Showing 69001 words to 72000 words out of 134612 words
hakan da muryarta.
Cikin shaƙyaƙyƙyiyar muryar tace.
"Ina mijina yake?"
"Ohh mijinki yana cikin ɗaki yana jirana,amma kuma yau a aikinsan ba mijinki bane koh,saiki bari idan mungama yabani madara na bashi mun more,in Lokacin ki ya zo saukusha naku"
"Jabeer Jabeer!!!"
Lubnah da ƙwallah masa ƙira a can ƙasan maƙoshinta tamkar mahaukaciyah.
"Shiiitt ko ya jiki bazai fito ba,domin na cemasa yayi zaman inazuwa,kinga ma ni tafiyata,inkinaso kiyi ta tsayuwa a wajen har hudowar rana"
Bombee tana gama faɗin haka maida ƙofar tarufe tana dariyar ƙasa kasa ta mugunta.
A ranar yanda Lubnah taga rana haka taga dare tana saƙe saƙe da shirye shiryen dawowar Jabeer gareta,ina kwana daya ma yayi a can amma ji take kaman an tsunduma ta a kogin ruwan zafi,taya zata iyah barinsa yayi sati a wajen wanann mai zubin karuwan,ita yanzu ma yakejin mai nene wani abu waishi kishi,da wasanta tayi kawai.
Maganin da Mahaifiyar ta bata gobe zatayi aiki dashi,itakuma a hankali zata kai sunanta wajen Boka zulumgum suyi aiki babba a gunta.
A bangaren Jabeer kuwa bashi ya tashi ba sai wajen karfe huɗu na dare.
Yana tashi kansa ya dafe na yan wasu mintuna kafin ya tashi daga kan gadon.
Kai tsaye banɗaki ya nufah ya iyo wanka haɗeda alwala.
Sallolin da ake binsa na ranar ya rama kafin ya fara nafilfili yana jiran shiga Sallar asuba.
Kasancewar baccin dayayi ba karami bane yasa daya gama sallar akan sallayar ya zauna yana karanta ƙur'ani a cikin wayar tasa.
Ƙarfe shida daidai ƙira ya shigo masa wayar na neman gaggawa da akayi a wani company dayake da share a ciki a kasar Roman,ƴar ƙaramar tsuka yayi kafin ya tashi zai shiryah.
Wardrobe ya buɗe inda yakeda extar kaya a shirye a ciki,ɗauka kawai yayi yasaka tareda zaran keyɗin motarsa.
Gida ya nufah kai tsaye sashen sa dayake part ɗin da Lubnah take,dan part ɗinsa dake side ɗin Bombee bai fara amfani dashi ba tukunna,har akayi gyaransa aka gama bai saniba,shin anakai wasu kayansa can ko ahah bai saniba.
Har yazo leƙa ɗakin Lubnah sai kuma yafasa,yayi mata text kawai,dan yasan comfirm ne bata tashi tayi sallah i yanzu ba,dama yaya bare iya tazo,yana nan ma sai yayi dagaske tukunna.
Inaga bayanan,yasan sai ya Allah jaka a ɗaki.
Ko Hajiya zeenah bai samu damar ganiba ya wuce,da niyyar ya ƙirata ya faɗamata,don zuwan na zayyi a ƙallah sati ɗaya ko fiyeda haka a can.
Jabeer bai tashi yiwa Lubnah text ɗin ya tafi ba sai kusan 12 na rana,iya kuluwa ta ƙulu,wato jiya yana sadi din Bombee bata ganshi ba,yanzu kuma yayi tafiya sai a waya ya faɗamata.
Hannu tasaka a kai kaman mai shirin rusa ihu,dan sannan ne sauƙowarta daga kan gado,shima dan yunwa ce ta tasheta.
Wurgi tayi da wayar ta bugu da kunnen gado,fuuuu tashiga banɗaki kaman zata tashi sama,tana banɗakin tana surutu ita kaɗai kaman tababbiyah.
Sai bayan ta shirya taci abinci kafin ta ɗauko wayar.
Key ɗin motar ta ɗauka ta nufi waje a zuciye,ta motsa da alama an tafi wajen zulungum👀.
