Showing 51001 words to 54000 words out of 134612 words
yanzu da shigo.
Ɗauke hannunta tayi daga bakin ƙofar inda ta dafa,kafin ta ƙariso cikin falon,a kan kujera mai ɗayah ta zauna wacce take facing ɗinsu.
"Sannunku,bansan ku suwaye ba,amma labari yazo kunnena tun lokacin da kuka buɗi baki cewar kuna neman Bombee a karo na farko. Lokacin danaji labarin wai wasu sunxo nemana nayi mamaki.
Mai kuke nema a gareni haka, dahar kukebin gari kuna nemana,koma menene nasan babban abune. Dan a lokacin da muruje yabaku labarina nayi zaton zaku haƙura kukoma inda kuka fito,saikuma kuka bani mamaki,dasafe ma sai aka ganku kunsake fitowa nemana"
Tsuru tsuru sukayi,lallai wannan matar taci wannan labarin da sukaji,wato duk yawon dasuke na nemanta tana sane kenan.
Har Hajiya zeenah ta buɗi baki zatayi magana kukan yaro ya ƙatseta,wanda Hilyaan ta shigo dashi tareda nufar inda Bombee take zaune.
Hannu ta miƙa ta karbeshi tareda tambayar Hilyaan ɗin.
"Mai yasameshi hakane,baya kuka irin haka akai akai,kuma likitan yazo ya dubashi kaman yanda nace?"
"Eh ya dubashi,inaga fah kaman ɗan zazzabine yake damunsa,sannan kuma kaman madarar da aka fara bashi jiyane yajawo hakn"
"A daina bashi madarar nan sai yayi wata shida tukunna,har yanzu bai girmaba,nidama nasan madarar nan rayiwa jikinsa girma,ki fita da ita daga gidannan,nafasa bashi ita,zan rage aikin zirga zirga na dunga shayarshi kawai,he need my time too,not only my matter"
Karban yaron tayi tana shirin fitar masa da mama,Hajiya zeenah ce tayi sauri bugar iliyah akan yabasu waje,da sauri kuwa yatashi bayan ya suri tiren kayan marmarin.
"Ohh sorry fah,banida manner ne sosai wani lokacin"
Bombee tafaɗa ko a jikinta lokacinda take sakawa yaron abincinsa a baki.
"Uhm ......uhm bakomai ne ya sakani tasowa daga inda nake nazo wajennan ba saidan wani taimako danake son kiyimin"
"Taimako wanne iri kenan kuma a guna?"
"Inasone ki auri ɗana na wani lokacin ƙayadadde,daga baya kuma sai a raba auren"
"Aure nikuma????? Kinsan mai kike cewa kuwa?"
"Ehh aure,karki damu babu abinda zai haɗaki da ɗana idan shi kike tunani,aikin dazakimin ba akansa bane,akan matarsane"
"Hhhhh nikuwa nasan ba abinda zai haɗani da danki,a labarin da aka baki da kuma wanda kika gani,kin shaida inada ɗa batareda aure ba,babu uwar dazata yarda ta haɗa ɗanta da mace irina,dole akwai abinda kike buƙata gameda kalmar auren.
Karki ɗaukeni jahila kaman yanda kikaji labari,wancan a dane ba yanzu ba,ki tafi kaitsaye ki faɗamin me kikeso"
Taƙaitaccen labarin lubna Hajiya zeenah tabawa Bombee,da irin ƙarfin ikon ubanta da kuma abinda take aikatawa. Sannan kuma taƙara da cewa.
"Ta hanyar aurene kawai zaki iya min maganinta,kasancewar ubanta yanada babban matsayi a kotu,idan abu kikayi mata ta hanyar kishi baza'a zargeni da komai ba.
Tana da ƙarfin hanya ta kowacce siga,idan nace zan turasashi yasaketa kuma tayi masa asirin dazai mutu a ranar,dan haka nayi bincike naga ke kaɗaice nakeda wacce zaki iya yimata abinda dakanta zata nemi sakin batareda matsala ba"
Ɗan guntun murmushi Bombee tayi,danta fahimci inda zancen Hajiya zeenah ya nufah.
