Showing 21001 words to 24000 words out of 94974 words

Chapter 8 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8660

hakane ranka ya dade Nagode sosai" sa Asmita sukayi a motar suka zuge gilas din motar tana kuka kamar ranta se fita ko ajikinsu suka ja motar suka tafi , se da sukayi nisa da suka ga kukan nata ze damesu suka shaka mata wani abu a hanci nan take bacci ya kwashe ta. ( kai rayuwa abin tsoro ne Allah karabamu da sharrin zuciya. )


Hankali kwance malam Mamman ya koma gida seda yakusan isa gidan tukun ya zuba kasa a jikinshi ya yi futu_futu yakoma kalar tausayi ya shiga gida abakin kofa yasamu Maryam ta doka uban tagumi tana jiransu ganin ya shigo shi kadai ne yasa ta mike tsaye dasauri ta ce" malam har kundawo ? yana ganka kai ɗaya ina Asmita?" Goge guntun hawaye ya yi ya ce" Maryamata munje munkai dinki mun fito zamu dawo taga yar baby ta ce ina siya mata acikin rububin mutane na nemi Asmita na rasa neman duniyar nan na mata amma ban gantaba" kukan kura Maryam ta yi ta cukumi wuyan malam Mamman" karya kakeyi dan iska munafuki mara tsoron Allah wallahi seka fito min da ƴata dama tunda naga ka fara son yarinyar nan zuciya ta ya rayamin wani abu mugu azzalumi kaje ka salwantar min da rayuwar yarinya " duk wannan maganar da takeyi da karfi takeyi tana kuka kuma tana damke da wuyan malam Mamman da iya karfinta, makobtansu jin hayaniya ya yi yawa yasa suka shigo , matan ne sukaje suka samu suka raba Maryam ajikin malam Mamman faduwa kasa ta yi tana kuka da birgima abin tausayi wannan zafin uwa ce kadai zatasan zafinshi in aka rabata da ɗanta .
Ɗagata sukayi suka kaita ɗaki suna tambayar ta abinda yafaru dakyar ta isa sanar musu su kansu hankalinsu yatashi nan take aka bazu aka fara neman Asmita hade da yin shela acikin garin damaturu.


*MAIDUGURI*


Suna dawuwa gida ko part dinsu bataje ba ta nufi part din Tajuddeen , ya fito daga painting room kenan ya ji an rungumeshi durƙusawa ya yi ya iso tsayinta yana ƙare mata kallo sosai ta yi kyau da uniform din slice smile ya yi ya ce" kinyi kyau" fari ta yi da ido ta rike kugu ta ce " tajujuna let's go and play on the field" be bata amsa ba yaje jikin bedside locker ya ɗauko wata hadaddiyar camera hoto yake so ya yi mata saboda uniform din sunyi matukar yi mata kyau sosai ɗaukanta a hoto yafara se iyayi take zuba mishi shi kuma yana snapping dinta se da ya gaji dan kanshi kafin ya ce" okay go and take up your uniform" tanajin haka ta fita da gudu zuwa part dinsu. uncle Hameed na kokarin fita yaci karo da ita " Asrah har kun dawo ?" Gyada mishi kai ta yi sannan ta ce" Daddy ka ciremin uniform dina zamuyi wasa da tajujuna " janta ya yi bakin kujera ya zauna ya ajiye wayoyin hannunshi ya cire mata uniform din sannan ya dauketa yaje ya mata wanka yasa mata kaya marasa nauyi ya ce " to adawo lafiya" tun be karasa cewa komai ba tafita da gudu tana mishi bye-bye murmushi ya yi sannan ya koma ya canza kayanshi dan ruwa yaɗan taɓa shi da ya mata wanka.


Wasa sukeyi a field din dagashi se ita yana koya mata gudu tun tana iya yi harta gaji tana zauna a tsakiyar filin tana turbune fuskanta daukar ta ya yi yasata awuyanshi suka koma ciki .




Kowa ya gama cin abinci sun gama abinda zasuyi har sun shiga ciki an kwanta se kuma asuba ta gari .








