Showing 87001 words to 90000 words out of 134612 words

Chapter 30 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8696

abin karyawar kenan,da alama tayi na marmarin ta bari.
Ɗakinta ya shiga tana kwance tasake baki sama tana bacci.
Ƙarisawa inda take yayi ya bubbuga gadonnata,shuru bata tashi ba saida ya buga da karfi tukunna.
Firgit ta tashi ta zauna tareda kaiwa iska duka.
"Wayyyo iyee na'am ya akayi"
Jijjiga kai yayi na takaicin rashin ilimi irinnta na addini.
"Haba Lubnah kin tashi a bacci maimakon kiyi salati kuma?"
"Uhm bansan kai bane shiyasa,amma irin wannan tashina dakayi sassafe,mai yake faruwane"
"Dama na shirya ne zan fita nazo ganinki,kinyi sallar asubu ma kuwa?"
"Uhm nayi mana mai ka gani"
"Vakiyi kama da wacce tayi sallahr bane shiyasa na tambaya,please ki dunga kulada da addini Lubnah"
"To shikenan zan kulada shi,saika dawo ni zan kwanta"
Tana gama faɗin hakan tasaki wata hammar tareda komawa baccinta,dayaga haka shima yabar ɗakin ya tafi aikinsa.




"Amma fah anty maryam ya bani mamaki,serious banyi zaton zaici abinnan ba jiyah,kinga kaɗan ya bari a kwanukan. Kai lalle na jinjinawa hannunki a girki,bari kuma zuwa anjima muga mai yarage a na safen shima"
"Shikuma karki je kiga babu komai mana"
"Wai aikuwa daya bani mamaki fiyeda wannan,yawwa naji muryarsa inaga ya tafi barinaje na ɗauko kwanukan"
Ajiye haidar tayi wanda yake a hannunta akan kujera tayi hanyar ƙofar dazata kaita sashen.
Itadai Bombee tana ta aikin ta a kitchen ɗin,tayi ƙwabin fukawa kala kala,da alama abubuwa zatayi dayawa.
Hilyaan ce ta shigo da kwanukan tana dariyah.
"Lahhh anty maryam wlh zancenki gaskiya,kaɗan yabari fah,ashe kice Mr CEO ɗin yanada cin abinci,saiki dage dayin girki kenan,tunda Allah ya haɗaki da miji mai cin abinci"
Barin kwabin datake tayi tareda kallon Hilyaan wacce takeyimata dariyah.
"Waini dama Hilyaan haka kike da surutune ban taba saniba sai yau,nayi zaton fah ke shuru shuru ce. To idan kingama zubar ɗauke min ɗa daga kujera kimaida shi ƙasa,kinsani sarai yanzu sai ya faɗo daga kai,shima kin koyamasa rigima irin taki"
A haka suna aikin suna wasa da dariyah har suka kusan gamawa,sauran wasu abubuwan kuma da babu da aiki Hilyaan tasiyo.
"Uhmm anty maryam tunda mukazo gidannnan baki taba fitaba,bakyajin wani iri na rashin fitar?"
"Uhm idan inaji ma yazanyi toh,duk sona da fita bazayyiyuba yanzu,saboda hakan akwai haɗari sosai,kinaso na fitane na ruguza mana shirinmu tun kafin lokaci yayi.
Ko kin manta yanda nafita daga garinnan kai.
Kekamma inaga da komawa bakin aikinki kikayi,kinga tahakane zaki samomin bayanin mai hake faruwa a wajen yanzu"
Jimm Hilyaan tayi,da alama batason maganar da Bombee tayi mata
"Kona koma ma bazayyi amfaniba,ko kinmanta cewar wanda sukayi abin basa nan,shikuma gen abdu manga shine babba a barrack ɗin yanxu,kona koma bazan iya dosar office ɗinsa ba ballantana kuma nasan mai yakeyi"
"Ehh to hakane kam,Abba (baban haidar)shikuma naji ance baya ƙasar ma tun lokacin da mutuwar ɗansa da kuma abinda team ɗinsa suka aikata yabaza duniyah,shikenan sai hope ɗinsa na ƙarin girma ya warware.
Hilyaan har yanzu na gagara yarda cewar banice silar wargajewar farin cikin wannann ahali ba,kona ce zan yafewa gen abdu manga da familynsa nayi ƙaryah"
"Kiyi haƙuri da sannu komai zai fito fili,bayama wannan Sameerah wacce kiji dan munafurci wai general ce ita yanzu,kuma amintacciyar Field marshal,kiji fah yanda suka karbi manyan kujeru suna zuba maguɗinsu yanda suka so"
"Kai Hilyaan ki shirya dole ki koma barrack,ina buƙatarki a can kota wacce hanya gaskiya"
"To shikenan tunda kince haka zan koma kodan a fito da zaluncin da akayi mana,amma fah idan komai ya warware bazan sake zama ba"
"Hhhhh ehh naji,saina turaki ƙasarki Cameroo koh?
"Tabɗi ai ƙafata ƙafarki anty maryam"
"Uhm idan kikayi aure ai dole ki rabu dani"
"Wannan kuma daban ai"
Snack sukayi kala kala,su cake,donout,cin cin dadai sauransu.
Saikuma handa made juice suma kala kala.
Bayan sun gama kinkima sukayi zuwa sashen Jabeer ɗin.
Zaman jerawa sukayi a cikin fridge ɗinnasa,komai da wajensa,saida suka cika shi famm tukunna.
Hilyaan ce tafara gyara sashen,ita kuma Bombee ta tafi yin abincin rana.
Kafin zuwa ƙarfe biyu sun gama komai,sun gume sashen da turaren wutah mai daɗin ƙamshi.
Ko ina sai ƙyalli yake da sheƙi kaman bashiba.
"Kai amma fah munyi aiki fah,nadaɗe banyi aiki irin wannan ba,"
Hilyaan ce take wannan zancen tana zaune a ɗaya daga kujerar falon.
Bombee ce tafito daga cikin ɗakinsa ɗauke da babban duvet (bed sheet)a hannunta ja.
Wurgawa Hilyaan tayi wacce take kwance.
"Raguwa kawai,maza karbi wannan kisaka min shi a washing machine ina zuwa"
"Wayyo ni na gaji,wai anyah kuwa bani ake sakawa a babai ba,daga gani kinason bawan allah nan,ji wanann irin uban aiki da muƙe niƙa tun safe,maza badai ƙazantaba da muhalli aradu.
A ina kika samu makullin ɗakinsa ma oho.
"A jikin makullin da aka bani yake,idan kin gama surutun kije kiyimin abinda nasakaki,sannan basai kin dawo ba,kiyiwa haidar wanka kawai ku kwanta tacan,hmmm zaki koma barrack ai zanga yanda zakiyi ,da alama tsokar jikinki tayi laushi tana buƙatar sabon horo"
Karba tayi ta nufi hanyar sashennsu,yayinda ita kuma uwar gayyar ta koma ɗakin cigaba da aikin.
Saida ta tabbatar tayi ma koma gyaran daya kamata kafin ta rufe sashen ta fita,ɗan murmushin gefen baki tayi tareda cilla makullan tana canfkewa.
"Mr Jabeer ka ƙaddara kawai kazo hannun Bombee,hmmm plan yafara aiki"




