Showing 105001 words to 108000 words out of 134612 words

Chapter 36 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8675

mutum zai gane basonta take ba,dan gashinan a cikin muryar a fili.
Duk falon shuru sukayi da zancen bombee suka kama wani sabo.
Da daddare misalin ƙarfe tara,bombee na zaune tana shan tea taga ƙiran Jabeer a wayarta.
da kaman bazata ɗaga ba saikuma ta ɗauka,batayi magana ba dan haka shine yayi daga ɗaya bangaren.
"Kisameni a falona akwai abinda zan faɗa muku"
Daga haka ya kashe wayar,cigaba da kurbar shayinta tayi a hankali saida ta gama kafin ta miƙe ta shiga ɗaki,nan ma ta daɗe kafin ta fito,wandone 3-quater a jikinta sai t-shirt,dukka kayan baƙaƙe,bata saka ɗan kwali akan ta ba iya ribbon ne kawai,ƙafarta kuma ɗauke da slippers.
Tun lokacin daya ƙira bombee ya ƙira sauran,har suka shirya suka fito ita bata taho,in anjima lubnah da Jawaheer su ja tsaki,itakam Jaleelah dama bata santa ba.
Ƙarar buɗe sashenta sukaji,a tare suka kalli inda zata shigo harda uban gayyar wanda yake zaune a Three seater,lubnah na gefensa sai Jawaheer Jaleelah a ɗaya bangaren,dan sune suka fara shigowa,itama Jawaheer saida tayi nata sarautar kafin tazo.
Tun ɗazu take hararar su Jaleelah da suke gefen Jabeer a zaune.
Ƙarar slippers ɗinta ne yacika falon,hannunta a cikin wandon ta.
A gaban Jabeer ta tsayah tareda ware masa hannu.
Shuru yayi yana kallonta dan baisan mai take nufi ba.
"Common beb give me a hug"
Tashi yayi tareda bin umarninta ya rungumeta kaman yanda ta buƙata,bakin sa yakai kusan kunnenta tareda cewa.
"Meyasa bakyayimin abu sai kinga idon wasu uhm"
"Ko bakasone to sakeni"
"Ahah ina zanƙi wannan jikin mai cikeda taushi da kuma ɗumi,inzan dawwama a haka bazan gaji ba,saidai tsiyar inna fita hankalina babu daman a taimakeni saidai a tafi a barni,a kawomin dalilin dazaisa na haƙura,amma bakomai zai kawo ƙarshen wannan dalilin"
"Sakeni haka ya isheka"
Tafaɗa tana zame jikinta daga nasa,komawa yayi ya zauna yana yi mata dariyar gefen baki,yayinda ta bishi da harara abinda ya faɗa.
Kallon Jaleelah tayi wacce take gefensa a zaune tace.
"Gimbiya tashi ki koma waccar mai ɗaya ki zauna koh?"
"Kallon mai kike cewa tayiwa bombee tareda mai da idonta ga Jabeer domin taji mai zaice"
Shuru yayi yarasa mai zaice,shin Jaleelah dake gefensa zai tasa bombee ta zauna ko kuma bombee zaice takoma kujerar gefe,wanda yasan da tayi hakan ya tabbatar saidai ta bar falon.
"Ohh kallonsa kike saboda kinsan yana sonki bazaice ki tashi ba ƴan mata?,to barikiji wani abu,idan abu mallakina ne ko kuma matsayina,ko bana sonsa a raina babu wanda ya isa yazo yamin shigar kai tsaye ya mallaka,idan takama komai zan iya miƙawa domin mallakarsa,dan haka tashi ki koma inda ɗaya amaryar take ki bani wajena tun kafin raina ya baci"
Jabeer ne ya buɗi baki tareda cewa.
"Jaleelah tashi ki koma wajen Jawaheer ki zauna kinji,nan ba wajenki bane wajen tane a ƙa'ida"
"Ni banga abin tashin hankali a wajen zama ba,umarninka shine abin bina,tunda ka buƙaci na bata wajen babu matsala"
Cikin sanyin jiki ta tashi a wajen takoma kusada Jawaheer.
Murmushin jin daɗin yanda ta karbi maganarsa yayi,dan dama hakan yakeso.
Jawabi ya fara ma su na zaman lafiya,inda ya zartar zai dunga yin kwana ɗaya a ɗakin kowacce daga ya dawo a tafiyar dazasuyi.
Sannan ya sanar dasu wata ɗaya zayyi ya dawo.
Bayan yagama jawabin babu wanda ta yi magana,hakan na nuna sun yarda da hakan kenan.
Daga nan kowa yakama hanyar sashensa sai goben.kowa fuska a murtuƙe,musamman ma lubnah da Jawaheer.
Washagari da safe aka shirya tafiyar su Jaleelah honeymoon tareda Jawaheer Duk da saida akayi dambarwa da Jawaheer akan tafiyarsu da wata matarsa.
Tunda safe ƴan aikinta suka fara ƙoƙarin shiryata,wanda wannan ne kwananta ɗaya a sashennata.
Yasha ado kam na alatun duniya na gani na faɗa,duk side din babu sashen dayakai nata kyau saboda bajintar da hajiya rabi ta nuna a barin dukiya a bikin ƴar tata.
Ruwan wanka masu aiki suka haɗa mata,su uku ne hajiya rabi ta haɗata dasu.
Kafinta fito sun shirya mata breakfast da kuma kayan sakawa,ta haɗe rai tashirya ta fito zuwa sashen Hajiyah Zeenah inda zasuyi mata sallama su tafi.
Tashiga falon kenan hajiya Zeenah tafito daga ɗakinta,Jaleelah kuma na zaune a kujera tana jiran Hajiya.
Tana fitowa kallo ɗaya ta wurgawa Jaleelah daga nan kuma tanufi Jawaheer tana ware mata hannu,rungumeta tayi tamkar ba surukarta ba,
"Yakk Daughter kintashi lfy"
"Yeah kalau natashi,yah Jabeer ɗin ya fito kuwa"
"Ahah baizo ba inaga yana sashen sa tukunna"
Madeenah ce tashigo falon ,bata kalli Jawaheer ba wacce suke magana da Hajiyah Zeenah,wajen Jaleelah ta nufa wacce ke zaune tamkar gunki.
"Anty Jaleelah ya kwanan baƙunta,ko zakizo muje ciki kai kafin yah Jabeer ɗin yazo?"
"Lfy kalau Madeenah,uhm to shikenan babu matsala hakan"
"Ke Madeenah baki ganin Jawaheer ne wacce a yanzu take matsayin matar yayanki,bazaki gaisheta ba"
"Uhm mommah wannan ma ai matar yayannawa ce,inaga ai babu banbanci duk wacce na kulama a ciki ɗayane"
Taƙarisa maganar tana bankawa Jawaheer harara,dan dama basa ga maciji da ita,haka lubnah ma,bombee kuwa basu taba haɗuwa ba face to face,shiyasa ta zabi Jaleelah a matsayin favorite ɗinta,yayinda iyakuma maleekah duk cikin amaren babu wacce tayi mata,tana jin ana zancen tafiyar ma bata fito ba,sai anjima tayi sashen Bombee acan zata yini.


