Showing 51001 words to 54000 words out of 94974 words

Chapter 18 - ASHE ZAMUGA JUNA COMPLET BY MRS ISHAM.txt

28 Dec 2024

8663

Sudais shi kadai ya ke da niyar zuwa gun aiki!", kwaikwayon yanda sukayi maganar Sudais ya yi yana"yen!yen!yen!ƙatti da ku agaban ƙannenku kuna wani shiririta shame on you guys" Ammi de ce musu ta yi"ku de ba'a iya muku,se anjumanku mu haɗu a dinning kawai".ta faɗa tana barin falon.
Duk watsewa suka yi a falon kowa yaje dan ya shirya .




Part din su suka shiga,cike da walwala Umaisha ta ce "muje ki sauka a dakin mu !"burki Sabriyah taja ta haɗa fuska ta ce "ke banason iyayi fa, na ce bazan sauka a wajanku ba dole ne!".zaro ido waje Umaisha ta yi tana mamakin hali irin na Sabriyah aranta ta ce "wai nikan wannan ba'a mata gwaninta ne?ohhh wato kowa da irin halinsa"karewa part din nasu kallo Umaisha ta yi,idonta ne ya sauka akan wani daki madaidaici wanda ya kasance extra room din dake part dinsu,bayan daki guda biyun dake cikin part dinsu din akwai daki madaidaici.


Gaba Umaisha ta yi ta ce "to muje dakin nan,ke kadai anan din,tunda kin fison zama ke daya,ai kadaici kadai ma se ya isheki.nifa inni ce wallahi bana iya zama Ni daya kamar mayya,ko yaushe nafison injini cikin mutane ai yafi dad'i, mutane rahama ne!,ke nifa bama wannan ba,abinda yasa bana zama ni kadai ina da matukar tsoro,se in ga kamar dodo ze kamani.yanzu ke haka kika zabawa kanki zama ke daya!?,haba Sabriyah ke haka za ki zauna Kamar wata mayya!?,"bin bayanta Sabriyah ta yi tana mamakin surutu irin na Umaisha tafiya takeyi amma se zuba takeyi kamar kurna, bata ko haɗiye yawu,jera magana takeyi ko gajiya batayi ba.sabriyah takasa dena kallonta,ita de tana fama da abinda yake damunta na sace Asmita ga kuma kawota nan da LTG ya yi ga kuma Umaisha da tasata a gaba da magana kamar wata yar jarida.


Dakin suka shiga, ya hadu komai akwai aciki.
Nuna mata yanda zata yi amfani da toilet din da kuma sauran abubuwan ta yi,kafin ta ce"kiyi wanka bari in kawo miki kayan sawa".ba tace mata komai ba toilet ta shiga,ita kuma Umaisha ta fita a dakin da hanzari,wanka Sabriyah ta yi ta ta wanke gashinta, daura towel din da ta gani ta yi. fito gashinta na diga da ruwa,tsane jikinta tayi ta goge dogon baƙin gashinta,tana zaune a gaban mirror ta shafa mai din da ta ganim ta taje gashinta ga handryer a kan mirror amma bata san meye amfanin shi ba kuma bata san ya akeyi dashi,ta cikin madubi ta hango kayan da Umaisha ta kawo mata,mikewa ta isa gaban gadon ta dauki kayan,warwaresa ta yi,abaya ce dark brown color har ƙasa yasha stones ta ko ina se kuma wando jeans black color wanda za'a sa ta ciki,tsaki ta yi a yayinda take wurgi da rigar akan gado ta ce "Tabb dijam waye ze saka wannan ƙatuwar rigar lallai kam ai dole in nemi wata rigar da zansa da wandon nan,ita kadai take magana ta nufi hanyar barin dakin daga ita se towel a daure a kirjinta ga rabin fararen tula_tulanta awaje,dakin da ta gani kusa da inda ta sauka ta shiga ta tsaya daga bakin kofa,ta ce "abani riga t-shirt!"Parsa da ita kadai ne tayi saura a dakin ne,ta ɗago kai ta kalleta ta yi murmushi ta ce"okay bari in kawo miki"da sauri ta mike ta nufi dressing room din su ta dauko mata sabuwar riga acikin ledarta ta fito ta bata,karba Sabriyah ta yi a wajen ta saka ta dawo da towel din kugunta sannan ta bar bakin kofar ta koma nata masaukin.


