Showing 81001 words to 84000 words out of 134612 words
duhu,ga babban titi motoci suna ta wucewa sun haska danjar su.
"Mlm ina ne nan kuma,mun iso abujanne"
"Yo wannan kuma na nawa,har fasinja kowa yakama hanyar gabansa,bakusan inda zaku bane kome?"
Saurin tashi tayi ta duba jakar kuɗinsu dake kunkuminta,amma babu ita babu alamarta.
Kallon yaron motar tayi ido a zare tace.
"Mlm ina jakar kuɗina toh,bangata ba ina ta kayanmu ma?"
"Haba Hajiya ni da nake gaba ina zansan inda jakar kuɗinku take,kayanku gashinan na saka muku a gefenku,dan Allah ku tashi zamu rufe mota"
Hawayene ya jirarowa Innayi lokacin data gano cewar wani ya ɗauke musu jakar kuɗinsu,gashi suna wajen da basusan kowa ba,takardar da inna Danejo ta bata tafara lalumawa domin ta nunawa yaron drivern,ita taji wayam babu ta fadi.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Shine abinda bakinta kaɗai yasamu damar furtawa,dan tasan sun shiga tsaka mai wuyah.
"Shugaba Zilliyah ki taimakeni kiyimin rai n roƙeƙi,wlh bansan cewar zata tafiba kinsanni kinfi kowa sanin halina,bazan barta ta tafi ba inda na sani"
"Kiyimin shuru,banza marar amfani,taya kika bari har tasan dashirin mu ta gudu,lokacin da burina yake dabba da cika komai ya watse,idan har itama waccar yarinyar tasan cewar Uwarta bata hannunmu,kina ganin zata zuba ido tayi shuru ne iyeee.
Dolene kisan abunyi,na baki nan da sati guda ki nemo,idan kuma ba haka ba......sainayi miki abinda bantaba yiwa wani yashi muniba.
Koda yake bata lokacina kawai zanyi,idan na barki babu abinda zaki iya akai,dan inaji a jikina sunyi nisa,gashi bakiyi mata turaren ba tun dare dana baki,saboda kinaso ƴar ki ta gudu koh.
Naaa tsinemiki laaarrii bazaki tana ganin daidai ba daga yau.
Nida kaina zanje na nemo su,dakaina zan je inda suke na ɗauko suruka ta,ita din mallakina ce,dukka su ukun nawa ne,nafara aiki akan su to kuwa bazan taba ja da baya ba."
Tana gama ƙarajin da ihun ta bace bata daga jikin madubin,bayan ta fesawa inna laari wani abu a jikinta.
Ihu inna laari tafara tana roƙon Zilliyah agazi,amma maimakon tajita,saima madubin dayayi fass ya fashe gida dayawa ya tarwatse.
Yana tarwatsewa kuwa inna laari tasaka ƙara tareda bingirewa tafara burburwa a wajen.
Zaune yake a personal gidansa ya rike kofin ruwa a hannunsa,da kuma magani,shibai sha ba shikuma bai ajiye ba.
Tunani biyu ne a cikin ransa,na farko shine na amaryartasa da Hajiya zeenah ta auramasa,duk yadda yaso ya fahimci ita wacece abin ya ci tura.
A yanda yaganta rannan zai ya rantsewa cewar bata haɗa hanya da hausawa ba inba dayaji tayi hausarba,sannnan a yanda ya karanci jikinta macece mai ƙarfi kuma jaruma.
Shikansa bazai yiwa kansa ƙarya ba yasan kyakykyawa ce fiyeda sauran mata daya taba haɗuwa dasu,a duk lokacin da idonsu ya haɗu dana juna sai yaji wani abu ya tsirga masa,ko dan saboda idanuwanta wasu iri ne shiyasa yakejin wani yarr idan ya kallesu.
"Hmmm kuma ma wai hadda yarone da itah,haba mommah meyasa kike min haka,taya zaki auramin matar da take ɗa hakan ma ɗan karami,bazawara ce ko kuma shegene ɗan bansani ba. Shin haka na koma kowa ma sai a auramin ita,"
Cikeda takaici yake maganar shikaɗai batareda mai sauraro ba.
