Showing 15001 words to 18000 words out of 94974 words

Chapter 6 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8656

boye miki ba Abdulhameed yana matukar kaunar yara nina sani komin daren dadewa ze ƙara aure saboda yasamu yara shima kuma ni bazan taɓa shiga hakkin shi ba , bazeyu ni bana haihuwa kuma in hanashi aure ba "


Sosai tabawa Ammi tausayi jikinta ne taji ya yi matukar sanyi , riko hannunta ta yi ta ce


" Ya isa shikenan kidena kuka , kamata ma ya yi kidinga godewa Allah , wasu fa neman ko da guda dayan sukeyi su samu amma ina Allah yasa babu haihuwa a ƙaddarar rayuwar su ,amma kefa kinga jininki aduniya , se bayan kin haife Asrah fa aka cire miki mahaifa , aduk san da kika kalleta ki dinga godewa Allah wasu neman guda daya ma sukeyi sun rasa , maganar Abdulhameed ze ƙara aure kuma ki kwantar da hankalinki ko da ze Ƙara aure wallahi bazeyi ɗan yaci mutuncinki ba, ɗan saboda yana matukar sanki, kuma namiji mijin mata hudu ne karma ki ce za ki sa wannan aranki . Ni yar uwarki ce ciki daya uwa daya uba daya nasan irin raɗaɗin da kikeji , Allah yana sane dake"


Murmushi ta yi ta kwantar da kanta akan kafaɗar Ammi " Nagodewa Allah dayasa nayi aure akusa da yar uwata , aduk sanda nake cikin damuwa ke kike kwantar min da hankali ina matukar alfahari dake anty hamdiyya"


Shafa kanta Ammi ta yi tana murmushi,son kanwar nata nasake ratsa ta.


Uncle Hameed da tun lokacin da suka fara magana ya shigo bedroom din yake tsaye abakin kofa yana harde da hannu a kirji , dukkansu biyun babu wanda ya san da yana dakin , karasawa cikin bedroom din ya yi se sannan ne suka ganshi saboda hankalinsu ya yi nisa cikin maganar da suke tattaunawa.


Durƙusawa Uncle Hameed ya yi agaban anty amarya ya rike kafaɗunta da dukkan hannayenshi biyu yasa idonshi cikin nata


" Abida wallahi babu irin wannan tunanin araina , eh tabbas inason yara inason inga yarana na shawagi atare dani amma ki yarda dani bantaba sha'awar haihuwa da wata mace ba in bake ba . Kuma godewa Allah zamuyi tunda seda muka haife Asrah kafin hakan yafaru ,kinga ai muna ganin gudan jininmu tana a tare damu me ze sanyamu bakin ciki? Kuma sannan koda ace bamu haife ta ba aka cire miki mahaifa wallahi bazan taɓa auro wata matar ba ,dan saboda ta haifa min yara ba ,babu wannan burin araina dake nafara rayuwata kuma dake zan gama duk runtsi duk dadi muna atare da junanmu , fatan da zamuyi shine muyi addu'a Allah ya raya mana Asrah dinmu muga lokacin aurenta da Tajuddeen "


Uncle Hameed ya ƙarishe maganar sa yana dan jan hancin anty amarya ,duk murmushi sukayi musamman ma maganar shi ta karshe da ya yi akan Asrah da kuma Tajuddeen.


Ammi ranta fal da farin ciki ganin kanwar nata ta ɗan saki ranta ,sake godewa Allah ta yi da yasa kanwarta ta auri namiji da yasan yakamata arayuwarshi me kuma sonta, saboda uncle Hameed yana da saukin kai sosai kuma an hadu andace ne shida anty amarya,sede ita tana da zafi bata daukan reni amma kam tana da kirki sosai kusan halinsu daya ne ita da Ammi .


Juyowa uncle Hameed ya yi ya kalli Ammi ya ce " ina matukar godiya anty da yasa ko yaushe kina me nuna mata hanya da kuma faɗa mata gaskiya "


Murmushi Ammi ta yi ta ce" Allah yabarku tare bari in koma part dina na bar wancan rigimammiyar tana bacci "


Mikewa ta yi ta musu sallama tafice.




