Showing 30001 words to 33000 words out of 85666 words

Chapter 11 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

data lula tace "na'am."
Yace "Rabi har yaushe zaki zauna kici gaba da ganin d'iyar d'an uwanki tana kokarin shiga matsala kizuba ido kina kallo ta
bakiyi yinkurin agazawa rayuwar ta ba?
koshin magana ta tatabbata yanzunne kuke son kulla zumun tar?
kokuma nuna son kanki afili?."
tayi saurin girgiza kai,
Yace "to idan ko bahaka ba meyasa zaku dage akan abunda kuke da tabbacin bazai yiwuba?."

Yakuma duban Ammee da Goggo Hadiza da Mommyn Jos yace "Halimatu Hadiza Hauwa'u Kuma hardaku wajen bada gudu mawa wajen jefa yarin yarnan cikin damuwa,
lallai Kuma kun kasan ce masu son kanku,
yakamata ku farga daga baccin da kuke."
Gaba ki d'ayansu jikin su yagama sanyi suka baiwa yayan nasu Wanda yazame musu uba ayanzu hankalin su baki d'aya,
Baba Salihu mutum ne Mai gaskiya dakuma fad'arta aduk sanda lokacin fad'arta tazo.
Ab'an garen Sulaiman Kuma yagama zurfafa cikin tunani aransa yake fad'in "lallai so makaho ne shiyasa duk wani tsanarda JUHAIFAH take nunamin ban tab'a Jin komai arai naba shiyasa nakasa fahimtar tsanar datayi mun.
Kiran da Baba Salihu yayi masane yadawo dashi daga tunanin dayake,
Dasauri yad'ago tareda fad'in
"na'am.

Baba Salihu yagyara zaman sa sannan yace "Sulaiman misali ace kanwar ka wacce kuka fita ciki d'aya ace batason mijin da aka aura mata sai yakaiga tana fita agidan mijin tagudu ba'asan inda tajeba hartayi kwanaki masu yawa bayan an sameta akuma maidata gidan mijin atilas ta ma ta sai ta Kuma zama Anya kuwa kana ganin zata yarda tacigaba dazaman kuwa?
Idan Kuma tayarda tazaunan yakake ganin zama nasu zai kasance."
girgiza kansa yy, Baba Salihu yace "Masha Allah daka fahim ci hakan dawuri, Sulaiman kasan cewa JUHAIFAH bata son ka?."
ji yy gaban kirjin sa yayanke shiru yy yakasa bashi amsar tanbayar sa,
Baba Salihu yaci gaba "Sulaiman baka bani amsata ba, nace kasan cewa JUHAIFAH bata son ka?."

cikin sarkewar murya yace"Eh..Eh..nasani Kawu."
Baba Salihu yace "to kasan da hakan Amma kadage sai ita baka tunanin yin hakan zai iya kun tatawa rayuwar ta harya iya shiru jefata cikin wani hali?."
Shiru yy baice komai ba sai bugun kirjin sa daya tsanan ta,

Baba Salihu yamike tsaye yasaka hannu a aljuhun sa yaciro takarda da biro yamika masa Yana fad'in "karb'i ka sauwakar mata har idan kaima bason kan ka kakeba."
Abba yabud'i baki dasauri Abba yad'ago da niyar magana, Baba Salihu yayi saurin dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu yaci gaba dafad'in
"karb'i nace."
Hannun sa narawa yakarb'i takarda da biron Yana rike dashi ahannun sa hannun sa sai rawa take,
Umma Rabi tace "Sulaiman kayi abunda aka umur ceka Dan shine kad'ai hanyarda zamubi mugyara kus kuren mu baki d'aya tabbas abunda Yaya Salihu ya fad'a gaskiya ce muryarta tahard'e kamar zatayi kuka tace
"kagafar cemu Yaya tunanin mu kwata-kwata yakasa zuwa Nan mun gode maka da ka kasance jigo arayuwar mu.
Takuma duban Sulaiman tace masa "idan munason JUHAIFAH cikin halin datake kokarin fad'awa kokuma ince tafad'an, to tawanna hanyar ce kad'ai zamubi mucito rayuwar ta,
dabbas idanunmu yarufe mun kasa fahim tar hakan sai yanzu,
nagane lallai kuskure mukayi dakuma b'arna, Sulaiman nace kayi abunda aka saka!."
Hannunsa na rawa yafara rubutun yad'ago yamikawa Baba Salihu takardan,Baba Salihu yakarb'a Yana duban takardan yace "kayi nazari daka kunce igiya d'aya idan darabo watarana sai kukoma idan ta amin ce da kanta,
yad'aga takardar sama yace "ga shaidar warware auren JUHAIFAH da Sulaiman ko ayanzu ta amin ce dashi atake anan za'amaida auren Dan haka duk lokacin da ta aminta dashi za'a maida auren.