Tunani na biyu kuma Jaleelah,iyah haɗuwa dakuma hada abinda ake so a wajen mace tagari dukka tana dashi,tunanin sa ɗaya shine auren,mata uku taya zai iya fuskantarsu ma tukunna.
Wata zuciyarce tace masa,kawai ka aureta,ai an auramaka mai ɗan ma a wani wajen dabaka san wacece ba ka rayu,sai wannan ne zai gagareka.
Ajiye maganin yayi da ruwan ya tashi ya saka kayansa,baiso komawa gidan yau ba,dan yau ɗinne Lubnah takoma sashenta sabo,wanda yasan shima an kaimasa kayansa can ɗin,ko sha'awar wajen bayason kalla bare kuma zama a cikinsa,idan yaki komawa kuma yasan bai dace ba ace matansa na wani waje daban shima yana wani waje daban.
Lallai Hajiya zeenah tagama tsara taswirar rayuwarsa a hannunta,wannan karon zai gwada ƙwatar ƴancinsa koda kuwa kadanne.
Tafiya kaɗance takaishi gidannansu,direct sashen iyayennasa ya nufah,baisani ba shin abban nasa zai amince ko kuwa ahah,dan karyace ai bai daɗe dayin sabon aure ba.
Su biyune a falon,daga Hajiya zeenah sai shi,da alama zance suke akan wani abun.
Ita kuma Hajiya zeenah da saƙa ta ulu a hannunta tanayi domin samun abinyi.
Bayan ya gaishesu zama yayi yai shuru,shibai tafiba shikuma bai ce komai ba.
Dariyar dattako Alhj Aliyu yayi kafin yace.
"Babban mutum yadai naga kayi shuru,kuma alamu sun nuna akwai abinda yake cikin ranka,mai nene a haka ka faɗa min ko mai nene.
Kobaka so faɗane a gaban mahaifiyar taka kanajin kunya"
"Ahhh nizaiji kunyah,saidai ko nauyi tayi masa kai a baki,idan kunyace kuma to barina baku waje ku tattauna,idan tayi wari ai zanji"
Hajiya zeenah tafaɗa tana dariyah zata bar ɗakin.
Saurin dakatar da itah Jabeer yayi tareda cewa.
"Ahah mommah ki zauna kawai,dama......dama inaso na faɗamuku ne cewar zan ƙara aure,akwai yarinyar danake so to kuma mahaifinta yace na turo ayi babbar magana"
Ɗan taƙaitacce bayanin Jaleelah Jabeer yabawa su Hajiya zeenah.
Jimm sukayi dukkansu kafin Hajiya zeenah tafara magana,wanda dama tunda yafara maganar ta tsaya da abinda take.
"Aure kuma yanzu,habadai aure ina kuma Auren shi........"
"Kinga kinga Momyn yara,kada ma ki ɗakko wannan zancennaku da kuke ta maimaitawa shekara da shekaru,bazan hanaki yabi umarninki ba,saboda ke kika haifeshi,amma kuma wanann karon bazanyi shuri ki tauye masa haƙƙinsa ba.
Duk tsawon lokaci ke kike aura masa wacce kika ga dama,wannan karon yazo miki da wacce yake so,dan haka bincike yakamata a ayi,idan har gidan mutuncine nizan saka ayi bincike akan hakan.
Godiyah sosai Jabeer yayiwa abbannasu,dan bayyi tsammanin zai amince tashi ɗaya ba.
Duk da cewar Abbannasa ya tari bakin Hajiya zeenah,amma yasan bazatayi shuru iyah hakanan ba.
Dole saita yi wani abun akai,shi hakan bai dameshi ba tunda mai nemo masa auren ya amince.
Bayan Jabeer ya tafi nasiha Alhj Aliyu ya zaunarta yayi mata akan lamarin da take tafiyar da rayuwar ɗanna ta,amma hakan bayyi mata ba.
Tana shiga dakinta tace "chabɗijan aure,yar uban wanne matsiyacin ce,daga yanda yabada labarin ɗiyar talakawa ce,waton sunganshi da alrziƙi da matsayi zasu mallakeshi koh.....hmmm dani kuke zancen."
Wayarta da ɗauka tana neman Number Hajiya rabi,domin susan abinyi.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________
Page 🖤21••22🖤
"Me kike faɗa haka Hajiya zeenah bana jinki,aure kuma wanne iri?"
