Showing 84001 words to 87000 words out of 94974 words

Chapter 29 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8674

basu labari.


Cikin dariyar mugunta Rameesa ta soma cewa "gwara da Allah yasa kuka dawo yanzu" cire hijab din kanta Sabriyah ta yi,dama bata saka hula ta ciki ba gashin kanta baki wuluk na daure da ribbom babba ja.
Ta ce"ai ke Rameesa in an ga kina irin wannan yar iskar dariyar taki tofa abun mugunta ne ya samu"sa'ke tuntsirewa ta yi da dariya.
"Dadina da ke Sabriyah akwai ki da gane abu.kinsan jiya Zoya da iklas sun je gidan ya Abbas,to wai su iyayen kinibibi suka fita siyan abu waje,a hanyar dawuwar su ne suka haɗu da wani wai yana son Zoya.nan ya fara cika su da surutu kamar wani aku.Sau uku suna ce mishi zasu tafi amma yana dakatar dasu,har ya kure hakurin Zoya,kin san mutumiyar taki,nan fa ta mishi tas bata raga masa ba!"dariya Asmita da Sabriyah suka kwashe harda tafawa.


Asmita dake cire safar ƙafarta ta ce"haba ke kuwa Zoya,kin yi saurayi amma shine zaki kora shi da masifarki".galla mata harara ta yi,"ku fa baku da hankali. dan de baku gansa bane Wallahi kamar wani ɗan shaye_shaye".


Haka suka ta hirarsu,suna shan dariya, Zoya har kwatanta musu yanda saurayin yake magana yana wani buɗe ƙafadata kamar wani boss take yi,su kuma suna kallonta kamar sun samu Tv suna dariya.






Daga masallaci ACP Jawan station ya wuce saboda kiran da DPO yake masa ya wuce misali.jikinsa ne ya bashi akwai abinda yake faruwa,shisa ana idar da sallah ya wuce direct station.
Yana shiga yaga yan sanda se shige da fice suke yi.
Yana shigowa suka sara mishi.
Office dinsa ya wuce ya samu waje ya zauna.shigowa DPO ya yi da tarin files a hannunsa da a ƙalla zasu kai guda goma zuwa sha wani abu.


Sara mishi DPO ya yi kafin ya fara magana "ACP!yau tunda garin Allah ya waye muke ta karban cases din kidnapping,i zuwa yanzu an yi kidnapping mutane sama da goma.shisa nake ta kiran ka,this is getting out of hand ACP".Shuru Jawan ya yi yana wani tunani,inde tunanin sa ya bashi dede to wannan aikin Italian Mafia ne.


Kallon DPO,ACP Jawan ya yi kafin ya ce"have a sit"zama ya yi yana"thank you sir ".


Danna kira ACP Jawan ya yi ya kira, commissioner a waya suka yi magana ya sanar dashi halin da ake ciki.


Suna cikin yin magana,wata mata ta shigo station din tana kuka haɗe da kururuwa.ta cika station din da kuka.


Tambayarta kurtun yan sandan sukayi nan take sanar musu da yaranta mata guda biyu da ta mallaka a duniya an yi garkuwa dasu.


Da sauri wani dan sanda ya shigo office din ya sanar dasu.


Fitowa suka yi ACP Jawan ya taimakawa yar dattijuwar ta mike ya zaunar da ita akan kujera yana lallashinta,da bata karfin guiwar cewa da yardar Ubangiji za'a ga yaranta.


*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*




Page 28,29,&30




*_Story & written_*



By


*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)






📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️






Three in one
Page 28,29&30








Rubuta report matar ta yi sannan ACP Jawan ya bada umarni aka mayar da ita har gidan ta.


Da haka shima ya koma gida bayan yasa yan sanda sun fara binciken yaran da aka sace.
Karfe 5:00 dede ya iso gida polisawa suka bude masa kofa,yana fitowa suka sara mishi fara tafiya ya yi suka yi kokarin mara masa baya hannu kawai ya daga musu, dakatawa sukayi suna "Yes sir".


Ko part din sa be shiga ba ya wuce na LTG nan ya samu baya nan,ga shi tun yana office ya ke kiransa be yi picking ba,dama LTG haka yake in ba wai shi ya kiraka ba tofa in ka kirasa ma,abanza domin baya daga kira se in ya zama urgent and important.




