Showing 42001 words to 45000 words out of 134612 words

Chapter 15 - Bakar Aya writing by Sadi Saknah.txt

16 Dec 2024

8671

gado"
"Yanxu dan kawai rayi miki wannan lafin shine kika yi mata duka haka,"
"Faɗamata dai,anyi mata aure ta kasheshi da baƙin halinta,ta dawo gida ita ba auruwa zatayi ba tana musgunawa ƴan gidan.akan fitsari shine zakiyimata wannan dukan dan baƙin hali,nasan ma ba iya akan fitsari bane akwai wani mugun nufinki dai daban"
"Ehh akwai mungun nufin,tunda take zuwa tana munafurcina ko kuma takemin raini kin taba hanata ne,shine danna ɗau mataki za'a ga laifina,in kinji haushi ki rama mata mana,kiga in ban kasheta a gidannan ba muss har lahira kum.........."
Fasss bata gama kaiwa ayah a maganar tata ba taji Daneji ta wanketa da wani zazzafan mari a kumatunta,kafin ta juyo tasake daɗa mata a ɗayah kuncin.
Idonta har kanƙancewa yakeyi jikinta yana rawa saboda bacin rai,nuna Bombee tayi da yatsa tareda cewa.
"Bombee........yanzu har kinyi girman da a gidannan zaki buɗi baki ki faɗawa addah laari haka,ehh lallai yau na tabbatar da baka haihuwar ɗa kuma ka haifi halinsa,kin nuna min iyakata tabbas,kuma naji daɗi da nunamin wanann halin da kikayi kinji"
Kecewa da kuka inna laari tayi jin abinda Bombee tafaɗa mata akan idonta,wanda suna cikin hakanne mlm Ahmadu shima ya shigo gidan.
Tambayar mai yake faruwa yayi,amma babu wanda ya tanka masa,ita Daneji tana faman yiwa Bombee faɗa,yayinda ita kuma inna laari take aikin share hawayen idonta da gefen zaninta,itakuwa wacce tafi dakuwa kukanta yafi na kowa yawa a gidan.
Larai kuma taga kan katanga tana sallallamin jin abinda Bombee tayi ɗin,dan tun ihun innayi na biyu take kan katangar.
Shi mlm Ahmadu dayake ta faman tambayar mai yake faruwa,bai samu sanin hakan ba daga wajen su,sai a wajen inna larai wacce take kan katanga tana kwararo masa bayani kaman recorder.
Tun kafin tagama faɗamasa mai yake faruwa ya zari igiyar awakai dake gefensa ya hau Bombee da duka,wacce take tsaye ƙinkam yana dukannta.
Tun yana dukannata da igiyar har saida ta yayyage ta baje a hannunsa,amma Bombee tana tsaye ta rufe idonta,sai ya zabga mata bulalar taɗan runtse ido kaɗan.
Shatu ce itama dake kan katangar tasamu damar faɗin
"Yanzu Bombee bazaki gudu ba irin wannan duka da ake miki"
Bayan ita babu wanda yayi magana,kowa baki ya buɗe yana kallon Bombee,yayinda shikuma mlm Ahmadu duk bayan duka ɗayah sai zuciyarsa ta ƙara tafasa.
Jefar da igiyar yayi yasake tsinkar tashanyar su ya cigaba da dukan Bombee da ita.
Wanda ita kuma a nata bangaren ba dukanne yake wahalar da ita ba,illah ƙoƙarin datake wajen cin galaba akan muryar datake yimata amo a cikin kanta.
Ba abinda take umartarta dashi illah tarama dukan da mahaifinta yake yi mata a lokacin,wanda har abada bata fatan taga hannuwanta sun aikata hakan.
Salatin dataji su inna laari sunayine yasakata buɗe idanuwanta da sauri,ba komai ta hanga ba sai mahaifinta kwance a ƙasa yana dafe da zuciyarsa,wanda tasan ko tantama bazatayi ba ta sanadiyyartane hakan ta faru.
Abin haushin kuma duk yadda taso ƙwakwalwarta tasaka zuciyarta jin haushinta abin ya faskara,saima haushin mahaifinnata daya turnuƙeta.
Tsugunnawa tayi a hankali zatakai hannunta kansa,caraff taji an rike mata hannu.
"Karki kuskura ki taba shi,wlh bakida wannan damar,ki bacemin daga gani yanzunnan"
Daneji ce tayi maganar wacce idonta yayi jajur ta tsanar halin Bombeen.




