Showing 15001 words to 18000 words out of 134612 words

Chapter 6 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8659

shekara ashirin da biyu baya,ya fara ne.................


_______*****________








Ayyiriri ayyiriri,Malm Ahmadu ya iyo amaryah a hayin Fulanin yanki, masu ƙura,itace ta farkon mace wacce aka aura da Garesu.
To ikon Allah,shikuma mai takaishi auren ƴarsu,ana fa cewa iri irinsu mayune,shine yaje ya ɗakkowa kansa irinsu,ƙyan ɗan macijine fah dasu wayannan mutanen,lallai Inna laari taga takanta,saita san irin zaman dazatayi da ita. Su fah maza kana zaman zamanka sai su ɗakko maka alaƙa ƙai,daga kawai ta shekara uku babu rabo shine har ya manta soyayyar da sukayi dandali ya auro mata fulanin ƙaurah"
"Hmm kema dai kya faɗa,muma ina gashinan masu haihuwar ma anyi mana kishiyar daga shekara biyu da aure,maza ai sai a barsu"
"Larai ta faɗa tana nuna Innar muruje da baki,wacce take alwalar Azahar"
Duk abinda suke tana jinsu,amma ko ci kanku bata ce musu ba,saima shigewa ɗaki da tayi.
Dare yana kawo kai guɗa ta cike anguwar tasu da kuma raye rayen fulani sama sama,wai hakan ma ba'ayi wani bidiri da al'adu ba,kasancewar iyayen yarinyar basason auren.
Malm ahmadu ne yadage akan sai ya aureta,lokacin daya ganta takai nono gonarsu talle,dayake yana kuɗi a lokacin sosai,duk anguwar babu wanda yakaishi girman Gonar Ganyen shayi,gashi yanada hanya sosai a kamfanonukan da suke siye da siyarwa dasu.
Tun daga bakin ƙofar shigowar tasu LAARI ta fito da fara'arta ta tarbi Amaryartasu. Al'amarin daya bawa aminanta ma mamaki,ba iya su dangin amaryarba,dan kafin shigowarsu babu irin abinda su Larai da danginta basuce ba akan abokiyar zamannnata ba,amma tayi shuru tai biriss da abinda suke cewa,sai daga shigowar amaryar ta bawa kowa mamaki.
Duk da hakan ba abine dama da bazai iya faruwa ba,kasancewarta mace mai shuru shuru kuma marar hayaniya,sannan kuma ta yarda mijinta,tunda tasan badan yana ƙinta yayi mata kishiyar ba.
Har ƙofar ɗakinta ta rakata tareda buɗe mata kai.
"Sunan Laari,nice Abokiyar zaman ki dakika shigo gidannan kika tarass,ina fatan zaki ɗaukeni kema abokiyar zama,sannan kuma zaki bani hadin kai mu samar da zaman lafiyah,Allah yasaka albarka da zaman lafiya a zamantakewar mu"
"Ɗan murmushi Daneji(an samo sunan ne daga Alamar "fari" a harshen fillanci,Ainihin sunan ta shine Fatima,taci sunan mahaifiyar baffansu. To kasancewarta fara sosai ko a gidansu yasa ake ƙiranta da Daneji).
"Inshaaallah zaki sameni mai binki sauda ƙafa Addah laari,nagode da ƙaunarki gareni,bansan da wane kalmomi zan yaba miki ba"
"Bakomai ki nuna min a ta fuskar halayyarki ma ya isa"
Daga haka Inna laari takoma turakarta wajen mutanenta,tabar Daneji da Nata ƴan uwan a sabon gidannata.
Sai bayan kwana biyu da kawowa amarya kafin ƴan biki kowa ya watse,aka bar amarya daga ita sai halinta.
A zaune take ta tafi tunanin yanda rayuwarta a sabon wajen zai kasance,musamman da tasam cewa yan uwanta na daff ta yin ƙaura zuwa arewancin nijeria,dan dama su ba mazauna bane,abinda iyayenta suke tsoro kenan dama ita kanta,shine su barta a wajen da basuda tabbacin dawowa.
Saidai komai yayi rintsi maganin sa Allah,haka iyayennata suka koyar da ita,dogaro da Allah a kowanne lokaci,duk da kasancewarsu masu tashi basuyi boko ba,amma karatun addini kam ko na garin bazasu nuna musu ba.