Koma wa nashi part din ya yi,wanka ya fara yi sannan ya sauya zuwa ƙananan kaya. ACP Jawan da LTG suna tsananin kama da juna sede abinda ya bambanta su shine, kwayar idonsu ya sha bambam dana juna LTG nasa golding eye balls wato Hazel eye balls,which is the combination of green, brown,gold.yake dashi wanda ya gado a wajen kakar su Ammi da anty amarya,hatta farinsa ma irin na turawa ne da kuma sumar kanshi,while ACP Jawan nashi kwarya idon sa brown ne shida Umaisha.






"Me yasa ke dakikiya ce kam Naziya!?,ke kullum a ce bazaki nutsu ki san ciwon kan ki ba!?,to ko mutuwa zakiyi se kinzo Maiduguri kuma bazan taɓa canza abinda na yi niya ba,gwara ma ki rufawa kan ki asiri ki zo ki dangwali arziki ki barsa a inda yake,in kika auri Tajuddeen ai ba ma mu kadai ba,gaba daya danginmu sun warke,amma tsabar doloncin da ke damun ki,kin ƙi nutsuwa ki bani haɗin kai.to na riga da na gama magana ta gobe_goben nan za ki ta ho.saura kuma ki zo ki dinga nunawa mutane wannan shegen sanyin halin naki"ita de tunda antyn nata ta fara magana kawai jinta take yi amma ita ko kadan bata son zuwa musamman ma da tasan manufar da ake son amfani da zuwan nata.ita ta riga da tasani ko mutuwa zatayi tasan bata ishi LTG kallo ba ɓalle har ya ce ze aure ta shisa ta ke ajiye kan ta inda Allah ya ajiye ta,ko zuwa Maiduguri ma sau biyu kawai ta taba zuwa.


Cikin sanyi murya irin na ta,ta soma magana.
"Anty khareema da kinyi hakuri da wannan burin na ki,ni takura min kikeyi,tun ba yau ba,kinsha min wannan maganar amma na nuna miki banida wannan ra'ayin.mijin da zan aura har gida ze zo ya sameni in sha Allah,amma kin dauki buri da son abin duniya kin daurawa kan ki.ki ji tsoron Allah anty khareema.ni de bazan zo abanza ki dinga ja min wulakanci ba".


Cike da Masifa da ya rufe mata ido ta ce"kam uban can dan uwarki Naziya Ni ki ke cewa in ji tsoron Allah?,in ban ji tsoron Allah ba tsoron ki zanji,yar iska bagidajiya,kar ki ga dan kina kanwata kice zaki faɗa min maganar banza in kyale ki,yar karamar ƴata ita ce sa'ar ki!,amma saboda reni ya shiga tsakanina dake har ina magana kina bani amsa ko Naziya???".ya mutsa fuska ta yi kamar tana gaban Ammuh din.


A hankali ta ce"ai dama ita gaskiya ɗaci gareta,to nide banaso babu yanda za'a yi in yarda kiyi mini dole akan wanda baya sona baya ra'ayina, shine kawai anty khareema".


Ummah dake gefen Ammuh suna saurarar abinda ta ke faɗa, domin wayar na a handsfree.


Ta mata alama da ta danne fushinta, ta lallaba Naziya din wuyarta tazo ne ai.


"Shikenan yar kanwata yanzu de mu bar maganar Tajuddeen ki shirya gobe ki zo ki kawo min ziyara".
"Ni fa anty khareema na san halinki kawai de wayo kike son ki min, Wallahi in na zo bazan wuce sati daya ba zan dawo,taraba!".
Haɗiye bakin cikin da ya tokare mata wuya ta yi, saboda inde ta ce zata tsaya suna sa'insa da Naziya tasan ba zuwa zatayi ba.
"Shikenan na amince yanzu zan tura miki 100k a account din ki,ki biya kudin motar".


Tabe baki ta yi ta ce"to Allah yakaimu goben da rai da lafiya ".


Ko amsa mata ammuh ba tayi ba ta kashe wayar dan haushin Naziya take ji,ita halin ta daban, se ka ce ba ciki daya suka fito ba.komai se ta dinga nuna tsoron Allah da kuma tausayi se kace tafi kowa,ga shi ita kuma ta kwallafa rai akan se ta haɗa LTG da Naziya aure,ita kuma Naziya na kokarin ba ta matsala..


