Showing 12001 words to 15000 words out of 94974 words

Chapter 5 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8653

jin abinda Tajuddeen yafaɗa ga kuma fatime takasa cewa komai se ma rawa da jikinta yakeyi da hawaye ,da sauri Hajiya babba ta karasa gaban Asrah dudduba jikinta ta yi bata ga komai ba hakan yasa ta cire mata rigar jikinta ta juya bayanta , sosai ranta ya sosu saboda jikin Asrah danyen jikine da ita kuma yarinya , jikinta yasaba da hutu bazata iya jure zafin da ze mata ba kafin ya warke,itama kanta ranta yabaci , duk kallon bayan Asrah din sukayi duk basu ji dadi ba runtse idanu anty amarya ta yi dan bazata juri kallon bayan ƴarta a haka ba. amma bazasu yanke hukunci ba se sunji ta bakin ita fatime din hakan shine adalci.
Hajiya babba ce ta soma magana " fatime meye yasa za ki mata wannan zanen bakiga itadin yarinya bace , da hankalinki da tunaninki" goge hawayen da takeyi ta yi sannan ta kwashe duk yanda sukayi da Asrah ta faɗa musu ta kara da" wallahi ina tsoron rasa aikina shisa na mata gudun kar anty amarya ta ce , banbi umarnin ta ba akoreni " dukkansu sallallami sukayi da rike baki tabbas sun sani Asrah batajin magana ga kuma karambani zatayi fiye da haka duk kallonta sukayi sun ƙasa ce mata komai, ita kuma Asrah se wuri_wuri take yi da ido kamar wacce ta yi sata wa sarki,Abbie ne yacewa fatime ta koma dakinta tare da mata gargadi karta sake maimaita irin wannan kuskuren, godiya ta yi musu hade da basu hakuri ta wuce dakinta kaltume ma tabi bayanta.
Tajuddeen kam tsaban takaici ma kasa magana ya yi,ya ja doguwar tsaki yajuya ze wuce part din shi , Asrah ta fara binshi ,juyawa ya yi ya kalleta " karki yarda inganki a part dina yau tunda bakyajin magana " fashewa ta yi da kuka ta zauna zaman dirshen akasa tana kuka , part dinshi yashiga yasa key yazauna yaname tausaya mata ,kara jinjina rashin ji da karambanin Asrah ya yi.
Daukanta Ammi ta yi ta wuce da ita part dinta ta mata wanka ta shafa mata magani awajen sannan tabata pain reliever, ta samu ta yi bacci .
Anty amarya,Abbu,Abbie ,Hajiya babba su kadai suka rage afalon suna jinjina lamarin Asrah.


Haka tasha baccinta har yamma ya yi su iklas suka dawo makaranta .




" Dad ! Meyasa yafini komai duk abinda ya nema yana samu , kuma familyn su yafi namu karfin suna , babanshi shine tsohon governor Maiduguri , dayan ƙanin babanshi babban alƙali ne a court of appeal , dayan kawunshi kuma babban doctor ne da kowa yasanshi a fadin duniya . wallahi dad na tsani Tajuddeen Mubarak Bishara! natsane shi!" ya ƙarishe maganar da karfi yana dukan glass table din dake kusa dashi seda ya fashe, matashin yarone wanda kusan zasu iya jerawa a shekaru da Tajuddeen , kyakkyawane shima fari , yanda yake magana zallar wutar ƙiyayyar Tajuddeen ne a cikin kwayar idonshi .
Wani babban mutum ne a gefenshi wanda daga gani mahaifin shi ne , da fa kafarɗar shi ya yi ya soma Magana" Fu'ad kenan duk yanda ka kai da tsanar su baka kaini ba , musamman inna tuna lokacin da nake neman kujeran governor ,saboda Mubarak Bishara na rasa kujeran nan daga karshe shine ya mulki Maiduguri,kuma ni zan tsaya maka se kafishi komai baze taba nasara akanka ba ,se ka nuna mishi kaidin jinina ne , Fu'ad Abubakar daula "


Murmushi ya yi ya ce" Dad sekayi alfahari dani amatsayin ɗanka domin ni din nan dakake gani nafika rashin imani!se na zamewa Tajuddeen babban matsala a rayuwarsa bama shi kadai ba gaba daya mutane se na zame musu bazana" kecewa sukayi da dariya harda tafawa kamar wasu abokai.