Saurin share guntun hawayen daya gangaro mata tayi,jin motsin mutum ya shigo ɗakin.
Inna laari ce ɗauke da ƙwaryar abinci a hannunta.
Ƙarisawa tayi inda Daneji ke zaune a hankali tareda dafa hannunta.
"Nasan kuka kikeyi,saidai bazan hanaki ba, ko kuma naga laifinki,domin kowa yasan abin sai anjure tukunna a saba. Dan haka kema kiyi ƙoƙarin daurewar kuma ki saki jikinki,komai zai wuce kaman bai faruba inshaaallah.
Da haka cikin sigar lallashi da jan hira Laari tayi nasarar saka murmushi a fuskar danejin.
Har suka fito tsakar gidan suna aiki tare,yar hira suke kaɗan kaɗan,yawancinta kuma Laari ce keyi,sai ta tambayeta ne tace,uhm ko uhmuhm.
Haka zamannasu ya fara gudana,cikin zaman lafiya da kuma mutunta juna,abin ba ƙaramin faranta ran malm Ahamdu yayi ba,ganin matannsa sun rungumi junansu suna zaune lafiya.
Inna laari ce keyin Abinci,ita kuma Daneji tayi wanke wanke da kuma shara,sannan ta gyara mata kayan abinci.
Bayan sati da kawo Danejine su Larai suka shigo ganin amaryah.
Tundaga zaure ta rankwaɗa Sallam,dan dama itace a gaba sai kuma Shatu tana binta a baya,ta riƙe hannun ɗanta Muruje,wanda ko sati bayyi ba da yaye.
"Salamu alaikum masu gidannan,gamu munzo ganin baƙuwa ta ganmu mu ganta,ta kuma ganemu"
Inna laari ce ta amsa mata wacce take cikin ɗakin girki tana hura wuta.
"To sannunku da shigowa,sai yai kuka zo ganin amaryar?"
"Iyyi to ya zamuyi,munyi ƙoƙari ma,ita ina bata nememu ba,sai mune muka zo ganinta"
"Hayen wuri kukayi ai,dama tana shirin zuwa muku"
Duk zancen tsakanin larai da Inna laari akeyi,shatu kan da daneji basuce komai ba. Sai bayan an gama gaisawane suka shiga ɗakin Amaryar.
"Ahhh babu laifi kam ɗaki yayi kyau,zamuga shin za'a kawo kazantar ɗaki,ko kuma dai duk sammakal ne"
Larai ta faɗa tana fitstsina ido tareda dukan ɗan ƙaramin kunkuminta.
Shatu ce ta kallin Daneji itama ta kalleta,amma larai ko a jikinta,saima surutu da ta cigaba dayi,da kuma ganin ƙwakwaf.
Itada kanta da abin ya isheta tabar ɗakin,tareda nufar ɗakin Inna laari,a bakin ƙofa ta tsayah kafin tashige ta kalli shatu.
"To ni barina yi ɗakin yawuron gidan,ta inda muke muyi namu yakin,wanda ko an fadama mutum bazai ganeba,saura kuma a zunguri hancina idan anga na kauda ido"
Itadai shatu bata ce mata komai,saima maida kanta da tayi kan Daneji wacce take zaune a bakin gadonta.
"Hmm kiyi haƙuri fah amarya,yanayin zamanne sai haƙuri,bazaka iya sanja mutum ba,saidai dole kasha maganin zama dashi.
Sannan abinda zan faɗamiki kiyi taka tsantsan sosai,karki saki jiki ki bada yardarki dabaɗaya,za'ayi miki abinda bakya tsammani.
Murmushi Daneji tayi,da alama bata ɗau maganar shatun da gaske ba,saima kauda zancen da tayi ƙoƙarin yi.
"Ayyah Addah shatu babu komai dai,Inshaaallah babu wata matsalar........kai ɗan saurayi ya sunanka?"
Ganin duk yadda take ƙoƙarin nusar da Daneji bata damuba,saima dauke zancen da take shirin yi,yasa itama Shatu tabar zancen tareda cewa.
"Ohh wannan sunan Umar,amma yara sun saka masa Muruje,kiji wani suna kaman na Warjayi"
Ƴar dariyah Daneji tayi,da alama sunan da kuma yaran sun bata dariya,haka ta zage tana ta tsokanarsa shikuma yana yi mata ƙiwuyah.
"Inasonsa ki bani shi innar muruje"
"Hhhhh baban sa zai dawo gidannan kenan,in kikayi haƙuri kema zaki haifi naki kaman yaune,saidai zai dunga zuwa miki yawon yamma"


