Showing 36001 words to 39000 words out of 94974 words
gaye ne kam. Ya ce"ya sunanka?"saurayin ya bashi amsa da"umar"
Jinjina kai ya yi kafin ya ce
" okay Umar!I need your help,shin akwai in da zan samu a rage mini gajiyata ne anan kusa ?"murmushi Umar ya yi ya ce"haba ranka shi daɗe kode ka manta a garin da kake ne Lagos ne fa! in mata ashirin kake so tofa zaka samu"gyada kai ya yi ya ce"akwai wacce kasani kyakkyawa,me shape wanda ze dau hankali kuma wacce ta iya tsabta?" "Ehh sede ka duba akwai hotunan su da kuma videos a wayata se in nuna maka su kazaba,kasan kaff garin nan babu kn da yakai afafa yawan ashawo."yana maganar yana laluba wayarsa acikin aljihun wandonshi ji ya yi wayam nan ya tuna ya baro wayar a reception ya ce"give me some minutes bari in dauko a reception"gyada mishi kai kawai ya yi.
Bayan kamar minti goma umar ya dawo hannunshi rike da wayar tashi shiga cikin gallary ya yi, ya mika mishi yana kallon hotunan duk yan matan babu wacce ta yi mishi acikinsu miƙa masa wayar ya yi ya ce"banga wacce ta min ba"da sauri ya karbi wayar ya lalubo mishi video wata tana rawa "ga wannan ka kalla na tabbatar da se ta burgeka"karba ya yi ya fara kallo.
Dirin jikinta da skin dinta haɗe da tsawon gashinta ne ya tafi da gaba daya ilahirin imaninshi be san lokacin da murmushi ya subuce mishi ba ya ce "tabbas wannan ta yi sede nafi son virgin wacce ni zanyi disvirgin dinta da kaina" "a afafa take Wallahi dan ma bakaga fuskanta bane kyakkyawa ce ta ajin farko kaff cikin afafa babu wacce ta kaita kyau" daga filo ya yi kuɗaɗe ne zube akan gadon bandir biyu ya lalubo ya ce"okay ga shi karike wannan"hannu na rawa Umar ya karbi kudin a iya rayuwarsa be taɓa riƙe irin wannan kudin ba wanda a ƙalla sun kai dubu ɗari biyu se jujjuya su yakeyi"Nagode!nagode sosai ranka ya daɗe"murmushi ya yi ya ce "karka damu gobe ka shirya se ka rakani can din in je in daukota. saboda bana iya yin bacci se na ji ni ajikin mace,zaka iya tafiya."cike da farin ciki ya bar dakin yana sake gode mishi domin kuwa shi yau ya haɗu da babban rabo.
Washe gari da wuri ya shirya yazo dakin nashi. bayan ya bashi izinin shigowa,zaune ya sameshi daga shi se singlet da guntun wando ga laptops a gabanshi jere akan gadon sun kai biyar mamaki ne ya kama umar aranshi ya ce"mutumin nan meyakeyi da wa'yannan laptops din?an ya ba ɗan yahoo bane kuwa?"shi kadai yake magana kuma yake tambayar kansa sanin babu wanda ze bashi amsar ne yasa ya gaisheshi ya ce"sir na shirya zamu iya tafiya?"kallon agogon hannunshi ya yi yaga almost 10:00am ya ce "eh bari in shirya se muje ka jira ni awaje inna gama zan sameka." "To shikenan"murda handle din kofar dakin ya yi ze fita ya ji yana waya abinda yaji ya futar shine..."wa ya gaya musu zasu iya dani?mutum nake me kama da aljan.just becarefull domin naji an ce shi aka bawa case din kuma yana da matukar hatsari ni na sanshi ku bi umarnina ku cece rayuwark...."be karasa maganar shi ba sakamakon ganin Umar da ya yi a tsaye a bakin kofar be fice ba.daga kai ya yi yaga suka haɗa ido da Umar din yana tsaye be tafi ba duk da yabude kofar watsa mishi harara ya yi ya ce "akwai wani abinda kake jira ne?"da sauri ya fice daga dakin zuciyarsa ya fara zargin shi,"shin wanene shi din?"tambayar da yake tayiwa kanshi kenan duk da a ido beyi kala da mutanen banza ba very gentle man.
Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.
Comment,like and share 🖋️🖋️
*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*
Page 14
*_Story & written_*
By
*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)
*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️
Page 14
Shiryawa ya yi cikin kananun kaya ya fito hannunshi rike da car keys a reception ya sameshi suka fito suka shiga mota umar ne ya dinga mishi kwatance har suka shiga cikin afafa, packing ya yi a bakin gate din gidan karuwan suka fito hannunshi na cikin aljihun shi se ƙarewa wajan kallo ya keyi ga yan mata se shige da ficen su sukeyi ko wacce babu isasshen sutura ajikinta,wata ce tazo wucewa Umar ya tsayar da ita ya tambayeta inda zasu samu boss lady,ita ta musu jagora har wajan boss lady kamar ko yaushe tana hakimce akan kujera dan daudun nan na yi mata yankan farce.
Shigowa sukayi su ka samu waje suka zauna boss lady na kallon shi tasan eh za'a samu kudi awajan shi nan take ta fara washe baki nan ya faɗa mata bukatarsa "ai inde wannan ne karka damu akwai tsala_tsalan yan mata agidan se wacce ka zaba"wani munafukin murmushi ya yi ya gyara zama ya ce"nooo!akwai wacce aka nuna mini kuma saboda ita kadai nazo nan but zan fi jin dadi idan ita din virgin ce" nuna mata video suka yi murmushin dake kan fuskan boss lady ne lokaci daya ya dauke ta haɗa rai ta ce "ka zaɓi duk wacce kake so acikin gidan nan amma banda Sabriyah"da mamaki su ke kallonta jin abinda ta faɗa.umar ne ya ce"amma meyasa banda ita?"boss lady ta ce "saboda ta yi laifi tana dakin horo se nan da sati daya za'a fito da ita sede in zaku dawo bayan sati daya"girgiza kai ya yi, ya ce"bazan kai sati daya a kasar nan ba!laifin me ta aikata haka ina da matukar bukatar ta"tabe baki ta yi ta ce "sarka na da yakai darajan Naira miliyan daya da rabi ta sace"murmushi ya yi ya ce "ki fito da ita zan baƙi million uku"zaro ido waje boss lady ta yi tana sake kallon shi ɗan son tabbatar da abinda ya faɗa bama ita kadai ba dukkansu mamakin shine ya kamasu gyada mata kai ya yi alamar tabbatarwa jiki na rawa ta cewa dan daudun "jeka fito da hot girl"da hanzari yabar wajan yana tafiya yana rangwada.
Bayan mintuna ya dawo yana gaba Sabriyah na binshi abaya gaba daya ta galabaita ga idonta ya kumbura sakamakon kukan da ta yi se ya mutsa fuska takeyi tsayawa ta yi agabansu.
ɗan daudun ya ce"boss lady ga ta nan"jin an ce ga tanan da akayi ne yasa ya ɗago kai ya zuba mata ido,kasa janye idonshi ya yi akanta kyawunta ne ya fisgeshi da be san lokacin da ya mike tsaye ya nufi inda take tsaye ba kanta a ƙasa hannu yasa ya ɗago habarta suka zubawa junansu ido, watsa mishi harara ta yi da idanunta da suke a kumbure cikin tsiwa ta ce" meye hakan dalla sakeni"ƙayitatciyar murmushi ya yi, ya ce "I like that ina son yarinya me tsiwa da rashin kunya irinki, so sexy"bata fahimci me ya ce ba saboda sauran maganar da ya yi din da turanci ya yi shi tsaki ta yi ta ja baya tana ci gaba da hararanshi.
Boss lady ta ce "ki dena mishi wannan shegiyar rashin kunyar taki saboda shine nan ya fanshe ki! ɗa yanxu kina can cikin dakin horo,ɗan haka binshi zakiyi har se ranan da ze koma idan ya tafi se ki dawo"wani irin bakin cikine ya tokarewa Sabriyah maƙoshi jin abinda boss lady ta faɗa satan kallon shi ta yi taga ita yake kallo yana mata murmushi se sannan ne ta kare mishi kallo balaifi ya burgeta.
