Showing 39001 words to 42000 words out of 85666 words

Chapter 14 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

Mai Kiran nasa murmushi yy, batareda yad'auki kiranba harsaida Kiran yatsinke kafin
yabi bayan Kiran nata.
Aysha tad'auka da sallama, Sadeeq yace "madam ya'akayine?."
Aysha tayi murmushi taredafad'in "normal wlh zamu wucen ne nace Bari nafad'a maka."
Yace "ok Nima yanzu shigowata gidan Kenan barinaje nadubo angon Nan sainafito mutafi."
Tace "to."
Sadeeq yakatse wayar yanufi bangaren abokin nasa,
Koda ya'iso bakin kofar yamurd'a handle yatura kafar yashiga da sallama.
cikin d'akin' ganin baigansa acikin d'akinba gakuma saukar ruwa acikin bayi,yansan cewar wanka yake,yazauna bakin gado,
Zamansa dakamar 10min MAHFUS yabod'e kofar bayin yafito,
Sadeeq yawashe baki Yana fad'in
"Gara dakafara Shirin dawuri,to maza sakaya muyi mukaiku gidan ku,kaga dare yakusa yi."
MAHFUS ya'isa gaban mirror yarataye karamar towel inda yake tsane gashin kansa,agefen mirror,saida yaja kujera yazauna daga cikin mirror Yana kallon Sadeeq d'in yace " wazakakai gidan?."
Sadeeq yace "kai da JUHAIFAH mana."
MAHFUS yace "wacece hakan?."
Sadeeq yy 'yarkaramar dariyar shakiyyanci maihad'eda zallar sokana yace
"D'alibarnan taka,Wacce kake alla-alla dare yayi dominta, dakuma hadirin dake tasowannan yasauko da ruwa,domin darasin dazaka Bata nayau yasamu damar shiga kwakwal warta dakyau."
MAHFUS ya wasa Masa mugun kallo daga cikin mirror tareda Jan tsaki yad'au Mai yafara shafawa jikin sa,
Shi kwata-kwata yatsani jin maganar ta,bare arika Dan gantashi da ita.
Sadeeq yamike tsaye Yana fad'in "Bari nayi alaula muyi sallah gashi ana kan Kiran sallar magriban ma,muna idarwa kawai saimu wuce."
Yanagama fad'a yasuce bayi.
MAHFUS yana gama shafa man yamike yaje yaciro kaya yasaka,
Yadawo gaban mirror yafeshe jikinsa da turare,sannan yajuya yanufi kofa.
Sadeeq kuwa Yana idar da alaular yafito lokacin MAHFUS yad'aura hannunsa kan handle nakokarin bud'e kofar.
Sadeeq yy saurin cewa "Kai Man tafiya Kuma zakayi kabarni nida zan kaika Kuma nizaka Bari cikin d'akin?."
MAHFUS baikula shiba saima ida murd'a handle d'in dayayi,dasauri Sadeeq yabi bayansa suka nufi masallaci.

Ana idar da sallan MAHFUS yariga Sadeeq fita yanufi acikin gida,
Sadeeq kuwa nazaune cikin masallacin baisan da fitarsa ba saida yajuyo gifen dayake yaga bayanan dasauri yamike yafito,
Can yahan gosa har ya'isa tsakiyar gidan, sauri yy ya'iso inda yake,Yana maida numfashi taredafad'in "Kai Man saikace maitafiya akan iska,yanzu dai mukarasa
ciki saisu fito mutafi ko?."
MAHFUS yajuyo dasauri yace "waini kabi kadameni dawani atafi-atafi,waishin kam awaje nakeni ba'agida nakeba yanzu?,
Kadaina cigaba da damuna Dan wlh ba inda zani,kaida kamasu saikaje kakwashesu kakaisu can gidan d'in,
Idan Kuma kaci gaba da damuna zamu Sami matsala dakai."
Sadeeq yace "todai nafahim ceka bakaso mujene na'yan mintunan nan, kana ganin zai zamo maka takura wajen morewa,tonidai kada aje a'illata 'yar mutane abitadai ahankali kada aje asauke Mata tulin shekarunnan aka."
MAHFUS kalallesa yayinda yaji ransa yamugun bace'
Mezaikaishi inda zuciyarsa zai tashi,
Ai ko gida d'aya zasu zauna sai yadanne zuciyarsa kafin ya'iya zaman,
Ballan tana Kuma ace d'aki d'aya haryakaiga kusantarta,
Allah yasauwake,
Yatofar da yawu gefe,yayinda yaji wani kyankyanin ta yataso Masa,
Yakuma kallon Sadeeq dakyau yace "banza d'an iska saikayi Kuma ai."
Yana kaiwa Nan yajuya yy wucewarsa.

