Showing 123001 words to 126000 words out of 134612 words

Chapter 42 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8673

aga mai sakamako zai bayar,wanda dama shine tashin hankalin.
A tsawon wannan lokacin banda roƙon Allah da fatan nasara babu abinda dangin Jabeer sukeyi,duk abinda ake a asibitin har sannan su Jawaheer suna sashensu itada Jaleelah,kaman yanda bombee tace kada su kuskura su fito suna ciki,zama daƙyar tashi daƙyar,saboda izayar da hilyan take shuka musu,abinda da jiki irinna masu hutu,duk sun goje sun sanja kama,komai su sukeyi a sashen dan bombee takori duk wata mai aiki daga sashen.
Lubnah kuwa tunda taji ance Jabeer ya bata,kuma ta tabbatar lallai aikinda tayi masa ya karye,saita ɗauki abinda takeso na amfani ta nufi gidansu.
Nan ma gidannasu ba daɗi gareshi ba,shi ammar ya tattara yabar ƙasar ma gabaɗaya,daya gane cewar ashe uwarsa ta saida haihuwarsa akan buƙatarta,itakuma matarsa daya narke akan sonta ashe cikin wani take shirin laƙana masa.
Shikuwa gen abdu manga yarasa ma mai zaice da brr na'imah,kokuma mai zai mata a duniyar nan yahuce ko kuma yagyara abinda tasakashi aikatawa na tsawon lokaci.
Dan haka tsinuwa yayi mata ta uwa ta uba,dagannan ya ɗau kayansa yabar gidan bayan yayi mata saki uku.
Ita sakin dayayi mata bai dameta ba,halinda ƴaƴan ta suke ciki yafi komai tada mata hankali,gakuma wasu munanan halittu da suke hanata sakat a duk lokacin data rufe ido.
Ganin yadda gidan ya cakuɗe yasa lubnah yin hanyar nata ɗakin,kuka tayishi har gaji ta sallama.
Ko nan da nan bata zuwa,koyaushe tana kusada banɗaki,saboda abinda yake ciyayowa daga ƙasanta,duk batajin zafi yanzu yazamo da ƙyar take zama kuma take tashi.
Yanke shawara tayi kan zata sayarda gwalagwalanta ta tafi asibiti neman magani,wataƙil sai ta dace,duk da tasan cewar hakan abune mai matuƙar wahala.


Wasa wasa anyi kusan sati guda da yiwa Jabeer tiyata,amma har yanxu bai farfaɗo,tun suna saka rai da tashinsa har sun fara karaya.
Bombee ce da Hajiyah Zeenah a wajensa suna kulada shi,kaman juyawa ta kuma goge jiki.
"Yakamata ki koma gida kawai zan kuladashi,tunda ba idonsa biyu ba,babu wani aiki sosai.
A gida kuma Baba yana buƙatarki,tunda shima bayida cikekkiyar lafiyah"
"Bombee ce tayi maganar wacce take zaune a kujera tana duba wani abu a labtop ɗinta"
"Eh hakane kam mommah kizo mutafi tareda Abdulmaleek,kuma kinga abdulkareem ma yana nan zai dunga leƙosu,Abba yana gida daga shi sai Madeenah kawai"
Maleekah ce tayi maganar itama,dan tun jiya suke fama da ita ta tafi taƙi fafur..
Ga mamakinsu kuwa saita tashi ta ɗauki jakarta,bakin gadon Jabeer ɗin taje inda yake kwance kaman gawa.
"Kayi haƙuri nasan banida ikon daina zargin kaina amma......"
Bata karisa maganar ba maleekah taja hannunta suka fita waje,wacce itama hawayenne a fuskarta.
"Anty maryam mu zamu tafi,gobe ta sassafe zan dawo"
"Okay ba matsala maleekah"
Daga haka bata sake cewa komai ba har suka tafi,jin wajen yayi tsit daga ita sai numfashin ta,yasa ta ajiye system tareda nufar inda Jabeer yake kwance.
Rigar da take jikinsa ta cire tareda ɗakko lotion ɗin da ake goge masa jiki dashi.
Tana zubawa tana gogewa da tissue har saida tagama tass kafin tasanja masa wata rigar.
Kayan baccinta tasaka kana ta hau gadon gefensa ta kwanta..
Kallon gashin idonsa take wanda sukayi zarara,gani take kaman bacci yake zata ƙirashi ya amsa.
"Kada ka cire tsammani da dawowa garemu Jabeer,dan Allah katashi daga wannan baccin daka keyi,akwai mutane masu muhimmanci a rayuwarka da suke jiran wannan farkawar,inka tashi nayi alƙawarin faɗamaka duk wani abu dakake buƙatar sani daga gareni"
A haka tana sambatun a jikinsa har itama bacci ya ɗauketa.