( *BISHARA'S FAMILY MEMBERS*)


*KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN AHALIN BISHARA*




Mubarak Yousuf Bishara shine babban ɗa awajan Yousuf Bishara, Mubarak Bishara shine tsohon gwamnan jihar Borno yanada mata uku,matar shi ta farko ita ce Hajiya Badeeya sunyi auren soyayya da ita duk da lokacin mata biyu ze aura saboda yana soyayya da Hajiya hamdiyya to se aka fara auren shi da Hajiya Badeeya bayan kamar wata uku
Kuma ya auro Hajiya hamdiyya tsakanin Hajiya Badeeya(Hajiya babba) da Hajiya hamdiyya (Ammi) akwai kyakkyawar fahimta suna zaman lafiya sosai kusan a tare suka samu ciki sede Hajiya babba ce ta fara haihuwa ta haifi ƴarta mace aka sa mata suna Sakeena bayan wata ɗaya Ammi ta haifi ƴarta itama mace taci suna Sameera tare suka taso yaran suna son junansu sosai saboda ganin yanda iyayen su suke zaman lafiya bayan shekara uku Hajiya babba ta sake samun ciki ta haifi na miji Aka sa mishi suna Abbas tana cikin renon Abbas ciki ya bullo tanaji tana gani tayi ciki da goyo wata tara ta sake haihuwa ta haifi na miji shima aka sa mishi suna Ahmed ,tsakanin Abbas da Ahmed be wuce shekara ba. ana haka Abbie ya sake aure ya auri Hajiya khareema tundaga nan ne kuma zaman lafiyan gidan yafara ƙaranci saboda Hajiya khareema ta tsani a zauna lafiya kuma ahakan ma Ammi da Hajiya babba basa biye mata, Hajiya khareema itama ta haife ɗanta na miji aka sa mishi suna Hafiz shekara daya da rabine tsakanin su da Abbas da Ahmed.


har izuwa wannnan lokacin Ammi bata sake samun wani cikin ba saboda dama planning takeyi domin karatun da takeyi bata so ta samu ciki ya ka tse mata karatu. Su Abbas nada shekaru huɗu kwatsam se ga ciki ya bayyana ajikin Ammi tunda ta fahimci tana da ciki ta fara kokarin ganin ta zubar dashi batare da kowa yasan akwai wannan ciki din ba,duk wani nau'in maganin zubar da ciki Ammi seda tayi amfani dashi amma ciki yaƙi fita yana zaune daram dam_dam hakan yasa ta tsani cikin kamar ranar mutuwarta,yanke shawara ta yi domin zuwa asibiti a yi flushing din cikin kawai nan ne doctor da taje wajen shi ta faɗa mishi abinda za'a mata shi kuma ya kira Abbie ya sanar dashi abinda take shirin aikatawa sosai ran Abbie ya ɓaci yazo asibitin ya sameta ya dauketa suka koma gida nasiha ya yi mata akan abinda takeson yi amma ta rufe ido ta nuna mishi ita batasan wannan ciki saboda karatunta yafiye mata shi.hatta Hajiya babba babu irin shawaran da bata bawa Ammi ba amma haka taƙi sauraran su hakan kuwa ya jawo musu babban saɓani ita da Abbie.wanda har ya kusa jawo sanadin aurenta wanda se da yakai manya sun shiga cikin lamarin acikin wannan matakin da ake ciki Isma'il Yousuf Bishara (Abbu)wato ƙani agun Abbie ya yi aure ya auri Hajiya hurairah.
Ammi babu yanda ta iya domin manya sunyi magana badan ta so ba haka ta reni wannan cikin amma inta kalle shi kamar ta sa wuka ta tsaga cikin ta fito dashi yabar jikinta takeji.ranar da ta haifeshi juyin duniya anyi amma taƙi ta bawa wannan jaririn nata nononta ɓacin rai da takaici ne yasa Abbie ya saki Ammi saki daya,hakan ne yasa ta nutsu bata tafi ko ina ba tana gidan saboda jegon da takeyi Hajiya babba ce tasamu ta shawo kanta da kyar ta fara shayar da shi ranar suna yaro yaci suna *TAJUDDEEN* nan ma da kyar aka samu Ammi ta yi hoto dashi a ranar sunan.haka Ammi ta dinga nunawa yaron nan tsana da kuma halin ko in kula in yana kuka ko kadan bata damu da daukan shi ba.Tajuddeen nada wata uku Hajiya khareema ta sake haihuwa ta haifi yara yan biyu maza wato Salim da Sahil bata jima da haihuwar su ba Hajiya hurairah ta haifi na miji itama aka sa mishi suna Sudais duk babu rata a tsakanin su.
Hajiya khareema ganin Ammi bata wani damuwa da Tajuddeen yasa ta daukeshi taci gaba da renon su tare shida su Salim da Sahil nan ne tasamu daman cusawa yaron ƙiyayya,tun yana karami kullum se ta faɗa mishi yanda aka sha fama da Ammi kafin ta yarda ta haifeshi har ya zama wa Tajuddeen kamar karatu kullum se ta maimaita mishi domin so takeyi maganar ya samu guri ya zauna dam acikin zuciyarsa.aikuwa haka akayi yaro yafara girma da wasu irin murɗaɗɗun hali da shegen taurin kai wanda ko ita kanta uwar riƙon nashi bayayi mata magana sosai ita dasu Abbie se suka fara tunanin ko de bebe ne baya magana.domin har ya kai shekara hudu baya wani magana kuma lafiyarsa kalau.daga wa'yannan shekarun ne fa Ammi ta fara kokarin jawo shi ajikinta domin farat daya taji son ɗan nata ya shiga xuciyarta lokacin tana da cikin jawan sede time is too late Hajiya khareema ta riga da taci nasara akanta domin ta juyawa Tajuddeen tunani ta hanyar makircinta ko da Ammi ta kira shi ba ya zuwa ko kusa da inda take hakan yasa hankalin Ammi yafara tashi danasani yafara ɗawainiya da ita.


