Showing 63001 words to 66000 words out of 134612 words

Chapter 22 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8664

bawa wani yaro a cinyarta nono,......uhm ......uhm danace mata wai kina ƙiranta sai tace wai....."
"Saitace wai me,anya kuwa ita kika gani,yanzu haka shirmenki ne,wacce amarya ce kuma budurwa za'a kawota da jinjiri"
"Wlh iyah itace wacce tashigo gidannan ɗazu a mota,bamuga dan bane inaga dan yana mota.
Cewa tace wai bataga wanda ya isa yasakata tashi tazo ba Ɗan ta bai ƙoshiba,saiki jira idan tagama kulada shi yayi bacci sai tazo,inkuma bazaki iyah jiraba ki haƙura"
Saurin tashi Sayyada-tateen tayi daga inda take zaune,saida Lylah dake gefenta ta maidata ta zauna,kuma daga yanda Maleekah ta faɗamata zancen tasan bazatayimata ƙarya ba.
"Yaunake ganin abu ni Maryamu,yau mai nakeji da kunnuwana,haka ta faɗamiki ki faɗamin,kin faɗa mata wacece ni a gidannan kuwa?"
"Eh nafaɗa mata Iyah,wani juya ido tayi ma da alama hakan bai dameta ba"
"Zo muje ki rakani wajennata dan malafar ubanta"
"Ahah iyah Sayyada,bai kamata kije ba,tunda tace zatazo ki bari tazo ɗin,daga nan sai a nuna mata iyakarta ,amma wannan kam bata goyu da zaniba"
Lylah tafaɗa tana alamun taya Sayyada-tateen jimami,nan kuwa a cikin ranta murna ce fall ganin faɗuwar guntun fadar Hajiya zeenah na tabb da rushewa a wajen Sayyada-tateen.


