Showing 30001 words to 33000 words out of 94974 words
fuskanta, innalillahi wa'innailaihi rajuun tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawa ce ta ajin farko tana da ɗan dogon fuska me dauke da dogon hanci kamar anzana pencil,kumatunta kuwa na dauke da dimple aduka biyu bangaren, wanda ko murmushi tayi se sun lotsa balle ace ta yi dariya ko kuma ta yi magana,tana da manya_manyan idanu masu jan hankali cikin idon din nata na dauke da oiling eyeballs ga dogayen gashin idonta dasuke ajere reras kamar wacce tasaka eyelashes sunyi gazar_gazar, bakinta dan karamine sosai pink color yanayin suffan bakinta kamar heart aka zana mata,gaban goshinta na dauke da lallausan saje dake kwance luf_luf gashin kanta ya zubo tundaga kanta har izuwa kusa da kugunta yanada tsayi da kuma cika sosai ,duk inda za'a sako kyakkyawa tofa wannan ita ce zatazo a farko domin makura ce wajan kyau, jikinta na sanye da wasu tsinannun kaya wanda dasu da babu duk daya , irin kayan da nora fatehi tasaka a wakar kusu_kusu , irin kayan nan na yan rawa da India ko larabawa ke sawa , dogon skirt ne wanda ya kasance a rabe biyu gefe da gefe ga ya matseta sosai hips dinta sun fito kayan se daukan ido yakeyi yana walwali rigan skirt din kuma bashi da maraba da breziya sede yadan fi breziya girma kadan tula_tulanta duk suna waje kadan ne acikin rigar , tsayin rigar ko cibiya be kaiba se wasu chain ne da aka musu kwalliya dashi ,hannunta na dauke da abun hannu kalan kayanta baƙi se kuma wani abun hannun da ya kasance silver color me kyau da design din suna ajiki yazauna dass a hannun, yarinya ce yar shekara goma sha bakwai.
Tunda ta shiga cikin filin nan aka fara kururuwa ana kiran sunanta , rawa tafarayi tana lankwasa kugunta kamar babu ƙashi ajikinta , ga kuma kirjinta da take jujjuyawa kamar wata yar India haka take rawa duk wani bangare na jikin na juyawa kamar ba mutum ba ,haka ta dinga rawa baji ba gani cike da kwarewa tanayi tana tauna chew gum din dake bakinta su kuwa mutanen da suke wajan se ihu suke mata ana watsa mata kudi ana kiran sunanta"*SABRIYAH*!*SABRIYAH*!*SABRIYAH*".
Se karfe goma dede ta gama show din rawan. nan take akafara zafga mata tafi raf!raf!raf jama'ar gurin se yabonta sukeyi da kuma zuzuta kyawun da Allah yamata sukeyi,tana kokarin barin filin wani saurayi yazo yasameta"Sabriyah wani ne ya ce yana son magana dake"zuba mishi idanunta masu daukar hankali ta yi cike da tsiwa ta ce" cele kaje kace mishi bazanzo ba" "Sabriyah karki yi haka babban mutum ne kuma daga gani za'a samu kuɗaɗe a hannunshi ki biyoni kawai idan be miki ba sekiyi tafiyarki"ganin inbatayi yanda yaceba ze bata ma ta lokaci kuma akwai wanda tabari yana jiranta sunyi dashi akan zasu hadu.
Bin bayanshi ta yi suka kutsa cikin mutane ko ajikinta,abakin wata mayyar motar kirar corolla s black color ya tsaya , juyawa ya yi yabarta atsaye awajen ,yar tsaki ta yi kadan kafin ta kwankwasa glass window din budewa ya yi hamshaqin attajirin me kudi ne zaune acikin motar murmushi ya yi mata ya ce "shigo mana hot girl" batare da ta bashi amsar tambayar da ya mata ba ta rankwafo ajikin motar kirjinta da fuskanta na ta cikin motar tana tauna cingum ta ce" ya! Lafiya ka sa akirani?"murmushi kawai ya yi dan ya lura yarinyar akwai zafin kai da tsiwa hade da rashin kunya ya kwantar da kai ya ce "ni baƙo ne a garin nan na kama hotel zan kwana biyu kafin in tafi !to sede bana iya kwana batare da na ji ni akusa da mace ba , shisa nakeso muje ki tayani kwana ko nawa kikeso zan sallame ki dashi"dariyar renin hankali ta yi ta ce"sede kuma kayi rashin Sa'a akwai wanda nayiwa alkawari zamu kwana , ga shawara akwai wasu matan anan kaduba su kawai se anjuma"ta faɗa tana juyawa ta tafi bin bayanta ya yi da kallo yanda shape din kugunta yake juyawa nan ne yaji ranshi ya sake biyawa da ita harta ɓule mishi sannan yaja motarshi.
