Showing 87001 words to 90000 words out of 94974 words

Chapter 30 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8673

bani na haifeta ba,tunda har ina hana Huraira aikata abinda take yi amma ta ƙi saurara na".


Su gaba daya their confused basu san abinda ya ke faruwa ga kuma Sabriyah da kanta ya fashe.


Kukan Sabriyah da Asmita ke tashi a falon.ganin Asmita ne yasa ummah dasauri tasa hannu ta cafkota,ta fara janta.


Hannun ummah anty amarya ta rike,ranta a ɓace ta ce"Huraira ki sa'ke yarinyar nan kar daga ni har ke, ran mu ya yi mummunar ɓaci kinji na faɗa miki ".
Dariyar renin hankali ummah ta yi"ai yau Wallahi yaran nan ba zasu ƙara ko awa daya a gidan nan ba barima ki gani"ta na gama fadin haka ta ture anty amarya da sauri Ammi ta riƙota.


Ji ta yi an riƙe hannun ta kallon wanda ya riken ta yi ta ga Saghar ne"Saghar ka sa'ke min hannu ko in saɓa maka".


Saghar da yanzu shigowar su falon suka tarar da abinda yake faruwa ne ya yi hanzarin rike hannun ummah.


Gently ya ce"ummah please ki sa'ke ta".
"To sannu ubana!na ce sannu ubana,to bazan sa'ke ta ba yau wa'yannan tsinannun yaran se sun bar mana gida nagaji da kallon su".


Ammi da ba ko da yaushe take saka baƙi a al'amarin gidan ba musanman ma abinda ya shafi Ammuh ko ummah ba.


Amma yau ummah ta kawo ta makura ganin abinda takeyi wa yaran .


"Babu wacce zata bar gidan nan Huraira wannan wani irin rashin imani ne haka,meye yaran nan suka tare miki,to na rantse da wanda ya halicce ni bazasu fita a gidan nan ba a yau,sede kiyi duk abinda zakiyi".


Dogon tsaki ta ja sannan ta fincike hannun Saghar da ya rike mata nata hannun.


Ransa ya ɓaci iya baci daga shi har Sudais da Abbu ganin abin kunyar da Ummah take aikatawa.
Idonsa a rufe ya ce
"Ummah ki sa'ke ta nace".


"Huraira ki sa'ke yarinyar nan,kar ki bari in sa'ke miki magana"cewar Abbu da ransa ya gama ɓaci domin ya gaji da halin Ummah yau kuma ga abinda ta bijiro dashi.


Hajjatiye na zaune akan kujera tana kukan cin mutuncin da ummah ta mata Hajiya babba na rarrashinta,Abbie ma yana tsaye ya zuba ido ya rasa menene abinda ze cewa ummah, LTG yana tsaye shima ya zuba musu ido shima be san mezece ba,ga Sabriyah da ya gani durkushe a ƙasa tana kuka.ga Asmita a hannun ummah taki sa'ke ta, Sudais in rasa ya yi dubu to seda ya ɓaci,ganin abinda ummah take yi.
Yan matan ma suna tsaye ganin tashin hankalin da aka tashi dashi yau a gidan nasu,suna tsaye suna hawaye,ga shi yanda ummah ta tsaya tana cin zarafin su Sabriyah abin be musu dadi ba ga faɗar da iyayen su suke yi.


Ammuh tana tsaye a gefe tana murmushin jin dadi, ummah bata taɓa burgeta ba irin yau da ta fita musu a giya.


Rike kugu ummah ta yi tana kallon cikin idon Abbu "ko zaka rabu dani ne ta dalilin wannan yaran?,se ka zaba ko ni Ko su".


Fisgo Asmita ya yi a hannun ummah ta faɗo jikinsa, jikinta har ya dau zafi ga rawan da yake abinda yake faruwa ya daga mata hankali dama ba wani isheshen lafiya ne da ita ba,yanzu kuma ga rashin mutuncin da ummah take musu.


Taɓa jikinta ya yi yaji yanda ya dau zafi rau.


"Saghar ka rabu da yarinyar nan,ko kuma...." Abbu ya ce "ko kuma me?,na ce ko kuma me ".


Tana huce da hura hanci ta ce "hmmmm.waya'nnan karuwan de se sun bar gidan nan su je can su ci gaba da rabawa yan titi,Yan iska marasa asali,yau yanda suka gama gantalewa a titi wani dan iskan ne ze aure su".