"Hhhhhhh kuma a yanda kika ban labari sai kikaga nayi kama da wacce mutum zai taso yazo yasakani abinda yake so na matsalarsa na magance masa,shin kama nayi miki da mai taimakon gyara aure?"
"Ba taimakona zakiyi kawai ba,aiki na kawomiki,auren iyah Wata shidane kawai,ko kuma gwargwadon yanda kika karya lagwonta,sannan zan baki Miliyan Ashirin idan kikayi min aikim"
"Hhhhh miliyan Ashirin?? Kibar wannan zancen,nizan tsara komai yanzu,shin na yarda da zanceki ko kuma akasin haka.
Hilyaan zata karbi bayanan komai danake buƙata gameda lamarin,zanyin bincike nan da gobe.
Ki saurari aikana daga nan zuwa goben,na sallameku zaku iya tafiyah idan takarbi bayanin danake so"
Daga haka Bombee ta ɗauki ɗanta tayi wata hanyar daban.
Bayan tafiyar tane Hilyaan ta zauna da labtop ta karbi duk wani abu daya shafi Lubnah da kuma shikansa Jabeer ɗin.
Mota Bombee tasaka aka maida su Hajiya zeenah inda aka ɗaukesu,inda suka shiga gidan da jiran tsammanin sako daga Bombee ɗin.
"Wai amma fah Hajiya tanada kyau sosai,yanda aka bada labarinta kuwa haka take"
"Hmm kyan ɗan maciji ba,kyanta bazai ruɗeniba kamar kai, tana gama abinda zatayimin zata ƙara gaba,kasuwanci ne zai haɗamu kawai. Na kula shima shegen ɗannata irin idonta ne dashi"
"Wai Hajiya anya kuwa bazaki kai tashin hankali ba gida,karki manta fah da ɗanta zataje,sannan yanda iliyah yafaɗa tana kyau,kar aje a samu matsala fah da Yallabai(Jabeer).
"Kumin shuru ko karen haukane yaciji ɗana mai zayyi da wannan matar,bayan haka ma anayin wananan ma zai aure wacce tun farko tadace dashi ai Wato Jawaheer,wannan bakomai bace illah Mai aiki wacce aka ɗakkota damin tayi a biyata. Mujira dai muji mai zata ce gobe,koma menene ni bazan fasaba daga kan ra'ayina"
......ku garzayah arewabooks domin Samun Cikekken labarin da kuma yawan pages fiyeda wanda kuke samu nan.
_*Sadi-sakhna ce*_
Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
_Mashaallah A yau Allah ya ara mana lokaci mun gama littafin BAƘAR AYAH na farko._
Ga duk ɗaukacin masoyana ina godiya sosai.
Gobe in allah ya kaimu zan fara post littafi na biyu a AREWABOOK.
Sannan kuma a ranar zan buɗe group a whatsapp.
Duk mai buƙatar littafi na biyu zai turo Naira *300* ta Wannan jaddawalin kamar haka.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Masu turo da kati zasu tura katin mtn ta nan
09035784150
Mutanen niger zaku tura *300f* ta wannan layin.
+227 97 21 16 15
Mai ƙarin Bayani ya tuntubeni ta layina
09035784150
Ko direct whatsapp message
https://wa.me/message/MAPXUDCCPXCGP1
______________****_______________
Page 🖤34🖤
Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka.
"Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan"
Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa.
"Wacece matar,tana waje har yanzu?"
"Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi"
"To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi"
"Wani kallon mai kuke ƙullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta ɗora dacewar"
"Wani kam iyani mai kuke ƙullawa da wannan matar ne kam,kardai kicemin dama wani abu zakuyi da ita shiyasa kikaxo,naga tunda kikazo garinnan ko gidan su iyah bakijeba,in kuka fice a gidannan da safe bakwa dawowa sai dare,gashi kince jibi zaku tafi"
"Ahhah bakomai fah karki damu,yau dama zan shiryah naje musu,har gidan Addah Sa'ade zanje"
Daga haka tayi saurin kawar da zance tayi ɗaki,inda Hajiya zeenah take.
Tana shiga ta maida labulen tareda ƙarisawa inda Hajiya zeenah take zaune da sauri.