Nan parlourn yakaca me dafad'in Allah yasa hakan shiyafi alkhairi,Baba Salihu yace "amin. yadubi Mommyn Jos yace "idan kk koma kisako ta amota tadawo gida idan Kuma bazai iya riketaba yaturamin ita ni zan riketa."
Yana kaiwa Nan yamike tsaye Yana fad'in
"to ni zan koma ke Hadiza yau Zaki koma ko zakiyi musu bakunta?."
Goggo Hadiza tace "sai jibi zan koma Yaya kaima dakabari idan Allah yakaimu gobe sai katafi.
Yace "a'a yau zan koma bazan kwana ba."
Abba yamike dasauri yabi bayan sa baiyi yunkurin dakatar dashiba Dan sanin halin sa na kaifi d'aya idan yafad'a tofa tazau nu,suna fita Abba yakira direba yace "kad'auko makullin mota yanzu yakai Yaya Salihu Yelwa."
direba ya amsa dato yy saurin wucewa ya tad'auko key
Baba Salihu yashiga mota Abba yy masa Allah yatsare direba yaja suka d'au hanya,

To zamu iya cewa Allah yatsare yakai ka Yalwan Shandam Mai tarin Yalwa Wanda ya'aje mutane masu daraja da kima da sanin yakamata gari Mai Arziki da tarin ALBARKA lfy👍🏻

A parlour kuwa su Goggo Hadiza suka tasa Sulaiman gaba Wanda yakasa ko kwakkwarar motsi,suka rika basa baki da nuna masa dacewar hukun cin da Baba Salihu yayanke,
suka Kuma bashi kwarin guiwa akan yabaiwa JUHAIFAH lokaci idan hankalin ta yakwanta sai yy kokari alokacin yasamu hanyar dazaibi wajen saci zuciyar ta har itama ta soshi kamar yanda yake son ta koma fiye da son dayake matan,
yaji dad'in fad'ar hakan har yasamu dama ya iya mikewa yabar parlourn,Umma Rabi kuwa har cikin ranta ta amnin ce da hukun cin Baba Salihu domin kuwa wannan shine kad'ai hanyar samun kwan ciyar han kalinsu baki d'aya.

Ranar su Ya Al'ameen sunyi farin ciki sosai da aka dawowa Shalelen su da farin cikin ta,washe gari Mommyn Jos tayi Shirin komawa gida su Ya Mujaheed suka ce su zasu kaita gida, Dan sud'auko JUHAIFAH daga gun,
batareda wani b'ata lokaci ba suka d'au hanyar Jos..
Gudun dasuke shararawa ne yabasu damar isa da wuri afar fajiyar gidan suka yi parking dasauri suka fito a motar suka nufi cikin gidan,
tundaga kofar parlour suka fara fad'in "Shalele kina ina?.
dagudu tafito daga cikin bedroom jin muryoyin datafi kauna suka had'e atsakiyar parlourn cike da murnar ganin su tashige tsakiyar su tana tsallen murna,
suko ido suka bita dashi suna kallon yanda tasauya lokaci guda,Ya Jabeer yace "kai Shalele JUHAIFAH dama da ciwo kk baro gida?."
Ya Mujaheed yace "nimadai abunda nakeson fad'a kenan."
Mommyn Jos tace "to ai saiku zauna kuhuta tukun sai kuji dad'in yima ta tan bayoyin."
sukayi dariya tareda zazzau nawa, Zulaihat tazo suka gaisa tareda zolayar juna irin nad'an kawu da d'an Goggo daga bisani taje takawo musu abinci Dana Sha,
suka d'an tab'a abincin,
Ya Al'ameen yadubi JUHAIFAH yace " Shalele tashi kid'auko mayafin ki mutafi."
aiko kafin yakarasa tamike da sauri tanufi bedroom tad'auko mayafin ta tadawo parlourn,
Mommyn Jos takalleta da murmushi d'auke akan fus karta tace "kai JUHAIFAH ina munyi dake bayanzu Zaki komaba Amma daga ganin yayunki saiki fasa."
Itama murmushin tayi tana fad'in "ai idan muka tafi zan Kuma dawowa."
Mommyn Jos tawaro ido tare dafad'in kuma guduwar zakiyi."
Ya Al'ameen yamike Yana fad'in "ai gudu yakare muda kanmu zamu rika kawo Miki ita lokaci zuwa lokaci."
yakalli su Ya Mujaheed yace "mujenku ko?."
suka mike Mommyn Jos da Zulaihat sukayi musu rakiya har gurin mota Ya Jabeer yashiga gaba mazaunin driver dama shi yatuko su sai Ya Al'ameen yazauna gefen sa Ya Mujaheed da JUHAIFAH Kuma suka shiga baya. har saida sukaga tashin su kafin suka koma ciki.