Jikin Saghar har tsuma yaƙe yi yarasa ya zeyi da maman tasu.


"Ina santa!ni nan zan aure ta"gaba daya kallon su ne ya koma kanshi jin abinda ya faɗi.
Kallon sa Asmita ta yi,maganar da yi ya da ki zuciyarta,ta rasa wani irin yanayi ta ji farin ciki ne ko kuma akasin haka.


Kamar wata mahaukaciya sabuwar kamu ta daka tsalle ta zo gabanshi ta ce"maimaita abinda kafada Saghar in ji,menene ka faɗa yanz_yanzun nan dan ubanka meye abinda kunnuwana suka ji mini, Allah yasa ba da gaske ba, ɗana da karuwa har abada baze yu ba".


Da karfi yanda kowa ze ji ya sa'ke furta "zan auretaaaaaaaa.....,ni ina son Asmee zan aure ta"kukan kura ummah ta yi ta chukumo wuyan Saghar kamar wacce ta samo tabin hankali ta soma magana"baka isa ba, baka isa ka zubar min da mutunci ba a dinga nuna ni ana cewa yarona ya auri karuwa,ina! karya kake yi,ko ubanka be isa ya sa ka aureta ba ɓalle kai".


Murmushin jin dadi da takaici Abbu da su Hajiya babba sukayi.


Abbu ya ce"dagaske Saghar kana son Asmita!?"gyada masa kai ya yi ko shakkan ummah dake rike da wuyan rigarsa be ji ba.


"To shikenan kasa a ranka kamar ka auri Asmita,baka da matar da ta wuce ta in sha Allah".


Yau in hauka ne yaci a ce ummah ta yi shi ganin abinda Saghar da Abbu suke da niyar haukata ta.


Kamar zata yi kuka ta ce "Isma'il ni zaka tozarta?to Wallahi tallahi ko zan yi yawo tsirara se na hana wannan cin mutuncin da kuke kokarin yi min, da rai na da lafiya ta bazan taɓa barin ɗana na cikina ya auro karuwa ba sauran da wani ya ci ya rage, budurwa sabuwa fil a leda zan aura masa yanda shine nan ze bude ta da kansa".
Runtse ido Sabriyah ta yi jin mummunar kalmar da ta jefesu dashi wai sauran da wasu suka ci suka rage,ina bazeyu ba,dole ne ma su bar gidan nan yau an musu irin wannan tereren tambadar basu san gobe wani kala za'a zo musu dashi ba.


Hajjatiye dake zaune akan kujera tana yar kuka ne ta rangwada gu ɗa"aiyiriyiri!, Ubangiji Allah ya maka albarka Isma'il na yafe maka duniya da lahira,gwara da ka gwadawa wannan mara mutuncin matar ta ka kai ka isa da ya'yanka.kuma inde da ranmu da lafiyar mu se an yi auren Asmita da Saghar sede in mutuwa za kiyi ki mutu.saghar Allah ya sanya alkairi ya nuna mana ranar auren naku mu yi rawa har da karya kwankwaso".


Ba Hajjatiye ba kowa dake falon wannan abin ya musu dadi jin Saghar ya ce yana son Asmita,su ga iya gudun ruwan ummah din.


Mutsu_mutsu take yi a jikinsa tana so ya sa'ke ta,kowa dake falon yana kallon su.
Can ciki ta yi magana.
"Ya Saghar ka sa'ke ni".
"Bazan sake ki din ba"shima ya mata rada a kunne.
Taga tabbas da gaske yake yi ,ba sa'ke ta din ze yi ba hakan yasa ta cize shi a damtsen hannunsa, sa'ke ta ya yi yana kallon idonta da har yanzu be dena zubar da hawaye ba,wajen da Sabriyah ke durkushe ga anty amarya na shafa kanta ta nufa ta zauna a ƙasa tana kwantar da kanta a kafadarta suna kuka a tare.


Folding din hannunta waje daya ta yi alamar roko.


