Showing 117001 words to 120000 words out of 134612 words
maryam shiɗin mu ceceshi,tunda babu abinda yayi?"
"Ahah koda kin ceceshi yazakiyi dashi,shikansa naga alamun ba cikekken mutum bane,sannan bakya ganin shine yakeson binta,barsu suje kawai gayyar tsiyah"
Bata gama rufe baki ba Zilliyyah taƙarisa shigewa cikin madubi itada ɗanta,wani haskene yafito mai ƙarfi wanda ya tarwatsa madubin kashi kashi..
Hakan a tare ya wakana da zubewar bombee ƙasa sumammiyah.
*** ***
Yauma kamar kullum yana tashi daga aikinsa yanufi gida,sashen lubnah ya nufa yacire kayansa yayi wanka.
Sallar la'asar ya haɗa da kuma magriba,ko Addu'a bayyi ba ya tashi ya naɗe sallayar,saboda lubnah tace masa kada yasake yayi Addu'a idan yayi sallah,ita kanta sallahr sa'a yaci bata hanashi ba.
Abincin daya shigo dashi a waje ya buɗe yaci,daga nan yasamu waje ya zauna.
Aikin da bayyi ba ya ɗauko yafarayi har lokacin isha,yana sallah yacigaba har cikin dare yana zaune.
Can kaman a sama yaji ana ƙiran sunansa da ƙarfi,bai amsa ba sai waiwayawa dayakeyi domin ganin mai ƙiran,bayan ƙirna yayi shuru sai yaji an kwaɗa masa wani abu a tsakiyar kansa,mai makon yaji zafi sai yaji tamkar ana warware masa wata igiya.
Riƙe kan yayi da hannyensa biyu,daga nan ya bingire a wajen sumamme.
*** ***
Tun safe har dare ya shiga brr na'imah bata zauna ba,yanzu ma zirga zirga take a cikin talatainin dare,saiga Gen abdu manga yashigo shida su lubnah,da sauri ta taresu tana duddubasu ko anyi musu wani abun,ganin komai sumul yasa ta maida ajiyar zuciya.
"Sannu maza muje ki wanke jikinki ki ci abinci ki huta,hmmm ai Lailah ta ɗebo ruwan dafa kanta,dani take zancenne"
"Mommy Lailah kuma,wacce lailan?"
"Wacce ta ɗaukeki mana?"
"Ba Lailah ce ta ɗaureni ba,maryam ce fah matar Jabeer,wacce nake faɗamiki muna sa insa da ita,tantiriyace ta bugawa a taro,domin bata tsoro ko kaɗan"
"Maryam kuma,to itakuma menene nata na kamaki"
"Uhm da alama tasan nayi wanannan aikin,dan cewa tayi bazata sakeni ba sai nayi wata guda,saikuma gashi wai ta sakeni a sati uku.
Ƙaƙƙarfa ce naji wasu yaranta hilyan da khmees sunace mata captain dai,yawwa akwai wani sunanta ma Bombee"
Zaro ido su brr na'imah sukayi a tare,wayarsa ya ciro ya danna wani hoto ya miƙawa lubnah.
Hoton bombee ne da kayan sojoji ta sara,kanta da jar hula irinta captain.
"Lahh itace ai,ya akayi na ganta da kayan sojoji,no wonder nake tunanin kaman na taba ganinta a barrack mana"
Wani duka brr na'imah ta kaiwa lubnah,dukkuwa da halin da take ciki.
"Nikam mai yasamu rayuwata na haɗu da dolayen ƴaƴane?
Tsohuwar maƙiyarki kina zaune da ita amma baki sani ba,har saida tagama dake kaff,Tazo da daɗi ma da bata barki kinyi watan ba,saikije ki wanke wannan dauɗar kana kici abinci."
Cikeda takaici ta wuce ɗakinta,ko ammar bata kalla ba wanda yake zaune akan kujera ya mimmiƙe ƙafafu.
Tana tunanin tasan kan matsalar ashe duk ba haka bane,koda yake itama bombee bazata gagareta ba,abinda yafi bata mamaki shine ya akayi taje gidan ƴar ta a matsayin kishiyarta batareda tasani ba,yarinyar da shari'a take nemanta itace take cikin garin hankali kwance,kuma harda sace mata ƴaƴa,duk yadda akayi fansa takeson dauka ta hanyar katse mata burinta na mallakar JAAN Company'.
