Showing 120001 words to 123000 words out of 134612 words

Chapter 41 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8657

girgiza kai,alamar ta daina kukan..
"Idan bakyaso na daina bazan sake ba,ya jikinnaki bakyajin wani ciwo koh?"
"Babu abinda nakeji bombee........kawai kawai bansaba ne ba dayin amfani da wasu wuraren"
"Zaki saba a sannu inna,komai zai wuce kamar bai faruba,duk wanda yace zai sake tabaki bazan barshi ba kowaye inna"
"Uhm naji,to kinci abinci yanzun,an sameshi mijinnaki?"
Jimm bombee tayi jin tambayar da ta aikamata,a ranta tana ƙiran sunan Inayah,tasan ita tafaɗamata mai yake faruwa.
"Ahah ba'a ganshi ba,karki damu inna zasu ganshi na gama abinda yasani zama dashi,yanzu babu komai tsanina dashi"
"Amm....."
"Inna yakamata ki huta,yanzu kika tashi bai kamata ki dunga damun kanki ba har haka "
Zama tayi a wajen tana kallonta,har saida ta koma baccin kafin tabar ɗakin..
Falo takoma inda su Inayah suke zaune.
"Yah innan take?"
Innayi ta tambaya cikeda zumuɗi.
"Ta yi bacci kafin na fito"
"Yah Jabeer ɗin kuwa an sameshi,yansu maleekah ma taƙirmu wai gatanan zuwa,da alama bata sani ba sai yanzu"
"Uhm dukka basu sani ba gidan,saida zan fito na faɗamusu,ki daina yimin zancensa haka,yanzu dai kawomin abinci naci nayi wanka kafin na faɗa..
Inna gama shiryawa zamu yiwa malam godiya mu tafi gida"
A cewarta ta rabu da sha'aninsu,amma lokaci zuwa lokaci sai duba waya take,domin ganin ko an ƙirata.
Duk abinda take a cikin motar kowa na kulada ita har suka isa gida.
Har suka isa gida dare yafari amma babu labarin Jabeer ba ɗuriyarsa,ƙiran waya daga wajenta tayi recieving sunfi sau a ƙirga.
A gidansu Jabeer kuwa duk sun taru a falon sayyada-tateen,kowa yayi jugum da abinda yake tunani.
Takaicin ɗaya ma yanda iyab sayyada ta cika musu kunne da surutu.
"Ohh ni sayyada ina jabeeru yashi ga a garinnan haka,anyi nema har angode Allah?"
"Hmmm nifa nafi zargin Wannan matar tasace ta ɗaukeshi,ba tace ita taɗauke lubnah bama,kuga fah irin azabar data ganawa sauran matan ma,duk yanda akayi dasu su fito daga ƙofar akaisu asibiti sunƙi wai ta hanasu fita?
Saida kuma ya bata lokaci guda ta ɗauke ƙafarta tabar gidan"
Lailah ce tayi maganar wanda suke zaune kujera ɗaya da Madeenah a falon.
Duk falon shuru akayi ana jin maganar Lailah,da alama kuma wasu dayawa a falon sun fara gasgata maganar tata,musamman duba da yanda ta zuba musu tujara ɗazu.
"Haba anty Lailah,wlh anty maryam bazata sace yah Jabeer ba,wannan wanne irin zancene?"
"Ke dallah rufemin baki,yanzu haka wani abun take baki a sashenta ta shanyeki kema,gashinan ta sakaki kina kaimata rohoton duk abinda yake faruwa a gidannan.
Ni wlh nafara yarda da zancen anty Lailah"
Madeenah ce tayi maganar tana hararar maleekah,yayinda ita kuma take kallon Lailah,jitake kamar ta tona mata asirin abinda take,amma tasan inta faɗa a yanzu batada hujja.
Tashi tayi daga falon ta nufi sashensu,dan tasan duk tarom da akayi a wajen babu abinda yake tsinanawa Jabeer ɗin,ƙarshema Lailah wata dama tasamu a wajen na yaɗa manufarta.
Ƙiran bombee tayi tashaida mata abinda ake a gidan,daga baya kuma tayi ta roƙonta akan ta dawo,saidai har sannan babu wata tsayayyar makafa.
"Dan allah anty maryam kidawo,nasan idan sunga dawowarki zasu daina yimiki wannan zargin,amma idan har kika tafi a yanzu za'a ce da hannunki a batansa"
"Ohh saboda ba'aga fitarsa ba kome,to duk mai cewa na dawoɗin kada ya fasa"
"Kiyi haƙuri amma gobe zanzo gidan,kema nasan kinaso ki dawo anty Maryam"


