Showing 30001 words to 33000 words out of 134612 words
sandal da safa,sai goge kayan take da handkerchiep kaman gaske,kayan kuwa blue Burberry ne yayi mata kyau sosai.
A bakin ƙofar gida ta hadu da mlm Ahmadu yana zaune a majalisar dattijai,nufarsa tayi tana bubbuɗawa,kana ganinta kasan anyi marar ji,ga kyau irinna maciji.
Sallama tayi a wajen tareda tsugunnawa a gavan su.
"Baba zan tafi jarabawar,a bani kuɗin cin abinci,dan sai yamma nadawo"
"To shikenan kokefah uwata,hakan ai yanada kyau sosai,maza ki rubuta mai kyau saboda kiciyo makaranta mai kyau,nasanki da ƙoƙari dama"
Ɗari biyar ya ɗauko a aljihunsa ya damƙawa Bombee,tasa hannu biyu ta karba tareda yin godiya,kafin ta juya ta tafi.
"Ahh ikon Allah anya kuwa itace?"
"Mlm Audu baban su muruje yafaɗa yana jijjiga kai"
"Ita ce mana,girma ne yafara zuwa an fara hankali"
Mlm Ahmadu yafaɗa ɗauke da murmushi akan fuskarsa,saboda jin daɗin yadda Bombee ta nuna hankalin nata a gaban dattijan. Addu'a yayi a ransa akan Allah yasa tacigaba a haka.
A bangaren mutuniyar kuwa tana shan kwanar gidannsu maimakon ta ɗau hanyar gidansu sai tayi hanyar jeji.
A hanya tashiga wani gini ta sanja kaya,daganan kuma tayi cikin jejin kanta tsaye.
Tadaɗe tana tafiyah a cikin jejin kafin ta iso wani gida a dokar jejin.
Hayaƙin dayake tashine mutum zai gane cewar akwai mutum a ciki.
Sallama tayi a bakim ƙofar gidan,muryar wata mata ce ta amsa mata dattijuwa.
"Bombee kece da hantsinnan,shugabannki baya nan yashiga jeji ɗazu"
"Gabas yayi ko yamma?"
"Ahah Bombee bazaki bishi ba ke kaɗai kina mace,kinfi ni sanin bayason kina shiga cikin dajinnan ke kaɗai batareda shi ba"
"Haba Inno har yanzu na,babu indan bansani ba a jejinnan,bariki gani"
Tun kafin wacce aka ƙira da inno tace wani abu Bombee ta nausa cikin jejin da gudu.
Gudu takeyi ta hanyar gabas maso kudu a cikin jejin,daga yanda take gudun tana tsallake itatuwan da suke kan hanya mutum zai tabbatar tasan takan hanyar gaba da baya.
Catt taja ta tsayah tanacikin gudun,kaman wanda wani yabata umarnin hakan.
Shuru tayi na wasu ƴan mintina tareda rufe idonta na ɗan wani lokaci.
Sunkuyawa tayi har saida ta fadi a ƙasa,mashin dayazo ta samanta kuma yah caki a jikin bishiyar gefenta.
Tashi tayi tareda yamutsa fuska tana duba bayan rigarta da lakar wajen ta 'bata mata.
"Haba shugaba,kasa na bata rigata a cikin wajennan"
Wani mutum ne mai tsantsan jiki,farin bafulatani ne,amma kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,duk cewa shekaru sun fara nunawa akan fuskarsa.
Dariya yakeyi tareda tafa hannyensa alamar jinjinawa.
"Da kyau ashedai bakya training a banza,menene yasa kika biyoni cikin daji,sannan ya akayi kikasan ina nan"
"Uhm na karbo kuɗin siyan nima kwari da bakata,tsawon lokaci ina tara kudi yau nagama tarawa.....tabb har yanzu bansan inda zan sameka ba,yau fah litinin,nasan dama tanan zaka iyo ai"
"Hmmm da alama ba iya idonki ne yafina sauran mutane fah harda jinki da kuma tunaninki,kinyi ƙoƙari dakika kaucewa harina,ya akayi kika lallami Babanki har ya baki kuɗinnan"
"Uhm bani yayi na siyah kayan kwalliyah,shine na taho nan"
"Meyasa bakya son yin abinda iyayenki suka ce toh,kullum ina faɗamiki kinada lokacin sanja ra'ayi akan bin hanyata,saboda ke macece ba namijiba"
Shuru Bombee tayi baya amsa masa ba,shima dama yasan bazatayi maganar ba,duk sanda yayi mata maganar tasanja ra'ayi.
