Showing 90001 words to 93000 words out of 94974 words

Chapter 31 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8670

akwai dalilin da yasa ya yanke wannan hukuncin ".
Ba ta ce mishi komai ba.


8:00pm dede lokacin cin abinci as usual ummah da Ammuh basu fito ba,haka LTG shima yana part din sa, uncle Hameed ya yi iya yin sa amma Anty amarya taki fitowa itama.


A bangaren su Umaisha ma dakyar suka sha kansu Sabriyah suka je dinning.


Kowa ka gani fuskar sa babu walwala da annuri,kawai de ana cin abincin ne,bawai dan yana shiga yanda ya kamata ba.
Kallon Asmita dake tsakuran abinci Saghar ya yi yana ajiye spoon din hannunsa,jikinta ne yabata ana kallonta haka yasa babu shiri ta dago suka haɗa ido,hararanta ya yi,dan haushi ta bashi da Abbie ya tambaye su ko suna son komawa afafa har da cewa eh.


Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi taci gaba da tsakuran abincin.
Bayan sun gama ne.zasu koma ciki Abbie. Ya ce
"Tafiyar ku da safe ne so be ready,kuma karku dau kaya da yawa saboda Monday akwai school kunji ko".
Ido kawai suka zubawa Abbie dukkansu suna tambayar kansu to me yake nufi?,kenan in suka tafi zasu dawo kenan,tunda ga shi har cewa musu yake Monday akwai school.


Ta rasa me zata ce kawai ta ce"thank you Abbie"kafin ta ja hannun Asmita suka wuce part din su,binsu a baya su Umaisha sukayi,kowa de ya rasa gane inda lamarin Abbie ya dosa.


Saghar da ya ƙasa hakuri ne ya ce"Abbie kenan zasu je su dawo ne?,Ni ban fahimta ba".


Fuskar Abbie ba yabo ba fallasa ya ce"ga shi nan de!"ya yi maganar yana fuskewa.


Be sa'ke cewa komai ba,ya miƙe yabar wajen.




Kamar yanda Abbie ya bukace su da suyi haka kuwa suka yi yar karamar trolley ta dauka ta saka musu kala biyu a ciki se dogayen hijabs.




Lieutenant general Tajuddeen




Yana nan a dakin bincike yana aiki,yaran da aka sace yau binciken sa ya tabbatar masa da Mafias ne suka sace su shisa ka ya maida hankali akan neman in da aka kai yaran,in har hasashen sa yabashi dede yaran da kuma masu kidnapping din Suna cikin garin Maiduguri kuma baze taɓa barin su bar garin nan ba se ya kwato yaran,karfe sha biyu ya kira Khalifa a waya ya sanar masa da ze kai Sabriyah Lagos gobe.






Tunda sukayi sallah asuba sukayi wanka suka shirya cikin dogayen rigunan abaya,daukan trolley din Rameesa ta yi sukayi fito falo.


Gaida kowa da suka samu afalon sukayi.dubawa ta yi taga anty amarya bata fakon hakan yasa ta haura part din ta sallama ta yi tana daga tsaye a bakin kofar,amsawa anty amarya ta yi.


"Mommy ina kwana?".
"Lafiya klau mommy's angel,how are you?".
"Am fine mommy"murmushi ta yi jin ta amsa mata da turanci,wato suna fahimtar karatu kenan duk da ma wa'yannan ƙananan words din bame wahalar wa bane.


"Mommy zamu tafi shine nazo miki sallama ki yafe min"shafa fuskarta ta yi,tana danne abinda yake yunkuro mata na baƙin ciki.


Ta ce"baki taɓa min laifi ba daughter, and in sha Allah za ki dawo wannan gidan da izinin Allah ta Allah".


Hawaye ne ta ji ya cika mata ido, hakan yasa ta rungume anty amaryan,.


Sun kusa minti uku a haka kafin ta zame jikinta ta ce"ko ma me ze faru kiyi min alkawarin bazaki taɓa komawa rayuwarki na ɗa ba?".


"Na yi miki wannan alkawarin mommy,".


Dawuwa falon tare sukayi.kowa ya hallara a falon ummah da Ammuh suna upstairs suna kallon duk wani abinda yake faruwa suna murmushi Finally burinsu de ya cika Sabriyah da Asmita sun bar gidan.


A babban filin farfajiyar gidan private jet na wajen, Khalifa su yake jira su fito,rako su har wajen sukayi suka shiga ciki.


