Showing 57001 words to 60000 words out of 94974 words
ta furta"dama banida lafiya ne,shine nake neman magani na ɗauka nan sashen ya Saghar ne".
Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita,hakan yasa kalma daya da ta faɗa be yarda dashi ba.
"Ayya!ka barni in fita ka ji!?"
Bindiga ya daura mata a kai, kamar ze harbeta ta kwala ihu.
"Wayyo na shiga uku na,dan Allah karka kasheni!, banason mutuwa yanzu,bazan ƙara shigo maka sashen ka ba"da iya karfinta take magana tana kuka jikinta gaba daya ya jike da zufa,ga cikinta se ƙa ra yake yi.
"Shut up "tsawan da ya daka mata wanda seda yan hanjinta suka ƙara tsurewa.
A bangaren su Rameesa kuwa tunda suka ji diran motocin LTG suka shiga tashin hankali sun san yanzu haka Sabriyah ta shiga hannu, duk jugum_jugum suka yi abin duniya ya damesu ga da_nasanin turata,jiki a sanyaye Parsa ta ce "ga shi kun ja mata,ni tun farko ban yarda da wannan shawarar ta ku ba,kunsan ya Taj no nonsense ne,yanzu ga shi abinda ya biyo baya".
Su de shuru suka mata dan basu da bakin magana.
Zoya ranta fes ko ajikinta se ma nishadin da take ciki na ganin LTG ya kama Sabriyah a part dinsa.
"Ni Wallahi hakan ya min dede, Allah yasa ya kakkaryata kowa ma ya huta, kunga gobe babu wacce zata sake yin gigin zuwa part dinsa in baya nan!, gaskiya na dade ban shiga farin ciki irin na yau ba".
Takaicin maganganun da Zoya ke faɗi ne yasa duk suka watsa mata harara.
"Ai ke kinyi a sara Zoya,yar uwarki mace na cikin wani hali shine ki ke farin ciki,meye ribarki in ya Taj ya mata wani abu!?,ke wannan mugun halin naki ne yake haɗa ni dake,yar iska kawai"cewar umaisha da ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci.
Rameesa da se yanzu ne ta samu bakin magana"kyaleta de mugun bakinki se ya dawo kanki".
"Can muku de yanzu kam "Zoya ta fada tana danna wayarta bata biye musu ba.
Tagumi Iklas ta yi ta ce"kun san me mu gwada kiranta a waya muji ko ta buya a wani wurin".duk sun yarda da shawarar ta hakan yasa suka kira wayar dake hannun Sabriyah.
Bindiga na a tsakiyar goshinta, kwakkwaran motsi bata iya yi ji takeyi in ta motsa LTG ze tarwatsa kanta da bindigar.
Wayar dake hannunta ne kira ya shigo,wayar na vibration, idonsa ne ya sauka akan wayar hannun nata karba ya yi, ya saka a kunne,muryar Umaisha ce ya ji tana magana cikin raɗa."Sabriyah fatan de ya Taj be ganki ba ko!?,kar ki fito daga inda kika buya zamuzo mu fitar dake".
"Naganta kuma ku dinma yanzun nan kafin in bude idona inasan ganin gaba dayanku a nan".yana sanar da ita haka ya kashe kiran.
A zuciyar Sabriyah ta ce"shikenan kuma kun shiga hannu,gwara kuzo ya harbemu tare din,shegu tunda ku kuka ja mini".
Sauke bindigar ya yi ya barta a wajen ya koma kan gado ya zauna,yana duba wasu files da major Marry ta ajiye masa.
Duk wannan budurin da ake yi Sabriyah bata bude ido ba se da taji ya cire bindigar akanta,kallon inda yake zaune ta yi,ta gan sa daga shi se short,zare idonu waje ta yi tana bin halittar jikinsa da kallo,sosai take ƙare masa kallo kamar zata haɗiye sa.
Unexpected ta ji muryarsa yana mata magana "banason irin wannan kallon yana fusata ni"da sauri ta ka war da kanta gefe dan batayi tsammanin yasan tana kallon sa ba.
Ba tare da ya dago ya kalleta ba ya ce"kneel down"gabanta ne ya faɗi jin abinda ya faɗa domin tasan ma'anar kneel down saboda,time din da suke yara inde sukayi laifi haka boss lady zata sa su yi,se sun kusan yin awa takwas a haka.