A safiyar ta kama hanyar barin gari tareda nufar zulungum da tarin buƙatunta.
Gudu take a mota tana tunanin irin cin fuskar da Jabeer yayi mata.
"Inaa dole ma nayiwa tufkar hanci,duka duka jiya fah ka kawota cikin gidan,har ka fara juyamin baya kaman wata kayan wanki,zakuwa kuga aiki da cikawa daga kai har ita ɗin"
A haka ta isa cikin dajin inda iya motarta zata iya shiga.
Takawa tafarayi da ƙafah tana ɗaɗɗage skirt,ita kaɗai tana tsuka kaman ansaka dole harta isa wajensa.
Tun daga nesa take gano hayaƙi yana tashi daga gefe bukkar,da alama wani abun yake dafawa.
Wata buta ce ta ƙarfe akan wuta tahaɗa ɗauda ko ganeta bakayi dakyau,kallo ɗaya tayiwa butar tashiga cikin bukkata,tun daga dosar ɗakin takejin gurnani kaman zaki. Yasake baki sama yana bacci kaman busuru,banda wari idan yasaki numfashi babu abinda yake fita daga bakin.
Wani kwano tasamu a wajen ta shamba da ƙafarta,aikuwa nan da nan yayi firgit ya tashi tareda ambaton sunan wani aljani a bakinsa(auzubillahi).
"Hmmm kai har bacci ma kake,muhimmin abune ke tafe dani wajenka tashi kayimin aiki yanzunnan"
"Ke yau ba ranar aiki bace,uwar matsafa ta bani hutun aiki yau,sanann karki damu kin kawo kukanki inda ya dace,An kawomin labarin sabuwar kishiryarki,saidai babban abin mamakin duk yanda naso samo sunanta cikin madubina ban samuba. Amma kibari zan baki wani magani wanda zakiyi amfani dashi..
Bazan faɗamiki mai maganin zayyi yanzu ba,saboda ƙa idarsa kenan.
Zaki dunga ɗiga masa jinin baƙar kuliyah duk bayan sati guda,har na tsawon wata uku. A wannan lokacin da maganinnan yake shan jini,ba'a yarda mijinki ya kusance ki ba sam harsai kinyi amfani da maganin tukunna. Inkuma kika kuskure toh fah zaki mutu mushe.
A sanann koh ƙafarki kikace ya tsugunna lasha,ke ko kashinkine tofah sai ya lasa dolensa""
Karbar maganin Lubnah tayi cikeda murmushi tasaka a jaka.
"Amma a ina ka samoshi,bayan kacemin yau ba aiki"
"Kedai kije ki jarraba maganinnan tukunna,kaman na sakinnan shima kedashi mutu ka raba ne.......!!!!"
** * **
Khamees ne yashigo sashen Bombee da wani labari na uzula,wanda ya samo a daren jiyan.
A zaune yake riƙeda document a hannunsa yana duddubawa kafin tafito.
Fitowa tayi sanye da riga da skirt a jikinta ƴan kanti,da haidar a hannunta yake gilu gilu da kai alamar bai tsayaba.
Hannu khamees yasaka ya karbeshi yana yimasa wasa,sai bangala dariya yake.
"Ahh lallai my boy ka samu sauƙi,gashinan idonka yana ƙarayin irinna mommynka sak blue"
Rolling Bombee tayi da ido tareda yin ƙaramin murmushi.
"Yah Khamees ka tashi lafiya,naji ƙiran gaggawa daga zuwa jiya,mai ka samo mana gameda su?"
Maida haidar yayi kan cinyarsa ta gefe,tareda miƙa mata file ɗin dake kan cinyarsa.
"Nasamo gidan su haidar bashi nisa daga nan,sannan shikuma uban gayyar target ɗinmu na samu bayanan komai nasa,gidansa companynsa harma da labarin iyalansa dukka"
"Ehh nima nasamu wasu bayanai dan gane dashi,amma ƴaƴan sa nawane?"
"Uhm ukune kacal,biyun mazane kuma basa ƙasar,ƙaramar cikinsu itace wacce mijinki yake aure,kinga kun haɗu a waje ɗaya kenan,saidai kiyi taka tsantsan kada tasan koke wacece,hakan zai bada matsala babba.