"Ummah kiyi hakuri ba abinda kike tunani bane,ki yarda dani,baki san ainihin abinda muke tattaunawa da Hajjatiye ba,kin zagemu kin kiramu da suna ye kala_kala,tabbas mu bamu da asali bamu da ahali,amma ba laifi muna jin dadin rayuwar mu a inda muka baro din,bamu taɓa kwadayin shiga wajen da Allah be kaimu ba,duk irin azabtar da mu da ake yi amma bamu yi kwadayin shiga cikin wasu ba.gudun gori da wulakanci duk da mu din wulakantattun ne kamar yanda kika ce,amma bama yarda a tozarta mu,muna iya kokarin mu wajen kare mutuncin kan mu.
Ba ma son zaman silar haddasa faɗa ko tashin hankali a cikin wannan gida na ku,domin kun dauke mu Kamar yaranku,kun nuna mana so da kauna har abada baza mu taba mantawa da haka ba, kuma zamu ci gaba da muku addu'a har iya rayuwarmu da gode muku.kun taka muhimmiyar rawa a Rayuwar mu,kun nuna mana hanyar dede,mun san mu su waye ne a yanzu.mun gane addininmu duk ta dalilin ku bamu da bakin da zamu gode muku.
Amma yanzu lokaci ya yi da zamu bar wannan gida bawai dan kun gazaba,sedan kar mu haddasa muku fitina,kafin muzo hakan baya faruwa amma daga zuwan mu ta dalilinmu kun fara samun saɓani.ku yafe mana mun gode sosai ".
Jikinsu ya yi sanyi sosai ganin yadda suke kuka tana magana.
Anty amarya ma sosai take kuka ga idonta ya yi ja.
In su Sabriyah suka bar gidan nan ba kowa aka yi wa ba sama da ita,domin yanzu jin kanta takeyi a matsayin uwa,taya zata juri rasa wata ƴar idan kuwa suka tafi bazata taɓa yafewa ummah da ta zama silar haka ba.


Muryarsa sukaji daga bayansu yana faɗin
"Babu wacce za ta bar gidan nan"kallon shi Sabriyah ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "ya Taj,dole zamu tafi domin kuma ku samu kwanciyar hankali".
Kafeta da ido ya yi,yana kallonta ya dede da yin observing din Sabriyah tana da matukar taurin kai,in ta kafe akan magana to bata taɓa sauya wa musamman ma in ranta na a ɓace.
Be sa'ke cewa komai ba domin tunda ya ji ta ce se sun bar gidan yasan ko da ba'a sani ba zasu iya bari din.


Gyaran murya Abbie ya yi da gaba daya he's out of words, takaici ya gama dabaibaye shi.


"Tashi kuzo nan Sabriyah da Asmita".
Miƙewa sukayi jikinsu a sanyaye suka je wajen Abbie din shafa kansu ya yi kafin ya rike hannunsu ya zaunar da su akan kujera kallon Saghar dake tsaye kamar dutse ya yi,"zo ka mata dressing din kanta nan da ya fashe".
Ba ce komai ba ya nufi clinic ya dauko first aid box.
Ya fara wanke wa Sabriyah ciwon kanta, runtse ido ta yi lokacin da ya fara goge mata da hydrogen har cikin ranta take jin zafin kawai daurewa takeyi,gaba daya ta kosa a gama su tafi.
Bayan ya gama ne,ya bawa Asmita maganinta tasha.
"Kuyi hakuri da abinda ya faru yau din nan tabbas an ci mutuncin ku,wanda gaba dayanmu ba mu ji dadin hakan ba,umman ku ba ta kyauta ba, ɗa na kowa ne amma ku yafe mata in sha Allah bazata sake ba,kun ji ko".
Gyada masa kai sukayi.
Ya ci gaba da magana"yanzu kuna da damar da za ku zaɓi a duk in da kuke son kasancewa,kuna son komawa afafa ne"ya tambaye su yana kallon ko wacce,da sauri Asmita da Sabriyah suka gyada masa kai tabbacin suna son komawa.


Murmushi irin tasu ta manya ya yi ya ce"shikenan zaku koma,kun ji ko, tunda gobe da jibi babu makaranta se ku je ko".da zallan mamaki dauke akan fuskan ko wanensu suke kallon Abbie jin abinda ya faɗa,domin kuwa babu wanda ya yi tsammanin abinda ze faɗa kenan,to menene yasa Abbie ze ce za su koma afafa.me yake shiryawa dan haka kawai bazece zasu je su afafa ba.to kode ya faɗa hakane dan ya kwantar musu da hankali.
Murmushin gefen baki LTG ya yi domin yasan abinda Abbie yake da niyar yi,kuma tunanin su yazo daya.




