Showing 18001 words to 21000 words out of 85666 words

Chapter 7 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

tabi bayan ta,
Suna isa parlour shikuma nakokarin fita sai tabi bayansa atare suka fita yana gaba tana biye dashi,suna isa kofar part d'insu yabud'e tayi saurin shiga tawuce ta isa bakin kofarta ta tura tashiga tamaida kofar tarufe tahaye gado tana mita,
Girgiza Kai yayi yawuce d'akin sa,


Washe gari bayan tayi break tashirya tatafi part d'in Umma Rabi,tundaga lokacin yazamo kullum a part d'in Umma Rabi take wuni,idan yadawo daga gun aiki kuwa saiya biya part d'in, Umma Rabi tasata sufito su koma nasu part d'in,suna shiga part d'insu kuwa zata maida kofarta tarufe.

Kwanta tashi asaran mairai,yau kimanin watan JUHAIFAH biyu kenan agidan amma fir tahana duk wata alakar dazai had'ata da Sulaiman,bata masa magana idan yanimi tayi masa magana tokuwa rashin kunya zatayi masa,kamar yanda tasaba yau dasafe tafito zata d'ibi abinci tana bud'e kofar sukayi karo dashi yafito daga d'akinsa saurin ja dabaya tayi tareda dalla masa harara tajuya zata wuce saiji tayi ya rungume ta baya yasaka kansa a'gefen wuyanta ahankali yy magana "wanna b'uyar ya isa haka yakamata ace zuwa yanzu komai yawuce,sai mud'aura ingan tacciyar rayuwa agaba."
Fisge jikin ta tayi
Ranta yayi kololuwa wajen b'aci, tamasa can gefe tafarayi masa wanin kallon sama da kasa tsabar bakin ciki takasa iya cemasa komai "Mtsww." taja wani dogun tsaki tajuya afusace takoma cikin d'aki,tana shiga d'akin tad'au mayafinta tana fad'in,


"Kai wanna mutumin yakure rainamin wayo ai wlh ganina dayake acikin gidan nema yasashi fara tunanin b'ullo da wanna salon, to gara nayiwa tufkar hanci tunkan tunanin nasa yafad'a masa ba daidaiba,Amma idan bai ganniba duk haka bazata faruba,danha bazanma zauna ba Zan tafi sai yasan wadda zai rika yi mata haka."
Tana kaiwa Nan da saurinta tayi hanyar kofa tabud'e ahan kali taleko kanta waje taga bayanan ahankali takara fita ta maida kofar tarufe, asannu tarika takawa cikin parlour har ta isa jikin kofar parlour nanma ahankali tabud'e tafita,da sauri-sauri take tafiya har ta'isa bakin get tabude tafita,tafiya tarikayi har ta isa bakin titi tana isa kuwa tatari Mai a daidaita tafad'a mishi inda zata tashiga suna isa tasauka tamika mishi 1k tajuya yace "tsaya kikarb'i canjin ki."batare da ta juyoba tace "karike nabar maka".
Dakarfi tashiga bubbuga jikin get d'in,maigadi yabud'e muryarsa yace "wanene?"
tace "kazo mana kabud'e sai na fad'amaka ko wacece tukun."
Yana Jin muryarta dasauri yabud'e karamar kofa, tayi saurin shiga yamaida kofar yarufe,tanufi hanyar part d'insu ta shiga parlour ta iske Ammee nakokarin shiga kiching,Jin karar bud'e kofa yasata juyowa baki da hanci tabud'e tana kallon ta, Ammee cikeda mamaki tace "ke JUHAIFAH meyaka woki meya fito dake daga gidanki yaushe-yashe ne aka kaikin da har zaki fito kizonan wama yabaki izinin fita kizo nan???."
Saida takaraso cikin parlour kafin tace "Ammee ni wlh bazan iyaba ni bazan iya zama agidan ba haka kawai ankaini anje an ajiyeni kamar wata mara gata Allah Ammee ni bazan koma ba,gaskiya wlh ni nama dawo gida kenan,wlh saidai aje ad'ebomin kayana da aka kaimun adawo mun dashi Dan nidai bazan komaba haka kawai kamar wata mara gata niban masan awani da lili bane aka d'auke ni aka kaini can."
Ammee ido takura mata tana kallon ikon Allah sannan tace "wani dalili wani dalili fa kkce? zaman auren ne awani dalilin?ke kinada hankali kuwa JUHAIFAH wai nikam kodai aljannu sun shafekine kam?baridai Abban ku yadawo tukun, iye him lallaima yarin yarna bakida han kali."
Itako JUHAIFAH cewa tayi "tokawai sai kace banida kata Allah nidai ba inda zan koma." juyawa tayi tashige d'akinta.
Ammee tabi bayanta da kallo cikeda mamaki,tana shiga d'aki tahau gado takwanta,tayi wani juyi tareda sauke num fashi tace "Kai wlh gida Mai dad'i in ba doleba wazai so barin gida haka kawai ban shiryawa barin gidaba suce wani wai aure wlh bawani zaman auren da zanyi."
tagyara kwan ciyarta.
Ammee ko kiching tawuce tana fad'in "sha-shan cin banza Abban naku zai dawo ai."