Kusan tare suka sake haihuwa Hajiya hurairah ta sake haihuwan namiji me suna Saghar,Ammi kuma ta haifi santalelen yaronta me kama da Tajuddeen wato Jawan.
Haka rayuwa yaci gaba da tafiya.bayan wasu shekaru uncle Hameed ɗan karamin ƙanin su Abbie ya yi aure ya auri kanwar Ammi wato Abida bayan anyi aurensu ta samu ciki kusan sau uku amma suna zubewa sakamakon matsala da take dashi a mahaifarta.daga karshe de itama atare duk su hudun suka samu ciki abun burgewa kamar wa'yanda suka haɗa baki.yaran mata dukkansu suka haifa,hajiya babba ta haifi Rameesa,Ammi kuma ta haifi Umaisha,Hajiya khareema kuma ta haifi Iklas, Abida da suke kira da anty amarya kuma ta haifi kyakkyawar ƴarta aka sa mata suna *ASRAH* amma sede ba a Nigeria ta haife ta ba saboda bayan aurensu basu jima ba suka koma California da zama saboda aikin uncle Hameed.Hajiya hurairah ta haifi Zoya haka suka reni ya'yansu cike da so da kauna bayan shekara ɗaya Hajiya hurairah ta sake haihuwar ya mace me suna Parsa.




*WANNAN SHINE KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN AHALIN BISHARA SE NAN GABA ZAN KAWO MUKU SAURAN TARIHIN NASU NAN NE ZAKUJI LAIFI NA BIYU DA AMMI TA SAKEYIWA TAJUDDEEN DA YASA HAR YA ƘULLA CE TA*




Mubarak Bishara tsohon gwamnan jihar Borno yanada mata uku ...


Matarshi ta farko ita ce Hajiya badeeya tana da yara kamar haka
Sakeena ita ce babba se Abbas se Ahmad, Rameesa.




Se matarshi ta biyu ita ce ta Hajiya hamdiyya tanada yara hudu sune...
Sameera se Tajuddeen , se kuma jawan se yar autarta Umaisha.