Duk gaisuwar da mutane ke aikamasa babu wacce yasamu damar amsawa,kansa ya asama yake tafiyah har ya nufi office ɗinsa.
A hankali ya tura ƙofar ya shiga,bai zauna a kan kujerar aikinna sa ba ta hutu ya nufa ya zauna,ganin zaman bazai yi masa ba ya kwana yana kallon cilin,yarasa mai shin wanne tunani zayyi a lokacin.
Ya kai akallah awa guda a hakan,har bacci yafara ɗaukarsa,a sama sama yajiyo murya Khaleel yana bugar kujerar dayake kwance.
Ɗan firgita yayi ya farka tareda ware idanuwansa a kansa,tsuka yasake bamai sauti sosai ba.
"Khaleel yaushe ka shigo ban kulada kai ba"
"Uhm ina zaka kula kana bacci,mai cewa a dage da aikine yake bacci a office?"
"Kamawa tayi shiyasa,akwai wani abune?"
"Ahah bakomai,kawai lekowa nayi mu gaisa,sai kuma na ganka a kwance,amaryar taka ta iso ne"
Yamutsa fuska Jabeer yayi tareda kallon gefe,kana gani kasan baima da niyyar bawa Khaleel amsar dayake bukata.
Dariyah kana ya ɗora dacewar.
"Ashe Maleekah ba kayar take ba,data shaida min zuwan amarya,yanzu gashi nayi comferm da kaina"
"Kaga Khaleel serious mafita nake nema,inaga wancan shawarar daka bani zanyi amfani da itah,dan bazan iya rayuwa tsakanin wadancan matan ba,ni daga ganinta ɗazu sainaga ma kaman gwara Lubnah da ita,gabaɗaya batayi kamada mata masu zaman aure ba,beside ma tafi kama da sojoji ko kuma masu aikin bodyguard"
"Hhhh bodyguard kuma? To maizaihana ta dunga binka duk inda zaka tana baka kariyah,ni wlh dakukayi maganar ta har naji inaso inganta"
Shuru Jabeer yayi bai sake cewa komai ba,dan dama shi doguwar magana ba'a jininsa take ba,don Khaleel ɗinne ma shiyasa ya zauna yake masa maganar.
"Ni banajin zan iya wai abuma yanzu,idan babu abinda kake dan Allah kozaka rakani wani waje,akwai abinda nakeson nuna maka"
Fitowa sukayi daga suka office ɗin suka nufi wajen parking motoci,a motar Jabeer suka fita dan dama a kusa yayi parking ba wajen da ake yi ba.
Hanya suka hau suna tafiyah,Khaleel ne kaɗai ke surutunsa shi yana jinsa,saidai ko yaɗanyi dariyah ko yace uhm,babu abinda yake buri da muradi illah ya haɗu da ƙyaƙykyawar yarinyar data sace masa nutsuwa,bashida abinda yake so a yanzu illah tozali da fuskarta.
Ɗan murmushi yayi shikadai Lokacin daya tuno sanda ya kaɗeta,duk yadda yayi da ita ya taimaketa ƙin bashi dama tayi,hakan ba karamin burgeshi yayi ba. Yana cikin duniyar tunaninne yajiyo muryar Khaleel yana tambayarsa dalilin dayasa ya kawo su ƙofar gidan.
Bai sani yana cikin tunani she sun iso gidan.
Fitowa yayi a motar yanufi ƙofar gidan,yasan idan yaga bai bashi amsa ba ai zai biyoshi.
Hakan kuwa akayi biyo bayansa yayi daidai lokacin da wani yaro mai kimanin shekara goma yafito daga gidan,tsaidashi Jabeer yayi tareda tambayarsa babansa.
"Yana ciki barina ƙiramuku shi "
Yana faɗin haka yakoma cikin gidan"
Bai daɗe ba suka fito a tare,yana ganin Jabeer ɗin yasaki fara'ah,yayinda shikuma yagaidashi cikin girmamawa.
"Ahh kune da safiyar nan,gidan ƙalau koh"
"Lfy ƙalau baba ya mai jikin toh"
"Jiki alhamdulillah dama ba wani ciwo ne sosai"
Bayan gaisuwar suna tsaye sunyi shuru,sunkuyar da kai Jabeer yayi yana sosa ƙeya,da alama akwai magana a bakinsa wacce yagagara furtawa.
Kulada hakan ta Malm Umaru yayi yasakashi cewa.
"Ahh yaro shigo daga ciki mana nan turaka ta ku gaisa da mai jikin koh?"
Aikuwa dama kaman Jabeer jira yake,da sauri yayi na'am da haka,ransa ƙall cikeda farinciki.
Duk abinda ake shidai Khaleel a tsaye yake tun bayan gaisawar da sukayi da mutumin.
Jan hannun Khaleel Jabeer yayi babu ko kunya suka shige cikin gidan.
Wani ɗaki aka kaisu na ƙasa,mai gajeren saman rufi,saida mashaallah a share yake tass babu ƙazanta a cikinsa.
Malm umar yana fita Khaleel ya zunguri Jabeer,dan dama jira yake dattijon ya fita. Cikin raɗa yafara tambayar sa cikeda muradin son ƙarin bayani.
"Kai bangane ba wai meyake faruwane,nan ɗin inane"
"Kai kam katsaya mana ka gani,"
Cikin ƙankanin lokacin Jabeer yabashi labarin haɗuwarsa da Jaleelah a taƙaice"
A zaune take a ɗakin mahaifiyar ta Inna Mairo,karatun hadda take wacce zata bayar da yamma.
Muryar babansu taji ya yana nemanta,hakanne yasa ta rufe ƙur'anin tafito.
Cikeda ladabi ta tsugunna tareda cewa cikin muryarta mai sanyi marar hayaniya.
"Baba gani"
"Yawwa dama wannan yaron daya kadeki ne yazo duba jikinnaki,ganin yanason magana dake yasa nace masa su shigo shida abokinsa kije ku gaisa "
Shuru Jaleelah tayi kaman bazata ce komai ba,sai daya gama kafin tace toh.
Tashi tayi tashiga dakinsu ta ɗauko hijabinta,hanyar ɗakin babannata ta nufah,cikeda itama fargabar sake haɗuwa dashi a karo na biyu,tun ranar da suka haɗu yayi mata gizo dama.
Suna cikin magana tayi musu sallama cikin siririyar murya taahiga ɗakin kanta a sunkuye.
Shuru sukayi yayinda hankalinsu yakai kanta,amsa mata sallamar sukayi daidai lokacin da ta zauna a can nesa dasu.
"Yawwa ya jikinnaki,i hope babu wata matsala sosai koh"
"Eh babu,ban wani ji ciwo ba ai sosai,Allah ya tsare,nagode da kulawa"
"Ohk ba komai,banji sunan marar lafiyar ba"
Ɗan murmushi tayi wanda yasaka dimple ɗinta motsawa kana tace.
"Sunana Jaleelah"
Daga haka hirar ta ƙare sukayi sallama bayan Jabeer ya ajiye mata bandir ɗin kuɗi,shima bata karba ba,bashshi yayi a wajen suka tafi bayan sunyi musu sallama.