Damaturu




" Wallahi yau se kin barmin gidana ke da wannan shegiyar ƴar taki ,domin wannan ba ƴata bace , ko kuma in kasheku na kashe banza " yana magana yana dukan matarshi dake kwance akasa tana kuka ga kuma wata yarinya yar karama kyakkyawa bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba tana rike da kafar mutumin tana kuka , sa kafa ya yi ya hambareta ta fa di ta fasa hancinta da bakinta , rarrafawa matar ta yi taje ta dauki ƴarta ta rungumeta suna kuka tare ,yarda belt din hannunshi ya yi ya tsaya gantsan_tsan akansu yanuna su da yatsa " wallahi Maryam karki yarda in dawo insamu wannan yar shegiyar a gidan nan in ba haka ba kuwa ƙonata zanyi da ranta sannan in haɗa dake , jaka mara mutunci kawai har ni za ki kalla kice wannan yarinyar yata ce bayan kuma duk cikin ahalina babu farin fata kinje kinyi zinan ki , kinsamu cikinta za ki ƙaƙabamin ita to tun wuri kinje ki fadawa kwarton naki bazan karbi shegiya ba " fuuuu yafice agidan kamar ze tashi sama ,Maryam na kuka tana gogewa yarta jinin dake zuba a hancinta da bakinta ta ce" Allah shine shedana wallahi ni ba mazinaciya bace , wannan yar takace kuma jinin ka, in sha Allah, Allah ze saka mana" kallon mamar nata ta yi ta ce" mama mu gudu kar baba yadawo yasamemu , banaso yadinga dukanki" wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tasa hannu ta share ta face majina ta ce" karki damu Asmita in sha Allah babu abinda ze mana tashi inyi miki wanka se in miki kwaɗon ƙanzo da kuli_kuli kici kijin ko" haka ta dauki yarta ta yi mata wanka da klin dan ko sabulun wanka babu agidan kuma bawai dan bashi da halin siya bane muguntace kawai irin na malam Mamman.


Gyara mata kwanciya tayi akan yamutsatsiyar katifar dake dakinta ta yi ta dauko fallen zanin daurawarta ta shifida mata , datse kofar dakin ta yi da sakata ta yanda koda malam Mamman yadawo baze shiga dakin ba .


Suna cikin bacci sukaji yafara doka kofar dakin kamar ze ballashi , afirgice suka tashi ,rungume Asmita Maryam ta yi ƙam ajikinta muryan malam Mamman sukaji yana " wato ni zakiyiwa wayo ko Maryam to gwarama kitashi ki bude in kuma ba haka ba a dakin zan ƙonaku dukkan ku biyu" .


" wallahi Mamman seda ka ƙona mu amma bazan taɓa bude maka kofar dakin nan ba ,tunda kai babu Allah azuciyarka mara imani kawai . Kuma ko mutuwa ka yi wallahi Asmita nada gadonka domin ƴar kace ta halak"
Ta bashi amsa tana kuka kamar ranta zefita , har lokacin tana rungume da Asmita datake a tsorace gani takeyi kamar baban nata konasu zeyi , babu wanda Asmita take tsoro aduniyar nan sama da malam Mamman domin yatsaneta kullum cikin dukanta yakeyi da aibatata ,kuma yaro yana sake jikine da wa'yanda yake sonshi , ga shi agabanta kullum se ya da ki mamanta.


Kokarin fasa kofar yakeyi amma yakasa saboda kofar karfece, makobtanshi ne suka shigo suna hanashi abinda yake da niyyar yi , komawa kansu ya yi ya karta musu rashin mutunci daga karshe yakoresu ya ce musu kar ya sake ganin ko wani munafikin a gidanshi.


