Showing 90001 words to 93000 words out of 134612 words

Chapter 31 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8700

ciwo yake na masifar da Sayyada-tateen ta kwana tana balbala mata,ita bata ci zomo ba amma kuma itace da gudu.
"Maleekah yanzu ina magana kikayi kunnen uwar shegu dani koh?"
"Mai zance miki toh Iyah,nayi iya yina,inkinka zakije to kije,amma karki manta idan abba yaji hayaniyah suma yakeyi saboda ciwonsa,kina zuwa kikayi hayaniya zai suma sai an kaishi asibiti"
Zaro ido tayi tareda yin gajeran tunani.
"Asibiti kuma ke ƴar nan,jikinnasa ne ya tashi kaddai"
"Jikinsa bai tashi ba,amma idan kikayi je kikayi hayaniya zai tashi"
"Ahah nikuwa ina zan bar jiki ya tashi ƴar nan,abinda ake neman lafiya tasamu,toh bazajen sashennaku ba,amma ki ƙiramin ita uwar taki,tacan kisaka ayimin kunun tsamiyah ki kawomim.
Ina nan ina jiranki,saura kuma ki maidani goruba ki shanya baki dawo ba"
Taƙarisa maganar tareda zama akan kujerarta tana hamma.
Jijjiga kai Maleekah tayi tana dariya ƙasa ƙasa,dan kuwa kaman tasani bazata dawo ɗin ba,kunun ma aikowa zatayi a kawo mata,bazama ta dawo sashen ba saita manta da zancen auren Jabeer ɗin tukunna.
"Haba fitinnanniyar tsohuwa kai,saida nace abba ya barni na bar kasarnan na tafi karatu yaƙi,babu abinda nake fuskanta a gidannan sai fitinar rigima.
Su ya Abdul sunji daɗinsu basama ƙasar,yah Jabeer ne kaɗai ke shan wahala damu.
Wai meyasa mommah ma take ta auramaka matannan oho,bazata barka ka huta ba.
Barina shiga sashennasa naga mai nene a ciki"
Ƙarisa maganar tayi cikin damuwa tareda yin hanyar dazata kaita sashen Jabeer ɗin.
Tafiyah take tana kalle kalle har ta isa wajen.
Wulgawar mutum tagani tacikin bishiyoyin wajen,saida tasake dubawa taga ashe mata biyune suka nufo hanyar da take,suma da alama sashen zasu shiga.
Tun daga nesa tayi tsammanin dama Matar yayannata ce da mai aikinta,dan su kaɗaine a wajen sai Lubnah,ita kuwa tafi haka girma sosai.
Suna iso wajen Maleekah ta kalli wani wajen,dan bata san mai zatace ba, cikin ƙaramar murya tace.
"Matar yah Jabeer ina kwana"
"Lfy"
Shine abinda Bombee tafaɗa mata a taƙaice kana tayi hanyar shiga ciki.
Binta tayi kallo tace a ranta.
"Daga ganinta kam dama batason mutane"
Hannun taga Hilyaan ta miƙomata tana murmushi,wacce bazata wuce sa'arta ba.
"Barka da Maleekah ykk"
"Uhm barka amma taya kika san sunana?"
"Lahh yaza'ayi ina zaune a gidannan matsayin mai yimata aiki kuma nakasa sanin familyn mijinta"
"Kenan itama tasanmu dukka"
"Babu wanda batasani ba gameda danginku. Karki damu da yanda tayi miki,batada saurin sabo da mutane,amma yanda kika ganta ba haka take ba,tanada kirki sosai antynnaki,kema zaki gane hakan wata rana"
"Uhm nagani kam,kowa yana cewa batada mutunci,amma nikuma sainaji ta burgeni kawai,barina tafi,amma bansan sunanki ba.
Dama lambunsan zai shiga"
"Ni sunana Hilyaan,tunda har kinzo nan kizo mushiga ciki mana ki huta"
"Ahah babu komai"
"Wacce irin ƙanwace bazata shiga gidan yayanta ba,zo muje ciki kada ki damu"
Hannun Maleekah Hilyaan taja suka shiga sashen Bombee.
"Yawwa tunda kingama surutun kinshigo ki ɗauko haidar ya tashi naji kukansa. Ni barina ɗebo kulolin abinci,nasan zuwa yanzu yagama dasu"
Saida tagama maganar ta kulada Maleekah wacce hannunta ke riƙeda na Hilyaan ɗin.