Gangarowa downstairs Ammi ta yi with full surprise taga yaran gidan gaba daya a hade awaje daya kusa da Abbie da alamar abu suke kallo ko kuma video call suke yi wani tunani ne ya faɗo mata a rai " to kodai da mom Rumanatu suke wayane?" ta ƙarishe maganar taname ci gaba da saukowa main part din.
( mom Rumanatu Bishara ƙanwa ce agun Abbie da kuma Abbu se kuma ita last born kuma shine uncle Hameed su hudu ne agun iyayensu. Mom Rumanatu tana aure a Katsina tare da ƴaƴanta hudu da kuma mijinta)


Zama Ammi ta yi tana kallon yaran nasu yanda suke ta shan waya da mom Rumanatu gwanin sha'awa hakan kadai ze nuna maka akwai kauna me tsanani a tsakanin su ta cikin laptop din ta ji muryan mom Rumanatu na tambayar ina Tajuddeen da Asrah suke Abbas yabata amsa da "Taj yana part din shi ita kuma Asrah ni yau tunda nadawo gidan nan ma ban ganta ba"Zoya ce ta ce "dazun munga tashi ga part din Ammi" haka suka dinga hira daga karshe yaran suka watse suna mata sallama.




Abbu ne ya shiga part din su saghar ya samesu suna zaune suna searching a goggle tsikayan muryanshi sukayi yana tambayar su"ina mamanku?"kallon_kallo saghar da sudais suka tsaya yi kafin Sudais ya ce"Abbu ni Wallahi bansan ina Ummah take zuwa ba kullum bata gida" girgiza kai Abbu ya yi jin abinda yaran nasu suke faɗa wato su ma gantalin da uwarsu take yi yana damunsu.
Cikin kwantar da murya Abbu ya ce "karku damu in sha Allah everything will be history, in ta dawo ku ce mata Ina da Shari'a gobe zan shiga kotu da wuri" "to Abbu Allah ya taimaka" saghar da sudais suka faɗa,amsawa ya yi sannan ya juya ya fice.






Se mun haɗu Monday in Allah yakaimu da rai da lafiya.




Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.




Comment,like and share 🖋️🖋️




🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




Page 08




*_ story & written_*

By




*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)


*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*








🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️







Page 08




Washe gari Abbu da wuri ya shirya dan zuwa court misalin 9:00am tunani ya fara yi na ko Hajiya hurairah ta na nan ko ta yi ficewarta dan jiya bayan ya shigo yaji shigowar ta bata nemi tazo taji ko yana lafiya ba ko akasin haka ba taje ta yi uzurin ta,shisa shima daya gama shirya wa ya fito be ko kalli inda dakinta yake ba yabar part din. me aiki ya gani tana kokarin shiga ta yi musu gyare_gyare nan ne ya tambaye ta ko taga Hajiya hurairah ta amsa mishi da"yau Hajiya da wuri ta fita tun asuba naga fitar ta"gyada mata kai kawai ya yi yasa kai ya wuce yana hasaso irin kwakkwaran matakin da ze dauka akan Hajiya hurairah domin abin nata yafara wuce gona da iri.


BORNO STATE HIGH COURT




" Ya me girma me Shari'a wanda nake karewa malam isah gwani ya kama abokinshi wato labaran sha'ibu yana kokarin yin lalata da matarsa Hajara , yana kokarin keta mata haddinta amatsayinta ta matar aure kuma mace , malam isah gwani yasan wannan kotu me adalci ne za'a bi musu hakkin shi ,shida matarsa Hajara shisa yakawo wannan ƙaran nan . ya me girma me Shari'a da wannan nake rokon kotu tabi musu hakkinsu , kuma labaran sha'ibu yakarbi hukunci dede da abinda ya shuka Nagode"


Lauyan na gama fadin haka cikin girmamawa dakuma sanin aikinshi yasamu guri ya zauna.


