Showing 54001 words to 57000 words out of 85666 words

Chapter 19 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

kibita kutafi." Shiru JUHAIFAH tayi tareda sauke wayar tamikawa Mommy jiki asan yaye,menene yasa Ammee zatace tabita gidan,
To me zataje tayi agidan.
Mommy tace Zahara "je maza kishirya Mata kayanta acikin akwati,
ta'amsa da to ta'is tabud'e wardrobe tashiga shirya Mata kayanta cikin akwati Saida tacika manyan kwatuna uku tam.
Har lokacin JUHAIFAH natsaye Alla Alla take tayi tabar gidan Dan gani take idan tazauna ma kamar ci gaba da zaman za'tayi,gaba ki d'aya gidan ya fice Mata arai bata kaunar takuma bud'e idanunta taganta cikin gidan.
Zahara tarika Jan akwatunan tana kaisu cikin mota,tana gamawa Mommy tariko hannu JUHAIFAH suka fito,tabud'e Mata sit in gaba tace tazauna Zahara Kuma tashiga baya Mommy tashiga mazaunin driver taja motar suka bar gidan,
JUHAIFAH naganin sun fita tasauke wani nannauyan ajiyar zuciya,wani'irin dad'i yaziyarci rayuwarta,hakika wannan gida yazame Mata tamkar kabari kamar yadda yasha fad'a Mata kafin shigowarta cikin sa.
Suna isa gidan Mommy tadai-daita parking suka fito, Zahara tashiga fito da akwatunan ma'ai katan gidan suka kwasa suka shiga dasu ciki.
Mommy takuma riko hannun JUHAIFAH suka nufi cikin gidan,
Itadai binta kawai take badun taso ba.
A parlour Mommy tazaunar da'ita saman kujera,
Mommy takirawo wad'anda suka shigo da akwatunan tanuna musu d'akin dalokacin auren su aka ajeta ciki
tace sushiga dashi cikin d'akin,ita Kuma tashige kicking taje tahad'owa JUHAIFAH abinci tadawo parlourn ta'aje gabanta tace taci.
JUHAIFAH dai bin abincin tayi da ido Dan Bata tunanin zata'iya ci,
Mommy tatilas tt dole Saida tad'an tab'a abincin kad'an,
Sannan tace taje d'aki tahuta,
Sanda Mommy taga shigarta d'aki
Kafin itama
tamike tashige bedroom inta.
Zama tayi bakin gado tashiga lalub'o numbern Daddy,
Daddy na hanyarsa na tahowa gida Kiran Mommy yashigo wayarsa,
yy picking na call in,tareda karawa akunnensa Yana fad'in "kamar kinsan Ida hanyar tahowa gida."
Mommy tace "to shikena sai ka'iso."
Yanayin yanda tayi mahanar kasan tana cikin damuwa yasa
Daddy saurin cewa "wani abunne?"
Tace "a'a sai ka iso."
Takashe wayar cikeda takaicin abunda MAHFUS ya'aikata.