Ihun da lubnah ta kwarara da safene yasakata firgit tatashi ta nufi dakin nata da sauri,bata ganta a dakin ba dan haka ta shiga banɗaki inda take jiyo kukannata.
A tsaye take a bakin sink tana kallon wani ruwa mai kauri da wari kalar ruwan ɗorawa,wanda yake fita daga ƙasanta.
Itama brr na'imah wacce take bayanta saurin toshe hancinta tayi tareda girgiza kai.
"Ba haka bane,hakan bazata sabu ba,ai baki cika wata gudan ba,bahaka mukayi da Zilliyyah ba,mai yasa haka zata faru"
Komawa dabaya take tana maimaita duk abinda yazo bakinta,har bata saniba tayi tuntube ta drawer gaffo.
Miƙewa tayi batareda duba gurdiyar datayi ba tayi hanyar ɗakinta.
Gen abdu manga ta tarar a zaune a tsakiyar gado yayi haɗa kai da gwiwa yana kuka tamkar ƙaramin yaro.
Magana brr na'imah tayimasa amma ko kulata bayyi ba,abinda ya faɗane taji tamkar notin kanta ya kunce.
"Na'imah kincuceni duniya da lahira,Allah ne kaɗai zaimin hisabi dake ranar gobe ƙiyama,kin zalunceni,kin rabani da aminina Bello,kinsaka naci amanarsa na zalunceshi na kashe masa ɗan sa,yarinyar da bataji bata ganiba kinsaka na ɗora mata laifin da bata aikata ba,aminina yariƙe ta amana,amma saida kika saka ya koreta daga gareshi a matsayin wacce ta kashe masa dansa.
Hakan bai isheki ba saida kika sakani farmakar dukiyar surukina Na'imah,nikuwa mai nene bakimin ba,Allah saiki innata saida tace kada na aureki tun farko,amma nayi kunnen uwar shegu da ita,ni a dole inasonki,yanzu mai gari ya waya damai na amfana a zamana dake.
Wannan iya abinda nasani kenan,wanda bansani ba bila adadinne nasan"
Komawa tayi da sanɗa da bar ɗakin batareda tayi magana ba,dan batada amsar waɗannan maganganunnasa,tabbas akwai gagarumar matsala indai aikin kansa ne ya kwance.
Ɗakin data ajiye madubinta ta nufah,tana yaye ƙyallen dayake jiki da kalli hotonta a tsaye a ciki kamar kowanne sauran madubai.
Sab'anin da dazata ga duhu baƙiƙƙirin,inata saka hayaƙi sai Zilliyyah ta bayyana.
Bata daddara ba hayaƙin da dauka ta banga,saida suka kare tass batareda madubin yayi komai ba.
Wani duka takai masa da ƙafa saida ya tawarwatse gabaɗaya.
Kaman lubnah itama zaman durshan tayi a wajen tana nata kukan,zagi kuwa sa tsinuwa babu wanda batayiwa Zilliyyah ba,gashi banda ƙaiƙayi babu abinda jikinta yakeyi,saidai ba kamar wanda zai zautata ba.
"Mommy ni......nikam zan koma gida wajen Jabeer....inaga idan naganshi komai zai dawo daidai"
Tana kukanne take maganar.
Ɗan tsayawa brr na'imah tayi da kukan tareda cewa.
"Yakikayi da ruwan dayake zubowan ya daina?"
"Ahah bai dainaba ƙunzugu nayi,idan naje gida saina wanke nasake saka wani,in yaciba a haka nashiga uku mommy nikam duk yadda za'ayi ma kiyi wannan masifar ta daina fitomin"
Bata maida mata martanin maganar ba,dan intace tanada abincewa ma tayi ƙarya,maida gabanta tasakeyi inda madubin yafashe yanzu,tanajin lubnah ta tada mota tabar gidan.
Cikin sanɗa ta fita daga motarta tashige sashenta,lokacin data shiga ɗakin Jabeer yana kwance a falo yana bacci,mamaki abin yabawa lubnah,saidai bata ce komai ba zage tashiga banɗaki,domin cire ƙunzugun dayake jikinta.
