Showing 72001 words to 75000 words out of 134612 words

Chapter 25 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8695

Bombee tayi tareda cewa.
"Karki damu ummah shikansa girkin zan baki mamaki akan sa,ba iyah wannan ba kaɗai"
"Wow mashaallah dakuwa kin burgeni sosai,mace duk inda takai da ƙwarewa kan wasu abubuwan,to a sameta ta bangaren girki ma ƴa ta,koba yanzu watarana hakan zai miki amfani a gaba ina faɗamiki"
Ɗaga kai Bombee tayi alamar taji.
Gen Muhammad dake baƙin ƙofah abin dariyah yabashi,kuma shi kansa Bombee baƙaramin burgeshi tayi ba yau ɗin,lokacin da aka juyo ana tayashi murnar samun jaruma kaamarta,cike da alfahari yake amsawa,danji yake tamkar ƴarsa ce ta cikinsa.
Wata takarda ce a hannunsa,wacce ya biya ya karba suna tahowa.
Miƙawa Bombee yayi tareda cewa.
"Ga kyautata ta musamman bisa bajintar da kika nuna a yau"
Tun kafin ta karba Haidar ya karba tareda buɗewa,takardune a ciki wanda suke ɗauke da sunan Bombee.
"Wow wow Bombee admission ne makarantar mu a Rasha Abba yabaki,kema yasaya miki form yabiya kuɗin makaranta da komai"
Zaro ido Bombee tayi jin maganar da haidar yake faɗa tamkar a mafarki yake yi mata ita,zamewa tayi kamar mutum mutumi,ta kalli wannan kana ta juya ta kalli wanann,tarasa ma shin mai zatace gameda labarin dataji,makarantar sojoji yasakata,hakan ma ba a ƙasar nan ba inda ɗansa yakeyi?
"Ƙwarai Maryam dagaskene abinda yafaɗa miki,munyi magana dama da aminina dake can wanda haidar take wajensa,nayi masa bayani akanki da kuma kuɗurinki na son cikar mafarkinki,a jiyan yagama cike ciken komai da komai na shigarki makarantar.
Dama akwai abinda zai maidani ƙasar,dan haka zamu tafi tareda a gama komai da komai kifara karatu da kuma karbar horo a can,duk da yakamata ace kinshiga tunda wuri,amma munyi musu bayanin ƙwarewarki kuma nasan zaki nuna musu hakan bazaki bamu kunya ba.
Yaraf ta zube akan gwiwoyinta akan abban tareda riƙe ƙafafunsa.
"Mezai sakani baka kunya da irin abinda kayimin abba? Ai ina mai tabbatar maka baxan taba baka kunya ba saima mamaki,Zanyi matuƙar ƙoƙarina nayi amfani da wannan damar daka bani.
Saidai gameda godiya bansan mai zancen ba akai,banida kalmomin dazasu isheni wajen godiyar. haidar Ummah ku taimakeni wajen godiyar wanann gagarumar kyauta dayayimin"
Dukkansu ɗagowa Bombee sukayi daga ƙasa,inbadan idonta ya daɗe da ƙaiƙashewa da kuka ba dayanzu ta zubar da hawaye yayi cikin kofi.
"Baki buƙatar yimin godiya maryam,ni kin wadatar dani dakika nuna ra'ayin yin aikin,saidai abu ɗaya nake so kiyimin alfarma shine......Duk da cewa muradin rankine yasaka ki yin wanann aikin,ina so ki saka muradin kare ƙasarki a farko kafin naki muradin,ta hakanne zaki zamo jarumar a ƙasarki ta gado,kuma ki zamo kariya ga rayukan al'umma.
Idan kikayi hakan kigama yimin godiya akan abinda nayimiki"
"Angama zanyi yadda kace abbah,daga yau zan ajiye muradina har sai na yiwa ƙasata aiki tukunna,na tsaida gaskiyah da kuma adalci tukunna,sannan zan tsayah na kare ƙasata da kuma rayukan al'ummata da rayuwata"
"Shikenan ku shiryah tafiya to Allah yamiki albarka"


