Showing 60001 words to 63000 words out of 134612 words

Chapter 21 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8665

ki koma motarki ki zauna"
Bombee tana kaiwa nan ta bayaninta ta maida glass ɗin motarta ta rufe.
Wata jijjiga Lubnah tayi,tama rasa mai yake mata daɗi,wai wannan yarinyar ce take mata magana haka,tukunna ma wajen wa tazo a cikin estate ɗin,yanayinta ne yasa tayi tunanin wataƙila baƙuwar Lylah ce,sai kuma wata zuciyar tace ta ƙira securtyn gidan.
Allah sarki bawan Allah,chiep securityn yana ɗagawa lubna tafara balbaleshi da masifah,ta inda take shiga bata nan take fitaba.
"Uban me kukeyi,menene ma aikinku a gidannan,maza kazo da kanka ka gani,wata banza ta hanani shigowa ciki,da saka motarta a bakin ƙofa,kuzo kuyimin waje da ita"
"Ranki ya daɗe kiyi haƙuri bari muduba CCTV camera,inaga kuma wajen wani tazo a cikin gidan,kada muyi mata magana yazama matsala"
"Matsala... Ina ruwana da wajen wa taxo tunda ta nuna min ta isa dan tasamu shiga wajennan sai tasan matsayinta yanzunnan,ku zaba shin fitar da ita daga baƙin ƙofar nan ko kuma Aikinku?"
Ai tun kafin Lubnah tasake cewa wani abun yayi saurin cewa.
"Aikina na ɗauka Hajiya,gani nan zuwa dakaina yanzunnan basai anjima ba"
Kashe wayar tayi tana jiran isowar tasu kaman yanda suka faɗa.
Yaseerah ce ta fito itama daga motar tazo inda lubna ke tsaye tana jijjiga kaman an jona mata wutar lantarki.
"Ƙawass mai yafarune,waye a cikin motar ko baci tayi?"
Duk maganar datake Lubnah bata kulata ba,har sannan tana sama,ƙarar fitowar motar securityn ta jiyo,saidai suma bayadda zasuyi su fito,dan Bombee ta tare hanyar fitowar daga waje.
Sagern Hudu ne ya fito daga motar,wanda shine shugaban security na estate ɗin gaba dayah,wajen motar Bombee ya nufah tareda ƙwanƙwasa mata ƙofah.
Zugewa tayi tareda haɗe fuska tace,
"Wai menene kuka dameni,idan kukayi haƙuri ma minti talatin na cika zan matsar da motata,basai kun takurawa rayuwata ba"
Kallon mamaki ya bita dashi tareda cewa.
"Kee wacece ke,shin tukunna ma mai kikazoyi gidanann,danni ban taba ganin mai kamarki ba a wajennan"
"Kai kai wai duk gidannan haka kuke ne,kowa inzai buɗi baki wacece ke,dole saini watace zanyi haka,kenan ban isa ɗaukar mataki ba idan akayimin wani abun?"
Tsawa Lubnah ta dakawa sagern hudu daga inda take tsaye,
"Lallabata ma kakeyi,yanzunnan kuyi waje da itah,ko tsoronta kukeji kai"
Sagern hudu yanajin maganar Lubnah ya ƙara ƙaimi tareda ficcina ƙananun idanunsu.
"Kinga madam koma me kike takama dashi ki fito daga motar nan yanzunnan,a matsar da motar"
"A kuda kuke so na matsar da mota meyasa kuma zan fito?"
"Ahhh wannan kuma madam daga baya kenan,dole zaki fito ki faɗamana menene dalilinki na zuwa nan wajen"
Shuru Bombee tayi bata bashi amsa ba,daidai lokacin da ta ƙayyade suna cika taga hannun sagern hudu yana shirin cakumo kirjinta,cikin zafin hannu ta riƙe a hannunsa tareda yimasa kallo mai ɗauke da alamar tambaya.
Idonsa tagani yana kallon kan ƙirjinta,tashi daya ta gane ba iyah niyyar fitowa yake da ita daga motar ba,harda wani mungun nufinnasa ma.
Yatsun hannunsa guda biyu na ƙarshe ta rike ta malƙwasa,nan da nan yabada ƙarar ƙass ta ƙaryasu.
