Showing 66001 words to 69000 words out of 134612 words
a hanya,koma wanne hukunci na yanke zakiji,amma mu baridai sai yasake zuwa kuma yazo da zancen tukunna"
"Uhm uhm Jaleelah karfah ki cuci ɗan mutane,maza nawa kika ƙi amincewa dasu"
"Ehh to saina amince da kowa koh,kekam ki zuba ido ki gani mana"
(Toh idan ana ustaxiyah da smiling ga ustaziyah da loving).
Sauƙe wayar tayi tareda kallon window na tsawon lokaci.
"Kai Madeenah koh,shine wato taje tasau baki tafaɗamata komai,gashi ban shirya sanarda hajiyah rabi abinda na shirya ba sam,yanzu babu yadda zatayi illah ta tunkareta suyi maganar kawai"
Tsakanin wayar tasu ba'a dadeba taji tsayuwar motarsu a bakin sashenta..labulen ɗakin ta ɗaga tana kallon su,daidai lokacin da Hajiya rabi ta fito tareda matsawa inda Jawaheer take tsaye,sai wani narai narai take da fuska. Kama hannunta Hajiya rabi tayi tana yimata sannu suka shigo.
Maida labulen tayi ta mayar,ita kanta tasan abinda haniya rabi takeyiwa yar ta baya dacewa,sannan batayi kama da matar dazakayi fatan da haifamaka jika ba.
Saidai muradinta shi ya dushe daka waɗannan kurakan tunda da farko. Kasantuwar alƙawarin da hajiya rabi tayi mata tun lokacin da aka haifin Jawaheer,kan cewar idan har Jabeer ya aureta,toh itakuma zata haɗe companynta na Royal fabric da Jaan Company su zama abu guda,wannan nasara da Hajiya zeenah tagano shiya rufe mata ido tasaka ganin duk wani abu da hajiya rabi zata aikata.
Yayinda itama a bangare ɗaya akwai dalilinta nayin hakan,tayi bincike da gano cewar Lubnah bata haihuwa,idan ta aurawa Jabeer ƴarta ta haɗe compnynsu,tasan sai bunƙasa fiyeda yanzu,kuma in ƴar ta haihu a gidan,tunda sune dalilin bunƙasar dole jikokinta ne zasu kulada komai a companyn,shiyasa lokacin da hafsa ta mutu itada yaronta har cikin ranta taji daɗin hakan,nunawa ne kawai batayi ba a fili.
Sallama tayi a falon farko,Hajiya zeenah na jinta tafita taryota,tun a bakin ƙofar bayan gaisuwa suka fara maganar datayi maƙasudin haɗuwar su a wajen.
"Mainnkeji haka ni Hajiya rabi daga wajenki,kaddai tun ba'aje ko inba shikenan kin ruguza abinda muka daɗe muna shiryawa a tsakanin yarannan?"
"Kibari kuje ciki,koma mai ake ciki duk zakiji,ba yanda kike zato bane Hajiya rabi"
Zama sukayi Hajiya zeenah ta bata labarin abinda ya faru tunda ga farko har ƙarshe,harma da matsayin auren da komai da komai.
Ajiyar zuciya Hajiya rabi ta sauƙe tareda faɗin
"Yawwa yanzu naji batu,amma cewarta na shekara ɗaya zata aureshi bai tasoba,wata shidan dakikace shi za'ai,ta gaggauta fitar mana da matarsa itama kuma tafita,tunma kafin ayi aurensu da Jawaheer ɗin,tunda itama nanda wata shida zatayi graduate"
"Ehh to yanda kika ce,amma bakya ganin idan aka faɗamata bazatayi shekara ba kada ta fasayin aikin,dan nikaɗai nasan wahalar dana sha kafin ta amince,yarinyar batada sauƙi ko kaɗan fah,bakiji fah labarin yanda suke da iyayenta bane"
"Kai rashin daɗina dake tsoro wani lokacin,kinason yin abu wani lokacin kina tsoro,ninasan zaman dakene yasa ma har kika iya kawota. Yanzu dai ki bari basai kin kawota ba,saidai kiyi ƙoƙarin faɗamata a dabara cewar tafara miki maganin kishiyarta da wuri,idan muka samu tagama da ita ko baikai wata shidan ba sai muce aikinta yaƙare kenan"
"Ehh to Hajiya rabi kin kawo shawara,kai tun safe kaina yake kulle,sai yanzu yafara suncewa,bari zan ƙirashi da daddare nayi masa bayanin matsayin auren danayi masa,dan baisan da zance ba tukunna,itama kuma zan faɗamata aikin da nakeso tafara min.