Wasu kayan ta sanja tasake fitowa falon,har sannan yana nan kwance a inda tabarshi,matsawa inda yake tayi tareda bubbuga bayansa.
"Honey lafiya kake bacci anan,duk saboda kana jirana na dawo koh,gani na dawo tashi ka ganni"
Tashi Jabeer yayi yana mutstsika ido tareda ƙarewa inda yake kallo.
"Anan nayi bacci?"
"Uhm yanzu nadawo naganka a wajen a kwance,common i miss you"
Lubnah ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin rungume Jabeer"
Saurin tureta yayi daga jikinsa yana mata kallon bakida hankali.
"Ya isa haka lubnah,duk abinda kikayi bai isheki ba har yanzu,kijira dawowata ki karbi sakamakonki,abin yatsaya kuma iya haka"
Miƙewa yayi tsaye ko kallonta bai sakeyi ba yashiga part ɗinsa ta falonnata.
Banɗaki ya shiga ya dauro alwala,yana share hawaye ya tada sallahr asubar da bayyi ba,bayan yagama yadaɗe yana kuka akan sallayar kafin ya tashi.
Babu abinda ya faɗo masa a rai sai Jaleelah,gwanda ma Jawaheer ita gidan ba baƙonta bane,amma ita fah babu wanda tasani a gidan saishi,amma haka ya ɗauke kansa tamkar bai santa ba sanadiyyar lubnah,koya takeji oho?
Yasan a yanzu tana matuƙar jin haushinsa ba kaɗan ba.
Naɗe sallayar yayi da sauri ya nufi sashenta,ko kulawa da neman abinda zai saka a cikinsa bayyi ba,gashi rana tayi sosai sha biyu takusa.
Murɗa ƙofar sashenta yayi ya shiga,rabonsa da taka wajen tun wata uku dasuka wuce.
Zaro ido yayi yana sake mutstsikawa,ko har yanzu bai farka daga mafarki bane kai?
Domin shidai yasan bahaka yasan falonnata ba,wanda a yanzu yake dauke da wasu danƙara danƙaran funitures da ba iya a nigeria bama anaji dasu.
Ma'aikata kusan ukune suke kai kawo a falon,kaman sansanin ƴar sarki,wata nasaka turaren ƙamshi,wata na gyara labulayen falon,wata kuma sai mopping ɗin falon take da wata na'ura mai matuƙar tsada.
Basu taba tsammanin wani zai shigo daga ƙofar dayake tsaye ba,dan haka ko kulada shi basuyi ba saida yayi gyaran murya tukunna.
Dukkansu zubewa sukai suna gaisheshi,duk da kana ganin mamaki ƙarara akan fuskarsu na ganinsa a sashen.
"Jaleelah fah tana ina,kota sanja sashene?
"Ahah Hajiya Jaleelah tana sashen Jawaheer yau"
"Sashen Jawaheer kuma?,mai tajeyi can kuma?"
"Uhm idan suka yi kwana ɗaya anan washagari kuma can suke zuwa ranka ya daɗe"
Abin yasha masa kai,saidai bai sake tambayarsu ba ya nufi sashen Jawaheer ɗin.
Yanda na Jaleelah yake itama hakan nata yake sakk iri ɗaya,kala ne kawai ta bambamtasu,saidai nan tsitt kakeji babu alamar sawun masu aiki.
Ɗakinta ya nufah,batareda yayi magana ba ya buɗe,dan duk a zatonsa hade kai sukayi suna mutunci,tunda ya ɗauke musu ƙafah,duk sai yaji yanajin haushin kansa gameda abinda ya faru.......
Tunanin dayakeyi yatsayar dashi cakk sakamakon abinda yayi arba dashi a ɗakin.
Ɗakin har yafi falon ƙwatuwa da kuma kaya masu tsada,wannan shine abin burgewar ɗakin,abin takaicin kuma wanda ya riski Jabeer dabai taba tunanin sa a mafarki ba shine ganin amarennasa a gado ɗaya tsirara haihuwa uwarsu suna masha'a.