Abu ɗayane yasa bai koreta ba shine,yasan idan ya korata gida ma bazata haƙura ba,zatabi wata hanyar ne inda babu mai kallonta ballantana ya kulada itah. Shikuma haka kawai yake jinta a ransa kaman ƴar sa wacce shi Allah bai bashi ba.
______****______***_____
Tun ranar da jarabawar su Bombee ta fito yake ta jelen wajen dubawa jarrabawar sa.
A zuwansa na ukune gidan headmastern,ganin abin yazama haka ya faɗamasa gaskiyar abinda yake faruwa.
"Mlm Ahmadu nasan kanason maryam (Bombee)tayi jarrabawa domin tayi karatu,amma fah ita ba karatunne a ranta ba,dan dama haka mukayi ta fama da ita lokacin tana gabanmu,tayin wani lokacin sati ma zatazo makarantar ba,duk lokacin data zo kuwa ba iya ɗalibai ba,mukammu saita caja mana ƙwaƙwalwa.
Badan mutuncinka ba dama bazata gama a makarantar muba korarta zamuyi,to yanzu ma zancen danake maka batayi jarabawar taka roƙa tayi ba.
Ko mai kama da ita bamu gani ba a wajen jarabawar,dan haka saikaje ka tambayeta da kanka.
Amma karka ce nina gaya maka,dan tace sai tayiwa ɗana duka idan na faɗamaka bata zoba,saboda nasan zata aikata yasa nayi shuru. Amma ganin yanayin daka shiga yasa na faɗamaka"
Yana gama faɗawa mlm Ahmadu haka yakoma cikin gida yabarshi a tsaye.
Haushine ya kama mlm Ahmadu jin abin Bombee tayi masa,wato dan iskanci babu wata makaranta da taje,shine harda karbar dari biyar babu ko kunya taje ta kashe.
Hanyar gidannsa ya nufa yana saƙawa yana kuncewa. Dabb dazai shiga gida dabara ta faɗo masa. Murmushi ganin yasamu mafitar tunanin dayake ciki.
Yana shigowa gidan yau ko sallama bayyi ba idonsa ya sauƙa kan Bombee,wacce taketa wurga sakwarar da inna laari tayi musu da ranar.
Daneji da Laari kwanonsu ɗaya tare suke ci,sai innayi kwanonta daban itama Bombee haka,da farko tare sukeci,tashi ɗaya Bombee ta tada tsiyah sai an raba musu kwanon abincin.
Masifah mlm Ahmadu yafara,ta inda yashiga batanan yake fita ba,kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai.
"kee Bombee yanzu dan zabar baki ɗaukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?"
"Danajene an gama shiyasa"
"Hmm to shikenan,ki rubuta ki ajiye,aure zan miki kawai na huta dake,tunda kinƙi karatu saiki tafi gidan miji?"
Ƴar dariyar tayi irin bata ɗauki maganar da ɗumi ba kafin tace.
"Aure kuma baba abokaina ma fah ba amusu aure ba?".
"Su suna da hankali,sun ɗauki iyayensu da mutunci,sannan kuma dasuka sakasu makaranta sunyi,basuyi taurin kai ba kamar ke,dan haka ko kinƙi ko kinso aure zan miki da ɗan gidan Jauro da suke ƙauyen gefenmu,BUBA,dama yace yana sonki nace karatu zakiyi,shima kuma ɗan tijarane kaman ke,saiku haɗu kuyi da rayuwa tare har lokacin nutsuwa yazo muku.
Ke kuma saiki fara shirye shirye,nan da wata ɗaya zansaka bikin,yanxu haka ma wajensa zan nufah"
Yana gama faɗin hakan ya kaɗa babbar rigarsa ya nufi waje.