Tana cikin cin abinci taji falon yayi tsitt,kowa ita yake kallo,ganin yanda take zuba abincin kaman magani. Duk da cewar taki yarda amma duk wanda yakalleta yasan tana cikin damuwa,wanda duk bazai rasa nasaba da bacewar mijinnata ba yau kwana guda.
Jiyama da daddaren hanya ta sanɗa tafita da mota,amma haka ta dawo batareda sanin inda yake ba.
Tunda tatashi har yanzu babu wanda tayiwa magana bayan gaisawar da sukayi da inna Danejo.
Maleekah ma data fito tana kallonta amma batayimata magana ba,kaman bata santa ba.
"Maryam inkin gama cin abincin inason yin magana dake....kafin sannan ke innayi haɗo mata kayanta ta tafi yau zata koma gidanta"
"Amma inna bakiji mai maleekah ta faɗa bane,duk abinda nayimasa wai zargina suke da saceshi"
"Uhm suda suke zarginki shiya zargeki,koda shiya zargeki ai badan shi zakiyiba saidan wanda ya baki umarnin yi. Balanta mijinki a yanzu yana buƙatar komawar ki gidanki,dan haka kishirya ki tafi gidanki,dama tunda dan banida ikon cewa komaine lokacin dakikace wai auren wucin gadi kikayi,da kinsani bazan barki ba sam.
Aure ba abin wasa bane dazaki sakashi lokacin dakika ga dama kuma daga baya ki cireshi.
Sannan banda kin maida mutane shakatafi zatonki waye baisan abinda kike ba,kowa yaganki yaga damuwa ƙarara a fuskarki dason sa a idonki,kawai taurin kai ne yahanaki rungumar hakan.
Indan tani kika ƙi komawa ma to ki manta,dan nan da sati guda wajen nawa mijin zankoma tunda na warke,niba kebace mai juyawa miji baya"
Zumburo baki bombee tayi tareda sunkuyar dakai tana kallon kwanon abincin,ai shikenan kuma yanzu babu freedom.
"Ehh inna wai kina nufin gembu zaki koma?,ai basai kin je ba,nanda jibi ma baba suna tahowa shida muruje,na turamusu kuɗin motama tun a jiyan"
"Ya taho kuma? addah laari fah?"
"Har yanzu baki daina maganar ta,ita kam ai ta daɗe a ƙyauyensu tuntuni,a can take wai ƴan uwanta suna mata magani"
Takarisa maganar irin bata dame taba.
Hannu inna Danejo ta miƙawa bombee tareda cewa.
"Kinci gidanku nan,wai yaushe zakiyi hankali ne kina babba,nakula babu abinda kika koya a wannan shekarun sai yanda zaki kama wancan ki yiwa wancan barazana koh?"
"Ohh inna to shikenan naji ki daina wannan faɗan kada ki samu matsala mana,Naji zan koma amma dole sai an sameshi tukunna inna,idan ba'a ganshi ba babu amfanin komawa ta.
Yanzu dai ke ishashshiya kinyi nasara,saiki tashi mutafi ko na ɗauko kayan haidar a gida na dawo"
Taƙarisa maganar tana hararar maleekah,wacce take ta dariyar komawar bombee.
"Wow you are the best inna,ke kaɗai ce mai tanƙwasa mana ogah,idan ta kafe akan ra'ayinta bata sanjashi da wuri"