Shigowa yayi da mota cikin harabar gidan,bayan yayi parking ya daɗe bai sako ƙafah waje ba,da alama magana yake da wani mai muhimmanci.
"Karki damu idan nazo gobe zan taho miki dashi,bayan nam ma idan da wani abun duk ki faɗamin.
Yau da daddare iyayena zasu zo nema min aurenki,wannan ranar jinta nake sosai a raina Baby,da sannu zaki kasance mallakina,nasan zan zama tamkar namijin dayafi kowa sa'a a rayuwarsa.
Bye I love you too baby take care"
Daidai ajiye wayarsa itama Bombee daidai ajiye Recoder datasaka a kunnenta,wacce take ɗakkomasa duk wata waya zadayyi a cikin motar sa.
Wani lokacin idan taji sirrinsa ne dabai shafi aikinta ba bata kunnnawa,wannan ne ta tsaya taji abinda yake faɗa.
Wani zirin haushin Jaleelah ne ya jiyarci zuciyar Bombee a lokaci guda,wanda ita kanta bata san kona menene.
"Jaleelah.....hasashena ya tafi daidai,duk matan dake kewaye da shi kece a ransa,sannan daga gani ko tsohuwar matarsa bayyi mata wannan son ba. Dole kema bincikena yabi takanki kenan,saboda zaki iya batamin budget"
Tafaɗa a hankali tana jijjiga ƙafah akan gadon.
