Saurin cire hannunta tayi daga na Hilyaan ta sunkuyar dakai,dan tasan matar yayannata bata tsammaci ganinta a falon ba.
Bata ce komai,duk da tayi mamakin ganin Maleekah ɗin,saima buɗe ƙofar da tayi na sashen Jabeer ɗin tashiga.
"Karki damu ba abinda zatace,zo muje ɗakina"
Binta tayi a baya kaman jela ,saida ta ɗauki haidar a ɗakin Bombee kafin suka nufi nata ɗakin.
Kuka yake lokacin data shiga,amma tana ɗaukarsa yayi shuru yana ƙinkishi.
"Shima idonsa irin na uwarsa"
"Uhm idonsu iri ɗayane"
Daga haka Maleekah bata sake tambaya ba,itama kuma Hilyaan batasake bata ƙarin bayani ba.
Wanka tayi masa a bandaki ta fito,tana shiryashi suna magana haka sama sama da Maleekah,wacce take zaune a bakin gado.
"Naga yau da makaranta ko bakije bane?"
"Uhm banida lecture yau,iyah Madeenah ce takeda,tun ɗazu ta tafi,kefa wacce makaranta kike?"
"Hhhh ni iya diplomer nayi na gama"
"Ayyah kuma kinaso kici gaba?"
"Eh to ina aiki ai bayan nayi karatun,na ajiyene saboda wani dalili"
"Ayyah da alama kinaji da matar yah Jabeer,dan naga tsakaninku kaman ba mai aiki da uwargidanta ba"
"Sai yaya da ƙanwa koh?"
"Ehh mana haka nagani?"
"Kusan hakan muke,dan Allah duk abinda kika gani a sashennan kada ki faɗama kowa mai yake faruwa a wajen,in ban roƙa dayawa ba hadda Hajiya zeenah ma"
"Lahh kada kidamu inshaaallah bazan faɗawa kowa ba,naji daɗin yanda kika sakemin karon farko daga haɗuwa"
"Nima naji daɗin maganarki,let be friend"
"Dama kuwa kaman kinsan banida ita,indai banida lecture zaman gidannan gundurata take,saina rasa mai zanyi,wayama gajiya nake da dannawa. Yanzu nasamu abokiyar hira.
I hope dai bazan takura miki ba koh?"
"Bawani takura,nima nasamu abokiyar hira ai da daɗi sosai"
Bombee ce ta turo ƙofa suna tsaka da hirar .
Suma itan suke kallo.
"Miƙomin ɗana inkin gama shiryashi,duk sanda kuka gama hirar saiku fito ku sameni"



_*SADI-SAKHNA CEH*_








____****🖤🖤****_____




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤27••28🖤








Bayan sati guda da yin baikon mata guda biyun,abubuwa da dama sun faru,ciki harda shaƙuwar data wanzu tsakanin Hilyaan da Maleekah,ga mamakin su kuwa Bombee batayi musu magana ba.
Kullum indai tana nan zatazo suyi girki su gama hirarsu,wani Lokacin ma suke kaiwa Jabeer nasa,ga gulma dasuke na zubawa Lubnah ido..
Shekaranjiya ta tafi gidansu har yanzu bata dawo ba.
Hilyaan ce ta kalli Bombee wadda take zaune tana aikinnata na gado,wato dube dube a system,kana ganinta kasan zaman waje dayan ya dameta,abinka da bata saba ba sam.
Tun ɗazu tana jin su Maleekah sunata hira,bata saka musu baki ba,saida Hilyaan ta kira sunanta tukunna kafin ta ɗago.
"Anty maryam"
"Na'am"
"Nace yau ma da yah Jabeer za'ayi abincinne"
"Ahah badashi zakuyi ba,ai banice kuma mai cidashi kullum ba,nawa lokacin dana ɗibawa kaina ya ƙare,iya mu kawai zakuyi"
"Amma anty maryam Lubnah fah bata nan kuma kinsan yasaba a gida yake cin abinci bakya ganin......"
"Bana ganin me,daɗin nice mai kulada abincin sa ko yaushe,menene aikin matarsa toh.
Kodan kuyi abincin ku zuba a kuloli,amma kada ku kai ku barshi a wajen"
"Kallon kallo Hilyaan tayi itada Maleekah,basudai ce komai ba"
Kaman wani abu Maleekah ta tuna,dan haka ta gyara zama tareda cewa.