*** ***
A zaune yake a zuba tagumi a gidannasa dake cikin barrack,abin duniya ya taru yayi masa yawa yarasa shin ta ina zai fara.
Sati guda kenan da barinsa gida,amma yanda yaga dare haka yake ganin rana batareda ya samu maslaha ba.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi daga waje,saida yaɗau wasu lokuta kafin yabawa mai ƙwanƙwasawar damar shigowa.
Gen sameerah ce tashigo Falon kanta a tsaye fuskar nan a murtuƙe.
"Sir"
"Samu waje ki zauna"
Takulada sauyawar shugabannata,saidai batace komai ba ta zauna domin taji mai zaice.
"Kimsamomin bayanan gameda Gen Muhammad Bello?"
"Eh nasamo sir,baya ƙasar nan yana India akan matsalar ciwon zuciyar dayake dashi,saidai iya ganin likita zayyi ya dawo.
Iyalansa kuma suna nan a garinnan cikin ƙoshin lafiya"
"Kin tabbatar baya ga haka babu abinda yake faruwa na matsala gameda su?"
"Ehh babu yallabai,amma mai yasa ka damu dashi dakuma halin da ake ciki"
"Saboda kinsani nima nasani mune sanadiyyar mutuwar ɗansa da kuma silar rashin lafiyarsa"
"Amma yallabai wannan abune daya faru da daɗewa,meyasa kake shirin dawo dashi baya?".
"Saboda na gyara kuskuren dana aikata a bayan,zuwa gobe zan miƙa kaina dana iyalina a kotu har dake. Kan miyagun makaman da muke shigowa dasu,kisan Haidar ɗan gen muhammad,barazanar mu na karbar Companyn JAAN,samun babban matsayi ta gurbatacciyar hanya.
Ita kuma matata zan maka ta kotu kan laifinta na rufe mugayen laifuka da kuma yiwa gurbatattun ayyuka shaidar bogi,sannan kuma sun haɗa da kisan kishiyoyin ƴar ta har guda biyu da suka haɗa da ƴata suka aikata..
Kekuma naki laifin shine An haɗa hannu dake wajen yin wadannan ayyukan dukka."
Tashi tayi ta tsaya tsaye tana kallon gen abdu,gabaɗaya takasa gasgata abinda kunnenta suka jiyo.
"Amma yallabai?"
"Karki ce komai,sannan kuma kada kiyi ƙoƙarin yin komai,gobe nida ke zamu ajiye uniform ɗinmmu na khaki,wani satin kuma zamu nufi kotu domin girbar abinda muka shuka,bayan barrack sun zartar mana da namu hukuncin.
Kike gidanki dayake nan ki zauna,domin na bada oder daga kin shigo kar kowa yabarki ki fita"
Jikinta rawa yake tana jijjiga kai,ko a mafarki bata taba tunanin haka rayuwarta zata ƙare lokaci guda ba. Kuma wai a kurkuku,duk bayan wannan abubuwan da tayi? Kai inaaa hakan bazai tana yiyuwa ba.
Tana nan ƙame kaman dutsi har yatashi yafita daga falon.