Wuni zubur tayi agidan batareda tafitoba Ammee ma bata bi takan taba, daf sallar magriba Abba yashigo gida Ammee tayi masa sannu da dawowa takawo masa ruwa sanna taxauna gefensa, Yana aje cup d'in tace "Alhj yarinyar Nan tadawo gida fa."
Dasauri Abba yace "wace yarin yar?."
tace "JUHAIFAH tunda safe take gidanna tunda tashigo na tanbayeta dalilin zuwanta sai cemin tayi wai Dan an maidata ma'rar gata shiyasa aka kaita can aka ajeta,tunda tashiga d'aki bata fitoba ko abincima bance taciba."
"Me kkce ko abinci ma bataci ba haba Halimatu Kuma da saninki kibarta da yunwa."
Ammee tace "Toni Zan kaimata bazata fito taciba ai haka tazab'ar wa kanta,ni 'yarnan mafa nafara tunanin bakanta d'ayaba wata kila aljannu sun shafeta."
Abba yamike yanufi d'akinta Yana fad'in mamana kenan 'yarrigima,yatura kofar yashiga akwance ya sameta,tana ganinsa
Tamike zaune tace "Abba ina yini."
karaso wa yy bakin gadon yace "mamana yau kinzo mana wunine?."
Baki taturo gaba tace "Abba nifa gida nadawo Kuma bazan koma ba."
Yace "to Mamana In banda abinki haka ake zaman auren abaro gidan mijin adawo gida Kuma da auren?."
Tace "nikam Abba gaskiya bazan fa koma ba kawai kullum nikad'ai bana ganin ku."
Yace "Mamana kenan 'yarrigima to dai yanzu tashi muje kici abinci tukun sai muyi magana."
tataso suka fito parlour,yacewa Ammee taje tazubo mata abinci,bayan taci abincin,
Abba yace "to kinaji ko Mamana tunda yau kinzo kin wuni saiki koma gidan ki sai wani karon Kuma sai kisake zuwa ki gai damu bari naje masallaci nadawo saina kaiki gidan."
bubbuga kafa tashigayi.
"Abba gaskiya ni a'a Allah Abba nifa bazan komaba."
Abba baice komai ba yafita yanufi masallaci.


