Showing 84001 words to 87000 words out of 134612 words

Chapter 29 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8676

yake tsaye a ransa kaman zancen yaron,ko ya akayi ta samu yaron tabbas yanaso ya sani dole.
Ba su Bombee ne suka bar inda suka zaune ba har sai wajen magriba tukunna,zuwa lokacin sun gama tsara yanda komai zai tafi..
Misalin wajen ƙarfe tara khamees yaƙirata,ɗauka tayi batace komai,komai ya faɗamata daga ɗaya bangaren ta tashi da sauri ta zauna.
"Me kake cewa? Inna da innayi sun gudu daga gida sunzo nemana? Ohh shittt ya akayi ma ban ƙira Muruje naji ya suke ba.....tsawon wanne lokaci...."
"Sati ɗaya,shin kana ganin suna cikin garinnan kuwa?"
"Ehh to in suna cikin garin yaci ace ai sunzo wajenki koh,tunda kince kin bawa inna Address ɗinki"
"Hmm ba lallai sunada address ɗin ba,in babu damuwa inaso ka ɗan nemo min clue na inda suke, kasan basu taba fitowa ba sai wanann karon,kada a samu matsala"
"Ohk shikenan kada ki damu,inshaaallah baza'a samu matsala ba"
Jefah wayar tayi akan gado tareda zama ta dafe kai na ɗan wasu mintuna,da taga hakan bazai mata ba ta barbaza gashin kanta tareda jan gwauron numfashi.
"Why innayi mainene haka yasakaku baro gida ku biyu meye dalili ,wa yace kuzo nemana,inada dalilina na barin inna a can,meyasa zaki kawo ta nan? .....to inna laari fah taya innayi zata gudu lokaci guda ta.............akwai abinda yake faruwa,ɗayan biyu.
Tabbas innayi taga abinda Inna laari take,ko taji zata kashe Innnata ko kuma zata kasheta itah.
Shiyasa suka gudo nan kenan?"
Ta daɗe ita kaɗai tana maganganu kafin ta tashi tanufi bayi..
Ruwa ta watsa a jikinta saboda zafin da ake,da alamar hadarine yake haɗuwa.
Kayan Patrol tasaka baƙaƙe misalin Wajen sha ɗaya zata fita.
Karo sukayi da Hilyaan tazo dama madarar Haidar,saboda kada ya dameta da kuka.
"Anty maryam lfy ina zakije haka da Darenan ana shirin yin ruwa?"
"Wani wajen zanje,yanayin a haka yafi daɗi ai,bakiji ance Duhun Damina itace sa'ar barawo ba,to hadda irinmuma masu bincike.
Waje tafita tabar Hilyaan a tsaye kaman gunki,dan ita yanzu ta daina bata mamaki ma sai tsoro.
Kai tsaye sashen su Lylah ta nufah,kaman yanda tayi tsammani kuwa akwai hasken fitila a store ɗin wajen.
"Yaune 18 ga wata,baki saba ranar da kika saka ba rannan kenan?"
Daidai kaiwa kunnenta taji ana magana.
"Ga takardun yabani,ka tabbatar ka musanya takardun project ɗinsa da waɗannan,karka taba bari a samu matsala,kaine secatrynsa nasan ya yarda dakai sosai bazai zargi kaine ba.
Na zabi haɗuwa dakaine anan saboda Karka a ganni a wajen na haɗu dakai,ka fahimta dai koh?"
"Ehh na fahimfa Hajiya,amma wannan abun fah hadda mijinki da duk companyn zai shafa,domin zai fita ne daga hannunsu ya koma wani wajen daban"
"Ina ruwana toh,nidai tunda zai biyani maƙudan kuɗaɗe ko gidannan ya karba mana ina ruwan ni.
Ina ganin kuɗaɗen a hannuna zanyi fiyattt na bar ƙasar shikenan"
"Uhm zan fita ni yanzu,idan nayi mintuna goma da tafiya saika bar wajen,saboda kar in case wani ya ganmu"
Tana gama faɗin hakan siƙaf siƙar ta maida lullubin kanta ta fita.
Saida Bombee tajira tabar wajen kafin ta shiga cikin store ɗin inda mutumin yake tsaye.
"Madam akwai wani abune bayan......"
