Showing 63001 words to 66000 words out of 94974 words
din Saghar ya koma bacci.
Kamar yadda suka saba yau ma haka karfe goma kowa ya fito saboda ya yi breakfast,anty amarya dake kusa da uncle Hameed, ƙa sa da murya ta yi mishi magana "daddyn Asrah dama tun jiya akwai abinda nake so in sanar maka to kuma se nayi bacci da wuri"murmushi uncle Hameed ya yi,ya ce "inajinki" "yanzu de ka bari se mun koma part din mu".ya gyada mata kai.
Uncle Hameed ya yi tambayar"ina Sabriyah!?", Rameesa iyayen surutu ta yi saurin faɗin "tana bedroom din ta, uncle ka san ita bata son cin abinci a dinning"girgiza kai uncle Hameed ya yi "wannan ba hujja bane"ya kalli fatime ya ce "je kice mata ina kiranta" "to" ta haura upstairs.
LTG shi ya rasa meye matsalarsu da yarinyar kowa maganar ta,shi ba wani son kallon fuskarta yake son yi ba.amma su daga sun zauna se sunyi maganar ta.
Saukowa dinning fatime ta yi ga Sabriyah dake bayanta sanye da wando jeans da riga ta yi donot da gashinta a tsakiya,
Tsayawa ta yi ta ce "ina kwanan ku"amsawa sukayi.ban da shi da ko ɗago kai be yi ba.
Uncle Hameed ya mata nuni da kujera dake gefen anty amarya "daga yau har sanda za ki tafi ki dinga fitowa Muna yin breakfast tare kin ji ko!?",gyada mishi kai ta yi sannan ta zauna, murmushi anty amarya ta mata.
Hajiya babba ta ce "yanzu ke ce kika zama cikiton yan matan suka zama guda shida,har na tuna da Asrah da tana nan nasan da yanzu ta damu kowa da surutu", murmushi uncle Hameed ya yi yana tuna irin rigimar da Asrah take yi.
"Da yanzu ta na nan nasan da tana gefen LTG ta dameshi da surutu,ko kuma wajen Ammi".
Duk murmushi sukayi hatta shi LTG din jin an fara hirar farin cikin rayuwarsa,hakan yasa shi murmusawa.
Anty amarya ta maida hawayen da taji yana son fitowa daga idonta,ta ce"nasan da Asrah na nan, da ta ce mommy ki goyani,hhhhhh!ko da yake ma nasan inta girma bazata yi ba,sede shagwabar da ya riga da yabi jikinta daga anyi mata faɗa zata fara kuka tana neman Tajuddeen dinta",duk jikin su ne ya yi sanyi sosai jin yanda muryar anty amarya yake fita.
Cikin zolaya dan ya kawar da damuwar kan fuskar anty amarya Saghar ya ce"Abokiyar faɗa ta ba, kullum se munyi faɗa, ga kuma LTG dake shiga mata faɗa, lokacin da LTG ya samu addimission,na yi farin ciki sosai saboda na sa araina in ya tafi zanci zalinta sosai"dariya sukayi gaba dayansu hatta LTG se da ya murmusa.amma babu wanda ya lura da hakan Saboda kansa dake ƙasa yana danna waya.
"Yanzu da zan samu ganin yar kanwar tawa zan jata a jiki sosai bazan taɓa barin muyi faɗa ba, ko da kuwa rashin jinta ya zarce na Umaisha da Rameesa"nan ma murmushi suka yi,yau de gaba daya hirar su akan Asrah ne,babu wanda ya saka abinci a bakin shi se hiran da suke yi,duk suna cikin nishadi da kuma kewarta sosai,a duk sanda aka fara hirar Asrah a gidan tofa se sun dau lokaci me tsayi sunayi domin tunawa da ita.
Murmushi Zoya ta yi, ta ce "bana manta lokacin da muna yara haka zamuje wajenta dan muyi wasa amma haka zataki binmu se munyi dakyar kafin nan zata yarda". "To kin manta lokacin da mukaje painting room muka dauke zanen da take yi muka gudu a hanya muka yagashi!"cewar umaisha.
Ammi ne ta yi dariya"ai yanzu da tana nan kaf dinku da mun aurar da ku "rufe fuska Parsa ta yi tana dariya.
Ummah dake gefe ta ce"wato anyi maganar aure kin rufe fuska"dariya sukayi,ganin tana ta dariya.
