Showing 102001 words to 105000 words out of 134612 words

Chapter 35 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8667

tuffah.


"Wlh fadeelah banason magungunan da Inna take sakani sha,ina tsoron fah kada a samu matsala kafin a gama bikinnan"


"Wacce irin matsala,babu abinda zai faru,keda zaki ɗaga dubai kisha amarcinki"


"Uhm ina son zuwa Kam amma fah kinsan bata yanda raina yakeso zanje ba"


"Kibar maganar nan haka kada tayi nisa,kar wani yashigo,muje na rakaki ki wanke lallen kada ya dame.


Ya kiraki ne Mutumin akan zancen sallamar ƙawaye?"


"Uhm munyi waya dashi dasafe,karkiji yanda yake tayimin zumuɗin ya ƙosa na zamo mallakinsa,yanaji dani sosai fa.


Batun sallama kuma kada ki damu kinsan zai baku sosai.


Kikace da yamma makarantarmu zasuyimin walima koh?"


"Uhm zasu haɗa walima,aikin cancanta suyimiki abinda yafi walima ma Hafiza Jaleelah"


Dariya sukayi a tare jin abinda Fareeda ta faɗa.










"Wai ka warke amma har yanzu naga baka shirin tafiyah sashenka,yau anyi sati biyu kusan.


Koda yake manene na damun kaina,ana kawo maka amarenka ai bazan ganka ba daga nan"


"Haka kike tunani,saidai in baki nemeni ba zaki ganni,bana manta Alkhairi ballanta irin wanda kikayimin.


Ohh tsayah wai kina nufin bazakiyi kewata ba inna tafi"


Ƙarisa saka sarƙar tayi tareda zaran gyalenta zata fita waje.


"Uhm kanka ake ji nina siyayya"


"Amaren zaki yiwa?"


"Saboda kaika bani kuɗin uhm?"


Dariyah Jabeer tareda sake komawa ya kwanta akan gadon nata,aikuwa fass haidar ya mari fusakrsa wanda yake zaune akan gadon.


"Maryam da alama ɗannnan naki shima ke ya iyo,kiga marin dayayimin"


"Ahah ba yanda za'ayi ya iyo ni,inaga ubansa ya ɗauko wataƙila"


Jimm yayi jin abinda Bombee tafaɗa.


"Akwai abubuwa da dama a rayuwarki wanda suke binne a ranki,shin a matsayina na mijin dakike aure bazaki faɗamin yanda kika samu yaronnan ba,duk da cewar alama dayawa suna son nuna asalin yaron bashida kyau,amma kuma zuciyata ta kasa yarda da hakan,kaman yanda takasa yarda da cewar cutarwa kikeson yi a gareni.


Sannan tawani bangaren inajin kaman kusanci tsakanina da yaronki"


"Kayi hakuri amma kozan faɗa maka menene asalin yaronnan badai yanzu ba,sannan inaga zaman dakayi dashine a kusa yasa kaji hakan,amma inkana ganin bakason ɗana bance kasoshi ba,babu wanda na tilastawa ya kalli dana a fuskar so ,tunda ina son abuna ya wadatar.


Batun aure kuma zuwa yanzu kasan matsayin aurenka a wajena,dan haka babu zancen boye boye a ciki,ni ma tafiyace,kowanne lokaci zan iya barin gidannan nan da wasu watanni shida masu zuwa"


"Abinda kike faɗa bazai dameni ba maryam,Saki a hannuna yake ina?"


"Kuma za'a iya saka ka kayishi koyaushe ba?"


Shuru yayi bashida tacewa har ta dauki ɗanta da jakarta tafita.






Har takusa shiga mota saikuma ta hango matar da aka kawo leƙen asiri tana leƙa windowanta.


Komawa tayi inda take tsaye tace.


"Ke mekike anan wajen,abinda aka turoki kiyi kenan?"


"Uhm Hajiya Maryam barka da fitowa,naga na gama aikin aka banine,shine nakeson na tambaya koda aikin dazan yi miki"


"Miye sunan ki?"


"Uhm Sunana Zaleeha hajiya"


"Toh Zaleeha (kallon mamaki tayiwa Bombee ganin takira sunanta kai tsaye batareda sakayawa dukkuwa da ta haifeta)


......miye kike yimin wannan kallon zatonki zance Inna ko kuma baba,uwata ce ke komai,kicire wannan a ranki,bana wannan shishshigin,ki nutsu kiji abinda zan faɗamiki.