Sun wani kanannaɗe tamkar macijai a waje ɗaya,deep kiss suke aikawa junansu,sai bayan sun raba bakinsu kafin Jawaheer ta shafi fuskar Jaleelah.
"My reddish slender i love you,ina sanki fiyeda komai nawa,ni nafi ganinki a ja maimakon baƙa........bantaba tunani ba ko a mafarki wai zan haɗu dake ido da ido kuma a waje ɗaya"
Hannun Jawaheer da kama tasaka a bakinta tana tsotsa,saida tacire kafin ta ɗora da cewar.
"Uhmmm nima haɗuwa ta dake is my blessing,saboda a lokacinne na koyi yanda zanfito da maƙudan kuɗaɗena nayi facaka dasu,abinda yafi bani dariya dake,shine yanda kike nuna kishina a dubai idan Jabeer yajani ɗaki.
Wow i love this side of you my lady,shifa yayi zaton sonsa nake koh???"
Dariya suka saka a tare,kana suka sake haɗewa waje daya.
Gabaɗaya basu kulada Jabeer ba wanda yake tsaye akansu jikinsa yana rawa.
Jijjiga kai yake saboda wani duhu dayake gani,lokacin daya samu kallonsa ya dawo daidai ɗakinsa ya koma da gudu.
Drawer dayake zuba magunguna ya buɗe,amma babu koɗaya a ciki,da alama bombee ce ta ɗebesu..
Gwauron numfashi yaja mai zafi yana murza kai,ganin abin bazai kaishi ba ya dauki makullan motarsa yanufi waje dasauri.
Ko gama bawa motar wuta bayyi ba yafigeta ya fice a gidan.
*** ***
Da farin silin ta haɗa ido lokacin data farfaɗo akan gadon asibitin.
Tashi tayi ta zauna tareda fige ruwan dayake shiga cikin jikinta.
Hilyan ce ta taso da sauri daga kan kujerar tanufo inda take.
"Anty mar...."
""Karfe nawa ne yanzu?"
"Uhm 12:30 ne"
"Ina inna tatashi kuwa?"
"Ahah bata tashi ba har yanzu,amma itama daidai lokacin dakika faɗi sanann ta suma"
"Maza tayarmin da motata yanzunnan barina gyara nafito mu tafi gida,nasan tana wajen da za'a kulada ita,Jabeer yana gida maybe zuwa yanzu nasan shima yatashi"
Daga kai kawai hilyan tayi tareda fita waje,abinka da jinin sojoji koda ya daskare,tun kafin tagama fitoda motar a wajen parking harta shiga wajen drivern ta karba a hannun hilyan.
Figar motar tayi da gudu zuwa gida,daidai zuwa shigar motar taga mota ta fita a gidan a guje kaman mai shirin tashi sama,bata kulada da waye ba tasaka kan tata motar zuwa ciki.
A bakin sashen su tayi parking,bata shiga part ɗintaba don tasan koda yajema to zaiga bata nan,lubnah kuwa tayi zaton tana gidansu,dan tasan zuwa yanzu taga sakamako.
Sashen Jaleelah ta nufah da sauri ko yaje can.
Masu aiki ta tarar suna ta goge,gaisheta sukayi,bata amsa ba saima jefa musu tambaya da tayi.
"Jabeer yashigo nan kuwa yanzu?"
"Eh yashigo ranki ya daɗe,saidai da mukace masa Hajiyah Jaleelah tana sashen Jawaheer to ya tafi can"
'Tabb Allah yasa bayyi mugun gamo ba ameen'
Tafada a ranta,cikin sanyin jiki ta nufi sashen Jawaheer ɗin,abinda take gudu shiya faru,domin tun a daga falon ta hango ƙofar ɗakinta a buɗe yanda ya barta,ga nan center table ya goce inda yayi hanya yabar falon.
Waya da ɗauka ta ƙira Security office na bakin get.
"Hello motar danayi clear da ita a bakin get wanene a ciki?"
"Ranki ya daɗe ogah Jabeer ne a ciki,kuma da alama baya cikin yanayi mai dadai,domin a zuciye ya bamu umarnin bude get ɗin"
"Kuma da kukaga haka babu wanda kuka ƙira koh?"
"Kiyi......"
Ƙitt ta kashe ƙiran tareda jan zuciya.