"Niii anty maryam kaman mommah ce tayi sanadiyyar auroki koh?"
"Eh ma kike gani"
Ajiye system din tayi tareda maida hankalin ta ga Maleekah,kaman dama tsawon satin wannan lokacin take jira.
"Kwana huɗu da suka wuce tagane cewa ina zuwa sashennan,shine tacemin akan nasaka mata ido,a duk lokacin da naga wani abu yahaɗaki da yah Jabeer na faɗamata,kafin ta kawo mai aikin dazata kulada shige da ficen matansa.
Mai hakan yake nufi kenan,abin yabani mamaki?"
Ɗan murmushi Bombee tayi kafin tace.
"Kenan kin faɗamata cewar ina bawa yayanki abinci"
"Ahah ban faɗamata ba,kullum halin da Jabeer yake ciki yana bani tausayi,burinmu mu ƴan uwansa Allah yabashi macen dazata kulada rayuwarsa,tunda yatashi a rayuwarsa ba abinda yasani sai aiki kawai,in yadawo gida bai san daɗi ba,saboda matar da Allah ya haɗashi da ita.
Daga baya Allah sai ya bashi matar dazai ji daɗin kasancewa da itah. To ance Allah baya barin wani dan wani,sai ya dauke abarsa.
Yanzu kuma dana ganki anty maryam saina Allah ne yadubeshi yabashi matar data dace dashi,wacce irinta yake buƙata a rayuwarsa,mai kulada shi sannan kuma jajirtacciyah wacce zatayi maganin maƙiyansa.
Kota wacce fuska ni kin burgeni,burinsa shine Allah ya shirya tsakaninku,naji daɗi sosai dana ga kina jawo ra'ayinsa da wanann abincin.
Dari bisa ɗari inkina buƙatar taimakona zanyi miki.
Batun kaiwa mommah kuma wannan labarin bazata taba jinsa ba daga bakina dai kam,intana wani abunma na kawo naƙasu a rayuwarku zanyi iya ƙoƙarina akai.
Dan haka anty maryam ki yarda dani,sannan koda kinada wani dalilinki na Kusantarsa,nidai a matsayina na ƙanwarsa ina mai roƙonki da koda na dan wani lokaci ne ki duba halin dayake ciki,sannan kuma ki tuna cewa yanada buƙatarki a rayuwarsa,koda kuwa bazai fito ya furta miki ba"
Hannayenta ta haɗa waje guda tana maganar tundaga cikin zuciyarta.
Sauƙe ajiyar zuciya Bombee tayi tareda barin falon ta shige ɗakinta.
Tashi Hilyaan tayi daga kan kujerar da take ta nufin inda Maleekah take.
"Taji abinda kikace Maleekah,kuma in mai tabbatar miki bazata taba cutar da ɗan uwanki ba,sannan sai inda ƙarfinta ya ƙare idan taga za'a cutar dashi.
Ita ɗin BAƘAR AYAH CE,amma itama cikin ta farine kaman kowacce Ayah.
Abinda mutane suka kasa fahimta shine,tana tsoron da batason wani ya kusanceta har yagano karyayyiyar zuciyarta,kuma yaci galaba akanta.
Amma ina mai tabbatar miki kaman yanda yah Jabeer ke buƙatarta a rayuwarsa,itama tana buƙatar kafaɗar dazata jingina tayi kuka akai,wanda naga hakan a tattare da mijinnata"
"Naga ta tafine batacemin komai ba,ina fatan dai ba bata mata rai nayi bako?"
"Ko ɗayah,da alama abinda kika ya tuna mata abinda yafaru a bayane,amma kada ki damu"
"Abinda yafaru a baya?,wani abune ya sameta?"
"Uhm abubuwa ma ba guda ɗayaba,in badan tanada jarumar zuciyaba da bazaki ganta haka ba,kedai kawai kizuba ido komai zai zama normal inshaaallah"
Cigaba da ƙarƙafawa Maleekah gwiwa Hilyaan tayi,har ta manta abinda ya faru tacigaba da tayata aikin..
Saida suka gama abincin suka gyara ko ina kafin Hilyaan ta raka Maleekah hanya ta tafi.
A bangare Bombee kuwa tunda tashi ga ɗakinta nata tayi shuru na wasu mintuna,ta zubawa window ido batacewa komai.
