Showing 99001 words to 102000 words out of 134612 words

Chapter 34 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8674

dai miƙomin maganin zazzabin nasha,ƙarfina ya zuqe a maganar danayi ɗinnan"
Ajiyar zuciya ta sauƙe,bata sake cewa komai ba ta miƙomasa maganin yasha kaman yanda ya buƙata.
Saida taga yasha kana ta tashi zata bar ɗakin..kamo hannunta yayi ya riƙe gam,ja tayi amma ya riƙe sosai da guntun ƙarfin dayake jikinsa.
"Dan Allah kada ki tafi ki zauna"
"Uhm saboda kana buƙata ta koh,sai nan da sati biyu bazan sake ganinka ba ballanta wani abun ya haɗamu"
"Uhm nan da sati biyu kikace ai ,kafinnan ki taimakamin wajen zama a tareda ni"
"Ina matarka meyasa baka ƙirata ba saini"
"Meyasa kike son maimaita maganar da kin riga kinsanta uhm?"
"To yanzu dai bazan zauna dakai ba,saboda nabar ɗana a ɗaki shika ɗai"
"Idan bazaki zaunaba zan biki to mu tafi sashenki,i hope hidima bazai miki yawa idan mu biyune koh"
Jimm tayi batace ahah ba bata kuma ce eh ba,tarasama mai zatace da taji maganar da yayi.
Hannunta yasake yana ƙoƙarin tashi,batada zabi ta taimaka masa suka nufi sashennata badan tasoba.
A gado ɗayah suka kwanta bayab sun saka Haidar a tsakiyarsu.
Abinda bata tabayi ba tunani ba kenan daga wajen mijinnata na wata shida.
Bayan sallahr asuba tunda koma bacci bashi ya tashi ba saida kukan haidar ya jiyarci kunnesa,buɗe ido yayi suka haɗa ido da Bombee,wacce take ta kiciniyar sakawa yaron diafer,da alama kuma yunwa yake ji ba son saka kayan ba.
Kallonsu yake cikeda sha'awar su,abinda yake mafarkin samu kenan,amma kuma bai samu ba a rayuwarsa,shine ganin matarsa suna zaune lafiya da kuma ɗansa.
Yaron kwata kwata baya kama da itah,illah abu ɗaya dasuka hada dashi shine idonsa kawai.
Kallon fuskar yaron yake ko zai sake ganin wani abu da suka haɗa da Bombee,saidai sabanin ganin hakan saima wani abu daya gani a fuskar yaron wanda yasaka ƙirjinsa bugawa.
Saurin kawar da kai yayi yana jijjiga kai. Inaa rashin samun yaro nasa na kansa,baikamata yafara ganin dan da baisan asalinsa ba a matsayin nasa.
Yana tsoron kar zama da yaron waje daya yasa soyayyar yaron tayi tasiri a ransa.
Yasan ko tsafi yake da baƙar zaba Hajiya zeenah bazata bari yahaɗa alaƙa da yaron ba.
"Tunda ka tashi na haɗa maka ruwanka,ka gama ina jiranka a dining"
"Bazaki tambayeni ya jiki ba"
"Jikinka na ganshi ba buƙatar tambayarsa,Fatan Shine Allah ya sawwaƙe kawai"
Daga haka ta suri yaronta sukayi waje,saida zata fitane ma yakula da kayan dayake jikinta,daga ita sai bom short da t-shirt.
"Ohh Allah ya bani ikon tafiyar da wannan bauɗaɗɗiyar baiwa taka,ba sonta nake ba,amma kuma zama tareda ita yana sakani cikin nutsuwar zuciya,na ganta tana ta hidimarta da yaronta yana sakani jin inama suɗin iyalina ne danake da iko akan su.
Narasa wanne irin yanayine haka nake shiga gameda su"
Bayan ya fito daga wanka ya kalli kayansa nazaman gida,da alama tashigo dakin kenan yana wanka.
Madara take bawa haidar a feeder sa Lokacin daya fito.
"Wannan yaron ya kai cin abincine,bazaki bashi mama ba"
"Na yayeshi wancan satin,madarar formular nake bashi,dama dan jikinsa yaƙi karbar madarane yasa na bashi nono"
Zaro ido yayi jin tsaurinta gameda yaronnata.
"Haba ke kuwa,shiyasa yake kuka kenan,bai kamata ya wannan yaron ki cireshi daga abincinsa ba,abune da kowanne yaro yakeson samu a wajen mahaifiyar sa.........."
"Nasani Mr CEO sannan koda da lokaci kadan bantaba yin abu danna cutar dashi ba,ina sonsa kaman yanda uwa take son danta,bukatar hakan ce ta taso.
Kuma a yanzu jikinsa ya karbi madarar fiyeda da"
"Uhm"