____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤 53••54🖤






Tun kafin asuba bombee ta tashi,saida ta tabbatar ta gyara Jabeer kafin tashiga banɗaki ta ɗauro alwala.
Nafilfili tayi kafin lokacin da alfijir zai keto,yanzu tana iya yin ibadunta yanda takeso batareda ciwon kai ba,saidai fah halin rashin haƙuri da ƙin ɗaukar raini takula su sun zama a jininta suke.
Tana nan zaune akan sallayah har haske yafara shigowa ta windown ɗakin,tashi tayi ta nufi bakin gadon ta zauna,kaman ko yaushe haka yake a yanda take barshi kullum batareda ya motsaba.
Tsira masa ido tayi ƙyam ko ƙyaftawa batayi,ita kaɗai tasan tunanin datakeyi a cikin zuciyarta,burin a yanzu shine samun lafiyar mijinnata,komai ma idan zaizo daga bayane.
Zamewa tayi ta ɗora kanta akan ƙirjinsa,a haka bacci yasake ɗauketa tana saurare bugun zuciyarsa wanda sai lura take jiyowa a hankali,shikaɗai ne kullum hope ɗinta datake dashi na cewar zai tashi wata rana..
Hayaniyar dataji a ɗakinne yasaka ta farkawa,Hajiyah Zeenah ce da kuma su maleekah,wanda ganin inda ta kwanta yasaka su sosa ƙeya.
Ko a jikinta ta tashi ta nufi banɗaki,sai bayan ta kintsa kana tafito.
Ƙasa ƙasa ta gaisheda Hajiyah Zeenah yayinda itama a takaice ta amsa tareda tambayarta ya mai jikin.
Suna nan zaune suma su inna Danejo suka shigo,saidai wannan karon akwai sabin fuska guda biyu,wato ummaruje da kuma Malam Ahmadu.
Duk da bombee tasan da zuwannasa amma ganinnasa bayan tsawon lokaci saida yabata mamaki..
"Baba"
"Na'am bombee ta ykk ya jikin mijinnaki,naji duk labarin abinda ya faru a wajen innarki da daddare,sannu kinji"
Bombee bata bari ya ƙarisa ba ta faɗa jikinsa,so take tayi kuka amma kuma yanzu ba lokacin kuka bane,dan haka kawai tayi shuru luf a jikinsa,innayi ce itama tazo ta baya ta rungumesu,ita kam tayi ɗan kukanta.
Ƙaramin hannu bombee taji ta bayanta ya rungumeta,dariya tayi tareda juyawa ta ɗagoshi jikinta,ɗan ta farincikinta nata na kanta,wato haidar.
Daga shi tayi sama yana ƙyalƙyala dariyah,banda mamma ba abinda yake faɗa.
"Um boy hadda kai aka zo asibiti?"
Ajiye shi tayi ƙasa tana ƙoƙarin boye farincinkinta na ganin ahalinnata saboda halin da ake ciki.
Abdulmaleek ne wanda ya tsugunna tareda kamo hannun haidar wanda bombee ta ajiyeshi a lokacin.
Kallon hannayensa yake da alama akwai abinda yagani daya tuna masa abu,saidai kuma shigowar Hilyan sai ya katse masa hankali daga kan yaron.
Kallonta yake yana kallon abdulkareem ma wanda shima ita yake kallo kafin ya kalli hilyan ɗin.
A tsawon wannan watannin gabaɗaya da dagula musu lissafi,a rana ɗaya saisu haɗu da ita lokaci guda, a wurare daban da kaya daban,amma kuma idan su suna tare guda ɗaya suke gani,kuma duk saita kallesu tayi musu murmushi.
Sun kasa gane wanne siddabaru takeyi a tsakaninsu.