Shiryawa ta yi tsab cikin riga da wandon ta zauna a dakin tana tunani ina zata samo Asmita,wani hanya ya kamata tabi ta samo Asmita, Rameesa ta shigo ta ce "hi yan mata!ance ki zo muci abinci." "nakoshi"cewar Sabriyah,barin dakin Rameesa ta yi bata sa'ke magana ba.




Kowa ya hallara a dinning table hatta LTG da major Marry duk suna zaune kowa ya fara cin abinci Rameesa ta dawo ta ce "Ammi wai ta ce ta koshi"gyada kai Ammi ta yi ta kalli fatime ta ce "ki shiryawa bakuwarmu abincinta,ki kai mata". "to Ammi" shiryawa Sabriyah abinci fatime ta yi,ta nufi upstairs.


Kallon Ammi anty amarya ta yi ta ce "Ammi yaushe akayi bakuwa!?, wacece haka!?"ta jerowa Ammi tambayoyi tana son jin amsarta,kafin Ammi ta yi magana Ammuh ta rigata cewa"wata karuwa ce Taj ya kawo"da mamaki anty amarya ta ce "karuwa kuma!?, kamarya karuwa!?"LTG de abincinsa kawai yake ci kamar be ji me suke faɗi ba.major Marry kuwa se kallon bakinsu takeyi yana magana amma bata iya gane ko da kalma daya da suke faɗa tunda ba Hausar take ji ba.


"Tajuddeen ne ya kawo ta duk da be faɗa mana dalilin da yasa ya kawo ta ba".
Ammi ta gayawa anty amarya jinjina kai ta yi taci gaba da cin abincinta.
Uncle Hameed ya ce"LTG meyasa ka daukota, kuma naji Ammuh dinku na cewa wai karuwa ce?".


Sipping din black tea din dake hannunsa ya yi ba tare da ya ɗago ba ya ce"bincike ne ya biyo ta kanta"daga haka be sa'ke ko da tari ba,su ma kuma basu sa'ke yunkurin sa'ke yi masa wata tambayar ba.
"Rameesa bakuwar na part din ku ne?" "Eh anty amarya tana can"Rameesa ta bata amsa tana kai soyayyen kwai bakinta.
Anty amarya ta ce"to mu gama,muje in ganta".










Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.




Comment,like and share 🖋️🖋️


🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




Page 18




*_ story & written_*

By




*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)


*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*




~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*








🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️



Page 18




zaune take a cikin dakin, fatime ta shigo hannunta da tray din abincim da ta shirya, harda mini flask din tea.
"Barka da safiya ga breakfast din ki" "yawwa", ficewa ta yi bayan ta ajiye mata.
Bude kulolun ta yi taga sinasir ne da miya yasha kayan hadi ga nama acikin kamar zasu yi magana,dayan kulan kuma farfesun kifi ne a ciki,daukan plate ta yi ta zuba ta fara ci.bayan ta gama,ta haɗa tea ganin arhan madara da milo yasa se da tea din nata ya koma kamar wani kunu tana sha ta rube ido,ji ta yi koshi har wuya sannan ta kwashe plate da cup din ta sa acikin tray. ɗaukar tray ta ajiye akan mirror ta dawo ta zauna.
Shigowa dakin anty amarya da Rameesa sukayi, ɗago kai Sabriyah ta yi suka haɗa ido,a tare sukaji zuciyoyinsu ya buga kamar an buga ganga.mikewe Sabriyah ta yi,har lokacin idonsu na cikin na juna,wani irin alaƙa ta jini ne yake fisgan anty amarya harta isowa ga Sabriyah da take kallonta kamar wata bakuwar halitta daga wata duniyar,sa hannu ta yi ta shafa fuskar Sabriyah da ta zuba mata manyan idanunta, lokaci daya anty amarya ta kusan burkicewa jikinta yana bata akwai wani babban alaƙar jini a tsakaninta da yarinyar amma ta rasa wani irin alaƙa ce wannan,kuma har wannan lokacin zuciyoyinsu be dena bugawar da yake yi da karfi ba.