Shine kawai abinda Jabeer ya faɗa,dan bashida tacewa a ciki,tunda ɗan ta ne kuma ikonta ne.
"Oh barina zo nabawa angon nan da lokaci kaɗan abinci,kar azo biki a ganka a rame"
Gogewa haidar bakinsa tayi tareda bashi abin wasa ta taho inda abincin yake.
Sai da ta gama zubawa kafin ya samu waje ya zauna yafara zubawa cikinsa.
Maganin yasake sha bayan abincin,kafin ya miƙe akan doguwar kujera..
"Naga ka samu sauƙi fiyeda jiyah,ka ci abinci kasha magani,toh bazaka tafi sashenka ba koka fita"
"Uhmm ni bazan tafi ba saina gama warkewa,saidai in korata kike toh"
"Menene amfanin ka taremin a sashe to bayan da naka,nina rasa mai yasa nake ta ɗawainiya dakai ba matar ka ba"
"Kema ai matata ce ina,ko kin sauke auren daga kanki?"
"Hhhhh habadai koda ni matarka ce amma ta wata hanyane daban,ka daina sakani cikin wannan matsayin"
Duk korafin da tayi Jabeer bai bar sashannata ba,dan inda sabo yafara sabawa da halayyarta. Sai wajen yamma kafin ya tafi,bayan ya yi wanka yaci abincin rana,wai suna yana jinya,amma ƙara ƙiba ma yayi fiyeda yanda tazo ta sameshi.
Yana fita itama tafara shiryawa saboda zuwan meeting din da zasuyi itada su Hilyaan,jiya yakamata suyi amma ta ɗaga saboda Jabeer.
"Zancen Dear gaskiya ne data faɗa maka,na fasa ɗora mahafinku akan wanann aikin,domin bazayyi min yanda nake so ba.
Dan haka ka gaggauta dawowa ƙasarnan kafin ba sanja shawara,kana jina koh"
"Ehh zan dawo,waye zaiqi zama ceo na company babba haka,gaskiya you are the best mommy"
"Wanann koɗaɗdiyar matar taka inzata zauna dakai a ƙasarka ta biyoka,in kuma bazata zauna dakai ba ka raba tsakaninku ka dawo gida"
"Kai mommy she have preganant,and you know i love her so much"
"Kai kuma ka sani"
Ta kashe wayar tana tsuka.
"Banda taurin kai irinna yaran yanzu,mai zayyi da wata baturiya oho,hakan ma ba musulma ba,Soon zanyi maka aure da wacce nake so,bazaiyiyu yayanta su gaji abinda nakeson ɗoraka akai ba kam"
"Hajiya akawomiki ruwane ki sha"
"Eh kawomin,da saikin tambaya,zamanki gidannan wata biyu yaci kinsan mai nakeso da wadda banaso ai"x
"Kiyi haƙuri Hajiya kai nne sai a hankali na tsufah,yanzu zaki faɗi magana an jima na manta.
Uhm dama inaso na tambayeki zanje ganin jikokina a wajen mamarsu da yamma Hajiya inba damuwa"
"Rose"
"Yeah Hajiya anything else?"
"Ki bawa Yalwa dubu biyar kudin mota zataje dubo jikokinta,
Ke kuma kidawo da wuri,karkiyi irin wancan zuwan ,mtsww wai nima narasa wanda zan dau aikin gogegoge sai tsohuwa,koda yake ba laifi kin iya aiki"
Taba gama faɗin hakan tashige ɗaki tabar Secatariyarta da Baba yalwan.
Naira dubu uku tabawa yalwan maimakon yanda Hajiya tace,sauran ta soke a nata aljihun.
Karba tayi kaman bata gane mai brr Na'imah tace bataba,godiya tayiwa Rose har ƙasa,inda itakuma take mata kallon raini .
Ɗakin masu aikin tashiga ta shirya kafin ta fito,tafiya take zugub zugub har ta iso wata kwana.
Wata dariyar yan duniya tayi tana kiƙƙifta ido wanda basuyi kamada na tsofi ba,dukkuwa da yanda tayi iya ƙoƙarinta wajen yin kwalliyar dazata tauye mata fuska,ka iya duniyanci mutum bai isa ganota ba.
Ta gefen ido take kallon wanda aka saka yafi bayanta,saida ta kula mota tatareshi tayi wuff ta faɗa wani butique.
Banɗaki ta shiga ta wanke fuskarta tareda saka kayanta wanda suke cikin buhun.
Powder da shafa da kuma jan baki,sai bakin glass tada saka.
Fitowa tayi tana taku irin na ƙwararru,a hanya suka bugi juna da wanda aka saka yabi bayanta,sai waige waige take yana neman tsohuwar dayake bibiya.
"Uhm guys baka ganine kana buge lady?"
"Am sorry madam bangani bane"
"Ohk ya wuce"
Dariyah ta sheqe da ita bayan ta tari taxi ta hau.