"Hajiya an kawo wasiƙa,inaga fah daga wajen Bombee ne"
Tafaɗa tana miƙa mata wasiƙar.
Karba tayi cikin sanyin jiki ta buɗe.
_Na amince da aikinki,saidai bisa sharaɗin nan masu zuwa. Maimakon miliyan ashirin zaki bani miliyan Hamsin,sannan kuma ba wata shida nake buƙata ba shekara gudan nake buƙata,idan kafin sannan nafitar miki ita daga gidanki contarct yaƙare daga nan,idan kuma na haura shekara guda ban fitarta ba nan ma contract ya rushe,zan kuma maido miki da kuɗinki.
Inkin amince da sharaɗina gobe za'a ɗaura auren a address ɗin dana rubuta,wata masallacin juma'ar garinnan.
Waliyyin ɗanki yazo gobe za'a ɗaura auren bayan sallar juma'ar,akwai wanda nakeso yaji aurenne,kekuma bakida haɗi sa hakan tunda ba garinnna kike ba.
Bayan ɗaurin auren Hilyaan zasuje itada khamees suyi duk abinda nakeso wajenda zan zauna yakasance.
Niba yanzu zan biku ba saina gama wani abun,kuma yarona bashida kafiyah a yanzu ,baxanyi tafiyah dashiba_
Wannan shine bayanina inkin yarda akwai takarda a ciki kiyi sign,akwai nawa sign ɗin a jiki,idan kuma baki yarda ba karkiyi sign ki dawomin da takardar haka.
From BB
Ajiyar zuciyah Hajiya zeenah tasake tareda miƙawa iyani takardar itama ta karanta.
"Inkinada biro kawomin zanyi sign"
"Hajiyahhh wai kin yarda da abinda tace,miliyan hamsin fah kuma kiji wasu sharudda kamar uwar mutane"
"Ki miƙomin biro kawai na amince dasharaɗinta,sa'a tace dana samu ta amince,idan bata amince ba inaji a jikina ciwo zuciyah zai kamani na takaicin lubna,wanda inna kwanta in miliyan ɗarine ma zan cinye ban warke ba. Dan haka ki miƙomin biro da kuma wayata,zan ƙira alhaji kan batun waliyyin Jabeer ɗin"
Daga haka iyani batasake cewa komai ba,sai miƙowa Hajiya abinda ta buƙata din.
Allah sarki bawan Allah da bai ɗauki duniyah a bakin komai ba,yana zaune akan kujerar sa bayan Madeenah ta gama Kawo masa maganinsa yasha bayan ya karyah.
Wayarsa ce tayi ringing,yana dubawa yaga sunan matar tasa,murmushin manya yayi kafin ya ɗauki ƙiran.
"To mai kuma yafaru uwar yara"
"Sai abu ya faru kafin na ƙiraka,yajikinnaka,ina fatan dai suna kulada maganinka akai akai"
"Ko kinannan ma dama ai suna kuladashi sosai,ya abinda kikaje nema,kinyi nasarane"
Eh ta amsa masa a hankali,dan tasani sarai ya ɗagota ganin ƙiranta yanzu,sabanin yanda take kirannnasa sai dare kawai tun zuwanta gembun"
"Nayi nasarar samun amincewarta,yanzu aure za'a ɗaura gobe,kayiwa Baffansu magana akan yin walin,inyaso saisu taho a jirgin dazaizo ɗaukar mu"
"Ahah Karki saka Abdullahi kan wannan maganar taki,kinfi kowa sanin yanda abin zai kasance,kedai ki bari akwai wanda zan turo goben idan jirgin zai taho. Saidai har yanzu kina ganin yin wannan auren shine mafitar wannan matsalar? Kaman yanda kika faɗa nabar miki ragamar abin,na zuba miki idone naga wanne irin gyara zakiyi?..."
"Komai yana tafiyah daidai, na tabbatar komai zai tafi yanda na tsara"
"To shikenan Allah ya baki sa'a,kin faɗawa shi ɗannaki abinda yake faruwane na aurennasa gobe?"
"Karka damu zan sanar masa a goben idan an ɗaura auren,kuma ma aiba yinsa zanyi dan........shikenan nan dai komai zaizo daidai"
Daga haka Hajiya zeenah tayiwa mijinnata sallama ta kashe wayar.