Har suka isa gidan bombee batacewa Maleekah komai ba,tana yin parking ta shige sashenta.
Itadai banda dariya babu abinda take yiwa matar yayannata.
Kayan haidar ta haɗa a ƙaramin trolly ɗinsa,har tazo fita saikuma ta juya wajen drawer da take ajiye abubuwa muhimmai aciki,harda su takardun Jabeer masu amfani da kuma nata..
Magungunan data ɗebo a ɗakinsa rannan tagani a ciki,tana cewa zata tsaya tayi bincike akan namenene har yanzu bata samu dama ba,saidai haka kawai jikinta yake bata bana lafiya bane.
Ɗaukar su tayi tana duddubawa,wata takarda ce ta faɗo a ciki kaman ta gida.
Ɗauka tayi tana nazarinta,lokaci ɗaya wani abu ya faɗo mata,da alama wannan gidan nasane tunda ga sunansa a jiki,sannan a cctv camera tanuna hanyar barin gari yabi,wannan address ɗin shima ba'a gari yake ba..
Saurin maida takardun tayi ta rufe tareda zarar key ɗin motarta,indai ba ɗaukeshi akayi ba kokuma yayi hatsari,to lallai yana can.
A ƙanƙanin lokaci ta isa gidan saboda gudun datakeyi.
Wata ajiyar zuciya tasaki lokacin da taga motarsa a wajen parking na gidan.
Ƙofar falon ta tura a hankali ta shiga,tsitt kakeji kaman babu mutum a cikin gidan.
Wucewa falon tayi ta nufi ɗakin dataganshi a buɗe.
Tun a baƙin ƙofar tafara cin karo da fankunan magani,hadda ƙwayoyin maganin irin wanda ta boye a gida.
Duk anyi zubar dasu birjik a cikin ɗakin.
Zaro ido tayi tareda rufe baki,ganin Jabeer a sheme a ƙasa bakinsa yayi shuɗi(blue)kumfar datayi fita daga bakinsa ta bushe,da alama ba sannan tafara fitowa ba.
Zaman durshen tayi tareda ɗagoshi jikinta tana jijjigashi,ta ƙira sunansa yafi sau a ƙirga amma shuru kaman maye yaci shirwa.
Ƙarar wayarsa tagani da alama ƙira yana shigowa,kuma wayar ba wacce yake amfani da ita bace,sunan data gani a jikine yasakata saurin ɗagawa har tana shirin sakinta a ƙasa.
(My doctor)
"H....ello"
"Hello hello ina Jabeer ɗin yake lafiya ƙalau kuwa yake,jiya naga ƙiransa da daddare,kuma naji numfashinsa yana ƙasa da sama,kuna ina yanzu haka"
"Muna.....amm wani gidansa ne nima sai yanzu na ganshi tun jiyan,yanxu haka baya motsi,bakinsa sai kumfa yakeyi"
"Innalillahi yanzu maza ki kawoshi General hospital,neorological ward yanzu yanzunnnan akwai problem babba"
Yana gama faɗamata hakan yakashe wayar.
Tashin hankali ba'a saka masa rana,bayan ta ajiye wayar rasa ma mai zatayi tayi,hatta fatar bakinta ma rawa takeyi.
Kinkimarsa tayi a jikin kafaɗarta ta fito dashi daga gidan,buɗe bayan motar tayo tana nishi tana komai tasakashi a ciki.
Babu bata lokaci tayi asibitin nan ma da wani gudun
Tun kafin su isa dama doctorn nasa ya shiryah tarbarsu,dan haka direct emergency akayi dashi babu bata lokaci.
Sai bayan an shiga dashi kafin ta tuna da wani abu waishi ƙiran wayar familynsa.






_*SADI-SAKHNA CEH*_








____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤 51••52🖤


Maleekah ta ƙira ta shaida mata tafaɗawa ilahirin gidannasu halinda ake ciki.
Tana kashewa wayar khmees ta ƙira shima tafaɗamasa halinda ake ciki.
Daga nan tacigaba da safa da marwa tana jiran fitowar doctorn domin jin mai yake faruwa.




*** ***


"Mommy mommy"
Tun kafin ta ƙariso sashen take sabga musu ƙira da waya a hannunta.
"Menene kike zabgamin ƙira kaman wata sabuwar makahuwa,kibarni naji da abinda yake damuna ma"
"Mommy anty maryam tasamo yah Jabeer,saidai lokacin data ganshi a sume yake,yanzu haka wai suna general hospital anshiga dashi emergency"
"What hospital kuma,maza-maza shiga ki ɗauko min mayafina,barina ƙira su abdul na faɗamusu,shikamma abdulkareem ai yana asibitin,barina fara faɗamasa"
Cikin sauri jikinta har rawa yake tafara danne dannen wayar,yayinda itakuma maleekah tashiga ɗauko mata mayafin.


