Showing 78001 words to 81000 words out of 134612 words
zakayi ma kaman baka san wa nake nufiba,taje ta ɗauki side ɗin dani naji shinake so a wajen,dan haka yau ka faɗamata tabar cikinsa ta ɗauki wani,dan wannan nakeso"
"Ina side huɗune,ki dau wani mana a wajen,kowanne ma naga yana da ƙofa ta cikin side ɗina,babu wanda yake gefe,dukka a round suke a wajen"
"Nidai shinake so,domin yafi kusada lambun shaƙatawa,iskarsa ma tafi ta sauran daɗi,kawai ni yafimin shi nake so"
"Uhm kin faye fitina Lubnah keba yarinya ba,wannan side ɗin ba yafi gefe fiyeda sauran,a haka kike sonsa?"
Hanyar ƙofa ta nufa zata fita yayi saurin riƙota.
"Dama babu wanda ke sona a gidanan,a wajenka kaɗai nake samun sukuni,kaima kuma yanzu karamin abu amma ka kasa yimin shi,shikenan to naga matsayina"
"Kibar wannan zancen,indai sashen ne muje yanzu na fitarta a wajen ki shiga,shikenan?"
Goge hawayen Lubnah tayi tareda jijjiga kai,kana ta ƙanƙame hannunsa daya saka a cikinta.
Makullin motarsa ya ɗauka tabishi a baya tana murmushin cin nasara,ba koranta ne batada hanyar yi ba,tafison tasaka mijinnata datake taƙama dashi ya koreta da kansa,taga yaya zatayi.
Shiga motar itama tayi yaja zuwa sabon wajen,a cikin ƙanƙanin lokaci suka kai gurin.
Lokacin sha ɗaya tayi rana tafito sosai.
Itace ta fara fitowa daga motar ta ƙwanƙwasa kofar kafin ma ya kashe motar.
Hilyaan dake jijjiga haidar a hannunta taji ana buga ƙofar.
"Ohh wai har yanzu anty maryam baki gama bane,wasu sunzo nemanki a waje to,ga haidar yana ta kuka shima."
Hanyyar ƙofar ta nufa tareda buɗe musu ƙofar.
Lokacin data buɗe ƙofar da Jabeer suka haɗa ido,wanda zuwansa wajen kenan ya kashe mota.
Kallo ɗaya tayi musu tareda cewa.
"Ku shigo"
Binta sukayi a baya har tsakiyar falon,wajen zama ta nuna musu tareda dan ɗaga muryarta.
"Anty maryam serious yanzu kam baƙi kikayi,gashi nace miki yaronnan kuka yake tayi"
Muryarta suka jiyo tun kafin tashigo falon.
"Ohhh baby yana missing mommy,Hilyaan ki ɗan bashi ruwa mana,ba yunwa yakeji ba,yaushe ma na zauna yasha"
Shigowa falon tayi ta dawo daga backyard ɗin gidan,tana goge gumin dayake fuskarta da wani ƙaramin towel.
"Kayan workout ne a jikinta baƙaƙe,riga iya rabin ciki,sai kuma wando iyah gwiwa,gashinta kuma ta kama shi da ribbon irin kayan,shima yana dauke da adon fararen star dake jikin kayan.
Kayan sun matseta,sosai fittet ɗin farar fatarta ya bayyana a ciki,ga kuma gumi dayake bin jikinnata.
Kallon mamaki tabi su Lubnah dashi wanda suke tsaye. Yayinda suma suke aikamata nasu kallon mamakin,musamman ma Jabeer dashi ganinta biyu dashi kenan.
Basar da kallon dasuke mata tayi tareda dan juya blue idonta.
"Ohh baƙi mukayi haka,sannunku da zuwa,saidai naga baku zauna ba"
"Hmmmm dama tun kallon danayi miki ranar a bakin gidannan,da kuma kallon danayimiki da daddare,nasan ke ba ƙaramar tatacciyar ƴar bariki bace. Ba kince ranar sai abinda kika ga dama zayyi ba,harda wani ranann nazo nemansa kika ce bazai fitoba,inna isa nima nasaka shi yayi yanda nakeso in yana wajena,to yanzu gashi na sakashi,korarki yazo yi a wannan side ɗin yanzunnan,saboda ni matarsa uwargidansa wannan side ɗin nakeso"
Zaro ido Jabeer yayi tareda kallon Bombee,jin abinda Lubnah take faɗa wanda bashida masaniya akan sa,ko kuma yaushe akayi shi. Ita ɗinma shi takalla tareda yimasa kallon basai ya sani ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci tajuye zuwa nata salon.