Tun kafin ya gama maganar Bombee ta kifah masa naushi a fuska,faɗuwa yayi yana dafe ta inda takai masa hari.
"Bani takardun Yanzunnan"
Tafaɗa tana miƙa masa hannu.
"Wacece ke?"
"Shine yafimaka amfanin ka sani a yanxu,zaka miƙomin takardun ko saina cewa wannan ya aikata abinda na sakashi"
Takarisa maganar tana nuna masa matarsa da ƴarsa an sata wuƙa a wuyansu suna bacci a gida.
Zaro ido yayi jiki yana karkarwa ya miƙa mata file ɗin.
"Yawwa yaron kirki,yanzu kaje gida ka kwanta da iyalanka sannan kuma kace mata kayi yadda tace,idan kuma tasake saka ka wani aiki ka tabbatar saina sani tukunna.
Kuma daga koda wasa naji kayi wani abun dazai cutar da companynnan saina saka fetur kuna bacci na ƙoneku. Dafatan ka jini sosai"
"Ehh.... Aradu na jiki,in so kike ma zan faɗamiki duk abinda nasani yanzu da kuma wanda yake sakamu,nidai kiyimin lamuni nabar garinma"
"Babu inda zakaje kana nan,batun wanda yake sakaku kuma nasan waye yake shi basai ka bata yawun bakinka ba"
Hanyar side ɗinsu ta nufah,zuwa lokacin har an fara yayyafah mai ƙarfi.
A ledar data zo ta ita ta saka takardun sannan tafara gudu gudu sauri sauri zuwa sashensu.
Kasancewar da ɗan tazara kafin ta isa har ta jiƙe zaraff,daidai shigowarta harabar wajen ta cire baƙar hular da take kanta,jiƙeƙƙen gashin kanta ya kwanta a fuskarta da ƙafaɗarta..
Hannayenta ta ware a cikin ruwan yana bin ko ina a jikinta,komai ta tuna ita kaɗai tafara murmushi idanuwanta suna rufe.
"Hmmm fashi kika iyo mana a cikin gida na ganki da kaya irinna barayi?"
Cikin sanyi yayi maganar a kusan kunnenta,dayaga har ya zo kusada ita batasan yana wajenba,ta tafi duniyar tunani.
Zabura tayi zata matsa sulu ya ɗebe ta,dan bata tsammaci kallon ɗan adam a wanann lokacin ba,hakan ma kuma kusada ita,bataji motsin zuwansa ba saboda ruwan da ake.
Saurin riƙota yayi ya ranƙwafah bata kai ƙasa ba..
Kallon fuskarta yake wadda hasken ƙwoyayen wutar wajen suka haske.
Yayinda itama shiɗin take kallo da nata zararrun idanuwan.
"Sakeni"
Tafaɗa a kausashe,bayyi mata musu ba kuwa ya saketan,jin tana shirin Kiss ta ƙasa yasaka ta jawo rigarsa suka faɗi tare cikin ruwan.
Tashi sukayi tana riƙeda hannunta wanda ya bugu,kallon hannun yake yanda tariƙe gwiwar wajen,kuma shima yaji ƙarar da hannun yayi.
"Am sorry barina gani"
"Kaga me,saikace kana magana da ƙaramar yarinya,ai duk laifin ka ne,menene na zuwa kusada ni kayi magana"
"Dannaxo kusada ke nayi magana sainace kiji tsoro,ke mekike a tsakar dare da baƙaƙen kaya?"
"Ina ruwanka da abinda nake zaman ka nake komai,saika barin in kaji ance an sace wani abu ko yanka wani gobe,saika tuhumeni"
Hannunta takama da ɗayan taja saida yayi ƙara,jijjiga shi tayi tareda miƙewa tsaye.
Duk abinda take Jabeer yana kallonta,yanda tagyara buguwar tashi ɗaya yasa ya share tantamarsa,tabbas ta taba aiki a wani wajen masu horon.
"Baki faɗamin sunanki ba miss sannan kuma idan bazaki damu ba inason mu haɗu akwai tambayoyin dazan miki,sannan haka kike a kowanne lokacin bakya shakkar nuna sassan jikinki a gaban mutane,hmmm ba mamaki naga hadda sakamakon hakan kikeda shi.