Ana idar wa Abba yashigo gidan, dai-dai lokacin motar Sulaiman yashigo yagyara parking yafito ya ya isa inda Abba yake,cikin gir mamawa yace "ina yini Abba."
Abba yace "lfy lau mu isa daga ciki."
Yy gaba Sulaiman na biye dashi suka shiga cikin parlour, Sulaiman yadur kusa yagaida Ammee,ta amsa tana tan bayarsa "yagida."yace "lfy lau."
Suka zazzauna,
Abba yadubesa yace " kabiyo Mamana 'yarrigima ko?."
Yace "Eh Abba dama Dana dawo gidane ban gan taba nashiga gun Umma batanan shine nace bari nazo Nan wata kila tananan."
Abba yace "Eh tanan Nan dama yanzu nake cewa Zan kaita idan nadawo daga masallaci,tunda kazo bari akira wota sai kutafi."
Abba yamike yanufi d'akinta zaune take akan sallaya bayan ta idar da salla,daga bakin kofa Abba yace "Mamana taso kizo."saiya juya yakoma parlour tamike tabi bayan sa,tunkan takaraso cikin parlour tahango sa zaune sai taja ta tsaya,Abba yace "karaso mana Mamana."
Tace "Abba nifa..
Abba yace "bawani abun naceba cewa nayi kikaraso Nan." yanuna kusa dashi,
Ahankali ta isa tazauna gefen Abba,
Abba yace "yauwa Mamana kinaji nako? Yanzu kibi mijin ki kutafi gobe idan Allah yakai mu zanzo da kaina gidan."
Tace "Abba..
Abba yace Mamana kada kice wani abu kibi mijinki kutafi kinji'?
bana cemiki zan zo gobe ba zamuyi magana."
Ammee kam fad'a tafara mata Abba yace tarabu da ita,dakyar ya lallab'ata tayarda,Abba yace "Sulaiman tashi kutafi."
Sulaiman yamike Abba yariko hannunta har kijin mota yakaita yashigar da ita shima Sulaiman d'in yashiga Abba natsaye har saida yaga yaja motar sun fita agidan kafin yakoma ciki.

Suna fita get tajuya ta dalla masa harara tace "wlh karkaga wai Abba yatilas tamin nakoma kayi tunanin zan cigaba da zamane agidan wlh ba abunda zai zaunar Dani agidan idan kaga na zauna ko Hmm."
tagirgiza kai,
Shidai komai bai ce mataba yacigaba da tukin sa,
Suna isa yana parking ta bud'e marfin motar tafita tanufi part insu tana shiga tawuce d'aki tamaida kofa tarufe da key,
Koda yashigo lokacin take murd'a key,kansa ya girgiza yawuce nasa d'akin.

Bayan kwana bakwai

tun randa yad'au kota daga gidansu Bata kara fita Koda sakar gida ba
Ko part in Umma Bata zuwa,haka zai gama zaman sa a parlourn harya fita bazata fitoba Koda kuwa karfe d'ayan rana zaikai haka zata rike yunwanta har sai yafita kafin tafito taci abin ci,
Shiko ganin hakan da takeyi sai da sassafi yarika fita Dan saboda tarika fita tanacin abincin da wuri,zuwan buga kofar dayake yimata a kwana kin can ma yanzu duk yadaina kodun hakan zai sanya mata kwanciyar hankali tasake sosai agidan.
Yau kamar kullum tamaso jikin kofa ta kasa kunnenta shiru bataji motsin saba sai ta bud'e kofar tafito tawuce dinning tad'ibi abinci tadawo cikin parlour takunna TV sanna tazauna tana cin abincin tana kallo,harta kamla cin abinci ta maida plt d'in tadawo takuma zama,zamanta keda wuya aka turo kofa,Koda ta d'ago taga shine,sai tamayar da idonta kan TV tacigaba da kallonta,
Yakaraso cikin parlourn yazauna saman kujerar dake fuskan tarta,Jin alamar ana kallonta sai tad'ago kuwa karaf suka had'a ido kawar da kadanta tayi saikuma tamike tazo zata wuce shi,yamike dasauri yasha gabanta yace
"Haba JUHAIFAH wanna wace irin rayuwace muke yinta acikin gidanna JUHAIFAH yakamata ace zuwa yanzu munzamo abud'a JUHAIFAH kitai makawa rayuwata."
wani irin kallo ta wurga masa tace "da alla malan bani hanya nawuce."
Yace "JUHAIFAH kisaurareni kibani lokacinki Koda sau d'ayane."
"Nace kabani hanya nawuce ko yayane kam?meye damuwar ka danine kam?meyasa kake damun kanka akai nane?."
Yace "dole nadami kaina akanki saboda ked'in wata abace agareni,ke 'yar uwata ce Kuma matata kingako yazama dole nadami kaina akanki."
Tace "to bari kaji nikuma duk wad'anna basa gabana Dan haka bani hanya nawuce."
Yamiko hannu yaruko hannuta yace "JUHAIFAH ki saurareni na rokeki.
Ta fizge hannun ta ta dalla masa harara tace "tsaya kaji mln kadaina wani zakewa akan tab'a jikina idan baso kk nayi maka abunda baka tab'a tunani ba wanna shine karo nabiyu kada kasake yunkunrin cika na uku idan Kuma ba hakaba Hmm."
Matsawa yy daf da ita cikin kakkausar murya yace"JUHAIFAH taba jikin ki yazama dole domin ked'in mallaki nace akan wani da lili zaki hanani tab'a jikin ki?bakida ikon hanani tab'a jikin ki."
Yana kaiwa Nan yajanyo ta jikinsa ya rungumeta,
Kara ta kwalla kamar wacce tafad'a cikin wuta,
Dasauri yacirota acikin jikinsa yasaketa' yana saketa kuwa ta dalla masa harara tareda murgud'a masa baki tajuya tawuce d'aki.
Zama yy saman kujera tareda dafe kansa,yarasa ta yadda zaibi yashawo kanta, me JUHAIFAH takeso yy mata wacce zaisa tafahim ce shi, gashi Allah yad'aura masa son ta,itakuma Bata son shi.
Itako tana shiga d'aki tafad'a saman gado lumshe ida nunta tayi a hankali ta furta "yadage dason tab'a jikina meyasa?."
tayiwa kanta da kanta tanbayar,lallai akwai abunda yake nufi aransa,sai Kuma tayi murmushi tace "Ya Sulaiman zuciyarka Bata fad'a maka gaskiyaba,ni JUHAIFAH bazaka tab'a samun abunda kafara tunani akaina ba,sai tamike tsaye tanufi bathroom wanka ta Kuma yi
Bata wani d'auki lokaci ba tafito,
Lokacin aka fara kiraye kirayen sallar Azahar dama tayi alaula saita shin fad'a sallaya tagaba tar da salla bayan tayi addu'o'in ta tamike.


