Showing 27001 words to 30000 words out of 94974 words
"Fu'ad I promi....."kafin ya karasa maganar shi afusace Fu'ad ya waigo ya kalleshi ya ce"get the hell out of my room I said I don't wanna see you kafice min da gani kawai"Abubakar Daula sanin halin ɗan nashi ne in be samu abinda yakeso ba yanzu se ya kusan tayar mishi da karamin haukanshi hakan yasa ya fice simi_simi a dakin.
Bin bayan shi da mugun kallo Fu'ad ya yi kafin ya daga kai ya kalli celling din dakinshi da karfi ya ce"shin kina ina neeeeeeeeeee Asrah? aina zan ganki?waye ya sace mini future wife dina Wallahi koma waye se ya yi da nasani arayuwarshi domin ni Fu'ad Abubakar Daula bazan taba kyale shi ba"
Kamar wani zararre haka yake magana kamar da wani a dakin, juyawa ya yi ya kalli yamma da kudu sannan ya ce "noooooooo! bazeyu ba ni Fu'ad Abubakar Daula nayiwa kaina alkawarin ni zan fara ganin Asrah komin daren daɗewa se munga juna,bazan taɓa bawa Tajuddeen damar samunta kafin ni ba,dole nine zan fara nemo Asrah sannan in aureta.tabbas hakan ne ze faru hhhhhhhhhhhhhhhhh"ya gama maganar yana kecewa da wata mahaukaciyar dariya.tabbas Fu'ad yana da matsala a kwakwalwar shi wanda shisaka komai ya yi yake ganin a dede yake.
Tofa ana wata ga wata dukkanin su biyu sun daukarwa kansu alkawari me girman gaske wanda .....
Fu'ad Abubakar Daula ya yi wa kanshi alkawarin shi ze fara samo Asrah,shi ze fara haɗuwa da ita komin daren daɗewa.
A yayinda Tajuddeen Mubarak Bishara ya dau wa kanshi alkawarin shi ne ze dawo da Asrah cikin rayuwar gidansu shine nan ze kawota gida komin daren daɗewa.
Shin waye ne ze fara haɗuwa da Asrah a rayuwa?shin Asrah zata rayu?shin su Hajiya hurairah da Hajiya khareema zasu cimma burinsu?.
Ku biyoni domin jin yanda zata ka ya.
*LAGOS*
A FAFA
Anguwar afafa, Babban anguwane da ya amsa sunansa acikin Lagos inde harkan karuwanci ne tofa babu inda yakai afafa babu irin tsiyar da ba'a tsulawa awannan wajen daga karuwanci,damfara,sata,yan rawa,shaye_shaye safaran mata ,renon kananan yara su girma suma ajefasu a harkan karuwancin manya_manyan jiga jigan karuwai ne a wajan,duk wanda yashigo wannan anguwar tofa yasan babu mutanen kirki aciki sede ko shima holewa yazo ayi dashi,gidajen karuwai ne birjik da gidajen gala komai anayi a Afafa,duk inda zaka wuce sekaga mata atsaye ko azaune dukkansu babu me kayan arziki ajikinsu ga masu shaye shaye agefe wasu kam ma a kan hanya suke baɗalarsu gurine na yar iska da dan iska , wucesu nayi na nufi inda naga yafi kyau awajen shiga nayi nafara tafiya ina kalle_kalle har idona yasauka akan wata ƙatuwar kofa me labulaye kamar makaroni ga hayaki dake fitowa awajen , ciki na nufa ina lekawa wasu yan mata nagani cike a babban falon dukkansu baza su wuce irin shekara sha sha takwas ko sha tara wasu na shan shisha gamasu shan w'iwi ga wasu can agefe suna can suna biyawa kansu bukata lesbian wa'iyazubilllahi abun ba kyaun gani .