Hannu tasaka a kunkuminta tayi wani malƙwaɗa tareda turo ƙirji gaba kaɗan. Yanda tayi sigar ko ƙwararriyar ƴar bariki albarka,musamman kuma data ƙara dawani rishe ido.
Lokaci ɗayah Jabeer yaji kamar wutar lantarki ta huda daga kansa har ƙarkashin ƙafarsa.
Lanƙwasa harshe tayi tareda yin taku biyu zuwa gaban Lubnah daff,harsun jin hucin juna,bakinta takai kan kunneta tareda yimata magana yanda babu wanda zaiji,tanayin magana idonta yana kan Jabeer wanda takafe idonsa a cikin nata,ta yanda bashida ikon ɗaukewa.
Saurin matsawa tayi da baya tana jijjiga kai.
"Wlh baki isa ba,ina ina kinyi kaɗan"
"Nayi kaɗan,to faɗawa mijinnaki kiji idan ƙarya ne,in kuma bazaki faɗamasa ba to yana nuna kin yarda dabinda na faɗa kenan.
Shin ya shiryah korata na bar shashennan?"
Harara ta bankawa Bombee tareda shikansa Jabeer ɗin,kana ta bangajeshi tabar shi a tsaye anan kaman mutum mutumi.
Bayan ta tafi idonsa ya maida kam Bombee tareda tunanin shin mai ta faɗawa Lubnah daya sanja ra'ayinta haka.
Itakuwa tana ganin Lubnah ta tafi ta maida ainihin fuskarta ta Bombee kaman ba itace take rausaya ba.
Samun waje tayi ta zauna tareda karbar haidar a wajen Hilyaan.
Nono tacire tasaka masa a baki nan da nan kuwa yayi shuru,faruwar hakan duk akan idon Jabeer,da sauri ya runtse idonsa ya bar falon bayan idonsa yayi tozali da abinda bai kamata ya ganiba,wanda yake da tabbacin yanda ƙwaƙwalwarsa tayi record ɗin hoton,ba lallai ya bace nan kusa ba,musamman dayake matse dama a kwanannan,Lubnah ta baro masa ruwa.
A haka yabar wajen kansa cikeda tambayoyi fall na mai yake faruwa,tukunna ma shin wannan amaryar tasa wacece ita?...
Bayan sun tafi kallon alamar tambaya Hilyaan ta jefi Bombee dashi,
"Anty maryam me yake faruwa mai kika faɗamata haka,kuma shikansa mutuminnaki naga da alama so kike ki jurashi a tarko,shin kin sanja plan ɗinki ne"
"Uhmm kinada tambaya Hilyaan,so nake kawai naga ya zayyi,sannan daga kallon danayi masa kamar Lubnah bata bashi lokacinta yanda yadace,duk wacce take son cafkar zuciyarsa zata samu a yanzu cikin sauƙi.
Magana kawai na faɗa mata,kuma da alama tayi tasiri a ranta fiyeda abinda kowa zai faɗamata."
Lokacin data kai bakinta wajen kunnen Lubnah,ƙankance murya tayi tareda cewa.
"Wai har yanzu baki ɗago lamarin bane uwargidan angona,a tunaninki idan kika koreni anan bazai so hakan ba,zamu baje lokacin mu tareda shi a sashena,sannan kuma idan kina nan ma duk lokacin dayake wajenki,zan yi irin wanann shigar nazo wajennan da suna motsa jiki,kaman yanzu daya kafeni da ido,kina ganin zaki iya jan hankalin sa ya ɗauke kannnasa daga gareni uhm?"
Juyawa Lubnah tayi ta kalli idon Jabeer wanda yake tsaye kyam a cikin na Bombee,take wani ƙululun baƙin ciki ya shigeta,ganin tafara samun galaba akan ta yasa ta ƙara dacewar.