_*SADI-SAKHNA CEH*_


____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤25••26🖤






Saida ya sauƙe wayar daga kunnensa kafin ya kashe komai na motar ya fito waje.
Maida murfin yayi ya rufe tareda nufar sashennasa yana ɗan Jijjiga key ɗin dake hannunsa.
Ɗan sauri yake da alama so yake ya sanja kayansa yabar gidan.
Hannu yasaka ya buɗe ƙofar shiga falon,sai kuma ya tsaya ya kalli wajen tukunna,domin yayi tunanin koba sashennasa bane,saboda ƙamshin ɗaɗɗan turaren daya tunkari hancinsa.
Ƙafarsa yasaka cikin falon,inda sanyin tile ya ratsa tafukan ƙafafunnasa,yayinda hankalin sa kuma da idanuwansa suka bazu cikin falon suna karemasa kallo.
"Anyah kuwa nawa sashen na shigo"
Yafaɗa a ransa.
Komai yayi ƙal ƙal kaman glass,kujerun ma kaman basuba..
Idonsa ne yakai kan kulolin abinci,kaman jiya yauma an ajiyesu a dinning ɗin.
Nufar inda suke zai buɗe yauma yaga menene a ciki..
Da ƙaramar takarda yaci karo a wajen an ninketa.
Buɗewa yayi domin ganin kai ta ƙunsa,rubutune bamai yawa ba
"Ban ajiye Juice akan dinning ba yana cikin fridge.Sannan inkana buƙatar wani abu ka dunga rubutawa kana ajiyemin"
Ajiye takardar yayi ya nufi ɗakinsa domin cire kayan aikinsa,har sannan sauyin dayagani a sashennasa bai bar cikin kansa ba.
Nan ma wani abin mamaki yayi arba dashi,an sanja bedsheet ɗinsa da kuma duvet,kayansa dasuke hanger an ɗebesu,an share an saka room freshner mai ƙamshi.
Jan dogon numfashi yayi tareda sakinsa hade da murmushin dabai san ma yaƙwace masa ba.
Banɗakin yashiga shima a gyare,dama yayi tunanin hakan.
Taƙaitaccen wanka yayi kafin yafito zai saka saffan kaya a jikinsa.
Shima wardrobe ɗin an masa gyara na musamman,wajen kayansa na yadi daban,suit daban,hakama na bacci da kuma na shan iska.
Da sauri yagama shiryawar yafito wajen abincin,dan na jiyama har yanzu ɗanɗanonsa bai barshi ba,ga kuma wani zai sake ɗanɗana.
Bayan yagama buɗe fridge yayi zai ɗauki juice ɗin data faɗa.
Anan kam harazana yayi tareda matsawa baya,wai anya kuwa ba mafarki yake ba?
Abubuwan sunyi wuya a ƙirasu da gaske ne,yanda yaganta batayi kama da matar gidan dazatayi waɗannan abubuwan ba,duk yasan tabbas akwai dalilinta nayin hakan,amma yagagara daina bashi mamaki abin.
Duk girman fridge ɗin an cikashi tamm da sinadaran motsa baki,kaman a super market
Snacks jucicess kala kala,kowanne kala da inda aka shiryasu..
Hannunsa yakai ya ɗauki wani cup da farin abu a ciki,anyi seeling bakin da ledar cup ɗin.
Buɗewa yayi ya zuba abakinsa,daya kafa bai ajiyeba saida ya kusa shanyewa,saboda yanda ƙamshin ayaba da kuma madara ya ziyarce shi ga kuma sanyi.
"Anyah kuwa wannan ba asiri tayimin ba nakejina kaman a wata duniyar daban,abin kaman yawuce ace ƙwaƙwalwa ta ɗauka,irin waɗannan abubuwan ko asiri takemin takeyi babu abinda zai dameni,in mutuwa ce ma tasameka a daɗi ba'a wuyaba.
Ɗakinsa ya sake komawa har sannan kofin yana hannunsa yana kurba,takarda ya ɗauka da biro ya dawo falon.
"Na dawo gida na tarar da abin mamaki wanda na daɗe banga irinsa ba,koda akwai wani dalilinki nayin hakan,amma nidai a zuciyata naji daɗin hakan,in bazaki damuba inason na haɗu dake zamuyi magana"
Yana gama rubutawa ya ajiye a inda ta ajiye nata kana ya fice daga sashen cikeda na nishaɗin tarbar daya gani.
Bai nufi sashen Lubnah ba sai ya shiga motarsa ya bar wajen,dan dama tun safe ta ƙirashi a office cewar bata nan,inda sabo ya saba sai tayi tafiyarta kafin tace masa ta tafi,tun abin yana damunsa har ya daina ma sakashi cikin ransa.