Karki sake koda wasa ki tsallake layin dana shata tsakanina dake,kiyi aikin da ita uwar mai wajen tabaki,inkinga dama ko numfashi nayi kije ki sanarmata bai dameni ba,saboda kaff gidannan ba wanda nake tsoro.


Amma kika kuskura na kamaki kina shiga lamarina saina sanjamiki kamanni,ba ruwana da tsufanki"


Tunda Bombee tafara balbalamata masifah kanta yake sunkuye bata ɗaga ba,har saida tagama dan kanta ta tafi.


Sai bayan tashiga mota tatafi kafin Zaleeha tabi motar da kallo tareda yin wani shu'umin murmushi.


"Hmm yarinya kenan,kina tunanin zanyi wani abun dazan bar kusada abin farautana yake,da sannu zaku zo hannu na dakake har su innayin,kuɗin mallakina ne,jininku fansa ne gareni nida aljanuna,anriga an bani,kijira yanda zan wargaza rayuwar daga no kina ginawa mai ɗauke da haske a cikinta"






Tun Bombee bata shagon dataje siyyaya ba taji wayarta na ƙara a jakarta.


Fitowa da ita tayi ta kalli sunan Hajiya zeenah a jiki,ɗagawa tayi domin jin mai zatace mata.


"Hello Hajiya zeenatu ya akayi?"


"Uhm tunda kika samu part kike zuba fantamawarki banganki ba,zan turo miki address kizo zamuyi tattaunawa gameda aikinda kikemin"


Tana sauƙar da wayar taga address ɗin gidan Hajiya rabi,dariya tayi tareda nufar gidan dasu innayi suke..


Sharp sharp ta sanja kayanta zuwa wasu masu mungun kyau a cikin waɗanda ta siya,A wajen Hilyaan tabar haidar ta nufi gidan,domin zai bata mata budget idan ta tafi dashi.


Riga da wando ne kayan na sai farin kimono data ɗora akai,bakin farin glass tasaka tsanrparent mutun ba ganin blue iris ɗinta,bakin takalmi tasaka hight heel mai matuƙar tsini,sai jaka ƙarama mai adon fari da baƙi.


Gidan a cike yake da mutane kasancewar gobe ɗaurin aure,duk inda ta keta kallo ake binta dashi harta shiga falon Hajiya rabin,daga gani private falor don ba kowa a ciki sai su biyu..


Fararen kujerune a ciki kawai da TV da Fridge ƙarami.


Ko sallama.


Kafin tashigo ɗin da Jawaheer ta haɗu,wacce har yellow take saboda Gyaran data sha.


"Bride to be zan iya sanin inda iyayenki suke?"


"Ke kuma mai kike a gidannan yanzu,ko baƙin ciki kike zan zama matarsa ke kuma aikinki ya ƙare zakiyi waje?.


Samun gu naga har kuɗinsa kike ɗauka kina facaka dashi koh?"


"Ba wannan na tambayeki ba,tambaya nayi ina uwarki take,ta buƙaci ganina idan kuma har na zuwa to ba wanda ya isa yasani dawowa"


"Kut harke wacece dazaki dunga yin magana da mommy haka"


"Ishashshiya ce,wacce ta isa ita uwar taki wacece daba za'ayi magana da ita haka ba iyee ko uwatace kai"


Mari Jawaheer takaiwa Bombee,a tunanin ta ai gidansu ne babu abinda zata iya,tun kafin takai hannunta Bombee takifeta da nata marin saida ta hantsila.


Cikin ƙanƙanin Lokaci har shatun hannunta ya fito a fuskarta.


Duk abinda suke akan idon Hajiya rabi wacce fitowarta kenan jin hayaniyar Bombee da Jawaheer.


"Innalillahi yauni naga fitsararriyar yarinya,yanzu ƴar tawa kika sheƙawa wannan marin har cikin gidana?"