Tun lokacin da suka fara hirar su suna ambaton sunan Asrah ta farajin kanta na wani irin juyawa,a duk lokacin da aka ambaci sunan se taji tsigar jikinta ya tashi ta rasa meyasa hakan,kuma ita tunda tazo gidan bata ga Asrah din da suke magana akai ba 'shin tana ina ne to?' ta jefawa kanta tambaya.
Dakyar ta kauda damuwar kan fuskarta ta ce "Ammi to ina Asrah din yanzu take!?".
Anty amarya dake gefenta ne ta bata amsa da "Asrah bata a tare damu,bamu san duniyar da take ba ko tana raye ko tana mace!,amma ni a har kullum ina da yakinin tana raye kuma ina jin kusancinta, ina rokon Allah yasa koda a ranar da zan bar duniya ne inga ƴata". tausayi sosai anty amarya ta basu,sun san tana cikin damuwar da ita kadai tasan zafin da take ji.
Shuru Sabriyah ta yi jikinta a mace.ashe kowa yana shiga irin wannan damuwar idan ya rasa farin cikin sa,ta dauka ita kadai ce takejin zafin rabuwa da Asmita.
Murya a karye ta furta"Nima na shiga irin wannan matsanancin damuwar da tashin hankali a lokacin dana rasa Asmita,kowa yana jin ba daɗi a duk sanda ya rasa wani bari na rayuwarsa".
Duk kallonta suka yi cikin jimami,Ammi ta ce"in sha Allah, Allah ze bayyana mana su".
Murmushi me ciwo anty amarya ta yi bata iya cewa komai ba.
Mikewa LTG ya yi a dinning din ya fice daga Mansion din gaba daya.
Bin bayansa da kallo sukayi sun san an fama mishi inda ke mishi ciwo ne yasa ya tashi ba tare da ya yi breakfast din ba.
Serving din kowa abinci Fatime ta yi.suks fara breakfast.
Tashi ta yi ta zauna a tsakiyar gadon da aka kwantar da ita. ƙarewa wajen kallo ta yi sannan tasa hannu ta fincike ruwan hannunta,tsoro ne yakamata ganin ita daya ce a dakin yasa ta fashe da kuka,kamar karamar yarinya.
Fitowa ta yi acikin dakin tana tafiya tana kuka harta iso cikin main part falo,bata dena kukan ba.
Cikin yarinta ta soma kiran sunan Sabriyah,tana tura baki .
Tana kokarin kai bread bakinta taji kamar murya Asmita ce ke kiranta hakan yasa ta kasa kunne ko zata sake ji, amma shuru hakan yasa tayi tunanin ko imagination da ta saba yi ne,dan haka kullum se ta ji kamar Asmita na kiranta.
Ci gaba da breakfast dinta ta yi,da ɗan karfi taji an sa'ke cewa "Sab.....ri....yah".
A zabure ta mike tsaye wanda yasa duk seda suka kalleta, tambayar ta Sudais ya yi "Sabriyah lafiya!?".
Cikin rawar murya kamar me shirin yin kuka ta ce, "ba kuji kamar ana kirar sunana ba!?,muryar Asmita nakeji"da mamaki suke kallonta amma ɗan son tabbatarwa se suka kasa kunnesu suma,nan sukaji "Sab..ri....yah" tabbas su ma sun ji an kira sunanta,da gudu ta bar dinning din suma miƙewa sukayi suka rufa mata baya.
Tana shigowa tsakiyar falon taga Asmita a tsaye se waige_waige take yi da alamar ita take nema,farar fatarta ya yi duhu ga gashin kanta daya hargitse kayan jikinta kansa ya yi datti.
Kamar a mafarki take kallon Asmita murya na rawa ta ce"My Jerry"da sauri ta juyo jin muryar Sabriyah,da gudu suka rungume junansu suka fashe da kuka me ban tausayi,sunkuyawa ƙasa sukayi har lokacin suna rungume da juna,shafa bayan Asmita Sabriyah takeyi tana kuka dan tayi matukar kewarta kukan farin ciki, da kuma na kewarta takeyi ga kuma ganin yanda duk ta lalace kamar ba Asmita ba.
Dakyar ta dakata da kukan ta ce "my Jerry su waye suka sace ki,ya akayi kika zo nan"a maimakon ta bata amsa se turo baki ta yi "my Tom ba kece kika gudu kika barni ba!,tom muje mu hau lilo kinji"zaro duk idanunta waje ta yi kamar zasu fadi ka sa domin tunda Asmita ta bude baki ta fara magana ta fahimci ba a hankalinta take ba ga yanda take magana kamar wata karamar yarinya me kananun shekaru.