"Shikenan zan koma sashe na gaba wanda yake kusada shi,sannan zan dunga zuwa nan ina motsa jiki a bayan sashenki,wazai ƙi lokaci guda biyu na mijinsa. Hakan zai mana daɗi nida shi,in kuma baki yarda ba ki tambayeshi yanzu kiji,shin idan nazo motsa jikin bazai tayani muyi ba ranar dayake wajenki uhm"
Dariyah Hilyaan ta fashe da ita dataji abinda Bombee tafaɗawa Lubnah.
"Uhm na gane,wato zakiyi amfanine da kishin dayake mata ki wanata a haka koh?"
"Yess haka abin yake,tunda zata dawo nan ,dole shima nasan zai dawo nan,abin zaifi tafiya yanda nakeso"
Takarisa maganar tareda dariyar da ita kaɗai tasan ma'anarta.
Tuƙin tuwo take magriba ta gabato,rana tayi ja a yamma.
Murya taji kaman ana ƙiranta a bayanta,bata kawo komai a ranta ba tacigaba da tukinta,domin tasamu ta gama da wuri,tsayawa tayi ta juyah muciyar tareda zare ido.
"Laariiiiii nasan kinji kirana,amma kike so ki juya bayanki daga gareshi,maza kizo ga kirana yanzunnan,ranar wanka tazo ta,duk yadda kika so da boye cibi a yau bazai boyu ba,inaso ki zo kiga mijin Innayi a yau"
Jikin laari rawa ya kama kaman mazari,jijjiga kai tafarayi hawayen takaici na zuba mata,amma tasan a gaba jeji baya tsiyaki take,babu hanyar dazata bi wajen bullewa daga halin ƙaƙani kayan data tsinci kanta ciki,wanda daman tasan da zuwansa tun ran gini da kuma ranar zane.
Hnayar dakinnata ta nufah tana jan kafa kaman ƙwai ya fashe mata a ciki.
Cikin sanyin jiki ta dauki tsinken turaren ta kunna,yana bugar madubin kuwa Zilliyah ta bayyana a jiki tana dariyar mugunta.
"Laari kenan,nayi zaton ai bazaki amsa kirana ba tunda nayimiki rana?"
"Ina na isa uwar matsafa mai daraja,gani gabanki na miƙa wuyah"
Innayi wacce sai yanzu tashigo gidan ta dawo daga gidan ƙawarta,duk yawancin ƙawayenta anyi aurensu,itace kawai tasaura a gida,ko kare bai taba shinshinarta ballanta na kuma murum yace yana so.
Abin ya daurewa mutane da dama kai,ganin gata kyakykyawa dakuma ilimi,batada makusa ko kaɗan,amma yanzu ko magana mutum bayaso mlm Ahmadu yayi masa akan Innayi,saboda yana tsoron kada yace yabashi ita.
Tukunya ta gani akan wuta da tuwo a buɗe ba a gama tuki ba,waigawa take ko zata ga inna laari amma bata ganta ba,ɗakinta ta nufah,har zata shiga saikum taja ta tsaya jin tana magana da,wata mata da bata san muryarta ba.
Abinda taji an faɗane yasaka gwiwarta yin sanyi tareda zubewa a wajen,ko kaɗa kunnuwanta sun kasa gasgata mata abinda take jiyowa.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________
Page 🖤19••20🖤
"Kindaɗe kina min magana akan auren ƴarki to ranar tazo,inaso ki shiryata tsaff ranar gobe da daddare zan turo a dauketa."
"Ammma shin shugaba zilliyah ina Zaki kaita kenan,dan Allah ki barmin ƴata a gabana,ita kaɗai taragemin wacce nake da"
"Yimin shuru laari,har yanzu baki san dalilin dayasa bata samu miji ba ,saboda na hana kowa ya kalleta da fuskar so,ita ɗin matar ɗanace,tunda aka haifeta ya nuna yana sonta daya ga hotonta,itace tayi daidai da wacce zata haifamin jikan dazai gajeni,dan haka zaman ta cikin mutane da kuma a gari ya ƙare,saina daji tareda aljanu,wanda nan gaba zasu kasance sune ahalinta"
Hawayene yake zubuwo a fuskar laari,lokacin dataji zilliyah tana zayyanomata Kaddarar data zabawa yar tata,wanda batada ikon magana akai ballantana kuma hanawa.