Larai ce a zaune ta baje ƙafa kan kujerar Laari zance yayi zance,wanda yawancinsa duk na Adashen da suke ne a anguwa.
"Uhmm daikuma naga yarinya tasake abinta tayi mursul,ga kulawar miji ga kuma ta kishiya,abin har ya taru yayi mata yawa"
"Ke larai,banda abinki dama ai jajir take lokacin data zo ma"
"Ohh to inaga idona ne yagani badaidai ba,nikam da badan nasanki ba,sai nace yarinyyar can asirin tayi miki,dan inajin labarin duk abinda kike mata a wajen malm,insun zauna malam ahmadu na bashi labari. Yayi tayimin tujara kenan wai ni naƙi a zauna lafiya."
"To kema ki riƙeta ku zauna lafiya mana larai,ni banga laifin shatu ba......"
"Ahah ahah nina gani inke baki ganiba,idan dole haka kawai banason ta saina ce inayi,gwanda tasan bani sonta,ta tsare tata rayuwar nima nayi tawa,innace zamuyi zaman da kuke da itama nayi ƙarya bazan iya ba"
"Kiji gulma irin ta maxa,wato mlm ne yake bashi labari?"
"Tabb yau kika sani,gulma ai ta daɗe da tarewa wajen maza,idan sun zauna a wannan majalisar,basa lazumi ko salati,sai aukin cin tsire da gulma,shiyasa kiga cikinsu tula tula kaman ƙore,kai sun barka da ɗumame da kuma cikon cefane"
Larai ta ƙarisa fada tana tashi tareda nufar ƙofa.
"To mu munyi nan,sai kun shigo,dan Allah kicewa magajiya zanyi ɗaukar wannan watan na adashen,auren ƴar yayata ya taso"
"To shikenan zan faɗa mata"
Daidai fitowarta daga ɗakin,itama shatu ta fito daga ɗakin Daneji,sallama sukayi musu suka fita.


............"uhhhhhh uhhhhhh" .........."laari Daneji fah amai take kwarawa tun daren jiyah,lafiya kuwa????.............








🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are


















____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]












*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________














Page 🖤11🖤






Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba.
Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen.
Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi.
Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin sasu manta lalurar tasa.
Daneji ce a cikin ɗakin madafah tana girki,tun jiya take jinta wani iri,amma haka ta daure,dayake ansan mace da dauriya da kuma murƙushe kanan nan ciwo da laulayi.
Doyar da take dafawa zatayi sakwara ta buɗe,saidai ƙamshinta yana bugunta taji amai ya taso mata.
Da sauri tayi waje tana ƙoƙodon amai.
Inna laari ce ta fito daga ɗakinta domin ganin mai yake faruwa.
Ruwa ta debo mata ta gyara bakinta tareda yimata sannu,suna cikin hakanne shima Malam Ahmadu ya shigo gidan ya dawo daga wajen ɗaurin auren daya fita da safe.
Inna laari yafara tambaya mai yake faruwa,saidai kafin ta bashi amsa Daneji tacigaba da aman da takeyi,saidai takai ga ta amayar da duk abinda taci da safe.
Kafin lokacin ƙalilan ta galabaita ta fita hayyacin ta,kamata inna laari tayi suka shiga rumfah ta zaunarta,inda shikuma malam Ahmadu ya fita ƙiran ƴar mai ganye,dake tsallaken gidansu,domin ta duba taga mai yake faruwa.
Basu daɗe ba suka shigo tare,takalmanta fantala fantala zani a tsangale,sai jijjiga kai take ƙanƙanin. Hannun danejin ta kama tayi shuru,kafin tafara wasu ƴan dube dubenta,can ta waigo ta kalli mlm Ahmadu tareda cewa.
"Iyyyeeee Alhandu alhandu,Yarinya ciki gareta,ƙaruwa ce ta samu sai kuyi murna ku godema Allah"
Tun kafin tagama maganar Mlm Ahmadu yafaɗi ƙasa yayi sujjada,tareda fashewa da kukan murna.
"Daneji ɗiyar arziƙi,allah shi miki albarka,haƙika kin sakani farinciki dana daɗe ban shiga ba a rayuwata,Allah ya saukeki lafiya. Inna ƴar mai ganye kinada kyauta ta musamman na wannan albishir ɗin,yanzu dame dame take buƙata kenan"
"Babu abinda take buƙata,illah tarage yawan aikace aikace amma ba wai kartayi ba,sannan a kulada abinci masu gidan jiki sosai,nagode nagode mlm Allah yayi albarka,ni bari na tafi toh Allah ya raba lafiya,zan aiko yaro da ruwan saiwoyi ya kawo mata ta dunga sha"
"Shikenan iyah mai ganye mun gode"
Duk abinda ake iya Iyah mai ganyece da kuma Malm Ahmadu,inna laari bata ce komai ba itada Daneji,wacce take ɗan sauƙar da numfashi a hankali.
"Sannu mai zakici toh,bari a nemo miki Kwankwason akuyah a dafa miki"
Ɗaga masa hannun Daneji tayi alamar yabari,amma mutumin ko kallonta baiyi ba,sai ma fita da yayi da sauri bajam bajam da babbar riga.
Binsa inna laari tayi da kallon kafin ta jijjiga kai tayi ɗan murmushi.
"Zaki iya isa ɗaki ko kuma na rakaki? Zan ƙarisa abinci"
"Ahah zan iya Adda laari nagode da kukawarki"
"Babu komai kisamu hutu sosai jikinki yayi laushi,bari yakawo naman saina dafa miki,Allah ya sawwaƙe ya raba lafiya"
Daga haka Daneji ta ƙoƙarta tashige ɗakinta,ita kuma inna Laari tacigaba da aikin abincin data bari.
Tundaga wannan rana Daneji ta gagara lafiya,kullum cikin laulayi take,yau da lafiya gobe kuma babu,abinci kuwa kusan kowanne kala bata iya cinsa.
Tun malm Ahmadu yana ɗokin magaji har zuwa yanxu abin yafara bashi tsoro da tausayi,inda yafara tambayar dama haka goyon cikin yake.
Inna laari ce take rawa take kidanta a tsakar gidan,ita kam daneji Ba sosai take fitowa tsakar gidan ba,in mutum ya ganta to zagawa zatayi makewayi ko kuma alwala.
Haka rayuwar tacigaba da tafiyah,da daɗi da kuma babu,har yazamto cikin daneji yayi girma sosai,ana saka ran ko yaushe zata iyah haihuwa. A lokacinne kuma aka dage dabata dan taimako,ita kanta inna laari ba'a barta a baya ba,takan samo mata ɗan taimako daga wajen mahaifinta,dayake shima malamine.
Ɗakin Danejin inna laari tashiga da ƙwaryar magani a hannunta,magana tayi mata kasancewar ta juya bayanta bata kallonta.
"Daneji tashi kisha maganinnan ya tsumu sosai,karkuma yazo ya sane"
Duk maganin da Inna laari take bata a dole take sha saboda rashin dadinsu,saidai saboda karta nuna mata kazawarta a ƙoƙarin datake da ita yasa ta yunkura ta tashi. Alkhairin da inna laarin tayi mata bazata iya ƙirgasu,ji take a yanzu bata da kowa na kusada ita kaman ta,musamman daya kasance batada kowa a garin,ƴan uwanta tunda suka tashi batasan a yanzu inda suke ba.