"Hmmm yadda na faɗamikinnan haka naji nima,yanzu haka na saka ayimin binciken yarinyar da iyayenta,abu daya na sani shine ƴar talakawa ce sosai"
"Talakawa kuma,da girmansa kuma ya ɗauko ƴar talakawa,ga waccar wadda kika ɗauko bata fara aikin komai ba,meyasa abu yake nema ya fita a hannunmu ne kai. To shin bakiyi ƙoƙarin hanashi ba kuma?"
"Uhm hakan bazai yiyu ba sam,domin duk abinda nake abbansu baya sakamin hannu,amma wannan karon yatsaya akan idan bai ga wata matsala ba,to zai aurawa Jabeer zabinsa.
Ni inaga mu zuba ido muga shin mai zasuyi kawai,idan an saka bikin kafin JAWAHEER tagama makaranta,to saimu matso da natan,idan kuma sun saka dayawa saimu jira"
"Ai babu wani zancen jira,makarantar banza makarantar wofi,Ki bari muji wanne lokaci suka saka muma sai mu saka daidai dashi.
Batun ita yarinyar kuma,saimu ƙarawa waccar yarinyar kuɗi tayimana dukkan maganinsu kafin ta tafi.
Ya kikaga hakan toh,kinga in ta gama dasu itama ta tafi,shikenan mun huta,makaranta kuwa idan so take,ko ƙasar wajene ma ai sai ya kaita tayi"
"Eh hakan yayi sosai,bari na zuba musu ido su gama shirin,sai ranar auren yaji mai na yanke"
Daga inda yaron drivern yabar su innayi basu motsaba,sai faman aikin neman Jakarta take,amma babu ita babu alamunta,haka ta gaji tabar neman ta fawwalawa Allah.
Alfijir ne yaketo gari ya fara haske,mutane masu rumfa a wajen,musamman ma ƴan abinci sun fara fitowa.
Wajen wata mai abinci innayi taja Danejo suka nufah,domin samun ruwan Sallah.
Daga ganinta musulma ce,amma kuma batayi kama da bahaushiya ba.
"Amm barka da safiyan Madam,dama ruwan sallah muke nema nida innata ko zaki taimaka mana dashi?"
Kallon bakusan mai kuke ba tayi musu,tareda cigaba da hura wutarta.
Maimaita maganar innayi tayi,wannan karon maimaikon tayi shuru,masifa tafarayi da hausarta wacce bata ishi bakinta ba,gwanda ma ta innayin mai surkin fillanci.
"Ke yarinya bani wajenan idan ke bakida aikinyi,ruwan haka yake a banza kaman kogi,kuɗi fah na saka na siyah"
Hannun innayi Danejo taja,alamar tazo su tafi daga wajen.
Hanyar wani layi suka nufa,suna tafiya kaman bazasuyi ba,abin duniya duk ya ishesu.
"Inna Danejo yanzu kenan a in zamu samu Addah Bombee,takardar ma ta faɗi banganta ba,gashi bamusan kowa ba a garinnan. Abu ɗaya na rike a takardar shine JAAN Estate,bayanshi na manta komai a jiki"
Tafiyah suka har aka fara shiga Sallah a masallatai.
Wani masallaci suka kawo sun shiga Sallah.
Ranadar masallacin innayi ta nufah ta ɗebomusu ruwan a cikin butar da tagani a wajen.
Kawomusu tayi sukayi alwalar suka sha sauran.
Zaninta ta shimfiɗamusu sukayi tada sallah. Suna cikinyi mutane suka fara fitowa daga masallacin,kasancewar haske yafara kowa yana kallonsu.
Wani dattijo ne suka fito daga masallacin shida wani matashi suna magana.
Idonsa ne yakai kan su innayi wanda suka sallah a harabar masallacin,tsayawa sukai suna kallonsu har suka gama.
Innayi ce data kuladasu ta taso ta ƙariso wajensu,tsugunnawa tayi har ƙasa ta gaishe da dattijon kafin saurayin.