Daneji takai lomar abinci bakinta,bata ƙarisa taunata ba ta tashi a wajen cin abincin,abin duniyah duk ya isheta.
Zama tayi a bakin gadonta tayi shuru tana kallon tagar ɗakin,rayuwar ta a baya tafara tunawa,yanda ta taso a gidansu cikin kulawa da kuma gata.
Bata taba tunanin zata tsinci kanta a irin wannan rayuwar ba,da farko batayi tunanin yin aureba ba acikin danginsu ba. Haka ta wayi gari tana wajenda babu danginta ko ɗayah,idan wani abu ya sameta,batada kafaɗar dazata jingina tayi kuka,har yau ta gagara sabawa da kaɗaicin datake ciki.
Aka zo zuwa lokacin data samu ciki,farincikine ya kamata,ko ba komai zata bude ido taga jininta a gefenta. A haka tafiya tayi tafiyah lokacin guda ta buɗi ido ta kalli ƴar ta kuma jininta a hannunta,a sannan tayi tunanin wahalar ta yanke zata raini ƴar ta cikin gata da soyayya kaman yanda ta samu,Saidai bata saniba ashe tsugunne bata ƙare ba. Sai ƴar ta tazo duniyah ta wata halitta taban,wanda tun a lokacin ta fara hangon irin ƙalulabalen dazasu fuskanta itada ƴar tata,musamman daya kasance cewar dama bakowane ya yarda da ita ba,kullum cikin zargi take akan ita mayyace.
Cikin dadi da babu daɗi ta raini ƴar tata har zuwa girmanta,a tunanin idan ƴar ta jure wahalar yarinta watarana sai labari.
Tashi ɗaya sai rishe ya juye da mujiya batareda tayi zato ba,sai yazamana abinda take gudun shiya afku.
Wato ƴar tata tayi nasara buɗe shaiɗanin dake cikin jikinta,wanda sukayi iya ƙoƙarinsu wajen binneshi a jikinnata.
Maimakon zaluntarta da yara sukeyi,sai ya zamo yanzu yaro idan bata ga dama ba ko fita daga cikin gidansu bai isa yi ba.
Abinda take gudun a ƙira ƴar ta dashi yanzu ya gauraye bakin mutanen garin.
"MAYYAH HATSABIBIYA"
To bayan wancan kuma ga wata sabuwar itama ta 'bullo,auren rashin gata mijinnata ke shirin yiwa ƴar tata,duk da tasan laifin na ƴar tata ne,amma kuma zuciya babu ƙashi,takasa daure hakan a cikin ranta.
Yanzu fargabarta ma ɗaya shine,shin Bombee zata yarda ta zauna a gidan auren idan ayi mata,babu abinda ya canza a halittar jikinta na ƴan adam ta take fuskantar haka,inaga kuma ita a wani yankin daban.
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]
*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________
Page 🖤21🖤
Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba.
"Inna......inannnaaaa"
Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa.
Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta hanyar baraxana akan ƴaƴannasu,dan ta kula mutanen agwagine,basu san komai ba sai soyayyar ƴaƴan su.
"Inna ki daina wannan damuwar haka,indai akan wannan aurenne ni zan iya sakawa a fasashi idan bakyaso"
"An zo wajen,ba auren dazai miki ne abin tashin hankali na ba,ke abinda zakiyi a aurenne abin tashin hankalina"
"Kaman yaya inna,taya zanyi shuru amin wai aure,wazai ganni yace nakai aure,ni babu abinda nasani akan wani aure,dan haka kuma bazanyi shi ba"
"Kinga koh,do wannan ne yasakani damuwa ba aurennaki ba,inkinason farincikina kuma ki daina ganin dakuwa ta,to ki dunga jin duk abinda babanki ya umarceki dashi,bana son kinayi masa musu akan abinda yasakaki"
"Hmmm nifah bawai inason yimasa gardama bane,kawai ni banson duk abinda nakeso shikuma yahanani,abinda bana so kuma kullum shi yake sakani,ni bana so ana shiga rayuwata irin haka,abinda ma yafi bani haushi shine,sai munyi magana dashi akan zanyi wani abu ya amince,daga baya kuma sai yaxo yacemin abinnan bai yarda dashi ba.
