Showing 66001 words to 69000 words out of 94974 words

Chapter 23 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8667

mutane uku ne a ciki biyu mata se na miji guda daya, dayar macen Mahaifiyar namijin da macen ne saboda kamar da sukeyi.


Fuskanta dauke da tarin damuwowi dan banace damuwa daya ba,ta kalli na mijin gabanta ta ce "Taheer har yanzu shuru babu labarin ya'yanku Lameer, shikenan ya bata kenan?, shikenan yanzu a kasar nan daga ka zama me gaskiya da riko da amana se anyi kokari an ga bayan ka?,sun salwantar da rayuwar Lameer".


Taheer shuru ya yi yana sauraran hajiyar ta su,tun lokacin da babban ya'yansu Barrister Lameer ya bata suke cikin wani hali na rashinsa,sun neme shi har sun gaji amma shuru babu labarin sa.


"Hajiya ni abun daure mini kai yake yi,su waye suke neman kashe ya Lameer,meye abinda suke bukata a tare dashi, gaskiya duniya yanzu babu gaskiya.ranar da mukayi waya dashi na ƙarshe shine ranar da ya ce min yana Lagos na yi farin ciki sosai da jin haka nan nima nake sanar dashi ina Lagos, se ya ce mu haɗu a wani restaurant akwai abinda yake so mu tattauna.mun gama waya dashi se nazo wajen yarinyar danake baku labarin inason in aureta, Asmita,ban bata lokaci a gun nata ba, na koma a hanyata na ta kiran wayarsa baya shiga har izuwa rana me kama ta yau babu labarin ya Lameer".
Yana magana ne cikin muryar me ban tausayi,domin shi da dan uwansa akwai shakuwa me karfin gaske,wasu ma har tunanin yan biyu ne su,komai din su tare aikine kawai kowa da irin nasa, Lameer lawya ne,shi kuma Taheer pilot ne,matukin jirgin sama.


Yar karamar kanwarsu me suna yusra, kyakyawa da ita daga ganin ta bazata wuce 17 yrs ba, ta yi tagumi tana kallon Hajiyar tasu da ya'yanta,dama tun can ita ba gwanar magana bace,da wannan abun ya sake faruwa kuma se ta sake zama shuru_shuru.


Hajiya ta ce"ya lamarin Asmitar da kake magana an sameta ne!?" "Ah ah Hajiya itama shuru"girgiza kai ta yi,jim kaɗan kuma ta furta"Sunan budurwar kan nan in naji se na tuna da kanwarka"
"Nima haka Hajiya".








Katsina state




Yau de Allah ya yi wa Hajjatiye ikon zuwa Nigeria,tana gidan mom Rumanatu,tunda ta zo ta sasu agaba se de su wuce Maiduguri ita ba zata iya zama anan ba, Abu Sufyan ne ya samu ya shawo kanta ta yarda kan cewa gobe da safe zasu tafi dama jiran su Abbie suke yi su dawo kuma su din ma yau da rana Flight din su ze yi landing.


Iftisan ba wani shiri suke yi da Hajjatiye ba,ba ta ma zama kusa da ita,domin inta zauna kusa da Hajjatiye tas take kare mata zagi bata rage mata, Jaleelah ce yar gaban goshinta.


Saukowa Ashman ya yi cikin shirin zuwa wajen aiki ya tadda su zaune a falo,gaida su ya yi yasa kai yafita,rike haɓa Hajjatiye ta yi ta kalli mom Rumanatu,"nikam Rumanatu wa'yannan sabga_sabgan balagaggun kam me kuke nufi da har yanzu baku musu aure ba!?,ki duba yaron nan da ya kamata ace yanzu yana da mata biyu yara takwas amma ace yana nan yana yawo fikau fiyau ba mata!"gyara zama mom Rumanatu ta yi ta soma magana"to Hajjatiye ya za muyi dasu yaran nan sunki maganar aure kwata_kwata,ko jiya seda mukayi wannan maganar nida ya'ya Isma'il,haka su Tajuddeen din ma shuru babu wacce yake da budurwa balle a yi maganar su dedeta maganar aure".
Gyara daurin dankwalin kanta da ta tokaro shi gaba ta yi, ta ce"ai duk ku kuka sangarta su, haba wannan abun kunya ne yara daga masu shekara ashirin da bakwai se zuwa da takwas amma a ce ba sa maganar auren to kode basu da lafiya ne!?,in yaso ni da kaina zan samo musu maganin karfin mazantaka ne!?,yoooo ina dalili,ga yaran matan ma duk sun balaga kalli kirjin yaran nan naki duk ya gama cika da kirgen dangi,har ya fara kwanciya basuyi aure ba". Hajjatiye ce ke magana amma mom Rumanatu ce take jin kunya dama Hajjatiye ita babu ruwanta ko a gaban waye duk maganar da yazo bakinta se ta fadeta sede ta barka da jin kunya,dan ma Allah yasa su Jaleelah duk suna bedroom din su.
"Shikenan Hajjatiye gobe de in mun je Maiduguri se a yi maganar".
Haka ta tashi ta shiga kitchen ta yi mata abincin da takeso da kanta.