Juyowa tayi cikin ƙosawa,takowa tayi har zuwa inda yake.
Gabaɗaya kayan jikinta sun lafe kana ganin komai nata a fili,sakamakon ruwan daya jiƙa ta jarabb,wata tafiyar girgiza take da gangan wacce batayiba ɗazu.
Tsugunnawa tayi a inda yake zaune bai tashi ba.
"Mutum yagani ya ƙyasa ma bai da ikon tabawa horone,ohh dama karkatacciyar bishiyar kuka ka ɗaukeni mai daɗin hawa ga kowa,wai ........to tun dare bayyimaka ba ka sanja wannan karatun gamedani.
Ni bishiyar giginya ce,sai jarumine zai iya kaiwa ƙarshe bai faɗo ba. Batun ɗana kuma kama dauke kanka daga gareshi,in ma bincike kake ka gano ubansa ba samu zakayi ba,nice nan mai shi ba wani ba"
Bata bari Jabeer yaƙara cewa wani abu ba ta kama hanyar sashenta,har tayi nisa ta juyo ta kalleshi,zuwa yanzu an fara taƙaita ruwan.
"Husbyy in magana kake so dani zanzo gareka,kawai ƙira na zakayi zaka ganni,zan turo maka numberta byeee"






_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤23••24🖤








Ajiyar zuciya yasake bayan tabar wajen.
"Wai mommah anya kuwa ba aljana ta auramin ba,wannan ce har uwa zata zaga uwa duniya ta auro maka ita,ita da take jin haushin halayyar lubna batada tarbiyya amma kuma ta auro wannan,indai nayi tunani daidai wannan tafi ma lubna rashin daɗin zama.
Babu shakka akwai dalilin daya saka mommah ta kawota cikin gidannan,duk yadda zanyi nasan bazata faɗamin ba,wannan kuma batayi kama da wacce zan tambayi abu a wajenta ba..
Tashi yayi taga cikin ruwan inda suka faɗi shida Bombee ya nufi sashensa,dan dama baccine yagagara kamashi shiyasa ya fito.
Gabaɗaya ya rasa gane wanne irin ciwone Lubnah,duk lokacin dayazo mata da buƙata sai tayi nesa dashi,yafaɗamata su je asibiti amma taƙi amincewa.
Duk da ma ba wani gamsar dashi take sosai ba,amma dai yafi babu da halin dayake ciki.
Ga waccar fitinanniyar yarasa dalili sau uku kenan haɗuwarsa da ita,amma kowanne idan sukayi sai yakasa ɗauke kansa daga gareta.
Yana cikin tunanin ne ya iso ɗakinsa,har yasaka kai zai shiga bayi yaji alamar ƙarar massage.
Dubawa yayi yaga number ce da kuma massage a ƙasa.
"Yane sai yanzu kasamu damar barin wajen,abinnan yana bani mamak,mai mata biyu yana shirin sake yin wasu mata biyun,amma kuma abu kaɗan sai yasakashi hawa on.
Uhmm da alama kenan ko matarsa tagaja kokuma shiɗin nada doguwar ƙishirwa,ohhhh karfa kace nafiye surutu,aje ayi wanka da ruwan sanyi naji ance yana taimakawa.
Saida safe Mai shirin zama angon mata huɗu"
Tsuka yaja ya jefarda wayar,ko mai yasa ma ya tsaya karanta message ɗin oho.
Banɗakin ya fada a zuciye,wato ma duk da duhune har tagane yanayin dayake ciki,kodah yake ƴar duniya ce mai buɗaɗɗen ido.
Har yagama wankan yafito ya kwanta yana tunanin abinda ya faru tsakaninsa da Bombee ɗazu.
Lubnah ce a zaune akan dinnng tana zubawa Jabeer abinci,wanda yake ta danne danne a waya.
"Honey ina ta magana baka jini ba,yaka kwana jiyah?"
"Yanda kike so na kwana mana Lubnah,bahaka kike so na dunga kwana ba kaman marar mata"
Wata dariyar jin daɗi tayi,jin ashe yana sonta ya damu da ita,kuma yanzu tagano ba abinda yake haɗa tsakaninsa da Bombee.