Taya inna kike tunanin zan yarda kullum yadunga yimin haka kuma........"
"Saurin buge bakin Bombee Daneji tayi,tareda yin magana cikin bacin rai"
"Wani nikam yaushe zakiyi hankali ne kam,kullum kina girma kina cin ƙasa,wannan harkar maganar tantiran zaki zo kina min anan kina cije min baki,kuma wai duk da mahaifinki kike. Kenan bashida ikon sakaki abu komai koke nufi?.
Aure kuma saura naji kinyi wata tsiyar akai nida kene dan kinga ana ƙyaleki koh? Tashi ki bani waje,aure babu fashi"
Cune baki Bombee tayi tareda barin cikin ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Daneji tayi,tabbas dolene tayiwa tufkar hanci,idan tana son su shiryah da Bombee da kuma ubanta.
"Allah kayi mana maganin matsala"
Tafaɗa cikin kasalalliyar murya.
Shirye shiryen bikin Bombee aka farayi da GOJE ɗan gidan jauro,wanda suke wata Ruga nesa dasu kaɗan.
Goje mutum ne majanuni,saidai shi ƙarin tsiyarsa harda innarsa wacce take ɗaure masa gindi,kullum idan yayi abu sai tace bashi bane,daga kan satar gaji ya fara,har yaxo kan satar shanu suje su sayar.
Yanzu har ta kai yana haɗa baki da ƴan daba ayi babbar sata,wani halinsa ma na takaici shine har fyaɗe yanayiwa ƙananan yara,idan an kai ƙara wajen HARƊO sai ya shafe zancen,saboda maƙudan kuɗin da Goje yake bashi.
Tun Bombee tana yarinya goje ya ganta yace yana sonta,da jauro yazo ya samu mlm Ahmadu da zancen ya fatattakeshi,akan ƴar sa saliha babu abinda zatayi da wani goje. Haka jauro yakoma yafaɗawa ɗansa abinda mlm Ahmadu yace,duk da shikansa da farko dama yasan abin bayyi ba,DAYEE ce matarsa ta dameshi saida yaje,wato mahaifiyar goje.
Yanzu kuma kwatsam jauro yana wajen shanu saiga mlm Ahmadu yazo ya sameshi,nan yake faɗamasa cewar ya amince da auren Bombee da goje,abin yabawa jauro mamaki,saidai yayi shuru bai ce komai ba,a ganinsa koma menene bazai zafafa ba,dan burinsa shine ɗannasa yayi aure kozai shiryu yazama mutum.
Lokacin da aka faɗawa goje baƙaramin farinciki yayi ba,danshi saboda kyanta dakuma idonta yake sonta,dan dama shi mutum ne mai son kayansa yazama daban dana kowa,lokaci guda aka tashi gyaran ƙofar gojen wacce take cikin gidansu,yaransa kullum cikin gyara suke duk na zuwan amaryar tasa nan da sati biyu masu xuwa.
"Goje ana maka sallama a waje"
"Wanene?"
"Bansani ba yace dai jauro yake nema,to da nace masa baya nan saiya ce kazo kai ɗin"
"Buge Indo yayi ƙanwarsa wacce tace anayi masa sallamar kafin ya fita waje"
Hayaniyace ta fara tashi a wajen,kana jiyo muryar goje dakuma wani daga cikin gida.
Inna dayee ce tayafa mayafinta tareda nufar ƙofar gidan.
"Kai goje mai yake faruwane,kaida waye haka,kace musu jauro bayanan yatafi Gassol jiya"
Idonta ne ya sauƙa kan wata yarinya a bayan wata mata,shikuma namijin sunata magana shida goje.
"Zakace haka mana ka bata mana yarinya,gatana ai bazata yi maka ƙarya ba,ka musa idan bakayi mata fyaɗe,aradu daga nan wajen jauro zan wuce nayi ƙararka"
"Ƙara akan me naji ana zancen ƙara kuma,wani akayi maka,kayanka akaci Mlm?"