"Lafiya yarinya na ganku anan,maikuke anan wajen da wannan lokacin,sannna kuma da alama ku baƙine koh"
"Eh baba mu baƙine,munzo neman ƴar uwata ne nida innata,saikuma mukayi rashin sa'a wasu suka ɗauke mana kuɗinmu a mota,shine mukazo nan domin muyi sallah saimu samu inda kuma zamu nufah"
"Innalillahi ana gamuwa da bata gari kam sosai,shin inane ita inda yayarta ki take?"
"Ehh takardar data bamu na address ɗin itama ta bata,abu ɗayah na sani a jikin takardar shine JAAN Estate"
"Wai yarinyar taya zamu gane kawai daga suna gidan,inda akwai address ɗin anguwarne dai da dasauƙi toh"
Jimm Innayi tayi daga inda take tsugunne,tarasa ma yake mata daɗi,inda zasu nufah ma shine babban tashin hankalin ta. Daga cikin tunanin tajiyo muryar dattijon
"Tunda kince baki san kowa ba,sannan kuma babu kuɗi a wajenku ballantana ku koma,gaki ɗiyah mace ita kanta innartaki naga kaman bata gani"
"Ehh baba bata gani sannan kuma bata magana,saidai tanajin abinda ake faɗa"
Jijjiga kai yayi cikin halin tausaya musu.
"Idan bazaki damuba akwai gida gefe da masallacinnan,yanada ƙofah tawaje da kuma ta cikin gidana,daki daya ne dashi sai banɗaki.
Ku shiga keda innartaki ku zauna,zan saka yusufu ya bincikomin inane jaan Estate ɗin sai ya kaiku,tunda shima tuƙin Taxi ɗin yakeyi.
Ku zauna wajen yafi muku yawon da baku san hannun wa zaku faɗa ba. Inyaso sai ki dunga ɗebo mana ruwa kina gyara masallaci dakulada shi kafin lokacin,dama maiyin aikin yarone ya tafi makaranta,sauran yara kuma sun zama na zamani"
Tun kafin ya gama bayanin innayi ta tsugunna tafarayi masa godiya kaman zata kifa,saida ya dakatar da ita tukunna.
Wajen inna Danejo ta nufah ta shaida mata abinda mutumin yace,da farko taji jimm kafin ta ɗaga kanta,amma kana ganin fuskarta kasan bataji daɗin yanda suka ƙare ɗin ba.
Dakansa ya Mlm Tijjanin yaraka su gidan,dama na mahaifiyar sa ne data rasu.
A lokacin innayi tashareshi ta shimfiɗamusu tabarma a ciki wacce ya aiko yaro ya kawomata,ta gama gyaran kenan aka sake turo musu da ɗumame na abin karyawa.
Wasa wasa anyi sati guda da dawowar Lubnah sabon sashe.
A iyah wannan lokacin anyi abubuwa da dama,ciki harda tambayo wa aure da aka yiwa Jabeer,take aka saka rana nan da wata uku. Itama hajiya rabi tana jin haka tace a haɗa dana ƴar ta.
Nan da wata uku kenan za'ayi tare,lokacin da Lubnah taji wanann zancen ƙaramar hauka ce kawai batayiba,musamman ma zancen Jaleelah wanda bata san dashi ba.
A bangaren Bombee kuwa hakan zai wani dameta ba,tayi sati ɗaya kenan a gidan,dan haka lokaci yayi dazata fara nata moving ɗin.
A zaune suka a harabar da yamma suna duba bayanan da khamees ya turo ma Bombee ɗazu.
Wajen a ƙawace yake da kujeru da kuma rumafah irinna zaman shaƙatawa,da alama dai domin zama a huta akayi shi.
Su ukune a wajen,Hilyaan Bombee saikuma Haidar wanda yake cikin Holding bed ɗinsa yana wasa a gefensu.
Shuru kakeji dukkansu babu wanda yayi magana,sun maida hankalin su kan document ɗin dake gabansu.
"Anty maryam banji kinyi zancen sabin amarennaki ba dazasu zo"
Hilyaan ta faɗa cikin sigar zolayah,kallon rabin ido Bombee tayi mata tareda yin ƙaramin murmushi.
"Wai meyasa Hilyaan kike abu kaman baki san komai ba uhm,dama nasan da zuwan Jawaheer koba daɗe da jima,amma kuma itama Waccar ɗin nayi tunaninta tun ranar dana ganshi yana duba Sashen dayake kusada shi.