Dafa ta ummah ta yi"haba Hajiya khareema,ke yanzu a ganinki in kina binta a haka kina tunanin zata yarda ta zo ne?,lallabata yakamata kiyi,kin tsaya kina mata tsawa da Masifa, ba kin san yaran yanzu ganin kansu suke yi dede da na kowa ba . abu me wuyar shine ta zo gidan nan, muddin ta riga da taxo tofa magana ya ƙare,duk da naga ita ma Naziya akwai taurin kai in ba haka ba,ana nuna miki hanyar arziki amma kina kaucewa tsaban yarinta da hauka".


Ajiyar zuciya ammuh ta yi,ita da ace tana da wata karamar ƙanwa tofa babu abinda ze sa ta tsaya bata lokacinta akan Naziya.tun ba yau ba suke kai ruwa rana da ita akan cewa tana son ta auri LTG amma ta nuna sam ita bazata auri wanda baya son ta ba.


"Ke de bari kawai Hajiya hurairah na daɗe banga jakar yarinya mahaukaciya ba irin Naziya. wai ni ina dubawa kanwata yanda rayuwarta ze yi kyau, amma wannan yar iskar yarinyar tana kokarin watsa min kasa a ido.ni banida matsala da Tajuddeen tunda da boka mauzau zamu haɗa sa Kinga kuwa ai soyayya shi da ita dole".


Ta yi shiru tana girgiza ƙafarta dake daure akan daya.
"Yanzu de bari ta zo din se mu ga ya abin ze kasance".cewar ummah.


Suna tsaka da magana masoyiya Parsa ta shigo dakin da wannan murmushin nata kwance akan fuskarta ta zauna tana me kwantar da kanta ajikin Ammuh.dakatawa da maganar sukayi saboda shigowar ta.
"Parsa daga ina haka"kallon ammuh ta yi ta ce "Ammuh ina falone, dama ina so in gayawa ummah gobe zamu je gidan anty Sameera ne nidasu Umaisha"haɗe fuska Ammuh da Ummah sukayi jin sunan da ta kira"meye zakuje yi gidan Sameera?",da mamaki ta kalli Ammuh kafin ta kalli ummah.
"Ziyara zamu kai mata tunda gobe weekend ne so i thought that was a good idea".
"To naji amma bazaku je gobe ba se next week,yanzu kije ki huta".
Murmushi ta yi ta ce"to ummah"ta shiga bedroom din Ummah ta kwanta.


Bin bayanta sukayi da kallo, Ammuh ta ce"Hajiya hurairah kinsan me nagani kuwa!?"girgiza mata kai ummah ta yi.


Ammuh ta sa'ke cewa"me ze hana mu haɗa Parsa da Salim aure,ni a ganina sun yi matukar dacewa".jimantawa ummah ta yi kafin ta ce"to ai ba mu san ko suna ra'ayin juna ba,sede mu tuntube su".
"Eh hakane kam in sha Allah zan yi wa,Salim din magana ke ma se kiyiwa Parsa din "cewar Ammuh.
A haka suka bar maganar tasu.(lallai kam, sunan wani abu wai kwamachala.parsa na son Sahil,nan kuma Ammuh da Ummah suna shirin haɗa ta da Salim).


Zaune suke a falon su,sun nutsu suna yiwa Asmita da Sabriyah lessions.
Kusan tsawon awa daya suka kwashe kafin nan suka gama,kai school bags din su bedroom sukayi suka dawo.


Asmita da take fama da ciwon kai ne,ta zauna tana daura kanta akan kafadar Sabriyah. tunda ta ga haka ta san akwai abinda yake damunta.


