Showing 75001 words to 78000 words out of 134612 words

Chapter 26 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8661

wanda sun tsayar da shawarar da gobe zasu nufi Cikin dajin inda Nau'urarsu ta nuna musu.
Gen Abdu manga ne a zaune yana kurbar lemo a kofi a cikin office ɗinsa.
Sameerah ce tashigo tareda sara masa,saida yayi mata alamar hannu kafin ta gyara tsayuwarta.
"Mai kika samo wannan lokacin kuma?"
"Sir yanzu kam nasamo wani abun,wanda ina mai tabbatar maka dazamu yi nasarar kaiwa Gen Muhammad ƙasa da tawagarsa,sannnan kuma ina mai gargadinka da cewar,Captain maryam tagano cewar,makaman dakayi order wannan karon Basuda kyau,idan takai wanann rohoton division,ina mai tabbatarmaka da zata ga bayanmu,ba iya ga babbar kujera ba,harma ga rayuwarka saita shiga haɗari,domin sanadiyyar amfani da makaman yajawo rashin nasarar da Rukunin sojoji tayi a harin daya gabata,yanzu haka sun nufi black room domin gano shaidu akan aikin da muke aiwatarwa.
Saurin ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tareda tashi ya tsayah,dunƙule hannunsa yayi tareda cije baki.
"Wannan yarinyar wai ya zanyi da itane,tun zuwanta wajennan na tsawon shekara guda,babu abinda take sai kawomin cikas,da kuma kawoma gen Muhammad nasara,da farko nayi zaton ƴar sace,sai daga baya na gano cewar riƙonta kawai yayi.
Yanzu toh ya kike gani,ta wacce hanya zamu bullo musu?"
Dariyar gefen baki tayi kafin tace.
"Karka daku yallabai baza'a samu matsala ba,sun riga sun gama amincewa dani,basuda masaniyar ina tareda kai,inaga kwantan bauna zamuyi musu,mu biyo musu ta bayan gida.
Kaman yanda suka ce zasu black room mu barsu suje ɗin,Akwai Detect camera da zamu saka a jikinmu domin gano inda muke,iyah haidar ne yasan yanda ake kasheta da kuma yanda ake Kunnata,tanada amfani da yawa kana kuma tana da matuƙar hadari.
Idan aka danna danger alarm ɗinta,to zata rarwatsa tsokar jikin mutum a area datake,idan aka sakata a wajen zuciya to mutuwa ne direct in aka hareta.
Nida haidar ne kaɗai mukasan yanda ake Hari da ita,zan baka controller a gobe inshaaallah,kafinnan zamu tsara yanda komai zai tafi"
Tafi Gen abdu manga yafarayi irin na alamar jinjinawar nan,Haƙiƙa ina Alfahari dake,zan haɗaki da mutanen dazasu taimaka miki,wannan karon ki tabbatar kinyi nasara,idan har hakan ya tabbata,to zan baki matsayin da kika daɗe kina nema"