Tallafo fuskarta ta yi da duka hannunta biyu ,"my Jerry meyasa kike magana kamar yarinya karama Meye abinda wayan'can mugayen suka Miki!?"oho ita de bata fahimci inda zancen ta ya dosa ba.hakan yasa ta zuba mata ido kafin kuma lokaci daya idanunta ya rufe ta kwanta ajikinta, jijigata Sabriyah ta yi taga bata motsi.
Suna tsaye a falon suna kallon su tausayinsu ya cika su,ganin irin shakuwar da ke tsakanin su,dole ne in babu ɗaya,dayan su ya shiga damuwa,ga kuma mamakin abinda ya faru da Asmita suke yi.
Kusa dasu Saghar yazo ya tsaya yaga yanda ta daga hankalinta.
"Sabriyah ki kwantar da hankalinki!jiya LTG Taj yasa aka kwato ta daga wajen yan ta'adda,ta samu matsalar ƙwaƙwalwa ne ta sanadiyyar shaƙa mata fodar ibilis din da suka dinga yi hakan ne yasa ta samu matsala ,in sha Allah zata warke".
"
Wani shock Sabriyah taji tunda ga tafin ƙafanta har zuwa tsakiyar kanta,wai Asmita ta samu matsala a kwakwalwarta.
Kamar wata wawiya ta ce "matsala a kwakwalwa kuma ya Saghar!?",gyada mata kai ya yi,kuka tasaka tana kallon kyakkyawar fuskar Asmita da ya yi fayau.
"Kiyi hakuri Sabriyah wannan kukan bashi da amfani ki mata addu'a kawai tunda Allah yasa Tajuddeen ya sa an kwato ta,ku taimaka mata,a kai Asmita daki"cewar Ammi.
Su Umaisha ne suka taimaka mata wajen ɗaukan daukan Asmita suka tafi part dinsu.
Zama sukayi a falon uncle Hameed ya ce "gaskiya na tausayawa rayuwar yaran nan duk da bamu san labarin su ba" "ni kaina rayuwar su tausayi yake bani,musamman da Sabriyah ta faɗa mini daga garin da suke".
"Tun jiya nakeson sanar da ku abinda ke zuciyata kuma nasan zaku bani goyon baya akan hakan".cewar Anty amarya,maida hankalinsu kanta sukayi domin jin menene take son sanar dasu.iya kan su ne a falon se su Sudais,su Umaisha kuma basa nan.
Ci gaba da magana anty amarya ta yi "na yanke shawarar zan yi adopting din Sabriyah in mayar da ita ƴata banason tabar wannan gidan,nayi rashin ƴata Asrah wacce ita ce farin cikina banida damar iya haihuwar wata yar,tunda banida mahaifan daukan wani cikin,tun ranar dana fara ganin Sabriyah naji ta shiga raina, Allah ya daura mini son yarinyar,jinta nakeyi kamar jinina!,kamar ni na tsuguna na haife ta haka nake ji.zan maye gurbinta da Asrah kafin Allah ya bayyana mini ita in rikesu su biyun.zan zame mata uwa da ba ta dashi,zan zame mata duk wani gatan da ta rasa,zan mata komai, makaranta boko da islamiyya".
Shuru ne ya biyo bayan,duk sun yi shuru suna nazari akan maganar da ta faɗa,sun san inde ta ɗauki Sabriyah din hakan ze rage mata raɗaɗin da takeji na batan Asrah,kuma inta yi haka zata samu lada.
"Mun ji bayanin ki kuma ni kaina,na gamsu da hakan sede ki bari su Abbie su dawo,se mu ji ta bakinsu tunda Kinga sune manya"cewar Hajiya babba,sun gamsu da zancen ta,tunda yaran nan in an barsu sun tafi ruwa zasu sake komawa.
"Ohhhhh!wato Abida ta nan ta bullo kenan,dole in samu Hajiya khareema in bata wannan sabon labarin"duk wannan zancen da Ummah take yi a zuciyarta take yinsa.
Suna a falon ne nurses guda biyu suka shiga sanye da uniform, Saghar ne ya kira su domin kula da Asmita shi bayi da wani isheshen lokaci.
Kallon kaltume Saghar ya yi ya ce"please kaltume dan rakasu dakin Sabriyah mana".
Bismillah ta musu ta yi gaba su kuma suka biyo ta abaya.dakin suka shiga nan suka samu Asmita dake a sume,ga Sabriyah a gefenta ta zuba mata idanu tana kallon ta ga tausayinta fal ranta,tama rasa ya zatayi,ji takeyi dama matsalar ƙwaƙwalwar ya dawo kanta.