Haka Maryam da Asmita suke rayuwar wahala agidan ko kadan basa samun farin ciki , farin ciki yakauracewa Maryam tundaga sa'in da ta haifi Asmita , jaririyar tana da hasken fata malam Mamman ya ƙyankyashe ƙasa ya ce shi wannan ba yar sa ba ce seda ko maryam na da kwarton da yake amfani da ita.






F and share 🖋️🖋️




🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




Page 07




*_ story & written_*

By




*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)


*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*








🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️







Page 07




Yau sati daya kenan , zanen Asrah harya warke dake bata da ƙyan jiki kuma tana samun kulawa sosai ,wajan yabushe ya yi baƙi ga sunan Tajuddeen baro_baro abayanta kullum in za'a mata wanka seta tsaya a gaban mudubi ta karkace gefe ta kalli sunan hakan ba karamin nishadi yake sataba, shikanshi Tajuddeen inya gani yanajin sanyi aranshi .


Kamar kullum tana painting room din Tajuddeen tana zaune Kamar wata uwar mata ta maida hankalinta tana zanen Tajuddeen , shikuma baya nan yana garden yana zaune , dan bazaka taba ganinshi acikin yan uwanshi yana hira ko wani abu da su ba .
Zanenta takeyi cikin kwanciyar hankali batasan su parsa sun shigo painting room din ba , kasancewar yau Friday da wuri suka tashi daga school .


Yanda tamaida hankali akan zanen ma batama san da shigowar su Zoya,umaisha,iklas,parsa,Rameesa ba ,tafiya suke yi sanɗa_sanɗa basa son tasan sun shigo dan so suke yi su dauke drawing din da take yi umaisha ce take directing dinsu yanda zasu yi ita ce boss.


A hankali umaisha tasa hannu tadauki zanen da Asrah takeyi suka gudu daga part din suna ihun" yeeeeeeeh mun dauke_mundauke"
bin bayansu ta yi itama da gudu dan bataso su yaga mata zanen ta, ɓace mata sukayi da gani bata gansu ba, dubasu ta yi ako ina bata gansu alamar ma kamar ba sa cikin mansion din , fitowa ta yi cikin compound din nan ma bata gansu ba , kuka tafarayi tana bubbuga kafa ,ga shi bata haduda yan gidan ba se masu aikine da masu tsaron gidan ne suke ta fita da shiga .
Garden ta nufa tana kukan ɗauke mata zanenta da sukayi kuma bata san inda suka yi ba,volume din kukan nata sake ƙaruwa ya yi lokacin da ta hangi Tajuddeen na zaune acikin garden din ,wajan ta nufa tana isa ta kwanta abayanshi,sa hannu ya yi ya jawota ta dawo gabanshi goge mata hawayen fuskar ta ya yi " hey! Why are you crying?" " to basu zoya bane ba! suka daukemin drawing dina ba suka gudu " yanda take maganar tana turo baki ya bashi dariya amma beyi ba kawai murmusawa ya yi ," Okay kyalesu zasu dawo kinji?" " Tom"


Sake kallonta ya yi ɗakyau ,dama so yake yafaɗa mata nan da kwana biyar ze tafi amma ba ya tunanin tanada wayon da zata fahimta .


Magana yafara yana kallon shuke_shuken dake garden din " Asrah zanyi tafiya ,zan jima amma ba sosai ba .I want you to take good care of yourself " narai_narai ta yi da ido ,se kwabula fuska takeyi tana shirin yi mishi kuka , " wai ke bakida aikinyi se kuka?" Girgiza mishi kai ta yi sannan ta ce" to bakai ne kace zaka tafi kabarni ba, nide se na bika" nan nauyar ajiyar zuciya Tajuddeen yasauke " Asrah sanda zamu tafi inda nake rayuwa daga ni seke na zuwa,za ki bini batare da izinin kowa ba "
Itade jin shi kawai takeyi bawai dan ta fahimci inda maganar ta shi yadosa ba .