magana na faraji da ɗan karfi hakan ya nuna me maganar nan tabbas tana da babban murya, hankalina ne ya rayamin da inje inga wacece haka ,dakin na shiga na leka kaina.wata rusheshiyar mata nagani katuwa ce tana da jiki sosai ga kuma tsayi gata munmuna baƙa tana hakimce akan kujera ga wani namiji na tsaye akusa da ita suna magana da alamun masifa take surfa mishi , sake zura kaina nayi aciki wasu yara ƙanana nagani wasu na zaune wasu kuma suna kwance masu kuka nayi yarane da akalla sun kai goma, ji nayi tana faɗin" Mark dama kai bagidaje ne bansaniba tunda nake dakai ka taba jin na siya yarinya da kudin da yakai duba dari bakwai ? amma dake bakasan muhimmancin kuɗi ba shine zaka batamin kudedena kasiyo yara masu mugun tsada har guda biyu ko? to acikin sallamarka, nunamin wacce ka siya dubu dari bakwai din inganta" shide duk masifar da take mishi yana tsaye kanshi a ƙasa saboda itace shugaba acikin Afafa magajiyar karuwai kenan sunanta boss lady ko kadan bata wasa inde ta kan kudine bata da tausayi ko kadan, sa hannu ya yi ya jawo mata Asmita da tashinta daga bacci kenan ta cigaba da kuka, kaita gabanta ya yi ya ajiyeta kare mata kallo ta yi ɗakyau daga sama har kasa, sosai taga Asmita tayi mata kyau, kallonshi ta yi ta ce"Allah yataimakeka da ace ba kyakkyawa bace wallahi da se kaga yanda zanyi dakai !fito min da wacce kasiya har million daya inganta" murmushi Mark ya yi jin uwar dakin nashi ta yaba mishi da taga Asmita yasan muddin ya nuna mata Asrah tofa zaucewa za tayi har ta ƙara mishi kudi, wajan Asrah dake kwance tana bacci bata farka ba yanufa yasa hannu ya ɗagota yakaita gaban boss lady.
Boss lady na kyallara idonta Akan Asrah seda yasa ta mike zaune daga kishingiden da take , a iya tarihin Rayuwar ta na karuwanci dakuma safaran yara ba'a taba kawo me kyau din Asrah ba sede masu madedecin kyau amma Asrah makurace , sa hannu tayi ta shafa fuskarta tana "wowwww! Mark aina ka samu wannan zazzafar yarinyar?" Bayanin komai ya yi mata kamar yanda su black suka faɗa mishi kuma ya faɗa mata kancewa yar Bishara family ne tsohon gwamnan jihar Borno, sannan ya sanar da ita koda ta tashi bazata iya tuna komai na rayuwarta ba , duk abinda aka faɗa mata dashi zatayi amfani , boss lady bata tabajin dadin aiki da Mark ba irin yau domin wannan yarinya mudin ta girma tasan zata samu maƙudan kuɗaɗe da ita.
Karawa Mark kudi ta yi sannan ta sallame shi ya tafi, har lokacin tagagara dena kallon Asrah, da muryanta me kama da anbuga ganga ta kwala musu kira " Teema baby da Rash baby duk kuzo nan "tana gama rufe bakinta wasu yan mata suka shigo dagasu se pant da breziya ƙafafunsu na sanye da sarka.
Teema baby da Rash baby su kansu seda Asrah ta tafi da imaninsu ga kuma Asmita itama kyakkyawa da ita.