Sadeeq yazaro wayarsa a aljuhu yy dilling numbern Aysha,
Tana d'agawa yace "kufito mutafi."
Tace "to."
Tamike tsaye tana fad'in "Zulaihat taso muhad'a kayanmu,
Sadeeq yace mufito mutafi."
Zulaihat tace "to.
Tasauka daga saman gado suka d'an tattarkasa kayakinsu,Koda suka gama had'a kayansu,
Zulaihat takalli su Hassan dasukayi matashi dacinyar JUHAIFAH,
Tace "Hassan kuso mutafi gida."
JUHAIFAH da tun d'azu da Mommyn Jos takirawo Zulaihat akan sukoma gida,jikinta yy sanyi gabad'aya,
Takalli Zulaihat dake mikowa yaran hannu tana yimusu alamar sutaso,yace
"Amdai batafiya zakuyi kunarniba ko?."
Aysha tace "to da tare zamutafi dake aike munkawo ki Kenan."
JUHAIFAH tatada yaran akafarta tasauko daga kan gadon tasauko dasu suma,tareda rike hannayen su,
Tace "lallai ma, baku isakam kutafi kubarni anan ba koku zauna,kokuma mutafi tare daku." Zulaihat tace "a'a JUHAIFAH taya zakice Zaki bimu ko kinmance zaman aure kk yanzu."
Nandanan idanun JUHAIFAH suka cika da kwalla, tabud'e baki za'tayi magana' sai ga hawaye shar-shar,
Saikuma tasaki hannun su Hassan tashiga bubbuga kafa akasa tana fad'in "Allah nidai bazan zauna ba."
Saikuma tarike hannun Zulaihat da Aysha gam,tace "Allah saidai in zamu zauna tare indan kuma bahakaba to saidai mutafi tare." Aysha tace "kiyi hakuri JUHAIFAH kizauna,ima kinaso mu zamurika zuwa gidanki kafin Zulaihat tatafi,in tatafima ni zan cigaba da zuwa."
Kuka tasake da karfe tana cigaba dafad'in "nidai bazaku tafiba inkuma zakutafi to saidai mutafi tare."
Sosai take kukan, gabad'aya
Zuciyoyinsu yakaraya, tausayinta yakamasu, sai suka shiga lallashinta da Bata baki Amma Ina saima Kara sautin kukan datad'ayi.