Abubuwa dayawa ne suka fara dawo mata cikin kai wanda suka faru baya,haƙiƙa kulawar da Maleekah ta nunawa dan uwannata ta burgeta,kuma ta tuna mata rayuwar datayi da tata ƙanwar,da kuma wadda tayi da haidar da ƴan uwansa,sun zauna da ita tamkar ƴar uwarsu ta jini.
Koda dai da rana ɗaya basu taba nuna mata bambanci dasu ba,sai gashi Lokaci guda ta sanadiyyarta sun rasa ɗansu,yaran sun rasa yayansu.
Mai yasa duk abinda ya kasance nata sai yah bacewa ganinta,mai yasa duk inda ta nufah sai wata masifar tafaru a wajen,inaga dagaske ƴan garinsu sukeyi,ita mayyace ba mutum.
A da bata yarda dasuba,yanzu kam tafara yarda da hakan,gaba ɗaya bata abu irinna sauran mutane,duk yadda taso dayin abu daidai abun ya faskara.
Kafin tazo duniyah iyayenta na zaman mutumci zaman lumana,sai kwatsam tashiga rayuwarsu,da farko koyaushe cikin bakin cikin ganinta tana wahala a hannun yara sukeyi,sai gashi daga baya kuma tazame musu fitina wajen dukan yaran kuma.
Tun tasowarta babu wanda tajawowa Alkhairi sai akasinsa,shikansa Maharbi uzairu saida ya koreta daga rayuwarsa tukunna.
Ubanta yashiga mawuyacin hali hakama innarta,hakan bai ƙareba yanzu gashi innarta ta shigo duniya neman ta rasa hanya,batasan a wanne hali take ciki ba.
Bata komai a yanzu a wajenta sai yaronta,wanda bazata iyah buɗar baki tafaɗi ubansa ba,dan itama har yanzu bata san waye ba tukunna,shin da wanne bakin zaya sanar dashi shi waye in ya girma ya tambayeta,tasan dole gudunta zayyi shima,bayan soyayyarsa da aka narka a cikin ranta,batajin dadai da rana ɗaya zata gaza wajen kareshi da dukkan wani mungun nufi.
Dashi aljanun jikinta suke samun galaba take ajiyemusu makamanta idan suka buƙaceta dayin abu.
Batagama da wannan ba kuma ga wani nashirin shigowa rayuwar tata..
Har cikin ranta tasan abinda take son yi ba daidai bane,wato yaudararsa da soyayyarta,amma kuma ta wata fuskar hakanne kadai damarta na samun ɗaukar fansar kisan Jabeer.
Tayi tunanin abun zai tafi normal,saikuma yanzu zuciyarta ta karye dataji roƙon ƙanwarsa.
Allah kaɗai yasan yanda soyayyar ƴan uwa ke burgeta,shiyasa dataji roƙonta lagonta ya karye.
Dafe zuciyarta tayi tareda saurin ɗauke hawayen dayake ƙoƙarin sauƙa.'
'Karkiyi kuka Bombee,bake yakamata kiyi kuka,haramunne kuka a gareki har sai kin ƙaddamar da aikinki,zuciyarki dolene takasance a bushe,ta hakanne kawai zaki iyah kare wandanda kikeso'
Ɗaga kai tayi alamar ta yarda da maganar zuciyar tata,duk da ta wata sigar tasan ba iya zuciyar bace,hadda shaɗanu wanda suke burin suga tana ɗaukar mataki.
Barin bakin window tayi ta taka zuwa inda haidar ke kwance yana wuntsila ƙafafu,yaron ya girma yayi wayo sosai,saboda kulawar dayake samu.
Zama tayi a kusada shi tana ƙarewa blue ɗin idonsa kallo,wanda basuda maraba da nata. Dariyah yake mata irin ta yaran da basusan mai duniyar take ciki ba.
Wanda hakanne yasa ita uwar tasa yin dariyar.
"Ka cigaba da dariyarka yarona,ko kowa yaƙika a duniyah momy tana sonka kaji. In anƙi Bombee to anƙi Haidar ɗinta,wanda yakeson Bombee yanason boy ɗinta. Nasan dole zakaji babu daɗi rashin uba,amma ni zan zameka dukka biyun,babu mai ɗagawa dan Bombee yatsa ya kwana da yatsan.
Kayi farincikinka,momy jaruma ce zata kulada komai kaji"
Ita kaɗai take yiwa yaron magana,wanda shi baima san mai take nufi ba,kawai dariyarsa yakeyi.