A zuciye ta karisa ɗakin da su Jawaheer tareda jingina a jikin ƙofar tana kallonsu.
Ganin basu san ma tana tsaye ba yasata yin tafi guda uku da hannunta.
"Hii less ladies the plessure has stopped,everything you did is on the camera"
(Barka yan mata,daɗi ya ƙare,komai kukayi yana cikin camera!!!)
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________
Page 🖤 49••50🖤
Rawa jikinsu ya fara suna neman abinda zasu tare jikinsu dashi.
Duk abinda suke bombee tana kallonsu daga inda ta jijgina
"Miye kuke wani karkarwa,ohh da bakusan ba daidai kuke aikatawa ba sai yanzu,ai bakuji komai bama tukunna sai kunji wanene yaganku a haka yanzu.
Mijinku yazo yana murna da farincikin faɗawa masoyiyarsa ya warke,gashi ya dawo gareta,amma mai zai tarar,a kwance yaganta da fitsara da kishiyarta,wato ɗaya matar tasa,shin idan kune wanne hali zaku shiga in kuka ga haka....?"
Shuru sukayi suna saurarenta,zuwa yanzu kowa ta samu towel ta ɗaura a jikinta,wayarta ta danna,can saiga hilyan tashigo ɗakin.
"Kinzo da bulalar?"
"Eh nazo ta ita,gata ma a hannuna,mai suka sata haka? Rabonki dayin amfani da ita kin daɗe sai yau"
"Ba surutu na tsayayi ba anan wajen,na turawa security da khmees kan su bi bayansa nizan tafi naga mai yake faruwa.
Ki tabbatar kinwa ko waccensu bulala ɗari ɗari,bayan sun gama su gyara kaff ilahirin part ɗinnan gabaɗaya,idan suka gama su wankemin kayana gabaɗaya,daga nan kuma zan faɗi abinda zasuyi gaba."
Har zata fita ta dawo ta kallesu,wanda idonsu ya raina fata.
"Jawaheer ce ta samu ƙarfin halin cewar"
"Mai kike nufi?"
"Bayi bayi kuka zama,da mai kuke tunani sai kawai naje nace ga abinda kukayi,ahah ahah wannan bazai faruba,ni dama na daɗe da sanin abinda kuke,hatta kadarorinku da su asusun bnakinku na sirri duk nasani,sannan kaff sashenku a cike yake dam da camerori wanda sukeyimin record na abinda kuke aikawa.
To ko iya haka na barku kunsan kuna hannuna,laifinku na cin amanar mijinku da sakashi cikin wani yanayi zaku girba.
Hilyan ki cika aikinki,sannan kibasu takardun dukka dukiyoyin da suka tara harda na banki suyimin sign kafin na dawo,duk kuma wacce ta kuskura ta saka ƙafa tabar gidannan batareda izinina ba,hmmmm ta kaɗe har ganye,sannan kuma yana gareku ku bari danginku su ɗau matakin abinda zanyi muku,a ranar zan shaida musu mai kuke.
Hilyan a cigaba da gashi"
Ƙirane ya shigo wayarta,dan haka da sauri ta fita tana magana.
"Me kun bishi baku ganshi ba har yanzu?"
"Ehhh har yanzu fah madam bamu ganshi ba,saidai cctv cameran da muka bi ya nuna cewar hanyar barin gari yabi"
Kashe wayar tayi tareda dannawa khmees ƙira,shima dai har yanzu dai babu wata kafa.
Duba lokaci tayi har an kusa yin la'asar,daga inda take tsaye a falonta tana jiyo ihun su Jawaheer waɗanda suke cin kakarsu a hannun matashiyar sojan.
Ɗakinta ta nufah ta ɗauko wasu takardu ta nufi sashen Hajiyah Zeenah.
Tundaga bakin falon take jiyo maganarsu da kuma ƙarar cokala.
A zaune suke a dinning tunda ga kan alhj aliyu har dasu Abdulmaleek,kasancewar yau juma'a dama tare suke cin abinci idan an saƙƙo a masallaci.
Ƙare musu kallo tayi na takaici kafin ta nufi wajen dinning ɗin ko sallama babu.