Se matarshi ta uku ita ce Hajiya khareema yaranta sune
Hafiz , se twins Sahil da Salim sekuma Iklas.




Alƙali Isma'il Bishara matarshi guda ɗaya ce


Ita ce Hajiya Hurairah tanada yara hudu sune .. Sudais, Saghar,Zoya ,parsa






Doctor Abdulhameed Bishara matarshi daya tal tilo ita ce Abida suna da yarinya sunanta Asrah.




*Karku manta da hakan*






Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.




Comment,like and share 🖋️🖋️


🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




Page 10




*_ story & written_*

By




*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)


*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*








🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️





Page 10






Yau babu inda sukaje ana hutun public holiday ba makaranta suna gida se rashin ji da suka ishi mutane dashi ga ɓarna kala da iri da sukeyi suna ɓatawa fatime da kaltume suna gyarawa , Ammi , Hajiya babba da anty amarya kuma basa gida sunje gaishe da kanwar Hajiya babba tayi rashin lafiya kwananta biyu a asibiti shine sukaje gaida ita Abbie kuma ya tafi meeting da ministan tsaro Abbu na kotu haka uncle Hameed ma yatafi hospital daga Hajiya khareema ( Ammuh sunan da suke kiranta kenan ) se Hajiya Hurairah (ummah suke ce mata ) su kadai agida se yaran Abbas hayaniyarsu ya dameshi hakan yasa ya musu magana amma sun ƙi de nawa da ya gaji kawai ya kwanta akan kujera ya zuba musu ido , musamman Asrah da Zoya da Umaisha,parsa sunfi kowa ƙin ji , Hafiz da Ahmad kam ma sun gagara ce musu komai.
Shigowa falon ya yi yaga yanda suka hau kan kujeru suna ihu suna tsalle " dalla kuma mutane shuru "ya daka musu tsawa suna ganin shine kuwa duk suka zazzauna akan kujeran sukayi mukui kamar basa gidan duk sun shiga rigar nutsuwa ɗan suna matukar tsoron Tajuddeen saboda ba shiga harkansu yakeyi ba , Hafiz ne ya yi dariya ya ce " yan renin hankali wato mu kuka rena da kunci gaba ai " nan ma shuru sukayi . Karasowa falon ya yi ya zauna yaja hular riganshi ya rufe mishi fuska sannan ya maƙala heaadphone a kunnenshi , se yanzu su Abbas sukaji gidan yadawo dede dasu Asrah suka nutsu suma suka fara hiran makaranta domin Abbas da Ahmad,Hafiz suna University .






_____" duk abinda ze faru gwara yafaru yau kawai ayi awuce wajan muje next step ayau ba se gobe ba yarinyar nan zata bar gidan nan " cewar Hajiya khareema dake zaune akan lallausan Chinese carpet me laushin gaske a gerden suna zaune ita da Hajiya Hurairah sunata kulle_kullensu sun gama tsayar da mafita kan cewa yau zasu sa a dauke Asrah komai sun tsara shi yanda yakamata jira sukeyi a daura abincin dare.




6:50pm


Su Hajiya babba basu suka dawo ba har se bayan mangrib sun dawo sun samu angama komai na abincin dare an jera akan dinning ma'aikatan gidan duk an kaiwa kowa abincinsa wanka sukayi suka fito dinning .


Duk sun hallara a kan kujeran cin abincin ansawa kowa nashi , Abbie ne ya kalli fatime ya ce" ina Hurairah da khareema?" ta bashi amsa da" sun ci nasu kafin ku dawo " gyada kai ya yi sannan kowa yafaracin abinci ,babu abinda kakeji se karan cokula kowa ya nutsu ana cin abinci ,suna gama ci suka farajin idanunwasu yafara musu biji_biji alamun bacci haka sukayi sallama kowa ya wuce bangarenshi , suna shiga ko minti biyu basu ƙara ba wani irin nannauyan bacci ya daukesu , daga yara manya masu aiki kowa seda ya yi wannan doguwar baccin . Ammuh da umma ne idonsu biyu . Fitowa sukayi sadaf_sadaf suka fara bincika gidan ɗan tabbatar da kowa ya yi bacci aikuwa kamar yadda boka mauzau ya faɗa musu hakanne ya kasance , komawa ciki sukayi suna dariyar mugunta daukan waya Umma ta yi ta kira number wani me suna Black yana dagawa ta ce " ku karaso duk sunyi bacci " banji me aka faɗa mata ba ta dayan bangarenta kawai naga ta ajiye waya tana murmushi tafawa sukayi ita da Ammuh.