Daddy kuwa narikeda wayar Jin tayi shiru yasashi fad'in "hello.hello kina jina" Nan ma Shirun yakuma ji
yasauke wayar ganin takashe yadubi driver yace "yi sauri mu'isa gida."
Cikin mintuna kalilan yakaisu gida
Suna isa direct d'akin Mommy Daddy yanufa,
Har lokacin tana nan zaune abakin gado,
Dasauri yanufi inda take zaune yanafad'in "hajiya meke faruwane?"
Mika Masa takardan tayi batareda tace komai ba,
Daddy yy saurin karb'ar takardan yashiga warwarewa yanafad'in
"To shikuma wannan namenene?..cak Daddy yahad'ye sauran maganar sakamakon yin tozali da abunda kecikin takardan,hannunsa nab'ari yamaida dubansa kan Mommy yace "what!saki,shi MAHFUS in dakansa yarubuta wanna!."
Tace "kwarai kuwa".
Nan Mommy tashiga bashi labarin yanda akayi hartasan yy sakin dakuma yanda sukayi da Ammee sannan tad'aura dafad'in
"yanzu hakama mun taho da'ita."
Yace "lallai kuwa yaronnan yatafka babban kuskure arayuwarsa ni zaiwasawa kasa a'ido,inayake yazo yy gaggawar mayar da'ita tun kafin yahad'uda mummunar b'acin raina".
Yy saurin ciro wayarsa yalalub'o numbern MAHFUS.
Dasauri Mommy tace "kada kace mishi yamai data tunda bayaso abarshi kawai,ai dama ninace inaso to yanzu Nima nace nahakura da yin auren nasa yy zamansa ahakan,Dan Allah Daddy kada kace yamaidata."
Tafad'a tareda had'e hannayenta biyu.
Daddy yajin jina Kai Dan yasan dagaskenta tayi maganar,saidai yy mmkn abunda yasa tafad'i hakan,ammadai bazai kyalesaba dole sai yanuna Masa b'acin ransa akan abunda ya'aikata.


Ab'angaren MAHFUS kuwa Yana barin gidan tafiya kawai yarikayi a mota batareda yasan inda zashiba,Yana cikin tafiyar nasa Kiran Daddy yashigo wayarsa,yasan za'ayi hakan Dan haka baidamu da abunda zaiji daga bakin Daddy ba,yad'aga Kiran.
Shiru yy Yana sauraran fad'an da yake yimasa yatabbata irin yanda Daddy yake maganar idan da suna kusane da bb abunda zaisa bai Kai masa hannu ba,
Kalmomin dasuke fita daga bakin Daddy masu zafi da nuna tsantsar b'acin rai tunda yake bai tab'a Jin kwatan kwacin irinsu sun fita daga bakin Saba,lallai yau yasan yakure b'atawa Daddy'n sa rai,Amma shi gani yake abunda ya'aikatan shine dai-dai,
Tunda Daddy yafara fad'ar MAHFUS baice kala ba,ya gangara gefen titi yakashe motar, harsaida yagama fad'ar yakashe wayar,kafin shima yaja motar yacigaba da tafiya.
Daddy nasauke wayar yajuya afusace yabar d'akin
Bedroom insa yashiga yad'an watsa ruwa yashirya yafito ya umurci driver daya kaishi wuse
Gidan mahaifan JUHAIFAH,Koda ya'isa Abba yy Masa kyakkyawar karb'a bayan sun gaisa Daddy ke shai damasa abunda yafaru, Abba yace Ammee ta sanar Masa da komai Dan haka bb komai sun karb'i hakan amatsayin kaddara,
Daddy yayita bashi hakuri daga karshe yanimi alfarman cigaba da zaman JUHAIFAH agidansa zuwa wani d'an lokaci kamar yanda matarsa tanema daga farko,
Abba yace bb damuwa Allah yatabbatar Mana da alkhairi.
Sukayi sallama Daddy yahayo matar suka koma gida.


Ab'angaren MAHFUS kuwa
Haka yarika yawo acikin gari sai daf magriba yakoma gida,a masallaci yatsaya Saida yy sallar magriba da isha'i kafin yashigo gidan, wanka yy sannan yy shirin bacci,juyi yarikayi akan gado gaba kid'a yarasa meke yimasa dad'i jiyayi gabad'aya kasar tafice Masa arai,adaren yasa aka shirya Masa barin kasar washegari damisalin karfe 4 na asuba jirginsu tad'aga.