Shiryen tafiyar su Bombee aka farayi,dan gabaɗaya gidan suka tafi,inyaso sai su dawo bayan angama komai.
Kaman yanda gen Muhammad ya faɗamata kuwa saida akayi mata gwaji wanda zai tabbatar shin zata iyah ajin da haidar yake,wato division 2C.
Duk da tasha wahala amma kuma tayi nasara,don saida tayi sati guda tana training tukunna.
Satinsu gen Muhammad biyu suka jiyo,bayan sun tabbatar babu wata matsala,kusan haidar yafi kowa murna da zuwan Bombee ɗin,wanda bai taba zato ba.
Bayan shekara Uku da zuwan Bombee Ƙasar rasha zuwanta nigeria baifi Sau uku,kowanne kuma hutun,shima dukka hutun ƙarshen shakane da ake basu. Abubuwa da dama su faru,ciki harda Nasarori data samu da a mission masu yawa da ake yawan turasu kasashe.
Ta girma kwarjini da haiba sun bayyana mata,Iduwanta sun saje da yanayin kasar,inba tayi hausa ba bazakace dama baƙar fata bace.
Tana farin jinin mutane sosai,saidai kuma kowa yasanta bata ɗaukan raini,mussaman ga waɗanda suke a ƙasanta a makarantar.
A cikin shekaru goma sha takwas tayi nasarar shiga matakin finale divition,wanda zasuyi shekara ɗaya a ciki kafin su gama.
Shikuma Haidar yagama nasa karatun wannan shekarar,saboda dama shi nasa bangaren na abinda ya shafi na'ura ne dakuma su haiking ko detecting,shiyasa dole zai koma gida ya barta.
Da farko yaso zama har sai ta gama,kuma dama Air force na yankinsu sun nemeshi yayi aiki dasu,Gen Muhammad ne ya nuna ƙin amincewarsa,kan cewar saidai su dawo gida suyi aiki a inda yake wato Abuja.
Hakanne yasa yataho barta saita gama tukunna.
Kuma dama a lokacin ma bata ƙasar sun tafi practical training a ƙasar Iraq. Wanda aka turasu duk yana cikin Exam ɗinsu.
"Wonder woman nikam zan tafi gida,abbah yacemin nakoma basai na jiraki ba"
"Dama menene najirannawa kaman wata jaririyah,Man a ɗaga hanya ayi gida kawai,saina iso nima inaga zanyi koƙarin gama aikina zuwa nan da wata shida"
"Haka ma zakice bakya kewata koh?"
"Nayi kewarka,Haleesa ce ni(Wata ƴar Lebanon ce a division ɗin su Bombee ta nace shi take so,hakanne ma yasa ta mannewa Bombee tana ce twin sister ce) dazanyi kewarka iyeee?"
"Mtsww dan Allah kibar zancennan mana,wai serious baki damu ba zan tafi na barki"
"Dama dani kazo,ina ka rigani zuwa,nayi ƙoƙari ma daya zamo iya ratan shekara guda zaka bani......kai sai anjima muna cikin sahara ga zafin rana,kayi distarcting ɗina,bakajin ƙarar bullet ne?"
"Inaji mana i know is normal ai,menene na ɗaga hankalin kece fah,Captain ta farko a School ɗin mace mai shekara goma sha takwas"
Yaƙarisa maganar yana dariyah.
"Gerrot bakada aikinyi Ka gaida su ummah,ina bata kewata danna buge mata yara wancan hutun koh"
"Ohh wannan keda ita"
Katse wayar tayi tareda yin ƙaramin murmushi tana tuno Alkhairin familyn gareta,wanda duk tsiyarta bazata manta ba.
Wanda gashi sanadiyyarsu tana shirin cika muradinta na zama jaruma,wacce zata ƙwaci kanta idan za'a zalunceta.