Ohhhh nagaji......i hope dai yana sugar littafin koh????








_*Sadi-sakhna ce*_


Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼






____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]










*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________










Page 🖤28🖤














Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa.
Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi.
Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi.
Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan.
A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya hau,saidai ba'a bashi gado ba gida suka dawo,tunda bayyi tsanani sosai ba.
Amma tunda suka dawo da la'asar har yanzu bai sake magana ba.
Runtse ido tayi lokacin da labarin ya riski kunnenta,babu makawa tasan itace silar hakan.
Saurin kawar da fuskar tausayin datake ciki tayi,tareda jan numfashi dogo kana ta furzarshi.
Kai tsaye cikin daji ta nufa ta mungun gudu,wanda kowa yakalli hakan yasan da gangan takeyi saboda ta gajiyar da jikinta,aikuwa abinda take nema ta samu,dan daƙyar da ƙarisa filin yin gwajinnata tana maida numfashi.
Idonta ne yasauƙa akan haidar wanda yake zaune akan reshen bishiya yana jin tuffah(Apple)a hannunsa.
"Wow irin wannan gudu haka kaman barewa,daga nesa fah nakejin ƙarar gudunki,anya kuwa ke mutumce,karfah nace da aljana nakeson yin abota"
Tubbbb ta tofar da wayu tareda watsa masa harara tace.
"Wai miye hadina dakaine,sannan da izinin wa kakeson shiga gonata?"
"Gona kuma,bakiyi shuka a wajen ba fah,in ma akwai ni bangani ba gaskiya"
Yakarisa maganar yana duban wajen a cikin fuskar zolaya.
Zaro ido yayi tareda matsar da kansa gefe guda,cattt kuwa ƙaramar wuƙar ta caku a jikin bishyar dayake kai.
Kafin ya dawo hayyacinsa sai ganinta yayi akan reshen a gefensa,fuskakokinsu suna tabb dana juna,ta zuba masa wannan fitinannun idanuwannata masu launin shuɗi a cikin nasa.
"Kutt kasheni zakiyi,sannan kuma yaushe kikazo wajennan iyeee?"
"Ba wannan na tambayeka ba,meyasa kakeson shiga rayuwata,wani ne ya aikoka? Sannan mai kake so dakake bibiyata,na daɗe ina kulada kai a wajennan tsawon sati guda,da farko banyi zaton nikake bibiya ba,sai daga baya na kulada hakan,waye kaiiiii?"
Tafaɗa cikin tsawa tareda dasa masa wuka a kan wuyansa.
"Habaaaa Bombee mai yayi zafi shiba wuta bane,babu abinda nake binki dashi,jarumtarki da kuma yanayinki ne kawai yake birgen,shiyasa nakeson ƙulla abota dake,bayan hakan kuma dama banga kowa a cikin wajenba wanda zanje wajensa"
"Daga ina kake?"
"Kaman yanda na faɗamiki sunana Aliyu,ni ɗan gidan General Muhammad Bello ne. An kawoshi nannne saboda wani case ɗin manyan yan fashi dayake wakana"