Suna gama wayar ya nufo emergency ɗin daga ward ɗinsu,tun a bakin room ɗin yahango bombee wacce take ta safa da marwa tana cizan yatsa,ajima ta zauna saikuma tasake tashi. Kana ganinta kasan tarasa mai zatayi ne.
A hankali yake tafiya har ya isa inda take,sallama yayi mata amma sam batajishi ba,gabaɗaya hankalin ta baya cikin kanta.
Maimaita sallamar yasakeyi wannan karon da ɗan ƙarfi.
"Am likita ya ake ciki ya tashi, mai ya sameshi babu matsal....."
Shuru tayi ta zancen tareda dafe kanta lokacin da taga ashe Abdulkareem ne ba doctorn datake jiraba.
"Ohh ashe kaine am sorry"
"Ahh no babu komai,amma dai ki kwantar da hankalin ki inshaallah zai samu lafiya,inkika cigaba dayin haka to kema zaki iya samun matsala,kowa yaganki yasan....."
"Ba kayi haƙuri amma ba wannan bayanin nakenson ji ba,shin zaka iya dubomin mai yake faruwa,ta hakane kawai zan iya samun kwanciyar hankali"
"Okay to shikenan bari su abdul su iso kafin na tafi,kada na barki ke kaɗai a wajen,kicigaba da Addu'a Allah zai bada mafita inshaallah"
Shuru tayi daga haka batasake magana ba,har Abdulmaleek ne ya iso wajen shida maleekah da saurinsu.
"Yanaganku ku biyu ina mommah take?"
"Uhm ta tsaya jiran Sayyada-tateen wai dole saita jirata,nikuwa danaga haka nafaɗawa yah abdul.M mutaho tare.
Anty maryam yadai ya ake ciki,a ina kika sameshi ne uhm"
"A wajen da banyi tsammani ba kuma nayi tsammani"
Kallonta sukayi su ukun da mamakin maganar ta.
"Ba yanzu ne lokacin daya kamata ayi magana akan wannan ba,Abdulkareem kaine likita,akwai abinda Jabeer ya daɗe yana boyewa kowa,wanda kuma abune mai matuƙar muhimmanci,kasamu likitan dayake gani kuyi maganar dashi,na tabbatar abinda yake damunsa yanada nasaba da halinda yake ciki yanzu.
Ni kaɗai naga yanayin dayake ciki ku baku gani ba.......it's so heartbroken"
Hawayen da maleekah take rikewa ne yazubo akan kuncinta,zama tayi a gefen bombee tareda rungumeta,wacce itama take ƙoƙarin wajen ganin zuciyartata bata karaya ba.


