Showing 18001 words to 21000 words out of 134612 words

Chapter 7 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8689

ko babban mutum bazai samu ba.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta jiyarci danejin a karo na ba'a adadi,ganin irin halittar da ƴar tata take ɗauke dashi,wanda tayi amanna tunda take bata taba ganin irin ta ba a rayuwarta.
Duk yanayin buɗe idon kaɗan kaɗan take irin na jarirai,amma hakan bazai hana mutum gano abinda yake tattare da yarinyar ba.
Runtse idonta tayi na wasu mintina kafin tasake sauƙesu akan ƴar,wacce zuwa yanzu ta rufe idanuwan da alama tayi bacci a bakin nonon. Cireta tayi a hankali,ta sake lullubeta a cikin zanin da take,kafin ta maidata wajen da take kwance ɗazu..
Tashi tayi tafara gyara ɗakin tareda ɗauko kayan dazata saka,har sannan jikinta a sanyaye yake na abinda tagani,a jima kaɗan ta kalli wajen da yarinyar take,a jima kaɗan ma ta kalleta,abin ya tsaya mata a rai takasa fitarwa.
Tana cikin hakanne malm Ahmadu ya shigo ɗakin kaman an jehoshi,labarin sauƙarta lafiya ya risƙeshi a waje.
Kai tsaye wajenda take ya nufa tareda ɗaukota ya rungume a jikinsa da rawar jiki.
Sumbatarta yafara ta ko'ina kafin yafara yimata ƙiran sallah a kunne.
Itadai Daneji tana tsaye da tsintsiya a hannunta bata ce komai har yagama rawar jikin.
Ɗagowa yayi ya kalleta da murmushi akan fuskarsa yace.
"Mashaallah nayi mata huɗuba,sannan kuma nasaka mata sunnan mahaifiyata MARYAMAH"
"Allah yaraya ta bisa imani,sannan kuma Allah yasa halin mai sunanta ya bita"
"Ameen ya Allah,kema Allah yayi miki albarka yabaki lafiyar shayarwa"
"Ameen kasake yiwa Addah laari godiya da ƙoƙarinta a gareni"
"Shikenan"
Kafin dare yayi mutane ƴan uwa da abokan arziƙi suna ta zuwa ganin Ƙaruwar haihuwar da akayiwa malam Ahmadu,wannan su shigo wannan su fita.
Har ƴan uwan su inna laari ma saida sukazo daga ƙyauyensu,Amma babu wanda yazo akace daga bangaren mai jego,duk da kowa yasan ƴan uwanta basanan amma abin yayi mata ciwo sosai,rashin danginka a kusada dakai abune mai ciwo matuƙa.
Da daddare saida Daneji tasha kukanta ta ƙoshi na rashin danginta,babu wanda zai zauna a gunta daga bangaren yan uwanta,sai dole yadikon su malam akan ce wata tsohuwa tazo yi mata zama.
Gashi yanzu tafara tara dangi itama nata na kanta,shin wa zata nunawa Ƴar ta a matsayin danginta zuwa gaba,ko kuma haka zata tashi batasan kowa nata ba,wanda itama tanada yaƙinin nangaba zata iya mantasu idan lokaci ya tafi.
Har akayi kwana uku da haihuwa babu wanda yagane cewar idon Jinjirar bana mutane bane,sai iya daneji ce kawai tasani,har yanzu kuwa babu wanda ta faɗawa,kullum fargabarta shine idan mutane sun gano mai zasuce gameda hakan.