Kiftawa abdulkareem ido Abdulmaleek yayi kafin yayiwa hilyan alama da ido kan tazo.
Ba musu tabi bayansa zuwa corridorn dayake ɗan nesa da inda ɗakin Jabeer yake.
Suna nan tsaye baicemata komai ba,itama batayi magana ba har abdulkareem ya iso wajen.
"Uhm shin kinsan wannan"
Ƴar dariya hilyan tayi tana kallon Abdulmaleek ɗin,mai yasameshi kuma yake tambayarta wanene ɗan uwansa.
"Aisha magana nake miki kin sanshi?"
"Na sanshi Dr. Abdulkareem ne ɗan uwanka mana"
"Okay to bayanni kina haɗuwa dashi?"
"What akan me zan haɗu dashi,kaima har yanzu ban amince da abinda yake tsakaninmu ba tukunna,saboda bakasan komai akaina ba, nikuma bazan iya faɗamaka ba"
"To amma duk sanda nake tareda ke muna magana sai yacemin shima yana tareda ke"
"Nikuma ohh.....minti ɗaya ina zuwa yanzunnan"
Barin wajen tayi da sauri,can anjima saigata ta janyo hannun Inayah sun taho,tundaga nesa da Inayah tagane mai yake faruwa tafara sunne kai,dan da alama ita take haɗa komai kenan.
"Kayi mistake inaga bani kake nufiba Dr abdulkareem,da alama ƴar uwata kake gani.
Kayi haƙuri ba sunana aisha ba Abdulmaleek.
Sunana Hilyan ita kuma wannan Inayah,mu yan biyune kuma marayu gaba da baya,bamusan kowa anan ba sai anty maryam wacce take tamkar jigonmu,iya wannan zan iya faɗamuku gamedamu mu zamu tafi"
Hannun tahaɗa tana roƙon su afuwa,amma Inayah ko a jikinta,saidai kana gani kasan akwai abinda take boyewa.
"Kince masa sunanki aisha,to amma nima cewa tacemin sunan ta aisha,kuma itace take tareda Ɗan uwana,inna ƙirashi kuma sai yace daga inda yake yana kallonki a wajen matar babban yaya,wani lokacin har hotonki yake turomin daya ɗauka a lokacin. Mu munyi tunanin mace ɗayace takeyin siddabaru"
Juyawa hilyan tayi cikin bacin rai ta kalli Inayah wacce take buya a bayanta.
"Inayah mai kika aikata faɗamin"
"Ohh ni babu abinda na aikata,kawai ranar ne naje shopping anty maryam ta aikeni sai ya ganni,najuya zan tafi sai yace min........'Am kaman aisha koh wacce take zaune a gidanmu'
Nikuma dana gano ke yake nufi da alama kince sunanki Aisha,sai nace eh itace.
Wannan ne fah kawai"
"To meyasa bazakice bake bace toh?"
"To miye dannace nice ɗin,kema naga ba sunaki Aisha ba ko?"
Murmushi su Abdulmaleek suka tsaya sunayiwa adorable twin ɗin dake sa'insa a gabansu,sun shagala da kallonsu har basaso su daina faɗan.
Abdulkareem ne yayi gyaran murya tareda cewa.
"Yanzudai ke hilyan bakece mai ɗaukar zafi ba nine koh,to na yafe abinda tayimin,dan da alama naga abinda tayin ya sakata nishaɗi sosai,saidai fah bazan yafe dukka ba har sai kin bani dama munyi magana tukunna"
Cuno baki Inayah tayi tareda ɗaga kai.
"Uhm nima anyimin ƙaryar sunan Aisha,dan haka abani damar yin maganar kafin nayafe"
Abdulmaleek shima yafaɗa yana kallon hilyan ta gefen ido,wacce duk kunya takamata sai matse hannun Inayah take dayake cikinnata.
"Ke dallah sakemin hannun zaki karyani,duk salon soyayyar ne haka"
Ta faɗamata daidai kunnenta,amma Abdulmaleek yaji ta duk da tafaɗa a hankali.
"Looovvee is in the air"
Dukka tareda suka juya suna kallon maleekah wacce takeyimusu tafi.
"Sannan kuma ga wani labari dana ji yanzu a gida danaje ɗakko abincin da aka manta.
Baban haneef shida anty Lailah suna nan sun saka iyah a gaba wai saita amince da Abban haneef ya karbi kujerar yah Jabeer,tunda bazai tashi ba"
Dukkansu a tareda suka zaro ido gameda labarin da sukajin.
"Hmmm nima danaji abinda ake faɗa ɗin nayi matuƙar mamaki,kumada alama iyah ta yarda da abinda suke faɗa,a kowanne lokaci zakuji an ƙira family meeting.