"Kunga wa'yannan yara guda biyun?so nake tauraronsu ya daukaku sosai a idon duniya, musamman wannan kyakkyawar.duk wani salon karuwanci da damfara,sata,salon duk wani makirci da kuma salon yaudara kuyi musu training na musamman ku koya musu rawa kuma ku kula dasu domin da kudi masu yawa na siyesu, so nake su taso da farin jini na daban acikin duk wasu karuwan dake gidan nan, Teema zoki tasheta har yanzu tana bacci"tashinta Teema ta yi , tashi Asrah ta yi ta zauna tana mutsutsuke idonta alamar baccin be ishe ta ba , turo bakinta ta yi gaba fara ƙarewa dakin kallo ta yi kafin tafara kallonsu ,kallon_kallo aka tsaya yi tsakanin ta dasu, tana kallonsu kamar idonta ze faɗo ƙasa so takeyi ta tuna aina tasansu amma tagagara tuna komai , shafa mata kumatu Teema ta yi" tace yanmata meye sunanki ?" Kallonta Asrah ta yi tanason tuna sunan nata amma ta gagara hakan yasa ta ce" bansaniba" murmushi boss lady ta yi ta ce"ɗakyau Teema samo suna me dadi ki saka matashi" nisawa sukayi kafin Rash baby ta ce" asa mata Sunaya ,yayi ?"girgiza kai boss lady ta yi alamar ko kadan sunan be mata dadi ba , ganin hakane Teema baby ta ce" to adinga kiranta da *SABRIYAH* sunan ya yi ko boss lady?" murmushi boss lady ta yi ta ce"sosaima kuwa ya yi dadi" kafin ta kalli Asrah da itade kawai da ido take binsu ta ce" daga yau sunanki shine *SABRIYAH* ,faɗa inji" gyada mata kai Asrah ta yi ta ce" daga yau sunana *SABRIYAH*" murmushi boss lady ta yi da su Teema, sannan ta maida kallonta kan Asmita da tazuba musu ido tana kallonsu , boss lady ta ce "ke kuma menene sunanki"a dan tsorace Asmita ta ce" sunana Asmita"
"Ku daukesu kuje dasu sashinku ku basu daki daya su biyu,ku musu wanka ku basu abinci zan turo da kayan su, sauran yaran kuma su ma za'a zo a kwashesu" cewar boss lady , riƙe hannun SABRIYAH Teema baby ta yi ita kuma Rash ta riƙe hannun Asmita suka nufi sashin su. Wanka suka musu sannan suka basu abinci me kyau suka faraci , tana cikin cin abincin ta shaƙe tafara tari kamar zata mutu dakyar ta iya furta"wayyo Tajujuna zan mutu" ruwa suka bata tasha Teema tana shafa bayanta seda ta gama tarin kafin , Teema ta ce"Sabriyah waye kuma Tajuju ?"shuru ta yi tanason tuna me sunan amma ta manta amma daga zaran ta rufe idonta kanta take gani da wani saurayi kyakkyawa suna zane dasauri ta bude idonta ta ce "nima bansan waye ba" abincin da bata karasa ci ba kenan ta tashi tahau gado ta kwanta, ficewa adakin sukayi dan su barsu su huta, kuka Asmita tafarayi tanajin tsanan mahaifinta na shiga cikin zuciyarta, jin kukanta ne yasa Sabriyah ta ɗago kai ta kalleta saukowa ta yi akan gadon ta zauna akusa da ita ta ce"meyasa kike kuka?" Kallonta Asmita ta yi ta ce"babana ne ya siyar dani awajensu yarabani da mamana" " to kidena kuka wata rana zakije gurinsu " gyada mata kai Asmita ta yi ta ce"kema ai siyar dake akayi"girgiza mata kai ta yi tace "to aini banida kowa, Tajuju kadai nake iya gani a idona"ta yi maganar cike da yarinta kamar zatayi kuka.sannan tana me rufe idanun nata sosai rayuwarta da Tajuddeen ya dinga mata flash a ido musamman lokacin da suke zane tana hango kanta tana zanen hoton Tajuddeen komai na rayuwarta dashi tana ganin shi afuskarta da kuma shi din bayanshi kuma bata ganin kowa a ahalinta .kallon abin hannunta ta yi ta kafeshi da ido tana kallo sannan ta yi murmushi ta ce" nasan wata rana zakazo gareni tajuju"