Hannunsa ya saƙala ta bayanta zuwa cikinta,tana tsaye a jikin table na dining tana gogewa.
"Nizan tafi yawon cin amarci ta amarena"
"Na riƙeka dama,nace kada katafi?"
Sake kwantar da kansa yasakeyi a gadon bayanta tareda yin magana,wanda hakan yakasata ajiye duster taja gwauron numfashi.
"Mr.groom wannan salon kuma namenene,ko so kake na fola maka na hanaka tafiya,shiyasa kakeyin haka"
"Bahaka bane zanyi missing ɗinki ne"
"Hhhhhh missing shin kana tunanin yakamata kayi amfani da wannan kalmar,dan Allah kaje tafiyarka suna jiranka,inna gama aikin gidannan inada abinyi sosai"
"Wai kina nufin bazakiyi kewata ba,bazakiji babu daɗi ba idan natafi?"
"Saboda kai iska ce ko ruwa,da babu su babu rayuwa,babu ɗaya ƙanwar biyu,barina je ana ƙirana a waya,Allah ya bada sa'ar shaƙatawa"
Daga haka tacire jikinta daga nasa tayi ɗakinta,ta barshi a wajen yana kallon hanyar data bi,haka kawai ya tsinci kansa da jin rashin daɗin tafiyar da zayyi ya barta,jiyake inama tace zataje su tafi,yasan hakan bazai taba yiyuwa ba.