Gidanmu nacan ɗayar hanyar ba wacce kikebi idan zaki je gidan maharbinna ba."
Sauƙowa tayi daga kan bishiyar ta soke wuƙar a kumkumin ta inda tacireta.
"Kaine mutum na farko daya tunkareni da niyyar abota batareda wani dalili ba,kodayake yanada nasaba da cewar baka sanni ba"
"Menene yasa baza'ayi abota dake ba,you are very "interested lady"
"Wanne yarene haka kayi magana dashi,uhm kaman yana kama da wanda malamai da copper ko kuma masu bibiyar wannan jejin suke magana dashi"
"Kutt bakisan turanci ba kina nigeria"
"Nasanshi yanda kayine yamin kama da ba irin na sauran ba"
"Hhhh inaga saboda ba a ƙasar nan nake zaune bane,nazo hutune na shekara guda shiyasa na biyoshi nan domin naga ya wajen yake. Baki amsamin tambaya ta ba,meyasa suke tsoronki"
"Kai baka gani ba,a ganina dai kaiba makaho bane,suna ganin kaman ni ba mutum bace saboda idanuwana"
Dariyah Haidar ya sheqe da ita,wanda hakan yasa Bombee binsa da kallon kaman yasamu tabin hankali.
"Wani blue iris ɗinki,da farko nayi mamaki kam sosai,amma kuma nida na zauna a ingland naga masu irin idonki da yawa,hmmm saidai gaskiya nasu baya shining kaman naki,amma duk wanda yagani yasan ai normal ne,akwai masu abubuwa rare da dama a duniyah"
zaro ido Bombee tayi jin daya faɗa mata cewar akwai masu irin halittarta a cikin duniyar nan a wani wajen nesa da ita,lokaci guda sai kwaɗayin da haɗu dasu yafara shiga cikin ranta.
Tambayoyi Bombee take yimasa yana bata amsa,wani yayi mata dariyah wani kuma kawai yabata amsa.
Lokaci ɗaya sai tasamu kanta da sakewa dashi batareda ta sani ba.
Shikuma ganin tasake tana maganar arziki dashi,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba haɗeda dauke kewa.
Basu ankaraba suna ta surutu sai gani sukayi rana tayi sosai.
Tashi Haidar tayi taga bakin ruwan dayake zaune ya kalli Bombee.
"Nikam barina tafi,sai anjima zan dawo,daganan zaki fara koyamun wasannan dakike da sanda"
Dariyah tayi tareda cewa.
"Lallai kuwa wasa,abinda nake yayi maka kama da wasa koh?"
"Komai dai menene nina tafi"
Ya juyah zai tafi saikuma taga ya tsaya,kasancewar ruwan take kallah batasan mai ya gani ba.
Muryar da bazata taba mantawa ba taji ya daki dodon kunnenta.
"Heheehhe iyeeee kice kin samu duniya kam,tunda har ɗan matashin saurayi kikayi bansani ba,da izinin wa kike gara rayuwarki haka"
"Da izinina mana,da dana wa zanyi,sannan menene ya kawoka inda nake?"
"Saboda na kwashi romon da bankai ga shaba kika katseni"
Ƴar dariya Bombee tayi tana kallon goje wanda yake tsaye tareda maza gudan huɗu ,bibbiyu a kowanne gefe.
"Ta yaya marar ƙafa zai hau tsani(bladder)? Uhm"
"Idan an hau masa ai ya wadatar,koda shi baxai iya hawa ba,a tunaninki dan bazan iya farmakarki ba shikenan zan bar abinda kikayimin ya tafi a banza ne,yau babu mai ƙwatarki a hannuna,saina maidake abun tausayi,abinda zanyi miki sai ya kafa tarihi a garinnan,dan ba'a taba yiwa wani mahaluƙi irinsa ba"