Ana idar da sallah yanufo gida har yasa Kai zai shiga d'akinsa saiya juyo yazo bakin kofarta yatura kofar ga Mamakin sa yajisa abude yashiga da sallamarsa,zaune yasame ta gaban mirror, ya isa inda take ya kura mata ido daga cikin mirror saurin mikewa tayi batareda tace dashi komaiba takoma bakin gado tazauna,
Daga inda yake tsaye yace "JUHAIFAH kinki ki saurareni bansan dalilin ki nakin saurara taba."
Adakile tace "dalilin kenan bana son ka."
Yace "inada tabbacin idan har kk sau rareni muka fahimci juna zaki koyi sona."
Wani irin kallo tayi masa tace "Allah ko?."
yace "kwarai kuwa kibani dama kigani."
Tace "Dan Allah malam fitarmin a d'aki."
tafiya yaso mayi zatonta fita zaiyi saitaga yanufota,
Cikin d'aga murya tace "kada kasake ka masoni idan baka fitaba kuwa ni Zan fita."
Yace "Babu inda zani saidai duk abunda zakiyi kiyi."
Tace "ko?." Yace "Eh."
Mikewa tayi ta janyo mayafin datayi salla dashi taja durowa tad'au kudi kafin ya an kara sai ganinta yy abakin kofa tabud'e tayi waje,
Baikawo komai aransa ba yafita ad'akin yakoma nasa d'akin Yana fad'in kokin je gun Umman madai zaki dawo.