JUHAIFAH nakwance akan gado Mommy tashigo d'akin,tamike zaune tareda gaida Mommy ta'amsa cikeda kulawa da sakin fuska,tazauna kusa da'ita tareda dafa kafad'arta
tace "JUHAIFAH kidai na Zama ke d'aya Zama Kai kad'ai Yana sanya tunanin da damu,sannan Ina rokanki Dan Allah kicire komai aranki kid'auka kamar komai bai faruba,kisake ranki da jikinki kiyi walwalarki kisa aranki cewa nanma gidan kune, duk abunda kk so kiyi in Sha Allah komai zai wuce,taso muje muyi break."
Tariko hannunta suka fito parlour,
Asaman dinning suka iske Zahara tana zaman jiran fitowarsu,
Bayan sun zauna Mommy tace "to kowa yy saving in kansa kalan nazubawa wani yace yamasa kad'an nidai Bari nasakawa kaina kowa yy takansa."
Zahara tace "Kai Mommy tun d'azufa nake jiranku junwa duk tagama cin yeni ni yakamata kifara samin."
Takarashe maganar tana dariya
Mommy tace "um idan bakuyi saving in kankuba Ina gama cin wannan duk zan had'a nacinye saidai kushiga kicking kusake girka wani."
Zahara tad'au plt tafara zubawa tana fad'in,
"Da alama Aunty JUHAIFAH ce za'abari da shiga kicking."
JUHAIFAH tayi murmushi tareda bin kulolin abincin dasuke jere kan dinning in kuloli biyarne Kuma ko wanne nad'aukeda nau'in abinci daban d'aukar plt tayi
Tayi saving in wainar kwai da Dan Kali tahad'a tea tafara ci ahan Kali.
Haka Mommy tarika janta da wasa ahakan kuwa har tasamu taci abinci Mai yawa,bayan sun gama suka dawo parlour JUHAIFAH tamike zata koma d'aki Mommy tace tadawo tazauna suyi Hira,
Tadawo tazauna suna kallo suna hirar wacce karfin hirar Mommy ce da Zahara takan sa Baki jefi-jefi,sunan zaune har lokacin sallar azahar tayi suka shige d'akunansu domin yin sallar,bayan JUHAIFAH ta'idar sai tahaye gado Dan son yin bacci.


Tundaga ranar kullum a parlour suke wuni Mommy Bata tab'a barin JUHAIFAH tazauna ita kad'ai,idan Kuma mommy tatafi wasu harkokin ta, to suna tareda Zahara.
Duk wata kula daya dace tana samu agun Mommy,wani lokaci idan Mommy zata shiga kicking takan cewa JUHAIFAH tazo suje ta tai maka Mata dawani abun.
Duk dacewa akwai ma'ai kata masuyin girki agidan Amma Mommy Bata tab'a yarda Daddy yaci girkin masu aiki dakanta take shiga kiching tagirka Masa,ananne Mommy tafahimci yarinyar bakaramin girki ta'iyaba,taji dad'in hakan aranta bakad'an ba.tunga lokacin idan zata fita saitacewa JUHAIFAH tayi musu girki kafin tadawo.

YAU kimanin watan JUHAIFAH d'aya agidan zuwa lokacin tasake har takan fito da kanta suyi hira,kawarta Aysha ma takanzo suwuni agidan kafin takoma.