Bayan sati biyu dayin aikin Jabeer aka ƙira family meeting domin tattaunawa akan waye zai riƙe Companyn na ɗan wani lokaci.
Duk da cewar babu wanda zaiso Alhj Abdullahi ya karbi Companyn,amma kuma kowa yasan shine yakamata ya hau.
Alhj aliyune ya fara magana tareda cewar.
"To Komai da ake ganin ya faru muƙaddarine daga allah wanda ba'a saka masa rana,Jabeer har yanzu yana kwance a gadon asibiti,sannan kuma likitoci sun tabbatar dacewa koda ya tashi toba lallai ne ya koma yanda yake ba a da.
Dan haka na yanke shawarar zan miƙa kujerar Companyn a hannun......."
"A dakata haka Abba"
Muryar bombee ce wacce shigowarta kenan ɗakin meeting ɗin.
"A ƙai'dar tsari na riƙon Company,wanda yakeda mafi kason share shine zai karbi shugabancin sa,duk da cewar shine na biyu a kaso na biyu a yawa.....
Alhj Abdullahi bashida lasisin hawa kujerar wannan Company,saboda bincike ya nuna ya daɗe da siyarda da share sa a hannun wasu dasuke son karbar kujerar nan,duk tsawon lokacin da takardun jabu yake aiki"
Kowa kallon bombee yake da mamaki wacce take nuna takardun Alhj Abdullahi a hannunta.
Cigaba tayi da cewar.
"Shugaban Company yana kwance halin jinya,mataimakin sa kuma bashida share ko ɗaya a hannunsa,shin za'a miƙa kujerane ga na waje.
Zuwa yanzu wannan yafara kallon wannan,ciki kuwa harda manyan mutane biyar da aka gayyato wanda sukeda kaso mai yawa suma a cikin Companyn.
Magana suka farayi ƙasa kasa akan kowa nason karbar ragamar Companyn,wasu a cikinsu har sun fara murna da labarin da bombee ta kawo,domin hakan shine babbar damarsu.
Wata harara Lailah taje makawa bombee,yayinda mutanen gidan suke ganin sakarci na abinda bombee tayi.
Faɗa yafara kaurewa a tsakanin mutanen,kowa yana iƙirarin shiya cancanta da wannan kujera,har yazamo hayaniya tafara yawa.
Buga table ɗin bombee tayi,saida kowa yayi shuru kafin tayi gyaran murya.
"Wannan kujerar da kuke magana akan ta ta mijina ce,ƙannensa dukka suna da aikin yinsu,ƙanin mahaifinsa kuma bashida takardun riƙe Company a yanzu. Sannan shi wanda ake ƙoƙarin karbar kujerar sa ai bai mutu ba da ransa.
Dan haka ni matarsa Maryam Ahmad,nayi alƙawarin zan riƙe wannan kujera na tafiyar da ita yanda ya kamata,batareda na bari ta fada hannun wanda bai dace,har zuwa lokacin da mijina zai samu lafiya ya karbi abinsa.
Uhm na manta ma ban faɗamuku ba,barona asibiti a yanzu ya farfaɗo daga doguwar sumar daya shiga.
Saidai likitoci sun tabbatar da cewar komawar sa normal sai a hankali.
Dan haka na ɗaura ɗamarar karemasa matsayinsa da kuma kuladashi,har zuwa lokacin dazai iya aikinsa dakansa.
Abba idan ka amince dabani kujerarsa na kulada ita kasaka hannu akan wannan takardar,nizan koma Wajensa a yanzu"
Tana gama maganar ta tsugunna a wajen da Alhj Aliyu yake zaune ta miƙa masa takardar.
Hannu yasaka ya karbi takardar yana murmushi.
Tashi tayi zata tafi taji yayi magana.
"Keda kike buƙatar saka hannuna meyasa kuma zaki tafi?"
"Abba ba dole sai yanzu zaka saka hannun ba,miƙa ragamar aikin ɗanka a hannuna kana buƙatar yin dogon tunani,zan jira har sai sanda ka amince kafin kasaka hannun"
Jijjiga kai yayi tareda faɗaɗa murmushin sa kana yayi sign a wajen da ake buƙata,mika mata takardar yayi tareda cewar.
"Na yarda dake ɗari bisa ɗari da dukiyarsa da kuma kulada shi,maleekah tana bani labarin duk abinda kike masa,babu abinda zancemiki sai Allah yayi miki albarka kuma yabawa mijinki lafiya kinji"
Kallon dattijon take cikeda shauƙin jin girmansa a idonta.
"Nagode Abba,ina mai tabbatar maka bazakayi nadamar miƙamin amanar dukiyar ɗanka ba"
"Ina fatan hakan"
Tashi tayi ta tsaya,lokaci guda ta sauya yanayin fuskar tata.
"Defuty CEO and directors,ina buƙatar kasancewarku a office 7:00 am na safe,akwai abinda za'a tattauna"
Tana gama faɗin hakan tayi waje da sauri,bata daɗe da fita ba sukaji tashin motarta.