Yana maganar gashin bakinsa yana ɗagawa,sannan yana haɗawa da dariyar mugunta. Tashi Bombee tayi daga inda take tareda kallon Haidar.
"Haidar kabar wajennan yanzunnan kar abinda zai faru yashafeka,karka damu bazan bari su bika ba,kabi ta bayana ka gudu"
"Ke kuma fah,kina ganin zaki iya da wannan mutanen,su waye su ɗin,sannan me suke nema a wajenki"
"Karka damu dani,zancen suwayd kuma bazan samu damar baka bayani akai ba yanzu,amma idan na rayu ko mun sake haɗuwa za faɗamaka"
Tana gama maganar ta turashi ta bayanta tareda yimasa kallon umarnin dole ya bar wajen.
Yana tafiyah kuwa taji muryar goje yana cewa
"Iyeee kice dagaske ashe kina sonsa tunda har kareshi kike,karki damu babu abinda zanyi masa,zaifi ciwo ma idan yaga masoyiyarsa anyi mata fata fata,zan in yanada wayo shin zai ƙara sonki? Ku lahanta min ita tukunna mazaje"
Yafaɗa cikin gunji.
Farmakarta sukayi a tareda da nufin kaimata mungun duka,saidai cikin sa'a tasamu nasarar tsallakewa ta hanyar yin tsalle tareda riƙe rishen bishiyar da take samanta.
Wuƙar kunkuminta taciro ta sokawa ɗayah a gadon bayansa,aikuwa yafasa ihu yayinda yaji azabar ta ratsashi.
Komawa dabaya sukayi ganin an shafe kusan daƙiƙa ashirin basu samu nasarar tabata ba.
"Kai ogah yarinyar fah ta iya faɗa da alama,ya kake ganin za'ayi?"
"Kuje mata kuma salon dabara mana"
Suna cikin hakanne goje ya sanɗeta tajuya baya ya sake mata sanda a gadon baya,kasa jure zafin dukan tayi,dan haka tafaɗi kasa tana maida numfashin wahala.
Wani sandan goje yasake narka mata a ciki,tasaki kukan mai nuna Alamar dukan ya shigeta.
"Wai ke mai iya faɗa koh,birice ke yau taki taƙare"
Duka yacigaba da kaimata ta ko'ina,babu tausayi babu imani. Tun Bombee tana nishi har yazamo jin dukan take kawai yana shiga jikinta.
Tsugunnawa yayi saitin fuskarta yana kallonta ɗauke da murmushi mugunta akan fuskarsa.
"Kai tulezi ku buɗemin ita ku fara yimata fyade har saina ce ku daina tukunna"
Rufe idonta tayi kirif tana jira taji ta inda zasu shigeta su keta mata mutunci. Duk iya kokarinta wajen ganin ya motsa gabobin jikinta abin ya faskara,dan kamar basa karbar saƙonta ma ballantana su motsa ɗin.
Shirinyewa tayi ta saddaqar tata taƙare daga wajen,a sama sama tajiyo hayaniyar mutane da kuma sautin takalmansu,wanda ta tabbatar bana masu yimata aika aikar bane.
Sakin ta taji sunyi sun nausa cikin jejin,yayin da karar sawunsu yake yin nisa,ƙarar na wasu kuma ya dunfarowa inda take kwance.........bata san shin masu cetonta bane ko kuma masu cutar da ita.
Ɗagata taji anyi an sakata a cikin wani abu mai tafiyah.