Karfe 10:00pm dede na dare wata bakar mota ta shigo gidan wasu masu bakaken kaya fuskokinsu duk rufe da mask suka fito suka shiga cikin mansion din da bindigu a hannunsu kai tsaye wajan Umma da Ammuh suka nufa su suka kaisu har part din anty amarya bude bedroom din sukayi uncle Hameed da anty amarya suna kwance sun sa Asrah a tsakiyar su , dariya umma da Ammuh sukayi kafin umma tasa hannu ta dauko Asrah ta mikawa daya daga cikin yan
kidnappers din da suka dauko ya karbeta yana kallonta mika mishi wannan kwalban turaren ta yi suka fito daga part din zuwa downstairs hankalinsu kwance bayanin yanda zeyi amfani da shi ta yi masa sannan ta sake faɗa musu da su tabbatar da sun kasheta karsu yarda su barta da rai suka amsa da to suka sa ta a motar suka ja suka tafi da Asrah dake baccinta peacefully.


Komawa ciki sukayi suna sauke ajiyar zuciya abinsu sukaje suka kwanta kamar basu san komai ba.


Tafiya sukayi me nisa sosai suka iso gurin wani daji kafin suka faka motar su, ogansu ne yafito da wata karamar wuƙa se sheki yakeyi ya seta dede wuyan Asrah ze yankata dasauri daya daga cikin yaranshi ya rike hannunsa " no boss karka kasheta yanzu fa samun wannan yarinyar da mukayi fa shima wani ƙarin samun kudine agurinmu " duk zuba mishi ido sukayi ogan ya ce " kamarya kenan ? ta ya zata zama ƙarin samun kudin mu?" " Boss kar mu kashe yarinyar nan kaga su fah 4million suka bamu akan mu sace ta mu kasheta . kasan Mark yana safaran yara mata zuwa Lagos a gidan karuwai kawai muje mu siyar mishi da ita se mu mishi bayani daga gidan da take saboda ya gudu da ita adaren yau domin in suka kai gobe a Maiduguri za'a iya kamashi" jinjina kai boss din ya yi dan gaba dayansu sun gamsu da maganar shi ya kalli Asrah kafin ya maida kallonshi kan yaron nashi " ya ce bawai naki ta naka ba kasheta fa sukace muyi kar kuma ta tona mana asiri " fito da kwalban da Umma ta bashi ya yi ya ce" ai inde da wannan magana ya ƙare " yafaɗa yana nuna musu kwalban dukkansu dariya sukayi suna jinjina basira irin nashi fito da hanky ya yi ya ɗiga turaren ajiki sannan ya shaƙawa Asrah abun wani irin miƙa ta yi da seda ta sandare idanunta suka firfito waje bakinta yafara fitar da kumfa , tsorata sukayi hankalinsu ya tashi gani suka yi kamar guba suka bata tana kokarin mutuwa goge mata bakin sukayi sannan suka tsura mata ido , ahankali_ahankali ta fara komawa normal kafin daga baya taci gaba da baccinta .


Jan motar sukayi izuwa can bayan gari inda zasu samu Mark din nan sukayi cinikin Asrah yabasu 1million suka tafi suka bar mishi Asrah.
Kallon Asrah mark ya yi sannan ya maida kallon shi kan Asmita da itama take kwance agefe tana bacci ga wasu kananan yara da su ma sun kai rai goma suna kwance Suna bacci nan yafara shirin barin garin cikin gaggawa.




Asuba ta gari .


Tashi uncle Hameed ya yi yaga babu Asrah a tsakiyar su amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login