Tun sanda taji wayar da Jabeer yayi a shigowarsa cikin gidan,har sannan bata motsa ba tana zaune,Hilyaan ce tashigo da sauri tareda cewa.
"Anty maryam yadawo ya sake fita fah"
"Eh nasani"
Daga haka batasake cewa komai ba ta nufi sashennasa,shurun data tsinci kanta dayi,da kuma shiga nazari yabata mamaki matuƙa,meyasa to zataji babu daɗi akan hakan.
Ahah ba babu daɗi taji ba,kawai yarinyar ce bata kwanta mata a rai ba sam,dolene tayi ƙwaƙwƙwaran bincike a kanta.
Ga wannan aikin data ƙirƙira nayiwa mutuminnan,badan komai bane saidan tashiga ɗakinsa tasamo bayanai gameda mai yake wakana,amma babu komai daya shafi abinda take so a ɗakin.
Haushine ya ƙulleta ɗazun ganin aikinta ya tashi a banza.
Yanzu batada zabi illah tasake shiga jikinsa sosai,ta hanyarsa ne kawai zata iya yiwa Gen abdu manga burki batareda ta saka mutanen ta a haɗari ba,itama kuma bataje ta aikata ba.
Wajen data ajiye abincin tanufah,kaman yanda tayi tsammani ya ajiye takarda kuwa.
Bayan ta gama karantawa mitstsiketa tayi tana cije baki.
"Ina ruwana dajin daiɗinka,yafimaka dakasan da wata manufa nayi badan kaji daɗiba,wato kaji daɗin abinda nayi a banza ni ban samu abinda nakeso ba koh? Hmm"
Kulolin abincin ta ɗauka tafito,tana murmushi wanda bawanda yasan ma'anarsa sai ita.
Jaleelah ce a zaune akan tabarmar daƙinsu itada Fareeda,suna ta taɗi akan ya aurenta zai kasance,dan yaune mutane zasuzo daga gidan su Jabeer.
"Iyeee nifah ban taba kawowa a rainaba Jaleelah zakiyi aure ba,ballanta kuma nan kusa,shikenan wato zaki tafi ki barni koh?"
Fareeda tafaɗa kaman zatayi kuka.
Kama hannun Fareeda tayi tareda yin guntun murmushi.
"Haba sweetynah inna tafi ai ba munrabu bane,nasan zaki dunga zuwamin koh,alaƙarmu bazata tatsayaba dannayi aure na tafi na barki ba ai"
"Eh naji dai,da alama wannan mutumin yaciri tuta tunda ya saye zuciyarki daga bayyanarsa lokaci guda.
Inna tace tundaga yanzu za'a fara shirye shirye,dan Baba bazaisaka doguwar rana ba sosai"
"Uhm hakana naji an faɗa,nima kaina auren a bazata naji yazomin wai zanyi aure,ko yaya ƙawayenmu zasuji"
"Ahh ya zasuji kuwa,yanda naji mana"


Hira suka cigaba dayi,gabaɗayah mutum bazai gane suna san auren yakasance ko ahah ba.


Tarba mai kyau akayiwa ƴan uwan Jabeer a gidan su Jaleelah,a mutunci da komai aka gama tsaida magana,nan da wata uku masu zuwa Auren Jaleelah da Jabeer,ba'a saka dayawa ba sannan kuma ba'ayita a ƙurraren lokaci ba.
Lokacin da Jabeer yaji wata uku aka saka baiji daɗi ba sosai,don yayi tunanin baifi wata guda ba.
Amma kuma su iyayenta suna buƙatar shirye shirye na aurar da ƴar tasu,sannan koda yace basai sunyi komai ba yasan bazasu yarda ba,shiyasa kawai ya haƙura tareda cewa Allah ya kaimu.