Hannu yasa yana kokarin daukar bindigar,a tsorace ta zube akan guiwowinta, ta yi kneel down din,ta daga hannayenta sama.
A cikin wannan yanayin su biyar din jere reras suka tsaya acikin kofar bedroom dinshi ko wacce jiki a mace.ganin yana kokarin ɗago kanshi ne suka shigo da gudu suka tsatstsaya,se zazzare ido suke kamar magen da ya yiwa kare sata.
Shuru sukayi suna jiran su ji abinda LTG ze ce.
"Be on your knees"abinda kawai ya faɗa kenan.
Kamar zasu sa ihu, haka suna ji suna gani sukayi kneel down suma a kusa da Sabriyah.
Tana fama da zafin da guiwowinta suke mata ga kuma hannunta dake sanƙare,amma tsabar mugunta itama tana under punishment amma hakan be hanata kwashewa da dariyar da batasan ta yi ba.ga shi tana son dakatawa amma ta gagara se kyakyatawa da dariya take.
Kallonta sukayi da mamaki ganin basu kadai aka sa punishment din ba harda ita. amma tsaban iya shege irin na Sabriyah dariya take musu,ita kuma babban abinda yasata dariyar shine,ganin tana kokarin rufa musu asiri a wajen LTG amma tsabar iyayi irin nasu suka wani kirata a waya ga shi suma sun jawa kansu kamar yanda suka ja mata, musamman ma inta haɗa ido da Zoya nan take wani sabon dariyar ya ke kamata,domin Zoya ce duk ta mata wannan mugun bakin harda cewa Allah yasa LTG ya kamata ya kasheta da bindiga yanzu ga shi dukkansu sun shiga hannu.
Hararanta Rameesa ta yi, ga shi babu halin yi mata magana gudun kar LTG ya kara musu wani sabon punishment din.
Slowly ya kalli inda take tsugune ta yi kneel down din har lokacin fuskarta na dauke da sauran dariyar da ta gagara shanyewa.
Mamaki ne ya kamashi ya fara tunanin meye yasata dariya kode punishment din da ya bata ne ta rena?.
Pointing dinta da yatsa ya yi,"come here".kamar anyi ruwa an dauke dariyar da takeyi ya dauke ta shiga firi_firi da ido,mantawa da LTG na wajen yasa take wannan dariya yanzu kam da ta ji husky voice din shi, ta shiga cikin rigar nutsuwa.
Ƙa sa da murya iklas ta ce"kiranki fa yake yi ,ki rufa mana asiri kije".
Simi_simi taje gabansa ta tsaya kamar bishiya.
Kusan mintunta biyar a tsaye be ce mata komai ba yana duba file din gabanshi.
Ranta ne ya soma baci cikin gunguni yanda baze ji ba ta yi magana"Ni fa ba kayan wanke bace da za'a shanya".
Cak ya dakata da bude pages din da yakeyi , maganar da tayi duk a kunne sa yajita,da hannunsa na hagu ya yi amfani wajen ɗauketa da marin da batayi tsammani ba se kawai jin saukar sa ta yi,komai ɗauke mata wuta ya yi na wasa sakonni ta fara ganin stars yana wucewa ta gabanta.dafe in da ya mare tan ta yi,tana jin wani abu na sukan zuciyarta kamar ana daɓa mata mashi.kukan da takeson yi ma ya ƙasa fitowa fili, haka ta haɗiye, tuna afafa ta yi yanda take yin yanda ta gadama in banda boss lady babu me sa hannu ya daketa,ko waye shi seta ga ta mishi rashin mutuncin da beyi tunani ba.zaman da takeyi a gidan nan a takure take jinta kawai de in da abin yake zuwa da sauki akwai masu ɗebe mata kewa badan haka ba da ko ta wani hali se ta bar gidan nan.tafi samun freedom din da take bukata acan gidan karuwan.
Sabriyah aka mara amma su Umaisha su sukaji zafin,,,tausayi tabasu ga tarin danasanin abinda suka aikata ta dalilin su ne zata fuskanci hukuncin da bata da sa hannu. yanzu ma ta dalilin su LTG ya mata wannan marin duk su suka ja mata,jikin su ya yi weak sosai, Parsa iyayen tausayi da son jama'a tun sanda LTG ya mari Sabriyah ta fara hawaye tana jin kamar ta jawo Sabriyah jikinta ta bata hakuri,amma tasan duk yanda LTG yake sonta yake ji da ita baze juri renin hankali ba.