Suna musu bye_bye a haka jet din ya tashi sama.sun tafi.






Lagos


Bayan sun isa Lagos ne motar ya zo ya dauke su ya ajiye su har cikin afafa a bakin gate din gidan karuwan da suka baro.


Duk wacce su ka haɗu a hanya se ta kallesu suna mamakin sauyawan da sukayi da kyaun da suka ƙara.


Sashen su na gidan suka nufa,suna shiga suka iske,anty Teema ita kadai tana zaune ta rame sosai ta yi baƙi ta kode kamar ba ita ba,tana daure da fallen zani.
Cikin tsoro suke kallonta a tare suka haɗa baki wajen cewa.
"Anty Teema".
Ta jima da cire tsammanin sa'ke jin muryoyin su a rayuwarta,bude idonta da bacci ya fara saceta ta yi taga dagaske yaran nata ne.
"Hot girl!, Asmita da gaske kune?,kun ga ni yanda na koma ko?, kullum addu'a ta shine, Allah yasa in gan ku kafin in mutu ashe de da rabon za mu ga juna?".


Gyara mata zama Sabriyah ta yi, tana me jin tausayin Antyn nasu,ganin yanda gaba daya ta canza ta kare.
Asmita kam ta ma gagara magana.


"Anty Teema meyake faruwa ne,,shin maganin ki ne ya ƙare?".
"Ai komai ma ya ƙare Sabriyah rayuwar bariki be yi ba ko kadan,yanzu abincin da zan sa abakina ma babu rabona da abinci tun jiya da rana.mutane biyu ne kawai suke taimaka min daga Cele se Nabiha suma tun shekaran jiya basu zo ba".
Ta yi shiru,can kuma ta sa'ke magana.
"Ku da Allah yasa kuka bar nan wani ƙaddarar ce ya dawo daku gidan nan?, kullum inna tuna bakwa s wannan gida ina jin dadi a raina domin jikina yabani kuna a hannu na gari,dubi yanda kuka yi kyau kuka canza kamar ba ku ba,cikin shiga na mutunci".


Yanda take magana ma dakyar take iya bude bakinta,se sukaji kamar basu kyauta ba na barin antyn nasu har tsawon Wannan lokaci basu san halin da take ciki ba.


Gyara mata dakin nata suka yi kafin suka dauki kuɗin da Abbie ya basu koda suna bukatar wani abu.
Suka fice, babban pharmacy suka je suka siya mata magungunanta, sannan suka tsaya a shagon trader suka siya kayan abinci.


Suna a hanya suna tafiya ne, suka hango cele na nufo su, da alamar ya ji labarin dawuwar su ne.


Yana isowa ya ƙare musu kallo sama da kasa kafin ya basu hannu suka tafa,su kansu sun yi tsananin kewar abokin nasu biye da yanda ba'a magana,sun yi farin ciki sosai da ganinsa haka shima bakinsa ya kasa rufuwa se yabon kyau da kibar da sukayi yake yi.nan ya taya su daukan kaya suka koma gida.


Asmita me girkin su ita ce yauma ta musu jallof din macaroni.ta zubawa anty Teema da yawa ta kai mata ta kai mata harda ruwa.


Kiran Nabiha a waya Cele ya yi ya shaida mata,su Sabriyah sun dawo.
Dama tana dakin su bata je ko ina ba,ai kuwa da gudu ta nufo sashen nasu.


Tana zuwa suka rungume juna cike da kewa.


Nan fa aka fara hirar yaushe gamo,suna hira a na cin abinci.
Ko da suka gama cin abincin ma baranda suka dawo suka zauna suna hira harda anty Teema,da ta ɗan warware dama har da yunwa a abinda yake damunta.


Labarin dawuwar Sabriyah da Asmita ya gama kararide gidan,tun shigowarsu dan daudu ya gansu da gudu ya je ya sanarwa boss lady cewa sun dawo, dariyar mugunta ta yi,domin dama ta dau alwashin in de suka dawo se ta yi musu abinda basu taɓa tunani ba.


Lokacin Sallah na yi suka tashi suka yi.

Bayan sun idar ne, Nabiha take basu labarin abubuwan da suka faru bayan barun su gidan,ta ƙara da.
"Amma meyasa kuka dawo?,ni de Wallahi banji dadin dawuwar ku ba,domin ko nice na samu wannan damar baza'a sa'ke kallon ko da inuwata ba, ɓalle kuma ni".