A bakin ƙofar gidan tayi parking motarta,ta daɗe kafin ta fito ta nufi gidan.
Innayi ce ta amsa mata sallamarta wacce take ta karatu,saboda makarantar jami'ar dazata shiga,wacce Bombee tace zata sakata.
"Innayi ykk ya karatu,ya kuma inna?"
"Lafiya kalau addah Bombee,su Hilyaan da inayah suna ciki,amma Maleekah bata zo ba"
"Meyasa bata zo ba,mun fa haɗu da ita a gida zata taho"
"Uhm naji Hilyaan tana cewa wai zasu tahone da khamees kaman"
"Ohh this girl,tanada rigima sosai,bana hanata biyema Khamees bane,su barni naji da wanda yake kaina ma na hidima"
Dariya innayi tayi,daga nan batace komai ba.
Ɗakin inna tashiga ta gaisheta,tana zaune a kan darduma tana jan carbi.
"Inna barka da yamma ykk,nayi magana da malamin dana ce zan kaiki wajensa,watakila sai a dace a wajensa"
Kama hannun Bombee tayi tareda nuna alamar suje su biyu.
"Ahah inna ke zaki fara zuwa,naki zai iya yin sauki yanzu,amma nawa dole sai nayi bincike gameda wacce tayi aikin,sannan kuma naki yafi wahalarwa fiyeda nawa,barina na tafi inna"
"Kitaaaafi anan wajen,bamason kizo wajennan Ta haramta mana kaiki wajen mahaifiyar ki kifitaaaaa"
Toshe kunnuwanta tayi tana cize baki,saboda yanda kan kemata kamar ana doka mata guduma.
Sakin hannunta tayi ta wuri tabar ɗakin,bayan tasake waigawa ta kalleta,tana son kasancewa da mahaifiyar tata,itama kuma tasan tana son ta ganta a kusada ita.
Sai bayan sun zauna sun kusa minti goma kafin Maleekah suka shigo itada khamees,dukkansu idonsu a ƙasa yake,Lokacin dasuka ga yanda Bombee ke aikamusu kallon tuhuma.
"Mal......."
Da sauri tazo inda Bombee take ta durƙusa.
"Haba antynah karkice haka mana,wlh ina sonshi kuma kinsan bashida wani mungun hali,ko kowa yaki ke mai auramin shine ai"
"Saboda a matsayina nawa"
"Na matar babban yaya mana,allah nasan kinacewa yah Jabeer yabarni tareda shi ta zauna,shikuwa inya faɗawa abba magana ta kare"
"A ganinki ba,Maleekah har yanzu banida matsayin dazan shiga sha'anin danginku,ko kin manta matsayina ne a gidan uhm?
Har raina soyayyarku da khamees ban ƙita ba,amma babu abinda na tsana irin jawo magana,shiyasa nake taka muku birki kafin abin ya fi ƙarfina.
Yanzu dai ba wannan ba,jiya da daddare kin ƙirani kan cewar Hajiyah zeenah bata yarda da abinda kike faɗa ba mai yasa?"
"Uhm mijinkine sila ba laifina ba,kina bashi kulawa da yawa har ya sanja yaƙara kwarjini da fara'ah,shiyasa Mommah tafara zargin akwai abinda yake faruwa,musamman dayace wai a gidansa yanzu yake cin abinci.tasan kuma Lubnah bata girki,shikuma bayason cin na ƴan aiki,shiyasa tafara zargin akwai abinda yake faruwa.
Naji kuma waya da maman Jawaheer kan cewa an samu ƴar aikin dazatayi aiki a sashen,ta yanda zata dunga kawo musu abinda yake faruwa"
Aikinki yayi kyau,Hilyaan fah mai yake gudana a barrak.
"Nothing important,naji dai Gen nacewa shirin daya daɗe yana jiran zuwansa ya rushe,da alama Jabeer bazai halarci meeting ɗin ba,dan haka sun ɗaga shi sai next month"
Dariyah Bombee tayi tareda cewa.
"Uhm kawai ƴar ƙaramar rashin lafiya na haɗa yayi da daddare,shine kawai"
Zaro ido sukayi suna kallonta,musamman ma Maleekah.
"Oh kawai na saka masa grape(inibi)a cikin jus,kuma dama yanada allergy dashi,sai yasakashi night fever da kuma small rash.
Amma naji da komai he is normal now"
"Amma anty Maryam meyasa,muma munsan bayason grape sosai"
"Amma nibai faɗamin bayaso ba,da alama bayaso nasani,shiyasa nayi amfani da hakan na ceceshi.
Mai kike tunanin zai faru inya halarci meeting ɗin,zai rasa kunerarsa a ranar ne,shine abin gen abdu manga ya shirya,tunda basusan muna da takardun Alhaji Abdullahi ba ballantana su dakata.
Inaya fah mai ya faru?"
Tun ɗazu take zaune bata ce komai ba,saida aka zo kanta kafin tayi gyaran murya dan lumshe ido.
"Eh to maganar gaskiya ba gen abdu manga ne zai hau kujerar ba yanda kuke tunani,dan haka aikin Hilyaan ya ƙare na bibiyar Sa a barrack.."
"Mai kike nufi da hakan Inayah?"
"Barr Na'imah itake kalmasa koma daga gida,ganin mijinta bazai mata yanda take so ba,yasa ta yanke shawarar ɗora babban ɗanta waro Ammar.
Wanda ya tare a ƙasar England da matarsa juliet,yanzu haka tana ciki,kuma suna shirin dawowa nigeria saboda yazo yazama CEO yanda ta tsara"
Abinda Inayah tafaɗa gabaɗaya yabasu mamaki,inda basu saka Inayah tajiyo ba da bazasu san barr Na'imah ce ke komai ba.
"Okay Hakane abin,dama nazargi haka,amma ban taba tunanin tsanar da tayiwa ɗannata kaɗan bace sai yau,wato yanzu ta nemeshi tunda zai mat amfani.
Zanga kuwa ta yanda zai zama CEO ɗin inanan.
Mungama meeting daga nan,sabuwar haɗuwa kuma sai nan da bayan zuwan Amarenmu.
Saboda nasan dukkansu zasuyi ƙasa da makamansu saboda zuwan bikin,muma mu huta haka."