Kaya suka gama sakawa baƙaƙe wanda zasu saje da aikin dazasu fitan.
Rataya bindigoginsu sukayi,saida suka tabbatar kowa ya shiryah kafin suka fito daga cikin inda suka buyan.
A hankali suke tafiya cikin sanɗa,kowa yana kallon inda kowa yake,saboda abinda suka saka a jikinsu,tafiya sukayi mai nisa suna bin na'urar datake nuna musu inda zasu nufa.
Wani waje suka iso a tsakiyar dokar dajin,ba gidane haka normal ba,haka yake square na ƙarfe,kallo kallo suke kafin suka rarrabu kowa ya saita,wasu kuma daga cikinsu suka shiga,saida na wajen suka tabbatar komai normal kafin suka shigo.
Ɗakuna a cikin wajen sukan guda goma,saikuma filin tsakiyar wajen wanda yafi ɗakunan girma,babu koma a cikin wajen sai warin tsatsa da kuma motocin yaƙi guda uku.
Duddubawa suka farayi kowanne daki,abinda suka samu ya basu mamaki matuƙa.
Dukka cikin wajen makaman yaƙi ne kala kala,harda wanda ba'a yarda ayi amfani dasu ba.
Hakan bai basu mamaki ba kaman ruwan wasu allurai dasuka samo a wajen.
Kawosu sukayi kan wani babban tebur a tsakiyar wajen sukayi,kowa ya zubawa abubuwan ido baya cewa komai.
"To yanzu waɗannan alluran akan wa za'ayi amfani dasu kenan,tabbas gen abdu manga ba baƙaramin murum mai hatsari bane,dolene mukai wadannan abubuwan zuwaga headquarter,domin ayi mummunan bincike akai"
"Hakane dama dole mu fitadasu bilal,ta hakane za'a yanke masa hukunci,sannan kuma mu ɗau fansar abokanmu da suka mutu a wajen yaƙi saboda mummunan aikinsa,irinsune suke sakawa a zagi sojoji kuma a dungayimusu kallon Azzalumai"
Fara tattara kayan sukayi da niyyar tafiya dasu,duk abinda suke Sameerah na tsaye tasaƙala hannunta tana kallonsu,saida suka gama haɗa komai kafin ta sheqe da wata arniyar dariyah tana tafa hannu.
"Captain maryam,da kuma captain haidar kuda mutanenku haƙiƙa kunyi ƙoƙari sosai,da tun lokacin da kuka fuskanci akwai wata matsala kukayi shuru,da baku kawo kanku mahallakarku ba,amma yanzu kam aikin gama ya riga yagama kun haƙa raminku da kanku.
Kuskurenku ɗaya shine bari da kukayi na san shirinku.
Saitata da bindiga bilal yayi zai harbeta,da sauri Bombee tayi saurin riƙeshi ganin abinda take riƙe dashi.
"Yana harbina zan dannan abinnan,duk wanda nice na saka musu na'ura ba haidar ba to zata tarwatse a cikii ƙirjinsu tareda Zuciyarsu"
"Me kina nufin a wajen zuciya kikayi injecting ɗin na'urar Sameerah,amma kinsa ba'a saka waje mafi hatsari,shiyasa dana cemiki wajen ƙirjina naga ciwo kikace cokata kikayi baki sani ba?"
Da murmushi ta daga masa kai alamar eh.
Juyawa yayi ya kalli inda Bombee take,fuskarsa dauke da nadamar abinda ya faru,domin gani yake duk laifinsa ne Sameerah tasan shirin su,da kuma abinda zasu aikata.
"Karki damu maryam,har yanzu muna da damar yin nasara,karku damu ku banasaka muku a wajen da zatayi muku illah ba,sannan nariga na danna tawa na'urar,nasan division ɗina sun karbi sakon,kuyi saurin barin wajennan yanzunna kafin lokaci ya ƙure"
Jijjiga kai Bombee tayi hawaye na ziraro mata,ba abinda taki jini irin ganin haidar ɗin a haɗari.
"Hhhhhh kunfah riga kunzo hannu,babu wanda zai tsira daga cikinku,bari kuga na fara da wasu"
"Tana gama faɗin hakan ta danan jar danjar datake hannunta,tass kakejin a ƙara a ƙirjin mutane biyu,da bilal da kuma Haidar"
Wata irin gigitacciyar ƙara Bombee tayi tareda ƙiran sunan sa kaman maƙogaronta zai fice.
A
Da gudu ta nufi inda ya tsaya akan gwiwoyinsa dafe da ƙirjinsa,kallonta yayi da idanuwan da suka rasa rayuwa a cikinsu,
"Bombee ƙawata,naso maidaki matata saidai hakan bazai taba yiyuwa ba,da alama banine mijinki ba Bombee,koma waye zai kasance mijinki kice masa yayi sa'a, Bombee kiyafemin abinda nayi miki daga haɗuwata dake,sannan ki nema min gafarar iyayena ma,ina sonki sosai"
Daga haka yafara faɗan kalmomin da batajin abinda yake faɗa har yayi shuru.
Jijjiga kai tafarayi tareda cewa,
"Bazaka mutu ba Haidar ina alƙawarin da kamin na ganin ranar dazan dau fansa,indan naƙi aurenka ne ka tafi,zan aureka Haidar kada ka barmu banida tamkar ka a wannan wajen,bazan juri rashinka ba,karkamin haka na roƙeƙa haidar,nima inasonka a har cikin raina"
Tana tsugunne a wajen taji khamees yana kiran sunanta.
"Maryam maza ki bar wajennan akwai haɗari"
Kafin ya rufebaki taji alamar samu mutane suna shigowa,saitata Sameerah tayi da bindiga zata harbeta,tun kafin ta harbetan ita ta fasa mata hannun da take ɗauke da bindigar,kafin ta karamata taji khamees ya fizgeta sun bar wajen.
Ƙoƙarin kwacewa take tana kallon wajenda gawar haidar take,
"Khamees kabari na ɗakko shi tukunna,sannann nayi daga daga da tsokar waccar tsinanniyar,sannan ne zan bika mubar wajennan"
"Kai Maryam ki fahimata mana,muna cikin yanayi mafi muni,dolene mubar wajennan,shikansa haidar idan yana raye zaiso ki bar wajennan"
Yayi maganar yana share guntun hawayen dayake zubo masa.
"Inji uban waye ya mutu,bazan bar wa......."
Ɗan duka yakai mata a wajen ƙasan kunnenta,nan da nan kuwa tayi shuru ta suma,kinkimar ta yayi yanufi fita da ita daga wajen.
Muryar Sameerah yaji wacce take ihun hannunta tana shunensu.
Shida Hilyaan ne kadai idonsu biyu,sai Bombee wacce yasaka a kafaɗa,gudu suke falfalawa a cikin daji har saida suka gaji suka tsayah.