Kasancewar private jet ne yasa kawai tafiya ce babu wani tsaiko a ciki.
Dubai suka nufah,inada Jaleelah ta zaba,taganan zasu nufi singapore inda itakuma Jawaheer takeso.
Jaleelah ce ta kalli Jawaheer a cikin jirgin tareda yimata magana,ganin Jabeer ya shiga banɗaki.
"Uhm nikuwa kaman kece Cat lady bah?"
Zaro ido Jawaheer tayi tareda ƙwaruwa a abinda ta zuqa,waiwayawa tayi ganin babu kowa ya kusa kafin tace.
"How on earth kika sani?"
"Lahh ba wani abin damuwa bane,naga baki daɗe da buɗe acct ɗin bama"
"Shine nace taya kika san nice cat lady a ciki,bayan bamu taba haɗuwa dake ba bare muyi wannan maganar,saidai idan kema......."
"Ehh haka ne nima,Kinsanni a wajen saboda baki san nice bane,zan faɗamiki user ɗina saboda wani dalili.
Nice black slender a wajen,hannunta ta buɗe ta nunawa Jawaheer wani tatoo a hannunta na hagun.
Zaro idon da Jawaheer tayi a yanzu har yafi na ɗazu ma.
"Kina nufin kice dama kece wannan babbar......."
Bata gama maganar ba Jabeer yadawo,dan haka suka sanja topic ta hanyar magana akan wani abun taban.








_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤 39••40🖤










"Banjinki sosai Inayah Ki ɗaga murya kaɗan"
"Ai babu dama ne anty maryam,wani abu muhimmi nakeson faɗamiki yanzu,wanda na tabbatar yakamata ki sani"
"Menene ina jinki"
"Uhm ɗazu naji brr na'ima tana wani surkulle a ɗaki,magana suke da wata mata,bayan kuma batayi baƙuwa na,sannan maganar batayi kama da ta waya ba sam.
"""Karki damu yake Komai bai bar hannuna yana ƙarƙashin ikona,tun kafin ta kasance a cikin komar ki ni tashiga tawa tun bata faɗo duniya ba,ita ɗin kyauta ce a gareni,kuma gidan aljanuna,dolene na maidata sai abinda na sakata,kokuma na ɗaiɗaita rayuwarta.
Inta kusada ita,kusa mafi kusanci saidai batada masaniyar hakan,su kansu sauran na san inda suke ta sanadiyyarta,ina jiran lokacine wanda zan aiwatar da ƙudirina akansu.
Ƴar kima kada ki damu,duk da bazata san nice ba,amma zan kulada ita fiyeda yanda kike sani,kedai kicigaba da abinda na muka umarceki dashi""""
"To haka matar naji tace"
"Iya haka kikaji,okay ba matsala kinyi koƙari,amma kisake kulawa fah kada su gane,yawwa kin taba shiga ɗakinta?"
"Ehh ina shiga sosai kaimata shayi"
"Madubi nawa ne a ɗakin nata?"
"Eh biyune,ɗaya yanada dreesing mirror da kayan shafe shafe,ɗaya kuma a tsaye yake an rufeshi da wani baƙin ƙyalle"
"Ohk na fahimta,naji abinda nakeson ji,sai an anjima"
Tana ajiye wayar rest room tashiga inda allon plan ɗinta yake,zana inna lari tayi da Brr na'imah sai tayi link ɗinsu da Zilliyyah.
'Okay inna fahimta daidai zancen da take na nice da kuma ahalina,wato bayan barinsu gyembu sun bata mata shirinta,hakanne yasa ta biyosu nan.
Tace tana kusa dani,amma duk shu'umancinta bazata iya bacewa ba ai,kuma tace tana kusa ba wai tasaka a ganni ba.
Duk yadda akayi tana cikin gidanann kenan kuma tayi badda kama'
Har tazo ajiye marker dake hannunta sai ta tsayah,tsohuwar dake musu aiki a sashen ta tuna,lokacin data tunkareta taji nauyin dayake kanta yana komawa ƙeyarta,data juya kuma taji yana komawa goshinta,maganar datakeji a kanta kuma a lokacin ta tsaya ɗiff.
Kenan aljanun dasuke kanta tsoron tsohuwar suka,kuma dama bata yarda da ita ba sam.
Ayar tambaya tasaka a sunan tareda yin murmushin samun nasara.
"Idan kuwa kece to lallai kinkawo kanki ramin kura......hahahaha"