Kallon wayar yayi bayan takashe
"Hmmm idan na faɗamiki ki kwantar da hankalin ki bakyajin magana,yaronnan ya girma,amma har yanzu son zuciyarki ya hanaki kigani,muje zuwa,ina fatan wannan abin dakika ɗakko dakanki yayi silar gane kurenki batareda wata babbar matsala na,nasan idan nahanaki yanxu damuwa zakisa a ranki dazai jawomiki ciwo......kai Allah ya kyauta"
Ƙara daga wayar yayi yasake ƙiran wani manager amininsa a company,wanda yasaka a boye ya dunga kulamasa da mai ake a wajen.
Magana sukayi akan yashirya zuwa gembun sannan kuma yazama waliyyin Jabeer ɗin a auren,Babu yanda zayyi,yasan idan yaƙi saka hannunsa yabarta taje tayi yadda taga dama,zata iya jawo matsalar dasai tafi bai saka hannunba.
A ranar su Hajiya zeenah basuje ko inaba,dan haka iyani ta samu damar fita zuwa ga danginta,itakuma Hajiya zeenah tasamu damar hutawa na zirga zirgar da tayi.
Washagari Ranar juma'a bayan an gama sallahr juma'ar ne mutane sukaji ana sanarwar ɗaurin auren.
Sunan da aka ambata shiya girgiza mutane ba kaɗanba,wai Bombee zatayi aure,shikansa uban amaryar bai san da zancen ba sai dayaji an ambaci sunan.
"An ɗaura auren JABEER ALIYU da kuma MARYAM AHMAD.kan sadaki Dubu hamsin"
Nan da nan kuwa kaman iska labarin auren Bombee yazagaya waje da dama,wasu sai murna suke zata bar garin tatafi. Yayinda wasu kuma har sannan basu gama yarda da lamarin ba.
A zaune take tana kallon window tayi shuru alamar mai tunani.
Hilyaan ce tashigo ɗakin tareda cewa.
"An ɗaura auren kaman yanda kika faɗa,amma miyasa ba aure bane normal kikayi shi cikin jama'a ba'a sirriba,mutane sai labarin auren sukayi"
"Saboda sonake kowa yashaida auren,musamman gidanmu,akwai wanda nakeso su sake ransu cewar na tafi,daga baya kuma saidai suga bayyanata batareda sunyi tsammani ba"
"Uhm toh shikenan yanzu kuma saime za'ayi,naji kince zamu farayin gaba kafin ki taho ko"
"Eh zakuje kuga wajen da tace zan zauna,inda matsala ku ƙira ku faɗamin,sannan ku saka duk abinda nake buƙata,nan da kwana uku zan taho idan nagama abinda nake"
"Hmmm yanda suka bada labari kaman matarsa batada mutunci"
Ƴar dariya Bombee tayi tareda cewa.
"Wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa na karbi aurensan,na daɗe bansamu abin nishadi ba kaman wannan,har na matsu naga abinda zai kasance,sannan kuma bayan lokaci mai tsayi finally zan koma garin Abuja"
Dan jijjiga kai Hilyaan tayi tareda fita zuwa ɗakinta,saboda tattaro kayanta,dan an sanja tafiyar daga gobe zuwa yau. Babu zancen bata lokaci yanzu zasu tafi tareda su Hajiya zeenah.
Tafiyah yake a mota yana jin labarin da ake a gidan rediyo,hankalin sa yayi nisa wajen sauraron shirin da ake na Filin zamantakewar aure.
Ƙarar wayar sa ce tashashi ɗauke kansa daga kan hanyar ya kalli mai ƙiran.
Sunan Mommah yaga akan wayar,hakanne yasaka ta a jikin mota wajen ƙiran waya. Sallamar ta yaji ta doki dodon kunnensa,a ransa yace yau kuma koda wannne tazo?
"Hello Jabeer kana jina?"