"Shikenan shugaba zanyi yanda kikace,indai ina tareda ke nasan bazan tagayyaraba,babban abin alfaharina ne na haɗa zuri'ah dake Shugaba,amma zan iya ganin surukinnawa ko a hoto,kwanaki naji kince bashida rabin fuska,sakamakon yanda wani aljani yakai masa farmaki"
"Eh bashida rabin fuska,shiyasa ma baya fitowa ga halittu suna kallonsa,ko kema bazaki ganshi ba,iyah matarsa ce zata ganshi idan an kaita gareshi,karki ji wai dan ya nakasa kiyi zagon bashida amfani,kasancewar bazai iya gadona ba yasan na yanke hukuncin samun jika wanda zai gajeni,dan haka ki yi gaggawar cika umarnin dana baki.
Ganan magani a cikin kasko,kiyi mata turare dashi,ta hakane idan na turo aljanun zasu samu damar ganinta a duniyar mutane su ɗakkomin itah"
Tana gama fadin hakan ta bace batt a jikin madubin kaman bata wanzu ba a jiki.
A bangaren Innayi kuwa tana gama jin abinda Aljanar tace taja ƙafafunta batareda sun ji ta ba tabar wajen.
Ɗakin Danejo ta nufah,tana zaune kamar kullum akan kujera ta saka gabanta gabas.
Tsugunnawa tayi a gabanta tareda kama hannayenta dukka biyun ta riƙe.
"Kiyi hakuri Inna Danejo,ki yafemin abinda nayi miki tsawon rayuwata,wlh dukka inna ce take sakani nayiwa Addah Bombee,nasan cewar itace tayimiki haka,kuma tayi sanadiyyar zaman Addah Bombee haka,amma banyi zaton abinnata har yakai haka ba.
Duk da cewar na kasance mai son kai,duk abinda take ban taba fitowa na sanarwa da kowa ba,saida a yau danaji tana da niyyar hallakani tukunna,amma duk da haka ki amincemin dama taƙarahe wajen gyara kuskurena,kodah kuwa zan mutu a hanyar hakan.
"Inna Danejo inason zan gudu daga gidan ubana,saboda abinda innata zata min,saidai bazan zama mai son zuciya ba a karo na biyu,inason na tafi tareda ke cikin duniyah na nemo Addah Bombee na kaiki gareta,daga nan saina nufi wani wajen daban.
Ta hakanne kawai zan iya gyara kaɗan daga abinda na aikata,Ki amincemin hakan kibini mutafi inna Danejo"
Innayi taƙarisa maganar tana sakin kuka tareda matse hannun Danejo a nata hannun.
Jijjiga mata kai tafarayi tareda ƙoƙarin zare hannunta daga nata,alamar bazata bita ba kenan.
"Shikenan tunda bazaki amince ki bini ba,tunda har bazaki tsallake taki wahalar ba meyasa zan tsallake tawa wanda bata ma zo ba,nayi alƙawarin bazan tafi batareda ke ba,dan haka zan zauna inna ta auramin ɗan matsafiyarta,idan na mutu ta sanadiyyar hakan kiyafemin abinda nayimiki a baya"
Tashi tayi zata bar ɗakin Danejo ta riƙo hannun ta.
Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalleta.
Hannunta ta miƙa a gefen Kujerar ta,tafito da wata farar takarda daga ciki. Hannun Innayin ta kama ta saka mata ita a ciki.
Mamaki ne ya cikata amma dai sai ta buɗe takardar.
"Addaress inda nake aure inna ,14 way JAAN ESTATE Abuja"
"Inna Danejo wannan address ɗin na inda Bombee takene?"