rike hannunta Asmita ta yi ta ce"to daga yanzu munzama kawaye sosai ko"Sabriyah ta ce"eh"."to Kinga basa nan kizo mu gudu kinji"Asmita ta yi maganar tana riko hannun Sabriyah ta fara janta saboda Asmita ta tsani wajan fitowa sukayi daga dakin basu haɗu da kowa ba lokacin har duhu ya fara yi.lungu_lungu suka fara bi domin guduwa har sun kai bakin gate se suka ga an rigada an datse kofar fita din ga shi sunyi nisa da inda suka baro ga garin hadari ne ya kankama sosai nan take iska yafara tashi aka fara yayyafi suna damƙe da hannun juna tsoro ya gama kamasu ganin yanda ruwa lokaci daya ya fara sauka kamar da bakin kwarya basu da wani option da ya wuce su koma.haka suke tafiya a yayinda ruwa ke yi musu mugun duka nan take jikin su ya soma rawan sanyi musamman ma Sabriyah hatta harshenta karkarwa yakeyi domin ita yar hutu ce bata saba da irin wannan rayuwar ba tafi sabawa da rayuwar ac da air conditioner.a hanyar su ta komawa sashin da suka baro suka mance daga ina suke suka dinga dabur_dabur ga ruwan na dukansu kuma har izuwa lokacin basu samu wajen fakewa ba zubewa akasa Asrah ta yi ga ruwa dake wucewa akasan kamar karamin kogi dungulewa ta yi waje daya tana kuka da iya karfinta har muryanta ya koma dishi_dishi Asmita zama ta yi kusa da ita itama suka hadu suna kuka har na kusan minti biyar kafin daga bisani ta ji Asrah ta yi shuru . matso da fuskanta dede da nata ta yi taga idonta arufe ga shi bata motsi dake yarinya ce se ta yi tunanin Sabriyah din bacci ta yi.haka suka kasance a wajen su biyunsu babu kowa.
Teema baby da Rash ne suka shigo dakin nasu domin dubasu ko akwai abinda suke bukata amma da mamaki se suka ga babu su a dakin hakan yasa suka dauki lema da torchlight suka fito suna dudduba su har suka hangosu da sauri suka isa inda suke bakaramin tashi hankalinsu ya yi ba ganin halin da suke ciki ba ga Sabriyah dake sume a ƙasa cikin ruwa cikin rudewa Teema baby ta ce "Asmita meya fito da ku awannan ruwan?me ya sami Sabriyah?"ta jero mata maganar a yayinda ta sa hannu ta dauki Sabriyah din ta saɓata a kafardata, Asmita dake rawan sanyi kuwa bata samu damar bata amsa ba haka suka koma sashin su kwantar da Sabriyah Teema baby ta yi akan gado ta cire mata kaya da sauri haka Rash ma ta canzawa Asmita kaya har lokacin Sabriyah bata farfaɗo ba hakan yasa Teema baby ta dauki lema ta nufi bangaren boss lady domin sanar da ita halin da ake ciki.sosai ran boss lady ya ɓaci wato yaran so suke yi su gudu ta yi asarar kuɗinta kenan jinjina kai ta yi a ranta ta ce"zan yi maganinku" kafin ta daga waya ta kira wani doctor ta sanar dashi akwai mara lafiya in ruwa ya dauke yazo ya dubata kafin ta kashe wayar ta juya kan Teema baby ta ce "ku kuna ina lokacin da su ke kokarin guduwa?nace kuna ina ?ko ba cewa nayi ku kula dasu ba kuɗi da yawa nasa na siye su da ace kudi kaɗan ne ko mutuwa sukayi Ni bazan damu ba amma bazeyu inyi asarar wa'yannan yaran ba,amma dake ku din ballagazazzu ne ga shi kun barsu suna shirin guduwa to wlh duk sanda yaran nan suka sake kokarin guduwa Teema abinda zan aikata agareki se kinyi da nasanin rayuwarki.banza kawai ɓace mini da gani ko na dauke ki da mari wa'yanda basu san darajan kuɗi ba" sosai idanun Teema baby ya cicciko da ruwa ta bar sashen boss lady da sauri tana me tausayin rayuwarta da kuma sauran da suka tsinta kansu acikin wannan halin nan ne ta sake jin kaunar Sabriyah aranta sosai domin yaran tunda ta gansu dazun taji tana mugun tausayinsu kuma ta yi alkawarin zata kula dasu sosai.