Abinda yafi bawa Daneji mamaki shine idan har ita datake bata nono tagane ƙalar ƙwayar idanunta inaga mai wanka kumafah inna laari,tana da tabbacin Inna laari taga abinda tagani gameda yarinyar,amma ko kaɗan bata nuna tagani ba,ko kuma bata gani bakai?
Ita kaɗai take tambayar kanta take bata amsa a ranta,abinda yashare mata tantama shine,lokacin da jinjirar ta shaƙi sabulu ta buɗe idonta kuma akan idon inna laari,amma batayi mamaki ba ko kuma nuna alamar zata sanar da wani abinda tagani.
Duk abinda take bata kulada Daneji tana kallon sanda taga idon yarinyar ba,hakannne yakara tabbatar mata ba lokacinne kallonta na farko ba a gameda lamarin,tasani tunda farko,boyewa kawai takeyi,to miyasa?.
"Addah Laari shin bakiga wani abu a tattare da yarinyar nan ba wanda ba irin na mutane ba?"
"Nagani mana,ƙwayar idonta ba kalar ta mutane bace,saidai babu yadda Allah baya halittar sa idan yaso,shi yayi nufin yaganta hakan,dan haka babu mai ja da ƙudurarsa"
"Hmmm hakane kam,nayi mamakine da kika gani amma bakice komai ba"
"Uhm mai zance Daneji,saina bi duniya nayi ta yaɗawa ƴar mijina an haifeta da wani irin ido?ribar mai zanci akan hakan,innayi hakan nima ai kaina na tozarta ba kowa ba,sannan ya mutane zasu kalleni kenan,idan Allah yayi kwananta ta fita kowa ma zai gani,fatana shine Allah yasa mutane su gane halittar Allah ce itama kamar su,karsu nuna ƙyamatarsu gareta"
Maganar da inna laari tayi baƙaramin faranta ran Daneji tayi ba,sai ta nemi kashi hamsin na fargabar halin da yar tata zata shiga ta rasa,yazamana itama tasaka a ranta cewar Allah ne mai halitta,kuma shi yayi nufin ya ganta a haka ba kowa ba.
Ranar suna gadan gadan aka hau abinci da yanke yanken kaji,bayan tunkiyar da aka yanka na aƙiƙa.
Mutane an ciki gida maƙil,a lokacinnne kowa yashaida yarinya taci suna Maryam,mahaifiyar malam Ahmadu.
Bakinnan kaman gonar auduga,kowa rana yasan malm Ahmadu yana cikin farin cikin marar misaltuwa.
Duk abinnan da ake Daneji kaffah kaffah take da Maryam,wanda tafara ƙiranta da BOMBEE,saboda kar mutane sugani su tsegunta,ana tsaka da taro kowa yaɗauka a ƙirƙiri abinyi na gulma.
Dan haka sai itada inna laari suka haɗa baki akan yarinyar bata lafiya,kowa idan yazo saidai ya kalleta daga nesa,itama data rufa musu asiri wuni tayi tana bacci.
Bayan anyi taro an watsen makwanta su larai suka tsayah aka gyara gidan tareda su,kafin bayan magriba sukayi mmusi sallama suka nufi nasu gidan.
Dare yayi gari yafara shuru Bombee tace batasan kwanciya ba,dawa Allah ya haɗata idan bada kuka ba.