"Eh ina jinki Mommah"
"Tamm Abbanku ya turo mana da jirgi ɗazu,yanzu haka muna hanyar dawowa,na sanja dawowar sai gobe,kaje gida ka faɗawa su Madeenah dawowa ta,na ƙira wayarsu bata shiga"
"To shikenan dama ina hanyar gidan zan faɗamusu"
"Ohh bazaka tambayi ya abin ya kasance bane?"
"Mekenan dama ba fasawa kikayi ba,shiyasa zaki dawo?"
"Ka taba ganin nasa abu a gabana na fasa,ai ka kwantar da hankalin ka,nayi nasarar shawo kan matar danaje aura maka,yanxu haka an ɗaura auren muna hanyar dawowa,ka fara ƙirgawa ka kusa rabuwa da wannan jarababbiyar matar"
Bata gama faɗin bayanin datake som ƙarisawa ba Jabeer ya kashe wayar,saboda wani bugu da kirjinsa yayi batareda ya shirya ba.
"Innalillahi Allah gani gareka shin wa nafi tsorone a cikinsu,Ummata ko kuma Matata,ga ..........."
Bai gama maganar ba yaji alamun yabuge wani abu a gabansa,da sauri yaja burkin motar,amma duk da haka daga yanda yaga mutane suna taruwa a wajen yasan akwai abinda ya bige.
Saurin fitowa yayi daga motar tareda ture mutanen da suka taru a wajen.
Bayan mace yake kallon sanye da milk ɗin hijabi,kowa sai sannu yake mata,ita kuma ta sunkuyar dakai batace komai ba.
"Subahannallahi baiwar Allah bakiji ciwo ba dai koh"
Ɗago darara dararan idanuwanta tayi farare tasss ta sauƙe su akan fuskarsa,daga kallon zubin yarintar fusakarta bazata wuce shekara 17 ko 18 ba,kyakykywace ajin farko idan ana samun irinsu,ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke tareda sauƙe idanuwanta tana kallon hannunta wanda yake dauke da ciwo a jiki amma ba mai yawa ba.
Wani irin yarr haɗe faɗuwar gaban Jabeer yashiga a lokacin guda,wanda tunda yake bai tabajin yanayin ga Wata mace na,harda kuwa marigayiyar matarsa hafsah.
Gabaɗayah notin kansa ya kunce,baisan lokacin da yakai hannu kan inda ciwon yake ba,tana ganin hakan tayi saurin ɗauke hannunta tareda cewa.
"Karka ta'bani"
Cikin wata murya mai ma'abocin taushi da sanyi.
"Jaleelah mai yasameki haka dama ke aka buge naga mutane,kinji ciwo sosai"
"Ahaha Fareeda ba sosai bane,mugafi gidamana kar dare yayi mana a waje"
Tafaɗa tana tattaro litattafanta da suka zube akan titi.
Dogon hijabi ne har ƙasa,sannna kuma akwai rubutun larabci a jiki hakanne ya tabbatar daga islamiyyah suke.
Ko kallo dayah basu sake yiwa Jabeer ba suka kama hanyar zuwa gida.har sukayi nisa Jabeer yasaka motsawa bare yayi ƙoƙarin basu hakuri ko yimusu magana,tun lokacin da muryar yarinyar tashiga kunnensa.
Shawarar da Khaleel yabashi Kwana biyu da suka wuce ya tuna....
""""Kasamu wacce zuciyar ka takeso ka aura,mai ilimi da tarbiyya,wacce zata kwantar maka da hankali idan suka tayar ma""""
Ɗan murmushi yayi tareda shiga motarsa yafara bin bayan ƴan matan.........
Kashshshsshshshhsshh Makaranta,anan muka kawo ƙarshen littafi na ɗayah a cikin Labarin Baƙar ayah.
Domin Samun cigaban labarin da kuma tambayoyin da suke cikin kanku,ko kuma son jin wacce chakwakiya ce zata faru kaman haka
__Menene maƙasudin abinda yafaru da mahaifiyar Bombee?
___shin kuna zargin inna laari kaman yanda Bombee ke zarginta?
___miliyan hamsin bashine kaɗai abinda zai iya sakawa Bombee ta amince da ƙudirin Hajiya zeenah ba,sannan kuma ta buƙaci shekara guda maimakon wata shida meyasa toh?