Saurin jijjiga mata kai tayi alamar eh shine,dunƙuke takardar tayi tareda cewa,shikenan na fahimta inna,duk da cewar a bansan yanda zan kaiki ga garin abuja ba a yanzu,amma zanyi iyah ƙoƙarina wajen kwatantawa. Barina ce wajen Alhaji labaran na aro kuɗi da sunan Inna,idan muka tafi nasan dole zata biya kuɗin."
Jijjiga kai nan ma Danejo tayi tareda zaro wata jaka ta miƙawa Innayin.
Kuɗine a cikin sabbi masu dumbin yawa,wanda tana tabbacin Bombee ce ta bata su ba kowa ba.
"Da ban so karbar kuɗinki ba,amma tunda na kula bakyaso na ranto kuɗin wani to zamuyi amfani da wannan kuɗin na kaiki wajen ta Da yardar Allah,abin ya isa haka.
Yanzu bari naje na nemo motar daxata fita da sassafe,saimu buyah a daji, su samemu a wajen su ɗaukemu"
Tana gama faɗin hakan tafita daga ɗakin Inna Danejo zuwa waje.
A Lokacin ana ta kiran sallahr magariba.
Sai bayan isha tukunna ta dawo gidan,kicibis sukayi da Mlm Ahmadu ya dawo daga masallaci.
Faɗa yafarayi mata a kan ina taje bata dawo gida ba har dare yayi.
Inna laari tana tsaye da buta zatayi alwala suka shigo mlm Ahmadu yanata faɗa.
"Baba kayi haƙuri,dama na dawo daga islamiyya ne shine na tsayah gidan Addah Ramma yin hadda,to da tsayi sosai shiyasa bamu gama da wuri ba"
"To naji,koma dai menene ki daina kawai dare a wajen irin haka kinji?"
"Eh baba zan kiyaye"
Hakan da tayi shiya hana inna laari zarginta dajin abinda suke,wanda hakan yabata damar yin shirin ta a cikin dare batareda kowa yasani ba.
Bata ɗebi kayan su dayawa ba,kaya kala bibbiyu ta saka musu a jaka,sai kuma wanda yake jikinsu.
Wajen takai kayan wajen drivenr dayake shiga cikin Jalingo,su kuma zasu fita da daddare sai ya samesu a can gaba.
Can cikin dare da misalin ƙarfe 1:00am Innayi ta buɗe ɗakinta siƙaf ta shiga ɗakin inna Danejo.
Bubbuga kafaɗar ta tayi ta tashi,dan har ta fara bacci ma.
Riketa tayi suka fito daga ɗakin,suna tafiyah a hankali har suka samu damar fita daga cikin gidan.
Duk da Inna Danejo bata gani,amma a tare suka juya suka kalli gidan,ita gidan ubanta da aka haifeta a ciki,yayinda ita kuma yake gidan mijinta,wanda aka kawota tun batasan mai yake mata ciwo ba,gashi yau zata barshi bada an saketa ba,saidan neman mafita,dan tasan idan har tabi zabin zuciyarta taƙi fita kaman yanda tayi alƙawari,toh rayuwar innayi kuma zata shiga cikin hadari wannan dalilinne yasa ta amince zata bita.
Juyawa suka yi tareda barin gidan,dukkansu badan zuciyoyinsu na so ba,saidan fitinar da take gidan wato inna laari.
Tafiya suke Innayi tana haska musu hanya har saida suka fita daga cikin garin.
Kafin asuba tayi sunyi tafiya mai nisa har zuwa inda Sukayi da drivern zai samesu.
Ruwa suka ɗiba a wani rafi dake wajen sukayi sallah,kafin gari yayi haske ma har drivern ya iso wajen,kasancewar dama fitar wuri yakeyi.
Fitowa yayi ya taimakawa inna Danejo ta shiga motar,saida ya tabbatar sun zauna kafin ya ja suka bar cikin garin tareda saita hanyar Jalingo,inda zasu samu motar Abujan su shiga.
A bangaren Mlm Ahmadu kuwa asuba tanayi ya nufi ɗakin Innayi domin ya kwanƙwasa mata tafito tayi sallah,jin yayi bugu har uku bata motsaba yasa yayi zaton ko tana Hutun wata ne,dan haka yayi tafiyarsa masallaci.