Karbar maganin tayi dayake cikin ƙwarya takaishi bakinta tana yatsine fuska.
Da kyar tayi kurba uku kafin ta miƙamata ƙwaryar ta koma ta kwanta.
Cikin dare malm Ahmadu ya zabura ya tashi,jin ana jan bayan rigarsa daga ƙasa,lalumar fitilah yafara yi domin ganin mai yake faruwa,don yasan bazai wuce Daneji ba,don yana shashimawa yaji bata wajen data ke kwance ɗazu.
Yanzu haka haihuwa ce,yafaɗa a ransa,don dama tun shigar watan haihuwar tata inna laari ta lamunce masa ya koma ɗakinta da zama,saboda kar haihuwa tazo mata cikin dare babu kowa a wajenta.
Baiƙi karbar tayinta ba,saima godiya dayayi mata,dan hakan baƙaramar dabara bace.
Haska fitilar yayi a wajen dayake jiyo motsin danejin,tana durƙushe ta kifa kanta da bakin gadon,ƙasanta duk ya jiƙe da ruwa yana ta malala mai haɗe da jini.
Salati malam Ahmadu yafara tareda buɗe ƙofar da sauri ya nufi ɗakin inna laari.
Tana bacci sai jin muryarsa tayi yana ƙiranta,cikin magagin bacci tafara tambayarsa.
"Lafiyah malam naganka a razane,ko haihuwarce kai tazo?"
"Ehh.....ehh itace ,maza kizo ki gani koda wani abu dazaki taimaka mata dashi"
Tashi inna laari tayi tabi bayan malm Ahmadu zuwa ɗakin danejin,wacce take kwance har yanzu a inda yatafi ya barta.
Ƙarisawa wajenta tayi tana kallon yanayin da take ciki,saidai da alama haihuwar takawo kai amma kuma dasaura,don babu alamar tahowar ɗan har yanzu.
"Inaga har yanzu fah da saura,amma barina kawo ruwa a goge mata jikinta,sanann kuma tacire wannan riga da zanin,suma bazata ji daɗinsu ba"
To kawai malam Ahmadu yace mata,domin aikinsa kallone kawai,bashida tacewa bayan hakan.
Yana nan zaune a gunta har inna laari ta dawo da ruwan dagama gyara mata jikin,sannan tabata fallen zani ta ɗaura.
Kaman jira kuwa take tafara nishi da yunkuri,har wajen fitowar asslatu suna kanta,tana nishi amma babu haihuwa,saidai yafi na ɗazu,tunda ana ganin kan yaron,aikinne dai har sannan da saura.
Yanda suka ga rana haka sukaga dare akan Danejin,wacce take fitar da nishi mai haɗe da ƴar ƙara na galabaita da gajiya.
A hanyar zuwa masallacine malam Ahmadu ya biya gidansu iya mai ganye,yake faɗamata abinda yake faruwa,aikuwa nan da nan ta shirya tanufi gidan,jiki yana bari taji daɗin kyautar da yayi mata wajen faɗar haihuwa.
Sai bayan rana ta fito gadan gadan haihuwar ta taho,inna laari tana gogemata goshi,ita kuma iyah mai ganye tana taimaka mata wajen fitoda jijirin.
Kaman jira shima yake kuwa ya canyare wajen da kuka,har makwantai ana jiyoshi.
Ɗago dashi iyah mai ganye tayi tana duddubawa,take kuwa tasaka guɗa.
"Ayayyyyyriririrrri malam Ahmadu yasamu ɗiya mace,barkanki dazuwa duniya ɗiyar Albarka"
Sai bayan tagama guɗar kafin ta kalli Daneji wacce take maida numfashin gajiya.
"Sannu sannu ƴar nan,sannunku keda abokiyar zamannnaki,dole kisha wuya kam,yarinya tafarkallah mashaallah,ga tanan kuwa jajir da ita kaman uwarta,ta amsa sunan ƴar Daneji.
Laari saiki taimaka mana da daro ruwan zafin da zasuyi wanka itada yarinyar."
"Ruwan kan daman an ɗumama tun tazu,saidai ko na kaimuku banɗakin kiyi mata wankan,kafin ku fito itama jaririyar sai a gyarata"
"To shikenan hakan ma yayi sannunki da ƙoƙari"
Kaman yanda ta faɗa ruwan takai musu banɗaki,inda iya mai ganyen zatayiwa mai jego wanka,yayinda itama ta haɗa wani a baho zatayiwa jaririyar.
Shigo ɗakin tayi da ruwan wankan ta ajiye,kafin ta nufi inda jinjirar take kwance a tsumman mahaifiyar tata,ɗaukarta tayi a hannunta tareda yin murmushi,kana kuma tashare guntun hawayen dayake kan fuskarta.
"Allah sarki jinin Mlm Ahmadu ne a hannuna,ashe zanga jinin malm Ahmadu da raina,duk da cewa banice na haifa masa ba,amma nayi maka murna dakaga jininka"
Lokacin da su iyah mai ganye suak fito daga wankan inna laari na zaune a ɗakin tana tsane ruwan jikin yarinyar,wadda tayi shuru a cinyar inna laarin tana jin ɗumin dayake ratsata.
Iyah mai ganye ce tafara magana tareda cewa.
"Hoɗan kiji yarinya tayi shuru kaman ba haihuwar yau ba,kokukanta bamuji ba na wanka"
"Ko kishi kike kai kinganta da juriyah zata ƙwace miki kujera kai iyah"
Inna laari ta amsawa iyah mai ganye cikin sigar zolaya. Suna cikin hakanne kuma kaman an tsikareta ta canyare da kuka kaman ansaka a speaker.
Nannaɗeta tayi a zanin tareda miƙawa daneji ita akan ta gwada bata nono.
Itama iyan mai ganye ƙara ƙarfafa mata gwiwa tayi cewar tashayar da yarinyar,musamman da sukaga tana kauda kai akan yarinyar tana nuna halin fulani.