Ƙarar azaba ya saka tareda fizge hannunsa yaja gefe yana kallonta cikeda mamakin karfin dayaji ta saka masa.
Key tayiwa motar ta bata diri,hanyar get ɗin ta nufah inda sauran securityn suke tsaye,nufarsu tayi da niyyar bi takansu ta shiga gidan.
Da farko basuyi tunanin zata cigaba da tafiya ba duk da sun tsayah....amma ganin tsakaninsu baifi taki ɗaya ba,kuma bata da niyyar tsayawa yasaka su bajewa da gudu,ɗaya kam har yatsansa t taka na ƙafah.
Tsalle yafara ya ihu tareda bin motar tata da kallo,wanda har ta bace a cikin gidan.
Saida ta ƙule tukunna sagern hudu ya juyar da kallonsa ga Lubnah,wacce itama tatsayah tana kallon abinda Bombee tayi.
Hannunsa yasake ɗunlewa tareda cewa.
"Hajiya kiyi haƙuri bari mushiga cikin muga wajen wa tazo,karki damu yanzu zamu koreta"
Bai tsaya jin abinda zatace ba yashiga motarsu suka shiga cikim gidan.
Itama Lubnah ganin cizon yatsa bazai kaita ya sakata shiga tata motar itada yaseerah suka bi bayansu.
A bangaren Bombee kuwa hankali kwance take tafiyah akan titin dake cikin estate din,har ta isa ga bakin part ɗin su Hajiya zeenah,dan shine a farko daga an shigo da kuma na su Lylah daga ciki kaɗan.
Parking motarta tayi a wajen da taga wasu motoci,wayarta tafitar tareda dannna sunan Hilyaan.
Ringing biyu da daga tareda yimata sallama daga ɗaya bangaren.
"Kinga babu bata lokaci sonake na kwantar da yaronnan,ya gaji da kwanciyar mota ga bayanin daɗi,ki fito ki nunamin part ɗin dazan zauna,ko kimin kwantance idan wani abu kike,zan wuce daga nan"
"Lahh anty maryam harkin shigo wai,kina ina kenan a cikin gidan?"
"Uhmm ina bakin wani part wanda shine na farko idan aka shigo ciki"
"Ohh part ɗin Hajiya zeenah kenan,muna ciki ai barina sanar mata da isowarki,mijinnaki ma yana wajenta yanzu ya shigo gaishe da ita"
"Kinga ni Hilyaan bana son wannan maganganun wanda naga kin koya tun zuwanki wajennan,inma wani abun suka baki kika sauya ni bai dameni ba,kawai ki fito ki nunamin masauƙina inason na huta,badan hotel ɗin dana sauka ana event a wajen ba maizai fitar dani da safennan kamar na ciwa wani bashi?"
"Sorry sorry Ogah ganinan fitowa yanzu nan karki damu"
Bayan kashe wayar Bombee a ƙalla tayi tsuka sunfi uku,ƙarar motoci taji sun faka a kusada ita,sa alama mutanen ta ne na bakin get suka iso.
Tana kallonsu dukkansu suka fito daga motar,shikam sagern hudu har sharce yake,saboda azabar data haushi na gurɗiyar yatsunsa guda biyu.
Fitowa itama tayi daga cikin motar tana kallon Lubnah wacce take tsaye tana zabga mata harara kaman zata cinyeta da ido.
"Ohh wato ke baƙuwar matar nan ce,no wonder kikejin haushina duk da bansanki ba mana"
Lubnah tafaɗa tareda yin murmushin gefen baki .
"Amma kaman banice dajin haushinki ba,ina fah kece kika dau da zafi daga farko,kuma har yanzu ma kinanan dajin haushinnawa,shin bakya ganin kallon da idanuwanki suke yiminne madam luban,ko aikamin kallon suke batareda izininki ba kai........ohhh kuma akan kawai na hanaki shigowa ciki sai lokacin dana shata sun cika,abin burgewar kuma saida suka cika kika shigo ɗin,common ƙaramar dokata kin kasa karyawa inaga babba kuma.......chchchchchc am feel sorry for you"
Bombee tafaɗa cikeda sigar zolayah,harda wani cuna baki kaman na kifi,hakan datayi ne lokacin ɗaya mutum zai dauka innocent ce.