"Wayyo jikina,wayyo bayana ku taimaka min yana ƙaiƙayi,wayyo zan mutu zan mutu nace"
Duk ihun da Inna laari take babu wanda ya jita,tana ɗakinta a ɗaure da sarƙoƙi.
Gaba ɗaya halittun jikinta sun sanja kamanni,babu wanda zai ganta ya ganeta a yanda take.
Wasu irin ƙuraje sun yayyame jikinta,da fuskarta ta jirkice.
Kurajen sunyi jawur saboda yanda take durja jikinta a duk inda ta samu.
"Nace kuzo ku taimakeni,Zilliyah ta cuceni bayan nayi ta bauta mata shine ta gudu ta barni.
Itace fah nabawa ɗan Danejo jaririnnan taba wa aljanunta suka cinye,nasa ta sakawa Bombee shaɗanu,wanda suke zukata da yi rashin mutunci ta daina tausayin iyayenta da daina sonsu,sannan kuma ta daina tsoron kowa a duniyah.
Nice nan laari nayi komai da komai.
Nina makanta Danejo na kumantata,nasa likita yace ciwone yayi mata haka duk fah nice nayi komai da komai.
Tunda na faɗamuku ku dawomin da ƴata Innayi nah innayi nah.
Nasan idan na kaiwa zilliyah ita ta aurawa ɗan ta,to zata warkar dani nakoma yanda nake,har kashemin Danejo zatayi itada zuri'arta,sanadin ta duk na shiga wannan halin nasan"
Mlm Ahmadu wanda yake bakin windownta yana jin abinda ta faɗa,share hawayen idonsa yayi tareda wurga mata Sinƙin biredin dayake hannunsa.
Tana ganinsa kuwa takaimasa wawura kaman dabba,haka da ledar ta dunga ci saida ta cinyeshi tasss .
Barin wajen yayi dan bazai iya jure ganinta haka ba sam.
Inhar abinda ta faɗa gaskiya ne,to kuwa bashida idon dazai kalli iyalannasa ba wanda suka shiga duniya.