Murmushi kawai suka mata,suka ka war da maganar.
Se karfe biyar Cele ya tafi Nabiha kam ta ce yanda ta yi kewar su dole tare zasu kwana duk da katifarsu baze ishesu ba.


"My Jerry nasan wannan abin hannun nawa yana a dakin nan namu,shisa ban taɓa tambayarki ba,dubomin a inda kika a jiye min".
"Ah ah baya a dakin nan ai ranar da kika bani ban cire ba,har lokacin da wayan'can mugayen suka sace ni yana hannuna bansan ya akai ya ɓata ba".


Jiki a mace ta ce"Tom shikenan bakomai yanzu de abin Tajuju na ya ɓata,amma kinfi min abun hannun daraja".


Nabiha tana zaune tana kallonsu tsananin kaunar dake tsakanin su ne yake burgeta, bata gajiya da son kasancewa a cikinsu.


Saura jallof din su ne suka cinye, se da suka tabbatar da anty Teema tasha magungunan ta kafin suka baro wajen ta.
Sukayi sallah isha sannan suka kwanta,nan ma ba bacci sukayi ba su ukun hira kawai suke yi kamar wa'yanda suka yi shekara uku ba su haɗu ba.se da bacci barawo yazo ya sace su.


Har karfe 8:00am na safe basu tashi ba saboda babu masallaci a kusa da ze kira sallah ɓalle su ji kiran sallah su tashi.


Suna cikin bacci suka ji saukar ruwa me sanyin gaske a jikinsu.a zabure suka tashi suna rawar sanyi, musamman Sabriyah jikin ta ne ya kama rawa bata shiri da ruwan sanyi shisa take kiyaye kanta da kuma lafiyarta domin ciwon nimoniya dake tare da ita.


Boss lady ne suka gani tsaye da babban bokiti tana tsaye akan su ga kuma bulala a dayar hannun nata.


Kafin su gama dawuwa dede ta fara shiga jikinsu da bulala,duka ko ta ina, dakyar suka samu suka kwace kansu suka fito a cikin sashen nasu suna kuka.


Ga kayan jikinsu dake ɗiga da ruwa Nabiha kam guduwa dakinsu ta yi.


Suna tsakar gidan suna kuka,sanyin dake kaɗa kayan jikinsu ne ya sa'ke tsananta rawar da jikinta yake yi.


Lallabawa anty Teema ta yi ta fito ta fara bawa boss lady hakuri, amma ko saurarar ta bata yi ba.


Karuwan dake gidan gaba daya taruwa suka yi suna kallon abinda yake faruwa.


"Kun gama yawon duniyar taku da kuma guje_gujen kun dawo kenan,ai ni banso ku dawo yanzu ba,yanda kuka sani a sarar kudina da kuma bata lokaci wajen neman ku yau se kun yabawa aya zakinta".


Bata hakuri suka shiga yi, tana matsowa suna matsawa baya,har suka fita gidan a bakin gate,zagi iri da kala babu wanda boss lady bata musu ba, Cele da ya hango dandazon mutane ne yasa ya iso wajen da gudun gaske nan fa ya tarar da abinda yake faruwa bashida ikon kwatarsu a hannun boss lady hakan yasa ya koma gefe yana bata hakuri.


Ga mutane da suka yi cincirindo suna kallonsu kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Sanyi ya gama ratsa ko wani lungu da saƙo na jikinta har wani tsuma takeyi idonta ya fara kakkafewa..
Lura da ciwonta ya tashi ne yasa Asmita ta rungumeta gam a jikinta tana kuka.


Ko damuwa da halin da Sabriyah ta ke ciki boss lady ba ta yi ba,ta daga doguwar bulalar injin da iya karfin ta, zata zafga mata,ta ji an rike bulalar ta baya, ja ta yi amma kamar ma bata motsa ba,da sauri ta juya dan ganin waye ne.


Bata iya ganin fuskarsa ba saboda face mask dake manne a fuskar tasa,hannu yasa ya dauke ta da lafiyayyun maruka guda biyu,ihu boss lady ta sa,dan tunda take bata taɓa jin marin da ya ratsata irin wannan ba,se da taji kunnenta da dayan idonta lokaci daya sun dena aiki.
Kafin ta gama dawuwa hayyacinta, yasa ƙafa ya kwasheta ta zube kasa warwas, ƙafa yasa ya take hannun nata daa take rike da bulalar da takalminsa,da ƙafarsa ya dinga dukanta kamar ya samu wani katon dabban jaki.