Amma bayan ni dake dakuma masu aikina amintattu babu wanda yasan da matsayin auren,kinaga mu sanar dashi domin karma yakai hankalin sa garets?"
"Ahhh haba haba Hajiya zeenah yaushe zaki fara wannna aikin,idan kuma matarsa ta tambayeshi matsayinta fah,munfiso kada kowa yasan yarinyar mai tafiyace wani lokacin,tahaka ne kawai zamu samu Lubnah taɗau zafi da itah sosai.
Amma idan tasan tafiya zatayi dariyama zatayi mana,kibar zancen iya mu sai mutanenki da mutanen,sannan ki shaida mata bakyaso kowa yasan matsayinta a gidannan,ta hakanne zamu samu komai ya tafi yadda muka tsara"
Shawarwarinsu suka cigaba dayi,duk akan yanayin yanda abubuwan zasu tafi musu ne.
A bangaren Jawaheer kuwa da suka barta a falo,maimaikon ta yi sashen su Maleekah,sai ta nufi lambun gidan,wanda yake a gefen new side na Jabeer.
Bata ɗauki mota ba takawa tayi a kafa tana kalle kalle har ta iso wajen sashen.
Har zata shige cikin lambun sai kuma tagano wulagawar mutum ta windown kitchen ɗin side din dake kusada da itah.
Mamaki abin yabata,dan duk zuwan ta gidan tasan ba mutum a bangaren,takawa take a hankali ta nufi sashen domin ganin waye a ciki.
Ƙwararrawar bakin ƙofar ta danna,kaman da minti ɗayah taji an buɗe bakin ƙofar.
Hilyaan ce ta buɗe mata ƙofar tana yi mata kallon mamaki kaman yanda itama takeyi mata,dan bata ganta a cikin yaran gidan ba,sannan a binciken da sukayi babu mai irin fuskarta.
Cikin ɗaure kai Hilyaan ta tambayeta.
"Shin......kozan iya sanin wacece ke,sannan kuma wa kike nema?"
"Sister ke zan tambaya wacece ke,yaushe kika shiga nan wajen,domin da babu kowa a ciki"
"Ikon Allah don da babu kowa a ciki sai akan ce yanzu za'a rasa wasu a ciki,matar wajence a ciki mana,dama ba domin a zauna akayi shi ba,to miyasa zai cigaba da zama haka bayan mai wajen tazo"
Daga yanda Hilyaan ta bawa Jawaheer amsa,lokaci ɗaya tagano wato itace amaryar da aka kawo kenan,wani kallon kanne ido Jawaheer tayi mata mai cikeda raini kana ta ɗora da cewar.
"Ko kece amaryar danaji labari ankawo gidan,to indan kinzo gidannanne kinga an baki nan side din kike wannan ƙafafar,da sannu zaki tattara bijenki ki bar gidannan,domin akan shanyar wata kika ɗora taki,ke in taƙaice miki ba iya shanyar ba,shikansa filin na wani ne.
Ɗan murmushi Hilyaan tayi,dan sai yanzu ta tuno akwai hoton ta a wanda aka turo musu,itace Jawaheer wacce za'a haɗasu aure da Jabeer.
"Kinga ki tattare kayanki ki cigaba da riƙewa,domin basu tsinke a gindin kaba ba,amma idan kina ganin zasu miki wahalar rikewa,to ga can kabar a ciki jeki kwance mata su"
Hilyaan tana karisa faɗin haka ta shige ciki batareda ta rufe ƙofar ba,saboda Jawaheer zatayi ra'ayin shigowa,aikuwa yanda tayi tunani ta shigo ɗin.
Bombee na zaune tana ta plan ɗin yanda aikin dazata gabatar a garin zai kasance.
Rigace a jikinta t-shirt pink,sai blue rabin wando itah gwiwa,santala santalan ƙwanjinta suna waje,wanda suka sha gyara da kuma hutu.