Sorry ayi hakuri a barshi haka,🤣🤣🤣🤣 bansan mai zance ba
























_*Sadi-sakhna ce*_


Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼






____****🖤🖤****_____




🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤




🖤 _BOOK1_ 🖤






Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]










*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03


*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________










Page 🖤29🖤








A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai.
Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka.
Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin.
Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska.
Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka ba a rayuwarta.
"Na ɗanɗin inane,sannan kuma waye ya kawoni wajen?"
Ta faɗa sanyaye,bata kai ga tantance hakan ba daga mariƙar ƙofar ya murɗa,wanda lokaci dayah ya murɗa da tunaninta,dan kuwa batasan wata ƙofa mai hannu yana motsi ba.
Haidar ne yashigo ɗakin,fuskarsa ɗauke da mamakin ganin idonta a buɗe.
Ɗaga murya yayi yanda na wajen ɗakin zai jiyoshi yace.
"Mommy kizo da sauri ta farka"
Ƙarisowa yayi cikin ɗakin tareda zama a gefen gadon da take kwance.
"Sannu Bombee yakinki,amma wannan mutane basuda imani a ransu"
"Meyafaru bayan wanda ya auku a jejin,sanann inane nan haidar ka kawoni"
"Muna zuwa mutanen suka gudu,sannan yau kwananki uku a kwance,nan kuma gidanmu ne"
Yana cikin yimata bayaninne wata ƴar dattijuwar mata ta shigo ɗakin,a kallon farko zaka hango kamanninsu da haidar ɗin,saidai matar tafishi hasken fata da kuma manyan idanuwa.
Murmushi tasakar wa Bombee mai taushi tareda zama akan kujerar dake madaidaicin ɗakin.
"Sannu yarinya yajikinnaki,gaskiya a yanda suka dake gidannan kinji jiki sosai,mai kikayiwa wannan mutane haka?"
"Babu abinda nayi musu Mommy,yaran tsohon mijina ne da muka rabu shekara biyu baya"
Tare haidar da mahaifiyar sa suka haɗa baki wajen cewar.
"Tsohon mijinki shekara biyu baya,yanzu ma nawa kike daza'ace shekara biyu baya kinyi aure?"
"Uhm hakana babana ne ya auraminshi saboda naƙiyin jarabawar tafiyah makarantar kwana,to a ranar farkon aurenmu ne.......yazo yimin fyaɗe na farmakeshi shine..........aka raba auren. Yanzu kuma yazo daukar fansar abinda nayimasa,saboda illar danayi masa na bazai sake haihuwa ba"
Dakatar da Bombee Hajiya tayi da maganar,dan tun a bayani farko tagano abinda ya faru,ita kanta tayi mamakin karfin halin Bombee ɗin,amma kuma saita barshi akan tayine dan ƙoƙarin kare kanta.
"Kinga ki daina yawan magana dan baki gama warkewa ba,Allah ya kiyaye nagaba,haƙiƙa kinyi bajinta sosai,dan dama haidar yasha bani labarinki tun kafin yamiki magana,koyaushe sai yazo yacemin yaga mace a jeji tana koyon faɗa.
Yanzu dai ba wannan ba,yakamata ki faɗamana gidanku domin a sanar da inda kike,danna san dole zasu nemi sanin mai ya faru dake"
Shuru Bombee tayi tareda tafiyah tunanin abinda yafaru kafin zuwanta jejin a ranar,abinda ta aikata a gidansu tasan babu wanda zai nemi sanin inda take,kuma ba wannan ne ma babban abin dakuwar ta ba. Ita kanta innarta fama take da lalurar rainon ciki,sannan asibiti sun tabbatar ba'ason ta dunga shiga damuwa,sannan kuma ga uwa uba abinda tayiwa mahaifinta.
Babu abinda take sakawa iyayennata sai tashin hankali,dan haka lokacin yayi daya kamata ta dakata da wannan abin haka.
Numfasawa tayi kafin tace.
"Iyayena basanan,a wajen maharbi uwaisu nake zaune"
"Uhm kaji ba dama saida nace maka mukaita can kace wai bananne gidansu ba,kana ganinta tana shiga gari"
"Eh inazuwa gidan yan uwana ne s garin"
Bombee tayi saurin kare kanta kafin wani ruwan yasake bullowa.
"To shikenan amma tunda yanzu kika tashi,ki bari nan da gobe sai mu maidaki can ɗin,yanzu zansaka haidar yaje ya faɗamusu abinda yake faruwa"