A yanzu bamu gama shiri sosai ba,dan haka bamu da buƙatar fara komai yanzu"
"Ehh nasani,tun jiya dama nasan wacece itah,kaga kenan bazan yi aiki da tsarin Hajiya zeenah ba kenan,muna buƙatar lokaci sosai akan hakan,domin suna da matuƙar iko. Kaifah ya yanayin zamanka a garin,baka ganin za'a samu matsala,tunda har yanzu baka cire siginal ɗinka ba,deactivate ɗinta mukayi,a kowanne lokaci zata dawo aiki idan tayi kusada na'urarsu,inaga kawai ka koma gembu,ni zanji da komai"
"Ahah ahhah Maryam bazaki iya ke kaɗaiba,sannan karki manta nima abinnnan yashafeni ba iya ke kaɗai bace,dan haka yanzu ma nayi secret booking na body checiking daza'ayimin,wannan karon zanyi nasarar cirewa inshaaallah"
"Hmm idan kuma ka gano a wajen zuciyarka take fah kamar........."
Bata ƙarisa sunan ba gabaɗayah yanayin fuskarta ya sauyah,ƙokarin haɗiye hakan tayi tareda sauya alakalar zancen.
Shima khamees shuru yayi bai bata amsa ba jin Mummunan labarin data ɗago mai cikeda abubuwa marasa daɗinji.
"Ya batun familynsa shin suna cikin ƙoshin lafiyah koh?"
"Lafiyansu kalau,na haɗu da ƙanwarsa ma jiyah a makaranta Nu'aimah,nasaka fuska bata ganeni ba,amma dai alamu sun nuna tana cikin ƙoshin lafiyah"
"Hmmm kenan alamu sun nuna sun ƙyale familynsa,dan haka bazamu kusancesu ba kada musake jawomusu wata matslar,mu barsu suji da rashin dasukayi ma a baya."
Cije bakinta Bombee tayi tareda dunƙule hannunta. Hilyaan wacce take bayan ta ne ta dafata a kafaɗa cikin sigar lallashi.
"Kiyi haƙuri anty Maryam,suma inshaaallah saisunga ƙarshensu"
"Wannan yazama wajibi,indai ina numfashi saina yi daiɗai da zuri'arsu ko bara sai nayi sanadiyyar data gagaresu.
A yansu basai wani lokacin ba wasan zai soma,ba gudu babu ja da baya,lokacin dazasu girbi abinda suka shuka yayi,saina saka wuƙa na yaga bargon mutuncin ƙaryar dasuka yafawa kansu,saina bankaɗo abinda suke boyewa mutane suna zaluntarsu. Khamees kayi koƙarin fitar da baƙar alamarsu a jikinka,idan kuma baka samu damar cireta ba ka koma kada kaima ka rasa rayuwarka,ka barni naji dasu,aradu ko ni kosune a garinnan,saina shayar dasu ruwan mamakin da suka daɗe basu kurba ba a rayuwarsu"
Kafin ta kaiga ƙarisa maganar idanuwanta sun kaɗa sunyi ja.
Tashi tayi kaman an cillata ta nufi ɗakinta. Jijjiga kai khamees yayi shida Hilyaan,dan su kansu abin yatabasu bare kuma itah,abin kawai cin rai sosai.
_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________
Page 🖤13••14🖤
_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_
Saida Bombee tashafe kusan sati guda kafin ta warware daga shock ɗin zaman motar da tayi,dama kuma kafin sannan ta jigata da rashin cin abinci datayi a Lokacin.
Iduwanta da farin POP ɗin dakin tafara tozali,zaro ido tayi cikeda tunanin shin yau kuma wacce duniyar ta kawo kanta,kodai kai buguwar datayi a cikin motar nan ta mutu,amma kuma a kawo ta farin waje irin wannann kaman wacce take aikata daidai,yanzu haka fah da laifuka masu yawa tabaro garinsu,taya kuma zata dace da wannan rayuwar.