Headphone ne a kunnen,wanda ta ɗorashi akan gashinta da ko parkin batayi masa yana kafaɗarta,kana ganinta bazakace ba mutanen yamma bace,saidai gashinta ne da girarta su baƙaƙene ba ja irinnasu ba.
Gabaɗaya duk abinda Hilyaan take da Jawaheer batasani ba sam. Saidai Hilyaan ta ɗauki wayarta ta kashe abinda take ji tukunna. Ɗagowa tayi tambayarta dalilin kashewar,a nanne idonta ya sauƙa kan Jawaheer wanda itama take kallonta da ido a zare,da Alama idonta ne yasakata yin hakan,itama Bombee ta kulada hakan,saidai abube daya zamema jiki ai.
Wani kumbure kumbure ta fara da zare ido tana ƙarewa wajen kallo.Kana ganin fuskarta kaga jinin tsiwa da rashin kwaba.
Tsayawa sukayi suna kallonta batareda sunce komai ba,itama ganin basu tanka mata ba kaman yanda tayi zato yasata zama akan kujerar dake kusada ita.
Kallon Bombee tayi cikeda raini tace.
"Ohhh kece ma'aikaciyar da aka kawo tayimin aikin waccar matar?"
(Tana cikin tafiyah zuwa wajen hajiya rabi tayi mata text ta shaida mata kan cewar ta kwantar da hankalin ta,ba an kawo Bombee bane domin Jabeer yana sonta,sai dan takori Lubnah itakuma ta aureta,amma basu faɗamata auren yarjejenya bane)
Kallon mai kike nufi Bombee tayi mata kafin taja ajiyar zuciya"
"Inna fahimci mai kike kinaso ne kice,kece amaryar masoyina,wacce aka kawo tafitar da tsohuwar matarsa,wacce ta takuramasa nikuma matsoraciya ce bazan iya ba,daga baya kuma bayan ta tafi dan rashin kunya sai naxo ina cewa ina sonsa"
Bombee tayi maganar cikeda maida mata magana,kana ta ƙara da yin murmushi a ƙarshe.
Aikuwa kaman yanda tayi tunani Jawaheer taji haushin maganar sosai,dan lokaci ɗaya ta hassala tafara magana cikin baƙincikin data shaƙeshi a makaranta dasafe bata samu damar amayar dashi ba dukka.
"Hmmm ke kinsan kuwa wacece ni,wlh banda aiki ne yakawoki da kin isa ko hanya ma ki haɗa dani,kuma bar cika baki kina wani cewa ke amaryarsa ce kina wani taƙamada kyan fatarki,wannan jikin babu tasirin dazayyi akan JJ ,keda banza duk ɗayane a wajensa"
Tana maganar ne tana nuna Bombee dayatsa,carfah kuwa takama yatsan tayi shuru.
Hakan datayi ne yasaka bakin Jawaheer mutuwa tana zazzare ido cikeda tsoro,musamman ganin yanda Bombee tahade fuska babu alamar wasa.
"Inda wanda kike magana akansa yana sonki da bazayyi aure har guda uku ba yana barinki,sannan zuwankin nanɗin yatabbatar kina cikeda jin haushin kasancewata matarsa... To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau,ba ayimin ɗaya na bari babu ɗaukar mataki,ko mata ɗari masoyinki ya aura idan ana aure,kedashi dasu baku isheni kallo ba,amma kaff cikinku har matar tasa wacce tayimin kan kara zanyi mata na itace,wannan sunnah tace hakan.
Kema zan barki ne danna farko kikayi,kuma batake nake,ki bari idan so kike ki tanka ki shigo gidan matsayin matarsa tukunna,amma yanzu nafiki iko da gidannan,ke ko karan gidannan ma yafimin daraja dake,bare kuma masu aiki ko mutanen gidan. Ki bacemin dagani yanzu kinada hayaniya zaki tayarmin ɗa daga bacci,aikin banza ku mata bakuda aiki sai faɗa da hayagaga akan maza kaman wasu kaji.
Ƙarisa maganar tayi tareda sakin yatsan Jawaheer kana taja guntun tsaki..