"Hajiya hajiya hajiya.....!!!!!"
Wata mai aikice take runtumawa Hajiya rabi ƙira a zaune,wacce tashigo sashennata da sauri kaman zata kifah.
"Ke Lu'ube mai yasameki haka kaman kinga Aljan"
"Hajiya.....hajiya Jawaheer ce hajiya,ta yanka tsintsiyar hannunta jini yana ta zuba,tana riƙeda wuƙar ta hanamu mu isa inda tak....."
Tun kafin tagama Hajiya rabi ta mangajeta ta nufi sashen Jawaheer ɗin da gudu,tun kafin ta isa take jiyo jan ajiyar kukan Jawaheer,da alama kuka tayi har ta godewa Allah.
Kaman yanda Lu'ube tafaɗa tana riƙeda wukar a hannunta,jini kuwa yanata zuba a hannun ba tsayawa,abinka da jikin hutu cikeda jinin lafiyayye,yasamu hanya ai ba tsayawa.
Wani jirine yake ɗiban Hajiya rabi saboda zunzurutun tashin hankalin datayi tozali dashi a yanzu.
Cikin rawar jiki take takawa zuwa inda ƴar tata ke tsaye,wanda itama jirin take saboda rashin jini.
"Jawaheer ƴata mai yasa haka,mai yayi zafi,mai kika rasa a duniyar nan ki faɗaminshi dahar kike ƙoƙarin tafiya ki barni akan sa?"
"Jabeer mommy,mommy kinkasa bani Jabeer,mutumin da tunda na buɗi ido na tashi da sonsa,kin kasa bani shi kullum sai kwana kwana kukemin.
Yau kawai saijin labari nayi wai an bashi mata ansaka rana,nikuma ina nan ina dakon soyayyarsa wacce take cin raina kullum.
Tunda bazaku banishi ba gwanda na mutu na huta kawai"
Tana gama faɗin hakan yafaɗi yaraff a ƙasa. Da sauri Hajiya rabi ta kinkimota daga ƙasan tana sharbar kuka kaman ƙaramar yarinya.
Ihu take tana ƙiran driver wanda yashigo ya taimaka mata suka kinkimeta zuwa mota sai asibiti.
Sai bayan Hajiya rabi taga anshiga da ita emargency an tsaida jinin kafin tasamu nutsuwar ƙiran wayar Hajiya zeenah.
Tana ɗagawa tunma kafin tace wani abu tafara zazzaga masifa_
"Kin kyauta Hajiya zeenah,ɗanki zai angwance nan da wata uku,nikuma ƴata zata mutu kafim sannan"
"Innalillahi hajiya rabi mai kike faɗa haka,van fahimceki ba wlh"
Labarin abinda ya faru ta maida mata ta waya,da sauri kuwa tashiryah zata taho asibitin,dan abin babbane sosai.
Hajiya rabi tana nan tana safa da marwa Hajiya zeenah tashigo aaibitin.
Da saurinta kaman an jehota,wajen ta nufah fuskarta itama ɗauke da tashin hankalin
"Yayah jikin yarinyar ta farfaɗo?"
"Ina kuwa ta farfaɗo Hajiya zeenah,har yanzu likitoci basu cemin komai ba,tun sanda nayi miki wayah nake zaune wajennan ban motsaba"
"Ahah aikuwa yakamata ki dan zauna ki samu nutsuwa,inshaaallah kyakykywan labari zamuji,kada ma ki damu kinji.
Ruwa ta dauka a fridge na wajen tabawa Hajiya rabi tasha,sunan zaune babu mai cewe komai wata nurse ta fito.
"Hajiya karki damu ta samu sauƙi sosai,saidai dayake jikinta yayi weak,to tana buƙatar ɗan hutu kafin ta dawo normal"
"Yanzu bacci take kenan babu abinda ya damet"
"Eh babu wata matsala,zaku iya shiga ma,amma kada ku tasheta daga baccin"
A tare suka shiga ɗakin da Jawaheer ke kwance,ita kaɗaice a ɗakin kasancewarta VIP patient.
Kaman yanda nurse ta faɗa bacci take hankali kwance,hakanne kuma yasake kwantar da guntun tashin hankalin ta hajiya rabi ke ciki.
"Da alama ta samu sauƙi,amma menene abinyi na gaba kenan?"
Hajiya rabi tafaɗa tana dafe da hannun Hajiya zeenah.
"Abunyi ɗayane shine mudawo da aurenta zuwa lokaci ɗaya da waccar matsiyaciyar yarinyar kawai,ta hakanne kawai zamu ceceta daga sake cutar da kanta.
Ajiyar zuciya ta sake jin abinda Hajiya zeenah tafaɗa,kuma dama abinda take so taji kenan tun dazu.
"Shikenan hakan yayi kam,yanzu idan tatashi zan sanar da ita,saiki sanarwa Abban shi Jabeer din ya turo kawunnanasa kumadu a saka itama wannan ranar"
"Karki damu da hakan,tamkar ya farune,dama ai babu wanda bai san da zancen ba,kawai a saka ranar dukka lokaci guda,kinga daga nan saimusan yanda zamuyi da ita waccar ɗin"
"To ya zancen waccar yarinyar kuma da kika kawo,bakya duba mai takeyi kina ganin hakan ba matsala"
"Nima nayi tunanin hakan,shiyasa ma na saka iyani tasamo min dattijuwa wacce zata dunga kulamin da shige da ficensu dukka,saboda barinta tayi abinda taga dama batareda sanina ba akwai hatsari sosai.
"Gaskiya kam,yanzu idan ta tashi sai a fara maganar shirye shirye toh"