"Ko zaki rama mata ne kai,ina ruwana da ƴar taji toh,ki koya mata tarbiyya idan bakyaso ta sha wuya intazo sashena. Hadda tadaina shiga abinda bai shafeta ba zaki nuna mata"


"Shigo muna son magana dake,yau za'ayita ta ƙare ma"


Babu ko ɗar kuwa Bombee tabi bayan Hajiya rabi hankalin ta kwance,bayan ta watsawa Jawaheer kallo wacce take dafe da kuncinta masu aikinta sun tafi da ita.


Kujera ta nufa a falon ta zauna tareda ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.


Inda harara tana kisa da Bombee ta mutu sau ba adadi a wajen su Hajiya zeenah.


Tissue paper ta ɗauka a gefen kujerar ta goge hannunta tareda cewa.


"Mtsww waccar ƴar taki ta ahafamin wannan yellown abun a hannuna,daga ji ma ƙarni yake,wai a hakan kuma za'a kaita wajen miji,ohhh Jabeer kaga taikanka kaikam"


"To nunamin Kinibibi irin naku na ƴan bariki,kinaso kice ba'a kyautamasa ba komai,kinada wannan huruminne a matsayinki na bare"


"Banida shida mai ɗa,dadinta dai nima inada ɗan ba juya bace,sai kiyiwa matar ɗanki wannan maganar baniba.


Back to business meyasa kuka kirani wajenanan,inda abinyi na kasheshi in bakuda tacewa zanyi gaba"


"Batun contract ɗin da nayi dake sauran wata ɗaya da satuka ya ƙare,inaso ki gaggauta fitarda Lubnah daga cikin gidan ɗana kafin Jawaheer ta dawo daga honeymoon,daga nan kuma kema na sallameki ki tafi kamar yanda mukayi"


"Idan naƙi yin hakan kuma fah"


"Zaki dawomin da ƙudaɗena a yanzunnan ki tafi nafasa aikin"


"Hhhhhh Hajiya zeenah kenan,kin manta na maida contract ɗinmu shekara guda,kuma kin yadda da hakan,sannan kuma a shirin mu babu zancen janyewa daga gareki.


Mai kika maidani bansan mai nake ba?"


"Kinyi kusan wata biyar a gidana,amma har yanzu babu wani yunƙuri dakikayi akan Lubnah,kina nufin kicemin bazaki tafiba ne komai,wai tukunna ma mai kike shiryawa wanda ban saniba."


"Dama to menene abuna da kik sani bayan labarin da Umaruje ya faɗamiki,kuma nina sakashi faɗamuku labarin,ba ra'ayin kansa bane,da ban sakashi ba babu abinda zaku sani gameda ni.


Hajiya ta wani gun bake kaɗai kika nemeni ba,nima na nemeki dana gane mai kikeso namiki,dan haka maganar tafiyata bata hannunki tana hannuna."


"Baki isa ba toh,yau innaga dama zansa ya sakeki"


"Nikuma na saceshi na sace amaren ma,ke harkema na daukeki na kaiki dajin dakika ratsa kika shiga inda nake,inna ɗaureki ko ihu bazaki iya sakewa ba harki mutu.


Saiki zaba,nina tafi saina jiki sweet in law ta"


Maida glass ɗinta tayi tana murmushi tabarsu a zaune Sukuti kaman gumakai.








_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤37••38🖤








Washagarin ranar Asabar aka ɗaura auren Aliyu Abdullahi da kuma Jawaheer Adulmumin & JALEELAH UMAR.
kan sadaki ko waccensu dubu hamsin hamsin.
Gabaɗaya gidaje biyun babu masakar tsinke na mutane.
Lokacin da iyayen Jaleelah sukaji cewar mata biyu za'a auramasa Lokaci guda ƙin amincewa sukayi,bayan sun san yanada wasu biyun dama.
Saidai abune da anriga an yi nisa,an ɗaura aure alƙalamin ya bushe,saidai muyi musu fatan zama lafiya kawai.
Duk da cewar Jabeer ya yage kan cewar bazayyi evrnt ba,amma Hajiya zeenah ta haɗa masa walima na uwa a harabar gidansu,wanda dukkka matansa zasu halatta idan ankawo su da yamma.