"Kasan yanda rayuwar su yake da mahimmanci a wajena kuwa!?,kasan yanda nakeson su ne?, dalilin son da nakeyiwa Sabriyah yasa na fara kaunar Asmita jinta nakeyi kamar kanwata,da nace ku sace ta,ta baku memory in kuma baya wajanta ku sa ta ta faɗa muku a inda yake, bawai ku kusan kasheta da cocaine ba,common yanda zaku yi aikin kuma baku sani ba,bayan kunyi laifin nan kuka bari har sojojin Tajuddeen suka gano inda kuke suka kai muku hari, kun cancanci tukuici daga wajena saboda babu wanda yake wargaza mini shirina ban bashi tukuici ba"Fu'ad ne agaban Samuel da kuma dayan da suka kamo Asmita su kadai ne suka tsira daga farmakin da su major Marry suka kai musu,nan take suka zo wajen Fu'ad din.


Magana yake musu yana nuna su da bindiga daga ganinsa kasan ranshi ya yi muguwar ɓaci,har kamanin sa ya sauya ya koma boss,bazaka ce shi ne wannan Fu'ad da Asmita da Sabriyah suke yabo ba,wannan kamilin Fu'ad,bawan Allah da babu ruwansa.


A kirji ya harbi dukkansu biyu suka fadi a mace.durkusawa ya yi, ya dangwali jinin Samuel da hannu ya shinshina a hancin sa,wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya sauke,yana jijiga kansa cikin nishadi miƙewa ya yi, ya fara rawa a wajen kamar mazari lokaci daya kuma ya dakata ya nutsu,ya sauya fuska izuwa abin tausayi kamar mutumin kirki,
Sunkuyar da kanshi ƙasa ya yi "yanzu shikenan kun mutu!?,bazaku taɓa dawuwa ba,ahhhhhh! babu abinda yakai jini kamshi,inajin dadi da tsintar kaina a farin ciki a duk lokacin da naga ina kashe mutane kururuwar neman taimako da kuma ganin zallan tsoro a cikin ƙwayar idon su yana ƙarfafa mini guiwa"ya yi maganar yana wani juyi.


Ya sa'ke cewa"my Sabriyah karki damu ina nan zuwa gareki,ke din tawa ce,zanyi faɗa da kowa domin ganin na kwato ki,my Sabriyah da taimakon ki zan ga bayan lieutenant general Tajuddeen Bishara"ya gama maganar yana kecewa da mahaukaciyar dariya.
Tabbas Fu'ad cikekken hatsabibin mutum ne da gane inda ya dosa se Allah da kuma mutum wanda ya fisa kaifin basira,ya wuce duk tunanin me tunani, yana da fuskokin da bazakayi tunanin ze iya yin muguwar muguntar da yake aikatawa ba,in ya juya mutumin kirki zakayi tunanin wani malami ne wanda yasan Allah yasan addini,amma in ya koma hatsabibinsa to ko shedan haka ya ganshi ya barsa,duk wanda ya shiga tarkon Fu'ad tofa sede ya yi addu'ar Allah ya kwacesa daga sharrinsa shine kawai.

Barin dajin ya yi ya fito bakin titi nan ya samu napep ya tara.






Shirye_shirye da girke_girke ake yi sosai na tarban su Abbie, family kowa yazo an hallara.


Anty sakeena da anty Sameera sun zo da yaran su,haka ya Abbas,ya Hafiz,ya Ahmad duk sun zo da familynsu gwanin ban sha'awa.kowa yana gida mazan ne suka tafi airport dauko su.