Maida hankalin ta gabadaya kan abinda takeyi,ko kallo na biyu batasake bin Jawaheer dashi ba lokacin datake barin falon.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
___****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________
Page 🖤11••12🖤
"Tunda muka fito daga gidan baka sake cemin komai ba,shin zuwa gaisuwar jiki ce ko kuma dai akwai wani dalilin a ciki"
Duk maganar dayake Jabeer bai kulashi sai murmushi dayake shikadai batareda yace komai ba.
Hakan dayayine kaɗai yabawa Khaleel amsar abinda yakeson sani.
"Ya dai wai ina zamujene naga baka kama hanyar zuwa office ba"
"Ohh sorry da gida zan wuce dakai ai"
Sakin baki Khaleel yayi yana kallonsa,wai dagaske yake sai ya wuce dashi bayareda ya sani ba,anyah kuwa abokinnasa baya cikin illusion.
"Kai wai serious duniyar soyayyar yarinyar can ka tsunduma da gaske?"
"To menene bata cancanta bane,ko haramunne kai"
"Kuttt yaufah amarya ta iso gareka amma kuma ka folawa wata a can nesa,kuma son aurenta kakeyi dagaske"
"Hhhhh amarya,wancan abinne amaryar,kaini fah inka dauramin waccar mai kama da aljanun zan tsinketa,kallo daya nayi mata naji bakin jininta yashiga raina,gabaɗaya mommah ce take rawarta take kidinta ita kadai,kai duk halin Lubnah wlh gwanda min ita sau dubu akan ta,ni bantaba ganin macen dabana ƙaunar kallon fuskarta kamarta ba"
"Hmmmm mutumina kadaina cika baki mana haka kayi shuru kawai da bakinka,to yanzu yazakayi da wannan wacce ka ƙira da Jaleelah ɗin,kasan fah ga Jawaheer ma a gefe"
"Ahhh ni yanzu nadaina damuwa,zuba musu ido kawai zanyi,kaman ta shawarar daka bani kan na auri wacce zuciyata ke so,ta hakane zan samu kwanciyar hankali"
"To ya batun adalci kuma inka makale a iya sashen wacce ranka keso,kana ganin su zasu amince da hakan"
"Ahhh wannan kuma yana ga mommah tunda ita ta aurosu"
Shuru Khaleel yayi da zancen,dan da alama abokinnasa yasha giyar soyayya maganganu yake kaman ba shiba,saidai yana fatan Allah hasa hakan shine sanadiyyar farincikinsa.
Nikam maidani na dau motata a office,kuma ma inada aikinyi,nasan Madeenah tana makaranta,da don ita zanje gidan"
Komawa sukayi companyn ya sauƙe Khaleel,daga nan yashige gidansa na sirri.
Hanyar kamar fita daga gari ya nufa,inda sabin anguwanni suke,wani gida ya nufah ɗan karami madaidaici kana kuma ƙayatacce.
Falor guda daya sai ɗakuna biyu a gidan da banɗakunan su,saikuma kitchen shima karami,filin gidan kuma shine na saka mota.
Gidan a share yake fess babu datti,saidai babu alamun mutum a gidan da alama ba'azama a gidan sosai.
Ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ya shiga ya zauna a bakin gado.
Drawer gefensa ya jawo wacce take ɗauke da magunguna pills dayawa a cikin robobinsu.
Roba ɗaya ya ɗauka ya jajjagi kwayoyi guda biyar ya zuba su a bakinsa, gorar ruwan dake kan drawer wajen ya dauka yabi su dashi.
Ajiyewa yayi yana maida numfashi bayan ya haɗiye,tareda komawa ya kwanta akan gadon.
Bayan kaman mintunan dabasu fi uku ba kuwa yafara lumshe ido bacci yayi awon gaba dashi.
Misalin ƙarfe takwas anyi sallahr isha,text ɗin Hajiyah Zeenah tagani tana kan sallayah tagama yin sallah,ko addu'a batayiba ta ɗauke sallayar ta ajiye gefe,kana gani ma dama kasan sallah kawai akeyi domin tazama dole.
Karanta text ɗin tayi,kan tana nemanta yanzu a part ɗinta akwai maganar dazasuyi.