Maleekah ce tashigo sashen Bombee taci kwalliyah,ƙannen ango ba zama,ƙaramin akwatine a hannunta,tundaga bakin falon take zuba sallama,Bombee najinta bata kulataba,sai Hilyaan ce ta amsa mata wacce take zaune a kujera.
"Uwargida sarautar mata,munzo dannar ƙirji fah,dafatan dai bakya suma ana zuba miki ruwa,kishiyoyi biyu lokaci guda"
"Mai ya kawoki keda kike tsaka da hidima?"
"Uhm kayan dazaki saka a walima na kawo miki,na bawa Lubnah nata ma,amma fah da alama mommah bataso baki kayanba,dan kamar karta bayar tayi,anty maryam wata ƴar tsamar kukayi ne"
"Wannan tsakanina ne da ita bai shafeki ba kinji,yanzu dai mayar mata kayanta,dan ba wani biki dazanje"
"Habaaaa anty maryam,ni wlh duk cikinsu ke ma nakeso na gani a wajen,dan allah kizo kowa na tambayan ina matar yah Jabeer ta biyu,kubiyu tunda aka fara biki baku fita daga sashenku ba,kowa na cewa baƙin ciki kuke,tunda har anty Lubnah tace zataje dan Allah kema kizo"
"Hmmm to naji uwar surutu naga kina shirin fita ina zuwa,ko matan yayannaki zaki ɗakko daga ɗaurin aure uhm?"
"Ahh habadai,zamuje ɗakko yah Abdulkareem ne a Airport,shi yah Abdulmaleek jiya ya dawo da daddare.
Lahh ashe ma anty maryam baki san Brothers ɗina ba,karki damu ai sun dawo kenan,Abbah ne yace lallai su dawo ƙasarsu suyi aiki,zan kawo miki su ku gaisa sosai."
"Bayan surutu wasu zaki gayyato min sashena kuma,to karma ki fara,maza shige kije zanzo taron"
Juyawa tayi wajen Hilyaan wacce takeyin game a waya,Inayah kuwa bacci take akan kujera..
Yau yini suka zo mata dukkansu,innayi tana bacci itada inna Danejo a ɗaki.


Haba big bros daga ɗaurin aure zai tafiya wajen amarya,ba zaka tsaya Dr.AK (Abdulkareem)ya dawo ku gaisa ba,rabonsa da gida fahi think 7 to 8 month,tun mutuwar sis hafsa koh?"
"Kake zancen rabonsa da gida ya dade,kaima ka dade ai vaka nan,daga Cewa Ka tafi yin wata 3 kaine kusan wata 6,ai abba yayimin daidai daya dawo daku dukka gida,bama ya wancan likitan bansan ya zayyi ba da zaman ƙasarnan yanzu"
"Hmmm ka barsu kawai Khaleel,duk yanda zasuyi ma zasuyine,daɗi sukeji ai su tafi sai sanda sukaga dama su dawo,sun girma har yanzu babu mai zancen aure a cikinsu.
Nikuwa ganinan kawai na buɗi ido na ganni da mata huɗu,kaman ana zamanin Era"
Dariyah Khaleel yakece da ita shida A.M(Abdulmaleek),wanda hakan yasake ƙular da Jabeer har wuyah.
"Haba big bro ka kamanta ratar dake tsakaninmu dakai da yawane,ga wanda zakayiwa nan abokinka ai,shine babban tujuru,ni barina fita Little sis na jirana zamu ɗakko wancan likitan a filin jirgi.
Favorite ɗin Mommah kenan,tun ɗazu take maganar ya iso kuwa?"
"Tunda kuka shigo duniyar nikam dama na zama bango ai mai daɗin jingina"
Jabeer ya faɗa yana sake gyara zaman hularsa.
"Kuma fah JJ Gaskiya A.M yafaɗa,kai kayi huɗu ni banida ko ɗaya,watan gaba zan turo ayi maganar mu da Madeenah dai inaga"
"Hmmm zo mu fara bi takan waccar kafin mu shige wajen Jaleelah"