"Sannunki da isowa"
Hilyaan tafaɗa fuskarta ɗauke da fara'a lokacin da suka iso wajen da take itada khamees.
Daga kai Bombee tayi wa Hilyaan kafin ta kalli khamees cikin kame fuska,kaman ba ita ke zolayar Lubnah yanzu ba.
"Barka da isowa yakk ya hanya"
Khamees ya faɗa cikin girmamawa,murmushi Bombee tayi masa tareda cewa.
"Hanya normal ne kasan dawar,ykk hope komai ya tafi normal koh?"
"Yeah komai kalau,amma nayi mamakin isowarki da safe haka"
Wani rolling manyan idanuwanta tayi,wanda hakan yasake bawa ƙwayar idanuwant show up,kafin tace.
"Jiya na shigo garin,so na tsayane a hotel badan hayaniyar dasuke yahanani sakewa ba,da bazan shigo yanzu na sai yamma"
Hajiya zeenah ce dake tsaye tayi magana cikin dan ɗaga murya yanda kowa zaijita a wajen,harda su Bombee da suke magana itada mutanenta.
"Toh amaryarce ta shigo da wuri haka,hala a gari kika kwana amma?"
Tsayawa tayi da maganar da suke da khamees ta ƙarisa inda Hajiya zeenah ke tsaye itada su Madeenah,harda Jabeer wanda ke tsaye a gefe kaɗan yana waya,saidai duk abinda ake akan idonsa a wajen.
Doguwar rigace baka a jikinta har ƙasa irin Butique ɗinnan,tasaka belt a tsakiyar rigar,wanda ya fitoda anihin shafe ɗinta,dama gata doguwar mace,mayafi tayafa akan rigar shima baƙi.
"Eh na iso ina fatan dai hakan bai zama muku matsala ba ina,irin na al'ada haka nan"
Bombee ta faɗa da ɗan murmushi kaɗan sannan kuma tana nunawa da hannunta.
Cikin dariyah irinta wayancewa Hajiya zeenah tace.
"Ahhh ehh babu komai,bari a rakaki an gyara komai ki huta kafinnan saiki shiryah kizo mu gaisa"
Daga kai Bombee tayi tareda kallom Hilyaan.
"Mu tafi koh kina tsaye"
Kallon Jabeer tayi juyawar datayi,idanuwansu ne ya sarqe da juna wanda shima kallon wajen dayayi kenan,wani kallon ƙasƙanci yayi mata yana bin kayan jikinta da kallo kaman yaga karya. Hakan ya batawa Bombee rai,amma sosai ba dam dama tayi tunanin hakan. Kallon kayi kaɗan tabishi dashi tareda juya idonta zata wuce,kamar irin takalli abinda bata buƙatarsa a rayuwarta tayi masa kallon kuskure.
Har suka shiga mota suka nufi sashen da ainihin part ɗin Jabeer yake Lubnah bata motsaba,yau taga wani abu waishi tashin hankali.
Sai bayan sun bar wajen taja wani mungun dogon numfashi tayi baya zata fadi.
Yaseerah ce tayi saurin riƙeta ganin tana shirin yin suman tsaye.
"Kambuuuuu menake ji kuma nake Yaseerah ni Lubnah,anya kuwa ban mutu ba ina raye??"
"Wanne irin mutuwa Lubnah,kina raye da ranki sarai,ki kalli kallon da Hajiya zeenah take miki ma,dan haka ki saita kanki karki nuna mata karyewarki nan da nam"
Ɗaga ido tayi ta kalli Hajiya zeenah wacce take yi mata kallon kaɗan ma kika gani daga aikina. Kafin ta juyah itada yaranta suka koma ciki.
"Yaseerah muje part ɗin da waccar matar ta nufah,taci nasara ta farko idan taci ta biyu zataga gadon baccina,dan haka yanzunnan ki wuce dani part ɗin basai anjima ba"
"Hmmm Lubnah kibari ba yanzu ba,saboda bakida wani makami a hannunki yanzu dazaki tunkareta,dan naga babu alamar tsoro a fuskarta,amma idan kika samo Jabeer a hannunki zuwa goben,shida kansa zai sakata tafita a ciki tunda zamansa takeyi"
Dahaka Yaseerah ta samu da ƙyar ta lallaba Lubnah ta yarda da shawarta suka bar wajen suma.