Daga haka hankalin Hajiya rabi ya kwanta,dandai bazata so ciwon ƴar ta ba,amma jin labarin abinda Jawaheer tayi ga kowa yasa An saka ranar fiyeda yanda take ma tsammani,da alama burinta zai cika na ganin Ikon Jaan family a hannun ƴar ta,zatayi komai kuwa wajen ganin sauran matansa biyu basu haihu ba kafin ƴar ta,dan ita Lubnah bata kawo mata treating kaman Bombee da Jaleelah.


Mutane basu yi tsammani ba sai jin labarin wani baikon sukayi na Jabeer,wato dai nan da wata uku mata biyu zai aura lokaci guda kuma rana ɗaya.
Surutu kuwa babu mai tsayar dashi na wannan labari daya taso.
Ko kaɗan Bombee bataji komai ba dataji labarin,dan dama tayi tunanin hakan daga Jawaheer ko Hajiya rabi,a duk lokacin da labarin baikonsa da Jaleelah ya isa garesu.
"Toh so funny,ashe gidannan zai zama filin nishaɗi kenan?"
Bombee tafaɗa tana ƙaramar dariyah.
"Meyasa kika ce haka anty maryam?"
"Ohh ke baki gani ba,mata uku a waje daya ai zansha kallo,kuma kowaccensu tanaji da nata salon"
"Naji kina zancen mata uku,amma nikuma mata huɗu nake tunanin zasu zauna a nan ɗin koh,beside ai kallo yana ga dramar dazakiyi dasu ,ni wannan zata fi burgeni"
Hilyaan tafaɗa tana kallon wani waje daban,yayin da a wani bangaren kuma tana dariyah ƙasa ƙasa.
"Hmmm karki sakani cikin jerin matansa masu zama suyi kishi dominsa,ni mai tafiyace inna gama abinda zanyi"
"Anya kuwa tafiyar zata yiyu in zuciyar mai tafiyar takafe anan din?"
"Hilyaan!!!"
"Yi haƙuri na daina,barima naje haidar ya tashi,haidar zakasha kallon faɗan mamarka da kishiyoyinta kenan"
Tana daga hanyar corridorn take iyo maganar,wanda yasaka Bombee yin murmushi tana Jijjiga kai.




"Maleekah ina faɗamiki ki bani hanya naje wajen ubanki. Ban cika Sayyada-tateen ba idan har na bari suka kashe min jika,mennene amfanina kenan a gidan."
"Iyah meyasa kike hakan,tun jiya da daddare nake fama dake,matan fah yana sonsu,kuma shizai zauna dasu,kemai naki a cikin to fisabilillah"
"Mai nawa a ciki,kinci gidanku da mai ruwana a ciki Maleekah.
Mata huɗu russ a tare,ta ina kunkuminsa zai gamsar da mata huɗu yana kuruciyah shiba sadauki ba,duk da kakanku jarabbene zai iya gado amma inashi ina Mata huɗu.
Saboda suna haifeshi saina barsu su tsufarshi da wuri.
Duk wannan ba laifin kowa bane sai zeenatu,munafukar mata,ta maida yaronnan kaman injinnnan mai kamada mutane nacikin Telebijin(robot).
Allazee aiki,inazaka aiki ina ka fito aiki,saisun nakasashi tukunna zasuji daɗi?"
Kanta Maleekah ta kama tana runtse ido,gaba ɗaya kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login