Duk inda ta wuce setaga mace da na miji sunata alfasha ko kuma mace da mace ko kallonsu ba tayi ba ta ci gaba da tafiyarta hankali kwance har takai bakin kofar da zata shiga ta hango rabin ranta na tsaye jikinta da wata yalolon riga yar karama, hannunta rike da kwalban piscup tana sha kadan_kadan rai abace Sabriyah ta nufeta , tana isowa wajan tasa hannu ta fisge kwalban totoline din a hannunta tayi wurgi dashi, ɗago kai Asmita ta yi ta kalli Sabriyah ta dan sosa gashinta ta ce" kiyi hakuri my Tom bazan sa ke shan wani abu ba"watsa mata harara Sabriyah ta yi ta ja hannunta sukayi kofar da tazo zata shiga ta ganta , tana mata masifa"wlh my Jerry zan fara ja miki Allah ya isa in kika sake bari naganki da kayan maye,ke bakisan illar shi bane . kinaso ki mayar da shaye_shaye abin ado awajanki to zamu samu matsala ta kan haka"murguda mata baki Asmita ta yi"nifa karki takuramin maganar illa kam ai rayuwata yadade da samun illa tun lokacin da ubana ya siyar dani akan dubu dari bakwai,ga shi yanzu na zama karuwa karfi da yaji , kidena min yawan wannan fadan naki banijin dadi.so nakeyi in tara kudi sosai ta yanda wata rana in na hadu da mahaifina zan wasa masa su afuska kuma in dauki mahaifiyata in siya mata gida da duk wani kayan more rayuwa"dakatawa da da jan hannunta da takeyi Sabriyah ta yi suka tsaya kallon fuskan Asmita tayi taga kuka takeyi hakan yasa ta rungumeta tana faɗin"ki godewa Allah ke kin ma san iyayen ki nifa bansan kowa ba bana tuna komai na yarintata kawai mutum daya nake iya tunawa Tajujuna shi kadai nake iya zana hotonshi kuma in inya tuna fuskarshi, yanzu mu bar wannan maganar zo ki rakani akwai wanda ya ce zan tayashi kwana yana ciki" goge hawayenta Asmita ta yi ta yi dariya jin abinda Sabriyah tafada wai akwai wanda zasu taya kwana.
Cikin dakin su ka shiga suka sameshi yana kwance daga shi se gajeren wando ya zubawa kofa ido da alamu ita yake jira.suna shigowa ya mike ya zauna yana murmushi , kallon tumbin shi Sabriyah ta yi tana yamutsa fuska" yan mata kindawo kenan ai tundazun ke nake jira zo mufara,nakosa in farajin dadinki" matsowa kusa dashi Sabriyah tayi ta ce "gaskiya ni bazan kwana dakai ba"dasauri ya ce"haba hot girl karki min haka wallahi ke kadai nake da bukata ko nawa zan baki ko 30mint muyi"girgiza kai ta yi "ni kudinka be dameni ba kawai de saboda wannan abun naka ne yasa bazan yarda kayi komai dani ba maganar gaskiya kenan"ta yi maganar tana tuttura baki Asmita dake gefe kam babu abinda takeyi da ya wuce aikin dariya dama wallahi tasan za'a rina kadan daga iya shegen Sabriyah kenan, ƙare wa kanshi kallo ya yi yana neman abinda take magana akai ,"hot girl saboda me kike magana akai ?"da kyawawan hannunta ta nuna mishi tumbinsa ,ɓata rai ya yi ya ce"ke banason iskanci saboda tumbina ne zakice bazaki yarda ba? ke da kike karuwa har sekin zabi da wanda za ki yi mu'amala?"gyara tsayuwarta tayi ajikin bangon dakin tana girgiza kai kamar wata me jin waƙa ta ce"eh naji ni karuwace ka faɗa da karfi ka ƙara da ihu kuma karuwar ma me lasisi, amma bazan bar me shegen tumbi kamar wanda ya haɗiyi tukunyan giya ya kwanta