Rana ta ɗago tafara zafi,anguwar tsit yara sun tafi makaranta safe.
Innayi ce a bakin rijiyah tana jan ruwa tana ƴar waƙa.
Zamansu a wajen yasa har ta saba da aikin datakeyin na kulada masallaci.
Dasafe zata kaɗe tabarmai ta share ta cika butoci dukka.
Inta gama tashiga ta karbo musu ɗunmame a gidan liman,idan suna yin aiki ko wani abun kuma ta taya matan gidan.
Bayan tagama cika butocin tas ta tabbatar ta gama tukunna ta tafi.
Kayansu da ɗebe a katanga tashiga musu dashi cikin ɗakin.
Kamar ko yaushe Danejo na zaune a tabarma ta tsurawa waje guda ido.
"Sannu inna Danejo"
Ɗaga mata kai tayi tareda yimata itama da hannu
"Jiya munyi magana da yusuf yace min yaji wasu na maganar wajen,daya tambaya aka gwada masa anguwar.
Dayake dare yayi shiyasa ya bar maganar,amma idan zai fita aiki zan sake tuna masa"
A karo na biyu nan ma ɗaga mata kai tayi alamar taji abinda tace.
Abincin karyawarsu tashiga ɗaukomusu bayan sun gama magana da inna Danejo.
Gaisar da matan gidan tayi cikin ladabi,su ukune a gidan kowa da gayyyar ƴaƴan ta,basu da wani ƙarfi sosai,amma kuma akwai rufin asiri.
Ta sunkuya zata ɗauki kwanon tuwon taji wata tsuka a samanta..ɗagowa tayi suka haɗa ido ta wata yarinya wacce zatayi ƙanwa da ita sosai.
Kallonta innayi take cikeda mamaki,dan bata san mai tayi mata ba.
"Aikina banza,ni bansan meyasa baba yake yayibo mana ƴan maula ba,haka kawai baka san mutane ba ka kawo su gidanka kana ciyar da ƙatti,nagida dama bai ƙoshi ba,inaga kuma an sake kawo karoro"
Tsawa wata mata tayiwa yarinya wacce take shanya kaya.
"Ke faɗima wannan wane irin sakarcine,sa'arkice kike faɗamata wannan maganganun,kefah dama bakida kunya da tarbiyyah"
Meyasa zata faɗi haka?,aikuwa uwar faɗima dake ƙofar ɗaki itama ta hayayyaƙo.
"Ahah kinga tsayah Innar yusufu,menene kuma na kawo rashin tarbiyya a ciki,a wani gida daban naje na raineta,inadai tare ta tashi da sauran ƴaƴan. Kuma ai gaskiya tafaɗa,kowama yagaji dabawa wasu ƙatti can abinci,kawai dai haƙuri ake dasu ya ciwon ido,tunda mai gidane ya kawosu"
Masifah suka fara abu ƙarami yanason zama babbba.
Fasa ɗaukar kwanon tuwon innayi tayi,ta koma inda tafito.
Saida ta tsayah a hanya tashare hawayen daya fito mata kafin ta shiga gidan.
Wai da gatansu da komai a wajen ubanta,yau sun ƙare a garin wasu ana yimusu gorin tuwo,badan komai ba saidan dalilin mahaifiyar ta. Wai su kenan da yanzu ta ɗan gani,inaga kuma Bombee wacce tabar gida a ƙananan shekaru,ga kuma innarta wacce take ɗauke da munanan lalurai na tsawon shekara da shekaru?
Bata taba jin tsanar inna laari a zuciyarta ba irinna yau.
Muryar yusuf tajiyo a bayan ta yana ƙiranta,tayi nisa da tunani ma bata jishi ba.
"Innayi innayi"
"Na'am hamma yusuf ina kwana"
Bai amsa mata ba sai tambaya da yayi mata.
"Me kike tunani haka inata ƙiranki baki jiba?"
"Uhm babu komai banji bane kawai"
"Ohk ki ɗauko kayanku kiyiwa cikin gida sallama,zamuje wajen mugani,inshaaallah inada tabbacin wajenne"
Murna ce tacikata fal ciki,jin labarin dayazo mata dashi,dan dama burinta tabar wajennan,suma mutanen suka takurawa su huta.
"Mungode mungode maka Allah yasaka da Alkhairi,babu abinda zamuce dakai sai Allah yajiƙan mahaifa yabaka masuyi maka"
"Kibar godiyar nan haka kije ki ɗauko kayanku,karki damu anyine Dan Allah"
Kaman jira take kuwa da sauri ta nufi gidan da aka basun..