Ammi ta ce"amma Abbie ta ya kuma za'a mayar dasu can din?,ko ka manta wata irin rayuwa sukayi abaaya?",daga mata hannu ya yi,shuru ta yi bata sa'ke cewa komai ba.
Duk masu son yi magana da su ka ga yanda Ammi sukayi da Abbie se suka ja bakin su sukayi shuru suna son ganin iKon Allah.


"Yawwa gwara de su tattara su bar gidan nan in ana so a samu zaman lafiya dani"cike da takaici Abbu ya juya ya kalli Hajjatiye ya ce "Hajjatiye kwanaki ba kin yi mini tayin auren Hajiya lubabatu ba?,to na amince zan aure ta ko zan samu salama da irin bakin cikin da Huraira ta ke cusa min".
Hajiya Hajjatiye abin nema fa ya samu dama tun shekaru uku da suka wuce take mishi maganar wata Hajiya bazawara da mijinta ya rasu tana da yaronta na miji guda daya tal,kuma matar na da kirki sosai ga hankali da sanin yakamata shisa ta yi wa Abbu kwadayin aurenta amma da ta masa magana se cewa ya yi shi yanzu baze iya yin wani aure ba matar sa da yaranshi zasu ga kamar ya yi hakan ne dan cin mutumci,amma yau shi da kansa ya ce yana bukatar aurenta.hakan yasa ta sa'ke rangwada gu ɗa.


"Se yau na san yarana jinina da halina suka dauko yau Isma'il ka nuna min ka haifu a cikina,ba a cikin ko wacce shegiya ba.uba da ɗa sun kusan angwancewa".ta yi maganar tana gyara daurin zanin ta.


Saghar da Sudais, Parsa ko a jikinsu da suka ji Abbu ya ce ze ƙara aure domin kuwa ummah ita ta jawa kanta da batayi haka ba babu abinda ze sa Abbu yin wannan maganar,yau ta kuresa ne,mutum me hakuri dama in aka kai sa bango to babu dadi.


Hajiya babba kam aranta ta ce "gwara a yi mata hakan ai ko zata yi hankali".


Ummah daura hannu akai ta yi tana"Isma'il ka yi kadan da ka wulakanta ni a gaban yarana,ba de aure ba to daga kai har Saghar din sede in bayan rai na ne zakuyi auren,a yi mugani in tusa zata wura wuta"ganin ta fara faɗe_faɗe ne Ammuh ta zo ta ja ta dakyar zuwa part din ta.


Parsa da idonta ya yi ja tsaban kukan da tasha ne,ta je wajen su Asmita tana basu hakuri.
"Dan Allah kuyi hakuri da abinda umman mu ta yi muku,.. tabbas bata kyauta ba,ku yi hakuri Allah yana son me yafiya,Dan Allah karku tafi please,mun riga da mun zama yan uwan juna baza mu ji dadi ba in kuka tafi kuka bar mu".
Murmushi yaƙe Sabriyah ta yi"bakomai masoyiya ummah ai kamar uwa take a wajen mu komai ta yi mana bazamu rike ta a zuciya ba,amma kam zamu tafi afafa".
Shuru ta yi tarasa me zatace musu ganin takeyi kamar laifin da umman su ta yi ne ya shafe su dayasa Asmita da Sabriyah suka dage se sun bar gidan.


Haurawa Anty amarya part din ta,ta yi tana hawaye saboda Abbie ya riga da ya gama magana,babu wanda ze sa shi ya canza se Hajjatiye ka dai,bin bayanta Ammi ta yi da sauri.


Sahil da Salim dake tsaye su basu da bakin yin wata maganar ma.


"Kuje part din ku lokacin sallah ya yi"part din su suka wuce su bakwai din.


A dakin su Sabriyah suka yada zango,kamar sune suka aikata abinda ummah ta yi haka suka hadu suna ba su hakuri more especially Zoya da Parsa.


Umaisha da ta yi tagumi kamar wata marainiya"Sabriyah tunda kin nace se kun tafi nide duk weekend se na kawo muku ziyara, Wallahi abinda ya faru yau din nan kamar a mafarki,babu wanda ya yi tsammanin haka zata faru".


"Karki damu ai komai ya wuce"cewar Asmita.


A Falo kuwa Abbie ne yake magana da Sudais da Saghar.
"Kun ji abinda Abbu din ku ya faɗa ko,ze ƙara aure fatan baku da matsala da hakan"Saghar ne ya fara magana saying.
"Allah yabasu zaman lafiya nide banda matsala"murmushi Sudais ya yi"Nima haka".