ajikina ba atoo kaje ka rage wannan cikin naka wasu insun ganka ma zasuyi tunanin cikin wata tara ne dakai"tunda yake ba'a taɓa ci mishi fuska da mutunci ba irin yau ba a harzuke ya kai hannu ze cakumeta ta gauce ta bude kofa ta fice a ɗari Asmita dake dariyar mugunta itama tabita abaya suna gudu suna dariya hade da tafawa "wallahi my Tom bakida kirki bawan Allah ya gama saka rai zaku kwana shine zakici mishi mutunci"far_far da idonta ta yi ta ce"to ai ina zan tsaya ma wannan katon mutumin" "to inya kai ƙaran ki gurin boss lady fah?"kwashe gashinta ta yi ta dauresu da daya daga cikin abun hannunta ga kayan jikinta ma sun fara takura mata "oho ina ruwana seta san yanda zatayi dashi"haka suka koma sashinsu suna tafe suna hira.suna shiga suka hangi anty Teema na zaune ga kwalin sigari agabanta da laita sede bata kunna ba alama ta tafi duniyar tunani ne domin ko shigowar su ma ba ta ji ba.
Zama sukayi Asmita ta ce"anty Teema mun dawo"se a lokacin ne ta fahimci cewa su Asmita su shigo girgiza kai ta yi murya a sanyaye ta ce"dama yanzu nakeson zuwa in kira ku na ji ku shuru kuma nasan in kunyi wasa bakwa daɗe wa" Sabriyah de tunda suka shigo ba ta ce komai ba se nazartan antyn sun takeyi"anty Teema dan Allah meyake damunki ne gaba daya kin canza ba kamar yanda muka sanki ba tun bayan mutuwar anty Rash gaba daya kin koma wata kala Wallahi ni gaskiya banajin dadin ganin ki ahaka"murmushin takaici anty Teema ta yi ta ce"ku haryanzu yarane amma abun da kullum nake faɗa muku shine karku yarda boss lady ta turaku wajan da za'a kwanta da ku domin daga za ran kun shiga wannan harka na karuwanci da take saka yara Wallahi rayuwarku ya lalace kamar yanda nawa rayuwar ya lalace nasan kusan abinda ya kashe Rash ciwon ƙanjamau ne ya yi ajalinta nima kuma ina dauke da wannan cutar.kullum cikin nadaman wannan rayuwar nake ina so inga iyayena bansan ko suna raye ko sun mutu ba, guduwa nayi daga gida saboda za'a min auren dole ashe a hannun boss lady zan faɗa na bijirewa iyayena nazo na shiga duniya.inde da raina da numfashina bazan taba barin boss lady ta mayar da ku karuwai ba yanda take buri duk da ta yi rabin hakan duk wanda ze ganku se ya kira ku da Wannan suna na karuwa se de ko in ba'a garin nan ba.rawa,damfara,shaye_shaye domin Asmita ke naga kin fara mayar da kanki yar shaye_shaye to dan Allah ki raba kanki da kayan maye domin ni nasan illar su.duk kun rigada kun faɗa wannan harkan yanzu jira takeyi nan da kwana biyar akwai manya_manyan masu kuɗi da zasu zo diban wa'yanda zasu kwana da su daga nan ne kuma zata fara safaran ku"tabe baki Sabriyah ta yi ko ajikinta ta ce"nifa anty Teema haryanzu ban ma ga na mijin da zan iya bashi jikina ba sede ko boss lady kasheni zatayi amma Wallahi bazeyu tasani inje wajan wani banza ba, wasar rawar da nakeyi ma kadai ya isheni shi dinma dan kawai innayi inajin nishadi ne amma badan haka ba babu abinda ze sani inyi yawwa"duk zuba mata ido kawai suka yi saboda sun san halin Sabriyah sarai akwai taurin kai bana wasa ba in ta faɗa magana tofa ko me ze faru ba zanjawa takeyi ba in ma zata canza se ankai ruwa rana.