Shafa kanta ta yi "my Jerry meyafaru ne naganki haka!?".
"Kai na ke min ciwo sannan kuma se in dinga ganin jiri na son kwashe ni".
Rameesa da hankalinta ya tafi gaba daya wajen ganin wani memes na abun dariya a facebook ta ce "kinsan dama you're still under medication dole wata rana kiji irin haka,in ya tashi miki Kisha maganinki se ki samu ki kwanta ki huta".
Miƙewa Sabriyah ta yi,da niyar ɗauko mata maganinta tasha,ta rike hannunta.
"Maganin wajena ya ƙare,sede bansan ko akwai a wajen ya Saghar ba".
"Eh shikam baze rasa ba"Zoya ta faɗa tana tapping bayanta.
Maida kanta kan cinyar Zoya Sabriyah ta yi,ta fice a falon ta nufi part din Saghar sallama ta yi hatta gaji amma bata ji alamar mutum ba,hakan yasa ta nufi downstairs, Hajjatiye kawai ta samu anan.
"Barka da hutawa Hajjatiye ".
"Yauwa sanariya,wa kike nema haka!?".
Yar guntun murmushi ta yi sannan ta ce"ya Saghar nake nema zan ƙarɓawa Asmita maganinta ne".
Kamar wani abun tashin hankali ne ya faru Hajjatiye ta soma salati tana riƙe haba.
"Yanzu abinda Saghar din yake aikatawa har ya kai haka,ohh ni hajja yau ni naga bak'ar mugunta, yarinya ba lafiya amma ya bata magani ma abu ya faskara ".
Baki a bude take kallon Hajjatiye jin yanda ta juya fahimtar maganar daban ita da ta ce tana neman sa ta ƙarɓawa Asmita magani,amma Hajjatiye tana wani magana daban yanzu wani in ya ji ai se a yi wani tunani daban.


Saukowa downstairs ummah ta yi ta ji abinda Hajjatiye take faɗa ga Sabriyah a gabanta nan take ta ji ranta ya ɓaci.


"Yanzu har kin samu damar da zaki iya kawo kar'ar ɗana dan kawai be bawa wancan kazamar magani ba,saboda yana taimakon ku yana dubata.shine har zaki samu kwarin guiwar kawo kar'ar ɗana?,da ma ɗan Adam butulu ne ba'a iya masa,duk yanda za'a yi wajen kyautatawa mage tofa bazata gani ba".tun da kika zo gidan nan dama naga kanki na wani fisga yana hayaki, wannan dalilin yasa, na ke kauci rashin kunyar ki,amma yanzu dole in taka miki burki tunda har yakai ki fara kawo kar'ar ɗan masu gida shida gidan ya kasance na ubansa ne. ku kuma fa taimakon ku akayi a ka bar ku anan amma yanzu dole zaman ku ya ƙare anan".
Jikin Sabriyah ne ya yi sanyi dama ita tasan in ba wai mutum me fahimta ba,ze yi wuya duk wanda yaji yanda Hajjatiye take mayar da magana ya fahimci kan zancen,dole za'a ga kamar kar'ar Saghar din ta kawo wajen Hajjatiye.


"Ummah kiyi hakuri ki fahimce ni bawai kar'ar ya Saghar na kawo ba. kawai ina neman sa ne in ƙarɓawa Asmita magani"daga mata hannu ummah ta yi alamar ta dakata bata son jin komai.
"Rufe mini baki bak'ar munafuka ke yanzu ki dubi kan ki, yanzu da kuma yanda kukazo gidan nan a tsiyace a wulakance wanne ku kafi kyau?,yau har kin yi gogewar da za ki iya taka ɗan masu gida!?,kina karuwa dake dube ki fa,mara asali, wacce ta gama rabarwa mazan titi kanta,da ke da wancan mahaukaciyar yarinyar yau din nan zaku bar gidan nan tunda ba gidan uban ku bane".
Jin yanda take goranta musu da aibata su ne yasa Sabriyah ta fara kuka, maganganun ummah ya so sa mata rai ta ci mutuncin su ta tozarta su.
"Yi mini shuru mara mutunci yanzu Huraira ko kunyar idona bakiji ba kika tsaya kina gorantawa yarinyar nan,anya kina da hankali kuwa?,". murmushin takaici ummah ta yi"Hajjatiye kenan dama ai bayansu zaki bi yaran da suka fito daga gidan karuwai ai babu abinda bazasu iya ba dan ganin sun siye zuciyar kowa amma banda nawa, kuma bazan taɓa lamuntar reni daga wajensu ba wa ni ko wa ya'yana".


"Ina magana kina bani amsa ko,eh lallai nuna min irin ta ki fitsaran da khareemar ta koya miki".
Damko hannun Sabriyah dake kuka kamar ranta ze fita ga zagin cin mutuncin da ummah ta musu ga kuma faɗar da yake kokarin afkuwa tsakanin ita da Hajjatiye kuma duk ta dalilin su.
Jan hannunta ummah ta yi da karfi kamar zata ƙaryata,ta fara janta da niyar fitar da ita daga cikin Mansion din, tirjewa Sabriyah ta fara yi tana bata hakuri tana kuka.