Na gansa kusan sau uku yana shiga wajen shida wasu ma'aikata yana dubawa,sannan kin manta lokacin da Lubnah take da faɗan bai kwana a gidannan ba?,na tabbata ba a gidan Su Jawaheer ya kwana ba,saboda kallo daya zakayiwa sha'anin kasan cewar ba soyayya a tsakani,Hajiya zeenah da kawartane suke rawarsu suke kiɗansu.
Da farko nayi zaton a gidan su yarinyar ya kwana,danayi bincike jiya kuma na gano gidansu sunada kamala sosai,to ɗayan biyune yake faruwa......"
"Kutt taya kika shirya waɗanann labaran,ɗayan biyun wannene"
"Ko akwai wajen wata daban dayake zuwa idan yana cikin matsala,ko kuma akwai wani waje boyayye dayake zuwa,wanda bayason kowa yasani,a yanda kuma naji labarin a mutuwar matarsa Hafsa an rasashi a gida na wani lokaci kafin ya dawo cikin mawuyacin yanayi.
Tabbas akwai wani abu dayake boyewa wanda babu wanda yasani,harda iyayensa ma"
Tafi Hilyaan tafara yiwa Bombee na alamar jinjina,sanann kuma takara dacewar.
"Gaskiya na jinjina miki,amma inaga wannan binciken da a akan Lubnah da familynta mukayi,ba'a kan Jabeer ba,saboda naga kaman baya cikin target ɗinmu koh?"
"Baya cikin target ɗinmu a zahiri,amma a boye shine babban target ɗinmu.
Kowa dayake cikin wasannan ƙarshen target ɗinsa kan Jabeer yake yin birki.
Hajiya rabi nata shirin shine ƴarta ta aureshi ta haifi ƴaƴa,itama kuma hajiya zeenah shirinta shine ta haɗe companyn hajiyah rabi dana Jabeer saboda JAAN yaƙara power.
Ita kanta Lubnah ba itace ta haɗu da Jabeer ba,iyayenta ne wanda suka haɗa komai,domin itama ta haifi ƴaƴa a gidannan,dasuka ga bazata haihu ba sai Gen Abdu manga yakeson Mallakar companyn yanzu.
Kuma ina mai tabbatar miki kwanan zai fara moving ɗinsa akan hakan. Sannan shikansa gidan da kike ganinsa akwai Akwai abinda yake going a cikinsa.
Zaro ido Hilyaan tayi tareda cewa.
"Ba.....bbban fahimceki ba Anty maryam"
"Meeting ɗin dayaje a wancan satin Gen Abdu manga shima yaje wajen,kinsan meyasa?"
"Ahah bansani ba?"
"Saboda shine nabiyu mai kaso mafi yawa na share companyn,a kowanne lokaci zai iyah ƙarbe shi daga hannun Jabeer"
"To abin da ɗaure kai,saboda taya Zasu bar wani yayi kusa da mai company a yawa share?"
"Ba a mutum ɗaya ya siya share ɗin ba,ya mallakesune da sunayen mutane a ƙallah Gudan goma,kuma shima kansa Juyashi ake yakeyin aikin, babban kifin yana duhu,shiyake juya komai.
Alhj Abdullahi ƙafafa yake yana tunanin shine da babban share na companyn,saidai ba haka bane.
Wannan ne dalilin dayasa matarsa take Nata aikin da daddare batareda kowa ya sani ba a boye,da alama mijinta take tayawa yaƙi.
Tohhh kinga anan wajen shin wanene Target ɗinmu idan muna son ruguza kowanne?"
"Jabeer!!!!"
"Done Plan yayi solving toh"
"Amma taya zamu solving a kansa,shi baida laifin ballantana mu kamashi"
"Akwai hanyoyin saka mutum a cikin tafin hannunka,basai da Laifi ba kokuma Soyayya"
"To taya zak......."
"Wait and see Hilyaan,lokacin zai faɗamiki koma menene"
Suna shirin tattarewa yamma tayi motar Jabeer tashigo harabar wajen baƙa siɗik da ita ƙirar daraja.
A hankali yake tuƙin irinna ƙasaita har ta kaita wajen parking inda sauran motocin suke.