Ab'angaren MAHFUS tunda yatafi kullum azuba idoyake Yana zaman jiran Kiran Mommy tunda har Daddy ya'iya Masa fad'a irin yanda yamasa lokacin faruwan sakin yasan fad'an da Mommy zata yimasa saiyafi na Daddy'n,Amma sai yaga akasin hakan kodaidai da sau d'aya Mommy Bata tab'a yimasa Koda flashin ne bare Kira,
Dafari yaji dad'in hakan sai Kuma daga Bata dayaga kwanaki sunata ja har Kuma lokacin batabi takan Saba, sai yaji duk ba dad'i Dan yasan Mommyn nasa tad'au fushin dazafi,
Shirin zuwa Nigeria yasoma yi yashirya karb'ar duk wani hukuncin da Mommy zatamishi,
Ranar asabar damisalin karfe biyar na yamma yasauko Nigeria,
Yakira Tanimu yazo yad'au keshi a airport,
Ko gaisuwar da Tanimu yake yi mishi bai iya amsawaba gaba kid'aya han kalinsa yakoma gida dakalar hukuncin dazai je yatar agidan.
Sai cewa Tanimun yy gidan Mommy zai kaishi yanzu-yanzun Nan.
Suna isa gidan yafito a motar yanufi ciki yayinda kirjinsa ke bugawa.
Da sallama d'auke abakinsa yashiga parlourn,
Mommy Zahara JUHAIFAH duk suna zaune,gabaki d'ayansu suka d'ago tareda duban Mai sallamar,
Wani'irin bugawa kirjin JUHAIFAH yy dasauri takawar da kanta,yayinda zuciyarta ke Karan tomata "shin kin mance dacewa Nan gidan sune meyasa su Ammee zasu zab'i zamanki anan gidan bayan wanda yahad'an yaraba,
Ab'angaren MAHFUS kuwa bakaramin mmk yy daganinta acikin gidanba,"to meya zaunar da'ita bayan nasallameta." Yy kwafa tareda karasowa ciki,yazauna kan kujera d'an nesa da Mommy kad'an,
"Saikace Kai katuka kanka kawani sake gabad'aya to yi maza kaje kawatsa ruwa Dan kaji karfin jikinka."
Maganar Mommy tadoke kunnuwarsa,
Dasauri yad'ago saiyaga tana dubansa tareda yin murmushi,
tsananin mmk yabai baye zuciyarsa,waishin dagaske Mommy ita take fad'a Masa wanna maganar shida yagama sadakarwa da shiryawa karb'ar hukun ci daga gareta.
katse Masa tunani tayi dafad'in "Bari Zahara takai maka abinci idan kayi wankan sai kaci.
Shidai bin Mommy da ido kawai yake harya Mike tsaye..........


Kuyi maneji ido yafara cewa bai yardaba Yasin dishi-dishi nake gani yanzu🤗


🅿️21


Yawuce bedroom insa cikeda mmkn Mommy bai tab'a sammanin Jin magana Mai sanyi daga bakin ta a'irin wannan lokacin ba.
Bayan yawuce Mommy tadubi Zahara tace "jeki Kai Masa abinci."
Zahara tamike itama zuciyarta cikeda mmkn yanda taga Mommyn takarb'i yayan nata Bata tab'a sammanin hakan ba,tashige kiching tad'ibi abincin takai Masa.
Mommy lura tayi da yanda lokaci guda yanayin JUHAIFAH yasauya,sai tayita janta da Hira da wasa danson kawar Mata dayanayin data shiga,
Itako JUHAIFAH jitayi zaman parlourn ya'isheta idan tayi yunkurin mikewa sai Mommy takawo wani hirar nadaban,haka zata koma tazauna,Saidaf magriba kafin suka bar parlour JUHAIFAH tunda tashiga bedroom Bata Kuma fitaba,sai washe gari data fito Taya Mommy had'a break shima suna gamawa Takoma d'aki,tatub'e kayan jikinta tashiga bathroom Mommy data gama kimsa sauran abubuwan tabiyota d'akin dakan ta lokacin tafito daga wankan Mommy tace tashirya tafito suyi break.tace to Mommy tafita itakuma ta'isa gaban mirror,
Simple makeup tayi tashirya cikin riga da sket na atamfa,Zama tayi bakin gado zuwa can Kuma tamike tafito Zahara kad'ai ta'iske kan dinning,Mommy na d'akin Daddy Dan yau Daddy nagida bai fita dawuriba.
tazauna sukafara break,tana d'ago wa tahan goshi Yana saukowa daga saman matakala tayi saurin kawar da kanta,aranta tace "shikuma rayuwarsa takare asama."
Yana sauka ya'isa cikin parlour yazauna,Yana zama Mommy nafita daga bedroom in Daddy takaraso inda yake,yagaisheta ta'amsa cikin sakin fuska,cikin kula Mommy tace "Bari nahad'o maka breakfast."
Tahauro dinning tahad'a Masa abinci kala biyar tad'aurasu kan tray,tad'auka takai Masa inda yake hakimce kamar wani sarki,
Tana Kai Masa takoma bedroom in Daddy.
Ahan Kali JUHAIFAH tamike tasauko daga saman dinning in tabi tabayan kujera tashige d'aki.