Ke duniya.......!!!!






_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤35••36🖤








Bayan meeting ɗin da sukayi ba ita ta dawo gida ba sai wajen magriba.


Tana zuwa kayan jikinta tarage,nan da nan ta hau haɗa abinci.


'Wani Lokacin tana mamakin kanta yanda ta damu da rayuwar Jabeer,abinda bata taba yiwa wani ba kenan,ko kai saboda aljanun kanta basa kulawa da tsakaninta da shine kai,shiyasa take jin bond din tsakaninsu yana ƙara tasiri a jikinta.


Tana cikin zurfin tunanin taji ƙarar rufe ƙofah.


"Uhmm ɗazu nazo bakya nan,meyasa in zaki fina bakya sanar dani inda zaki uhm?


Ko so kike kema ki zama iri ɗaya Lubnah akan haka"


"Ba maraba akan hakn,amma kuma akwai banbanci,inda da buƙatar tambayar ma to Hajiya zeenah zan tambaya bakai ba"


"Meyasa ita take aurenki?"


"Wani abu mai kama da hakan dai"


Ganin yanda take amsa masa maganar yasa ya rabu da ita ya watso ruwa ya tafi masallaci.


Lokacin daya dawo ta kammala abinci ta saka a dining,zama yayi ta zuba masa yaci ya ƙoshi kafin ya sake ficewa.


Koda babu biyayya irin yanda yake son macen dazayyi rayuwa da ita ta kasance,amma kuma badai kulawa da cikinsa ba kam,da kuma kayansa da ɗakinsa.


Dan har ya zauna yaci abincin tana ta danne danne a system bata cemasa ƙala ba,yakula akwai abinda yake ranta,dan haka ya fita yabata waje..


Ƙarfe goma ya dawo gidan ya shiga ɗakinta.


Tana kwance daga ita sai wata riga iya gwiwa,wacce ta ɗage saboda kwanciyah,haidar kuma yana cikin gadonsa na yara a gaban gadonnata.


Tunda ya ɗora idanunwansa akan cinyoyinta ya gagara ɗaukewa,abinda ya taru masa tsawon lokaci ne yafara koƙarin taso masa.


A hankali yafara takawa har zuwa inda take kwancen,a bakin gadon ya zauna tareda kaiwa hannunsa kan cinyarta..


Duk da yanda ƙwaƙwalwarsa keson hanashi,amma kuma zuciyarsa tana muradin hakan,kuma tafi da hannayensa.


Cikin sanyi yake shafa duk inda rigar ta bayyana,vai ankaraba yaji caraf Bombee ta tashi tareda riƙe hannunsa,hakan da tayi ne yasa ya faɗa jikinta suka koma kan gadon..


Kallon idonsa take shima yana kallon nata,gashi duk ya bada ƙarfinsa akan ta.


Tana ƙoƙarin tureshi daga kanta shikuma yasamu damar haɗe harshensu waje guda.


Yadaɗe yana sarrafa harshennata batayi yinƙurin hanashi ba,saida taji yana shirin wuce gona da irine ta hanyar son rabata da rigarta yasata ta zame jikinta.


Numfashi yake sauƙarwa mai ƙarfin gaske yana ƙoƙarin saita kansa.


"Please.....mmmmaryam help me please"


Jijjiga kai tafarayi tareda yin magana cikin karyayyiyar murya,wacce take nuna tsantsar tausayinsa.