Umaisha ce ta sauko tana neman Jawan Ammie ta sa ta kira mata shi zata bashi sako,duddubawa ta yi bata ganshi ba ta tambayi matar Ya Abbas ina yake,nan take ce mata ai duk sun tafi dauko Abbie,"okay"ta ce mata sannan da sauri ta nufi part din LTG.


Seda ta shiga sannan ta yi sallama knocking ta yi a bedroom dinsa.izinin shigowa ya bata,da sauri ta shigo ta matso kusa da shi,"ya Taj Ammi ce ta ce in kiraka" "okay ina zuwa"ficewa ta yi ta barsa,bin bayanta ya yi kusan a tare suka shiga part din Ammi ,samunta sukayi ta gama shiryawa cikin dakakkiyar less,ta yi kyau sosai tsantsan kamaninta ya sake fitowa da LTG da Jawan da kuma Umaisha,anty Sameera ta fi kama da Abbie sosai.murmushi ya sakar mata ta yi masa kyau sosai da yasa ya gagara boye farin cikinsa.


"Tajuddeen,dama tambayarka zanyi ko Sabriyah ta baka labarinta!?".nan take mood din fuskarsa ya sauya jin sunan da ta ambato mishi. da yasan akan wannan abun take neman sa,da babu abinda ze kawo shi,shi meye hadin shi da ita da zeji wani banzan labarinta da babu komai a ciki se karuwanci da fitsara,ko da kusa dashi bayason yaganta,shi mutum ne da ya tsani yaga karuwai na shawagi hakan yasa a USA kaff seda ya rufe gidan karuwan da suke can ya tsani abinda suke aikatawa hasalima shi kyamar su yake yi.
Cike da bakin ciki yake kallo Ammi ya ma rasa ya zeyi can de ya ce"please Ammi karki sake mini magana akanta"yana gama fadin hakan ya juya ya bar part din nata, yana tafiya shi kadai se tsaki yake yi kamar tsaka,dole ne ma daga zaran an gamawa dayar treatment dinta ta warke ze koresu su bar gidan,baze iya jure ganin shige da ficen ta a gidan ba.


Tana sauri batasan waye agabanta ba ta ji ta buge shi,ja baya ta yi tana kallon sa, haɗe fuska ta yi tana kokarin wucewa hannu yasa ya jawota da karfi seda ta ji kamar hannunta ze fice daga jikinta.
Hannu ya sa ya damki gashinta, ƙara tasa"ka sa'ke ni,akwai zafi!mugu kawai azzalumi kai baka da wani aiki se mugunta"tunzurashi kalmar mugu da ta kirasa dashi ya yi,runtse idonsa da ya yi ja lokaci daya.ya dunkule hannunsa,jijiyar hannunsa ya fito rudu_rudu,da wannan hannun nasa in yakai mata naushi to sede a haifi wata amma ita kam bazata rayu ba,duk namijin da ya yiwa naushi da wannan hannun nasa, tofa sede gawa,wurgi ya yi da ita ta faɗa hannun uncle Hameed da tun haurowan shi ya ga abinda yake faruwa gudun kar a yi bacecciya ne yasa da hanzari ya iso upstairs din,kuma ya yi dede da wurga Sabriyah da LTG ya yi, Allah ya bashi ikon rikota ta faɗo hannunsa,sannu ya yi mata yana duba ko ta ji ciwo ajikinta.


Bin bayan LTG da tun lokacin da ya wurgata ko juyowa beyi ba, balle yasan wani hali take,ya yi tafiyar sa, girgiza kai kawai uncle Hameed ya yi,ya dagata ta mike.
"Sannu kinji!?"gyada masa kai ta yi tana riƙe kanta da taji yafara mata ciwo, saboda damƙar da ya yi wa gashin bana wasa bane ko lokacin da boss lady take damƙar mata gashinta bata jin wannan azaban domin ya ninka na boss lady sau dubu.
Fahimtar da kanta yana mata ciwo ne yasa uncle Hameed jan hannunta zuwa kan kujerar ya zaunar da ita sannan ya kama kan nata yana mata addu'a.