BAYAN WATA SHIDA




A cike filin yaye ɗaliban da ɗumbin mutane,wasu na farincikin gamawar ƴanuwansu,yayinda wasu kuma nasu ƴan uwan sun mutu a practical ɗin dasukayi.
Ƙiran sunaye ake ana basu certificate ɗinsu na shaidar zama cikakkun sojoji.
Anƙira mutane da dama wanda yawanki dukka mazane..
Ana zuwa rukunin mata itace sunanta yazo a na uku,bayan wata ƴar rashan sai kuma ƴar sudan sai ita.
Ita kaɗai tazo ta karbi nata Certificate ɗin cikin sarawa da nuna girmamawa ga manyan nasu.
Kai tsaye tana karba Dorm ɗinsu ta wuce na mata taɗauki ɗan ƙaramin akwatinta.
Daga nan kuwa tajawoshi zuwa waje.
Sa haseela suka haɗo daga gani dama ita take jira.
Gaisawa sukayi kafin tacewa Bombee. (Cikin harshen turanci)
"Maryam yana ganki ke kaɗai,bazakiyi party ko kuma irin hotuna da Familynki ba,zuwa gobe saiki tafi"
"Ahah bana buƙatar wannan abubuwan,family nama basusan da dawowata ba saina isa tukunna su ganni, Dan sunyi zaton ina cikin Masu fita ne nanda shekara guda"
"Eh haka ne,amma ainihi da sai wani wata shidan zamu fita dake,gaskiya keme sa'a ce maryam"
"Kuma jajircewa,dan saida na jajirce tukunna ba iya sa'ar ba,kinga tafiyata nan dama tunjiya nayi booking na jirgi"
"Ehh am maryam Uhm Haidar.......?"
"Ki ƙirashi idan nemansa kike kin matsu,natafi tacan tacan"
Bombee taƙarisa yimata maganar tana cikin tafiya,saida tayi nisa ta ɗagomata hannu batareda ta juyoba tafiyar kena......


Ƙarfe 2:00pm Agogon nigeria Da Niger Jirgin su Bombee ya sauƙo daga rasha,kasancewar tana cikin guda uku na rukunin mata,yasa a cikin kyautar jinjinawarta kawai tiket dama na jirgi.


Bayan ta jo fitowar daga jirgin saida ta tsayah tukunna ta shaqi iska na daƙiƙu.
Murmushi tayi tareda cewa.
"Na dawo da wacce kuma za'a fara Allah masani"
Sanye take a kayan sojoji,ko sanjawa batayiba daga inda ta aka sallameta,After long dress ta ɗora akan kayan baƙa,sai ta saka hulama baƙa akanta,mai makon Jar hularta ta uniforma.
Boot ɗin sojojine a kafar ta,wanda take tafiya kaman tana faret saboda tsabar sabo.
Ga fatar jikinta tana nan da farinta,saidai kana gani kasan bawani jin dadi ta samu sosai ba.






_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤15••16🖤




Mutane da dama a wajen idonsu na kanta,musamman ganinta da Kayan sojojin rasha ɗin,kuma ga idonta ya nuna daga can ɗin take.