Ciki_ciki ta ce"to barin inje inyi wanka"bata sauraresu ba ta bar sashen ta nufi nasu abakin kofa ta tarda Asmita zaune gaba daya bata cikin walwalar ta tafi duniyar tunani Nabiha na ciki ta daura musu abinci. har Sabriyah ta shigo Asmita bata sani ba ji kawai ta yi an rungumeta dagowa ta yi dan taga waye.ganin sabriyah ne yasa ta yi ihu ta rungumeta itama suna dariya "my Tom ya akayi tabarki kika fito?"Asmita ta tambayeta. nan Sabriyah ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da ita,Nabiha dake gefen su ta ce "gaskiya wannan gayen ya kyauta kawai ki bishi ki bashi kaya"hararan wasa Sabriyah ta mata ta ce "duniya da ƴaƴanta za bashi ba kaya ba"dariya sukayi dukkansu Sabriyah ta ce "my Jerry tashi mu shirya dan ƙafata, ƙafarki tare zamu je in ya so yamma se mu dawo amma nikam bazan kwana a wajan shi ba".
MAIDUGURI
Kyawawan yan matan Bishara's ne zaune a falo su hudu babu mutum daya ko wacce da abinda ta keyi daga me danna waya, se me cin snacks,sauran biyun kuma suna ludo.
"Zoya miƙo mini laptop ɗin ki zanyi downloading,nawa na barshi a balcony"Umaisha ce ke yi wa Zoya magana tana kwance ko juyowa batayi ba balle ta bata laptop din nata tana kwance akan kujera tana chatting.
"Dama dena bata baƙin ki kikayi, kinsan iskaci irin na Zoya ai,shisa na tsani Wallahi magana ya hadani da ita shegen girman kai da renin wayo"Parsa ta faɗa tana watsawa zoyan harara saboda ta tsani halin Zoya tana da mugun shariya duk da uwa daya uba daya suke amma hali be zo daya ba,jin abinda Parsa ta faɗa ne yasa Zoya ta mike zaune kanta babu hula gashinta bashi da tsayi sosai a kafardata ya tsaya tana sanye da riga bubu na atamfa ta ce "nikam Parsa ina wasa dake ne!? ko kuma reni ne da har kike kokarin zagina?"tsaki Parsa ta yi suka ci gaba da ludo da sukeyi ita da iklas.
A harzuke Zoya ta yi kan Parsa zata kai mata duka saboda tsakin da ta mata ya bata mata rai sosai,hannu Umaisha ta sa ta jawo rigar Zoya "meye haka!? dan kawai ta faɗa miki gaskiya shine za ki daketa? Wallahi Zoya ki canza hali" "ina ruwanki kanwar ki ce ko kanwata?" Saketa Umaisha ta yi ta ce "to Wallahi ko ke kika haife ta bazan bari ki dake ta ba se kace wani girmanta sosai kikayi tsakanin ki da ita shekara daya ne amma se shegen son girma kamar gembo"duk wannan rikicin da Zoya da Umaisha sukeyi su iklas da Parsa basu kula su ba saboda dama sun saba kullum cikin faɗa suke,ke Zoya shariya ko zaka shekara kana mata magana bazata kulaka ba amma duk wannan abun nata batayiwa sauran brothers din su dan tasan duka zatasha iya kaci su Iklas din takeyi wa se kuma wanda be santa ba,ga bak'ar magana. ita kuma Umaisha tsokana da shiga abinda ba'a sa da ita ɓa.babu ruwanta kowa natane tana da saurin sabo bata da girman kai komai dinta simple ne a kwai barkwanci tana kuma son yan uwanta musamman ya'yanta Tajuddeen.