Gabatar mata da kansu sukayi ,su ka sheda mata sune masu bawa Asmita kulawa,ta yi murna sosai duk dama ita dayanta za ta iya kulawa da Jerry dinta.a zuciyarta kam mamaki ya kasa dena mata,a ce LTG ne ya ceto Asmita,batasan da wani irin baki zatayi amfani wajen gode masa ba.
Dan Allah ki dan bamu waje zamu dubata ba dan ranta yaso ba haka ta fita ta basu guri.
Ruwan Allura dayar nurse din ta ja a syringe,ta je gaban Asmita ta tsaya tana jan hannun rigarta kasa zata mata,kamar wacce tasan allura za'a mata ta mike da sauri ta ɓige hannunta,ta koma can kuriyar gado ta manne tana kuka,duk iya kokarin su na ganin sun rike Asmita su mata allurar amma abin ya ci tura,saukowa ta yi da gudu zata bar dakin taga Mutum a tsaye a bakin kofar, faɗawa jikinsa ta yi ta rungume shi gam kamar zata koma Cikinsa.
"Banaso!banso!banaso!,ka ce musu kar su mini banason allurar can".,a hankali yake kokarin rabata da jikinsa amma ta ƙi sake shi ga kukan da takeyi,dama ya yi tunanin hakan ze iya faruwa shisa ya biyo bayansu.dede kunnanta ya ce"kyalesu duk se na musu duka, ni da kaina zan yi miki allurar kinji,daga nan se in daukeki ke da Sabriyah muje wajen lilo,da kuma shan ice cream bayan nan se in siya miki biscuits da minti ko".cikin ƙaguwa ta ce "yeeeeeeeh!kuma ma kaima ai zaka hau lilo din ko!?",ta tambaye shi tana kyalkyalewa da dariyar murna, gyada mata kai ya yi,bata ga hakan ba domin tana rungume a jikinshi,kuka ta sa'ke sawa tana bubbuga ƙafafunta,dafe kai ya yi yau yaga ta kanshi,cikin nutsuwa da magana me dad'i wa patient ya ce "Meye kuma Asmee?", "To ai ba kace zaka hau lilo din ba!",ba shi ba hatta nurses dake kallonsu seda su kayi dariya jin maganarta.
"Eh mana ni zan kai ku,dukkanmu zamu hau lilo kowa ma ze hau, shikenan!?"raba jikinta da nashi ta yi tana kallon shi, ta tafa hannu ta fara tsalle_tsalle,juyawa wajen su nurses din ta kallesu tana musu gwalo,ta ce"bazaku hau lilo baaaaaaaa!"dariya kawai suka yi mata,rike hannunta ya yi ya kaita bakin gadon ya zaunar da ita.
"Doctor Saghar!ta ƙi yarda muyi mata allurar". "Karku damu zan mata da kaina"Saghar ya faɗa yana sunkuyawa a gabanta,hannu yasa cikin aljihun wandon sa ya fito da chocolate diary milk,ya mika mata,karba ta yi tana washe baki, ba tare da bata lokaci ba ta bare ledar chocolate din ta fara sha tana lumlumshe ido,cikin dabara ya karbi allurar a hannun dayar nurse din,ya ɗan zagaya ta bayanta ya mata shi,tana shan chocolate dinta ta yi dama_dama da bakinta da chocolate batama san ya mata allurar ba.
Doctor Saghar na matukar burgesu ya kware sosai akan aikinsa, kwararren doctor ne da ake ji dashi,in yana gaban patient dinsa zakayi tunanin ko a gaban kanwarsa yake,yanda yake maida kansa kamar karamin yaro, musamman in yaje duba patient din da suka kasance yara ko kuma masu matsala irinta Asmita, ya nada saukin kai da kuma zolaya,amma wani lokacin bayason magana.
Miƙewa ya yi ze bar dakin da sauri ta riƙo bayan rigarsa ta shagwaba fuska, kallonta ya yi yaga yanda ta yi da fuska.
"Dan bika ka ji?" "Ah ah ki bari yanzu zakiyi wanka ki sa kaya masu kyau se ki bini kinji!?, Kinga kayan jikinki sun yi datti"kallon kayan jikintan ta yi taga sunyi dattin,turo baki ta yi "to karka gudu"gyada kai ya yi sannan ya fice a dakin,dede ze bar part din nasu ya hadu da Sabriyah dake shigowa.