Cikin aljihun rigar shi yasa hannu yafito da wani box me matukar kyau , budeshi ya yi yafito da wasu abin hannu masu matukar kyau da tsada me daukar hankali, guda biyu na diamond silver color, yanayin design din ma kawai abin kallo ne ya hadu sosai,abin hannun yana da adjust za'a iya ragewa kuma za'a iya ƙarawa saman shi kuma anyi rubuta " T&A" wato Tajuddeen da Asrah kenan .
Kamo hannunta ya yi na dama yasaka matashi ya ragesa yakoma dede hannunta yanda nan gaba inta ƙara girma ita da kanta zata iya ƙara shi , " woww, tajuju ya yi kyau sosai! I love it " ta faɗa tana shafa abin hannun se santin kyau din abin hannun takeyi , saka nashi shima ya yi a hannunshi bakaramin kyau ya mishi ba , ɗago kai ya yi on a serious face ya kalleta ya ce


" ko da wasa karki yarda ki rabu da wannan abin hannun kinji ko"


gyada mishi kai ta yi tana murmushin farin ciki , mika mata tafin hannunshi ya yi


" Promise me bazaki taba rabuwa dashi ba ko da bama tare. "


Daura hannunta ta yi akan nashi ta ce


" I promise you tajuju , I am going to keep it safe "


Tana gama faɗar haka ta sauko daga kan kujeran ta ruga aguje , da kallo yabi bayanta . Aranshi ya ce


" Nasan zuwa nan da 10 years za kiyi hankali sosai, za ki zama budurwan da babu wanda ze yi gigin neman soyayyarki domin kuwa kedin matar Tajuddeen Mubarak Bishara ce "


Kokarin shiga mansion din ta keyi taci karo da Saghar da Hafiz suna kokarin fitowa , ja baya ta yi sanin Saghar ze iya maketa , watsa mata harara ya yi ganin yana hararanta ne yasa ta murguɗa mishi baki amma shi be ma lura ba Hafiz ne kawai ya gani. yasa kai ya yi gaba yabar Hafiz a tsaye awajan ta . Kallon ta ya yi yaga se washe baki takeyi kamar gonar auduga ,shi dariya ma ta bashi ya ce


" Asrah wannan murnan da akeyi haka na meye ne ?"


Batare da tabashi amsar da ya tambayeta ba ta nuna mishi hannunta dake dauke da abin hannun da Tajuddeen yasa mata, riko hannun ya yi yana " wowwww, gaskiya ya yi kyau sosai wallahi inyaaa Asrah din Tajuddeen dinta " shi kanshi bakaramin kyau abin hannun ya mishi ba yanayin design din so simple ga shi na diamond ne silver color ga shi first alphabet din sunansu ne ajiki T&A ,se yabawa yaketa yi ,


" To kar fa ki yarda shi a garin ƙiriniya kinji ko?"


Gyada mishi kai ta yi kafin ta sa ke rugawa aguje cikin gida abinta duk wanda ta hadu dashi se ta tsaya ta nuna mishi abin hannun da Tajuddeen yabata .


karo ta ci dasu umaisha suna neman ta ga zanen a hannun Zoya sun raba shi gida biyu"Asrah kinga parsa ta yaga miki drawing din ki ko?"cewar umaisha tana nunawa Asrah zanen dake hannun Zoya yana a yage,turo bakinta Asrah ta yi ta ce"i don't have your time!look at my banglesssssss" ta yi maganar tana jujjuya musu hannunta matsowa duka suka yi suna so su kalla ta ruga aguje ta barsu a wajan.


Part din su ta shiga da gudu , akwance ta samu anty amarya tana bacci dan ciwon kai ne yake damunta tashigo saboda ta kwanta , hawa kan gadon ta yi , shigewa jikin anty amarya ta yi tana ta mutsu_mutsu kamar bera , bude ido ta yi tana hararanta dakyar ta iya cewa


" Asrah kinsan Allah zan dakeki , bakisan banida lafiya bane kinzo za ki dameni tashi ki tafi gun Ammi"


Sadaf_sadaf ta mike saboda tasan halin mommynta sosai dukda yanda take matukar sonta tofa Hakan baya hana in ta yi laifi ta mata duka domin anty amarya no nonsense ne bata daukan reni tana da zafi in aka kureta .