Buɗewa yayi ya fito tareda nufar hanyar sashensa,maganar Lubnah ya jiyo wacce taji muryasa tafito daga sashenta,shi duk yayi zaton ma bata gidan tunda taji labarin auren dazayyi.
English wear ne a jikinta tasha ado sosai,tundaga nesa take fuɗemasa baki kamar gobar auguda,saidai daga yanda take dariyar zatakasan cewar bahar zuciyarta bane.
Takowa take cikin tafiyar mai son jan hankalin wanda ake yiwa.
"Honey ina kuma zakaje,tun ɗazu fah nake jiranka,kuma saika wuce batareda kaga ya nake ba koh"
Tayi maganar cikin karayar zuciya,dan ita gabaɗaya a tunanin ta sashen Bombee zai shiga daya nufi wajen.
A yanda tayi abun kwata kwata bayyi mata kyauba,shikansa Jabeer sakin baki yayi yana kallonta, "Mata iyayenmu" yafaɗa a ransa.
Kasa rike dariyarta Hilyaan tayi,ganin tafiyar da Lubnah takeyi,aikuwa tunda babu wanda ya ɗauremata baki tasaki dariya.
A tare Jabeer da Lubnah suka juya inda Su Bombee suke zaune,danshi sai yanzu ma yagansu.
Idonsa akan Bombee ya sauƙa,wadda fatarta take sheƙin yamma,ga kayan sun amshi jikinta sosai.
Gajeran kallo ta aika masa na dan mintuna tareda murmushi,kana kuma ta maida kanta kan system .
Kansa ɗaurewa yayi,yarasa shin murmushin dawa take,dashi take data kalleshi kokuma da abinda Lubnah tayi ko ga mai aikinta.
"Kuttt yaushe har kina matsayin ƴar aiki kika samu damar yin dariyah a inda nake,yau saikin faɗamin dawa kike,barganin kina aiki a ƙarƙashinta kuma tare kuka zo,ko uwarta ce bazan ɗau raini daga gareta ba ballantana ke"
Hilyaan ce ta kalli Bombee wacce bata ɗago ba,amma kuma fuskarta ya nuna Ranta tafasa yake,dan ita kanta Hilyaan sai tayi shakkar fuskartata.
Takowa Lubnah tayi zuwa inda suke.
"Kifaɗamin dawa kike a wajennan dahar kika samu damar dariyah,ko wacce kike zaune dominta bata isa ballantana ke"
Yanda Lubnah take maganar ne da izzah yabawa Hilyaan haushi,ɗaure fuska tayi ta tashi zata mayar mata martani(abin sojoji ya motsa).
Tun kafin ta miƙe taji shugabar tata tayi magana.
"Don't,ke yanzu in kare marar sarka a wuya yayi miki haushi saiki juya ki rama?"
Ɗan murmushi Hilyaan tayi bayan ta watsawa Lubnah kallon baki kaiba.
Hakanne yasake ƙuleta ta hassala zata fara faɗa.
Buga tebur ɗin Bombee tayi tareda miƙewa suna kallon kallo a itah.
"Lubnah kowa kike ya isheki haka,da akayi kason haƙuri kaɗan aka bani,to tun ɗazu zakika zageni kika Ɗebeshi,karki bari ki shiga list ɗina tun lokacin shigarki bayyi ba,hakan bazayyi miki daɗin.
Kije can ga mai riƙe da igiyarki yana jiranki,idan kika tasarmin yaro daga bacci wlh bazakiyi baccin daren yau ba. Idan kina musu try me please"
Yanda take bata saƙon kausashe nan da nan yakai inda takeda muradin yaje.
Jabeer ne yayi gyaran muryah bayan gama jawabin Bombee ɗin.
Tunda suka fara ƴar tsamar yana tsaye ya haɗe hannu yana kallon su,haka kawai yaji yanada buƙatar yasan wacece amaryar da mahaifiyar sa tayi masa,idan yanada buƙatar hakan dole sai ya matsa jikinta yasan ya take.
Beside tunda zai haɗa mata huɗu,dolene ya dunga tsayawa yana ganin mu'amalar dake tsakaninsu. Duk da yasan dana ba kyau zatayi ba koda yace zayyi koƙarin gyarawa.
Ɗan jijjiga kai yayi bayan ya kalli inda yaron yake kwance,babu abinda