"Ahah Hajiya nagode da ɗawainiyar da kukayi dani na wannan lokacin,amma inason tafiya yau"
Hajiya Zulaiha ce mahaifiyar haidar ɗin ta taimaka mata tayi wanka da dabara. Saboda har yanzu akwai ciwuka a jikinta sosai,ƙarfin hali kawai take danta nuna taji sauƙi.
Abinci Ta haɗamata marar nauyi taci,tareda magungunan da mahaifin haidar ɗin ya siyo mata wato Janar Muhammad Bello.
A leda Hajiya Zulaiha ta ɗaure mata maganin dakuma wasu abubuwan makulashe wanda zasu tafi dashi.
Ɗakin da take kwanca ta shiga,suna ta hira da Haidar cikin raha da nishadi,kaman sun shekara da sanin juna.
Dukkan hiran dayake mata bai wuce na labarin yayunsa biyu mata ba,da kuma ƙannesa ma biyu mace da na miji,wanda suka tafi makaranta basu dawo ba.
"Uhm kace kana da yan uwa sosai,ni kam mu biyune kawai a wajen mahaifinmu,daga ni sai ƙanwata,itama tana wajen innarta"
"Bombee kin shiryah tafiyar kuwa yau,bazaki sake yimana kwana ɗaya ba"
"Ahah zan tafi ai zan dunga kawo muku jiyara"
"Wai ai inaga nanda sati ɗayah zamu tafi,kafin sannan kam ki kawo mana ziyara idan kin samu sauƙi,yanzu ki fito Baban su haidar na nemanki a falo,zai maidaki gida shida Haidar"
Ɗaga kai tayi cikin girmamawa alamar taji abinda Hajiya Zulaiha tace.
Mutum ne mai yawan murmushi kaman haidar ɗin,sannan gashi dogo kakkarfah......uhm soja mazan fama kenan.
Tsugunnawa Bombee tayi kaɗan ta gaisheshi cikin girmamawa.
Ga mamakin ta kuwa bai ƙyamaceta ba kaman ƴan garinsu,dan da fara'ah ya amsa mata. Har yana tsokanarta wai tafi ɗannasa jarumta.
"Da haidar yabamu labarin yanda kika tareshi har ya samu guduwa a lokacin naji kin burgeni sosai,kuma fah ko kunyah bai jiba yana namiji wai mace tatare masa faɗa,mai makon ya tsayah yaji dasu......"
Dariyah dukka wajen aka saka banda haidar wanda ya cune fuska kaman ƙaramin mai yaro mai feeder.
Kuɗi ya ciro ya miƙa Bombee,amma juyin duniyar nan taƙi karba,dan ita tun lokacin da Innarta tayi mata magana akan kuɗi,sai ya zamo bata fiyeson ko kyauta tadunga karba a hannun mutane ba,ballanta na kuma sata.
Haka dole ya ƙyaleta ganin duk ƙoƙarinsa amma taƙi karba,Hajiya Zulaiha yabawa a ƙarshe kan tayimata siyayya to takaimata.
Da haka Bombee tayi sallama ta matarda taji tashiga ranta,bayan innarta da kuma inna shatu Hajiya Zulaiha itace mace ta biyu data jita a ranta.
A bakin ƙofar gidan suka ajiyeta,bayan Haidar yabata ledar ta Hajiya Zulaiha tace yabata.
Inno tana tankaɗen tuwo taganta tashigo tana tafiyah a hankali,alamar babu lafiya,dan dama kwana biyu tana cikiyarta shuru.
"Ahhh Bombee mai ya sameki haka?"
Bata kai ga amsawa ba taji muryar Haidar yana gaisheda inno,mamaki tayi dama biyota yayi?
"Uhm baka tafi bane dama?"
"Ah iya abbane ya tafi,ni sai anjima zan tafi idan naci tuwon inno"
Yakarisa maganar yana ƙifta mata ido,bai san mutane ba amma har ya shige gaba,ta faɗa a ranta,a fili kuma tana binsa da harara.
Shine yabawa inno labarin abinda ya faru,inda suka jajanta sosai.
Sai bayan ya tafi da daddare Uwaisu yanayimata sirace na maganin gargajiya yake cewa.
"Kwananki uku kenan a gidansu,amma kuma maimakon ki wuce gida sai kika iyo nan meyasa,innarki fah jiya taxo nan tana tambayar ko kinzo nan,inno tace mata kinzo amma kin fita.
Nasan tayi hakanne domin ta kwantar mata da hankali,nima tun a jiyan nake nemanki"
"Ahah baffah bazan iya komawa gida yanzu ba,saina samu sauƙi tukunna,Saboda abinda na aikata,wanda kuma duk inna laari ce ,ni banason matar nan wlh,inna kuma ji takeda ita kaman innarta,shikuma goje.......hmmmm"
Tafaɗa tana cizon baki.
"Kee Bombee to miye dalili ciki danta ji da ita,ke kanki shaidace yanda ta riƙe innarki hannu bibbiyu sanda aka kaita gidanku,kowa yana shaidan halinta na kirki"
"Eh kowa yana shaidanta,amma ni zuciya ta abu daban take faɗamin gameda itah,kuma da sannu zan gwadata domin share tantamata. Shikuma goje aradu ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login