Acikin mota Hira sosai suke cike da nishad'i Nan suke shai da mata cewa Baba Salihu yaraba auren ta,
murna sosai tayi harda 'yar rawarta daga zaune,
suka rika yi mata dariya cikeda Jin dad'in ganin kanwarsu farin cikin ta yadawo, yamma lis suka shigo gari suka d'au hanyar unguwar su Koda suka iso bakin get hon Ya Jabeer yy Mai gadi yawan gale musu get yashige ciki Yana daidaita parking suka fito direct part d'in Ammee suka nufa.
Ammee Abba Aunty Nuwaira Aunty Rukayya duk suna zaune a parlour suna zaman jiran iso warsu,
Fuskarta d'auke da murmushi suka shiga cikin parlourn Ammee da Abba suka bita da kallo har suka karaso cikin parlour,
Aunty Rukayya da Aunty Nuwaira sai zolayar ta suke tajecan kuryar kujera tarakub'e, Abba yy mata alama da hannu akan tazo inda yake, jiki asab'ule tanike tazo inda yake, yariko hannunta yazaunar da ita kusa dashi,yadub'eda Yana fad'in "Mamana bakida lfy ne?."
Tayi Mamakin Jin magana Mai taushi daga bakin Abba bata tab'a zaton haka Abba zai tareta da shiba tayi zaton gamuwar su da Abba bazatayi dad'i ba,
sai gashi Yana yimata magana cikin nuna kulawa,
Sai ta girgiza Kai alamar a'a.
Abba yajin jina Kai aransa yake fad'in lallai kwan ciyar hankali ma wani abune jibi yadda yarinya tasauya lokaci guda,saiyaji tausayin d'iyar tasa yalullub'e shi,
Ammee ma ab'an garen ta tausayin d'iyar tata yagama cikata,
Hira sosai suke cikeda nishad'i Abba da Ammee sai janta suke da Hira irin Mai nutsar da zuciyarrana tun tana d'ar-d'ar har tasaki jikin ta,su Ya Al'ameen suka mike danufin tafiya part d'insu domin sud'an huta gajiyar hanya sai itama tamike Abba yace "ina zuwa Mamana?.
Komai batace ba sai kallon yayun nata tayi,"Zaki bisune?.cewar Abba Kai tagyd'a alamar Eh,yace "to jeki." dasauri tabi bayan su Koda suka fito waje Ya Al'ameen yace suje part d'in sa wucewa da ita sama yy d'aya daga cikin d'akunnan dasuke sama yace tashiga tayi zaman ta, tundaga ranar zaman JUHAIFAH yadawo part d'in Ya Al'ameeda lokacin Aunty Rukayya tahaifi su Hassan da Husain suna jarirai,
Sai yazamo rainonsu yadawo hannun JUHAIFAH saboda mugun son datake yimusu.
Tun suna jariran take d'ibansu surikwana tare harkuma yanzu dasukeda shekaru 3 aduniya kwana sabar shakuwar su idan kagansu zaka rantse ita tahai fesu dad'i dakari Kuma gasunan dasuke Kiran ta dashi Mamy.