Harabar da aka gyara domin walimar ba ƙaramin ƙawatuwa yayi ba sosai.
Da ko ina haske wajen yake dukkuwa da cewar yamma ce da rana a sama.
Wajen zaman amare da ango kujeru biyar ne,ta ango daban sai biyu a kowanne bangarensa. An ƙwatasu matuƙa,kuɗi kam in yana magana daya koka..
Gaba ɗaya wajen shigar kala biyu akayi,maza Blue shaddah,mata kuma yadi ne mai tsadar gaske pink.
Da mutane suka fara taruwa sai combination ɗin yadace da decoration na wajen.
Amaryah Jawaheer aka fara Rakowa itada tawagarta ta tsayah a bakin wajen,sannan sai Jaleelah wacce itama ta tsayah a ɗaya bnagaren.
Jabeer ne a tsakiyar su a filin.
Shadda ce a jikinsa kaman ta sauran mazan,saidai kunsan Shigar ango dole zata fita daban da saura..
Suma ga amaren haka take,yadine a jikinsu pink iri ɗaya,saidai anyi masa ado da blue a jiki. Sai mayafin dayake kansu shima blue mai adon roses pink.
Dukkansu sun haɗu babu da yasarwa.
Mc ne yafara magana ganin bayyanar wanda aka kafa taron dominsu.
"To mashaallah amare da ango su bayyana a wannan fili,yanzu zamu buƙaci suje ga wajen zama,saidai zamu buƙaci ango ya riƙe hannun matayennasa yayi musu jagora"
Idonsa yakai kan Jaleelah wacce take kallonsa da cute fuakarta ta cikin mayafinta mai shara shara wacce tasha kwalliyah,murmushi tayi tareda zura hannayenta a cikin nasa,karon farko kenan dayaji tattausan hannunta a cikin nata,nan da nan kuwa yayi ji wata ni'imah tana jiyartar jikinsa.
A ɗaya bangarenma wani hannun yaji yaciga cikin hannun nasa,lallausa kuma mai dauke da hutu.
Juyawa yayi bnagaren itama Jawaheer,wacce ta saka nata idanuwan dara dara a cikin nasa.
A lokaci guda ya runtse hannyen dukka,tareda fara tafiyah suna binsa a hankali har sukayi masauƙi a wajen.
Su Hajiya zeenah wanda suka kallon show ɗin sai murmushi suke,duk da taciki na ciki,dan iyah Jawaheer suka so gani dashi bada Jaleelah ba.


Basu daɗe da zama ba itama Lubnah tashigo filin da nata kayan irinna su Jawaheer,saidai babu mayafin fuskar irinna amaren.
Bayan zaman an shafe kusan minti goma ana jiran zuwan Bombee,mutane har sun fara magana ƙasa ƙasa,don dama kowa labarinta yakeji bai santa ba. Wai amaryar data kawo kanta gidan miji da safe,koya take oho ba wanda yasani.
Takun takalminta suka jiyo ta shigo wajen,daga yanda suka jiyo takalmin mutum zai san kayane a jikinsa haɗaɗɗe mai ɗaukar rai.
Saidai sabanin haka sai ta bawa mutanen wajen mamaki,Hijabi ne a jikinta pink har ƙasa,sai nikaf ɗin data saka blue,hakama mata biyun da suke binta baya,suma iri ɗayane kayannsu da nata,saidai su nasu nikaf ɗin babu ado a jiki irinnata.
Cike da izzah take bada sautin takalmin dake ƙafarta,bayan tasha baƙar safa ta hannu data ƙafa.
Saida suka rakata ta zauna kafin suma suka zauna a wasu kujeru dake wajen zaman sauran mutane.
Tun daga shigowarsu har zuwa zamansu wajen tsitt yayi baka jin bakin kowa,saboda shigar tasu tabawa kowa mamaki sosai.
Banda Jabeer wanda suka haɗa ido ta Bombee ya Jijjiga kai yayi dariyah,dan a iyah saninta yayi na zamansa yasan zatayi yafi hakan ma.
Kuma da alama badan jan hankalin mutane tayi ba,saidan batayi niyyar nuna fuskarta bane ga mutane saboda wani dalili nata.
Abdulmaleek ne yakalli Khaleel tareda cewa.
"Wannan wacce ta shigo yanzu da wasu mata da hijabi itace matar big bro ta biyun?"
"Uhm da alama itace,danni ma bansanta ba"
"Baka santa ba kamar yah,kana garin baka santa ba kuma,taya haka zayyi wu?"
"Haba Abdulmaleek tunda yace maka bai santa ba da alama batason nuna fuskarta ga mutanene,tunda shi ya santa ai shikenan"
"Kai habadai Abdulkareem,duk da rashin son jan maganarka wannan abin jane,zan samu little sis muyi maganar,inason nasan wacece"
"Sai kace dole?"
"Eh dolene kuma kabar wannan zancen,kaima dole dakai zamuje ka ganta taganka"
Ganin Abdulmaleek yasamu maganar sai ja yake,yasa Abdulkareem yin shuru,yayinda a bangare ɗaya kuma Khaleel yake tayimusu dariyah.
Haka aka gama taron kowa ya watse,bakin mutane ɗauke da maganar matar Jabeer da biyu da irin shigar da tayi.