Yar rubuce rubuce alƙali Isma'il Bishara ( Abbu) ya yi idonshi manne da farin glass.


Karewa kotun kallo nayi nan na sake fahimtar babban kotu ne ga al'umma a cike maƙil da kotun kowa ya yi shuru ya ka sa kunne ana sauraran wannan shari'ar , dakuma son jin hukuncin da alƙali ze yankewa mai laifin duk sun matsu suji .




Ɗago kai alƙali ya yi bayan yagama rubuce rubuce ya ce
" Kotu ta yankewa labaran sha'ibu hukuncin bulala 100 abisa kokarin yin zina da matar aure tare da cin taransa na dubu ɗari sannan kuma ze bawa malam isah gwani da matarsa hakuri."


Yana kammala fadin haka ya buga guduma
Aka amsa da " kotuuuuuuuuu"


Mikewa ya yi polisawa da lawyer's suka bi bayanashi domin takewa babban alƙali baya har packing space din kotun bude mishi motar jami'an tsaron sukayi ya shiga , motoci goma ne suka fita a kotun don zuwa gidan Bishara .


Kowa dake cikin kotun se alhamdulillah sukeyi da hukuncin da aka yankewa labaran saboda irinsu ne maciya amana da koda anbasu amana zasuci tunda ga shi yaje yana kokarin keta haddin matar abokinsa , hakan ya zama izina ga yan baya.wa'yannan sune mutanen da zaka nemi Allah yarabaka dasu domin ba abokan zama bane .






BISHARA'S FAMILY




Motacin da suka rako alƙali suna gama shigowa motar Hajiya hurairah yashigo Packing ta yi ta fito tunda tafito Abbu yake kallonta ranshi na ƙuna saboda tafita batare da izininshi ba duk da ba yau ta fara ba , ganin yana jefa mata harara yasa ta dauke kanta kamar bata ganshi ba ta wuce ta gabansu kanta asama , mansion din ta shiga ta ƙare mishi kallo ajiyar zuciya ta sauke ganin yaranta suna zaune suna kallon Tv a main part din dan rabonta dasu tun asubahi data fita agidan part dinsu ta nufa hankalinta kwance bata damu da tambayoyin da Abbu ze mata ba domin kuwa tana dede dashi har ta yi nisa a haura steps taji an dafa kafaɗarta juyawa ta yi dan ganin waye haka .


Murmushi suka sakarwa juna lokaci da ta juyo jan hannunta Hajiya hurairah ta yi zuwa part din.


Tana shiga suka tafa hade da yin shewa zama sukayi abakin gado .


Hajiya khareema ta ce " aminiyata faɗamin ya ake ciki ya kukayi da boka mauzau , shafamin inji nakosa "


Dariya Hajiya hurairah ta yi ta bude hadadden handbag dinta tafara fito da kayan tsubbun da boka mauzau yabatasu masu yawa sosai daga kan layoyi dakuma wasu abubuwa akulle a ledoji.


Wata bak'ar leda ta dauko yana ƙunshe da wani maganin tsubbun aciki. ta kalli Hajiya khareema ta kashe mata ido ta ce


" Yau din nan jinakeyi nafi kowa farin ciki , kinga nan da gobe zuwa jibi ? to labarin yarinyar da take kokarin bata miki aiki yakare batt zasu nemeta su rasa na tsawon har abada"


" Heeeee kai kawata inaji dake wallahi shisa nadauki ragamar wannan aikin nabaki shi a hannun ki kafin a zo mataki na biyu" cewar Hajiya khareema tana bata hannu suka tafa , ci gaba da magana Hajiya hurairah ta yi.