Da kyar anty amarya ta tattara nutsuwarta waje guda,under her breath ta ce,"ya sunanki?"
Muryar Sabriyah na rawa ta amsa mata,"Sabriyah"
"Ke din yar wata gari ce!?kuma sannan meye abinda ya kawo ki gidan nan!?"
"Ni yar Lagos ce a afafa,kuma wani mugu ne, ya kawo ni gidan nan, ga shi an sace mini yar uwata'.
Iska anty amarya ta furzar daga bakinta me zafi ta ce"Allah ya bayyana ta,bari in je se anjuma".


Rameesa suman tsaye ta yi a wajen ganin yanda anty amarya da Sabriyah suke tsananin kama,amma se wanda ya zuba musu ido sosai ze fahimci hakan,duk da tunaninta be kawo mata kan cewar akwai wata alaƙa ba,amma ta yi matukar mamakin yanda suke kama fiye da tunanin me tunani.


Da sauri anty amarya ta juya ta fice daga dakin ta nufi part dinta,bin bayanta Rameesa ta yi.ba ta cimmata s hanya ba.daki anty amarya ta faɗa, zubewa akan gado ta yi, numfashinta na fita dakyar,jawo maganinta ta yi tasha,nan ne taji nutsuwa ya fara shigar ta, cikin tsantsan damuwa ta shiga magana"ƴata Asrah kina ina ne?,ganin wannan yarinyar da nayi de naji tamkar kece a gabana,jikina yana bani kina raye.ya Allah na rokeka da sunanka tsarkaka ka bayyana mini ƴata cikin aminci".kwararo addu'o i sosai ta shiga yi.


Jiki a sanyaye Sabriyah ta zauna a bakin gado tanajin wani irin kadaicin da tunda take bata taɓa jinsa ba, fashewa ta yi da kuka me cin rai da ta rasa dalilin wannan kukan da takeyi, haɗe kanta da guiwa ta yi tana kuka me sauti haɗe da shesheka, zuciyarta ce ta tambayeta.
"To kukan me kike yi haka?"
Ɗago kanta Sabriyah ta yi,a fili ta furta "Nima bansan kukan me nakeyi ba"
"To ai ba'a kuka dole seda dalili"
"Kila kewar Asmita ne ya dameni"


Ita kadai ta dinga magana da zuciyarta,in ta yi maganar ta gaji kuma seta saka kuka,nan take idanunta ya yi ja.
Durkusawa ta yi a ƙa san tiles din, ta zauna ta ci-gaba da kukan.
A wannan halin major Marry ta sameta, cikin hanzari ta iso wajan ta tsuguna tana tambayarta abinda ya sameta cikin harshen turanci.
"Beautiful girl!why are you crying like this!?,did someone said something bad to you!?".


Ko daya daga cikin kalmomin da major Marry ta faɗa Sabriyah bata gane ba, ɓalle ta bata amsa goge fuskarta ta yi,ba ta cewa major Marry komai ba,tunda de ba gane maganar juna zasu yi ba.


Ganin Sabriyah ta ƙi kulatane yasa ta ce"okay dear sorry for bothering you, LTG wants to talk to you! let's go".


Major Marry ta yi maganar tana ɗago Sabriyah.
Rike hannunta ta yi suka fice a part din.
Su parsa suna zaune a cikin falo,suka ga fitowar major Marry rike da hannun Sabriyah, Umaisha ce ta fara magana "Sabriyah in zo in raka ku ne!?".


Kallonta Sabriyah ta yi fuska ba yabo ba fallasa ta ce"ah ah ba se kinzo ba".


Dariya sukayi banda Zoya da ko kallonta batayi ba, hasalima haushi ta ji da taga yanda Umaisha suke janta da zolaya.
Parsa ne ta miƙe ta bisu a baya ta ce"nide Wallahi sena biku". kallonta kawai Sabriyah ta yi taga tana mata murmushi, itama murmushin ta mayar mata.
Sannan suka fice garden suka nufa tun daga nesa suka hango LTG zaune akan kujerun da suke cikin garden din yana sanye da army trouser se rigar t-shirt me budeden gaba, sojoji kuma na zagaye dashi ta ko ina,ga wasu maza guda biyu da aka musu daurin huhun goro da igiya zaune akasa.
Karasowa wajan sukayi major Marry ta jawa Sabriyah kujera ta zauna.


"Ya Taj ashe kana nan dazun muka ta neman ka bamu ganka ba"ta yi maganar tana shagwabe fuska.


Wayarsa yake dannawa cikin kwanciyar hankali tunda suka iso wajen be ko daga kai ba.