A ranta tace"ashe dai maganin ya fara aiki tun kafin ma na kammala aiki dashi"
"Ahhh honey karka ce haka,kasan nima na damu dakai,kawai dai lalurine yasaka,amma kasan yanda nayi kewarka kuwa,kaima ai zakamin shaida akan haka"
Bayan ta gama zuba abincin miƙa masa plate din tayi gabansa,kallon abincin yayi kaman bazai ciba saikuma ya dauki cokalin.
Fiiii yaji an ƙwace cokalin dayake hannunsa,yayi zaton Lubnah ce,saikuma yaga ta gefensa aka karbi cokalin.
Jiyawa yayi suka haɗa ido da Bombee,wacce ta cuke fuska tareda ɗaga masa gira,alamar yane.
Lubnah ce ta tashi daga kan kujerar da take,dan tsabar masifa tana cinta.
"Kututu ke wacece da har zakizo cikin sashena batareda izinina ba,kuma ki karbi cokali daga wajen mijina,mai keki nufi da hakan,kina zargina ne da saka masa wani abun dazaki hanashi ci?"
Dariya Bombee ta shaƙe da itah kana ta ɗora da cewar.
"Kinga niba wannan ce takawoni ba,bance ki fallasa kanki tun banzo kan wannan aikin ba.
Dalilin zuwana shine a ina aka ce yazo sashenki yaci abinci ranar girkina,kodan banyi magana ba sai ayimin abinda aka ga dama?"
Taƙarisa maganar tana ɗaure fuska tareda naɗe hannayenta a kan ƙirjinta,kallon Jabeer ɗin take wanda yariƙe kansa,da kuma Lubnah wacce ta tsaya sheƙeke ta saki baki na mamakin Bombee ɗin.
"Hhhh ranar kwananki wannan kuma ke kika sanshi,Jabeer bai tana yin matar dana raba kwana da ita,sanda nagana dama ina neman sa babu ruwana da kwananki,kaman yanda yanzu anan yazabi yaci abinci kuma baki isa ki hana ba"
"Zakuwa a fara rana kwana daka kaina,kuma wlh in kinga yaci abincinnan ban ɗau mataki ba to ƙaddara na mutu,in inada rai kuwa hakan bazai faru ba.
Mijina tashi mutafi nayi Girki tun ɗazu nake jiranka,yau ranar kwana nane,daga nan har zuwa sati guda masu zuwa,saboda karka manta bakayimin sati guda ba yadda akeyiwa kowacce mace,idan kuma zaka tsallake hukuncin mai sama toh,in ra'ayinka ne bazakaci abinci na ranar girkina to kaje kaci a waje,idan kuwa kazo sashen ta kaci abinci a ranar...........karkuyi ma hasashen hukuncin dazan ɗauka akan hakan"
Ajiye cokalin tayi a kan tebur ɗin tareda nufar hanyar waje.
"Lallai nayarda wuyanki yakai yanka bakisan dawa kike karawa ba"
"Lubnah ce wacce take kashe kishiyoyinta saboda tana tsoronsu,abinda ni kunya ma zai bani da wannan tsoron,innaga dama yanzu ma zan iya kasheki,dan haka bashine farau ba a wajena,nakashen rayukan da bazan taba iyah ƙirgawa ba,kuma na mutane,keda kika kashe guda biyu kinsan bazaki haɗa kanki dani ba,dan ko iyayenki ma a tafin hannun suke"
"Hmmm kinzo kina tadamin jijiyoyin wuya akan kwananki,kinsan ranar kwanannaki ne kika barshi ya kwana a sashensa jiyah?"
Hannun tasaka a bakinta tareda kallon sama,kaman mai wani muhimmin tunani.
"Uhm Lubnah kenan,duk wanda yaga mijinki yasan bai samu nutsuwar iyali ba na kusan sati guda. To ke mai kike kenan haka ta faru.
Ina mai gagaɗinki fah,sama tayiwa yaro nisa saidai ya kalla da ido.
Husby ina jiranka kada abinci yayi sanyi"
Taƙarisa maganar tana huro masa air kiss.
Duk abinda suke har suka gama in dutse yayi magana to Jabeer ma yayi musu.
Komawa Lubnah tayi ta jangwaba akan kujera,lallai Bombee tana bata mamaki,dama akwai irin waɗannan mutanen?.