*** ***


Tun lokacin da Jawaheer tagane wacece Jaleela,shikenan suka ɗinke,babu zancen faɗa kuma,koyaushe tareda suke komai,sai dare yayi kowa ta tafi ɗakinta,wacce Jabeer ke wajenta ya shiga.
Tun zuwansu a ranar ya aiwatar da ibadar aure shida Jaleelah,duk da cewa yanda yake tunanin zaiji bahaka yaji ba,amma kuma yasan babu wata matsala,dama kowacce mace da kalar ta.
A bangaren Jawaheer kam washagari a buɗe yasameta,duk sai bayyi wani mamaki sosai ba,dan biri yayi kamada mutum.
Da safe kyauta yayi musu mai tsoka,yaso yabawa Jaleelah wanda yafi yawa,saidai kuma yana tsoro kada yayi ba daidai ba.
Dan haka yabasu iri ɗaya,saidai a wajen mu'amala kam yafi nunawa Jaleelah kulawa fiyeda Jawaheer,ga mamakinsa in suna tareda yake yiwa Jaleelah maganar soyayya bata damuwa sosai,yawanci idonta baya kansa yana kan Jaleelah,domin taga wane reaction zata bayar gameda maganar tasa,tana mayar masa martani kuwa zata ɗebi fushi tayi gaba fuuu.
In hakan yafaru haƙuri Jaleelah take bashi,kana daga bisani tabi bayan Jawaheer ɗin,akan zata bata hakuri,ko kuma wani lokacin suje tare.
Shi har yawon ma ya isheshi,ga bombee ko sau ɗari zai ƙira numberta bata ɗagawa,yayi ƙiran watan har ya gaji ya haƙura,ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya tafi ya barsu,wani bangare na zuciyarsa kuma yana son zama da Jaleelah a nan ɗin,maybe Jawaheer ce ta bata masa budget. Domin Allah yaga haƙuri yake na nuna mata kulawa,ba kaman yanda zuciyarsa take so.
Watansu guda a dubai suka nufo Singapore,a nan kam barsu yayi ya tafi wani uzurinsa,akan sai bayan sati biyu zai dawo,su suka cigaba da yawon buɗe idonsu tare.


*** ***
"Haba Mommy har yanzu baki ƙarisa bani ɗaya mahaɗin maganin ba,wani satin fah Jabeer zai dawo,nagama shirin yanda zanyi yakwana a wajena idan baki bani abin yanzu ba taya zan gama shirin to"
"Kaii Dear kinada ɗaga min hankali,baki ganin kullum busy nakene,ga Shari'ah sun sha min kai,ga shi wancan shashashan ɗan unnawaki,tunda suka dawo ƙasar jiya ya shiga sashensa banganshi ba..
Shi a dole matarsa tanada ciki,motsi kaɗan ya dubata motsi kaɗan ya dubata,ni ina tunanin anya ma kuwa ɗan cikinta nasane?"
"Meyasa kikace haka mommy,ko shima yanada irin matsalata bai sani ba kai?"
"Uhm da alama,amma bar wannan zancen ba yanzu ba zanyi maganinsu ne idan naga dama,baridai aikina ya kammala.
Yanzu mai kikayi shirin bayarwa kafin aikin yaci"
"Ohh sai an bada wani abu?"
"Ehh ƙwarai ma kuwa,mai zaki bayar a faɗama ta,kuma kada ki manta banda kuɗi fah,abinda kuɗi baya saya take karba"
"Uhm zan bada mahaifata tunda batada amfani"
"Bakiji nace miki mai amfani take karba ba?"
"Uhmm to nabada lafiya ta"
"Kutt bakida hankali ne wai,taya zakiyi ikon babu lafiyah?"
"Ahah ba iya haka ba,amma da sharaɗin idan bazasu karba ba har sai nayi wata ban haɗu da wanka nake mulka ba,in mutuwa kuma yayi babu zancen ɗaukar lafiyar,kinaga yayi?"
"Hmmm ina jiyewa dabbancinki,tunda kince haka shikenan,saiki kafa masa sharaɗi akan kada ya kuskura yayi wata guda baki ganshi ba"
"Ehh hakan yayi indai zan samu biyan buƙata"