Ba wuce da amaren sashensu ba,wajen Hajiya zeenah aka kaisu,anan zasu zauna kafin gobe su wuce honeymoon.
Itakuwa Bombee da Maleekah suka taho,sai mita take akan meyasa suka saka nikaf.
Kallonta Bombee tayi bayan ta yage nikaf ɗin ta jefar,dan dama duk ya isheta abinka da rashin sabo.
"Wai nikam Maleekah yaushe zaki dunga ɗago abinda yake da ma'anane,kina ganin aikinmu zai tafi daidai idan na bayyana fuskata..
Kaff cikin garin abuja nemana ake ruwa a jallo,ga kuma plan ɗin danake na ceton wannan companyn naku,sannan kuma kinga Hajiya zeenah ma zataji daɗi ganin ban nuna fuskata ba,duk da nasan abube mawuyaci tacigaba dayin moving ɗinta akaina yanzu.
Kinga ni bikinku fah bai dameni ba yanzu ma jinake kaman akan ƙaya nake sabida zafin kayan jikina,bariga na yage su na huta".
"Um nace ba anty maryam kafin ki shiga ɗaki,kinga ƙannennaki kuwa su ya Abdul?"
"Eh nagansu mana,ina masu kama dake su biyu,mai zanmusu to daga ganinnansu"
"Ahh babu anty maryam,allah ya barmana ke"
Daga haka maleekah ta zauna suka cigaba da surutu dasu Hilyan.


Tunda suka dawo daga wajen dinner bayan sunje masallaci suka nufi sashen mahaifiyar tasu,abdulkareem ne ya zauna a one seater,yayinda shikuma Abdulmaleek ke zaune a kujerar da madeena take,danne danne take a waya hankalinta kwance,saidai da alama da saurayinta take,dan yanda take jefa murmushi akan fuskarta jefi jefi.
"Ke wato hira kike da chatting koh,wanene"
"Kai yah abdul,yah khaleel ne fah kawai,shima kuma yana tambaya ta abune"
"Ba waninan naga kina murmushi ai,ku yaran yanzu kun baci da hira"
"Kai A.M,menene bacin aciki,yanzu duk wannan ace bazatayi hira ba,to mai zatayi kenan uhm"
"Eh to naji,ke maganace dama a kan matar big bro,meyasa ta rufe fuskarta ne a wajen taron can,kyaune da ita da bata son a ganta sosai,ko kuma big bro ne yake kiahinta da yawa kai"
"Wlh yah Abdul bansani ba,dam nni ma ganina da ita uku ne inaga,saidai ka tambayi mutuniyarka itace mai yini a sashenta"
"Yess yawwa bari my girl tashigo nasan zanji komai daga wajenta ai,dama ku biyunnan ba'a samun abin arziƙi daga wajenku ai"
"Hmm kaika fiye surutu kai......"
Yana cikin magaanr ne Hajiyah Zeenah ta shigo sashennata.
"Ahh ku kuma anan kuke zaune,duk rashin son mutanene ko mai,amma shikuma wannan fah dannsan ba rashin son mutanene ya zaunarshi a falona ba kam"
Taƙarisa magana tana kallon Abdulmaleek ɗauke da murmushi akan fuakarta.
"Hmmm mommah wai nan ɗin jira yakeyi fah yaji labarin matar bro da tarufe fuska"
Lokaci ɗaya Hajiyah Zeenah ta tamke fuska da taji mai abdulkareem yace.
"Mai zayyi mata idan yaga wacece,nifah banason shiga sharri ba shanu tam.
Kuyi harkar gabanku,karma ku damu da saninta tamm"
Daga jin yanda ta kausasa murya akan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login