A bangaren Sameerah kuwa sojojine suka shigo wajen,domin saƙon Haidar ya isa garesu,iya Sameerah ce kawai a wajen tana riƙe da hannunta,tana ganinsu tasaka kuka tareda cewa.
"Yallabai ka taimakeni,captain maryam ce ta kasheshi tareda ɗaya Sojan,nima dan bata sameni bane wajen makasa da ta kasheni,inbaka yarda dani ba ka duba bullet ɗin da shaidar dukka natane,a ƙirjinsu dukka ta harbesu"
"What ina take,sannan mai kuke a wajennna"
"Uhm in labene jiya sai naji suna zasu jawoshi wajennan su kasheshi,to dana biyosu saina ga sun harbeshi,shi wancan yana cikinsu,amma sai yace bazai yi shuru ba,shine shima suka kasheshi,danayi kokarin cetansa nima ta harbeni,tana shirin kashenine haidar yace ai yatura saƙo division ɗinmu,shine sukaji tsoro suka gudu"
"Itada waye a tareda ita?"
"Uhn.......uhhh itada Mataimakinta ne captain Khamees"
Sameerah tana gama basu labarin ƙaryar ta suma,gawar haidar da bilal suka ɗauka inda a daren aka baza neman su Bombee a cikin garin abuja da kewaye.
Labari yana isa kunnen gen Muhammad yafaɗi jininsa ya hau,da farko bai gaskata abinda Bombee ta aikata ba,saida shaidu suka fito,kuma ta rashin bayyanar Bombee yasa yafara yadda hakanne,saidai duk yadda yayi tunanin menene dalilinta na hakan yakasa ganowa.
A kwana basufi uki ba labarin abinda Bombee tayi ya karafde cikin barrack da kewaye,kowa banda tsinuwa babu abinda yake yimata.
"Lokacin da Bombee ta farfaɗo a cikin kogon da suka buyah,taji labarin abinda yake faruwa,wanda Hilyaan ta jiyo musu,tunda ita babu wanda ya zargeta,zuciyarta ba ƙaramin tafarfasa tayi ba.
Yanzu kenan da wanne ido zata kalli iyayen haidar,bayan suna mata kallon wacce ta kashe musu ɗansu.
"Khamees inada wajen dazamu je,dolene mu bar garinnan kafin komai ya lafah,dolene na dawo na ɗauki fansa,ke Hilyaan ki koma bakin aikinki kawai"
"Ahah cap......anty maryam,na ajiye Aikin soja harsai ranar da sunanki ya wanke zan kasance taredake idan harkika bani damar hakan"
Shuru Bombee tayi batada abin cewa,dan gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi a lokacin,haka zata ƙare rayuwarta kenan ana yi mata sharrin kisa,anya kuwa zata iya sake yarda da wani ma????......




***DAWOWA LABARI***


















_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK 2_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]








Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!


Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin


https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31




Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.