Itako fita tayi gaba d'aya agidan, tatari adai daita tace yakaita tasha tana zuwa Tasha tanimi motar Yelwan shandam tahaye suka d'au hanya,
Yamma lis suka shigo garin Yelwa Mai tarin albarka,
Abun hawa tatsara zuwa gidan Baba Salihu,tana sauka tabiyasa kud'insa tashiga gidan da sallama,
Baba Salihu nazaune atsakar gida Yana alaulan sallar magriba ya amsa sallamar' yad'ago Yana fad'in "wanake gani haka kamar JUHAIFAH."
Tayi murmushi tace "nice Baba."
Yace kece adaren Nan Kuma kamar ke d'aya naganki ko sauran suna waje ne?."
tace " a'a ni d'ayace."
yace "to maraba karasa daga ciki."
Tace toh,dagudu Amira da Walida 'ya'yan Baba Salihu suka taho suka run gumeta suna fad'in "oyoyo Shalelen Abba."
itama cikeda murnan ganin 'yan'uwan nata ta run gumesu,kana suka janyo hannuta zuwa d'akin Mama wato mahai fiyarsu,
Itama Mama tayi murnar ganin JUHAIFAH sosai takumayi Mamakin ganinta ita kad'ai, suka zube sakiyar d'aki Mama takawo mata abinci da ruwa tanaci suna hira, bayan data gama taje tayi alaula tarama sallolin da ake binta tadawo suka cigaba da hirarsu can dare sosai kafin suka kwanta.
Washegari dasafe bayan sunyi break suka Kuma bud'e sabon hira,Mama tashigo tace "JUHAIFAH wai kije inji Baban ku."
tace "toh."tamike tafita da sallama tashiga d'akin' ta durkusa takuma gai sheshi,ya amsa,kana yace "JUHAIFAH tun jiya Dana ganki sainaji kwata-kwata hankalina bai kwanta ba wanna zuwan naki yafimun kamada baro gida kkyi batareda an saniba,dankuwa wanna zuwa naki bana shiri bane danni tunda nake dake ban tab'a ganin kinzo garinna ke d'ayan kiba, Kuma na tabbata Yahaya bazai tab'a barinki kizo ked'aya ba,koda kuwa ba agidansa kikeba,Kuma na tabbata Goggon ki Rabi bazata barrki kifito ke d'ayaba hakakuma mijinki Sulaimanu shima bazai bar hakan ta faruba."
"JUHAIFAH." yakuma Kiran sunanta kana yace "meya fito dake daga gidan mijin ki?."
Shuru tayi tareda sunkuyar da kanta kasa,
Yakuma cewa "JUHAIFAH dake nake meya fito dake daga gidan mijinki? Inaso inji daliline." Tayi kasa da murya tayi raurau da ido tace "Baba nifa nacewa su Abba banason auren Nan sukacewai saidai inje in zauna nikuma bana son shi."
Shiru Baba Salihu yy daga bisani yace "dan saboda hakanne kk baro gidan mijin?."
tace "Eh."
yace "to naji tashi kije."
Tamike takoma d'aki suka cigaba da hirar dasuke...............



08034690723




Mommyn Twins ce🌺


BAZAWARACE' ITA!🌺



بسم الله الرحمن الرحيم

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IFwQqToBiiCHVosgNITJ4q


IDAN KINSAN BASIYA ZAKIYA BA DAN ALLAH KADA KIYI JOIN KIKARAN TA FREE INKI KWAI😂AWUCE GURIN
IDAN KUMA SIYA ZAKIYI SAI KIYI JOIN DAN SAMUN KARIN BAYANI SAI KONZO🤝🏻



INA MAI FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA NARAGE KUD'IN LITTAFIN DAGA D'ARI 300 ZUWA D'ARI 200
WAD'ANDA KUKA BIYA D'ARI 300 ZAN MAIDA MUKU NAIRA 100 AYAU D'INNAN DUK WACCE TASAN TABIYA D'ARI UKU TO TAYIMIN MAGANA ZAN MAIDA MATA NAIRA D'ARI


YANZU NOVEL D'INA YADAWO NAIRA 200 KACAL GAMAI BUKATAR SIYA SAITAYI MIN MAGANA TAWANNAN NUMBER
08034690723
KOKUMA JIYI JOIN D'IN GROUP INNAN🖕🏻
NGD🤝🏻 ___________________________________


🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________



By✍🏻
Rasheeda S Director



🅿️7


Yau kwananta uku tun randa Baba Salihu yakira ta baikuma ce mata komaiba,baikuma Kira waya yace gatanan tazoba, suma Kuma daga Abujan basu Kira shiba,Itako
tasake abinta tashige cikin 'yan'uwan ta.