Taxi tazo tara,tana saka hannu zata shiga motar taji anyi mata magana a bayanta.
Security su uku maza. Turanci suka farayimata dan a tunaninsu batajin hausa.
"Am madam daga ina haka,shin zamu iya ganin katin Visa ki?"
"Eh akawai visa amma akwai wannan ma"
Ta mayar musu magana da hausa tareda miƙamusu ID card ɗinta na Shaidar ɗan ƙasa.
"Ko kunfi buƙatar visa kai ba ID card ba"
Taƙarisa magana a zuciye,shuru sukayi cikeda mamaki,wanda hakan yasa itakuma ta juya tashi taxi ɗin.
Kwatancen inda zai kaita tayi masa,tareda kwanciya a jikin kujerar motar tana sakin ajiyayyen numfashi na gajiyah.
Kaman ance da Nu'aimah ta ɗaga kai,tana taimakawa mai aikinsu bawa shuka ruwa,ido biyu sukayi da Bombee wacce take a tsaye a gabanta ta naɗe hannu tana kallonta.
Mitstsika idanuwanta tayi domin shin taga dagaskene Bombee ce a gabanta kowa.
"Addah Bombee dagaske kece nake gani kuwa"
"Uhm ko kin taba ganin wata aljanar dama mai kama dani?"
"Ummah addah Bombee tadawo,wlh dagaske nake kin ganta a waje.
Hajiya Zulaiha ce suka fito a tare itada Farouq.
"Ƴa ta wannan tafiyar kuma fah,ko matsala aka samu a makarantar kika dawo yanzu?"
"Ahha ummah na gama,jiya akayi bikin yayemu ma,a sannan na hau jirgi na taho gida"
Ƙarisowa wajen tayi tareda kama hannun Bombee ɗin
"Naji daɗi danaji cewar kin gama cikin sa'a,saidai banji daɗin yanda kika ɗaukemu ba,tunda har za'ayi bikin gamawarku ki taho batareda munsaniba"
Ɗora ɗaya hannun nata tayi akan na Hajiya Zulaiha kafin ta ɗora da cewar.
"Ahah ummah banason ɗoramuku nauyine dayawa a kodayaushe,inada kuɗin dazanyi amfani dashi na taho shiyasa kawai ban damu abba ba,nasan idan na faɗa zai iya cewa ma shizai ɗakkoni,bayan busy yake da aiki. Karki damu komai lafiya tunda na dawo zance wuce ummah"
Bombee taƙarisa maganar cikin sigar neman afuwar abinda tayi.
"To shikenan,amma kinyiwa kanki saidai ki zauna a ɗakin Nu'aimah,tunda naki kam baa gyare yake ba,babu wanda yasan da dawowarki"
Daga haka Hajiya Zulaiha tajuya ta shiga cikin gidan suma suka bita a baya,tun a hanya Nu'aimah tafara bata labarin abinda tayi missing.
Bayan taci abinci tayi wanka lafiyar gado tabi,bata daɗe da kwanciya ba su Haidar suka dawo daga waijen aiki shida Abbansu,Hajiya Zulaiha ce ta sanar dasu dawowar Bombee ɗin. Suma sunyi mamakin hakan,duk da zuwa yanzu sunsan halin kayarsu.
Deciding sukayi kan bazasu tasheta ba,gwanda ta huta tukunna.
Hakanne yasa basu haɗuba sai a wajen cin abincin dare.
Hirar yaushe gamo aka fara bayan an gama cin abincin dagannanne kuma magana mai muhimmanci ma tashigo na gameda matsayin Bombee a yanzu,dakuma abinda yadace tafarayi a lokacin.
"Toh maryam yanzu dai tunda kin dawo lfy ɗauke da sakamakon da ake so shine abin farincikin.
Saura kuma aiki,nayi magana da gen captain ɗin dake division ɗina,Zai adding sunanki da ɗaya daga cikin Captain din dake ƙarƙashinsa,idan kinje saiki ga yanda abin yake,domin za'a baki wanda zasu kasance a ƙarƙashinki"
Murmushi Bombee tayi kafin da ɗora dacewar.
"Nagode abbah da duk karramawarka a gareni,inshaaallah zanyi aiki da gaskiya kaman yanda nayi maka alkawari,bazaka taba samuna da wani mungun nufi ba"
"Yawwa naji daɗi hakan,kisake zuwa ki huta kafin zuwa goben to,akwai kyautar dazan miki na wannan gagarumin jarumta da kikayi"
Dare yaɗan raba an daɗe da isha,baccine yagagareta duk yanda taso da tayishi,hakanne yasa ta fito filin gaban gidannsu tana kalle kalle,dama ga farin wata ya haske ƙasa daga sama.
Riga da wandone a jikinta,amma basu kamata ba,sai ƙaramin hijabi data saka ita kafaɗa.
"Ka fito najika"
Fitowa haidar yayi daga inda ya labe yana ganinta,nufar ta yayi yana murmushi na ganinnata,dan dama yaso tunda ta dawo suyi magana amma basuyi ba.
"Ke ma kinkasa baccin koh,hmm har yanzu horon rashin bacci da daddare nima baibar jikina ba,inaga kuma yake?"
"Haka fah,dan ni nafijin daɗi bacci da rana akan dare,ganinsa nake kaman shine lokacin aikina,musamman dama daya zamo ni basuda wani banbanci sosai a wajena"
"Oh wanann ganin darennaki koh,shin ne Dagaskene abinda mutanen garinku ke fada akan idonki ko kuwa"
Ƴar karamar tsukar takaici Bombee tayi kafin tace.
"Hmmm ƴan ranin hankali ba,naje nayi bincike akan hakan,matsalar aljanuna bata shafi idona ba,kowanne zaman kansa daban,kuma kowanne nasan dalilinsa"
Zaro ido haidar yayi tareda cewa
Kina nufin dagaske suke ba kalau kike ba"
"Kana tsoron karna cutar dakaine wata rana?"
Jijjiga kai yayi cikeda jin kunyar zaburar dayayi.
"Ahah idan cutarwane ai da kin cutar dani tun a baya,sannan kuma nine dakaina na tunkare ki ai,duk da nasan kinsha banban da sauran yaran danake gani a lokacin,musamman a cikin mata. Amma yaya idonki kuma menene dalilin dayasa aka haifeki dashi a haka"
Yafaɗa tareda ƙoƙarin kauda wancan zancen.
"Ka fiye tamabaya Haidar,inka matsu kaje kayi bincike akai kaman yanda nayi,shin mai yasa idona ya kasance a haka."
Ta ƙarisa maganar tana ɗaga masa gira,alamar tana challenging ɗinsa,da haka ta bar wajen ta kyaleshi.
Jijjiga kai yayi tareda cewa.
"I love this nature of you maryam,you are amazing"