Wannan kenan,bayan ruwa ya dauke likitan da boss lady ta kira yazo ya duba Sabriyah kuma ya gano ta kamo da (pneumonia) nimoniya hakan yasa ya rubuta mata magani sannan Asmita ma ya rubuta maganin mura sannan ya kara musu da kar a dinga barin Sabriyah tana mu'amala da ruwa sosai musamman ma me sanyi Sannan ya tafi abinshi.
Washe gari se karfe goma Sabriyah ta farka daga bacci Teema baby ne a dakin se Asmita ruwan wanka ta daura ta mata wanka da ruwan zafi ta haɗa mata shayi da biredi yanda Asmita ta karya.
Bayan ta gama ne tabata magani ta sha haka Teema baby ta dinga kulawa da Sabriyah hatta warware.
Bayan sati daya su Asmita, Sabriyah sun shaƙu sosai da Teema baby da Rash kamar da can sun san juna haka suka koma kiran su da anty Teema da anty Rash,dake sun samu masu ɗebe musu kewa har sun fara sabawa da wajan kuma har zuwa lokacin boss lady ba ta zo ba.
Yau ma suna zaune Sabriyah na gaban anty Teema tana yi mata kitso amma dake gashinta yanada tsantsin gaske se yaƙi kitsuwa haka ta gyara mata gashin,agefe daya kuwa anty Rash ne da Asmita suna kwance suna baccin rana akan katifa,basuyi tsammanin zuwan boss lady ba kawai ganinta sukayi akan su"ke Teema baby tashe min Rash da wancan yarinyar"tashi anty Teema ta yi taje ta tashi Anty Rash mikewa sukayi suna gaisheta ta amma sannan ta maida kallon ta kan Sabriyah da Asmita ta ce"wato naji kuna kokarin guduwa ko? warning nazo muku duk sanda kuka sake yunkurin gudu karnuka zan sa su biku su cije ku,su cinye naman ku har se kun mutu.kun ga wannan gidan duk wanda ya shigo gidan nan baya fita har abada sede ko in mutuwa ya yi,to nan gaba in kuka sake yunkurin guduwa mutuwa zakuyi kunde jini ina?."cike da tsoro sukace mata to sannan ta ce wa Anty Rash"kizo ina neman ki."
Bayan fitan su ne Anty Teema ta sake musu faɗa ta ce kar su sake kokarin guduwa.
Haka su Sabriyah da Asmita suka ci gaba da rayuwa a gidan karuwai tare da yaran da aka kawo su tare har an fara musu duk wasu training din da boss lady ta ce ayi musu salo kala _kala ana koya musu tun suna ganin abun wani iri har ya bi jikinsu.
Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.
Comment,like and share 🖋️🖋️
https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹
Page 12
*_ story & written_*
By
*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)
*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️
Page 12
*This is just the beginning*
AFTER TEN YEARS OF LIFE (bayan shekaru goma na rayuwa)
Gidan rawan cike yake da mutane maza da mata ga manyan mutane masu zuwa daukan yanmata suje su kwana dasu,in banda filin da za'ayi rawan babu wani space aciki ko ina damke yake da mutane kowa so yakeyi yaganta yakuma ga rawanta na musamman da takeyi me daukan hankali,shisa duk karshen sati suke biyan kudi suzo su ga rawanta,kamar yadda aka saba yauma karshen sati ne ranar Lahadi kenan karfe 8 nadare, duk sun zauna ita kawai ake jira ta karaso.
Kunna wata wakar India akayi wanda nora fatehi tayishi me suna kusu_kusu.
Cike da yanga take tafiya jikinta se juyawa yakeyi kamar wata macijiya,tundaga tafin kafarta nafara ƙare mata kallo har sama.
Kalar fatarta fara ce irin farin nan mai kyau da tafiya da hankali babu mis ko ta ina fari sumul ga jikinta da se sheki yakeyi , doguwa ce amma ba can sosai ba matsagaiciya ,Siririya bata da jiki sede akwai shape sosai tana da hips ga kirjinta dake cike taf da tula_tulan dukiyar fulani suna atsaye se daukan ido suke ,cikinta a shamule yake sosai kamar wacce batacin abinci, komar da kallona nayi izuwa