"Dan Allah ummah kiyi hakuri Wallahi abinda kike tunani ba haka bane".
Ummah na janta tana cewa "yau ai ko gidan nan gidan uban ku ne se kun barshi dama haushin ganin ku nakeyi a gidan".
Zubewa a ƙasa ta yi amma hakan be sa ummah ta dena jan nata ba,Fatime da kaltume ne da suke kitchen suka jiyo hayaniyar dake tashi suka shigo da gudu fatime ta haura part din Hajiya babba domin sanar da ita tasan Ammi,da anty amarya suna can.kaltume kuma ta nufi part din Abbie domin sanar dashi.


Riko dayan hannun Sabriyah Hajjatiye ta yi ranta a matukar ɓace ta ce"ki sa'ke ta nace Huraira Wallahi zanyi mummunar ɓata miki rai,kar ki bari in miki rashin mutuncin da kowa se ya yi dana sani".
Idon ummah ya riga da ya rufe in bawai fitar da Sabriyah ta yi daga cikin gidan ba hankalinta ba ze taɓa kwanciya ba.tana haki ta ce"Wallahi ko da zakisa Isma'il ya sakeni ne yau tofa wa'yannan tsinanun annoban se sun bar gidan nan ko kuma ni in bar musu gidan"kamar za su raba Sabriyah gida biyu haka suke janta,Ummah na ja Hajjatiye na ja,wani irin wawan fisga ummah ta mata a hannun Hajjatiye da yasa seda ta buge kanta da glass din flower dake falon nan take gefen kanta ya fara zufar da jini domin glass din irin me karfin nan ne,duk da buguwa da ta yi dashi amma hakan be sa ya fashe ba.
Azaban da ya ziyarceta ne yasa ta kwala razananniyar ƙara da seda illahirin gidan ya amsa.
Tana riƙe da wajen da ya fashe tana kuka.
Abbie da Abbu kaltume ta samesu ta sanar dasu abinda yake faruwa,da hanzari suka baro part din nashi a hanya kuma suka ki kar'ar da Sabriyah ta yi hakan yasa suka sa'ke sauri gudun kar a yi barna.


Haka su Ammi ma Fatime cikin tashin hankali ta sanar dasu abinda ya faru,suma babu shiri suka fito a hanyarsu ta zuwa downstairs ne suka jiyo ihun Sabriyah.




Rameesa da tun dazun suna jiran dawuwar Sabriyah ne suka ki wannan gigitancen kar'ar da tayi ne yasa suma suka fito da gudu har da Asmita.


Sahil da Salim da yanzu shigowar su gidan suma suka ji ihun ne hankalinsu ya tashi.suka shigo da gudu.




Suna zaune a dakin bincike su hudu suna meeting akan kidnapping din da aka fara yi ne, LTG jikinsa ya bashi kamar akwai wani abu da yake faruwa hakan yasa ya Kunno CCTV din falo nan take ya hango yanda ummah ke dragging din Sabriyah da ke durkushe a ƙasa tana tirjewa ga kanta dake zubar da jini.
"Ohh shit"LTG ya faɗa yana miƙewa da sauri ya fice a dakin binciken,kallon system sukayi suka ga abinda yake faruwa suma da sauri suka rufawa LTG baya da ya riga da ya ma bar part din.


su Ammi ne suka riga kowa shigowa falon se su Abbie da gudu Hajiya babba ta je tasa iya karfinta ta fincike Sabriyah dake kuka abin tausayi a hannun ummah.
Boyeta a bayanta Hajiya babba ta yi "hurairah an ya akwai sauran hankali a tattare dake kuwa?, wannan wani irin mugunta ce dan fisabilillahi?".


Watsawa Hajiya babba banzan kallo ummah ta yi "dan Allah dakata Hajiya babba ke kinsan abinda yarinyar nan ta aikata min kuwa?".


Anty amarya da tana karasowa wajen Sabriyah ta rungumota a jiki,tana sa gyalenta ta goge mata jinin dake zuba a kanta.


Bude baki ta yi zata yi magana, Abbu ya daka mata tsawa ranshi a ɓace.


Su Asmita da shigowar su falon kenan suka ga abinda yake faruwa ta je ta rungume Sabriyah itama ta fashe da kuka duk da basu san abinda ya faru ba.


"Lallai Isma'il yau matar ka ta nuna fin ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login