Washagari da safe tare dukkansu suka nufi barrak din,karon farko tun a ganin level ɗin aikinta ta samu matakin captain batareda matsala ba,zabi aka bata na ta karbi gida ko kuma zata zauna a side din captain dake dorm ɗin mata.
Da farko gen Muhammad yaso ta zauna a gida ta dunga zuwa,musamman dan haka ya bata sabuwar mota dalleliya a matsayin kyautarta,amma haka taja ta tsayah akan a barrack zata zauna,dan haka dole ya ƙyaleta,saita dunga zuwa musu da yawo.


Kayan jikinta ta cire,daga ita sai towel mai adon zanen kakin sojoji,banɗakinta ta nufah na cikin dakinnata,kira ta jiki ba'a magana,musamman kuma jikin daya samu fitaccen workout yanda ya kamata.
Minti biyar ma basu cikaba ta fito daga wankan.
Sharp sharp tasaka kaya ta nufi kitchen ɗinta dake cikin side ɗinta na dorm ɗin.
Omlett ta haɗa na kwai gashashshen biredi sai ruwan tea.
Cikin ƙanƙanin lokacin ta gama komai tayi niyyar fita.
Mai yi mata aiki ce tashi tafara,dan ta faɗamata kan cewar sai tagama komai kafin tazo ta gyara.
Kai tsaye division dinsu ta nufah,inda zata ga ƴan team dinta da suke karƙashinta.
Mutane biyar ne,mata uku maza biyu,wanda Haidar ne yazaba mata da kansa,da alama dama yasansu kenan,itace baƙuwa a cikinsu,daga yanda suke magana da dashi kafin ta iso.
Ɗagowa yayi ya kalleta tana tsaye ƙiƙam tasaka hannun a aljihun wandonta.
"Haidar sannu da aiki,da abokanka ka haɗani ko kuma da waɗanda zasu tayani aiki?"
"Da dukka biyun na haɗaki,kuma zasu taimaka miki fiyeda yanda kike tunani,wannan abokina ne munyi wata shida dashi tare,Shine second captain Wato Khamees ,sai sauran Mabiyan a hankali zaki sansu dukka"
Ƙaremusu kallo Bombee tayi na dan lokaci,kaman yanda yafada kam basu da matsala daga ido,amma dai lokaci ne zai bayyana komai.
Tundaga wannan ranar Bombee takama aiki haikam babu kama hannun yaro,wanda har takai tayi shekara guda tana aiki. A iya cikin wannan lokacin tayi aiki na bajinta da dama,wanda hakan yasa gen Muhammad yakeji da ita da kuma alfahari da ita.
Lokacin tantance Field marshal yayi,za'a dauki ɗayah tsakanin Gen Muhammad da kuma gen Abdu manga.
Kowa a yanzu iya ƙoƙarinsa yake wajen ganin ya kai abokin takararsa ƙasa,shikuma yayi nasara,domin tsawon lokaci aikinsu a kunnen doki yake tafiyah,dole ana buƙatar zakaran dafi.
Harbi ne yake tashi a ta kowanne sako a cikin dokar daji,inda aka tura su Bombee aiki wannan karon.
Ƙirane ya shigo wayar Bombee ta sojoji,saurin dannawa tayi taji muryar Khamees.
"Hello Captain An samu matsala fah,maza kuyi gaggawar barin wajennan muma gamunan tahowa"
"Mai yafaru captain Khamees?"
"Makamanmu dukkansu basuda,mutanenmu da dama sun rasa ransu,ciki harda yan team ɗinmu guda biyu,Saikin kai hari kiji bindigar taki harbawa,kokuma kayan mu ba bullet protection bane mai kyau,idan bullet biyu suka sameshi yagewa yake,akwai matsala sosai,muyi gaggawar juyawa da wuri,Fitilar ma ɗaukewa suke na goshinmu kum......."
Tun kafin yagama magana wayar ta katse,zaro ido Bombee tayi tana kiran sunansa amma shuru bai amsa ba.