Shima dama Jabeer tun haɗuwar da sukayi a hanya shida Bombee da zata wuce yashiga motarsa ya bar gidan,cikeda sabon wani tashin hankalin dayasan zai dawo ya sameshi ko ina yaje.
A zaune take ta tattara hankalin ta gabaɗaya wajen bawa haneef break fast ɗinsa,kasancewar daƙayar yakesha saida dabara tukunna.
Mai aikinta ce ta shigo falon da rawar jikinta fara gaisheta.
"Ahh indo kece da sanyin safiyah haka,wata sabon gani kenan,ban ƙiraki ba kikazo da wur"
"Uhm Hajiya Lylah dama wani abune yake zagawa a cikin gidan,shine nace barinazo na shaida miki nasan baki sani ba"
"Mai ya faru haka da safennan, ince dai ba wata satar mai aiki tasake yiba?"
"Ahah ko ɗaya ba wannan bane,dama amaryar da Hajiya zeenah ta aurawa Yallabai ce ta zo gidan yanzu da safennan,naji ma har tana maganar wai a hotel ta kwana jiya kafin ta iso gidan"
"Mee amarya da safe,hotel dai,yau itada wa suka zo haka har suka kwana a hotel,tana amaryar da aka ɗaura aure kwana uku da suka wuce?"
"To kowama haka yace,kuma abin mamakin ma bata gaisheda Hajiya ba,shikansa yallabai bata kulashi ba,kuma naji Sagern hudu yana cewa wai ta takawa yaransa yatsan kafa da mota a shigowa"
Shuru Lylah tayi tana jin abinda indo take faɗa har takai ayah kafim ta sheqe da dariya tana cewa.
"Hhhhhhh kice Hajiya zeenah ta ɗebo ruwan dafa kanta,wannan shi ake ƙira da an gudu ba'a tsira ba kenan.
Kinga bar wannan zancen bana nan bane,bari na je sashen Iyah sayyada na sanar mata,cigaba da kulamin da Haneef kafin na dawo.
Tana gama faɗin haka da rawar jiki ta nufi sashen Sayyada-tateen,cikeda zumuɗin yafa mata wannan labari dataji,wanda tasan idan taji ba ƙaramin daru za'a yi a gidan ba,dan akwai ta dasan mata masu al'ada da kuma tarbiyya,idan taji irin wacce Hajiya zeenah takawomusu cikin zuri'ah,za'a kwashi ƴan kallo.








_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤7••8🖤










Lokacin data shiga Sayyada-tateen tana zaune akan carpet ɗin falonta,da kwanon tuwon semo a gabanta miyar kubiyah,kana shiga warin yajin daddawa zai bugi hancinka.
Labari suke tayi da wata mai aikinta wacce take itama dattijuwace ta manyanta,labari suke tayi tana warfa lomar ɗumame hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.
A bakin ƙofah Lylah tayi sallama tareda shigowa cikin falon,kallo daya Sayyada-tateen tayi mata tacigaba da taɗinta wanda sukeyi akan Ruwan kogi na ƙauye.
"To dakika shigo bazaki zauna ba kika tsayamin akai kaman naci miki bashi,mai ya kawoki wajena ma da sanyin safiyar nan oho,dan nasan ta Allah bata kawoki ballanta ta annabi,saidai ta allaro"
Duk sababin da Sayyada-tateen takeyi babu wanda Lylah ta tanka,don ba wannann ne ya kawota ba,burinta shine bata Hajiya zeenah a wajen Sayyada-tateen ɗin,ita kuma tasamu shiga sosai,ta hakkanne take ganin zata fara takunta na farko,wajen karbar ragamar gidan daga hannun ta.
"Uhm iyah ya ƙafar taki,ina fatan tayi sauƙi koh"
Miƙa ƙafar Sayyada-tateen tayi tana kallonta,wacce take luwai da ita kaman bata tsofi,magana tayi da tuwon a bakinta.