Damisalin karfe uku na yamma JUHAIFAH ce a kiching tanata kokarin had'a abincin dare,yau ita d'ayace a kiching in Mommy tatafi unguwa.
wayarta dake d'aure kan durowar kiching in tafa tsuwa alamar shigowar Kira ta'isa inda wayar take tad'au wayar tana duba Mai Kiran nata sunan Aysha yabayya afuskar wayar tagyara tsayuwar ta tareda picking call in,takai wayar kunnenta tana fad'in "hello Aysha ykk."
Daga cikin wayar Aysha tace "lfy Lau gamu ahanyar zuwa gidanku."
JUHAIFAH tace "wani gidan namu?."
Aysha tace "inda kk Mana."
"Gidansu dai nikam gidan mu na Wuse,kedawa kuke zuwan?." cewar JUHAIFAH
Aysha tace "nida mutumin ki Salim B.A yanzu fitowata muka had'u dashi ni banma ganeshiba har Saida yymin magana
Bakiga yanda yy wani katoba,
wai saidai nakawo shi gidan ki kugaisa yanzu hakama
muna hanya."
Dariya JUHAIFAH tayi tace "dagaske yaushe yazo kenan?."
Aysha tace "wlh ban saniba saidai idan muka iso tanbayeshi."
Tace "to sai kun'iso."
Tasauke wayar,
tana ci gaba da dariyar tuno da lokacinda suke makaran ta.
Salim B.A tare sukayi primary dasu
JUHAIFAH ajinsu d'aya basa shiri da
JUHAIFAH ko kad'an kullum idan
suka zo makaranta sai malamai sun rabasu fad'a Salim irin yarannanne MASU zolayar tsiya,har ya mannan Mata wani suna
Dazarar yashigo aji zai fara fad'ar JUJU aduniya JUHAIFAH tatsani sunan nan,
shikuma yace gaban yad'auke,idan yafara zolayarta yana fad'in JUJU sai tad'au jakar
makaran tarsa tayita jefi da litattafan sa,Aysha tayi tayi taraba fad'an takasa har sai malamai sunzo
kafin suraba
wannan fad'ar,gobe Kuma bashi zai Hana idan suka Kuma had'uwa suyi fad'an ba,
har sukazo primary 4 suna tare zuwa lokacin koya zolayetan ma Bata
damuwa sai yabaro sit inda yake yadawo nakusa da'ita yazauna yaci gaba da zolayarta,har abun nashi yadawo Bata dariya Dazarar yafara sai takama yi Masa dariya idan yace Mata JUJU sai tace Masa Mai kan kwai,lokacin da sukaje primary 5 suka dawo shiri sosai da'ita har yazamana sit insu d'aya,lokacin akayiwa baban sa transfer zuwa Rivers State sana diyyar rabuwarsu kenan.