Kafin likitocin dasuka rufu akan Jabeer su fito,tuni bakin wajen ya cika da ɗumbin mutane,harda Hajiyah rabi da kuma gidansu Jaleelah wanda suma suka samu labarin kwanciyar tasa,banda ƴan wajen aiki dasuke ta zuwa.
Lokacin da likitocin suka fito daga ɗakin aikin su kansu saida sukayi mamakin yawan mutanen dasukayi dafifi a bakin wajen.
Cikeda damuwa babban likitan ya kallesu kafin yayi magana.
"Uhm dan allah wasu dayawa si ɗan yi gefe,bamason hayaniya a kuda nan wajen,sannan ina buƙatar wasu daga cikin familynsa na kusa zamuyi magana dasu"
Wannan ya kalli wannan,daga ƙarshe dai ƴan biyun ƙannennasa suka tashi domin bin bayan likitan,Hajiyah Zeenah ce ta tashi zata bi bayansu itama,dan dama tun ɗazu datazo batace komai ba tana takure a gefe,su kansu ƴaƴan tunda sukaji abinda tayi jiya babu wanda yayi mata magana.
"Am mommah dakin zauna basai kinzo ba,saboda zai iya yiyuwa abune da bai kamata kijiba a yanayin dakike,Anty maryam ke taso muje domin yakamata aje da matarsa"
Zabin Abdul.K yayi bayyiwa mutane da dama daɗi ba inka ɗauke maleekah saikuma su danginta wato su hilyan da innq Danejo.
Tashi tayi batareda tace komai ba tabi bayansu. A zaune suka samu likitan yana ɗan bubbuga biro akan benci,alamar yashiga tunani.
Sallam Dr.Abdulkareem yayi masa kafin suka ɗanyi magana ta likitoci.
Maganar serious Doctorn Jabeer ɗin yafara,dan haka dole sukayi shuru suna sauraransa
"Ehh wato da dafarko banyi niyyar faɗa muku abinda yake damunsa ba,amma tunda abin yazama haka dole ne na karyah rule na patient akan jinyarsa.
Jabeer yana ɗaukene da Matsala ta INSOMNIA,wato cutar da bata barin mutum yasamu bacci da dare batareda magani ba,ko kuma inya samu baccin ma to saiya tashi yajishi a gajiye tamkar bayyi ba.
Shekara uku dasuka wuce yazo shi gwaji nan wajena saboda matsalar cutar,wato lokacin da matarsa tabiyu ta mutu,a lokacin bata yi serious na sosai,amma saboda yawan tension dayake ciki da kuma fargaba a koda yaushe yasa dole muka ɗaurshi akan treatment.
Maimaikon dayana karbar kulawa tayi sauƙi sai abu daya cigaba da hawa,musamman ma a mutuwar matar sa ta uku,wanann lokacin saida muka sakashi bacci na tsawon sati guda kafin yake gane mutane sosai.
A nanne ma damu akan yasanar da familynsa abinda yake damunsa,amma duk da haka yaƙi amincewa,a cewarsa koda sunjin babu abinda zai sanja,musamman mahaifiyar sa haka taso ta ganshi kullum cikin aiki dakuma bin umarninta,koda kuwa hakan zai saka watarana ya faɗi ya gaza.
Magani nasanja masa zuwa wanda yafi nada ƙarfi kaɗan,saboda yadunga samun bacci ya wuce wannan stage ɗin na damuwar,saidai ba'a daɗe ba kuma wani tension ɗin shima yashigomasa wanda magance cutar yayi wuyah a lokacin.
Dan ma akwai lokacin dayazo yasameni yana farincikin yake faɗamin wai akwai matarsa da idan yana kwance a waje tareda ita ko kuma yashiga sashenta yana samun nutsuwa sosai,har yayi bacci batareda shan magani ba.
A lokacin ni kaina nayi murna da farinciki danaji haka,domin mun saba dashi sosai tamkar ɗan da na haifa.
Saidai me.....jiya da daddare nasamu ƙiran wayarsa yana magana numfashinsa yana fita sama sama,tun a lokacin naketa ƙiran wayarsa har Allah yasa ita matarsa maryam da ɗauka,to itace ta kawoshi asibiti ɗazu"
Tun kafin suce wani abun sukaji sautin kukan Hajiyah Zeenah a bakin ƙofah,da alama duk taji abinda likitan yafaɗa akan matsalar ɗannata,anya kuwa zata ƙira kanta da uwa kuwa,wannan abinda ta aikata har yaushe.
"To menene dalilin shiga wannan condition ɗin dayayi a yanzu,sannan me ya haifar masa hakan"
"Bansan dalilin daya sakashi shiga cikin wannan halin ba,amma koma mai menene babban abune sosai,sannan abinda ya haifar shine wanda zan faɗamuku dana ƙiraku........