Danejo na zaune sai jin gudun innayi tayi,tana shigowa tafara haɗa kayansu waje guda,kaman tasani kuwa tayi musu wanki.
"Inna Danejo Allah ya karbi addu'ar mu,yau zamu bar wajennan,barina baki mayafinki ki saka mu tafi inna"
Cikin murna take maganar,wanda har hakan yasaka Danejo yin murmushi itama..
Kasancewar basuda kaya dayawa,nan da nan ta haɗa kayan tafito dasu waje.
Kaiwa tayi motar yusuf ɗin ta dawo da rawar jiki.
Inna Danejo taraka mota ta zauna kafin ta shiga cikin gidan su yusuf ɗin,ɗunkule hannu tayi tareda jan numfashi,dan Allah yagani batason hulɗa da mutan gidan.
Sallama tayi basu ma jitaba,har yanzu faɗan da aka fara da ita bai ƙarisa mutuwa ba.
Wajen babbar matar gidan ta nufa tareda cewa.
"Innar yusufu mu zamu tafi,hamma yusuf ya samo gidan da addah ta take"
Tun kafin wacce aka faɗawa tayi magana sukaji ance.
"Allah yayi lokaci yayi,allah ya tura ƙeyah abu yayi kyau,ni dama tunda kuka shigo gidannan na ƙyalla ido na ganki hankali na bai kwanta ba,nasan ko yaushe za'a iyamin shigo shigo ba zurfi,amma tunda zaku tafi na saki raina,kuje umma da gaida ashshe"
Matar yusufu ce mai maganar tana tafa hannu,fitowarta kenan daga ƙofarta taji maganar innayin,dan ko bacci bata iyawa sosai,tayi ƙiru da kunne tana jira taji ta inda mijinta zai aureta,saikuma taji zancen tafiyarsu.
Jijjiga kai innar yusufu tayi tareda yiwa innayi fatan Alkhairi.
Rashin basu san tafisu matsuwa tabar musu gidanba.
"Shikenan mu zamu tafi,dan Allah kiyiwa mallam godiya,mungode sosai da taimako"
"Bakomai innayi ki gaida Addar taki kinji,Allah ya tsare"
Da sauri tabar gidan saboda zumuɗin su tafin.
Tana shiga motar kuwa yusuf ya tada motar,dan dama ita yake jira ta fito su tafi.


"Kin tabbatar kuwa yadda yafaɗamiki haka kikeyiwa maganin"
Brr Na'imah ce tayi maganar,tana tsaye a bakin ƙofar ɗakin Lubnah na gidansu,ta jingina da jikin ƙofaj.
"Eh mana mom,nazuba jinin na farko,nanda sati biyuma zan sake zubawa,inayin yadda ya faɗa.
Aina matsu nagama haɗin maganin naga wanne iri aiki zayyi.
Mom yakike ganin tasirinsa toh"
"Maganine mai ƙarfi,koda de da rana ɗayah kada kiyi wasa dashi,sannan kuma inkikayi amfani dashi to fah ki tabbatar bakiyi sati guda ba batareda kinga wanda kikayiwa ba,shima kuma ya ganki,idan ya wuce sati guda baku haɗuba,to fah ƙarfin maganin zai fita daga jikinsa,har sai kinsane ƙunzugu dashi yasake kusantarki tukunna.
Yawwa dafatan kina sane da kashedin daya miki koh?"
"Tabb ina zan manta,ina sane dashi,wow i can't wait na mallakeshi a hannuna,kice na kwantar da hankali na ma matannsa su xo,ta hakane zan baza mulki a tsakanin matansa yanda nakeso"
"Hakan kam ƴa ta,nima zanso ganin ranar dazaki fito tamkar jaruma a cikin matan,sai abinda yace zasuyi,matuƙar suna san zaman gidansa,yayinsa shi kuma sai abinda kikeso zayyi"
"Kai abin yayi wlh"
Lubnah tafaɗa tana buga hannu akan kujera cikeda jin daɗi.
"Nima zanso ki mallakeshin a yanzu,tunda zulumgum yake son baki wannan maganin nahanashi,saboda amfaninsa baizo ba,sai yanzu tukunna"
"Amfani kuma mom,mai haɗin maganina dakuma wani abun"
Shu'umin murmushi brr Na'imah tayi tareda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login