Shuru Hilyaan tayi tana kallonta,dan taga mai zatayi idan ta gama bawa haidar abicinnasa,abinda tayi tunani ne ya faru,dan Bombee batada niyyar kiran da kakar mijinnata tayi mata.
"Amma anty maryam kinsan fah tana can tana jiranki,kuma kincemusu kina zuwa"
"Ohhh wai har yanzu suna jirana,kaii nifah tunda nayi tafiyar nan bansamu wani hutu ba"
"Idan kikaje kika dawo ai saiki huta,dan allah karki fara daga yanzu mana,tunda shekara zamuyi ki dan bari a ja lokaci mana kafin a fara"
"A fara me,me kika maidani ne,jarababbiya? To naji barina je naji mai zata bani take nemana"
Sungumar ɗanta tayi a kafaɗa,har taje bakin ƙofa taga Hilyaan bata tashi ba"
"Yana ganki a zaune,bazaki jeba ne"
"Ahah jeki dawo dangin mijinkine,ni inanan kidawo ki sameni,Allah ya takaita abinda zai faru a wajen"
Hilyaan tafaɗa tana dariyah ƙasa. Taƙaitacciyar harara Bombee tabata kafin ta nufi sashen Hajiya zeenah,inda Sayyada-tateen take zaman jiranta.
Shuru kakejin falon babu mai cewa komai,ajima kaɗan Sayyada-tateen taja tsaki,a ƙallah tayi sunyi cikin carbi.
Tashi laylah tayi tareda cewa.
"Uhm inaga wannan amaryar fah bazata zo ba tafi ƙarfin amsa ƙiranmu, nibarin tafi toh haka"
Tashi tayi zata bar falon,har taje baƙin ƙofar suka haɗa ido da Bombee,wacce ta dakko danta daga cikin mota ta nufo hanyar shiga sashen Hajiya zeenatun.
"Toh ga amarya nan ta amsa ƙiran bayan tagama shan ƙamshin"
Komawa tayi ta zauna babu ko kunya,saboda yanda gulmar san ganin mai zata kasance take cinta.
Kujerar da take facing Sayyada-tateen Bombee taje ta zauna,idan ido yana kisa daya kashe ta,amma ko a jikinta kaman an tsikari kakkausa.
"To kun ƙirayeni gani nazo,mai zaku bani"
Tafaɗa bayan tasaka ɗan ta cinyah tana kallon Sayyada-tateen.
"Kuyi sorry fah barku kuna jira,ɗana ne yake bukata ta,kunga kuwa bazan barshi ba nazo wani ƙiranku"
"Ɗanki wanne irin ɗa?"
Sayyada-tateen tafaɗa tana kallon Bombee dakuma Hajiya zeenah,wacce tayi shuru kaman ruwa ya cinyeta.
"Ɗa mana irin kowanne,ƴaƴan kala kala ne dama"
"Ton ina ubansa ko dangin ubansa dazakizo mana da ɗan wani cikin gida,oh yanzu dama zeenatun bazawara ta aurawa ɗannata,wanne wace irin badaƙala ce"
"Kinga ni bansan ubansa ba ballanta na wasu dangin ubansa,ni kaɗai yakeda kuma zan tsaya masa,menene a ciki ,sauran zancenki kuma bangane su ba"
"Bakisan ubansa ba,kina nufin kice mana shegene?"
"Haka dai kika ƙirashi,ni ɗa nake gani a gabana ,shege kuma ai zagine kawai"
"Hoɗan kekuwa ƴar nan suwaye iyayenki,sannnan wacce irin tarbiyya sukayimiki da ko ƙasashen Aranaku ba'ayinsa,aradu basai gobe ba gidannan zaki bari,tunda nake bantaba ganin tambaɗaɗɗiya yake ba,shege zaki kawomin cikin zuri'ah....hhhhh Kai Kai kai ke Maleekah ƙiramin meeting yanzunnan inason ganin kowa"
Ganin Sayyada-tateen tafara kuka ne yasa Bombee ɗaukar ɗanta,kana ta kalli Hajiya zeenah.
"Wainikma Hajiya zeenah aiki nazo miki kokuma fama da matsalar iyalanki? Tun wuri ki sanar musu su daina shafani cikin lamarin rayuwarsu,nima kuma batasu zan shiga ba,idan kuma ba haka ba zan nuna musu kala ta banida daɗi,musamman tsohuwarnan,haka kawai nagidanmu basuyimin ba wasu bazasu dameni su takuramin ba,kowa yayi rayuwarsa"
"Gabaɗaya suka kalli Hajiya zeenah tareda maimaita kalmar ..."Aikeeh "... A tare.
Batada lokacin su ballantana samun lokacin yi musu bayanin tambayar dasukayi wanda dama bada ita suke ba,dan haka ta ɗora danta a kafaɗa tayi hanyar waje hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.