Tun tanayi Daneji na rarrashinta har abu yafara fin ƙarfinta,dan shiɗewa take muryarta har dunshewa take dan Kuka.
Shikansa malm Ahmadu take ɗakin inna laari yayi sawu yakai sau uku,kl yaushe idan yazo sai yace tabata tasha,tun tana ce masa taƙi karba har ta rabu dashi.
Ruwa ta ɗebo a kofi tana tofi tana shafe mata jikinta,tunda ta kula babu zazzabi a jikinta,sannan cikinta bai kumbura ba bareta ce ciwo yake mata.
Haka tayi ta shafe ta da ruwan addu'o'i,sai kuma tayi sa'a tafara sauƙe ajiyar zuciya lokaci lokaci,can wajen asuba tayi ƙitt kaman an kashe rediyo.
Ida tai Daneji yanda taga rana haka taga dare,ga gajiyar bikin suna,sa'arta ɗaya ma Ba sallah zatayi ba ko girki,dan haka da rana ta samu damar rama baccin.
Wasa wasa an kusa shafe wata ɗaya dayin suna,kullum babu fashi sai Bombee ta kwana tana ihu,idan asuba kuma tayi tai shuru kaman ruwa ya ɗauke.Tun abun suna ɗaukarsa kukan jinjirai har abun yafara sakasu dasa ayar tambaya. Bangaren Daneji kam harta fara mantawa da wani baccin dare yanzu.
Bankaɗa labulen ɗakin tayi zata shiga ta fito daga wanka,turuss tayi a bakin ƙofar ganin malm Ahmadu rike da Bombee a hannunsa yana kallon idonta,ita ma kallonsa take da shuɗayen idanuwan nata na yara,kana kallon kan fuskarsa zaka hango tsagwaron mamaki da kuma irin mutum yaga abu a karon farko.
Ɗago fuskarsa yayi ya sauketa akan Daneji wacce ta shigo daƙin jikinta yana ɗigar da ruwan wanka.
Saurin sunkuyar da kanta tayi bata bari sun haɗa ido ba,dan babu alamar wasa a idanuwannasa,tambaya ya jeho mata kai tsaye.
"Fatima menene wannan?"
"Idanuwanta ne"
"Dama haka suke tun farko,kokuma yanzu sukayi?"
"Haka take dasu aka haifeta"
"Meyasa kuma ina matsayin mahaifinta baki taba faɗaminba,kenan da bangani ba shikenan harsai ta girma ta fita naji a bakin mutane kome,idan kuma hakan ciwone kika barta dashi ya wuce gaban kwatance fah,yakike ganin za'ayi,kullum ina faɗamiki banason wannan shuru shurunnki,zai iya kaiki ga aikata danasani"
"Kayi haƙuri banason ka shiga damuwane idan ka gani,sannan bansan ta yanda zan sanar dakai ba,na faɗawa addah laari ma tafaɗa maka tace baruwanta"
"Eh baruwanta mana,ke kinga laifinta a ciki,tazo ta faɗa ace dama Allah allah take ya faru ta faɗa? Maza saka kayanki mutafi wajen maganin gargajiya da kuma na nasara,wannan abin ai bana zama bane,waya sani ma ko bata gani ke baki sani ba,inaga ma yanada alaƙa da kukanta da daddare,ko ciwo ma suke mata"
"Tana gani fah dasu"
"Taya kika san tana ganin"
"Idan nasaka mata haske ina tafiya dashi tana bin hasken"
"Ni ban yarda da wannan zancen ba,maza shirya mu tafi asibiti a ji shin mai yake damunta"








🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are


















____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]










*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________
















Page 🖤13🖤


Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci.
Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa.
Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa.
Yana tafiyah yana waiwayen ƴar tasa.
"Ki kulada ita fah kar wani abu yasameta kafin mu isa.......yi shuru uwata kinji,bari muje a baki magani su daina yimiki ciwo,irin wannan ido haka akan wane daliline bazayyi ciwo ba,hmmm Allah dai ya kyauta."
Magana yake tayi shi kaɗai,itadai Daneji bata cemasa ci kanka ba,sai rarrashin ƴarta da take tayi,har suka isa asibitin wanda bashida nisa da anguwarsu.
Kafe mashin ɗin yayi,ya kar'bi ƴar suka shiga asibitin..
Nan ma dayake litinnin ne layi har bakin asibitin,kasancewar kuma yahaɗa yanayi da damina,jinyace jinyace sunyi yawa.
Wani bakin banci yasamu a gefe ya nunawa Daneji ta zauna,kafin yabada yarinyar ta riƙe,shikuma yashiga ciki domin yayiwa likitan magana akan lalurar tasu.
Feeder Daneji ta fitar tana bawa Bombee ruwa,wacce taga kaman alamun fatar bakinta ya bushe babu ruwa. Dadai lokacin ne kuma wata mata itama da goyo tazo ta zauna zata since yaron ta tabashi abinci..
Daneji bata kulada ita ba sai gani tayi ta miƙe dasauri,hannunta yana rawa ta toshe bakinta.
Ja da bayan da takene tana nuna inda Daneji take,yasa kowa hankalinsa yadawo wajen da sauri.
Bakinta yana rawa tafara cewa.
"Wayyo ba mutum bace,wani abu nagani a radu a hannun matar nan"
Kowa maida idonsa yayi kan Daneji,wacce tasake rungume ƴar ta a jikinta,tareda sunkuyar dakai,ji tayi kaman ƙasa ta buɗe ta nutse ciki,mai aka ɗauki ƴar tane,bayan zuwanta duniya su kaɗaine suka san lalurinta,yau ɗaya wata tagani harta tozartasu. Shin itama ba uwa bace da ɗa a hannunta,bata kunyar yiwa wata uwar haka a matsayinta na uwa?
Suna cikin hakanne ana ta hayaniya malm Ahmadu ya dawo wajen,inda ya tarar kowa yana nuna Daneji wacce take zaune kaman mujiya ta rungume Bombee.
Bankaɗe mutane yayi ya isa gareta,tareda tambayar ta mai yake faruwa.
Zayyana masa abinda yafaru tayi cikin ƙaramar muryah mai cikeda damuwa.
Aikuwa cikin tunzura ya juya ya kalli matar,wacce take tsaye tana zayyana yanda taga idon Bombee.
"Uhm malama na tambayeki mana,shin wannan da kike riƙeda shi ɗanki ne?"
"Eh ɗanane mana"
"Idan ace misali lokacin dayazo duniya sai kika kulada cewar gashin kansa korene,sai kike saka masa hula a koyaushe idan zaku fita waje,to ƙwatsam watarana sai wata mata itama mai ɗa,ta fara nuna ɗanki a bainar jama'a tana cewa.....wannan ɗan mayene ba mutum bane,dukkan mutane sai suka yi caaa sai sun ga ya ɗanki yake,wasu ma har zakinki suke.
Ita kuma tana tsaye a gefe tana sake bayyana yanda ɗanki ba mutum bane,shin ya zakiji a ranki a lokaci?"
"Meyasa kayimin wannan misalin,amma dai amsa a bayyane take,yanda nake son ɗana zanji tamkar ta daba min mashi a cikin zuciya,sannan zanji baƙin ciki a matsayinta na uwa bata gani ba take tozarta nawa ɗan"
"Alhamdulillah kinbawa kanki amsa,to waccer matar da kike tozarta ƴar ta fah,ita yazataji a ranta?.
Ita ɗin matata ce,yarinyar da kike ƙira kuma mayyace,ƴata ce ita ɗin,haka aka haifeta watan baya da kalar nata halittar idon,shin akwai mayen da ake ganeshi ta halittar idone,dan kawai ƙwayar idonta shuɗine sai aka ce itaba halittar Allah bace?.
Ita kin muzanta tata yarinyar,kuma sannnan ko kunya bakyaji kina tsaye kina ƙara maida bayanin,a matsayinki na uwa kuma tirrrr da halin wasu matan"