"Ina kayana ɗanki yaci ai da sauƙi,ƴata ya lalatawa rayuwa,in baki yarda ba kata ki tambayeta,kaita lungu yayi yai mata fyaɗe,sannan kuma ya gargaɗeta akan kada ta faɗa.
Jiya yarinya tafara amai ashe ciki gareta,saida nabata azaba kafin ta faɗamin gaskiya. To bazan yardaba aradu sai anbimin kadu.
Kuma yarinya dole ya aureta tunda ya lalata ta"
Dariyar rainin hankali inna daayi tayi,tareda tafa hannaye.
"Heeee sai yanzu ka sosa inda yake maka ƙaiƙayi mlm,kace kawai ƴar ka tagama yawon dambaɗewa kanason mannawa ɗana ita saboda kaji zayyi aure,to ahirrr dinka munfi ƙarfinka munfi ƙarfin wanda ya tsaya maka ma.
Ba wajen jauro zaka kai ƙaraba ka kai cikin gari ma idan kanaso,haka kawai kowa sai yazo yana laƙawa yaro sharri,dan kawai kunga yayi farinjini yaki auren ƴaƴan ku,duk ina sane da abinda kuke ai,kowa so yake ƴarsa da auri goje saboda ta haifamuku ɗa namiji kuci dukiya,toh aradu baku isa ba.
Kaikuma ka bacemin daga ƙofar gida,ko kuma nacewa arɗon kunzo har gida kunyimana sharri.
"To shikenan tunda haka zakice,kowa a rugar nan yasan tsiyar da ɗanki keyiwa Al'umma,amma saiku danne kurufe,saboda kuna da hanya a wajen Manya,babu komai a akwai Allah,zakuga yanda zaku ƙare dashi.
Lalatacciyar uwa mai boye laifin ɗanta,zaki samu wanda zai yi maganinsa kuma babu yadda zakiyi"
Mahaifiyar yarinyar ce tafaɗawa inna daayi cikin muryar kuka,hannunta rikeda dana yar tata wacce itama take kukan.
Dan takaici shi uban ko magana bayyi ba,sai turasu dayayi suka tafi. A hakan ma daayi bata barsu ba tana iyowa daga bakin ƙofar gidanta.
Sai bayan sun 'bacene Inna daayi ta juya takalli goje wanda yake yangara hakora yana hura hanci,shi a dole an bata masa rai,amma kana ganin idonsa kasan bashida gaskiya a lamarin.
"Yanzu duk yanda nayi dakai akan kadaina wanann halin yanzu aure zakayi baka daina bako,a hakan kake tunanin zasu baka auren idan suka san haka kake?"
"Na nawa kuma ai sun riga sun sani,a tunaninki haka kawai zasu bani aurenta tana hankali, hmmmm itama tantiriyace lamba ɗaya.
Saikiyi shirin karbar tantiriyar suruka inna"
Zaro ido inna daayi tayi tareda jan ajiyar zuciya.
"Kuma kasan hakane ka nace saiak aureta,yanzu duk ƴaƴan dana kawo maka ka aura kaƙi,dama dan ka auromin irinka ne cikin gidannan,aikuwa zan saita mata zama,dakanta zata bi yanda kowacce mace take a gidan aurenta"
"Hhhh a tunaninki zan kawo matata ki dunga yimata izaya ina kallo,ba iya son Bombee ne yasakani aure nan ba,saboda naga yanda zatayi dake a cikin gidannan ne,baki san halinta ba sunanta kikeji,amma kije ki buncika ki gano da kanki"
'Dama hakane ?' ta faɗa a ranta.
_____*_____*_____*___
"Ungo karbi kisha yanzu nan"
"Wannan ɗin menene inno?"
Bombee tafaɗa tana yamutsa fuska
"Kinci gidanku banace karki tambaya ba,ki shanyeshi yanzu nan,wacce zatayi aure ai saida gyara,kuma gobe ma ki tabbatar kin dawo,sannan dama na riga na hanaki bin Shugabannki jeki,karki ƙara yin tsalle tsallen nan bana mata bane"
Duk abinda inno tak faɗa Bombee tana jinta,ba abinda takeyi sai dariyah ƙasa,ita mantawa ma take da zancen sai anyi maganar tukunna.