"Bana son rashin kunya kuma bana son me yin sa,be very careful around me, Kiyi kneel down anan" ya yi maganar yana ajiye file din ya tashi ya shiga toilet yabarsu a wajen,yana barin gurin Sabriyah ta yi kneel down din da ya bata umarni akai.
Cikin rada Rameesa ta mata magana"we're sorry darling,kiyi hakuri kinji bazamu sake irin wannan wasar ba"murmushi ta mata like nothing happened."Mtsssw!ai ni kam kun cuceni, I won't forgive any one of you, kun haɗa abunku kunja ya Taj ya haɗa dani acikin punishment".duk suna jinta babu wanda ya kulata suna durkushe kamar basu jita ba,haka Zoya ta yi shuru dan kanta.
Se da ya ɓata 20 minute yana wanka sannan ya fito sanye da jallabiya ash color ya yi fitting dinsa sosai,kyawunsa ya sake fitowa,ta kasan ido dukkanin su suke kallonsa saboda tsoron kar ya kamasu suna satan kallonsa,shi mutum ne da ya tsani yawan kallo,ya tsani a zura mishi ido ana kallonsa,kamar yanda ya sanarwar Sabriyah yawan kallo na tunzurashi,amma duk da haka seda ya kamasu suna kallon shi cikin tsawa wanda ke haɗe da ɓacin rai "what are you looking at!?,ko kunga dodo a jikina ne!?"ya faɗa rai a ɓace,kallon ƙa sa suka koma yi a tsorace.
Kwafa ya yi kafin yaje gaban mirror ya gyara gashinsa da hair brush,, falo ya fita ya barsu a bedroom din ya zauna ya yi saving din kanshi abinci,fried spaghetti da akayi da chicken.be wani ci sosai ba even though favorite dinsa ne.
General ne ya kirasa suka fara waya akan binciken da yake yi,ba wani jimawa suka yi suna magana ba, email ya shiga yaga anturo mishi da wani short video da wani unknown email account, playing video ya yi yaga macece daure a jikin kujera se shaƙa mata cocaine ake yi,a ƙa san video anyi Caption da "ka rabu da Sabriyah nikuma se in saki wannan yarinyar".shuru ya yi na Wasu sakonni. nan ya fahimci wannan ita ce yarinyar da Sabriyah ta damu da zataje nemanta.
Cizan red libs dinsa na ƙasa ya yi kafin ya kira major Marry a waya.
Be bata damar yin magana ba ya ce "find that girl in any cost, don't waste my time"."okay LTG "cewar major Marry, sannan hanging call din.
Yasan dole in de yasa aka kwato Asmita to Sabriyah cikin ruwan sanyi zata ba shi memory card din babu jayayya, bayason ya shiga hakkin su ne na nuna mata karfi tunda tun farko, su alhakin wannan memory yake wajen su, shisa baze takura ba yafi son tabashi cikin salama.
Duba time ya yi, yaga lokacin dawuwan Sudais ya yi,ya fita daga part din,palour ya samesu su uku suna zaune, Sudais,Sahil da Salim,kusa da kujerar da Sudais ke zaune ya zauna shima.hira suke yi shide ba wani sa baki yake yi a hirar ba se jifa_jifa.
"Nikam ya Hafiz ya dawo ne?"kallon Salim da ya yi tambayar Sudais ya yi, ya ce "dama baya nan ne?,dazun naga missed call din sa ina aiki , kuma yanzu ma na manta ban kirashi ba ".
"Ehh sunyi tafiya da matarsa da yaronsu,amma kamar gobe zasu dawo nake tunani,ko kuma in su Abbie suka dawo".
Haka suka dinga hiransu seda aka fara kiraye_kirayen sallah mangrib ne, LTG ya mike"lokacin sallah ya yi".
Yana sanar dasu haka ya fita bin bayan sa suka yi.
Bayan sun dawo daga masallaci ne,ya nufi part din shi,biyosa suka yi suma.
Juyowa ya yi ya kallesu ya tsare su da ido"maye kuma kuke bina!?"kunshe dariyar dake son kufce musu sukayi kafin Sahil ya basa amsa"yau a wajen ka zamu tare,tunda ka dawo bamu samu lokacin taɗa rayuwar duniya ba".jin abinda Sahil din ya faɗa bankwarakwai wai taɗa rayuwar duniya se kace wasu mata.