"Hmmm ƙafata bazata durƙushe da wuri ba,domin nayi mata horo mai tsanani na tafiyah,dan daga ƙyauyenmu har Samunaka nake zuwa a ƙafah.....ohh wato soma kuke nima na koma kaman Aliyu ku samu yadda kuke so ko,ta Allah to ba taku ba ehe"
"Ahah iyah niba wannan ne yakawo ni na,dama wani zancene nake tafe dashi mai muhimmanci wanda naga yakamata ki sani"
"In ma wannan zancenne da audillahi yayi min na zakiyi aiki a company bazan yarda ba,nice nan nace ban yarda ba,inkuka shiga aikin maza wazai kuma rike muku gidan,matan da suke gidannann bazasuyi aikin gwannati ba,dan kunka daulah bazaku kawomana tsarin nasara ba sam..... Yo ke Laure mai za'ayi da matar datake aiki a wajen maza,mu zamanin mu ina muka san haka sai su,su a dole ga ɗaliban nasara"
Shuru Lylah tayi tana kallon Sayyada-tateen,gaba ɗaya ta hanata tayi mata bayanin abinda ya kawota,in tafara magana saita cafe tayi wani layin daban,abin duk ya isheta.
"Iyah nifah ba wannan ne yakawoni ba,Hajiya zeenah tana can ta aurowa Jabeer wata mata daga can Gembu,yarinyar bata san tarbiyyah,yanzu haka zancen danake miki yanzunnan shigowarta cikin gidannan,wai tun jiya tabaro garinsu ita kaɗai,a hotel ta kwana na cikin gari,yau kuma tashigo cikin gidan. Ko Hajiya zeenah bata gaisar ba tanufi sashenta,shikamma mijinnata aka ce koh Kallonsa wai batayi ba,har fah mai aiki ta takawa ƙafa a shigowarta"
Shuru Sayyada-tateen tayi da kunne tanajin maganar da Lylah take da zubomata,wanda ta tariyo da wajen mai aikinta indo.
Tana gama bayanin Sayyada-tateen ta tafa hannu tafara sallallami.
"Lahaula wala ƙuwata yau ni Sayyada inagani abu,ke laure wai wannan zance haka yake?"
"Eh ƙwarai kuwa Hajiya sayyada,ɗazu kam naji ma'aikata suna maganar shigowata nan wajenki zan kawomiki yaji"
Shuru Sayyada-tateen tayi dan yanzu tarasa ma kuma abin bafah,a jima tace uhmm......in anjima tace uhmmm. Sudai sunyi shuru suna kallonta sai ajajjaba abin takeyi.
"Wannan shine uhm inji kuturu,ke La'ilah(Lylah),tashi tashi muje yanzunnan ki rakani sashen ita zeenatun naga yarinyar,bazan lamunta ba,wannan ai shine iya shegen wai layyah da kare,muje ki rakani yau zata san takawo mana tantiriya zuri'ah,yo ko ƴar aikice ai ban lamunci wacce zatazo ta ruguza tarbiyyah ba,ballanta matar gida,hakan ma kuma ta Jabiru,shida yake babba a yaran gidan. Abin ai zai mana yawa shege da hauka,ga wata can bamu gama hucewa da tujararta ba,za'a sake takalomana wata kuma,so ake a maida min gidan ƴaƴa sansanin barikin taƙadarun mata?"
Tana tafe a hanya tana sababi,itadai Lylah bata ce komai ba sai binta take a bayah,banda dariyar jin daɗi ƙasa ƙasa babu abinda take.
"Ke la'ilah wai ina baban gidanne da jikinsa?"
"Kai iyah,nifah sunana Lylah,miye kuma wani la'ilah kaman zakiyi salatin,shekara da shekaru amma kinƙi kama sunan common suna"
"Kee Butar Ubaki,miye kuma comon wato zagina kikayi koh,dama kema bawani son ki nake ba,saida na hana audinllahi auroki ya tuƙe,da ƴar kyauyenmu ya aura da tuni suna nan da yaransu ina,Amma yaje ya auroki kin Haifi ɗa kaman gammo duk a kanannaɗe,ke anya kuwa Iskokai basabin danginku ma?"