_*SADI-SAKHNA CEH*_




___****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤9••10🖤










A ranar Sayyada-tateen wuni tayi tana maida labarin abinda Bombee tayi mata,wacce a ƴan shekarunnan babu wanda yataba yi mata,ga kuma babban abin takaicin har sannan Hajiya zeenah batace komai ba,duk yadda takai ga yimata kashedin da koreta,zance ɗaya take faɗamata shine akwai dalilinta na aurota cikin gidan.
A zaune take laure tanayi mata tausa itakuma Maleekah tanayi mata fifita,duk AC dayake kaɗawa a ɗakin bai ishetaba sai an mata fifita da mahuci.
"Kai iyah yakamata ki daina wannan ɗaukar zafin da shekaru irinna ki,tunda tacemiki tanada dalilin kawota inaga akwai dalilin,kibari mana ki gani"
"Bawani dalili,ta rainani ne kawai saboda taga ƴaƴan ta sun kawo kai cikin gidannan suna rikeda komai,shima Aliyun da kaina zanje na sameshi,akan me zai dunga barinta tanayin yanda taga dama a gidannan,idan nayi magana dukku haɗu ku rufemin baki kuga munafukai masu uwa koh,to bazan bar wannan ya wuce ba,dole zata bar gidannan,bari ayi meeting nan da wani satin zan saka a zartar da hukuncin korarta tunda ta kalli tsabar idona tayi min tujara,.......hmmm harda shigomana da shege cikin gida,kaman tasamu gidan gala a agege"
Dariyar da Maleekah take rikewa ce tasamu damar ƙwacewa,aikuwa kaman Sayyada-tateen neman inda zata huce takeyi,duka dakaiwa Maleekah a baya timm,wanda hakan yasaka ta sakin nishi tace.
"Kai iyha naga bani nakar zomonba,wlh tafiyata zanyi na barki,tunda nazo ina miki dannar fushin ma baki ganiba,mun bata dake nayi fushi,zanga mai yimiki kunun turawan idan dare yayi ai"
Tashi Maleekah tayi tabar ɗakin tana cuna baki.
Zaki Sayyada-tateen ta malmala mata,da alama sun bata ɗin,laifin uwarta ya shafeta itama.
"Ke kaure barmin kafar nan haka,tashi kibani waje zan kwanta,wannan mutanen gidan na kula so suke su kashe ni dan kwanana bai ƙare ba,Haba har ina matsala daga wannnan sai wannan? Ohh ni mairamu Sayyada"
Fadawa tayi kan laullausar katifarta mai kamada ta jarirai,ita kaɗai a hankali tana magana.