Tashi Jabeer yayi ya nufi bakin ƙofah,da gudu Lubnah tazo kusada shi tana narai narai da ido.
"Wai naka nufin wajenta zakaje kenan,bazaka ci nawa abincin ba"
"Kinga ni office zan nufah inada abinyi,wannan childish ɗinnku karku sakoni ciki,kinga nayi muku magana tunda kukeyi"
Ajiyar zuciya Lubnah tayi lokacin dataga ya shigo motarsa yabar wajen.
Hilyaan dake tsaye a bakin labulen windowan juyowa tayi inda Bombee take zaune.
"Anty maryam ya tafi bai shigo yaci abincin ba"
"Eh nasan dama bazai shigo ba,amma itama baici nata ba"
"Uhm fitowarsa kam baikai ace yaci abinci ba,abinda yabani mamaki shine,baya cikin agendarki kuma basonshi kike ba meyasa kike shiga lamarinsa saboda Lubnah toh?"
"Saboda shine ma babbar agenda ta kaman yanda na faɗamiki jiyah,ina son kullah alaƙa dashi koma wacce iri ce,ko ƙiyayya ko kuma soyayya,tahakane zan san mai yake faruwa cikin sauƙi.
Ƙarfe huɗu yake dawowa na yamma,kafin sannan ina buƙatar yimasa girki"
"Mee girki,yau kece mai yin girki anty maryam,uhm wanda ke abincin ma bai dameki ba. Da alama su miji an samu ɗageshim"
Harara ta watsa mata,da sauri tabar wajen tana dariyah.


"Iyani inason ki samomin mata mai ɗan shekaru,da kuma maza biyu wanda zasu dunga kula da sashen Jabeer,saboda babu masu aiki a sashen"
"Hajiya basu yakamata su samu masu aiki ba,kowaccensu naga kaman tana da mai aikinta fah"
"Ba irin wannan mai aikin ba,inason wacce zata dunga kulamin da shige ta ficensun tana kawomin labarin.
A ganinki nakai wannan hatsabibiyar yarinyar sai nayi shuru na zuba ido,tunda tazo gidan yau satin guda kenan banji tace komai ba.
Ina ta buƙatar saka wacce zata dunga kawomin mai take ƙullawa itada lubanan"
"To shikenan Hajiya na fahimta,zan bada cikiyar mai aikin,mai ɗan shekaru wacce bazata bada matsala ba koh"
"Ehh inkin samo kimin magana"
Da jaka a hannunta dama taci ado,da alama wani waje zata je.
Ƙarfe uku tanayi Bombee ta shiga kitchen tayi abinci mai rai da lafiyah,a haka babu wanda zai kalleta yace tashiga makarantar koyon abinci,wacce Hajiya Zulaiha tasaka su itada Nu'aimah,banda wanda suke a gida.
Jijjaga kai tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,lokacin data tuno maganar Hajiyan.
"Ki koyi iyah abinci da sarrafashi maryam,duk da kina ganin ke sojace amma ai ke macece,watarana hakan zayyi miki amfani,ita zuciyar namiji da kike ganinta,ana iya kamata da abinci. Bakisan shiyasa na kama ta babanku ba,innayi magana ta zauna kawai"
Bayan barinta barrack shiyasa batason yin abinci,saboda duk lokacin datazo yi sai hakan ya tuna mata da Haidar da kuma familynsa,wacce har yanzu takasa yarda cewar ba itace silar shigarsu cikin halin ni ƴasu ba.
Da wuri tagama abincin tazuba a kuloli,wanda tun zuwanta sashen sai yanzune tayi amfani da kitchen ɗinma sosai.
Ɗaukar abincin tayi ta nufi ƙofar dake corridor ɗin gefen ɗakinta,wacce zata kaita sashen Jabeer ɗin.
Ajiye abincin tayi ta buɗe wajen da makulli kana ta shiga.
Kalle kallen sashen takeyi,babu laifi kam ya haɗu matuƙa,kuma yayi daidai ta sashen namiji.
Ƙofofi shidane a falon,huɗu wanda suka haɗa sauran sashenne,ɗaya ta shigowa daga waje,saikuma ɗaya wacce zata shigar da kuma wani fili,inda anan ɗakuna biyu suke,oppsite ɗinsu kuma kitchen ne da dining a wajen.