" Wannan maganin da kike gani acikin bakin ledar nan shine za ki san hanyar da za'ayi asashi a abincin gidan nan gabaki daya kowa yaci harta masu aiki, jami'ai, masu gadi da kuma mutanen gidan! daga zaran sunci abincin nan dake dauke da wannan maganin tofa sufa labarin su yakai monday domin bacci zasuyi sosai yanda har a shigo adauke Asrah aje akasheta ma bazasu taba sani ba se safiyar washe gari .
Maganin zesasu ne suyi dogon bacci me nauyin gaske , rikeshi a hannunki"


Ta faɗa tana miƙa mata sa hannu Hajiya khareema ta yi ta karbe shi tana jinjina kai cike da farin ciki.
" sekuma wannan layar kinganshi nan ? acikin gidan nan za ki binne shi , tayanda ze hanasu yunkurin neman yarinyar sannan kuma zasu manta da ita na har abada ke in taƙaice miki ma babu wanda ze sake koda ambatan sunan Asrah "
Jinjina mata ta yi da babban yatsar hannunta kafin Hajiya khareema ta ce..


" gaskiya hurairah kedin fa bata wasa bace , shin boka mauzau yabaki wanda yarinyar zata manta komai nata harta sunanta ?" " Eh yabani ga shi nan ma " tafada tana fito dashi acikin jaka, kamar ruwan turare yake ɗan kaɗan a kwalba gyara zama Hajiya hurairah ta yi ta soma magana " kinga wannan kuma kadan za'a saka acikin hanky se a shaƙa mata a hancinta daga zaran ta shakeshi tofa ko kanta bazata sake tunawa ba daga nan ma mutuwa zatayi saboda duk wanda ya shaƙi wannan turaren shida sake rayuwa kuma se wani ikon Allah"


Ajiyar zuciya Hajiya khareema ta sauke sannan ta sa hannu ta kwashi kayan tsubbun nasu ta saka acikin yar handbag dinta ta kalli Hajiya hurairah ɗakyau ta ce" kinyi mini kokari sosai kawata , kuma in sha Allah zan cika miki burinki na mallakar dukiyar wannan ahalin gaba daya , yanzu bari in wuce in tafi in samu in adana wa'yannan kayan kar mijinki Abbu ya shigo yasamemu " tana magana tana tafiya da sauri_sauri dan batason su hadu da Abbu a hanya saboda ta lura kamar yafara zarginsu , bin bayanta ta yi saboda tarakata , sosai suke murna yau ce rana ta farko da zasu fara cin nasara akan wannan family din.


Bata koma ciki ba har se da taga Hajiya khareema ta bace mata da kallo kokarin komawa takeyi idonta yasauka akan Abbu da yake daff da shigowa daure fuska ta yi itama sannan takoma ciki ta tsaya , yana shigowa babu abinda ya ce mata fa ce zaman da ya yi akan manya_manyan kujerun da suka zagaye falon nasu , ganin bece mata komai bane yasa ta shiga kitchen ta dauko mishi ruwa me sanyi ta kawo mishi sannan ta tsiyaya a glass cup.


Abbu de da ido kawai yake binta takaicinta ma ya hanashi magana saboda Hajiya hurairah kamar ba zaman aure sukeyi dashi ba duk sanda ta yi niyar fita ,fita takeyi abinta ako wani irin lokaci kuma tadawo aduk sanda ta yi niya abin na matukar kona mishi rai , aduk sanda ta fita se ya mata faɗa daga karshe yakara mata da nasiha kullum cikin cewa take bazata karaba.
Daukan glass cup din ruwan Abbu ya yi yasha ya ajiye duk tana zaune a kujera me zaman banza tana kallonshi.


Rike haɓa Abbu ya yi ya ce" Hurairah Ina kikaje yau tunda asuba kika fita ?"