Duk a kanta take wannan magananun,abu daya yadawo da ita zahiri shine muryar Hajiya Zulaiha dataji,wacce takeyiwa wata yarinya mai suna Nu'aimah.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda cewa. Inaga to a cikin mafarki take idan ta farka komai zai zo daidai.
Mikewa tayi daga kwancen da take tana dafe da kanta,wanda har yanzu bai daina yimata ciwo ba.
A hankali ta zaro kafafunta daga kan gadon ta saƙƙo.
Cikin sanyin jiki take tafiya har fito falon,a nan kallo yake wajen Bombee,dan sakin baki tayi dagaske tana kallon sama,inda decoration lamp take lanƙaye a sama.
Muryar Hajiya Zulaiha taji tana ƙiran sunanta cikeda dariyar ganin abinda Bombee take,ta saki baki galala.
"Bombee kin tashine,naga kin rike kai har yanzu yana miki ciwo ne?"
Sakin kan tayi tareda ɗaga kai a hankali,jawo hannunta Hajiya Zulaiha tayi ta zauna tareda kawo mata abinci,babu bata lokaci kuwa ballanta fulako ta hau kansa kaman gareshi aka aikota.
Saida Bombee tasake sati a gidan su haidar babu wanda ya tambayeta dalilin biyosu da tayi,sosai hajiya Zulaiha ke kulada itah. Babu laifi tasake dasu sosai,musamman Haidar shida ma tasanshi,sai Nu'aimah itakuma kanwarsa,da kuma Farouq sai Nabeelah. Rayuwa suke gudanarwa mai abin sha'awa da tsari,sannan kuma ga kayan alatu komai yaji,kasancewar Gen Muhammad Bello babbane sosai a barrake na sojoji dake abuja,Aikin dayaje gembu ma na shirye shiryen ƙara masa girma ne.
Yau tunda safe Hajiya Zulaiha ke jirga jirga a kitchen itada Nu'aimah. Saboda dawowar Gen Muhammad daga Rasha,wanda yatafi kaiwa wani result ɗin case daga headquarter su wancan satin.
Haidar kuma shida Bombee suna game a falo na combat,gabaɗaya sun cika wajen da hayaniya.
Kallonsu Hajiya Zulaiha tayi daga kitchen ta jijjiga kai,dan takula Bombee akwaita dason gagara da kuma shirgi na maza,shiyasa ma tasu tazo ɗaya da Haidar,musamman da baya da abokai dama sosai,saboda rashin zaman sa a ƙasar.
Babu yadda Gen Muhammad baiyyi dashi ba akan su tafi tareda tunda a can Rasha yake karatu amma yaƙi tafiyah,ganin sannan Bombee bata tashi ba,sai kawai ya fake da cewar ai hutunnasa bai ƙare ba da saura.
Da murna Farouq suka taroshi daga waje bayan drivernsa ya ɗauko shi daga airport. Duk murnar taryarsa da suke Bombee tana kallonsu daga inda take zaune,ɗan murmushi kawai tayi tareda sha'awar ganin kansu a haɗe,abinda ta tashi tarasa tsakaninta da ƴar uwarta kenan wato shaƙuwa,tun ranar data gane cewar munafurci takeyi mata bason gaskiya ba.
Saida yaran suka gama murnar oyoyon kafin Bombee tayi masa sannu da dawowa,da fara'a ya amsa kaman ko yaushe,sai kace ba soja ba.
Bayan komai ya lafah yayi wanka ya huta aka fito cin abinci gabaɗaya,su Nu'aimah sai labarin makaranta suke masa da kuma tambayar tsarabarsu..
Magabar da baban su haidar ya jeho mata bayan gama cin abincinne yasakata cikin nazari kafin ta bada amsa.
"Maryam kin shiga motarmu kin boyimu amma har yau baki faɗamana dalilin hakan ba,munyi shuru bamu tambayeki ba saboda kada kiji babu daɗi a zamanki tareda mu,shin mai menene yasakaki barin danginki kika zabi biyomu nan?"