*** ***


Tun safe take kulada shige da ficen Zaleeha a gidan.
Hasashenta kuwa ya fara tabbata,tabbas akwai abinda tsohuwar take kissimawa,ba Hajiyah Zeenah take yiwa aiki ba,aikin kanta takeyi kawai,tunda yanzu ai Jabeer baya nan,bai kamata tacigaba da saka ido ba.
Kokai itama Hajiyah Zeenah da hannunta aciki.
Ita kaɗai dai take saƙarta tana kuncewa,har lokacin dataga tafita daga side ɗinnasu ta tafi.
Kamar jira take kuwa da sauri tafito daga sashenta ta nufi ɗakin Zaleehan,dan dama shekaranjiya ta Copy key ɗinta data tafi banɗaki.
Buɗewa tayi tashiga ɗakin,tanajin cikin kanta ana bata umarni ta fita,amma tayi biris dasu tacigaba da bincikenta.
Su ƙoran maganine,kayin su macizai,hadda na jinjiri da gani,magunguna kam ba'a maganarsu su.
Idonta ne yakai kam madubin dake ɗakin,sak iri ɗaya dana ɗakin inna laari wanda tasani,saidai shi wannan maimakon adon yellow,da jini aka shafe gefe da gefensa,wato na ogah kenan.
Saida taƙare share tantamarta kafin ta fito daga ɗakin.