Dasauri JUHAIFAH tafito daga kiching rike dawaya akunnen ta tana fad'in "har kun'iso to gani fitowa."
Dasauri tashige d'aki tad'au gyale ta yafa akafad'ar ta tafito,
Can tahangosu Salim nakan mashin insa Aysha Kuma natsaye,tunkan takaraso inda suke Salim yafara dariya Yana tafa hanna yensa Yana fad'in
"JUJU kece haka?".
takaraso inda suke itama tana dariya tace
"Maikan kwai kaima Kaine haka kadawo wani babba kayi wani lukutu dakai."
Aysha tace "ai wlh Nima dakyar na'iya ganeshi badun yy min magana bama dasaidai nawuce shi abina."
Salim yakallesu yace "aini girmanku yafi bani mmk dubi yadda JUJU tawani katuwa wai har aure kkyifa,yaushene kk daina kwasan littattafai na kina jefi dasu innan."
Dariya sukayi gabaki d'ayansu, JUHAIFAH tace "todai yanzu kuzo mushiga ciki tun."
Salim yace "a'a wlh wucewa zanyi bakiga jakata abayana ba yanzu haka Dad Ina jirana yake da yamman Nan zamu bar garinnan,badun had'uwar damukayi da Aysha bama ai da inaga yanzu mun d'au hanya,ita take fad'a min wai kinyi aure,nasha mmk wai JUJU ce tayi aure,nace takawoni gidan ki mugaisa kafin mutafi."
Yatada mashin insa Aysha tace "bafa tafiya zakayi kabarni ba maidani inda kad'au koni zakayi".
Tagyara tahaye bayan mashin d'in
"Au kema tafiyar zakiyi?."
Cewar JUHAIFAH
Aysha tace "aikan Mama nafito fa shine ya ciccib'oni mukayiwo Nan."
JUHAIFAH tabud'e Baki zatayi magana motar MAHFUS yashigo cikin gidan
Kawar da kanta tayi tamaida kallonta ga su Aysha
tace
"Allah sarki gaskiya naji dad'i sosai Mai kan kwai an girma ashe tunda har aka iya tunanin azo agaidani."
Salim yace "shikenan JUJU an girma yanzudai andaina jefi da littattafan mutane."
Tace "to ya'isheka haka Mai kan kwai inba so kk muyi fad'a ba."
Takarashe maganar tana dariya shima dariyar yy yajuya mashin insa Yana fad'in "to sai wani lokaci kuma."
Ci gaba da dariyar tayi tana d'aga musu hannu har suka fice agidan,
Sannan tajuya tanufi ciki,
tana shiga cikin parlour ta tadda MAHFUS tsaye tazo zata wuce tagefensa yy saurin Shan gabanta cikin tamke fuska tareda binta da mugun kallo yace
"Idan kinsan maza Zaki Rika kawo Mana gida to kikoma gidan ku kirika Kai mazan can!."
Yafad'a yanawani huci, kallo d'aya tayi Masa sai tarab'e gifensa tawuce batareda tace Masa komai ba,shikuma yajuya yanufi bedroom insa.
Zahara da fitowarta kenan taja tatsaya sakamakon Jin abunda yake fad'an,Yana wucewa dasauri tabi bayan JUHAIFAH ta'iske ta tana had'a kaya cikin akwati,dasauri ta'isa inda take tarike hannunta tana fad'in
"Aunty JUHAIFAH me kkyi haka?".
JUHAIFAH tace "Zahara kyaleni gida zan tafi,ance Masa bama da gidane kokuma ance Masa dason Raina nake zaune muku agidan."
Zahara tace "haba Aunty JUHAIFAH Dan yace Miki haka saikice Zaki tafi gidan ku kadafa kimance bashi yakawo ki gidannan ba Kuma yanzu bazaman sa kk ba Mommy ce takawoki da kanta,tunda ba'ita tafad'a Miki hakan ba ai inaga baikai yadame kiba."
"Zahara Nan gidan kune yanada iko akai shiyasa yafad'i hakan, to mezai sani naci gaba dazama gidan bayan Nima inada namu gidan."
Zahara tace
"Dan Allah Aunty JUHAIFAH kidaina fad'ar haka, Dan Allah kimance dashi shi yafiye surutu ke Baki ganin ko inda yake bana zuwaba Amma kullom sai yanemo laifin da zai kakabamin,Nan da kwana kad'an ma Zaki nimeshi kirasa danshi kamar maintashi muje mu yake."