Ɗaukan bulalar ya yi,ya ci gaba da dukanta dashi ihu da kururuwa boss lady take yi na neman a gaji amma babu wanda ya yi gigin kusanto su domin wanda yake dukan nata majiyin karfi ne, kar ya hada dasu, se ma ƙara ja baya da suka yi,da yawansu suna hamdala da godewa Allah da ganin irin wannan rana.


Kallo ɗaya Asmita ta masa ta gane shi.
A hankali ta furta"ya Taj???"


Seda ya yiwa boss lady dukan mutuwa yaga numfashinta na kokarin daukewa ne ya kyaleta.ya yi dede da isowar manya_manyan motoci guda bakwai wajen.tika_tikan sojojine suka fiffito a ciki kafin.


Sudais ya fara fitowa,se Sahil da Salim, Saghar, ACP Jawan.


Tun kafin su iso wajen suke bin boss lady dake kwance a ƙasa da kallon tsana,su Abinda LTG ya mata ma kwata_kwata be ishesu ba.


Da sauri suka karaso wajen Asmita dake rungume da Sabriyah tana a sume kuma har yanzu jikinta be bar tsuma da rawa ba,daukan ta sukayi suka sa ta a motar Salim da ACP Jawan suka wuce da ita asibiti.domin halin da take ciki.


Ɗagota Saghar ya yi daga ƙasan, kayan jikinta danye, cire jacket din cikinsa ya yi ya rufa mata.kafin ya ja hannunta izuwa cikin motar.


Kallon fuskarta ya yi "Asmee ta daƙe ku ne"gyada masa kai ta yi alamar eh.


Komawa ya yi inda yabar su boss lady ya karbi bulalar hannun LTG ya ci gaba da dukan boss lady kamar Allah ne ya aikoshi.


Haɗe fuska Sudais ya yi,ya rike sa "meye haka Saghar baka da hankali ne?,ko so kake yi ta mutu ba tare da na samu damar yi mata nawa dukan ba?, dallah malam bani bulalar".
Ya kwace bulalar a hannunsa shima ya je ya yiwa boss lady nashi dukan kamar baze barta ba,ko ina na jikinta se da suka fasa shi.
"Ah ah lallai kun ban mamaki,yanzu meye nufin ku kenan?,so kukeyi ku ce ni bazan daketa ba?,bayan kuma seda na daukarwa Parsa alkawarin yi mata dukan tsiya".Sahil ya faɗa shima yana karbar bulalar a hannun Sudais.
Kallon dan daudun dake tsaye a gefe yana yarfe hannu ya yi nan take ya tuna da labarin da Sabriyah ta basu,wato de wannan shine wannan dan iskan dan daudun?.


Shako wuyarsa ya yi ya fara jifgarsa,seda ya mishi lilis kafin ya barsa ya sa'ke dukan boss lady.


Sude yau mutanen afafa sun ga tashin hankali,dama kowa haushin boss lady suke ji,yau ga shi Allah ya haɗata da dede da ita,ko motsi ta gagara yi tana yashe a ƙasa a wulakance.


Asmita na daga motar se ihun dad'i takeyi taso ace Sabriyah taga irin dukan da aka yiwa boss lady,yau Allah ya rama musu abinda take musu.


Wasu manyan katafila ne suka shigo wajen masu rusau.


Sudais ne ya dauki loud speaker ya dawo tsakiyar filin ya ce"an yanta kowa,duk wacce take son kanta da lafiya ta bar gidan nan,domin yanzun nan za'a rusa gidan nan, kowa za'a bata kudin da zata gyara rayuwarta kuma ku koma gaban iyayenta,in kuma ba haka ba.... shikenan de".kafin kace kwabo sun fara tattara abubuwansu,sauke glass din motar Asmita ta yi ta kwalawa Cele kira,da sauri yazo inda take.
"Cele akwai wayoyin mu a dakin mu taimako ka dauko mana"cikin gidan ya shiga ya dubo musu wayar su da trolley din da suka zo dashi.
Tunda ta kira Cele Saghar yake kallon su, yana tambayar kanshi meye kuma hadinta da wannan zuciyarsa ce take son cusa mishi wani tunani da sauri ya ka war yana"astagfirullah"gudun kar shedan ya yi nasara akansa.
Kauda idonsa akan su ya yi.
Kawo mata su ya yi ta karba tana mishi godiya.
,suna gamawa aka fara rusa gidan,motar polisawa ne suka iso wajen nan LTG yabasu umarni aka sawa boss lady ankwa suka jefata a bayan motar kamar wata trash.