Tsaki ya ja"Nifa banison surutu bazaku addabeni ba kusa yaran nan suna dawuwa daga wajen aiki su biyo ku "(yana magana ne akan Saghar da Jawan)dariya sukayi Sahil da Salim cikin shakiyanci suka ce "Yes sir" a tare suka shigo part din nashi,shi yama manta da yabar wasu aciki.
Zama a palour su kayi suka fara hirar wajan aikin su nan ne de LTG ya saka baƙi,kasa_kasa suka fara jin sheshekar kuka Kuma bana mutum ɗaya ba,ka sa kunnawan su sukayi suna son gasgata abinda kunnesu yakeji, tabbas kuka ne yake fitowa daga dakin LTG amma to su waye ne a ciki,cikin tuhuma suke kallonsa.
Sudais ne ya tambayeshi"LTG Taj!su waye suke kuka a bedroom dinka!?",seda Sudais ya tambayesa tukun ya tuna da su Sabriyah da ya bari a ciki,kusan awowinsu uku kenan suna ciki ya ma manta da al amarinsu ashe suna ciki.ko a jikinsa babu alamar ya damu ya furta"yaran nan ne suka zo mini bincike nasa su kneel down"ya yi maganar can cikin makoshi badan suna kusa dashi ba to da bazasu taɓa jin abinda ya faɗa ba.
Da sauri Sahil ya mike yana"masoyiya"yana kiran parsa yana shiga cikin dakin LTG, dukkansu suna tsugunne kamar yanda ya barsu,sun ci kuka harsun gaji,sun galabaita fuskar nan da ido ya yi ja sosai kallo ɗaya zaka musu su baka tausayi.
Da sauri Sahil ya isa gaban Parsa yasa hannu yana kokarin mikar da ita tsaye,karan azaba tasaka ko wani ga ɓa na jikinta ya rike ya yi tsami ga kuma ciwon da suke yi, kuka take yi sosai ganin bazata iya tashi da kanta bane yasa ya zaunar da ita.
"Sannu masoyiya!ku ma bakwa jin magana me ze haɗa ku da part din LTG ba ya nan".kallon su ɗaya bayan ɗaya ya yi sun bashi tausayi,idon sa ne ya sauka akan Sabriyah da ke kneel down din rakube ajikin bangon dakin,ita kam tsabar wahala ko idonta bata iya budewa.
Lamarin LTG ya bashi mamaki yanzu har da wacce yake bincike akanta din ya saka kneel down din bayan su Umaisha ne suka mishi laifi(Ni Ko araina na ce ai kai Sahil kawai kayi shuru ba kasan komai ba,ita Sabriyah ce ya fara kamawa!hhhhhhh).
Shigowa sukayi dakin banda LTG dake zaune abin sa a palour.
Rike kugu Sudais ya yi duk da baya wani wasa da su sosai saboda a cewarsa basa jin magana.kwashewa da dariyar mugunta ya yi yana binsu da kallo musamman da idonsa ya sauka akan Umaisha da ta marairace fuska tana kallonsa, maimakon ta bashi tausayi amma se ma sake basa dariya ta yi.
"Ba kun ce bakwa jin magana ba!ai ko nine na kuskura naji ko da labarine kunje part dina bincike to abinda LTG ya muku kadan ne". hararansa Sahil ya yi "yanzu Sudais dan Allah basu baka tausaya ba?, shine zaka wani tsaya kana dariya jibi yanda suka galabaita"dage kafadunsa ya yi alamar i don't care.
"Ka duba har da Sabriyah fa da ba wani biye musu takeyi ba"Sahil ya sa'ke magana yana musu nuni da Sabriyah dake gefen su.
A tare Salim da Sudais suka kalli inda Sabriyah take,zaro manyan idanunsu waje suka yi cike da mamaki Salim ya ce "yanzu tsabar iskanci irin naku se da kuka jawa yarinyar nan!?,nasan de Wallahi babu ruwanta".
Zoya dake fama da kanta tana kuka ta ce"ya Salim ita ce fa,ya samu tana mishi bincike"mugun kallo ya watsa mata saboda be yarda da abinda ta faɗa ba.
"Karya kikeyi Zoya da bansan rashin jin ku bane!".
Kamar zata yi kuka ta ce "shikenan ai"
Wajenta yaje ya taimaka mata ta zauna. duk zaunar da su sukayi.
Rameesa da Umaisha ko magana basa iyayi sede binsu da kallo da suke yi ,yau LTG yabasu a jikinsu.