A filin harabar gidan ta zauna sunata waya da innayi,tanayi mata ƙorafin karatu da wuyah sosai.
"Kinga ni ba ƙorafin karatu na ƙira kiyimin ba,bayan ni da kuma hilyan akwai wacce ta taba zuwa gidannan?"
"Ehh...to banda almajirai dai,sai wata mata da ta taba zuwa wai a taimaka mata da ruwa,daga nan banga kowa yaxo ba,saidai bansani ba ko ina makaranta"
"To koma menene ki faɗawa sauran dukka su tabbatar baku sake barin wata baƙuwar fuska tashiga gidannan ba,kina jina koh?"
"Ehh naji addha maryam,uhm ki cewa maleekah lafiyah jiya naga ta dawo gida da wuri,bayan kuma tace sai yamma?"
"Cikinta ne ke ciwo,nan tazo ta kwantamin ai har yamman.
Kinji abinda na faɗamiki ku kula,idan nayi solving wani abuma dukka zaku dawo nan gabana,wajennan jikina bai bani akwai safe ba,kowanne lokaci komai na iya faruwa"
"Hakane kam amma addah ki dunga zaton alkhairi a kullum"
"Iyee wai kurace zatace da kare maye,don ruwa ya doki babban zakara koh? Duk ba uwarkice ta faro komai ba,yanzu gashi duk da ta haukace ban huta da warware abinda ta ƙulla ba"
"Kiyi haƙuri addah bombee dan Allah "
"In banyi haƙuri na kashe kaina zanyi na barku da ita ta ɗaiɗata ku?,
Sai anjima ki kulada kanki da kuma inna,sannan ki maida hankali kiyi karatu kinji?"
"Uhm naji"
"Tamm"
Tana nan zaune har zaleeha ta shigo gidan ta ƙullin leda a hannunta.
Ƙwallamata ƙira tayi da ƙarfi,da sauri kuwa ta amsa tataho.
"Gani Hajiyah"
Wata yatsina bombee tayi,aranta tana cewa ƴar wasan kwaikwayo. Tasan dole tayi taka tsantsan,komai tayishi a iya cikin ranta kawai.
"Uhm nace ba jeki sharemin Wajen training ɗina ta baya,kiyi sauri kuma kafin magriba tayi"
"Hajiyah naji kince bazan yi aiki a sashenki ba"
"Dama ina ni nace,to yanzu kuma na sanja magana,na gaji dayin ayyukan gidan,hutu nakesonyi,dan haka kice ki sharemin yanzu,ko kuma kibar aiki a sashennan"
Ga hasashenta kuwa da sauri ta nufi wajen sharar kafin ta koreta,da alama komai zatayi indai baza'a koreta ba.
Kaman yanda bombee ta faɗamata kuwa sai wajen magriba ta gama sharar,lokacin ta tashi a wajen tashiga ciki,bakin ƙofar shiga falonta taje ta ƙwanƙwasa mata.
Buɗewa tayi tareda cewa.
"Har kin gama sharar?"
"Eh nagama hajiya"
"Ohk to jirani ina zuwa yanzunnan"
Bata daɗe da shigaba tafito da kwanon abinci a hannunta.
"Gashinan idan zaki ci,nayi yamin yawa"
Taƙarisa maganar tana miƙawa Zaleeha kwanon,tantamar karba tayi da farko,saidai daga ganin yanayin yanda bombee take mata tasan batasan ita wacece ba,dan haka ta tsugunna har ƙasa ta karbi kwanon ta tafi.
Sai bayan tabar wajen bombee tayi murmushi tareda cewa,
"Hmmm zakici bantan ubanki dani kike zancen,inkin fini da rarrafe aradu nikuwa saina fiki da tafiya"
Wayarta ta ɗakko da sauri ta bugawa wani ƙira.
"Hello khamees maza kazo yanzunnan,domin da daddare nakeson ayi komai a gama zuwa safiya,na tabbatar zata ci abincin"
Tunda zaleeha taci abincinta da bombee ta bata,bayan ta gama dubashi babu wani magani a ciki,dan in akwai dole zata gani ne.
Tunda taci abincin ta kwanta a wajen sai bacci,bata tashi sanin mai yake damunta ba saida ta bude ido ta ganta a asibiti.
Bombee ce a tsaye a window tana ta zuba tsuka da mita.
"Haba tsiyarka da tsoho kenan,daga sun kwanta kuma ba kanta"
Tarin da zaleeha tayine yasa ta juyo ta kalleta.
"Hajiya mai ya faru"
"Ohh shine tambayarki,jiya naje yimiki magana akan jagwalgwalon sharar dakikayi min na ganki a kwance numfashinki yana sama da ƙasa.
Likita yace kinsamu heart failure,wataƙila kinsaka abu a ranki ne.
Yanzu dai gashinan ya cire miki jinin daya taru a gefen ƙirjinki,ki duba zaki gani,ni zan tafi idan kin gama warkewa ki faɗawa likitan zan turo mota a ɗaukeki"
Tana gama maganar ta zari jakarta tayi waje,sai bayan ta fita ta tuncire da dariyah.
"Zilliyyah kinshigo hannuna finally,you are my ride to successed"
Ita kuwa zaleeha jugum tayi tana tunanin maganar da bombee ta faɗamata.
'anya kuwa ba wani abu ta saka mata a abinci ba,to kuma ya akayi bataji komai ba,kuma in abu tasaka mata ta tabbatar na mutuwa zata saka mata,wanda kuma aljanunta bazasu bari taci ba,inaga to ciwonne da ita,gaskiya batasan ita wacece ba kam tunda har tayi mata magani'
Tana cikin wasiwasinne likitan ya shigo da magani a hannunsa da kuma plate na abinci.
"Iyah sannu ya jiki,ki dunga kulada lafiyarki sosai,banda takawoki da wuri da tuni abin yayi tsanani,yanzu dai zamu riƙeki nanda sati guda kafin ki tafi"
"Sati guda kuma likita,ahah bazan iya zama ba,jikina bayason wajennan,kabani maganin na tafi,zanyi amfani dashi yanda ya kamata"
Da farko yaƙi amincewa,amma ganin yanda ta damu yasa ya bata maganin tareda kafa mata sharaɗu na musamman.


Bombee kuwa a hanya tazo shiga motarta suka ci karo da wata likita,ɗagowa tayi zata fara magana,saikuma ta zare ido tareda cewa.
"Kuttt Rahama.....serious kece,yana ganki da farin kaya bayan na khaki?"
"Uhmm labari da yawa Captain maryam,tun bayan da aka miki wannan shunen komai ya rikice,Gen Muhammad yau da lafiya gobe babu,ƙarshe ma ya ajiye aikin,nima ganin haka yasa na tafi karatun likitar mata,yanzu haka nice babbar likita mai duba mata a asibitinnan,amma muje office mana ki sha ruwa Captain

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login