Yar ƙaramar tsuka tayi,da bazata jeba,saidai kuma tana bukatar miƙe ƙafa,kuma Haidar yadaɗe dayin bacci a ɗakin Hilyaan,dan yanzu daya shiga wata na huɗu madarar tafara ƙarbar jikinsa,matsalarsa ma na laushin ƙashi tafara raguwa.
Doguwar rigace a jikinta,dan haka hijabin datayi sallah jundumeme har ƙasa yana jan ƙasa a mayar.
Tafiya take tana bubbuɗawa a cikin hijabin,kai daga nesa saikace aljana,ita kanta yanayin shigar tata yabata dariyah,wayaga da rana ayi shigar gyale da daddare kuma ayita burmemen hijabi.
Tayi ta kalle kallenta a hanya kafin ta isa sashen hajiya zeenatun..
Babu ƙowa a falon,dan haka kao tsaye dakinta ta wuce dan tasan tana can tana jiranta..
Ko sallama batayiba ta samu kujera ta zauna bayan ta naɗe hijabinta wanda yataru a ƙasa.
"Naga kin daɗe baki ƙariso ba,baki hau mota ba da darennan bakya tsoro?"
"A ina kika ganni kika bani aiki,a cikin gari kika gannin cikin gidan kaman sauran mata? Banji tsoron daji ba sai wannan cikin gidan,yanzu dai ba zancen nadaɗe ban iso ba,menene dalilin wannan ƙiran"
"Amma dai yakamata ki dungayiwa manya magana da kaurin lafazi,kada ki manta fah ɗana kike aure?"
Wata dariyar shaƙiyanci Bombee tayi tareda cewa.
"Idan akwai wanda yasan wacece ni a gidannan to bayanki ne,hasalima wannan halayyar kika gani kika nemeni. Hajiya zeenah kada ki manta wacece take gabanki,ke yakamata kisan dawa kike hulɗa,yaushe ma kika samu dama har zakiyimin ƙira da daddare kuma nazo,dan kinga inayimiki laushi?."
Cikin ɗaure fuska da tsayayyun ido takarisa maganar,ba wuyah sai ranta ya baci..
Shakkarta ce tashiga Hajiya zeenah wanda sai yanzu taga hakan,wai chakwakiyah tun ba'aje ko inaba anya kuma batayi kuskure ba. Share tantama tayi a ranta tareda cewa.
"Yanzu dai ba wannan ba,dama ɗazu na yi shawara,shin maizai hana ki fara dayimana maganin matarsa a cikin wata shida na farko idan babu damuwa"
"Meyasa kika ce haka,sannan wai ni meyasa bazakuyi maganin ta da kanku bane tunwuri"
"Nariga na faɗamiki halin da ake ciki,so nake da furta dakanta cewar ya saketa,idan ba haka ba inna tilasta shi ya saketa to zai mutu.....idan mukayi maganinta da kanmu kuma uwarta bazatayi shuru ba,wato Brr Na'ima.
"Brr Na'imah Hashim wai"
"Eh itafah kinsan ta ne?"
"Uhm amma basosai ba shikenan zanyi shawar ni barin na tafi"
"Yawwa bayan wannan kar Jabeer yasan dalilinki na zuwa gidannan,ta hakanne sirrin mu zai rufu sosai"
"Uhm bakuso yasani itakuma yarinyar dazai aura yaakayi ta sani "
Alamar rashin sanin mai take faɗa Hajiya zeenah ta nuna,ta hakanne tagano cewar Hajiya rabi ce tafaɗawa ƴar ta kenan,saboda kartayi mata kallon matar masoyinta. Komai yana rufe a gidannan.
"Lahh shikenan karki damu ma bakomai ni na tafi"
Daga haka Bombee ta tashi tanufi hanyar nata side ɗin.
Dariyah ta sheqe dashi tareda cewa.
"I solved some puzzle,hmmm Hajiya zeenah kenan,idan bangane mai kuke ƙullawa ba basunana Bombee ba wacce sunan ke zama kan harshen duk mutanen data zaga.