...............Shuɗiyar ƙwayah kuma(blue iris),kodai bata gani kai.........daneji da faɗa a ranta.








🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama'are


















____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]












*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________














Page 🖤12🖤




Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska.
Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta.
Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature ɗinta fitowa fili.
Boyayyan murmushi Daneji tayi ganin halittar yar tata farincinkinta tareda gode ma Allah daya azurtata da itah.
Maman ta buɗe na hannun dama inda yarinyar take,tareda ƙokarin saka mata a baki da taimakon iya mai ganye wacce take tsaye a kanta.
Saida taga yarinyar takama nonon kafin tabi bayan Inna laari zuwa wanke kayan data bata.
A hankali take jan ruwan nonon cikin rashin iyawa zuwa cikin bakinta,yayinda ita kuma Daneji ta tsareta da ido,ko da wasa ta gagara ɗauke idonta daga kanta.
Idonta ne yafara motsawa alamar zai buɗe,wanda hakan yabata mamaki matuƙa,yarinyar da aka haifeta yanzu tana shirin buɗe ido,kawar da hakan tayi a ranta ganin daƙin da duhu,sannan kuma idan aka buga larasi da ƴaƴan zamani hakan bakomai bane.
"Daga haihuwarki yau har kina ƙoƙarin buɗe idonki,lallai kina da wayo sosai t.........."
Tsaida maganar tayi a ƙasan maƙoshinta,ganin launin idon dayake kallonta,ba baƙi ba ko kuma mai ruwan ƙasa ƙasa ba,da ake samun wasu yaran sukan zo dashi,nata launin idon shuɗine ne siɗik,kaman ba idanuwan bil'adama ba,duk wanda yarinyar takalleshi da idanuwan idan bayyi jarumta ba zai iya jefarta yagudu,saboda yanda suke ɗauke da wata haiba a cikinsu,da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login