_____Ga Luban....Ga Bombee.......Ga Jawaheer......sannan kuma ga zabin shi uban gayyar wato ........Jaleelah!!!!!
Wacce chakwakiyace zata balle tsakanin wannann matan idan suka kasance ƙarƙashin inuwa guda,gasuda halaye mabanbanta???
Sannan waye uban ɗan Bombee,shin Jaan family zasu yadda tazo musu da shege cikin gida???kuma shin zata iyah maganin Lubna kaman yanda tace...........
Masu magana sunce BAƘAR AYAH.......Itama cikinta farine. Shin wacece baƙar ayah a cikin matannan,anya kuwa zata kasance farar kaman sauran Baƙaƙen Ayar???
Kaɗan kenan nasan daga amsoshin da suke cikin kanku,Amma karku damu duk zaku samesu cikin sauƙi idan kuka cigaba da bibiyar littafin a Arewabooks.
Ku sauƙe app ɗin kana kuma kuyi search littafin BAKAR AYAH zai fitomuku waral domin karantawa.
Ga wanda basu ganeba domin ƙarin bayani su tuntubeni ta wannan layin
09035784150
Wanda bazai iya karantawa ba a arewa book shima yayi min magana domin shiga group ɗin littafin,idan an gama kuma sai ya siyah littafin document a wajena.
SADI-SAKHNA najiran isowarku makaranta❤❤❤❤ mu haɗe a littafi na biyu,ina yinku cikin carbi🤣🤣🤣
Alhamdulillah Alah kulli halin
___****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15
______________****_______________
Page 🖤1••2🖤
Tafiyah suke Jabeer yana binsu a baya bataresa saninsu ba har suka kai gida.
Kallon ƙofar ya tsaya yi yana nazarin tsarin gidan daga cikin motar.
Wai dama akwai irin waɗannan gidajen a garin abuja?? Kodaga nesa mutum zai gane yanayin rashi da ma'abota gidan suke dashi.
Katangar gidan duk ta zube ta wani wajen saboda rashin ƙarfinta,kuma ya haɗu da yawan ruwan sama dayake kwaranyah a kanta na tsawon lokaci.
Kofar gidan babu wani ishashshen makari,wani langa langane a gefe,da alama dashi ake amfani wajen kare gidan da daddare.
A taiƙacedai gidan na masu ƙaramin ƙarfine sosai.
Numfasawa Jabeer yayi bayan ya gama kallon gidan,inda ba biyota yayi ba yaga tashiga gidan,bazai taba cewa daga nan ta fito ba.
Abinda yafi bashi mamaki shine yanda taƙi karbar taimakonsa,bayan kuma tana rayuwa a gida irin haka.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan,waigawa yake domin samun wanda zai aikata cikin gidan,idonsa ne ya sauƙa kan wani yaro yana riƙe da kwanon a hannunsa,fuskarsa dama dama da miyar tuwo,da alama tunna jiyane,dan tuwon bayyi kamada wanda aka dafashi sannan ba.
Cikin ɗauke kai daga kallon fuskar yaron ya fara magana.
"Uhm mutumina nace zona aikeka mana,shin nanne gidan su Jaleelah koh?"
"Eh nanne gidan su ina anty hafeezah koh?"
"Eh inaga itace,shiga kace ina sallama da mahaifinta idan yana nan"
"Nawa zaka bani to idan na ƙiramaka shi?"
Mamakin maganar yaron Jabeer yayi,yanzu wannan yaron har yakai bazayyi abuba sai an biyashi?
"Karka damu shiga ka kiramin shi tukunna"
Hanyar gidan yaron ya nufah,bayan wani ɗan lokaci sai gashi sun fito tareda wani farin dattijo mai kamala da dattaku.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna,maganar yaronce ta katsesu da cewa wani abu bayan sun gaisa ɗin.
"Malam baka bani kuɗin ba toh"
Kafin Jabeer yayi magana Dattijon yace.
"Wanne kuɗin za'a baka,har yanzu baku bar wannan ɗabi'a ba koh,ohhh wai yaro baisan a sakashi abu ba sai an bashi kuɗi? Wuce ka tafi gida"
Da sauri yaron ya wuce yana zumbura