Gun ta nufah ta ajiye abincin a dinning table.
Fridge ɗin wajen ta buɗe,tayi zaton zataga abubuwa dayawa,ga mamakinta babu komai sai ruwa kawai sunyi sanyi sosai.
Komai na sashen kaman bamai mataba,babu datti kam amma kuma babu gyara ma,da alama inya shigo yayi abinda zayyi ya fita shikenan,dan babu abinda aka taba a wajen.
Fitowa tayi daga sashen ta koma nata.
Hilyaan ce akan machine na gudu tasaka earpiece a kunne.
Saida ta kashe abin kafin tajita.
"Ohh sorry anty maryam ban jiki ba"
"Naga alama ai,shin akwai sauran snack ɗinmu dakikayi mai yawa?"
"Ahah babu sosai sai gobe zanyi,mai zakiyi dashi?"
"Nasamo hanyar kama wancan mutumin a hannuna ne batareda wata wahala ba"
"Kaman ya?"
"Kedai ki bari,gobe akwai aikin dazamuyi"
Yamma lilis Jabeer yashigo gidan,dan yau gabaɗaya basu zauna ba shida Khaleel da kuma managenrsa,kan projest ɗin da companynsa yakeyi.
Har yayi hanyar sashen lubna yadawo ya shiga nasa,yanda kansa yake yi masa caji,yasan ba komai zata ƙara masa ba sai ciwon kai.
A kasalance ya shiga falon kaman koyaushe,har yazo shiga ɗakinsa sai kuma idonsa ya hango masa kulolin dake kan dining ɗin.
Da farko yayi zaton na Lubnah ne,saikuma ya tuna bata kawo masa abinci,saidai yaje sashenta yaci.
Takawa yayi a hankali zuwa wajen kilolin ya buɗe guda ɗayah.
Farar shinkafa ce zara zara da itah,an dafata da dankalin turawa da kuma karas da green beans.
Ƙaramae ya buɗe inda lafiyayyiyar miyar nama take,lutsu lutsu da ita tasha mai sai kamshi take.
Ga kuma jug na lemon kwakwa da abarba.
A yanda yaga abincin bayyi masa kamada na Lubnah ba,sannan yasan Hajiya zeenah ma bazata kawo masa abinci nan ba.
Ɗakinsa ya nufah yayi wanka yasaka kaya marasa nauyi,kafin ya dawo wajen abincin domin ya ɗan taba,dan inyace bayajin yunwa yayi ƙarya,irin zirga zirgar daya wuni yana yi.
Wasa wasa shida zaici kaɗan saida yakusa ganin bayan abincin,dan babu laifi yayi masa daɗi sosai.
Ruwan lemon ya tsiyaya a cikin cup shima ya kora,har lumshe ido yayi,yanda ƙamshin sa yabugeshi a hanci.
A bangaren Lubnah kuwa dama bata wani ajiyemasa abinci ba,dan tasan ba lallai yake cin abinci ba a yanzu,kota kawoma sai yace yaci kafin ya taho,shiyasa tana gama abinda zatayi ta hau danne dannen wayarta.
Washagari yafito zai tafi office yaga an ɗauke kwanukan jiya,an saka wasu sabi daban.
Da sauri yanufi wajen ya buɗe.
Egg rolls ne da kuma bread anyi masa suyar ciki da kwai mai haɗi,saikuma kunun gyaɗa mai zafi.
"Uhm duk yadda akayi waccar fitinanniyar ce ke ajiye abincinnan,kuma nasan dole akwai wani dalili nata,dan batayi kama damai biyayyar gidan aure ba sam.
Koma menene a ranta ni gaba takaini,wanne darene jemage bai gani ba"
Kafaɗasa ya ɗaga alama ruwanta,ba kunya ya zauna yaci abincin ya ƙoshi yauma.
Sashen Lubnah ya nufah bayan yagama domin yaga ya take,yanason shiga sashen Bombee domin sauƙe haƙƙinta koda kaɗanne,amma kuma haka kawai bayason abinda zai haɗasu da ita sosai,dan kwata kwata batayi kama da irin matan dayake so ba sam.
Babu kowa a falon wayam,yau ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login