Ɗan nisawa ta yi tana tuno me za ta faɗa mishi can wani tunani ya faɗo mata a rai . " Abbu ina wannan ƙawar tawa rukayya? to ita ce mamar ta ba lafiya shine ta ƙirani mukaita asibiti" girgiza kai Abbu ya yi saboda ko kaɗan be yarda da wannan maganar na taba ,dama ita inde tafita bata rasa abin faɗa uzuri kala_kala kullum da irin karyar da take mishi , mikewa ya yi yana cire babbar rigar jikinshi yarike a hannu ya ce " nasha faɗa miki na tsani irin wannan fitan hurairah ko kadan banaso amma , bazakisan banaso ba sena dau mataki akai " yawuce yabarta awajen zaune. tabe baki ta yi sannan ta fito daga part din nasu zuwa can main part din gidan ta nufa saboda kiran yaranta Sudais da Saghar da kuma yara matan ta.
(wlh mata da yawa ba su dauki irin wannan fitan abakin komai ba zakaga mace ta fita aduk lokacin da take so batare da izinin mijinta ba.wata kam ma jira take yi yasa ƙafa ya fita yana sa kafa ya fita itama zata bazama nata wajen,bayan kuma hakan da mata keyi kwasarwa kanmu zunubi mukeyi duk taku daya da za ki taka Mala'ikun Allah na tsinuwa ne gareki.shin menene ribar haka kina saɓawa mahaliccinki, babban abinda yake kashe aure kenan saboda babu abinda maza suka tsana sama da irin haka musamman ma su dawo gida suna tsammanin zasu tarar da matan su agida amma ah ah bakya nan kuma fitan naki bawai da izinin shi ba hakan ne ze tunzurshi yasa ku fara samun saɓani,ba ma wannan ba wasu matan basa tunanin tsautsayi kin fita batare da sanin mijinki ba ƙila ma yace miki karki fita kika ƙi jin maganar shi wani tsautsayin ya rifta wa gari ya waya?Allah yasa mu dace ya bamu ikon gyarawa Allah yasa a fahimci wannan kuskure ne.)






Ammi,Hajiya babba,Anty amarya duk suna zaune a main part suna hira gwanin burgewa,anty amarya ta warware taji sauki dama damuwar da tasawa ranta ne yake damunta haryaso ya kwantar da ita . Shigowa falon Hajiya hurairah ta yi bakinta dauke da sallama atare suka kai idonsu kanta sannan suka amsa zama ta yi akan daya daga cikin kujerun aka ci gaba da hiran da ita, daga zaran sun haɗa ido da anty amarya se ta sake mata wani munafukin murmushi da ita kadai tasan ma'anarshi ranta fes , anty amarya ta rasa gane wannan murmushin da Hajiya hurairah takeyi ma ta na menene hakan yasa ta tsame bakinta daga hiransu ta yi shuru kamar bata wajan saboda dama bawani yi sukeyi da Hajiya hurairah ba musamman da taga sun shaƙu sosai ita da Hajiya khareema.


Kallonta Ammi ta yi kawai ta girgiza kai tasan sarai saboda Hajiya hurairah anty amarya ta yi shuru ,


Hajiya Babba ta ce" Abida ya kikayi shuru kuma?"yaƙe anty amarya ta yi ta ce " ah ah bakomai Hajiya babba" bata yarda da abinda ta faɗa tasan dalilin Hajiya hurairah ta yi wannan shurun.


" yauwa dazun Abbie dinsu naji yana faɗin Asrah itama gobe za'a mata registration a makarantar su iklas tunda yanzu kundawo Nigeria da zama " anty amarya na kokarin bawa Hajiya babba amsa karaf Hajiya hurairah ta riga ta cikin suɓutar baki da ita kanta batayi tsammanin bakinta ze furta haka ba ta ce " ai karma ku wahalar da kanku kan makarantar Asrah bayida amfani" se da ta tuna abinda ta yi kuma ta datse harshen ta cike da da nasanin abinda ta faɗa, duk zuba mata ido sukayi jin maganar da ta yi wai saka Asrah a makarantar bayida amfani hakan yasa suke kallonta cike da son jin ƙarin bayanin dalilin da yasa ta fadi haka,me take nufi kenan.


Yar dariyar borin kunya ta yi saboda batason suyi zargin wani abu dangane da abinda ta faɗa yasa ta ce" eh mana nide

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login