"Ni barin ma inje in canza wannan kayan sun dameni"ta yi maganar tana mikewa sannan ta sa hannu ta kwashe duka kwalin sigarin dake gaban anty Teema.
Riko hannunta Asmita ta yi idonta sunyi ja sosai ta ce"Sabriyah wai ke bakya tunanin gida ne,bakya son barin nan?"dawuwa ta yi ta zauna ta fuskanci Asmita ta ce "to yazanyi?koma ina son komawa gida su waye iyayena?bansan su ba ku kadai nasani se kuma tajuju na kullum shine yake zuwa mini a mafarkina,ku kadai nake dashi shisa ma ni ban taba kwadayin barin wannan gida ba domin inna barshi ma bansan ina zani ba.kefa kina son barin nan?"ta gama maganar tana jefawa Asmita tambaya gyada mata kai Asmita ta yi"tabbas ina son zuwa gida ina son gani n mamata in jini acikin jikinta sannan in tara kudin da yakai yawan million dayan inje in samu fuskan babana in watsa mishi su wannan shine burina"sosai Asmita tabawa Sabriyah da anty Teema tausayi domin daga yanayin muryanta kadai ma in ka ji kasan deep down her heart akwai babban ciwo arayuwarta domin kullum se ta yi mafarkin lokacin da malam Mamman ya rabata da gida ya je ya siyar. da wannan dalilin ne yasa ta faɗa harka shaye_shaye ko hakan ze taimaka mata ta manta da komai amma hakan be samu ba,shafa fuskanta Sabriyah ta yi ta ce"za ki je gida wata rana tashi muje mu kwanta mubar anty Teema ta huta"mikewa sukayi suka mata sallama suka shiga nasu dakin bin bayansu da kallo kawai anty Teema ta yi tana rayawa aranta ina ma ace tana da damar kubutar da wa'yannan yara guda biyun.
Dakin nasu balaifi ɗan matsakaici akwai katifa ga gefe kuma wadrobe na sa kayan su se risho da wasu tukuye da kwanukan da basu fi biyar ba.
Suna shigowa Sabriyah toilet ta shiga bayan ta watsa sigarin da ta dauka a gaban Anty Teema a cikin dustbin,ta cire kayan jikinta ta yi wanka ta daura zani a kirjinta ta fito ta zauna abakin katifa tana duba basilin dinsu ganinshi ta yi ta dauka ta fara shafawa Asmita ma wanka tashi ga bayan ta fito ne ta dauko musu wani yalolon riguna masu dogon hannu suka saka suka kwanta dan yau a gajiye suke sosai musamman Sabriyah da tayi rawa.
Washe gari basu suka tashi ba se misalin ƙarfe goma dukkansu brush sukayi suka yi wanka suka zo suka zauna a dakin nasu Asmita ta ce"my Tom nikam bazamu karya bane kin wani kwanta"mikewa ta yi ta ce "naga ai bakice kinajin yunwa ba nadauka se anjuma ne ai"tsaki Asmita ta yi ta ce "Wallahi kina da matsala kinsan karfe nawa ne yanzu? nikam in akwai kudi a hannun ki bani inje in nemo mana abinda zamu karya dashi"kasan filo Sabriyah ta daga mata kudin da ta damfari mutumin jiya ne naira dubu goma ne ta dauko dubu biyu ta ce"ya yi ko in ƙara?kar mu cinye kudin kuma muzo muna muzurai tunda Kinga kowa a gidan nan shi yake ciyar da kanshi" " gaskiyan ki ne hakan ma ya isa tashi muje mu dawo se mu daura nasan anty Teema ma ta farka."mikewa sukayi suka fice dukkansu babu wanda yasa gyalle balle hula duk gashin su a fake kamar wasu arna Asmita na sanye da riga me guntun hannu red color da wando trequater grey color,Sabriyah kuma riga ce ajikinta yar guntuwa ya tsaya mata a guiwa duk da rigar play ce amma seda tudun hips dinta suka fito hankali kwance suke tafiyan su har sunyi nisa suka jiyo murya a bayansu tana"ku jirani dan Allah" dakatawa sukayi suna jiran nata Asmita ne ta ce "Nabiha kuma ina zataje take wannan saurin" "wa ya san mata ne"cewar Sabriyah.iso wajen su tayi ba laifi itama tana da ɗan kyau black beauty ce daga ita se wata guntuwar mini skirt da karamar riga kanta yasha kitson attachment ta ɗan yi kwalliya a fuskarta.