Tattausan murmushi Parsa ta yi nan ainihin kyawunta ya sake fitowa saboda dariya da murmushi dabi'ar ta ne shisa idan ta bata rai har kamar kamanin ta sauya wa yake hakan ya rigada yabi jininta abu mawuyacine Parsa ta bata rai sosai akai,bata iya dogon fushi da mutum ko da kuwa mutum ne ya bata mata rai to ita zata bishi ta bashi hakuri, dan su ci gaba da magana,ko da wani abu kayi ko ka faɗa dan yabatawa Parsa rai tofa kayi abanza saboda ita babu ɓacin rai a cikin rayuwarta komai dinta murmushi ne haka zalika tana son yan uwanta sosai,shisa take jin haushi duk sanda taga abinda Zoya takeyi wa mutane.
Murmushi ta yi ta ce "haba ku kuwa maganar ma nadauka ya wuce,Zoya kiyi hakuri baxan ƙara ba kinji!?kema Umaisha kiyi hakuri Zoya ba zata sake yunkurin dukana ba.kun ji masoyana ina sanku sosai"ajiyar zuciya Zoya da Umaisha suka sauke kusan a tare, murmushi Zoya ta yi ta ce "shikenan masoyiya bazamu sake ba,yanzu ku tashi muje muyi sallah kunga an idar da la'asar a masallaci kar su ya Sudais su zo su ga ba muyi sallah ba."
Rike haɓa Umaisha ta yi cike da neman tsokana ta ce"Allahu Akbar!! yau wa ze mutu Zoya na yiwa mutane wa'azi!! gaskiya Allah ya miki albarka masoyiya, kullum ki dinga mata kafin ku fito da safe ko......"bata karasa maganar ta ba taji an wurgo mata filo tasan aikin Zoya ne dariya sukayi harda iklas da ta yi tagumi tana kallon su tana dariya,guje_guje Zoya da Umaisha suka fara yi a falon suna dariya Zoya ta nace se ta kama Umaisha.
Murmushi da baya daukewa akan fuskar Parsa ba tare da dalili ba yana nan azuciyarta ta ce"duk wani farin cikina ze biyo baya ne,bayan naku ina matukar kaunar ku family na".
Nufan hanyan fita falon Umaisha ta yi tana kallon bayanta bata san akwai mutum a gabanta ba kawai taji ta buge mutum,ja da baya tayi ta dago kai ta kalleshi mugun kallo da yake mata ne yasa taji gabanta ya faɗi lokaci daya ta shiga rigar nutsuwarta. Zoya dake Binta a baya ma tunda taga waye ne yasa simi_simi ta gudu sama, haka iklas da Parsa duk guduwa sukayi.
A kausashe ya ce "bana hanaku wasan banza ba!?ko har yanzu ku yara ne!?"ya tambaye ta yana kallon fuskar ta da ta sunkuyar dashi ƙasa, girgiza mishi kai ta yi dan tama ka sa magana.rankwashi ya mata a kai wanda se da yasata ta yi ƙara ta daura hannu awajan tana shafawa.
"Ina dankwalin ki yake!?yaran nan yanzu ba a isa a faɗa muku magana ku ji ba kenan ko!?" Gudun kar ya sake ka fa mata wani rankwshin ne ya sa ta ce "dan Allah ya Sudais ka yi hakuri Wallahi baxan sake fitowa ba hula ba!"
Kallon gashin nata da yake kwance a gadon bayanta ya yi ya ce"in na sa ke ganin ki ba hula ki sa aranki ranan kwanan wannan gashin naki ya ƙa re.matsa kiban guri ko in yi ball dake."da sauri ta matsa tabashi hanya ya wuce ta bishi da kallo,fari ne dogo kyakkyawa yana da ginan nen jiki yana sanye da farin uniform na custom da hula komai dinshi fari alama daga office yake.murguda mishi baki ta yi kafin itama ta sa kai ta wuce ciki.
Duk dramar da akeyi Rameesa na daga saman upstairs tana kallon su tunda ga lokacin da Zoya da Umaisha suka fara faɗa har zuwa lokacin da suke guje_guje da kuma shigowar Sudais din.banda dariyar mugunta babu abinda takeyi tana"Umaisha Wallahi in bakiyi wasa ba wata rana sede kiji ya Sudais yasa almakashi ya gimtse miki wannan gashin naki"ita kadai take magana tana dariya.