3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150


Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU


Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150


______________****_______________










Page 🖤17••18🖤








***DAWOWA LABARI***






Shirye shiryen komawa new side Lubna takeyi,dan bazata fara sabon aikin da boka zulungum yabata a wajenba.
Gobene kuma dawowar Jabeer daga Tafiyar dayayi,kuma goben takeso tasakashi ya kori Bombee daga side ɗin da take,dan da ita yadace badawata can banza ba.
Haka ta wuni tana saƙawa da kwancewa ita kaɗai.
Muryar Bishirah ce ta katseta daga tunanin abinda tashirya gobe tayi,
"Uhm ranki yadaɗe an samo baƙar kuliyar kaman yanda kika ce"
"Yawwa Bishirah na gode,dafatan dai babu wanda yaganki da ita koh"
"Eh babu wanda ya ganni,a cikin kwali na shigo da ita,nasaka mata maganin bacci a kifin kaman yanda kika ce"
"Shigomin da ita yanzunnan"
Fita Bishirah tayi,bata daɗe ba sai gata da mage a hannunta,ta langabe sai bacci takeyi.
Duk da tsoron dayake cinta haka ta daure ta karbi magen tareda nufar ɗakinta da ita,bayan tayiwa Bishirah gatgaɗin kartaji wannan zancen.
Banɗaki ta nufi da ita inda ta ajiye suƙa da kuma maganin. Wanda yake cikin kasko.
Hannunta yana rawa yana komai haka tasaka wuƙar ta yanka wuyan magen,jini ne yafara zuba a cikin kaskon,inda magen tafara shure shure,amma haka ta riƙeta gam da hannu biyu jinin yana ɗiga,a duk Lokacin daya ɗiga sai yayi cuuu kaman ruwa ya ƙone ajikin abu mai zafi. Da haka har ta gama tass kafin ta jefa gawar magen a cikin leda tasaka a durt bin.
Ɗaukar kaskon maganin tayi ta maidashi inda tayi masa kyakykyawar ajiyah.
"Anyi ɗayah,hmmmm duk wanda kuka rabi Jabeer kun shiga uku da baƙin ciki,zanso naga idanuwanku ranar dazanyi masa asirin da ko lasar ƙafata nace yayi sai yayi batareta musu ba. Wuyar wata ukun tacika,zakuga abin mamaki da idanuwanku"
A zaune yake akan gado yasaka fararen kaya marasa nauyi masu laushi na bacci.
Waya ya danna tana ringing amma har yanzu ba'a ɗauka ba,tun kwana uku da zuwansa yagama abinda ya kawoshi,da gangan yaki komawa saboda abinda zaije ya tarar,musamman daya samu suke waya da Jaleelah,koyaushe suna maƙale suna zubawa juna soyayyah.
Wannan lokacin yayiwa Jabeer daɗi da har bayason su shige daga cikin rayuwarsa.
Yana cikin saƙar zuci Jaleelah ta ɗaga ƙirnnasa.
Da sauri yakai kunnensa domin kar yayi Missing zazzaƙar muryarta,aikuwa kaiwarsa keda wuyah yayi kicibis da itah.
"Assalamu alaika masoyina"
Saida ya lumshe ido na tsawon lokaci kafin ya amsa sallamar
"Wa'alaikissalam Sarauniyar zuciyar Jabeer"
Daga nan suka cigaba da hirarsu kaman kodayaushe,maganar aure ta sako masa akan Mahaifinta yace ya turo.
"Yah Jabeer idan har dagaske sona kake babana yace katuro ayi maganar aurenmu,domin na faɗamasa cewar muna soyayya dakai,kuma ya yaba da abin har yayi bincike akan ka"
"Uhhh to shikenan karki,nafiki zaƙuwa wajen ganin na mallakeki a matsayin matata,bakisan yanda nake jinki a cikin zuciyata bane shiyasa,ina mai miki alkawarin cewar dana koma gida zan samu abba da maganar,inshaaallah aurenmu bazai wuce nan da nan Wata uku ba"
"Dama nasan bazaka ƙi amincewa ba,kaman yanda kake son kasancewa dani nima a wajennawa hakan take,ina sonka sosai,ka burgeni matuƙa daka fara zuwaga iyayena kafin a tunkareni,hakan maxa dayawa suka kasa aikatawa"