"Ya Saghar yana ganka anan?" "Asmee taki yarda nurse din su mata allurar shine na yi mata da kaina"murmushi ta yi "okay nagane"har ta juya zata shiga,ya kira sunanta dawuwa ta yi ta tsaya tana kallonsa.
"Ki bi ta aduk yanda tazo tunda Kinga ba'a hankalinta take ba, kwakwalwarta ya koma na yarinya me shekara takwas a duniya,ki bita a hakan se mun fi samun saukin komai,karki yi kokarin tuna mata abubuwan da suka faru, hakan ze sa ta fara ganin flash wanda hakan zesa ta koma wata matsalar kuma daban.shi wannan matsalar nata baya bukatar gaggawa,kulawa da kuma magani masu kyau da manyan allurai take bukata.zan turo mata da chocolate anjuma".
"Shikenan ya Saghar zan kiyaye"a haka suka rabu shi ya fice ita kuma ta shiga bedroom din,samun Asmita ta yi zaune a tsakiyar gado daga ita se towel a daure.
Tsayawa kawai ta yi,tana kallonta har yanzu mamaki be fita a ranta ba,wai yau Asmita ce, a haka kai gaskiya rayuwa abar tsoro ne.
"My Jerry waya baki chocolate!?"ta mata tambaya tana zama a gefenta.
Washe baki Asmita ta yi seda ta ɗan yi jim kamar wata me tunani can kuma ta ce "me kyau ne yabani"dariya ta yi wato Saghar din ne me kyau,hmm lallai kam gaskiya ta faɗa domin gaba daya mazajen gidan suna da matukar kyau me tafiya da hankali uwa uba suna shigen kama da juna,haka yan matan ma.
Surutu Asmita take ta mata,ita a hakan wai labari take bayarwa,wani maganar dakyar Sabriyah take ganewa.
Wanka masu kula da ita suka mata,suka shiryata cikin dogon riga na material ɗinkin play,ta yi kyau sosai duk da akwai rama a tare da ita, dankwali za'a daura mata,ta da ka tsalle tace bata san zancen ba,ita sede a raba gashinta gida biyu a mata fakin haka kuwa sukayi mata da dogon gashinta.
Su Rameesa ne suka shigo dakin su hudu,banda Zoya dake part din Ammuh.iklas hannunta na dauke da abincin da Ammi ta turo ma Asmitan.
"Hi! Asmita yakike?"su ka faɗa tare, tana kwance ta yi filo da cinyar Sabriyah,dago kai ta yi tana kallon su,ta kuma ƙi musu magana,"my Tom inyi musu magana!?"ta tambayi Sabriyah,gyada mata kai ta yi.
"Ku ma zakuje lilo din ne!?,ni an min wanka an yi mini kwalliya ma na shirya me kyau nake jira" "eh mana duk zamuje, yanzu ki fara cin abinci tukun nan"Iklas ta yi magana tana buɗe mata plat din abincin,chips ne da miyar hanta se soyayyen kwai.
Maƙe kafaƙa ta yi alamar bazata ci ba,rike hannunta Sabriyah ta yi tana shagwabe fuska itama"to shikenan karki ci din,ni kuma bazan je lilo din ba tunda abin hakane"da sauri ta jawo plat gabanta dan bataso Sabriyah ta ce bazata je ba,"yauwwa ko kefa"ta faɗa tana fara bata abincin abaki,su Umaisha bakaramin burgesu sukayi ba,duk da ya kasance Asmita bata cikin hankalinta amma kaunar dake tsakanin su be gushe a wajenta ba,tana bata abinci abaki tana yi mata hira,suna dariya.
Tayasu hira sukayi har lokacin sallah Azhar ya yi suka tashi suje suyi.
Ya yi saura su biyu a dakin nurses dinma sun fita, Asmita bacci ya dauke ta,in ta ga Asmita sanyi takeji a ranta,yanzu mutane biyu ne ya yi saura ta ji halin da suke ciki, kwana biyun nan tana yawan mafarkin anty Teema tana ce mata yaushe zata dawo se in tana kokarin bata amsa se ta farka.
Se kuma Fu'ad da batama san ta ina zata fara binciko shi ba,fatan ta ɗaya shine Allah yasa yana cikin koshin lafiya.wayarta yana a dakin su na afafa,lokacin da suka fito ita da Asmita zuwa wajen Taheer, basu fito da wayoyinsu ba,ga shi bata rike number Fu'ad akanta ba ɓalle ta kirashi.
Kano state
Falo ne me girma,me kyawun tsari gwanin burgewa,