Bayan wasu d'an lokuta Amma takira wata nurse tazo har gida tayiwa JUHAIFAH gajin ciki Nan nurse d'in keshaidawa Amma batada ciki hankalin Amma yadad'a kwanciya Dan dama tun dawowar ta takeyimata kallon Mai ciki,
Zuwa lokacin rayuwar JUHAIFAH tasauya tadawo JUHAIFAHn ta nada kyanta farinta duk suka dawo ramar datayinna duk babushi yanzu hankalin ta yakwanta gatan datake samu ayanzu yazarce na baya, Sulaiman kuwa yanzu yasamawa kansa salama yalallashi zuciyarsa akan son dayakewa JUHAIFAH dan ko sau d'aya bai tab'a yunkurin zuwa bikoba,
Har Kuma lokacin bata tab'a fad'awa wani cewar 'yan fashi sunyi mata fyed'e ba ta bar abun azuciyarta dukda wani lokacin idan tatuna hankalin ta namugun tashi haka zata yita lallashin kanta harta samu nutsuwa.

Wanna shine labarin JUHAIFAH

*********************

Cigaban labari


Yau sauran kwana uku auren MAHFUS da JUHAIFAH damisalin karfe 12 nadare ringing d'in wayarta yatada Tamika hannu tad'au wayar tareda kallon screen d'in wayar dasauri tamike zaune ganin numbern dayake kiranta ko turamata sako wani zuciyar yace ta'aje wayar kada tad'auka wata zuciyar Kuma tace d'auka idan yafad'a Miki badaidai ba kema kifad'a masa tayi picking na call d'in ahan kali takara wayar akunnen ta,saiji tayi yace................



08034690723



Mommyn Twins ce
*____________________________________*


BAZAWARACE'ITA




*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*




By
Rasheeda S Director



👉🏻WANNAN SHINE LAST ~FREE~ ~PAGE~ INA IDAN KA/KI NABUKATAR CIGABAN LABARIN SAIKI SANBAD'OMIN NAIRA D'ARI 200 KACAL👌🏻 ZAKIJIKI A GROUP INDA ZAKI SAMI CIGABAN LABARIN
TUNTUB'I WANNAN NUMBER
08034690723
IDAN KINA BUKATAR HAKAN🤗
_______________________________



🅿️10




Yace "saura kwanaki uku suka yarage Miki, kiyi tattalin wad'anna kwanakin Dan kada su sub'uce Miki batareda kin moresu ba,bayansu kuwa kunci ne."
Dasauri tace "waye Kai?mekake nufi dani?wlh duk abunda kakeji dashi Nima gaban nad'auke." yace "kinji' tsorone?ki adana kallomin ki watakil Nan gaba suyi Miki amfani." Yana kaiwa Nan yakashe wayar,ciro wayar tayi akunnen ta tana binshi da kallo saikuma tayi wurgi da wayar asaman gadon tasanya hannunta cikin baki taciza yatsar ta hakika tana matukar jin zafi aduk sanda yajefeta da wad'anna muggan kalaman masu masifar rikita ta, tarasa tayadda zata fara fassara kalaman sa,
Tad'au tsawon lokaci kafin tasami barci yakuma d'aukarta.

Sosai ake Shirin biki
Gidan yacika da 'yan'uwa mutanen Yelwa sun iso Mommyn Jos ma da Zulaihat sunzo su Umma Rabi duk sun hallara agidan.