Malam Ahmadu yana gama faɗamata hakan ya nufi inda Daneji take sunkuye tana kuka.
Yayinda ita kuma kowa idonsa yakoma kanta,itama ta sunkuyar da nata kan cikeda kunya da nadamar abinda ta aikata.
A hanya suna tafiya malm Ahmadu yasamu waje ya faka mashin ɗin.
Itama Daneji ganin hakan yasa ta saƙƙo daga kan mashin ɗin tana kallonsa.
"Wai yaushe zaki bar wannan kukan iyee,shin kukanne magani komai,tun yanzu ma kina kuka inaga idan ta girma tafara shiga mutane fah,idan ta shigo gida an ƙirata da mayyah kuka zakiyi kaman yanzu?"
Jijjiga kai tayi alamar ahaha,sai can kuma kaman bazatayi magana ba tace.
"Mai likitan yace toh,sannan meyasa muka taho"
"Yace zuwa yanzu bazayyiyu muganshi ba,sannan ni daga ganin abinda ya faru nafara tunanin inaga abin bana asibiti bane,saboda babu wata jinya da yaro ke zuwa da irin wannan ido,nafi kyautata tunanin shafen aljanu ne,dan haka gidan Malam ALWASU zamu je,ya duba yaga koda maganin dazai iya bamu."
"To shikenan hakan ma yayi,nima dama bana tunanin abin asibitine wannan,bata kuka fah sai dare yayi,sannnan ............."
"Sannan me inaso ki fadamun mai kika gani bayan nan"
"Idan .....idan na haska fitila ko zan ɗauketa.....sainaga idon yanayin haske a cikin duhu,kaman idon kuliya ko kura idan an haska da daddare"
Cikin kiɗima mlm Ahmadu yazaro ido,jin abinda Daneji ta faɗa,tohhhh ikon Allah.
"Maza maza hau kan mashin mu tafi asibiti,wannan ba abune daza'a zauna ba,tabbas dagaji aikin aljanu ne"
Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso ƙofar gidan mlm Alwasu,tundaga bakin ƙofar gidan mutum yana gani yasan gidan mutanene rabi bokaye rabi kuma suna fakewa da harkar malantaka.
Almajiraine a ƙofar gidan birjik sunata karatu,sai ƙofar gidan a tsakiya,daga can kefe kuma wani ɗan zaurene na kasa,an lanƙaya su jajayen ƙyalle a jiki da baki,kowanne anyi masa rubutun larabci,duk maitarka baka isa faɗin mai aka rubuta ba.
Wani yaro suka tasa daga cikin masu karatun,tareda tambayarsa inda Mlm Alwasu yake.
"Kai ina mlm yake?"
"Yana cikin zaurensa suna ganawa da hajiya,zaku iya jira ko kuma ku dawo idan an jima"
"Ahah bari mu jirashi ba matsala,ku cigaba da karatu koh"
Suna nan tsaye wacce aka ƙirada hajiyan tafito daga cikin zauren. Tabbas Hajiya kam,dan itace mai neman kujerar chairman na Sardauna LGA a lokacin.
Ƙarisawa su mlm Ahmadu sukayi suma daga ciki,domin kaiwa tasu buƙatar.
Shiga sukayi tareda zama akan buzun dayake gabansa.
Har kusan tsawon mintina biyar da zaman su amma bai ce musu komai ba,yana zaune a inda yake ya rufe ido,hannunsa kuma ɗauke da wani zankaɗeɗen carbi yana ta ja.
Abinne yabasu mamaki,wanann ya kalli wanann wannan yakalli wannan.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana,dan yafara ƙosawa da zaman,saidai tun kafin ya buɗe baki mlm Alwasu ya katseshi ta hanyar ɗaga masa hannu.
"Hmm karkace komai,barina gama da wannan tukunna"
Saida yagama ɗin kafin ya buɗe idonsa akan su.
"Inajinku yanzu mai yake tafe daku,na raka Hajiya ne ta addu'a har saida tabar yankinnan,shiyasa kuka ganni nayi shuru,amma yanzu ina jinku"
"Allah gafarta mlm dama lalurine yasamemu na aljanu,yarinya ce aka haifeta,amma kuma sai tazo da wani irin ido kaman na karashiya,sannan innarta gata tacemin bayan launin idon,har haske yake irinna kuraye idan aka haska da fitila da daddare,kuma kwana take bata bacci kullum.
Kaga kuwa wannan ba aikin kowa bane sai aljanu,shiyasa mukazo koda taimakon dazaka taimakemu dashi"
Ƙarisa magana mlm Ahmadu yayi ta sigar roƙo a wajen mlm Alwasun,wanda yayi shuru yana jin bayani.