Gaba daya gidan seda aka rusa shi kaf wajen ya koma farfajiyar fili.


Ko wacce dake cikin gidan se da aka bata 300k(dubu ɗari uku ta nemi sana'a sannan ta koma gaban iyayensu.
Asmita ce ta gabatar musu da anty Teema da ta rene su.
Shiga motar sukayi harda Cele da anty Teema, Nabiha suka tafi asibitin da aka kwantar da Sabriyah.


Alhamdulillah har ta farfaɗo tana zaune Jawan da Salim se janta da hira suke yi tana dariya.


Shigowa dakin suka yi,ko ya jiki LTG be mata ba,sama fitar da ya yi, yana "karku bata min lokaci,ina jiran ku kuzo mu wuce"daga haka ya fice be ko juyo ba, murmushi Sabriyah ta yi tana bin bayansa da kallo tana tuna,lokacin da take kokarin suma shine mutum na karshe da tayi tozali dashi,duk da yana sanye da face mask amma seda ta gane shi.


Kallon anty Teema Sudais ya yi ya ce "duk kan ku zaku koma Maiduguri tare da mu".
Cikin farin ciki suka ce sun amince.


Bayan awa daya suka kimtsa private jet guda uku suka yi amfani shi ya kwashe su zuwa Maiduguri.


Karfe 8:00 suka iso Maiduguri motoci na fake yana jiransu.
Shiga,ciki suka yi suka dauki hanyar gida.
Su Umaisha na jin dirar motoci suka sa ihu da tsalle suna
"Su Sabriyah sun dawo".
Dariya Ammi ta yi,anty amarya ihun su da ta ji ne yasa ta sauko downstairs din.


Tun kafin motar ya gama fakin Sabriyah da Asmita suka bude domin sun hango su Umaisha gaba daya sun nufo motar da suke da gudu,suma da gudu suka fito suna rungume juna.


Ciki suka shiga gaba dayansu.rungume su anty amarya ta yi tana murmushi.


Kowa ya yi murna da damuwar su, su Ammuh de basa gida,tun safiya suka nufi wajen boka mauzau.


Naziya ta zo tun ranar asabar wato ranar da su Sabriyah suka bar gidan kenan.


Bayan wasu yan gaishe_gaishe da akayi ne, suka yi wanka. abinci a ka kai musu,har lokacin bawai jikin Sabriyah ya gama warwarewa bane kawai tana karfin hali ne.


Yanda suka karbi su Asmita haka suka karbi Nabiha ita ma cikin sakin fuska.


Kiran wayar Sabriyah anty amarya ta yi ta ce mata ta zo su kwana a part dinta haka kuwa a kayi itama dama ta yi kewar mommyn nata.


Washe gari Monday tun kafin su Nabiha su tashi daga bacci har sun gama shiryawa cikin uniform driver yakai su school.


Haka suka ci gaba da rayuwar su kamar babu abinda ya faru ko da su ummah suka gansu a gidan basu ce komai ba.


Bayan zuwan su da kwana uku ne aka samarwa Cele aiki.anty Teema kuma aka bata gidan dake cikin gidan,da masu yi mata hidima.




Har yanzu ana kan sace yara da ake yi daya bayan daya,...


Wata ranar talata Umaisha da Iklas sun fita shopping a hanyar su ta dawuwa aka tare su sannan aka kashe driver da ya dauko su,aka ɗauke su.


Shuru_shuru ana jiran dawuwar su,amma Shuru har yamma ya yi nan fa aka fara neman su.motar da ya daukesu aka gani bakowa a ciki se gawar driver dake yashe a ƙasa.


Hakan yasa suka fahimci an yi garkuwa dasu ne.




Lokacin da suka ji wannan labarin hankalin kowa ya tashi.an yi binciken amma Shuru bayan su an sake sace yara yan mata goma.


Har karfe sha biyu suna zaune a Falo sun yi carko_carko,kowa ka gani kasan yana cikin matsananciyar damuwa.


Su Sabriyah sun yi kuka yar sun gaji suna zaune a Falo.


Kiran waya ne ya shigo wayar LTG,kin dagawa ya yi domin a halin da yake ciki bayajin ze iya yin magana da kowa,kira ne kan kira yake shigowa,kallonsa Abbie ya yi "Tajuddeen waye haka yake kiran ka Kaduba ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login