Madeenah ce zaune a garden tana duba abinda da aka ce takai na defence ɗinsu,dan dama rukuni rukuni akayi,sai yanxu nasu yazo,hankalin ta gabaɗaya ya tafi kan abinda zata faɗa idan lokaci yayi..
Jitayi kaman a sama an fixge takardar datake hannunta.
Dagowa tayi suka haɗa ido da Jawaheer,wacce tasha riga da wando irin falazo ɗinnan pink,sai mayfi karami data naɗe iyah kanta dashi,dan kyau kam tayi kyau,ko mahassadi zai yaba mata,saidai gabaɗaya yanda akayi shigarne indai tanada mai ƙwaba bazata fito da ita ba.
Ƙare mata kallo Madeenah tayi tarda cewa, wai hakan ƴar hausawa ce,Allah dai ya shiryah. A ranta.
Miye kike kallona kinga ajin dayafi naki koh,saura ma shigowata cikin gidanku matsayin matar yayanki,shine wancan lokacin har jimin ciwo koh,saboda kiyimin lahani kina baƙincikin haskawa ta,to ta Allah bataki ba Jawaheer tana nan ƙalau"
Ƴar dariyar rainin hankali Madeenah tayi tareda cewa.
"Hhhh matar yaya manya,kai da alama matan yayan dayawa,indao wannan matar tasa ce dana gani da safe,bazaki kai labari ba a hannunta,bismillah ka wajennan"
"Yeheyeh kullum zancenta kadai ake ji,to waye yafaɗamiki ina jin tsoronta,wanann lokacin da shirina zan tunkare ta,bazan taba bari ta mallake shi ita kadai ba,sonsa a jinina yake gudu,babu jada baya kijira kiga,ina gama school nanda 6 month zakusha mamaki"
"Ohh wai Lubnah kike zance ne yanzu,hala dai mai ɗaure miki gindin batasan cewar Masoyinnaki yayi sabuwar amarya ba koh,ai yau ma tatare da safe,ke kiji wata zazzafar soyayya dan allah"
Wani zare ido Jawaheer tayi tareda zare karamin glass ɗin dake idonta.
"Whatt mai kike cewa aure,no no badai my JJ ba,bazai sake wani aurenba saini,itama tsohuwar matarsa fita zatayi ballanta kuma wata tashigo"
"Zancen kikeso kiyita ji,wai ance da gwauro ya iyali,zaikije kiyi zazzafan bincike kiga shin har kin isama nayi miki ƙarya a munzalinki"
Fizge takardunta tayi a hannun Jawaheer din,wacce gabaɗaya ilahirin jikinta ke zuba rawa.
Juyawa tayi ta nufi hanyar barin garden ɗin,har tana tuntube a hanya da dogon takalminta mai tsini,wani kallo Madeenah tabita dashi tareda cewa.
"Wahallalliya" a hankali.
Ikon Allah ne kaɗai zaikai Jawaheer inda ta nufah lafiya.