Kin bukaci na yimuku maganin Lubnah da farko saboda kufitarni daga shirinku a cikin wata shida nan gaba,wanda shine daidai lokacin aurawa Jabeer Jawaheer. Sannan bakuso shi yasan matsayina a gidanann saboda kada matarsa taji. Wannan duk plan ɗin Hajiya rabine,amma kuma ta sanarwa da ƴar ta saboda ta kwantar da hankalin ta.
Ke kuma Lubnah wato ke ƴar barr Na'imah ce da kuma Gen Abdu manga.
Wow puzzle ɗina ya warware cikin sauƙi,shirina yana tare a waje ɗaya batareda na saniba,am sorry Hajiya zeenah,kin kawoni cikin gidannan,amma abinda naga dama dakuma tsarina zanyi,in takanki ya biyoma saidai kiyi sorry"
Tafiyah Bombee take tana fara'ah da nishaɗi,da alama tasamo bakin zaren matsalolinta,tasamu fili tasamu doki,saura sukuwa kawai yarage mata.
Ba ita ta isa part ɗinta ba sai wajen 9:30pm,tana shiga taji shuru tsitt,da alama su Hilyaan sunyi bacci itada Haidar kenan.
Safah da marwa take a tsakar ɗakinta,taje kana ta dawo,tarasama mai yake mata daɗi a duniyar nan ta maliki yaumiddini,ƙarfe kusan goma amma Jabeer bai dawo gidaba,kaddai ya dawo kai ya tsayah a sashen amaryarsa kaman yanda tun ɗa zu zuciyarta ke raya mata ammma taƙi bata hadin kai.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi,data fara gasgata hakan,mayafinta ta ɗauka ta fitah da gudu zuwa sashen Bombee.
Saidai har taje bakin ƙofar kuma sai tadawo wata zuciyar tace mata,karkuma kije kiyi mungun ganin dazai rikita miki ƙwaƙwalwa.
Turus tayi a bakin ƙofah tareda komawa cikin sanyin jiki,jidake banda tafarfasa babu abinda zuciyarta keyi,gaba ɗaya ko wata huɗu batayi ba da fita a cikin ƙangin kishi har takoma wani.
Ganin idan takoma cikin ɗakinma ba bacci zatayi ba,yasa kawai ta nufi wajen motarta a daren ta nufi sashen da Bombee takeyi,ba mungun gani ba inma aljanin ganine gwanda tayi data kwana da wasiwasin kar ko mijinta yana wajen wata,watan ma wacce tayimata cin fuska a lokacin farko.
Bombee wacce bata dade da shigowa ba,tasaka kayan bacci kenan taji anan ƙwanƙwasa mata ƙofar bakin part.
Jim tayi kan wanene yake buga ƙofah haka a zuciye?
Ganin zai tayar da masu bacci yasakata nufar bakin ƙofar,ko ɗankwali bata ɗaura ba gashinta yana ɗaure ribbon.
Ta na'urar jikin ƙofar ta leƙa domin ganin wanene,Lubnah ce a tsaye ta kama kunkumi tana jijjiga tareda tsumayin a buɗe ƙofar.
Tun kafin ta buɗe ƙofar taji Lubnah tasake buga ƙofar tareda cewar.
"Ki buɗe ƙofar nan kifito min da mijina,munafukar Allah nasan daga kallon dayayi miki da safe badai kan yabiyoki dan Allah ba saidan nemarsa dakikayi"
Dan murmushi Bombee tayi tareda zare ribbon ɗin dayake kanta kana ta barvaza gashin kannata a gadon bayan da ƙafaɗunta.
Yamutsa rigar jikinta tayi tareda ɗageta ta sokata a tsakanin mamanta,ta yanda cibiyarta zata buɗe ana kallonta..
"Let have some fun"
Tafaɗa tareda buɗe ƙofar,hammar ƙarya tayi tareda kallon Lubnah ta lumshashshun idanuwa cikin maganar hamma.
"Baiwar Allah lafiyah,mai ya kawo ki side ɗin amarya dawannan daren,wani abun kike nema?"
Sake hassala Lubnah tayi tareda ƙarema Bombee kallo,wacce take tsaye a gabanta gashi a babbaje,ga matarta a mai laushi dakkyau cikin kayan bacci masu ɗaukar hankali,kana ganinta kam babu shakka kasan sun fagen soyayyane tafitar hankali,dan jikinta ya nuna