Mommy da fitowarta daga d'akin Daddy Kenan tajiyo sautin kukanta,cikin hanzari tanufi d'akin dasuke d'in, Zahara ma sautin kukan natane yafito da'ita daga cikin d'akin ta,dasauri tabi bayan Mommy,
Mommy tatura kofar cikin hanzari suka shiga cikin d'akin,
Ganinsu curko-curko atsyene ga JUHAIFAH nata faman rusar kuka tana bubboga kafa akasa,dakaga kukan dai yahad'u kashi biyune, shagwab'a dakuma kukan gaskiya.
Dasauri Mommy tace "menene meyasameta wani abunne yafaru!?."
Tajero tanbayar tana duban su Zulaihat.
Zulaihat tace "wlh ba abunda yafaru,waidun kawai muntashi zamu tafine shinewai saidai muzauna kokuma mutafi da ita."
Mommy tasauke nannauyan numfashi,Dan gabad'aya tagama tunanin wani abunne yasameta take irin wannan kukan,saikuma tayi murmushi ganin yanda take kukan shagwab'a yafi asalin kukan yawa.
Mommy tariko hannun ta tana fad'in "tahonan kinji kiyi shiru abinki d'iyata,ai hakan bayana nufin kunrabu Kenan ba zasu Rika zuwa miki."
Tadubi su Zulaihat tace "in kun tafi yau koge kuje Mata can gidan nata."
Sukace "to.
Zulaihat taroko hannun Hassan tace "kuzo mutafi."
Dasauri JUHAIFAH takwace hannunta ahannun Mommy takama hannun yara,dasuketa faman Kiran "Mamy Mamy." Cikin muryar kuka tace "sukam bazasu tafi."
Mommy tace "to shikenan kubar yaran kawai."
Zulaihat tace "fa'ance mukoma dasu gida, kuma gobema akwai School."
Mommy tayi shiru tarama ta'in'da zata bullowa lamarin,
Tace JUHAIFAH kiyi hakuri duk randa babu makaranta sai arika Kai mikisu,badun makaran tar tasuba saisu zauna Miki,
Kiyi hakuri kibarsu sutafi."
Mommy takarb'i yaran ahannunta tamikawasu Zulaihat,suka karb'i yaran dasauri sukafita,zubewa tayi akan gado takuma fashewa da kuka,
Mommy ta isa bakin gadon tashiga rarrashin ta,hartasamu tad'an sassauta kukan nata.
Sannan Mommy takalli Zahara tace "zauna kitayata Hira inazuwa."
Zahara tace "to."
Tazauna bakin gadon kusa da ita,
Mommy Kuma tafita,
Tanafita d'akin Daddy tanufa tanashiga Daddy yy saurin juyowa,Dan shima tun farin kukan nata yaso fita Amma tuno surukace dakuma muryar Mommy dayaji agurin shiyasashi bai fitoba, yarika kaiwa da komowa acikin d'akin,shigowar Mommy yanzu yy saurin cewa "yaya lafidai meyasameta?."
Mommy tasauke numfashi tace "'yan'uwan tane zasu tafi shine take kukan,Kuma wai sai dai abar Mata yaran yayanta ta suzauna tare to Kuma gobe akwai makaranta shiyasa,"
Daddy shima numfashin yasauke jin bawani babban Abu ne yasata kukanba,
Yace "Allah sarki taga zasu tafi subarta Aure Kenan maicireka adangi yajefaka cikin wasu dangin, Kuma hakan bawai yananufin karabu danaka dangin bakenan,
Zanzu kamma yakamata sutafi gidan su,shi Son in Yana inane?."
Mommy tace "aini rabonda insashi a'idanuna ma tun shikaran jiya."
Daddy yace "him Son Kenan Bari nakirashi."
Yad'au wayarsa yalalub'o numbern sa,

Yana kwance akan godo wayarsa tafara bada haske alamar shigowar Kira, yad'an mirgino tareda yanyo wayar,ganin numbern Daddy sai yy picking call d'in yad'aura wayar akunnen sa yace "hello Daddy."
Daddy yace "kana inane Son?."
Yace "inagida fa Daddy."
Daddy yace "wani gidan?.'
Yace "cikin gidannan Ina d'akina."
Daddy yace "to kafito kazo kad'auki matarka kutafi gidan ku."
Daddy nakaiwa Nan yakashe wayar.
Jiyayi kamar Daddy yanasa Masa mashi akahon zuciya,wai matarsa. saiyaji kalmar tatsaya Masa azuciya,wai dagasken gidad'aya zasu zauna da ita,saiyaji gabakid'aya zuciyarsa ta lalace,wani irin haushinta da tsanarta suka dad'a baibaye cikin zuciyarsa.
Mikewa yy yashige cikin bathroom kamar yanda yake a duk sanda bakin cikinta yahanashi sakat saiya sanyawa kansa ruwa kafin yaji sakat,
Hakama yanzu yy yasakarwa kansa ruwa domin samawa zuciyarsa sassaucin abunda yakejin.