"Kayi hakuri Jabeer amma bazan iya ba sam,hakan zai karyamin plan dayawa idan nayi"


"Saboda kin tsaneni shiyasa bazaki bani kanki ba,ina buƙatar taimakonki a yanzu maryam a matsayina na mijinki,bakya ganin lokacin da muka ɗauka bai......."


"Badan na tsaneka bane Jabeer ko kuma dan bana tausayinka,inda inada ikon baka wannan taimakon zan baka kaman yanda na yi maka sauran abubuwa.


Bazan iya baka kaina ba alhali bansan matsayar aurena ba a gareka"


"Kamanya,kina nufin zan sakeki idan na kwanta dake,ko kuma na juyamiki baya,bahaka nake ba maryam"


"Nasan ba haka kake ba,hasalima ba wannan dalilinne suka sakani hanaka kaina ba.


Jabeer aurena dakai yarjejeniya ne na tsawon wata shida wanda mukayi da mahaifiyar ka,banda na maidashi na shekara guda da yanzu saurana wata guda na bar gidannan,yanzu haka ma tana kan bakarta dana gama mata aikinta kowanne lokaci zan bar gidannan..


Dan haka banason ka saka ranka akan macen da koyaushe zata iya tafiya,tunda matarka ta ƙaurace maka,kayi haƙurin sati biyu mata biyu russ za'a baka.


Amma ni tamkar mafarki ce,duk yanda zaka tsaya a ciki dole zaka buƙaci farkawa,dan haka ina taimakonka ne ka farka kafin lokaci ya kure maka"


"Hmmm duk naji bayaninki,nasan bazai wuce saboda kina da zafin zuciya zakiiya korar Lubnah,shiyasa ta auroki,wannan dalilinne kenan kullum take gargaɗina dana nisanceki badan zaki cutar dani ba saidan itake buƙatar hakan.


Nikuma zan nuna miki cewar dasannu zaki zama mallakina Maryam,duk da bansan mai nakeji a kanki ba,amma kuma zuciyata tana bani bazan jure rashinki a cikin gidana ba"


"Wannan duk maganar zuciyarka ce,amma a yau idan Hajiya zeenah taga dama zata iya raba aure mu,abu ɗayane zai hanata yi shine tasan bazan yadda ba,saboda contarct ɗin mu bai ƙareba"


"Shikenan zanyi ƙoƙarin yin nesa dake har saina jaddada matsayin aurena dake Maryam,abu ɗaya nake so koyimin,shine ki yi ƙoƙarin kar mommah ta soke contract ɗin dake tsakaninku"


Ɗaga masa kai Bombee tayi alamar ta yarda,daga nan yadafa yafita daga ɗakin.


Da kallon tausayi Bombee tabishi kafin ta gyara kwanciyarta badan don bacci zaizo ba.


"Kabani lokaci Jabeer kafin nayi tunanin zama dakai ko akasin haka,amma ita kanta mahaifiyar ka saidai kayi haƙuri,amma in shirina yazo kanta bazan ragamata ba sam"










"Mommy kina ganin zan haska a bikinnan kuwa yanda ya kamata?"


Jawaheer tafada tana dudduba uban lallen da ake zana mata,duk wanda yaganta daƙyar zai ganeta,yanda tasha uban gyara da kuma kwalliyah..


Yaune za'ayi bridal shower,duk da cewar uban gayyar yace babu wani event da zayyi,su dama gidan su Jaleelah mahaifinta bayason wasu bidi'o'i a biki.


"Ƙwarai ma kuwa dear,kinyi kyau fiyeda yanda kike tunani,ina mai tabbatar miki idan ya ganki sai ya rasa tunanin sa"


Murmushin jin daɗi tayi jin abinda mahaifiyar tata ta faɗa,gobene ɗaurin aure,bayan an ɗaura zasu je gidan su na kwana biyu,daga nan su wuce honeymoon na Wata guda,kowaccensu zata samu sati biyu,zayyi sati biyu da Jaleelah sannan yayi sati biyu ma da Jawaheer a ƙasashe daban daban.


A bangaren Jaleelah ma ado na musamman danginnata sukeyimata,na gargajiya mai ratsa jiki,duk wanda ya ganta saiya sake,yanda fatarta tayi sharr da ita tamkar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login