Sa'ke kan ya yi ya ce "yanzu ya kike ji!?" "Da sauki uncle" "ki dena shiga lamarin Tajuddeen kin gan sa baya wasa da yara ko kadan,zan iya cewa tunda nasan shi da yarinya daya nasan ya yi rayuwa me tsayi yana wasa da ita harda dariya,kuma in kinji yana dogon magana to da ita ne.shi mutum ne me murɗaɗɗen hali,a hakan ma yanzu mun samu ya sauko,se de addu'a"ya karasa maganar yana yar dariya.
Tunda ya fara magana take kallon shi haɗa ido sukayi,ta yi saurin sunkuyar da idonta.
Camly cikin wani irin yanayin son jin wata yarinya ce LTG yake so haka da yiwa magana da wasa ta ce"amma uncle wata yarinya ce haka!?",ya ce "Asrah!ita ce farin cikin Tajuddeen yana sonta sosai yarinyar da yake da burin aure in ta girma,so ne me karfin gaske a tsakanin su".jikinta ne yafara rawa ta rasa dalilin da yasa duk sanda aka ambaci sunan Asrah se taji tsigar jikinta ya tashi,Wannan shine karo na biyu da taji wanann sunan a yau yanzu jikinta rawa yake yi.da mamaki uncle Hameed ya kalleta ya ce"Sabriyah lafiya ko de baki da lafiya ne!?"yana taɓa wuyanta ya ji ko zazzaɓi ne amma jikin babu alamar zazzaɓi.rasa amsar da zata bashi ne yasa kawai ta ce"babu komai uncle". "Kin tabbata?"ya tambayeta yana kallon ta,gyada masa kai ta yi.
"Ya jikin yar uwar taki ta samu bacci ko?",nan ma gyada masa kai ta yi, murmushi kawai uncle Hameed yake aikinyi,be san meyasa inde yarinyar tana a tare dashi se yaji kamar yana tare da yarsa ta cikinsa wacce ya haifa,se yaji yana sha'awar ya ta janta da hira.
Bude baki ya yi da niyar yin wata maganar ya ji horns din motoci sun shigo gidan, murmushi ya yi,ya ce "madallah sun dawo kenan,tashi muje ki rakani tarbo baƙi"bata iya masa musu haka ta mike yana rike da hannunta suka sauko main part,da mamaki matan su ya Abbas suke kallon uncle Hameed da yarinyar da yake tare da ita suna tambayar kansu wannan kuma wacece kuma daga ina?,maye hadin ta da uncle Hameed da har yake rike mata hannu baya tsoron matarsa ta gansu?,Ammuh da mugun kallo ta bisu har suka fice, tana me aiyana abubuwa aranta kallo ɗaya tayiwa Sabriyah tun zuwanta gidan ta ji ta washi yarinyar ta tsaneta,se kuma labarin da ummah ta kai mata wai anty amarya tana son adopting dinta ta zama yarinyarta,dole ne ma tasan yanda zata yi ta kora Sabriyah ta bar gidan.




Fitowa waje sukayi shi da ita suka tsaya suna jiran su abbu su fito daga motar.bubbude musu akayi suka fito,sauka idon Abbie da abbu ya yi akan uncle Hameed dake tsaye riƙe da hannun Sabriyah,basu yi mamaki ba saboda duk tunanin bakuwarsu ce,kila acikin surkansu ne wata tazo da ita. su ya Ahmad suma suna mamakin wannan bakuwar fuskar da suka gani, cike da farin ciki suka rungume juna uncle Hameed na musu sannu da zuwa,raba jikinsu Abbie ya yi yana kallon Sabriyah dake tsaye a gefen su sanye da riga da wandon jeans babu ko dankwali a kanta.
Kallonta ya yi sannan ya kalli uncle Hameed "Hameed Wannan yarinyar fa?,yar waye!?"abinda Abbu yake shirin tambayarsa kenan se Abbie ya rigasa.shima uncle Hameed din kallonta ya yi cikin zolaya ya ce "ƴata ce"da alamar tambaya suke kallon shi cikin tuhuma.dariya uncle Hameed ya yi ganin irin kallon da suke binsa dashi ya ce"just kidding!, bakuwarmu ce, shikenan?",dariya suma sukayi.


"Yarinya ya sunanki!?"Abbie ya tambayeta" "Sabriyah"ta basa amsa cike da kunyar da bata san tana dashi ba.
Murmushi Abbie da abbu sukayi.
Kafin ya sake cewa"to Sabriyah ina dankwalin ki!?ba ki san babu kyau yawo babu dankwali ba!?"girgiza mishi kai ta yi alamar bata sani ba,kallon juna abbu da Abbie sukayi,katse zancen Saghar ya yi,ta hanyar faɗin"Abbie mu karasa ciki".shiga ciki sukayi ,kafin su zauna su Rameesa suka zo dukkansu suna musu oyoyo,yanda su duka suka kam kame abbu da Abbie ne yabawa mutanen falon dariya.
Abbie ya shafa kansu"oyoyo!yan matan Abbie"cikin shagwaba Parsa ta ce "munyi missing din ku sosai kunje kun daɗe" "we missed you too masoyiya,yanzu kam ai mun dawo".