Ab'an garensu Daddy kuwa Koda yakashe wayar,yadubi Mommy yace "Him Son Kenan komadai meye yanzudai yakare wani guje-guje da b'oye-b'oye duk sunkare tunda aka rigada akayi auren."
Mommy tayi murmushi cikeda Jin dad'in kasan tuwar Auren d'an nata wacce tad'au tsawon shikaru tana burin ganin wannan ranar tace "yaro Kenan anayimasa gata shikuma Yana turewa."
Daddy yakalleta ganin yanda tayalwata fuskarta da murmushi, yasan cewa tana cikin farin ciki nazuwan wannan ranar, yace "shikenan yanzu korafi yakare andaina samin yaro gaba da korafi ko?."
Mommy tayi dariya tace "him bakorafi bane ai gaskiya nake fad'a Masa,yanzun bagashi tun jiya da aka d'aura Auren darajarsa tadad'a karuwa a'idon duniyaba,ai ita Aure rahamace."
Daddy yajinjina Kai dagamsuwa da'abunda tafad'a,
Tun kan ad'aura Auren shikansa Daddyn yake d'aga kiran manya manyan mutanen dasuke kiransa domin tayasa murna,banda wad'anda suka taho daga kasashe daban-daban,
Barekuma shi kansa MAHFUS d'in.
Yasan cewa darajar d'an nasa yakaru fiyedana da.
Cikin tsigar zolaya yace
"Saura jikoki ko?."
Dariya Mommy tayi tace "Allah yakawosu dayawa masu albarka."
Daddy ya'amsa da "Amin.
Juyawa dasauri Daddy yy Yanufi kofa yana fad'in, "Masallaci zantafi Jin kukan yarinyarnan yahanani tafiya gashi har antada salla."
Yabud'e kofar yafita.
Koda aka idar da sallah Daddy yy ta baza ido kazaiga MAHFUS Amma baigansaba har wajen masalllacin yafito nanma baigansaba,
Shiru yy aransa yace "wato ko masallacin ma baizoba Kenan."
Fita yy gaba d'aya daga cikin masallacin
yanufi cikin gidan direct d'akin MAHFUS yanufa.

