba, sakamakon raunin da ke ƙafar sa,burinsa shine ya samu wanda ze yarda dashi ya dauki wannan ma'adar memory card din,yabasa da yake tare da shi.waigowan da zeyi se yaga sun kusa cin masa acikin bakar motar hakan yasa ya faɗa cikin wani restaurant (cin abinci)da ba kowa aciki alamar sun tashi a aiki,ya buya a kasan table,haka wa'yanda suke binshi a motar suka shigo cikin wajan suka neme shi amma basu gan shi ba,fita sukayi a wajan cin abincin suka ci gaba da neman shi,nauyayyan a jiyar zuciya ya sauke ya fito daga kasan table din yana goge zufan da ke kan fuskarsa.fito da memory card din ya yi yana tunanin waye ze bawa wannan memory, saboda duk mugun shirin su ya rigada ya yi recording a ciki.kallon ƙafarsa ya yi da yake daure da rigarsa gudun kar jini ya dinga zuba saboda harbin bindigan da suka mishi, amma da yake gudun ceton ranshi ya keyi hakan yana mishi jin raɗaɗin da karfasa yakeyi.


Motsi yaji a bayan shi hakan ne yasa ya juya, daya daga cikin ma'aikatan restaurant din ne, kallon tuhuma take bin shi dashi kafin ta ce "Malam daga ina!?kuma ne kake yi a ciki nan a irin wannan lokacin!?" "Ki taimake ni in kwana anan,wasu ne suka biyo ni zasu kashe ni."cikin tsoro ta ce "what!!su waye su din kuma meye alaƙar ka da su!?"be iya ce mata komai ba se ma runtse idanunshi da ya yi ganin hakane yasa ta rike hannunsa ta taimaka mishi suka shiga can ciki wani dakin dake cin restaurant din ta taimaka mishi ya kwanta, warware rigarsa daya daure ƙafar dashi ta yi,ganin harbin bindiga ne yasa duk ta rikice ga shi ita ba doctor ɓace ɓalle ta cire mishi harsashin.
Shi ya dinga faɗa mata yanda zata yi har ta cire harsashin yana ƙaran azaba itama tana kuka saboda ba aikin ta bane,bayan haka kuma mata suna da matuƙar rauni.






Wayewar garin yau ne Fu'ad ya fara shirin tafiya ji yakeyi kamar kar ya tafi saboda har ya fara kewar su Sabriyah da Asmita duk da ya musu alkawarin ba ze daɗe ba ze dawo, sannan babu yanda be yi da Sabriyah kan ze siya musu gida su bar afafa ba, amma fir ta ƙi ta ce ita babu in da yafi mata can dinm hakan yasa babu yanda ya iya ya kyaleta ya dauki makudan kuɗaɗe ya basu.
Fitowa ya yi da trolley din kayansa ya samesu a falo suna zaune, mikewa sukayi da suka ga yafito su ma da nasu trolley din su a hannu.karewa Sabriyah kallo ya yi daga sama har ƙasa tana sanye da wandon jeans crazy blue color,se riga me daguwar hannu me high neck white color gashin kanta ta sa'ke su a bayanta murmushi ya yi ya ce "Sabriyah kinyi kyau sosai"ba ta bashi amsa ba illa murmushi kawai da ta mishi .duk babu dadi takeji domin sabo turkin wawa ne.fitowa sukayi daga hotel suka shiga motar shi yakai su har afafa,fitowa sukayi daga motar suna wa juna bye_bye,se da ya tabbatar sun shiga cikin gidan sannan ya wuce, komawa hotel din da ya baro ya yi, ya canza daki daban ya kama wani.wasu mutane ne sukayi knocking ya je ya buɗe musu kofar, wasu zabga_zabgan matasa ne su bakwai suka shigo dakin ko ina na jikinsu a murde yake wani irin alama sukayi da hannunsa alamar girmamawa gyada musu kai kawai ya yi,kallon su ya yi cikin harshen yaren French ya ce "kun kama shi ne!?"dayan su ne ya ce "ah ah ya ɓace mana amma ko ta halin ƙa'ƙa se mun kama shi domin inde wannan daukan ya fita shirin mu ya tashi a banza!" "To ku gaggauta yin hakan, in kuma ba haka ba ku fuskanci hukunci,domin ya riga da ya kwashi duk wani sirrin mu a cikin wannan daukan da ya yi.gobe zan bar Nigeria ku tabbatar kafin in tafi kuzo mini da albishirin kun kasheshi."ya gama maganar idon shi na kansu. Sa'ke yin wannan alamar sukayi kafin dukkansu suka haɗa baki wajan faɗin "we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union."suna gama fadin hakan suka fita acikin dakin hotel din suka tafi.


A bangaren su Sabriyah kuwa ko da suka shiga ciki basu samu Anty Teema ba,zama sukayi acikin dakin suna ta hiran irin kyautatawar da Fu'ad ya musu.wayar Asmita ne ya yi ƙara dubawa ta yi taga saurayinta Taheer ne hakan yasa ta dauka tasa a kunne hira sukayi sosai har take sanar dashi sun dawo afafa.


Se karfe biyu na rana Anty Teema ta dawo jin kamar motsin sune yasa ta leka dakin nasu tun daga bakin kofar dakin ta fara magana "in ya!!, yara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login