Zama sukayi gaba dayansu,ana faman gaishe da su Abbie da kuma yi musu sannu da hanya,ganin sun shiga rububi ne yasa Sabriyah ta fece zuwa dakinsu.ita bata cusa kanta cikin abun familyn duk da familyn na burgeta sosai yanda suke da son junansu da girmamawa.


Shigowa dakin ta yi ta ga wayam babu Asmita da tabarta akan gado tana bacci dubata ta yi a toilet nan ma wayam bata nan shiga dakunansu Umaisha ta yi nan ma bata ganta ba.hankalinta ya tashi tafara tunanin ina Asmita kuma ta shiga daga ɗan fitan ta da ta yi din nan.




Book one ya kusa karewa remain some few pages,na yi wa mutane 20 na farko discount din 200,zasu biya 300 kenan.idan mutum ashirin na farko suka gama biya ze koma 500 domin wannan shine standard price dinshi.luckiest 20 people ku hanzarta biyan naku.😍😍😍😍😍💝




Comment,share and like.


*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*




Page 23&24




*_Story & written_*



By


*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)








*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*






📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️






Page 23&24




Da gudu_gudu ta fito daga part din tsaban ta rude ma bata san wani part ta shiga ba, ita de tasan neman Asmita take yi,a tsawace ta ce "ke meya kawo ki nan!?,za kizo ki shafa min najasa ko to fice tun kafin na lahira yafiki jin dadi"mugun kallo ta watsawa Ammuh,"Mtsssw!ni in banda tsautsayi meze kawani wajen ki,je kiji da matsalar dake gabanki tsohuwar banza kawai"a harzuke ta kai hannu zata mare ta, tayi gaggawar rike hannunta ta ce "Wallahi ko a mafarki ki ka ga kin mareni to kiyi gaggawan tashi daga wannan mafarki domin murde hannunki zan yi ya koma baya,babu ruwana da girmanki,ki kalli cikin kwayar idon nan tawa in kinga kunya a ciki, to ki dau mataki akaina,yanda kika tsane ni ,haka na tsaneki kuma ina da tabbacin nawa ya ninka naki"ta sake mata hannu ta fice dan neman Asmita ne a gabanta bata da lokacin ɓatawa.
Suman tsaye Ammuh ta yi tana ta nanata maganar da Sabriyah ta gaya mata,ji take kamar an watsa mata garwashi a kirji,lallai dole ne ta dau mataki akanta saboda taga alama yarinya nan in ta samu guri zatayi abinda yafi haka.kwafa ta yi "za ki shiga hannu".


Ta duddubata a bangaren sama bata ganta ba hakan yasa bata da wani zabi da yawuce ta dawo downstairs.
Kusan yawanci ma basa nan,matar ya Hafiz ce a falon se Zoya da kuma yara.


Bata tambayi ko daya daga cikinsu ba. da taga de bata falon kawai ta fita,a waje ne ta tambayi securities ko sunganta,dayan su ne ya sanar da ita tana garden ,yana gama faɗa mata ta nufi garden din da sauri,tun kafin ta iso ta hangota zaune akan lilo dake cikin wajen.girgiza kai ta yi, ta karasa wajenta ta baya batare da tasani ba ta rike lilo ya tsaya ,juyawa ta yi tana ɓata fuska "my Tom ki bar mini lilo na" "Asmita meyasa kika baro can ki ka barni ina ta nemanki gaba daya hankalina ya tashi,banason sa'ke rasaki a karo na biyu".
Tasan abu ne ma wuyaci ta fahimci me take nufi.hakan ya sa ta ci gaba da turata a lilon,ita kuma tana dariyar farin ciki,haka suka kwashe mintuna Ashirin a haka.


Dakatawa Sabriyah ta yi,gaba daya ta gaji tana riƙe ciki ta ce"My Jerry zo mu tafi se anjuma mu dawo ko?",gyada mata kai ta yi ta sauko akan lilon.ta rike hannunta suka bar garden din suka koma ciki.


Muryar Ammi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login