Harara Lylah ta makawa ƙeyar Sayyada-tateen,wacce take gaba tana tafiyah tinkis tinkis sai surutu take zubawa kaman rediyo,dan takaici ma shuru tayi bata tanka mata ba.
Hajiya zeenah ta tashi kenan daga dinning zata shiga ɗakin ta Sayyada-tateen ta rafka sallama a ƙofar falon.
Maleekah ce ta taho da gudu tareda hugging ɗin Sayyada-tateen.
"Ohh my dear kakus,biyoni kikayi kinga banzo ba?"
"Hmm ai barni ɗiyar albarka,ba biyoki nayi ba nasan ai zaki je,wajen wannan tujararriyar uwar taki nazoni,naji wani mummanan batu yana zagawa"
Cuno baki Maleekah tayiwa Sayyada-tateen,dan dama daga ita sai Abdulmaleek,sukadaine ke shiri da ita a gidan.
"Haba kakus kodanni bazaki daina yiwa mommy haka bane,zanyi fushi dake fah"
"Ke kijim yarinya,yau ɗin hadewa zakiyi da iya kinunamin ni barece,yo yi fushin mana ai inada Audu ma idan kika tafi,bariki ga na zauna kafar nan tawa sai a hankali"
Kujera ta samu a falon ta zauna,gyalen dayake wuyanta tacire ta ajiye tareda kallon Hajiya zeenah.
"To haziƙa mandiyah babu iso kuma babu sannu da zuwa,gaisuwar ma saina roƙa ko me?"
Matsowa inda take Hajiya zeenah tayi tareda gaisheta,bata amsa gaisuwar ba dan dama ba ita ta kawo ta ba.
Ɗauke kanta tayi tareda kallon Madeenah wacce take tsaye tana kallonsu,dan ita dama bakasafai take shiga shirgin mutum ba ,inya shiga natane dai bazaiji da daɗi ba.
"To sarauta nima sarautancin zakiyi min,narasa cikinki ke da jabiru wayafi iyah shege"
"Hmmm kinga iya ni makaranta zan wuce inada defend dazanyi kanki ake ji,inna gaisheki ma naga ba amsawa kike ba,ina san gaisuwata saina ajiyeta saboda gaba"
Daga haka ta saƙala jakarta tabar falon,dama iliyah yana jiranta a mota.
"Ke zeenatu wajenki nazo naji dahirr daga bakinki,shin da gaskene kin aurowa Jabiru taƙadariyar mata? Kuma bada izinin kowa ba,bansani ba dangi basu saniba,yaushe yaron yazama naki ke kaɗai,a iska aka miki cikinsa bashida uba?. Wai kekam wacce iriyar uwace kam,kinfiso yaronnan yayi ta fama da bauɗaɗun mata"
Shuru Hajiya zeenah tayi tanajin Sayyada-tateen tana ta masifah,itadai batace komaiba.
"Kiyi haƙuri iyah yanxu kam koma menene yariga ya faru,sannan a matsayina na uwarsa inada dalilina akan hakan,saboda in matsala ce ba a taimakonka,in kayi ƙoƙarin gyarawa kuma sannan za'aje ana zundenka a gaba,ko kunya ba'aji"
Takarisa maganar tana kallon lylah,wacce take zaune a kujera tanajin abinda yake faruwa.
"To maganin haka iyah a kiramiki yarinyar mana ki ganewa idonki da kanki idan ƙarya akewa mutum"
Lylah ta fada da biyu,dan itama dama tanaso taga ya yarinyar take da idonta.
"Hakane kam zancenki la'ilah,ke Maleekah kije kice mata ina ƙirnata yanzunnan a nan sashen tazo ta sameni"
Amsawa Maleekah tayi tareda toh,ta fice daga falon.
Bayan kaman minti talatin suna zaune tadawo daga inda aka aiketan.
Shuru tayi tana kallon wanda suke falon tana zare ido,alamar taga abinda yashiga hankalin ta,tsaida idanuwant tayi akan mahaifiyar ta,tareda yimata alama da ido kan tayi magana? Ɗaga mata kai tayi da eh,wanda hakan yasa Maleekah tamayar da idonta wajen Sayyada-tateen,wacce tayi ƙamo tana jira taji mai za'ace.
"Uhmm Iyah naje nasameta a falo tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login