Matsalarsa tayi girma har ta taba masa ƙwaƙwalwa jini yashiga da wani position,sannan kuma yasha magani fiyeda overdose ma,aikin da muke akan sa tun ɗazu na cire toxin ɗin maganinne daga cikin jininsa.
Munyi nasarar yin hakan,saidai akwai aiki a gaba shine zamuyi masa tiyata akai mu zuqe jinin,hakan zai iya zuwa da abubuwa da yawa.
Idan munyi nasara zai tashi batareda ya manta komai ba,kuma inshaallah har matsalarsa ta rashin bacci zata kau.
Idan kuma aka samu akasin haka zai iya tashi,amma kuma zai rasa tunanin sa,inayayi yawa harda rasa hankali ake samu.
Sannan a kowanne bangare idan aka yi zai iya shiga coma wanda bamusan iyah Tsawon lokacin da zayyi ba yana kwance.
Kowanne possibility a ciki 50-50 ne"
"Idan kuma ba'ayi tiyatar ba kuma mai zai faru?"
Sai yanzu bombee tayi magana tun ɗazun datake wajen.
"Uhm idan ba'a yiba zamu sakashi ne a na'urar dazata dunga saka ƙwaƙwalwarsa bacci duk bayan wasu awanni,wanda hakan is no a solution"
"To kawai ayi tiyatar,na tabbatar inshaallah zai tashi lafiya,batun shiga coma kuma muna masa fatan kada ya shiga doguwa,zamuyi ta masa Addu'a har Allah yasa yasamu lafiya,akwai wanda suke jiran tashinsa,dan haka inshaallah zai tashi batareda matsala ba.
Ina kyautata zaton hakan,idan akwai wajen sign na matarsa ga bani nayi,inason barin wajennan"
Dukkansu basuce komai ba har likitan ya miƙa mata takardar.
Karba tayi cikeda dauriya,duk da kowa yana kulada yanda hannunta yake rawa..
Sign ɗin tayi cikin sanyin rai ta miƙa masa takardar ta fita a wajen,hannu tasaka da ɗauke ƙwallar hawayen da take shirin zubomata.
A bakin ƙofah ta samu Hajiyah Zeenah a zaune tana rabzar kuka,kaman bata ganta ba haka tawuce tabarta a wajen,haushi iya haushi take ji gameda ita,domin duk abinda yafaru da rayuwarsa tana da kaso mafi tsoka akai,shine dan munafurci tazo ta takure tana kuka..
Shirye shiryen tiyatar aka farayi bayan an biya maƙudan kuɗi,sai zuwa washagari zasuyi masa tiyatar,kafinnan jikinsa yayi relax ba kaman yanzu ba.
Sau ɗaya aka bawa su bombee damar su ganshi,shima kuma ta glass ɗin ƙofah ne,daga nan kowa aka bashi damar tafiya gida,domin basa buƙatar kowa ya shiga wajensa.
A gidan baya take a motar,dan yanzu batada ƙarfin tuƙa wani abu waishi mota.
Gidanta direct hilyan ta wuce da ita hadda su sukkansu,domin a halinda take cikin tana buƙatar zama a cikin mutane.
Wanka hilyan tasakata tayi tarama sallolin da ake binta kafin takawo mata abinci.
Nan ma daƙyar taci abincin sama sama,daganan ta kwanta bacci ya ɗauketa.
Tsakar dare bombee ta tashi ta ɗauro alwala tafara salloli,tun tanayi har jinkinta ya gaji da zauna,anan ma Addu'a tacigaba da zubawa kala kala,duk akan neman lafiya ne ga mijinnata,wanda yake gadon asibiti rai a hannun Allah..
Tun duru duru ba'a daɗe dayin sallahr asuba ba suka nufi asibitin,kasancewar da wuri za'a shiga tiyatar.
Duk da cewa ba magana zaimusu ba ko yasan suna wajen,amma ganinsa kafin ya turashi ɗakin ma abune da basaso ya wuce su.
Ƙarfe 7:00 am daidai aka gama shirya tiyatar,suna nan tsaye a corridor ɗin aka turoshi,duk jikinsa an sassaka igiyoyi.
Ƙuri sukayi masa da ido kaman idan suka ƙirfa zai bace,da haka suna kallo har aka shiga dashi ɗakin ƙofah taja tarufe.
Hajiyah Zeenah da sayyada-tateen a tare suka saki kuka suna zubewa a wajen.
Kowa a wajen bashida bakin faɗa musu suyi shuru,alhj Abdullahi ne ma wanda abin bai shigeshi sosai ba yake ƙoƙarin basu haƙuri,itakam Lailah batazo bama tun zuwan ta na jiya,a cewarta ɗanta itama bashida lafiya,intazo ma ba abinda zata ƙara ko kuma ta rage.


Ƙarfe shabiyu daidai aka gama tiyatar,kuma Alhamdulillah anyi nasara,yanzu kuma sai ya farfaɗo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login