"Shikenan zaku iya tafiya, Tajuddeen ka tsaya kai".
Barin falon sukayi ya rage daga Abbie, Abbu, Hajiya babba, Hajjatiye, LTG.
Dama uncle Hameed ba ya gida duk wainar da aka soya baya nan be san abinda ke wakana ba.


"Tajuddeen nasan ka fahimci dalilin da yasa nace yaran nan zasu koma afafa gobe?"gyada kai ya yi without saying anything.
"Good,ka sanar wa Khalifa shi ze kai su a private jet din ka,daga nan kuma se ku yi abinda ya kamata".


"To shikenan Abbie dama na daɗe da son yin haka kawai wani aikin ne nakeson kammalawa amma tunda bukatar hakan ya taso za'ayi".


Abbu dasu Hajiya babba de basu fahimci inda zancen Abbie da LTG ya nufa ba shisa kawai suke kallon su.


Barin falon ya yi domin dauro alwalar sallar mangrib.


Se da suka tabbatar da babu sauran yaran da suka rage a downstairs din kafin.


Abbu ya rarrafo akan guiwowinsa yazo gaban Hajjatiye ya daura kansa akan cinyarta murya a sanyaye with full of regret ya soma magana.


"Ina me baki hakuri a madadin Huraira,naji takaicin wai yau matata ce ta tsaya tana yiwa mahaifiyata rashin kunya,dan Allah ki yafe min,in sha Allah se na dau mataki akan abinda ta aikata yau din nan".
Shafa kansa Hajjatiye ta yi ta ce "ban amince ka ce zaka dau mataki akanta ba,ni a wajena komai ya riga da ya wuce,ka dena damun kanka".
Murmushi Hajiya babba ta yi wannan dalilin ne suke sa'ke son surkar tasu,ko min irin masifar da zaka ga tana yi tofa bazata yarda wani abun ya ruguza ahalinta ba,wanda be san ta bane kawai zece tana da faɗa.


Magana sukayi sosai kafin Hajjatiye da Hajiya babba suka haura upstairs jin an kira sallah.


Su kuma suna jiran su LTG su fito su tafi masallaci.




A part din Ammuh kuwa,ummah se faman Safa da marwa takeyi tunda suka shigo ta kasa tsaye ta kuma kasa zaune.


Ita kan ta Ammuh lamarin ya girgiza ta,


"Hajiya Huraira dan Allah ki nutsu mu san mafita, wannan Safa da marwa da kike yi babu inda ze kai mu".


Zama ummah ta yi"kamar ni Isma'il ze tozarta a gaban yara da kuma kishiyoyin balbali na?".
"Calm down first wannan fa ba wani babban matsala ba ce amma duk kin bi kin tayarwa da kanki hankali,ko kin manta abinda zamu iya aikatawa ne".
"Hajiya khareema ina sane amma dole raina ya ɓaci kishiya fa?,tun da be min kishiya ba se yanzu da na girma ga yara na sun gama girma shine ze min kishiya".
Matsowa kusa da ita Ammuh ta yi dan ta lura har yanzu Ummah bata dawo dede ba.


"Ki shirya ranar Lahadi muje wajen boka mauzau,daga auren shi Abbu din harna Saghar din se mun watsar dashi".
Se sannan ne taji hankalinta ya kwanta ruwa me sanyi ta bata tasha.




Bayan sallar isha uncle Hameed ya dawo kai tsaye part dinsu ya nufa.
Tsaye a jikin window ya iske Anty amarya, kallo ɗaya ta mishi ta kauda idonta,tunda yaga haka yasan cewa akwai wani abinda ya faru ga idonta da ya kumbura tasha kukanta hatta koshi.
Wajen ta yi nufa.
"Amaryata me yake faruwa na ganki haka"murya na rawa ta sanar masa da duk abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa,kafin ya shigo din nan Hajiya babba da Ammi suka fita a part dinta bayan sun gama rarrashinta.


Jawota jikinsa ya yi yana bata hakuri shi kanshi be ji daɗin abinda ya faru ba, yasan Abbie baze taɓa yanke wannan hukuncin ba,batare da kwakkwaran dalili ba.


"Kiyi hakuri in sha Allah a wannan karon bazamu rasa yarmu ta biyu ba Sabriyah, Allah yana sane da mu,kuma ya Mubarak nasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login