"Miƙomin yarinyar naga mai yake damunta,tabbas daga bayaninka kam abin yayi kama dana aljanu,saidai shikansa shafen aljanu kala kala ne,bazamu gane wanne daga haka ba."
A jiye yarinyar yayi akan cinyarsa,tareda dafa kanta sannan ya rufe idonsa.
Ya daɗe a haka can ya buɗe ido da ƙarfi akan su mlm Ahmadu,hannunsa rawa yakeyi da kuma bakinsa,sai can kuma ya tsime kaman bashi ba.
"Tabbb tabbas abinda kuke tunani hakane,yarinyar tana ɗauke da baƙaƙen aljanu masu haɗarin gaske,saidai ba a jikinta suke ba,ajiya sukayi a cikin idanuwanta,shiyasa suka sanja kala,kuma take gani tamkar irin na aljanun"
Bazai yiyu mu iya cire ajiyar ba batareda mun tsire idon ba,saidai amma zamu iya 'boye ajiyar a jikinta,ta yanda bazasu tuno da ajiyar ba har abada,ta hakane zasu manta da lamarin su barta tayi rayuwarta.
Saidai da sharaɗin karku dinga barta kullum cikin fushi,sannan kada ku barta takai farmaki akan komai,daga lokacin da tayi ƙoƙarin buɗe wanann ajiyar da kanta,to fah kuma babu komawa da baya,dole saidai ku sallama ta,domin zata kasance tamkar mabuɗar bala'i a gareku.
Sai ku zaba shin ayi aiki ko kuma kar ayi?"
Tsuru tsuru su mlm Ahmadu sukayi,suna jin bayanin da mlm Alwasu ya basu,dama su tun wuri sunyi tunanin aljanu ne gareta,biri kuwa yayi kamada mutum,yau ya zasuyi a wannan duniya ta maliki yaumiddini.
"Mlm a boye ajiyar dayake jikinnata,zamu yi ƙoƙarin rainonta akan kartayi fushi kokuma shiga damuwa,bazan juri ganin an ciremata ido ba gaskiya,tunda dai kace bazasu san inda take ba to inaga hakan ma yayi"
Daneji ce tafaɗa tana matse guntun hawayen dayake idonta.
"To shikenan tunda kun zabi hakan za'ayi aikin daya tace,akwai maganin dazan baku yanzu a dunga zubawa a ruwan wankanta,sannan kuma dana turare wanda za'a dunga yimata da daddare.
Bayan sati ɗaya kuma zaku dawo ayi yanka ayi sadaka,sannan ayi anihin aikin daza'a boye ajiyar jikinnata"
"Mungode mungode Mlm Allah yasaka da Alkhairi,yanzu kenan nawane kuɗin abin sadakar"
"Abin sadaka sai nan da kwana bakwai idan nagama aikin,yanzu za'a fara shirye shiryen haɗa duk abinda ya dace"
"To shikenan mlm muzamu tafi,sannan za'ayi yadda kace,sai nan da zuwa ranar bakwai ɗin"
Daneji ce ta karbi yarinyar wacce take bacci abinta daga hannunta mlm Alwasu suka tafi"
Sai bayan sun fita da kaman minti talatin mlm Alwasu yasaki ajiyar zuciya.
"Tabb yau wannan yarinya mainene takamai mai abinda yake damunta,ni kaina duk iya ƙoƙarina duhu kawai nake gani,amma zanyi iya ƙoƙarina dai daga nan zuwa satin a gani"




🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are


















____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]












*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________














Page 🖤14🖤







A haka suka koma gida cikeda ta'ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu.
Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za'ayi mata.
Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta.
Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har an shafe watanni biyar,tun su Danejo na boye Bombee idan sukaji sallama,har yazamo mutane sun gane abinda yake tattare da ido.
Dama ance idan rana tariga ta fito,tafin hannu bai isa rufeta ba.
Kuskus a cikin jama'a har zance yabaza gari ko ina ya ɗauka ƴar gidan mlm Ahmadu mayya ce,tun Danejo batajin mai yake faruwa har zance ya dawo kunnenta.
Inna laari tana sayar da kayan miyah,wanima da gangan yake tsallake anguwarsu yazo gidan su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login