MAHFUS kuwa tun shigar sa bayi daya sakarwa kansa ruwa bai fitoba saima Zama dayayi acikin bath, kamar macenda akewa sit bath,
Harkuma lokacin ruwanda kesauka daga cikin shower baifasa sauka akansaba,
Yad'au tsawon 30min ahaka sanna yamike yakashe showern yafito daga bayin.
Fitowarsa yy dai-dai da shigowan Daddy d'akin,
tsayuwa Daddy yy Yana kallonsa cikeda mamakin ganin kayan jikinsa ajike sharaf sai tsiyaya suke, gakuma kwayar idanunsa dasuka sauya.
Daddy yace "Kai MAHFUS menake gani haka?."
Daddy yy tanbayar Yana nunashi dayatsa,
Bin jikinsa yy dakallo saikuma yamaida dubansa ga Daddy yace "wanka nayi."
Daddy yace "wanka?dakayan jikin nakane kayi wankan?."
Kai yagyad'a alamar Eh. Daddy yy shiru tareda nazartar yanayinsa nad'an wani lokaci,sanna yace "to jeka tub'e kayan kazo yanzu kutafi Kai bakasan dare yy bane."
Komai baiceba sai wucewar dayayi yaje yaciro kaya,yashiga bayi,
Daddy natsaye,harya canzo kayan yafito,
Ganin har lokacin
Daddy natsaye Nan cikin d'akin yasashi isa gaban mirror yad'au keyn mota yakwashi wayoyinsa. Daddy yy Masa alama da hannu akan yazo yawuce yasakai yafita Daddy yabibayansa, suka sauko kasa,a parlourn kasa suka iske Mommy,suna karasowa parlour Daddy yace wa Mommy "jekifito Masa damatarsa sutafi."
Mommy tace "to."
tajuya tawuce d'akin da JUHAIFAH take,
Tana kwance harlokacin batafasa shashekar kukan ba.
Mommy takaraso cikin d'akin tana fad'in "JUHAIFAH taso kizo kutafi kidaina kukannan haka Dan Allah."
Takamo hannunta tamikar da'ita tsaye,
Tace Zahara "d'auki akwatinnan kikai motar Yayan ki."
Zahara tace "to. Tad'au akwatin tafita dashi.
Mommy tad'au mayafinta tasaka Mata akai tajanyo hannunta sukafito,
Wani irin fad'uwa gaban kirjinta yy lokacinda idonta yasauka akansa,dasauri tad'auke idonta akanshi harsuka karaso inda suke kanta nakasa.
Daddy yadubeta cikin kula yace "haryanzu batadaina kukan bane?."
Mommy tace "wlh haryanzu batadainaba."
Daddy yace "Aida anbar Mata yaran inyaso sai akarb'o musu uniform insu sai gobe MAHFUS yakaisu makarantar."
Dasauri yad'ago Jin abunda Daddy yafad'a,
"Hm watoma har yara takedasu."
Yafad'a aransa,jiyayi bazai iya cigaba da tsayuwa agunba, saiya mike yabar parlour.
Mommy tace "Zahara je kiching maza zakiga basket kid'auko shima kikaishi motar."
Tace "to.
Daddy yakalli JUHAIFAH yace "kiyi hakuri kinji."
Kai tagyad'a alamar to.
Mommy tace "muje shikam yy gaba.
Koda suka fito lokacin harya shige cikin mota abunsa,
Mommy takarasa da'ta jikin motar tabud'e Mata gaba tace "shiga kinji."
Ahankali tashiga cikin moyar tazauna Mommy tamaida marfin tarufe,Zahara tayi saurin karasowa tabud'e gidan baya tasaka basket d'in aciki.
Mommy tace "tokuje Allah yatsare.
Dagashi har itan Babu Wanda ya'amsa addu'ar Mommyn.
Yatada motar maigadi yy saurin wangale Masa get,su Mommy natsaye harsaida sukaga fitarsu kafin suka koma ciki.
Ahankali yake Jan motar,harsuka fita daga layin dasuke suka d'anyi tafiya maid'an nisa kafin ya yagan gara wata layin duk Kuma acikin Maitama.
D'an tafiya kad'an suka Kara suka iso bakin wata makeken get,
Matsa horn yy batareda Bata lokaciba aka wangale get din,yakusa hancin motar ciki.
can cikin parking lot ya'isa da motar yana dai-daita parking,Yabud'e marfin motar yafito yamaida kofar yarufe tareda fitowa daga cikin parking lot in,kafin ta ankara harya'isa jikin wata gilas datake iya hanhowa daga inda take zaune acikin motar.
Asannu tad'aura hannunta jikin marfin tabud'e tafito............