Gaban Hajiyah Zeenah taje tayi dire mata takardun dasuke hannunta..
"Sign"
Ta wulla mata biro tana kallonta,itama Hajiyah Zeenah kallon bombee take cikeda mamaki.
"Baki gane takardun bane ko kuma nayi miki bayani tukunna"
"Amma......."
"Nagama miki aikinki,in baki yarda ba kije sashenta ki ganta da idonki,nice nan nayi kidnapping ɗinta dama bakowa ba,dan haka gatacan na dawo da ita sashenta.
Ɗaiɗaita rayuwarta kikasakani nayi tayanda zata buƙaci saki daga wajen ɗanki da kanta,yanzu ba iya wannan nayi ba,harda karya asirin datayimsa nayi.
Dan haka nina gama aikina a wannan gidan da a waje yakeda kyau amma cikinsa kurkune..
Kin haɗa familynki kuna cin abinci cikin kwanciyar hankali,batareda kinsan inda babban ɗannaki yake ba tun safe,ni kuwa anya ma kece uwarsa? Da alama bakya neman inda yake sai zakiyimasa aure ko kuma zai kulamiki da dukiyar gidan.
Nizan tafi daga nan,mun gama aiki dake tunda na cika aiki,jan jira idan kika samo ɗanki daya fita daga gida dun sassafe a zauce sai ki tambayeshi ya sakeni,inkuma takaicin duniya ya kasheshi matan dakika auramasa kuma sai nayi takaba..
Ga waɗannan takardun(ta faɗa tana sake wulla mata wasu takardun)
"Share ne na Companyn ku dayake hannun brr na'imah,wacce ta daɗe tana shiri na karbar sa daga hannunku,nasakata ta fanshesu da ƴaƴan ta.
Ba iya ita kaɗaiba a kwai sauran mutane irinta masu son Companyn,ni yanzu zan tafi ga nawa iyalan sun jirana,ruwanku ku ɗau matakin da kuma nemo halinda ɗanku yake ciki"
Wani kallo tabi dukkan table ɗin dashi kafin tafita daga cikin falon a zuciye.
Yanda kasan ruwa yazo ya cinye falon haka sukayi.
Dan jin maganganun bombee sukayi kaman a mafarki,lokaci ɗaya kuma suka fara ƙoƙarin yadda zasuyi.
Hajiyah Zeenah kuwa wacce takula da hankalin su yabar kanta,ɗakinta ta wuce da sauri tana yarfe gumin dayake zubo mata,shikenan bombee ta gama da ita a cikin iyalanta,yanzu kowa yasan abinda ta aikata,dama kuwa saida alhj Aliyu ya faɗamata cewar zatayi nadamar kawo bombee cikin gidanta.
A bangaren uwar gayyar kuwa direct gidan malamin ta nufa inda mahaifiyar ta take.
A zaune taka akan gado wata mata tana bata shayi a baki,gefenta kuma Inayah ce da innayi suna riƙe da hannayenta ta kowanne bangare.
Tsaida kallonta tayi akan ƙofar inda bombee take tsaye,kana ganin kallon kasan ta dade batayi ba,saidai ta alama tagane ƴar tata sosai.
Hawayene yake zubowa akan kumatun bombee,sai yau tasamu hawayen ta suka zubo,bayan wasu shekaru dasuka shuɗe an hanata sakinsu daga jikinta..
Zubewa tayi a gaban innar tata cikin karayar zuciya,kanta ta ɗora a cinyarta,take kuwa tafara rabzar kuka kaman anyi mata saqon mutuwa,saidai kanajin kukan kasan irin wanda mutum ya daɗe yana tarawa ne.
Ganin hakanne yasa su Inayah da matar da take bata abincin barin ɗakin da sauri,domin su bawa ƴar da uwar waje.
Saida inna Danejo ta barta tasha kukanta kafin ta ɗora hannunta akan bayanta tana bubbugawa.
"Bbb.......bommbeee"
Tafaɗa a hankali cikin ƙaramar murya,kamar mai son koyon magana.
"Inna inna ta kin ƙira sunana innata"
Ɗagowa tayi da fuskar shabe shabe da hawaye tanayiwa inna Danejo dariyah..
Hannu tasaka tana share mata hawayen tareda