A bakin ɗakin taci karo da doctorn zai shiga.
"Mr Jabeer kin dawo,ɗazu nashiga bakya nan sai nurse kawai na gani"
"Uhm wani urgent abune ya taso,ɗazu kacemin ya tashi amma ni banga wani cigaba ba sosai"
"Bazaki gani a haka ba dama,amma yanzu baya numfashi da inji da kansa yakeyi"
Nurse ɗin da bombee ta buƙata a bata ta suna zaune a gefe guda.
"Sister Haleema shin akwai wani abu da kuka gani gameda shi?"
"Ahah babu komai doctor,saidai kaman yatsansa ya motsa,naga ya motsa daga yanda yake"
Ƙarisawa wajen bombee tayi da sauri tana nazarin abinda suka faɗa.
Kafin wani lokaci ƙanƙani kowa labarin farfaɗowar Jabeer yabaza yan uwa,saidai har yanzu baya motsi sosai,abinma sai yafi bada damuwa fiyeda da.
Da daddare bombee kwana tayi tana nazari gameda aikin da Jabeer yake,in bata gane abuba ta ƙira khaleel ta faɗamasa,dan da farko shi ta cewa ya karbi Companyn amma firr yaƙi ya manna mata.
To yanzunma dai kusan komai shizayyi,tunda ita ga kulada Jabeer.
Kaman koyaushe datayi asuba bata koma ba,zama tayi a bakin gadon tana ƙare masa kallo,alamar motsawa taga idonsa yanayi.
Fitila da ɗakko da sauri ta haska,tabbas hakane ba idonta bane yake mata gizo,fatar idonsa ne suke motsi.


"Mashallah nasan dama zaka tashi bazaka cigaba da barmu muna jira ba koh,ka tashi ka nuna musu,wanda burinsu shine faɗuwarka"
Maganganu tacigaba dayi amma ba amsa.
''Anty Maryam yah khaleel wai yana ƙiran wayarki,shin dagaskene 7:00 za'ayi meeting ɗin?"
Madeenah ce ta tambayeta cikin muryar bacci,ita da maleekah yau a nan suka kwana,tunda ita bombee tana bukatar zuwa aiki.
"Ohh wayar tawa inaga tana silent,kice masa eh yasanardasu nima yanzu zam shirya"
Tana gama faɗin hakan ta shiga banɗaki.
Bayan ta shirya kafin ta tafi saida su maleekah suka sha kashedi,kan ko motsi ɗaya suka gani suƙirata su faɗamata.
Abin harsai da yabasu dariya,itakuwa babu ruwanta.


Bakwai daidai tayi parking a ƙofar Companyn,ga wani baƙin glass data tare fuskarta dashi,wata tafiya take ta kasaita,duk da safiya ce amma kowa ya fito,don kowa yaci abinda aka faɗa na zuwan sabuwar CEO Mr Jabeer,wato Bombee.
Secretary yace tazo da sauri ta karbi jakarta zuwa cikin office ɗin.
A hawa na sha shida yake final floor yake,dan haka saida ta elevator,office ɗin ta nuna mata.
Saida ta ƙarewa ƙofar kallo kafin tashiga.
Mashallah wajene a tsare yasha kayan Alfarma irin na zamani.
Office ɗin Secretary ta wuce ta nufi na shigaban wato na CEO.
Akan table ɗin Ta ajiye mata jakar tareda komawa gefe ta tsayah.
Ƙaremata kallo bombee tayi bayan ta zauna a kujerar tans juyawa.
"Miye sunanki"
"Sunana Fadeela ranki ya daɗe"
"Tun yaushe kike aiki anan"
"Shakera uku kenan,amma nakusa dainawa zanyi aure nan da 6 month inshaallah,amma ƙanina ya cika gurbin aikin zai cigaba da aiki da ogah"
"Good Allah ya taimaka,menene schedule ɗina na yau?"
"Ranki ya daɗe basuda wani yawa,iya gabatar dakene ga directors dakuma Share holders,saikuma sign dazakiyi a takardun sabbin ma'aikatan da aka ɗauka"
"Ohk muje ki kaini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login