Mommyn Twins ce


🅿️13

Koda tafito daga cikin motar tuni shikam yashige ciki,asannu tarika tafiya har'ta'isa kofar data gansa tsaye d'azu, ahankali tad'aura hannunta kan glass in tazugeshi gefe,ahankali tasaka kafarta ciki tamaida glass in tafufe,bayansa tahango Yana haura wa step,ta'isa tazauna kan kujera tareda buga uban tagumi,shagal tuwa tayi dakallon parlour Wanda yaji kayan alatu Dana more rayuwa,
Ab'angaren MAHFUS kuwa
Yana idda tajima haurawa step innan yabud'e kofar dazai sadashi da parlourn sama,yanashiga direct bedroom insa yashige yatub'e kayan jikinsa yauya nana bacci yahaye gadonsa.
JUHAIFAH ko nazaune acikin parlour ahankali tafarajin bacci nafizgarta,saita gyara kwanciyarta akan kujera taja mayafin kanta tarufe Rabin jikin,kasan cewar mayafin batada wani girma shiyasa' bai'isa rufe jikin ta dukaba,
Dunkulewa tayi guri guda saboda sanyin AC dayagarwaye ilayirin parlourn,ahaka bacci yad'auketa.
Can cikin bacci tarikajin wani irin masifaffen sanyi,
Bud'e idanunta tayi jikinta nacirawa Dan sanyi,mikewa tayi zaune tatankwashe kafafunta tadun kule guri guda tareda cusa hannayenta cikin gyalen datarufe jikin ta dashi,sosai sanyin keshiga jikinta ga sanyin yahad'u Mata biyu ga sanyin AC ga sanyin iskar dake busowa daga waje Yana shigowa tacikin windown parlour,
Sosai jikinta ke b'ari dasauri tazuro kafafunta kasa tamike tsaye, waige-waige tashiga yi Dan nimawa kanta mafaka,
D'akuna tagani guda hud'u Nan cikin parlourn,
Biyu tagefen damanta,
D'aya na kallon d'aya,sai corridor atsakiyarsu
Sai tagefen hagunta shima haka tsarinsa yake,
Dasauri tanufi d'akunnan dasuke gefen damanta tamurd'a handle na d'aya daga cikin d'akuna biyun,saijinsa tayi arufe gam,
Tayi saurin juyawa tamaso d'aya kofar nanma jinta tayi arufe gam.
Zamewa tayi tazauna Nan cikin corridor,Jin sanyin dake cikin gurin yama zarce na inda tabaron,cikin hanzari takuma mikewa tanufi d'akuna biyun dasuke jere can d'aya b'angaren,hannunta nab'ari tad'aura kan handle dukda batada tabbacin cewa shima d'in abud'e yake, tamurd'a handle saiko kofar tabud'e,dasauri tatura kofar tashige ciki,
Aiko wani masifaffen sanyine yayi Mata maraba acikin d'akin,akid'ime tarika waige-waige tana neman ta'inda makunnin AC dake aikin busa sanyin dake kokarin birkita Mata lissafi yake.
Idonta yasauka Kai tayi hanzarin Isa takashe AC,tana juyowa tayi ido biyu da hotanta d'aure kan bedside,
"Shinedai." Tafad'a aranta,hoton tane Wanda yake cikin d'akinta acan gidansu, hakan nanuni dacewa wannan shine d'akinta kena,ta'isa bakin gado tahaura dasauri taja blanket tarufe jikinta asannu d'umin blanket d'in yarika rasata cikin kankanin lokaci bacci yad'auketa.

Washegari
Da asuba
MAHFUS yafita zuwa Masallaci baidawoba saida gari yy haske sosai,
yanashigidan a parlourn kasa yatsaya d'aya dagacikin d'akunnan da JUHAIFAH jiya tatab'asu tajisu akullennan shi yanufa Yana Isa jikin kofar yazula key yabud'e kofar yashige cikin d'akin,
Laptop d'insa yad'auka saman durowa yafito yarufe kofar yahaura sama.
Zama yy bakin gado tareda kunna laptop d'in yajima Yana lallasawa daga bisani yamike yashiga tub'e kayanjikinsa yashiga bathroom,yy wanka yafito yashirya tsaf cikin kananun kaya yy shardashi,makullin matarsa yazara yafito daga cikin d'akin yasauko kasa direct parking lot yanufa,harya bud'e marfin motar zaishiga saikuma yasaki marfin,tuno dajiya yaga Zahara tasaka wani Abu a sit d'in baya,saiya bud'e bayan akwati yagani da basket,d'an tsaki yaja yaciro su ya'ajesu agun yashige motar yaja yabargidan.