"Ina zakuje"Sabriyah ce ta bata amsa da"bakin titi zamuje siyan kayan karyawa! kefa ina zuwa?"murmushi ta yi ta ce"wani sabon kamun kifi nayi yace inzo da safen nan shine na fito" "okay to munje in yaso ke kya tsaya abakin shagon nasan za ki samu abun hawa"cewar Asmita tafiya sukeyi suna hira har suka iso shagon da zasu shiga din nan suka rabu da Nabiha ita kuma ta hau mashin ta tafi.
"Me shago kabamu idomie da kayan shayi da biredi" Asmita ta faɗa ko ajikinta duk da ta kalli layi ake bi a shagon juyowa mutanen sukayi suna watsa musu harara wata krista ce ta ce"uban wa kuka fi gadara anan da zaku zo kuga layi bazaku bi ba sede ku wani ce abaku kaya"ke Sabriyah da bada ke akeyi ba yar ta ran aradu da ka a harzuke ta ce "ubanki mukafi gadara shisa mukace abamu" "kan uban can ubana kika zaga?" "Iyi shi na zaga ko akwai matakin da za ki dauka ne"ganin su Sabriyah sun fita budewar ido yasa ta yi tsaki ta ce "aikin banza zakisan kin zageni" me shagon ganin zasu tayar mishi da faɗa a shago ne ya ce "me za'a baku?"sake faɗa mishi Asmita ta yi aikuwa da sauri ya haɗa musu ya mika musu suka bashi kudinsa suka tafi, akan hanya suna kan dawowa Sabriyah ta ja dogon tsaki kallon ta Asmita ta yi ta ce "me kikewa tsaki haka"da ido ta nuna mata gabansu wata farar jeep ce a fake mutumin ciki ya zubawa Sabriyah ido kamar wani tsohon maye kasa_kasa da murya Asmita ta ce"my Tom kin san shine naga yana miki irin wannan kallon kwarillan?" bata rai Sabriyah ta yi ta ce"ehh nasanshi jiya bayan na gama show cele yazo yasameni wai mutumin na kira na,ni Wallahi be burgeni" "ohhh nagane amma Wallahi karki kuskura mutumin nan ya tafi be baki wani abu ba ahh! kinsan de kayan abincinmu yakare "yanda Asmita take mata magana cike da umarni ne abin yabata dariya.
Isowa sukayi kusa dashi basu ce mishi komai ba ya ce "ku shigo mana in sauke ku?"girgiza kai Sabriyah ta yi ta ce"ba bukata ya akayi?me ya kawo ka?" Kare mata kallo ya yi ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce"yau de ina neman alfarma kizo ki tayani kwana" cike da gadara ta ce"okay naji"murmushi ya yi"yawwa hot girl ga shi bari in baki transport ga kuma address dina"ya yi magana yana fito da band din dubu daddaya guda biyu daga cikin aljihun shi ya mika mata wanda a ƙala ze kai dubu ɗari.karba ta yi ta ce"okay "sannan suka wuce shi se da suka tabbatar da ya tayar da motarshi sannan suka fito da kudin suka kirga dubu ɗari ne cas tafawa sukayi Sabriyah ta yaga address din nashi da yabata ta ce"bari anjuma cele yazo zan bashi yaje ya siyo mana kayan abinci".
Bayan sun koma ne sukayi abin karyawa sukaci dama sun rigada sun kaiwa anty Teema nata duk suna baranda suna hira su uku boss lady ta shigo tafiya ma dakyar take iya yi saboda kiba da ya mata yawa ita da wani dan daudu suka shigo dauko mata kujera