With his sexy voice ya ce"yeap am here do you need anything?"
Cikin jin dadi Parsa ta ce "yes!Muna son muje mu siya ice cream, chocolate and some yogurt".
Yanda take lissafin ne ya bawa major Marry dariya...ita de Sabriyah da ido kawai take binsu.


"Give her the ATM"cewar LTG,fito da ATM da suka kusa takwas major Marry ta yi ta mikawa Parsa guda daya.


Tsalle ta yi tana"thank you sweet bro".da gudu tabar garden din,dan taje ta bawa su Umaisha labari.yau ai tunda ATM ya shiga hannunsu se abinda hali ya yi.






Ajiye wayar hannunsa ya yi,ya ɗan kalli wa'yannan mazan da suke daure da igiya, "kun san wannan!?"ya faɗa yana nuna musu Sabriyah da ido,a galabaice daya daga cikinsu ya ce "ah ah Wallahi bamu santa ba".


Gyada kai ya yi "ke kin san su?"harara ta watsu musu ta ce "Ni ban san su ba."


"Shikenan!amma shi ogansu ai kin sanshi tunda har kukayi kwanaki goma a hotel,yanzu ina so ki sanar dani aina zan sameshi!?"tunda ta ji ya ambaci tayi kwanaki goma a Hotel da wani ta gane magana yake yi akan Fu'ad.


baƙi ta buɗe da niyar zata yi magana ta ji ana mata rada a kunne,kuma ba muryar kowa bane, fa ce na Fu'ad"my Sabriyah dan Allah karki nuna musu kan cewa kin san ni,nemana suke yi,ruwa a jallo,saboda su kasheni,babu abinda na musu kawai zalunci ne irin na soja.ki taimaki rayuwata dan Allah Sabriyah"
Shuru ne ya biyo baya hankalinta ya yi gaba wajen sauraran abinda Fu'ad yake ce mata,a dayan bangaren kuwa tana mamakin taya hakan ya kasance amma wannan ba shi bane damuwarta,abinda yafi damunta jin wai nemansa suke yi su kasheshi,hakan ne ya tayar mata da hankali, tambayar kanta takeyi,shin menene abinda Fu'ad ya musu,bawan Allah da Babu ruwansa,kamilin mutum me kyautatawa mutane.
Wannan dalilin ne yasa tasa aranta ko da kasheta zasu yi ba zasu taɓa jin wani abu dangane da Fu'ad a bakinta ba.


Ganin ta yi shuru ta faɗa duniyar tunani ne yasa LTG ya da ki table din gabansun da karfi,har seda ta firgita tana kokarin mikewa.


"Zauna"
Ya yi maganar fuskarsa kamar hadari.
"Inajinki"
Cikin inda_inda ta soma magana"ni ban san akan waye kake wa'yannan maganganun ba,ka kyaleni in je in nemo yar uwata'".ta karisa maganar idonta na ciki da hawaye.
LTG dama yasan za'a rina saboda shugaban kungiyar Italian Mafia ba karamin shu'umin mutum bane zeyi fiye da haka ma.yasan ko shekara daya zasu yi yana tambayarta game da shi bazata taɓa faɗa masa komai akan sa ba,kamar yadda shugaban Italian Mafia ya yi blackmailing din ta shima dole ne ya yi blackmailing dinta saboda ta wannan hanyar ne kawai ze samu ta yi magana, saboda shugaban Italian Mafia yana kokarin juya mata tunaninta ne da karfin sihirinsa..


Kallon major Marry ya yi ya mata alamar da ta komar da ita ciki.


"Okay"


marairace fuska Sabriyah ta yi "dan Allah ka taimakeni ka mayar dani inda ka dauko ni,sun sace mini yar uwata' akan wani abun da baya wajen ta yana wajena,sun saceta bansan a wani hali take ba".tana magana hawaye na zubowa daga idanunta.


maida kallonsa kanta yayi,jin abinda ta faɗa. yana me son gasgatar da hasashen da ya keyi game da abinda Sabriyah ta ke magana yana wajenta,fatan shi ɗaya shine Allah yasa wannan ma'adanar memory card din ne a wajenta.


"Akan me kike magana meye a wajen naki!?"ya faɗa yana tsare ta da mayun idanunsa,ka war da kanta gefe tayi saboda bazata iya kallon cikin kwayar idanunsa ba,ji ta keyi kamar akwai guba me zautar da mutum acikin idanun nasa.wannan dalilin yasa ko da yaushe take avoiding din haɗa ido dashi.