"Bana biyo bane domin naƙi mahaifata inason zama dakuba,nabiyokune saboda banida wani zabi dazayyi sanadiyyar fitata daga garin saiku kaɗai. Sannan kuma inada muradin mallakar ƙarfi da kuma iko,ta hakanne kaɗai zan kare kaina akan gaskiya ta,harma da innice da laifin. Wannan shine maƙasudin shigowa rayuwarku danayi,Dan Allah abban Haidar kasakani inda zan samu training na ƙarfi wanda zan yi amfani dashi wajen kare kaina da kuma rama abinda akayi min. Inason koda zan koma garina sainayi ƙarfin dana fi gaban nuna yatsa balllanta zartar min hukuncin da banida masaniya akai. Ka taimakeni da hakan koda yana nufin akwai abinda zan biya dashi"
Sauƙa Bombee tayi daga kujerar tana roƙon abban haidar a ƙasa har cikin ranta.
Hajiya Zulaiha ce ta tashi daga kan kujerarta ta ɗagata,dan shikammma yarasa mai zaice illah gyaɗa mata kai dayake cikeda alfahari da zancenta,domin haka yake son yaga mutum da zuciya.
"Karki damu yarinya naji batunki,kuma indai maganar dakika faɗa hakane tabbas zan taimakeki,nima kukana zaki sharemin lokacin da nima zan sharemiki naki,shi wannan nayi nayi dashi yaɗau fagen daga a makarantarsu,amma sai ya ɗauki fannin masu aiki da na'urah. Karki damu zanyi iya ƙoƙarina wajen taimakamiki akan cikar mafarki inshaaallah"
Godiya Bombee tafara suburbuɗawa Gen Muhammad kaman yabiya mata kyautar makkah.
Tundaga ranar Bombee taƙara sakin ranta a cikin sosai,saidai kusan ko yaushe bata gida tabi gen Muhammad barrak,dan wani Lokacin tun kafin ya isa motama ta rigashi shiga,haiƙan take shiga cikin masu training,wani Lokacin ayita mata dariyah amma baruwanta. Shima kuma gen Muhammad hakan ba ƙaramin burgeshi yake ba,dan sai ya zauna yayi ta mata zancen abinda yashafi yaƙi da sojoji kaman ya samu abokiyarsa.
Wasa wasa an ja lokaci,haidar yana shirin komawa makarantar sa ta horon sojoji tundaga matakin yarinta.
Kullum maganar sa shikenan zai koma,ita kuwa Bombee hankalin ta gabaɗaya ya karkata a zuwan barrak ɗin datakeyi,dan a ganinta wanann zuwan da take anan zata koyah.
Kaman kullum yauma tabiyo gen Muhammad itada haidar,kalle kallen wajen takeyi cikeda shauƙi,matsawa gefen haidar tayi tareda cewa.
"Naga yawancin sojoji anan gidansu yake,maiyasa ku naku yake cikin gari toh?"
"Hakan ra'ayin abbane,bayason zama cikin barrak ,inta kama ma shikaɗai yake zuwa ya zauna har yagama abinda zayyi,ummah ce take tsoron zaman nan ɗin,tun tana amarya aka taba kawo hari,to datagani shine sai tasamu trauma da zaman barrak"
"Ohh na fahimta,shiyasa idan ana zancen zuwa bata magana"
Ɗaga kai haidar yayi tareda yin murmushi daya tuno irin tsoron ummansu gameda wajen.
"Oh na manta yau anan training na harbi, da kuma faɗa,ko zamuje mugani?"
Da hanzari ya nufi wajen da ake gudanar da gwajin,dan yasan dole Bombee zata biyoshi domin ta gani.
Raba mutanen wasa akayi gida biyu,maza sune keyin na faɗa,yayinda mata kuma suke na harbi,kalar harbin akwai na Bindiga,na kwari da baka,da kuma danƙo.
Sukuma maza akwai dambe,langa da kuma Kabali.
Lokacin da su Bombee suka isa wajen anyi wasu wasannin tuntuni,dan haka basufi saura guda biyu a gamaba.
Daga langa wacce ake a lokacin, saikuma Na kwari da baka shine a ƙarshe.
Abin hari suka saitah inda aka bada alama kafin suka harba.
Ansamu ta uku da kuma ta biyu,amma sai na ɗaya mutum biyu sukazo daidai,wanda sune suka samu nasarar sakawa a zagayen da jan launi yake.