"Ke kuma ke dawa kike wannan dariyar kamar wata kun kuncecciya!?"cewar Ammi da fitowar ta kenan daga part din Hajiya babba ta hangi Rameesa se dariya takeyi rungume Ammi Rameesa ta yi kafin ta tsagaita da dariyar nata ta ce"Ammi Wallahi su Umaisha basu jin magana wata rana se sun wayi gari sunga anyi musu malu,sun san sarai su ya Sudais,ya saghar,ya Jawan,ya Salim,ya Sahil, se sun musu magana akan saka hula ko dankwali amma su basu ji"dariya Ammi ta yi, ta mata marin wasa ta ce"ja'ira ke dinma yaushe kika fara saka dankwalin ina se da Jawan ya dake ki kafin kikayi hankali?"turo baƙi Rameesa ta yi"ni Ammi dena tuna min."dariya sosai Ammi ta yi kafin ta ce "nikam ɗaga ni,in yi gaba"dagata tayi tana dariya ta yi part din su da gudu.girgiza kai Ammi ta yi aranta ta ce "yaran nan kude bazaku taɓa girma ba".
Duk suna zaune a part din su, Umaisha na zaune har lokacin hannunta na bisa kanta tana shafawa,Zoya ta ce "Allah ya taimakeni da ya Sudais ya ganni Wallahi nasan yau jikina se ya faɗamin saboda yau da safe kafin ya fita aiki seda ya mini rankwashi" "ke nifa tunda ya Jawan ya taba lafiyar jikina nadena yawo ba hula,ku ai bakwajin magana kun san sun tsani suga mutum ba hula akanshi"cewar Rameesa dake zaune kusa da Parsa,gyara zama Parsa ta yi ta ce "bama maganar basa so ba babu kyau ne yawo gashi awaje kuma duk mun sani yakamata mu gyara saboda shedanu"haka suka dinga hiransu Umaisha de batace musu komai ba,dan har lokacin kan nata na mata zugi.
"Anty amaryanmu me kike dafa mana ne naji irin wannan kamshi me dadi haka!?"juyowa ta yi ta ɗan yi murmushi ta ce"abincin dare ne Saghar !me kake so a yi maka?"ta yi maganar tana kallon shi.
"Ni banason komai na fi son abu liquid haka ko romon farfesu kawai amma kar asamin nama kawai romon nakeso."
Rike baƙi Anty amarya ta yi ta ce "ku fa likitocin nan kunfi kowa kinibibi,da kai da uncle din ku kuna bani mamaki wai kuce ku bazakuci abinci da daddare ba sede kawai abu ruwa_ruwa.muda mukeci de ga shi bawai lafiya kuka fi mu ba."dariya Saghar ya yi "Anty amarya bazaku gane bane,da kun san illan cin abinci me nauyi da daddare tofa da kun dena domin ze sa muku upset stomach" "dallah yi mini shuru jeka zan biyoka da romon"sa kai ya yi ya fice yana dariya yabar Anty amarya ma tana darawa.
Bayan sun yi sallar isha kowa yadawo sun hadu a dinning table banda Abbu da Abbie da ba sa ƙasan.
Serving din kowa abincin da ranshi yake so fatime da kaltume suka yi,a tsanake suke cin abincin Ummah ta kalli Saghar ta ce "yau da ka dawo me ya hanaka zuwa ka gaishe ni Saghar?!" Ajiye spoon din hannunshi ya yi ya zuba mata ido domin ta taɓo mishi inda yake mai kaikayi Ammi ce ta daura hannunta akan nashi alamar kar ya ce komai,amma ya gagara shuru"kin zauna agidan ne ɓalle mu ganki mu gaisheki!? kullum kina hanya baƙi da lokacin Abbu ɓalle mu yaranki to aina nasan zan sameki har in ce zan gaida ke ummah!?" "Saghar ya isa haka"cewar Hajiya babba,spoon din ya dauka ya cigaba da shan romonshi ,mikewa ummah ta yi tabar dinning din.
Kamar yanda na faɗa de yawan