JUHAIFAH dai shiru tayi, Zahara tamam mayar dakayan kafin tafita,
Ita Kuma tamike tashige bathroom.
Bayan tafito daga wanka tasaka kaya sai tayi Kwan ciyarta har Saida taji muryar Mommy kafin tafito tayi Mata sannu da dawowa takoma ciki.
Koda lokacin cin abincin dare yy Mommy tasa Zahara taje takira wota,Koda Zahara tazo takiratan tacewa Zahara tana zuwa Bari tayi sallar Isha.
Bayan ta'idar da sallar tafito parlourn,zaune ta'iskesu tsakiyar parlour Mommy Daddy MAHFUS da Zahara,ji tayi kamar takoma ahan Kali ta'isa tazauna kusa da Zahara,
Tayi kasa da kanta taredafad'in "barka da dare Daddy."
Daddy yad'ago da sakin fuska yace "yauwa JUHAIFAH barkanki."
Kallonta
Mommy tayi sai taga yanayinta ya sauya,sai tamaida dubanta ga MAHFUS Wanda ketacin abin cinsa kamar baya gurin,
Takuma maida idanunta kan JUHAIFAH,tazuba Mata abinci tatura matashi gabanta tace "sa hannu kici,asan yaye tasaka hannu Dan batason tarika jayeyya da Mommy'n batawani ci meyawa ba tacire hannunta,
Mommy tace "wai kin koshi kenan JUHAIFAH?."
JUHAIFAH tace "Eh". tamike tsaye
Mommy tace "inakuma zakije?."
Ad'an marairaice tace "zanje nakwan tane bacci nakeji."
Mommy tace "to jeki kwanta Saida safe."
Ta'amsa da tom ahan Kali tawuce tashiga d'akin, Kwanciya tayi kan gado tarufe idanunta yayinda maganar MAHFUS nad'azu yarika yimata yawo azuciya,wato yanaganin dan tazauna agidannan Yana tunanin yasaketa' Taki tafiyane idan bahakaba tomeye tufinsa?,ita tamarasa dalinlin dayasa su Ammee sukace tazauna agidannan toko sun gaji da'itane?.
Da ire-iren wad'annan tunanin bacci yad'auketa.
Washegari bayan sunyi break taso komawa d'aki ganinsa zaune cikin parlourn Amma Mommy tahana Dan idan zata tashi sai Mommy takawo wata zancen ahaka tahakura tazauna.
Saidai gabaki d'aya jitake kamar tana kan Kaya,Koda Mommy tatafi bedroom in Daddy dasauri itama tamike tashige d'aki.

Kwanansa biyar agidan yatattara yakoma inda yafito ranar daya koma walwalar JUHAIFAH dabanne agidan,harsai da Mommy tafahimci hakan.
Tunda yakoma yakasa gudanar da aikinsa yadda yakamata sai yarikaji kamar yajima sosai da dawowan yanason komawa Nigeria,gawani irin yanayin dayakeji dashi kansa bazai iya fassara kalarsaba, tun naran dayazo kasar ya'iso da mugun ciwon ciki da mara,yasha Lipton da lemun tsami Amma basuyi Masa amfaniba Dan abun sai gaba-gaba yake,tun Yana daurewa yalallab'a yafita gun aikin sa har yakaiga baya'iya fita yanzu,cikin kankalin lokaci yagama fita hayyacin sa,
Kwance yake akan gado sai murkusoso yake ciwon yau yafi nakullum Dan yau yahad'u Masa da azabebben zazzab'in ko'iya bud'e idanunsa bayayi, Jc Mai aikinsa ne yashigo d'akin daniyyar gyara Masa d'akin ganin halin dayake ciki yasashi saurin Isa gaban gadon,hankali tashe Jc yashiga tanbayar sa meya sameshi,shidai bai iya bashi amsaba sai ci gaba da kakkarwa yake acikin bargon daya dunkule kansa ciki.
Cikin hanzari Jc yad'au wayar MAHFUS dake saman durowa yakira numbern Dr Wanda yake dubashi idan bashida lfy,batareda b'ata lokaciba Dr ya'iso ganin halin dayake ciki yasa shi cikin hanzari yashiga bashi taimakon gaggawa,daga bisani yayi Masa allurai.
Dr baibar d'akin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login