Domin sake tantancewa sai akan matsar dashi nesa fiyeda na da,nan ma kuma sai ya zamo sun sake sakawa a gida iri ɗayah.
Sake matsar dashi akayi nesa sosai,wanda hakan yasa suka tsayah kallon kallo,kowa tana tunanin ɗayar ta fara.
Alamar farawa aka basu,inda kowa ta harba,amma babu wacce nata ya isa ga kan abin,hakura akayi kan za'a raba musu kyautukan kawai daidai da daidai.
Bombee dake gefen haidar ta kalleshi tareda cewa.
"Kai ina son nagwada harbawa a inda abincan yake,kana ganin zasu barni nayi?"
Uhm alamar tunani ya tafi kafin daga bisani yace.
"Ehh toh amma jirani barina faɗawa abbbah ko zai tambayesu"
Wajen da manya ke zaune haidar ya nufah tareda yiwa abbannasu magana a kunne,Bombee daga inda take tayi shuru tana jiran taji ko shin zai amince.
Murmushi yayi tareda ɗaga kai kana ya kalli inda Bombee take,suna haɗa ido ta sumkuyar dakai cikin jin kunyah.
Tashi yayi tsaye tareda gayyato hankalin mutanen wajen kansa,dayake shine babban baƙo na wasan nan da nan aka bashi haɗin kai.
"Ku dakata haka,ƴa ta tabuƙaci a bata dama tagawada harbi,shin ina fatan hakan bazai zama matsala ba koh?"
Alƙalin wasanne ya kunna mic tareda cewa.
"Hakan bazai zama matsala ba yallabai,ina take ta shigo filin wasa,bari a matso mata da abin harin kusa"
"Ahah ku barshi inda yake,ganin nisan dakuka sakane yasata jin sha'awar gwadawa"
Shuru wajen yayi bayan sunji bayanin Gen Muhammad,kowa burinsa bai wuce yaga mai harbin ba.
Alama gen Muhammad yayiwa Bombee akan tafito,aikuwa kai a sunkuye tashiga filin kaman mutuniyar arziki,dan dama akwaita da iyah saka fuskoki kala kala.
Mai kulada wasanne wanda kuma shine coarch ɗin dake horar da harbin ya miƙomata kwari da bakar,wacce take ɗauke da kibau guda uku aciki.
Karba tayi tasaita mata riƙo a hannun.
Wani shu'umin murmushi tayi tareda cewa "An dade ba'a haɗuba" a ranta.
Zaro kibau ɗin tayi dukka ukun ta saita su akan tsirkiyar kwarin,muryar Alƙalin wasan taji yana cewa.
"Uhm guda ɗayah zaki saka a jiki ba uku ba"
"Dokace dole sai guda ɗayah,idan ba doka bace karka damu zan iyah harba dukka ukun a lokaci ɗayah,ina harba biyar ma ba iya uku ba"
Shuru yayi mata tareda bata waje badan ya yarda ba.
Karkata kanta tayi tareda lumshe idonta ɗaya domin tasamu damar saita wajen,aikuwa tana dawowa da kanta tasakesu a tare..
A tare suka sauƙa a kan alamar jan dake tsakiyar allon harin dukka su ukun..
Lokaci ɗaya kuwa wajen yaɗauki shewa,kowa na yaba bajinta da kuma ƙwarewa irin ta Bombee.
Gen Muhammad shine yafara tashi yayi tafi,kafin sauran mabiyansa ma suka farayi cikeda jin daɗin su.
Coarch ɗin da kansa ya ɗauki kyautar na ɗayan ya lanƙaya wa Bombee a wuyah,sukansu wanda suka yi wasan ta burgesu matuka.
Haka taron ya watse kowa na zancen harbin da Bombee tayi,yanda suke mamakin ita batayishi har haka ba,dan ko kaɗan bataga nisan idan suke tunani ba ita.
Suna shigowa gida haidar yafara bawa ummansu labarin abin yafaru.
Dariyah tayi tareda tayata murna amma taƙara da cewa.
"Uhm nida kitchen tashiga ta haɗa wani abincin sabon samufuri da saitafi burgeni sosai"
Matsowa inda take