Ab'an garen JUHAIFAH kuwa
Bayan tayi sallar asuba,bacci takuma komawa karfe 8 tafarka,wanka taje tayi sannan tafito,
Bayan tashirya tazauna tad'au wayarta takunnashi numbern Ya Al'ameeda talalub'o tayi dilling in numbern,
Bugu biyu yad'aga,
Tanajin yad'aga saita fashe dakuka.
Hankali tashe Ya Al'ameen yace "Shalele meke faruwane wani abunne yasameki."
Komai batace mishiba saicigaba dakukan datayi,tanajin yacigaba datanbayarta hankali tashe.
Cikin muryar kuka tace "Ya Al'ameen haka mukayi daku ko? yau kwanana nawa Amma shine bakuzo bako Ina kuncemin kullom zakurika zuwa,to shikenan tundama hakane niyanzuma zanzo?."
Ya Al'ameen yace "a'a Shalele kada kizo,ko kinzoma bazaki Sami kowa agidan ba,dukanmu muntafi Yalwa idan muka dawo zamuzo kinji?
Kiyi shiru ko."
Kai tagyd'a kamar Yana ganinta,
Yacigaba dafad'in "kadafa kije ko'ina kizauna muna dawowa zamuzo."
Tace "tom."
Yace "Yauwa Shalele kinfasan yanzun kin girma ai yanzu kecema gabada Jabeer."
Dariya tayi tareda share guntun hawayen dake makale a'idonta,aduk sanda su Ya Al'ameen sukace wai yanzu tagirmi Ya Jabeer sai abun yabata dariya, musan idan tatuno Ya Jabeer har gemu yakedashi Amma sai suce wai yanzu tagirmeshi, duk sanda suka fad'amata hakan saikanta yarika fashewa adole ita irin yanzu tazama babbannan.
Tace "to shikenan Amma yanzu yaushe zaku dawon?."
Ya Al'ameen yad'anyi shiru Dan Yana nazarin kwanakin dazai fad'a Mata, Aunty Rukayya dake zaune kusadashi tanajin duk abunda suke,Jin tanbayar da JUHAIFAH tayimasan,dakuma amsar daya gaza batan,sai tad'ago hannunta tayimasa nuni da yatsunta hud'u.
Dasauri yace "kwana hud'u zamuyi mudawo."
Tace "to shikenan Allah yakaimu."
Harsunyi sallama tayisaurin cewa "yauwa Ya Al'ameen bawa Amira da walida wayar,naji dalilin dayasa basuzoba."
Ya Al'ameen yad'anyi Jim,ganin yanda idan yatoshe wannan hanyar saita b'ullo dawa.
Yace "yanzunnan Maman su ta'aikesu basu dawoba tukun."
Tace "to idan sun dawo kahad'ani dasu."
Yace "to Bari sudawon sai nahadakun."
Tace "tom.
Yakashe wayar tareda sauke numfashi, Aunty Rukayya tadubeshi taredafad'in "him yau Yaya yayi karya,Yana gari D'aya dakanwa yace wai bayanan".
Takarashe maganar taredayin dariya,
Shima dariyar yy tareda yanyota jikinsa yace "to ai bani kad'aya nayi karyarba,harda matar Yayan." Murmushi tayi "nikuma karyar me nayi?."
Tafad'a tana dad'a kwantowa jikinsa,
Shafo gefen fuskarta yy sannan yace "meyasa kkce nace kwana hud'u zamuyi kafin mudawo?." Tace "abunda yasa nafad'a kaga yau kwananta biyu,idan akahad'a da hud'un Dana fad'a yabada kwana shida,to idan kadawo da kwana hud'un zaka Kara kwana d'aya akai,saiyabada kwana bakwai,tunda bawai ranar daka dawonne zakuje gidan nataba,kaga lokacin tacika kwanaki bakwai agidan miji lokacin zaku iya zuwa kudubata.
Ya Al'ameen yadad'a rungumota ajikinsa,yace "Kai my Ruky akwai basira,badun kinanan ba watakila sai tafahimce bamutafi wani Yalwa ba."
Aunty Rukayya tadad'a fad'ad'a murmushin ta,tace ai shima my Ameen d'in badai basiraba,Rukyn ma agunsa takoya."

JUHAIFAH kuwa tana gama wayar tamike tsaye ta'isa jikin window,labulen windown tazuge gefe tareda zuge glass d'in shima,
tsayu tayi jikin windown tana bin tsararren barfajiyar gidan dakallo,Nan idanunta yasauka cikin parking lot,zuka-zukan motocine guda hud'u afake agun, sai rumfa D'aya Wanda kenuni dagun zaman mota d'ayace Amma bamotar agun,ido takurawa rumfar da bamota cikin Nan tahango akwatinta da basket aje agun,ido tawaro Dan tuno da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login