Zaune take ad'akin kamar kullum
murd'a handle akayi tayi saurin kallon kofar
Dasallama Aysha tashigo d'akin rikeda babban laida ahannunta ta isa tazauna bakin gado kusa da ita, tace "JUHAIFAH ko sallamar ma baki amsaba bare kicemin sannu?."
baki tatab'e madadin tabata amsa sai cewa tayi "meye wanna."
tafad'a tareda nuna laidar data shigo dashi, Aysha tace "kayan kine d'azu Ammee takirani tace naje na anso agun tela."
JUHAIFAH tayamusa fuska tareda kawar da kanta gefe,
Cicciro kayan tayi acikin laidar tarika d'agasu tana fad'in "Kai gaskiya wlh Ammee tasan kalar kayan dazasu dace da ke kallifa kigani gaskiya ran bikinnan sai anyi dagaske kafin a'iya ganeki."
Cikin hasala tajuyo tana fad'in "narantse idan kk Kara kawomin wata maganar biki sai mun kwashi 'yan kallo dake,Kuma kikwashi wad'anna kayan kifita min dasu ad'aki."
Tana kwiwa Nan tamike tsaye tazo jikin window tazuge labulen windown gefe,tad'an saka hannayen ta tadafa jikin window tana kallon kasa,tacikin glass,
Aysha tashiga mayar dakayan cikin laidar tana fad'in "in kwashe inkai ina?ai saidai insa Miki su acikin wardrobe."
Daga inda take tsayen tace "to wlh kisaka kigani idan ban kwashesu nawatsar dasu ta window d'innan ba."
Aysha dai shiru tayi batace komai ba tagama maida kayan cikin laidar sai tagyara masa zama akan gadon.
Har ta bud'i baki zatayi wa Aysha magana sai Kuma tayi shiru takurawa get ido lokacin da Mai gadi yawan gale shi,
Jirin tsadaddun motoci ne suka kusa hancin su cikin gidan ahan kali suke shiga cikin gidan d'aya bayan d'aya, zafafan motoci guda biyar suka paka a farfajiyar gidan,ganin yanda tamaida hankalin ta gaba d'aya agun yasa Aysha mikewa tazo jikin window,
Asannu aka bud'e motar farko wata farar mata tafito da murmushi d'auke akan fuskarta,watama takuma fita agefen maizaman banza, motar dake bayan motar farko shima matane guda hud'u su kafito aciki,kallo d'aya zakayi musu kasan sun jiku da naira,kodaga suturar jikinsu,
Sauran Motoci uku kwa diraibobin dake Jan motar ne Kawai aciki suma fitowa sukayi,
Matar data fito da farkonnan tajuyo inda wad'anna maza guda ukun suke tace "kufito da kayan kushigar dashi ciki."
Suka amsa da to.sanna kowannen su yabod'e motar daya tuko suka fara fifffito wa da kayan dake cikin motocin.

Ya'ilahi ya'lillahi, wasu zuka-zukan akwatuna ne aka rika shiga dasu part in Ammee,kowacce mota guda nad'aukeda set in akwati d'aya dakuma manya manyan gana masgo guda uku acikin sa.
Matannan suna tsaye harsai da aka gama shiga da kayan kafin suka rufawa kayan baya.
Dasallama suka shiga cikin parlourn,Wanda mutane ke cike dam cikin parlour,
Aka Amsa musu sallamar tareda yimusu maraba da zuwa aka basu gurin zama suka zazzauna Nan akashiga gaggai sawa cikin sakin fuska wajunansu harda d'an hirarsu kamar wanda Daman can sunsan juna,Nan da Nan akacikasu da drink,
D'aya daga cikin matan tace "munkawo lefen surukar tamuce aduba idan akwai abunda Babu sai ayimana tuni sai mu kawo kodaga Nan zuwa gobene."
tafad'a tareda nuna akwatunan,
Umma Rabi tace "ato madalla maraban ku."
matar tace "tomu zamu koma sai mun jiku."
Umma Rabi tamike tsaye tace "Rukayya Nuwaira Zulaihat kuzonan."
Tafad'a tareda shigewa wani d'akin dake gefen kiching,sukabi bayan ta, kayakin tsarabar dasuka tanada domin masu kawo kaya,tace dasu sud'iba sufito dashi sukai musu mota,manya manyan langunane Wanda aka shakesu da donut da meat pie dadai sauran su sai drinks kala-kala suka Rika kwasa suna Kai musu mota,Umma Rabi takomo parlour taciro kud'i ajakarta naira dubu d'ari uku Wanda shima aka tanada tukuici gamasu kawo lefe,Tamika musu ta na fad'in "gashi wanna tukuicin kune mungode sosai."
Suma sukayi musu godiya suka tafi.