Har 10 tayi shuru innayi bata fito ba,inna laari harta haɗa abin karyawa,ga wanke wanke ƙudaje nata bi,kuma so take dama tayi mata turaren yanzu,kafin zuwa dare ya bi jikinta.
Hanyar ɗakinnata ta nufa tana magana.
"Wai nikam innayi wanne irin bacci kikene haka,ai kamata zuwa yanzu kam kin tashi kin fito koh kuma ga........."
Maganar tace ta katse lokacin datayi arba da ɗakin innayi tace ɗaukeni a hankali,dan babu ita babu alamunta a ɗakin,sai wata fara takarda a kan gadon.
Fitt ta fito daga ɗakin tana salallami kaman an jeho ta,turakar mlm Ahmadu ta nufah tana ihu .
"Mlm maza fito innayi ta bata banganta ba,da alama bata kwana a gida ba,babu ita babu alamunta sai wannan takardar,yau ni laari naga takaina"
Duk ihun da inna laari take bayyi magana ba,saima takardar hannunta daya karba ya buɗe.
"Aslm baba kayi haƙuri ka bawa inna ma haƙuri.
Amma bazan iya zama ba saboda wani dalili wanda bazan faɗeshi a yanzu ba sai nan gaba idan har na rayu.
Na tafi nida inna Danejo zan kaita wajen Yar ta addah Bombee,ta hakanne kaɗai zan rage laifin dana aikata"
Ninke takardar yayi tareda nufar ɗakin danejon,wanda itama inna laari tabishi kaman jela.
Kaman yanda ta faɗa a takardar kam Danejo ma bata nan,ya tabbata sun tafi tare kenan.
Sauƙe ajiyar zuciya mlm Ahmadu yayi,yarasa ma mai zaice,banda Inna laari wanda tasaka hannu a ka tana ihu,yagagara cemata komai.
Fita waje yayi ko za'a samu mafita,domin zaman sa cikin gidan babu abinda zai haifar,tunani ne fall a ransa,musamman daya tuna shekaru dasuka wuce a baya,Lokacin da ƴaƴan sa suke ƙanana,yayi rayuwar farincikin da bai taba zaton zayyi ta ba,a yau kuma sai gashi ya rasa komai na farincikinsa. Tabbas yasan hakan jarrabawa ce daga Allah,shiyasa ma yake fatan Allah ya bashi ikon cin ta.
A wajen inna laari kuwa ba kukan Batan ƴata bane yafi damunta,kukan wanne irin tashin hankali zata fuskanta ne a wajen ZILIYYAH,sannan kuma ga Danejo ma ta tafi,idan Bombee tayi nasarar samunsu,tasan idan suka sake gamuwa saita Allah,wai Jaka a ɗaki.
Saboda gudun da Drivern yake kuma ya kware sosai,da rana tsaka suka isa Tasha a cikin jalingo ina zasu hau motar taraba.
Masa innayi a siya musu a wajen da ruwa a cikin kuɗin suka ci.
Kana suka yi sallah tareda samun dan hutu,kafin a gama yin lodi a motar dazasu shigan.
"Inna Danejo kin gaji koh,kiyi hakuri yanzu zamu shiga mota,inshaaallah muna isa abuja sai mu bawa masu mota address ɗin su kaimu,da sannu nasan zata nema miki magani ki warke inna"
Tana jin abinda innayi takecewa,amma batace komai ba,dan itama har ga allah tayi kewar ƴar tata sosai,abin tsorom shine bata san a wanne yanayi zata sameta ba ne.
Suna nan zaune sukaji ana ƙiran sunansu,innayi ce ta taimaka mata ta tashi suka nufo motar,dan tun ɗazu suka biya kuɗin motarsu dama.
Ƙara nausawa sukayi kan hanya,tareda kama niyyar barin nahiyar su ta taraba.
Tafiya ce aka farata kaman ta yada dan shege,sannan abinka da basabunba tuni bacci mai nauyi ya ɗebesu a motar.
Basu suka buɗe idanuwansu ba saida muryar yaron motar ta jiyarci kunnensu.
"Ke ƴan mata,iya maza tashi zamu kai mota wajen ajiya mu kulleta"
Firgit innayi tayi takalli yanda gari yayi