** ** **

A zaune take a kan kujera guda ɗaya dake jagaye a falon,waya ce a hannunta tana magana,daga yanda takeyi mutum zai gane da masu harkar kasuwanci takeyi.
Dariyah take darewa dashi,tareda jijjiga manya manyan sawunta masu kama da tuke. Da alama wayar tanayi mata daɗi,ta samu riba a kasuwanci.
Ƙarar fashewar abun glass taji a gefenta,tana waiwayawa tayi arba da Jawaheer tana fasa tambulan ɗin da akayi ado dasu a bakin shigowa falon.
Tashi Hajiya rabi tayi da hanzari ta nufeta,ganin ƴar tata tana koƙarin yiwa kanta illah,riketa tayi tareda duba hannayenta wanda tasamu ƴan yankuwa a jiki.
"Ke Jawaheer mai yafaru haka"
Shuru Jawaheer tayi tana wani fisfigewa kamar ƴar yaye.
"Bakyajine kiyimin magana mai yake faruwa da har zaisakaki yiwa kanki illah haka"
"Mom kibarni ki ƙyaleni shin kinsan abinda najiyo kuwa,wai wai........."
Sake fashewa tayi dawani kukan batareda ta ƙarisa ba,saida Hajiya rabi tayi da kyar kafin ta cigaba da bayanin.
"Mom kinaji wai Jabeer aure yayi yau ma amaryar tazo gidan"
"Me aure kuma wanne iri,kai haba haba duk wanda ya shaida miki wannan zancen yayi ne domin yasakaki jin haushi"
"Wlh mom da gaske nakeyi,Madeenah ce fah tafaɗamin yanzu a makaranta,ko ajin ma banshiga ba na dawo,ni wlh mom kisan yadda zakiyi,ni shi nakeso na aura mom in bakiso na mutu da ciwon sonsa to kiyi wani abu akai".
Kama hannunta tayi daga tsayen ta zaunar da itah,har sannan tunda ta kama kasan bakinta batace komai,jan ajiyar zuciya tayi tareda shafa kan Jawaheer.
"Tabb lallai hajiyah Zeenah tayimin abinda ban tsammata ba daga gareta,aure?? Yo yaushe ma hakan ta faru bansani ba ina zaune. Yi shuru autana haka kinga duk kin yanke hannunki jini yana zuba,ko asibiti kai zamuje......"
Jijjiga kai Jawaheer tayi fuskarnna shabe shabe da hawaye.
"Ni bazan je ba,mom kefah kika ce Nice matarsa,yanzu kuma gashi can ya auri wata matar bayan waccar,ni nagaji da jiran dakuke cewa nayi,ina gama makaranta zaki auran shi"
Tana maganar ne tana sake matso wani hawayen,wanda hakan yake sake ruɗar da hajiyah rabi.
"Kinga jeki ɗaki maza ki gyara fuskarki kizo muje asibiti a gyara miki hannun,ta can sai mu wuce gidan Hajiya zeenatun,dan ƙiran wayama bazai yi ba dole sai naje,amma kafin sanann barina ƙirata naji shin dagaskene. Maza jeki shiryah,wannan abinda kika fasaɗin kuma masu aiki suzo su fita dasu,ki kwantar da hankalin ki autanah"
Tashi tayi dasauri ta nufi dakinta,musamman da taji har gidan zasuje.
Barinta wajenne itakuma ta samu damar ƙiran Hajiya zeenatu.
Ƙiran Hajiya rabi taga ya shigo wayarta bayan shigowarta ɗakin ta dawo daga Aliyu.
Tana ɗagawa tun kafin ma sallama tajiyo muryar Hajiya rabi cike da magana a bakin.
"Hajiya zeenah mai nakeji ne haka yarinyah tazo tana shaidamin wai Jabeer yayi aure,dagaskene ko ahah"
"Eh dagaskene hajiya rabi,amma ba yadda kike zato ba,shima duk yana cikin plan ne,inaga konayi maganar waya bazaki fahimta ba"
"Ahh menene na damuwa ga mota cikeda mai,Jawaheer taji labarin a makaranta wajen Madeenah,tadawomin gida harda yanka hannu,bari idan na kaita asibiti aka duba hannun zamu shigo. Dole kan zanso jin mai zaifaru,sannan ya akayi kika yi komai banma sani ba"
"Hajiya rabi dakin bar dukkan maganar nan saikinzo ɗin,hakan danayi nayine domin ƙarin nasarar aurensa da Jawaheer"
Daga haka suka kashe wayar akan komai sai an haɗu a tattauna.


** ** **

Ganin sun tafi kuma basuda niyyar ɗaukar kuɗin da suka ajiyene yasaka saka hannu ta daukesu,fitowa tayi daga ɗakin ta nufi inda inna mairo ke har haɗa mata wanke wanken dazatayi kafin ta fito daga wajen gaisawa dasu Jabeer ɗin.
Mika mata kuɗin tayi tareda cewa.
"Inna gashi suka ajiye a ɗakin baffah,nace musu ma su barshi amma saida suka ajiye"
Ɗagowa inna mairo tayi daga sunkuyen tareda amsar damin kuɗin.
Ɗan murmushi tayi tareda cewa.
"Ayyah yaran kirki harda wahala haka,bari a ajewa baffanku,ya fita sun fita ai tare dasho,anya kuwa iyah bugewar hatsarin ce Jaleelah"
Tafaɗa tana kallon Jaleelah cikin sigar zolayah,.
Murmushi tayi tareda jawo gyalenta tashige ɗaki da gudu.
Tana shiga kan katifarta ta faɗa tareda sakin murmushi,wayarta ta ɗakko a gefen katifar ƙaramar nokia,sunan Fareeda ta dannawa ƙira.
Daga can ɗaya barin aka farayin magana..
"Yadai hafeeza Jalee kewata kike hakane bazaki bari muje makaranta ba,yah mai yafaru nasan inaga akwai batu"
"Uhmm wannan wanda ya kaɗeni ne yazo gaisheni yanzu,sunansa Jabeer bakiga ba yanada kirki sosai"
"Lahh farkon sunan ku ma ɗaya,To amma ke mai zakiyi dashi,ko kinfaɗa soyayyarsa kai?"
Fareeda ta faɗa cikeda mamaki
Shurun da Jaleelah tayi batace komai ba yasata tabbatarwa maganarta gaskiya ce kenan.
"Kibari zamuyi maganar kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login