Part din Ammi ta shiga bata samu Ammi a dakin ba hakan yasa ta ɗale kan gado ta rufe kanta acikin bargo inba mutum ya lura ba ,bazesan akwai mutum akai ba.
Shigowa bedroom din Ammi ta yi tana manne da waya akunnenta tana waya da Hajjatiye se buhun masifa take zazzaga mata , Ammi de kunshe dariyarta takeyi tana bata hakuri .
Zama Ammi ta yi akan gadonta , Asrah jin an zauneta ne yasa ta fasa kara tana kokarin tashi .
A razane Ammi ta tashi akan gadon kirjinta nadukan tara tara se "innalillahi wa'innailaihi rajuun" takeyi ko kadan batayi tunanin mutum bane awajen , tsorata iya tsorata ta yi saboda lokacin da take da cikin Tajuddeen haka yataba faruwa da ita, shine yasa hankalinta ya tashi .
Asrah jin an ɗaga ta ne yasa ta ya'ye bargon ta fito kallon_kallo suka tsaya yi ita da Ammi, tafa hannu Ammi ta yi tana sallallami " ungo naki Asrah ja'ira kawai " ta faɗa tana mata daƙuwa , ita de ba ta ce komai ba se fiki_fiki takeyi da dara_daran idanunta


" Kai yarinyar nan kin tsoratar dani wallahi Allah yashiryeki ! Yaushe kika shigo bansaniba?"


Kwabe fuska ta yi tana kwanciya akan gadon , ta ce " ai mommy ne ta koreni " kamar zatayi kuka ta yi maganar , murmushi Ammi ta yi dama tunda ta ganta tana kumbure_kumbure tasan akwai wani zama ta yi akan gadon itama cikin kwantar da murya ta ce


" Ba koranki mommynki ta yi ba , bata da lafiya ne shisaka . Idan mommynki ta yi miki faɗa kidena bata rai babu kyau kinji ko?"


Gyada kai Asrah ta yi , rungume Ammi ta yi tana gyara kwanciyarta ajikinta , kallonta Ammi ta yi cike da son yar kanwar nata sauke idonta ta yi akan hannun Asrah dake dauke da abin hannun da Tajuddeen yabata , rike hannun ta yi tana ƙare mishi kallo nan ta fahimci ta inda Asrah ta samu , ajiyar zuciya ta yi aranta tana " ya Allah kai kadai kasan karatun kurma , Allah ka tabbatar da alkhari dake tsakanin Tajuddeen da kuma Asrah "


Kallon fuskar Asrah ta yi taga har ta yi baccinta , ahankali ta kwantar da ita akan gadon ta rufe ta da bedsheet , ta mike ta nufi part din anty amarya .




" Abida anya kinsha magani kuwa ? nasanki sarai da ƙin shan magani tashi kisha " cewar Ammi da bata dade da shigowa bedroom din ba .
Mikewa zaune anty amarya ta yi tana dafe kanta ta zuro ƙafafunta ƙasa.


Magani Ammi ta dauko da ruwa a glass cup ta bata,babu musu tasa hannu ta karba tasha sannan ta jinginu ajikin , makeken gadon ta na alfarma.


Sosai Ammi ta kare mata kallo kafin ta girgiza kai
" Abida meyesa kike saka damuwa aranki yakamata ki fawwalawa Allah komai "
Wasu hawaye masu zafi ne suka gangaro mata


" Anty hamdiyya dole in damu , musamman inna tuna kan cewa bazan sake haihuwa ba , karki manta fa ancire min mahaifa , har abada bazan sake haihuwa ba. Asrah ita kadai Allah ya bamu wallahi anty hamdiyya bazan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login