"Amma nafaɗamiki fah cewar inada mata biyu,kina ganin hakan babu matsala"
"Babu wata matsala nidai a wajena,dan haka kada ka damu,nasan kanada damar riƙesune shiyasa ka auresu. Allah da kansa yahalattawa na miji auren mata huɗu,idan har zai iya adalci a tsakanin su,dan haka indai zakayi adalci a tsakanin mu shikenan"
Da farko Jabeer baiji daɗin yanda bata nuna kishi ba,duk da kuwa hakan yake fata,amma kuma dayaji bayaninta sai bai kawo komai a ransa ba.
Hirar su suka cigaba dayi har lokacin da zuciyoyinsu suka raya musu su bari.
Wayar ta ce tayi ƙara da misalin ƙarfe takwas na safe,juyawa tayi tana lalumar haidar,bata jishiba dan haka tayi tunanin ko Hilyaan ce ta ɗaukeshi.
Wayar ta ɗauka tareda zame bargon dake jikinta kaɗan.
"Yadai khamees da safennan?"
"Hmm yanzu ne safen koh,koda yake ashe amarya ce fah.
Binciken danakeyi ya kammala,Gen abdu manga shije na biyu a kason Share mai yawa na companyn mijinki, meeting ɗin daya gudana ma kwana uku da suka gabata yaje wajen,wanda inada tabbacin akwai abinda yake saƙawa"
"So yake ya ƙwace companyn daga hannun Jabeer,da farko yayi shurune saboda in Lubnah ta haifi yara one day sune akai,amma yanzu ya sanja plan saboda ƴar sa bata haihuwa dagaske kenan........sai kuma me,kayi nasarar cire na'urar jikinka?"
"Uhmm nayi nasara,nawa tana hannun dama ne,nikuma ina checking na hagun"
"To yayi kyau"
"Uhm tun kwana uku baya aka gama meeting ɗin,amm mijinki bai dawo ba sai yau,bazaki bincika mai yake ba a wannan lokacin"
"Wannan kuma kofin shayinsa ne,ruwansa yasha ruwan tea ko kuma yasaka madara,baya cikin lissafina a yanzu,bari zanyi plan da wanne zan fara ƳAR KO UBAN.inbaka da abin faɗa zan koma bacci"
"Kutt bazaki fara shirye shiryen taryarsa ba bacci zaki......"
Tun kafin ya gama Bombee takashe wayar tayi jifa da iya,tareda maida pillow ta kwanta.
Abinci na gani na musamman Lubnah ta jaɗawa Jabeer domin taryarsa.
Yana shigowa mamaki ne yakamashi ganin a side ɗinsa tahaɗamasa girkin,taji kwalliya cikin wata doguwar riga ja,ba lafi tayi mata kyau sosai.
Murmushi tayi masa maiɗan ɗauke da alamar takaici,saurin gusar dashi tayi tareda takowa inda yake.
"Sannu da dawowa farincikin ran Lubnah,nasan dama bazakake kaga halin danake ciki ba,side ɗinka zaka fara shigowa,shiyasa nayi komai a nan wajen"
Alama ya nuna narashin kyautawarsa akan hakan,atleast tunda zamansa take,yakamata ya je ya ganta tukunna.
"Kiyi haƙuri luby na gajine shiyasa ban je wajenki ba,amma nayi niyyar idan nagama shiryawa zan shiga ai"
Karya kai tayi irinna ƴan duniya kafin tagyara annunrin fuskarta.
"Shikenan na karbi uxurinka,yanzu tunda ka gani muje na tayaka shiryawa ko?"
"Bayyi mata musu ba,dan yanada buƙatar hakan sosai. Ita ta taimaka masa ya cire kayansa,kana ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗan zafi,babu yadda bayyi ta ita ba kan tazo ta tayashi wankan amma taƙi.
Abin tsoronta ɗaya shine kada taganshi yana wanka zuciyarta ta jata ta aikata abinda boka ya mata gargaɗi akai,na kada ta kuskura ta bashi kanta har sai ta gama wata ukunnan tukunna chass.
Taya fito daga wanka ma bata ɗakin,tana can wajen shirya masa abinci,wanda shikansa yasan ƴan aikine sukayi,ba itace ta dafaba.
Duk yadda taso nuna kisisinarta kan yaci abincin kaɗan yaci ya tashi.