Kallon Sojan dayake gefenta tayi,yana da ƙoƙarin saita kunamar bindigarsa amma taki yin aiki,ga fitilar sa ta mutu.
Wani ta gano a nesa ya saita shi,da sauri tayi super a kansa suka faɗi tare.
Hularsa ce ta cire taga wanene.
"Hilyaan dama kece,ina sauran suke,sannna mai yasamu bindigar kika saka harbi"
Saita ji muryar kafin tace.
"Captain inaga da matsala,fitilunmu duk sun mutu,bindigogin ma basa aiki fah"
Ɗaga ta Bombee tayi tareda runtse ido kana ta buɗe,maza ki koma da baya ki faɗawa saura su koma maboyarsu,bari zanje na taho da Tawagar su Captain khamees.
"Ammma captain maryam bakida fitila a hannunki,taya zaki bani taki"
"Dama riketa nayi ba amfani nake da itaba,kedai kiyi yadda nace kawai,maza ki koma"
Tana gama faɗamata haka ta nausa cikin duhuwar dajin kaman an cillata.
Da ƙyar da siɗin goshi suka samu damar barin wajen,bayan wasu a cikinsu sun rasa ransu.
Sati guda akayi ana zaman makoki na rashin Abokan aikinsu da sukayi. Duk da kowa bai kawo komai ba a rashin nasarar,amma su Bombee sun sakawa abinda ya faru ayar tambaya,hakanne yasa suka fara bincike a boye batareda sanin kowa ba.
A zaune take itada khamees a ƙaramin office ɗinta na division din,haidar ne yashigo da kayan aiki a jikinsa,ɗazu yaga ƙiran Bombee bai samu damar zuwa ba sai yanzu.
Gaisawa sukayi da khamees hannu da hannu,sai kuma salute daya mikawa Bombee na wasa.
"Yah captain naga kirnaki inakan aiki,meyake going haka?"
"Uhm inason sanar dakaine cewar,muna buƙatar taimakonka na wani abu dayake faruwa gameda barrack"
Labarin mai suka fuskanta a wajen yaƙi ta faɗamasa dukka,shima kansa yayi mamakin hakan,babban abin ayar tambayarma shine yadda a cikin manya babu wanda yace wani abu kan lamarin.
Ajiyar zuciya ya sake tareda cewa.
"Shikenan naji abinda kukace,inshaaallah zanyi iya ƙoƙarina wajen na taimaka,akwai abokiyar aikina danake son na shigo da ita ciki,tana da jajircewa,kuma taƙware wajen binciken irin waɗannan abubuwan"
"Uhm bazan hanaka kawota ciki ba,amma baka ganin akwai matsala kuwa musaka wata bare?"
"Kai Bombee kidunga koyon yarda mutane mana"
"Ohk shikenan Allah ya taimakemu,amma koma wani bazai taimaka nikam bazan bar rayuwar mutanena ta tafi a banzaba haka nan"
Su shidane sai wacce suke aiki tare na binciken na ura wato Sameerah,sai kuma kuma Bombee da khamees,Hilyaan da kuma Bilal Ɗaya abokinsu daya rage.
A cikin sirri suke aikin batareda sanin kowa ba saisu kaɗai,suka fara gudanar da aikin binciken.
A wani bincike da haidar suke gudanarwa da daddarene suka samo wani clue a cikin daji da daddare,domin akwai motoci dake shigowa suna fita,basa yin hakan kuma sai cikin dare,wanda suke da tabbacin cewar yanada nasaba da bindigoginsu,domin bayan yin yaƙin,tun a hanya wata mota tazo ta tafi da makaman dukkansu,kuma sunga shigar motar wajen a Camera.
A dare suka sanar da su Bombee abinda yake faruwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login