Acan Abuja kuwa hankalin kowa yatashi,tunda Sulaiman yafahimce JUHAIFAH Bata cikin gidan hankalinsa yy mummunar tashi,yahaye mutarsa yanufo gidan Abba,Nan suka shaida masa batazoba hankali tashe Abba yashiga Kiran waya aduk inda yake zaton samunta Amma duk wanda yakira sai yace masa bata gun sa,yad'aga waya zai Kira Baba Saluhu sai yy wani tunani ya'aje Dan yanada tabbacin har idan ya kirasa fad'a zaiyi masa har idan yaji cewa JUHAIFAH batanan, domin tun abaya yafad'a masa cewan yaji labarin JUHAIFAH batason auren to abarshi kawai Dan gudun faruwan matsala,shikuma Abban yace a'a bahaka bane labarine kawai,bare yanzu Kuma yakirasa akan wanna Zan cen lallai kuwa zaiyi masa fad'a,
Abba har yamike zai fita saiya yadawo yad'auki wayarsa yalalub'o numbern Goggo Hadiza yasanar mata abunda ke faruwa sanna yad'aura dafad'in "ko tazo can Yelwan?." Goggo Hadiza tayi salati tasanarwa uban giji,tace "wlh ni kam anan gurina Bata Nan saidai ko tanacan gidan Yaya Salihu,Dan rabona da gidansa tun wancan satin dayawuce,Amma dai bari naje can gidan nasa Allah dai yasa tana can d'in."
Abba yace "to badamuwa."
yakashe wayar,
Gaggo Hadiza batayi kasa agoiwa ba tazari mayafinta tanufi gidan Baba Salihu,
Tana shiga gidan muryar JUHAIFAH tafara ji sai dariyarta take dasu Amira Goggo Hadiza baki tabud'e tace "lallai JUHAIFAH agai shiki Allah dai yashirya, kinsa hankalin jama'a yatashi ke ko kinanan hankalin ki kwance."
JUHAIFAH dariya tayi tace "la Goggo yanzu muke cewa zamuje gidanki."
Goggo Hadiza tace " JUHAIFAH sai gyaran Allah."
tanufi d'akin Baba Salihu azaune tasameshi itama tazauna tace "inayini Yaya."
yace "lfy lau Hadiza yaginan da yaran dai?."
tace "lfy lau."
Nan suka d'an tab'a Hira irin na 'yan uwan can Goggo Hadiza tanisa tace "Yaya dama JUHAIFAH Nan tazo anacan ana aikin nimanta hankalin kowa yatashi ashe-ashe tana nan anan."
Baba Salihu yace "Eh tanan yau kwananta uku' tace Bata so meyasa za'a tilas ta mata dole Dan haka zata cigaba da zamanta anan."
shiru Goggo Hadiza tayi Dan tasan halin Baba Saluhu tasan waye shi,
Shima shirun yy sai daga bisani yace "Zan maidata gida da kaina."
Goggo Hadiza tace "to shikenan Allah yatai maka."
Tayi masa sallama tafito ad'akin gun Mama taje suka gaisa kana tayi mata sallama takoma gida,
Kwananta biyar a Yelwa Baba Salihu yasata tashirya dakyar tayarda tashirya suka nufi Tasha' basu d'au wani lokaci ba motarsu tad'aga

suna isa direct gidan Abba suka nufa,abakin get Mai adaidaita ya ajesu suka shiga cikin gidan,da sallama Baba Salihu yashiga cikin parlour
Yana gaba tana biye dashi,su Abba suka amsa sallamar tareda yimasa maraba da zuwa suka isa suka zauna,Ammee sai wurga mata harara take itako wani had'e rai tayi adole ita gamai gaskiya d'inna,
Su Abba suka shiga gaida Baba Salihu
Daga bisani Ammee tamike taje takawo masa abinci da drink,JUHAIFAH mikewa tayi tashiga kiching tad'au plt tazuba abinci tad'au abincin zata fita Ammee tashigo sai tawani turo baki gaba Ammee tace "ke zonan. tafad'a tareda ruko ta, "wato ke bakyaji duk abunda za'a fad'amiki bashi zai saki kiji bako?."
"To Ammee ni menayi Kuma."
Ammee tace "au mema kikayi kike tan bayata ko?." tad'aga hannu zata kai mata bugu,
tab'are baki zatayi kuka Ammee tayi saurin saketa tace "Bari Yaya Salihu yatafi zakiga abunda zan miki."
Aje abincin tayi tana fad'in "ma bazan ci abincin ba."
Ammee dai Bata cemata komai ba tayi fice warta, itama tafito tana matse ido,Abba ne yafara ganinta yace "ke menene?."
kallon Ammee tayi sai ta matse ido saiga hawaye,Baba Salihu yakalli Ammee yace "ke Halimatu mekika mata?."
Ammee tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login