Haka gidama tashi ga tafita,sunata aikin shirye shiryen biki. Jiya fitowar ta takalli ana shigowa dakayan gado cikin gidan,babu abinda take ayyanawa a ranta sai irin kuɗin dazasuyi idan ta siyarsu.
"Lahh inno gwanda dakika tunamin,dama fah inason naje nayi ɗan bincike akan shi wannan gojen"
"Ahah karki je dakanku,ki bari Mlm yasaka ayimiki,wai sau nawa zan faɗamiki ki daina hakane kam,tashi ki tafi gida ma ya isa haka,sai gobe kuma"
Tashi Bombee tayi batareda tayi musu ba takaɗe rigarta,wajen da yayi ƙasa.
Hanyar ƙofar gidan tayi batace komaiba ta kamo hanyar barin jejin.
Jijjiga kai inno tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,duk cewa batayi mata musu,amma hakan bashi ke sakawa tayi abinda tasakata ba. Tasan ko tsafi take da zaba Bombee bazata haƙuraba sai tayi binciken dakanta.
Haka take wata irin murɗaɗɗiyar yarinya ce itah,da kaɗan kaɗan tsoro sai barin cikin idanuwanta yakeyi,a hankali take sauyawa zuwa wata macen taban.
Da farko abin kaman ƙuruciya,amma kuma tana girma tana ƙara fitar da halayyarta na tsayawa akan ra'ayinta.
Duk da kasancewarta ba mai sabo da mutane ba,amma haka kawai Allah ya haɗata da jinin Maharbi Uwaisu,shida matarsa inno,basuda ɗa ko ƴa shiyasa sukejin Bombee har cikin ransu,duk su kansu sunsan batada daɗin sha'ani.
Hasashen inno bai tashi a banza ba,maimakon Bombee takama hanyar tafiyah gidansu,saita kama hanyar da zata kaita rugar su goje a ƙafa.
Tana tafiyah tana ƴar waƙa,irin wanda takeji a gidan rediyo,harta isa ga rugar.
Lokacin anyi magriba duhu ya kawo kai,wani mai gasa masara ta haɗu dashi a bakin hanyar yana da aikinsa.
Tsugunnawa tayi kaman abin arziƙi tace.
"Uh dan Allah bawan allah idan bazaka damuba tambaya nake"
"Allah yasa na sani toh"
"Inaso ne ka faɗamin duk abinda kasani gameda Goje dake rugar nan,kama daga mugayen halayensa harma da abinda yake aikatawa"
Kallon bakida hankali yayi mata,tareda yin dariyar rainin hankali.
"Mai yasa kake dariyah,bazaka faɗamin ba ko kuma kana tsoro"
"Tsoro? wazanji tsoro,tambaya ma kike akan meyasa bazan faɗamiki,dallah tashi ki bani waje tunda bakida hankali"
Kama bakin tiren gashin masarar tayi kaman mai shirin watsa masa garwashin a jikinsa.
"Ke me kike haka?"
Rashin hankalin nakeso na nuna maka banida shi kaman yanda kake tsammani,shin zaka faɗamin ko kuma sai na gasaka kaima da abinnan.
Zaro ido yayi tareda cewa.
"Keee ki bari aradu ina tsoron faɗamiki,zance yadawo ace a wajena kikaji"
"Tom tunda tsoro kake sai zabi na biyu,kwatanta min gidansu"
Kwatancen yafarayi mata batareda musu ba har ya gama.
Tashi tayi zata tafi,maganar sa ce ta ƙatseta ta tsaya catt.
"Mm....me zakiyi a gidansu,yarinya bazai ƙyaleki bafah idan wani abu kike nufinsa dashi,sannan kuma innarsa ta ɗauremasa gindi,ko ƙara kika kai baza'a saureriki ba"
"Wow kaga ka bani amsoshin tambayoyina dayawa,karka damu ba wani abu zanyi masa ba,kawai zanje gun innarsa ne na tambayi waye shi,dan nasan tafi saninsa fiyeda kowa"
_*Sadi-sakhna ce*_
Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