"Am......amm......dama wani Barrister Lameer ne ya bawa Asmita ma'adanar memory kan cewa ko ta wani hali mu tabbatar da mun miƙa wannan abun wajen hukuma,ita kuma ta bani.shine suka kashe Barrister Lameer din,suka biyo mu har gida aka sace Asmita".


Zuba mata ido kawai ya yi,yana sauraranta,lumshe kyawawan idonsa ya yi ganin ya samo abinda suke nema har gida,domin lokacin da suka jefo da Barrister Lameer kan titi yayi dede da i sowarsu wajan nan suka fara ɓarin wuta har suka samu suka kashe wasun su wasu kuma suka kama su,anan ne Barrister Lameer ya sanar dashi kan cewa ya bawa wasu yan mata ajiyar memory din.kiran ambulance sukayi aka dauki Barrister Lameer zuwa asibiti domin a bashi taimakon gaggawa.


Ashe wa'yanda yake nema tana tare dasu.


Idonsa a lumshe kamar me bacci ya furta, "bani memory card din!"
Mikewa Sabriyah ta yi, "ban yarda dakai ba,babu dalilin da zesa in baka wannan memory ko da kuwa kasheni zakayi"tana gama maganar ta fara tafiya,zata bar garden din.cizan libs din sa na kasa ya yi,ya ce "in dan kika bani,nikuma na yi miki alkawarin nemo miki yar uwarki a duk duniyar da take".


Cak ta dakata da tafiyar da takeyi jin ya ambaci ze nemo mata Asmita,da sauri ta juyo ta dawo inda yake zaune ta ce "ni kuma muddin ka nemo mini ita zan baka wannan memory card din".tana ga fadin hakan ta sa kanta ta wuce cikin gidan,ta barsa zaune a wajen murmushi ya yi.
kawai yana binta ne cikin ruwan sanyi ta ba shi,amma in ya gadama a yanzu ze ƙarbi memory a wajanta,domin duk wani motsin mutanen gidan nan yana sane dashi,amma ze barta ya ga iya gudun ruwanta.
"Find the other girl,and kill this bastards"abinda ya ce kenan sannan ya mike,a tare sojojin dake wajen suka sara mishi.barin garden din ya yi wasu daga cikin sojojin suka bi bayan sa.




Kallon wani soja major Marry ta yi, ta ce "Khalifa! hand me the gun"miko mata bindiga ya yi,.nan take tsoro ya dira akan fuskokin wa'yanda za'a kashen suka fara neman afuwa.


Ko ajikinta ta seta kansu ta ɗa na kunamar bindigar sannan ta sake shi akan goshin na farko nan take ya fadi awajen matacce,haka dayan ma ta harbeshi a goshi.


Bindigar da ta yi amfani dashi,bayi da ƙara hakan yasa mutanen gidan basu ji kar'ar ba, ficewa ta yi itama taname basu umarnin su kwashe gawan nasu a wajen.


Birkita dakin ta yi kamar wata mahaukaciya tana neman breziyar ta,amma bata gani ba hakan ya daga mata hankali sosai,wanda yasa ta fara zargin ko wani ya shigo ya dauke ne musamman inta tuna da yanda sukayi da LTG,leƙawa kasan gado ta yi nan ta gansa yashe awajen. ashe da ta fito daga wanka ne ta yi wurgi dashi kan gado se ya faɗa bayan gadon.


Da hanzari ta shige kasar gadon kamar wata bera,daukowa ta yi ya,ta na kokarin fitowa ta ji muryoyinsu a dakin suna "to ina kuma taje?"


Fitowa ta yi hannunta riƙe da breziyar nata ta gansu dan tsuke fuska ta yi,bata ce musu komai ba.


Kallonta sukayi suna mamakin ita kuma me yasa ta shiga ƙasan gado.Rameesa ta ce"Sabriyah me kikeyi a kasan gado kuma".
Ajiyar zuciya ta yi "breziya ta na dauko" "okay!dama zamuje shan ice cream ne mukace bari muzo muce ki shirya muje".


Yatsina fuska ta yi ta ce"ku je kawai bazan samu zuwa ba".


"Sabriyah kin ka sa sakin jikin ki damu,kingan mu nan ko kadan bamu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login