Sashen su Hajiya zeenah ya nufa domin ya gaishesu,A wajen Alh aliyu mahaifinsa yafi tsayawa suna ta hira,daga baya ya ɗau mota ya nufi wajen Khaleel,zai rakashi gidansu Jaleelah.
A hanyar zuwa gidan ya tsaya yayi siyayya mai matuƙar yawa kafin suka nufi gidan,dama tasan ta isowarsa.
Sauƙa ta musamman akayi musu,basu Jabeer ne suka baro anguwar su Jaleelah ba sai bayan isha,salloli ma duk a unguwar sukayi.
Shikansa Khaleel yana jinjina irin soyayyar da Jabeer yake yiwa Jaleelah.
Lokacin daya shigo sashen Lubnah tana kwance da waya a hannunta,ta saka kayan bacci tana kan gado.
Ɗan zabura tayi tareda ɗagowa takalli Jabeer ɗin,dan gabaɗaya bataji shigowarsa ba sam.
"Uhmm kina wannan chatting ɗin inata sallama koh"
Cikin kasalalliyar murya mai cikeda alamar gajiya da buƙata yayi maganar.
Gaban Lubnah ne ya bada sautin dumm kaman ganga,ganin Jabeer da kayan bacci,dan tasan mai yakawo shi.
Matsowa yayi inda take da niyyar kama hannunta,saurin matsawa tayi kaman taga aljani.
Wanda hakan yasashi yin mamaki matuƙa.
"Lubnah lafiyan ki kuwa?"
"Iyee na'am dama .....dama ina period ne"
"Hmmm period a wannan lokacin,har yanzu bansan yaushe kike period ba,idan akwai abinda yafaru ko wata matsala ki faɗamin ina jinki?"
Yana cewa matsala wata idea tazo kanta,saurin saitawa tayi tareda yin magana cikin sigar tausayi,yanda tasan zai yarda da ita.
"Kayi haƙuri dama banason sanar dakaine kada kaji babu daɗi,na kamu da ciwon sanyine a tafiyar dakayi,to shine dana je wajen maganin gargajiya suka bani wani nayi amfani dashi na tsawon wata uku,amma a wannan tsawon lokacin kada na bari ka kusanceni.
Kayi haƙuri ni kaina da farko nayi tunanin hakan zaisa na shiga haƙƙinka dan haka.........."
"Ahah karki shiga damuwa,lalurine yana iya hawa kam kowa,indai wannan ne babu matsala,Allah ya baki Lafiya,Yakuma kaimu har sai kim warke ɗin.
Ni barina tafi side ɗina toh"
Yaƙarisa maganar yana sumbatar goshinta.
Tashi yayi ya nufi ƙofah,har yayi nisa ya juyo tareda cewa,
"Amma bakya ganin bazamuje kiga likita ba gobe?"
"Ahah sunce kada nayi amfani dana likita har sai na gama tukunna"
Ohk"....yafaɗa cikin sanyin gwiwa,a yanda yake ji yayi zaton zata taimakeshi da wata hanyar,amma sai tama koma kan wayarta hankalin kwance,hakanne yasa shima yabar ɗakin ya nufi nasa sashen.
Da safe bai samu tashi da wuri ba,kasancewar yanda yakai dare bayyi bacci ba yana fama da laluri.
Sai wajen ƙarfe goma ya shirya ya fito.
Da Lubnah yauma yasake yin karo tayi kwalliya cikin lace tana tsaye a bakin dining,wanda yake cikeda kayan karin kumallo.
Murmushi tayi masa tareda tambayar ya tashi lafiyah,shidai a mamaki ya amsa,dan bai saba ganin hakan ba.
Surutu take tayi masa yana cin abincin har ya gama tukunna.
Yatashi zai tafi sai yaji tace.
"Amm Honey Dama magana nakeso muyi mai muhimmanci"
Komawa yayi yazauna domin jin mai zataje,dama yayi tunanin hakan,domin ruwa baya tsami banza.
"Shin idan kanada mata guda biyu,waye yakamata yafara zabar abu a cikinmu?"
"Kece yakamata ki fara zaba"
"To amma meyasa wancar matar taka tafara zaban wajen zama a new side kafin ni"
"Uhm wacce matar kenan"
Dan shi har cikin ransa yamanta wacce take magana akai,saida ya tuna da auren da Hajiya zeenah tayi masa kafin abi ya faɗo cikin ransa.
"Ohh nunamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login