"To yanzu ke Umaisha tashi ki wuce part din ku"Sudais ya yi maganar fuska babu alamun wasa.
Marairaicewa ta yi kamar zata yi kuka"ya Sudais Wallahi ƙafata sun yi tsami,bazan iya tafiya ba"kamar zata yi kuka ta ƙarishe maganar.
Hararanta ya yi ya ce"to ina ruwana?,ku de ba rashin ji ba?".
Shigowa dakin ya yi, ya tsaya daga jikin kofar ya harde hannunsa a kirji.
Salim ne ya kallesa "LTG a yi musu afuwa bazasu karaba"
"Su bar mini part kafin in canza ra'ayi"
Dariya sukayi dukkansu mazan banda shi LTG din.
Sahil ne yasa hannu ya daga Parsa,dakyar ta iya mikewa ta rike shi gam tana cize libs dinta saboda azaba.
Taimaka mata ya yi,ya kaita har part dinsu ya ajiye ta akan gado sannan ya koma.
Mikawa Sabriyah hannu Salim ya yi yanaso ya taimaka mata.
"Ban gama da ita ba ku barta anan ita".
Kallonsa sukayi jin abinda ya faɗa.
"Haba LTG wannan fa bakuwarmu ce,dan Allah kabarta haka".Sudais ya yi maganar yana kallon shi.
kamar wanda yake magana da gini haka LTG ya sharesa be kulasa ba,ganin haka da Sudais ya yi yasan baze bar Sabriyah din ba.
Wajen Zoya Salim ya je yana hararanta ya dauketa can kuma ya fashe da dariya"ƙaramar mara kunya,yau kinci Sa'a ba dan tausayin da kika bani ba ko kallon ki bazanyi ba".
Ita de batace komai ba Allah _allah takeyi ya fitar da ita daga part din,suna kokarin fita Sahil ya shigo.
Ɗaukan Rameesa ya yi da se" wayyo Allah! Abbie ƙafafuna sundena aiki" "za ki mini shuru ne ko se na sauke ki!?"shuru ta yi dan tasan karamin aikin Sahil ne yabarta agurin.
Kwashe su sukayi a wajen ya yi saura daga Sabriyah se Umaisha, Sudais kam ma waje ya samu ya zauna suna magana da LTG.
Gasu Sahil da Salim tunda suka dauki Rameesa, Iklas, Parsa, Zoya bazasu ƙara dawowa ba.
Tagumi Umaisha ta yi tana hawaye zaman da tayi dinma kwata_kwata be mata dadi ba rabin hips dinta ya gaji,kallon Sabriyah da ta jingina kanta da jikin gini idanunta a rufe kamar me bacci,ta yi sannan ta maida kallonta kan LTG da Sudais da suke magana.
Fashewa ta yi da kukan takaici ganin sauran yan uwanta duk an kwashe su saura ita,tunda Sabriyah LTG kam ya ce be sallame ta ba.
Ta kasan ido Sudais ya kalleta yaga yanda take kuka bil haƙƙi, murmushi ya yi.
"Kukan me kike wa mutane"ya tambaye ta yana tsare ta da ido.
Tsinkayar Muryar sa da tayi yasa ta dago suka haɗa ido,irin kallon da taga yana mata ne yasa ta sunkuyar da kai,ta riga da tasan inde Sudais ne ze dauketa to zatayi shekara a haka.
Ji ta yi an dagata sama a tsorace take kokarin sa ihu ta ji,muryarsa"shiiiiii!be quiet"tunda take bata taɓa kawowa a ranta yau ya Sudais ze taimaka mata ba, saboda yadda yake cin zalinta da kuma mata faɗa, babban abinda ya fara haɗa su shine rashin saka dan kwali.
Zubawa kyakkyawar fuskarsa ido Umaisha ta yi tana kallonsa.
Har ya kaita part din su bata dena kallon da take mai ba,kallon cikin nata idon ya yi kafin yaci gaba da tafiya. bedroom dinsu ya shiga, duk sun baze akan gado suna kwance ko wacce se ya mutsa fuska suke yi masoyiya Parsa kam tana toilet ta yi wanka ta tsaya danna ƙafafunta da ruwan zafi.
Sauketa akan gadon ya yi,shi bayan dariyar da suka bashi har da haushi.
Kallonsu daya bayan daya ya yi,"meyasa kuka ja punishment din ya shafi Sabriyah,ku