Bayan tafiyar su,
Goggo Hadiza da Mommyn Jos dawasu kannen Ammee guda biyu da Maman Aysha suka taso suka shiga sassauke akwatunan Umma Rabi dawasu 'yan'uwan nasu sukuma gana mazgon suka shiga bud'ewa, gana masgon farko zallan takalmane acikin sa sadaddu, bazan iya kiyaste yawan suba, nabiyu kuwa jakukkunane acikin ta dam, na uku sarka da 'yankunne ne dam cikin ta,
na hud'u kayan kwalliya ce, na biyar turaruka ne, nashidan Kuma sleeping dress ne kala-kala cikedam,
Cirowa suka farayi ganin yawan su yasa suka daina cirowar saidai koka yazo yaleka cikin ganan.
Su Goggo Hadiza suma Koda suka bud'e akwa tunan sai tsayuwa kawai sukayi tareda zuwaba kayan cikin sa ido,lallai ba shakka naira tayi kuka anan tabbas naira na aljuhun maishi wanikayan sai amale.
Dasauri Zulaihat ta'aje wata jakar data d'auka taketa juyashi ahannunta tafice daga parlour,tanufi part d'in Ya Al'ameen
Tana shiga direct d'akin' JUHAIFAH tanufa tunkan takaraso take fad'in "JUHAIFAH lallai yau nadad'a tabbatar da baki amsa sunan Shalele abanza ba." tatura kofar tashiga har'alokacin tsaye Aysha take ajikin windown ita Kuma tana zaune akan gado,
Zulaihat takaraso cikin d'akin' da sassarfa tahayo gadon tarun gumeta,tace "Kai gaskiya JUHAIFAH natayaki murna wlh tunda nake ban tab'a ganin kayan aure irin nakiba duk bin kwakkwafina nakasa kiyaste yawan adadin kayan,
Saidake mata agidan MAHFUS Tukur Shali,idan bashi d'inba bazai iya narka irin wannan dubbanin naira akan kayan lefe kawai,ai saisu manyan Wanda zasuta Zare naira basusan suna ciraba,Allah dai yasamu amada macin ki."
Tureta tayi ajikin ta tareda wasa mata harara tace "uban wa yace Miki ni matarsa ce?akan wani can siyarsa kirika nukurkusani,Toni ina ruwana ma da kayansa."
Zulaihat tace "ke matarsa ce mana abinda yarage shine ashafa fatiha kawai jama'a sushai Dan mudai mun rigada mun shaida saura shaidar jama'a kawai yarage mukai mishi ke."
Cikin hatsala da zancen Zulaihat d'in tace "to uwata tobasai kizo kijani kikai mishi ni d'in ba,narantse dakeda Aysha zamuyi bura'uba daku idan baku daina kawomin kwatan kwacin irin wannan zancen ba Mttssww."
Taja dogon tsaki takwanta tareda juya mata baya,
Zulaihat suka kalli juna da Aysha sai suka kwashe da dariya,
Aysha tace "Zulaihat duk wad'annan kayan danaga anshuga dasu part in Ammee duk natane?."
Zulaihat tace "wlh duka natane kinsan Allah gajiya nayi da kirga kayan shine nataho nan."
Aysha tace "a bazanyi mamaki ba tunda kayan daga tsatson Tukur Shali yafito wannan bakomai bane daga cikin dukiyar su."
Zulaihat tace "ai kam wannan haka yake waye baisan Tukur Shali ba afad'in kasarnan harda ketare."
Afusace JUHAIFAH tajuyo tana fad'in da Allah kufita kuje waje kuyi surutun naku ni kuna cikamin kunne."
Aysha tace " Zulaihat taso muje nabaiwa idona abinci."
Zulaihat tamike tana fad'in "aikam yau sai idon naki yace yakoshi da kansa muje dama akwai wasu akwa tunan daban leka cikin suba, kinga daganan sai munimi angwayen kinga har yanzu basuzo sun caske Mana kud'ad'en Nan ba Kuma yakamata a ce yaune zamuje su gyaran gashi da sauran su Amma ace haryanzu amarya batayi kod'aya daga cikin suba."
Aysha tace "to ta'ina zamu fara nimansun?."
Zulaihat tayi shiru nad'an wani lokaci sanna tace "Kuma hakanefa Amma to zamu iya samunsu ko tawayane basai mu kirasu tawayar JUHAIFAH ba."
Zunbur tamike tafara binsu da wani irin kallo,sannan tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login