Showing 9001 words to 12000 words out of 85666 words

Chapter 4 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

da bazaurar yafara,to ashe kuwa dun kaima kayi bawata aba bace,

Yace "Mommy to tunda bazaura kukeso na aura, to kucan zamin wata ba wanna ba,wlh Mommy wanna yarinyar ko kyauta akabani bana so,bazan Kuma aure taba,

"To ubanmu,to bari kaji aure ba fashi kaman anyi angama ko kaki ko kaso sai anyi aurenna idanma wani abun kashawo kazo kakeyimin wanna haukan to in kara fad'ama aure ba fashi,

Fuuu yajuya yafita ad'akin idanunsa gabad'aya sun gama rufewa,far fajiyar gidan yafito ya nufi parking lot,lokacin Sadeeq yashigo gidan yana kokarin dai'dai ta parking, ya hangosa zai shige cikin mota,kafin ya ankara sai ganinsa yy har yashige cikin motar tareda yin wani uban ribas,baki Sadeeq yabud'e ganin yadda yabaiwa motar wuta akuje mai gadi yabud'e get kamar zai kwashe mai gadin sabar gudu,

Sadeeq yakoma cikin motar sa da sauri yabi bayansa, gudu yake shararawa kamar zai tashi sama,
Sadeeq shima binsa yake dukda tazara dake sakaninsu,tundaga nesa yafara danna horn ganin hakan yasanya jami'an tsaron dasuke tsaron get d'in bud'iwa da hanzari.
Yadanna hancin motar sa ciki,kashe motar yy batareda ko duba inda ya tsayan ba,yafita acikin motar ko key bai cireba yy ciki,

Bibbiyu yake had'a step's Nan da Nan yahaura sama yana isa jikin kofar ko Knocking baiyiba ya murd'a handle ya kusa kansa ciki.

Daddy nazaune sai ganinsa yy ya fad'o masa cikin Office ko Knocking ballan tana sallama.
Mikewa tsaye yy tareda fad'in Kai Son lfyrka kuwa?
Batareda yabaiwa Daddy amsaba yace
"Daddy Dan Allah narokeku ajanye wanna auren,
Daddy bazaurace fa, idan Kuma baza ajanyeba to acan zamin wata matar koda kuwa ita wacce za acanza zata kasan ce ba zaurarce itama Na amince,indai har za afasa da wanna yarinyar.

Daddy yace "zauna Son yanuna masa kujerar datake fuskan tarsa,
zama yy yanafad'in "Daddy kace ka janye.

Daddy yadubesa da kyau yace
"Son abunda kk nimanna bazai yuwuba dan ha kayi hakuri kawai ayi aurenna,dukda bansan dadilinka na fad'ar hakanba.

"Daddy nidai wanna yarin yarce bazan iya auren taba,Allah da gaske bazan jureba zuciyata baza ta tab'a jurewaba.


"To Amma menene da lilinka nakin amin cewa da aurenta kakuma ce ka amince a auramaka wata koda itad'in bazaurarce?

"Daddy ita d'in..sai kuma yy shiru,

Daddy yace "ita d'in me?ina jinka,
Shiru yakumayi,
Daddy yace "zancen banza,me kk so duniya tad'aukeni mutumin banza ko?haka kakeso ko?fad'amin nace,
Kai yashiga girgizawa,

"To Dan saboda wata da lilinka mara ma'ana kk so ka zubdamin kima,sai akace maka bazaurar ita ba mutum bace?koko a kanka aka fara,to bari kaji wanna karon bazan tab'a goyon bayan karyaba,Dan haka katashi kaje kafara Shirin aure,sanna Kuma ina mai umurtar ka yau d'inna kaje gidansu yarinyarna kaji me takeda bukata kayi mata,wanna umurni nake baka,tashi maza katafi.

Ji yy kamar Daddy ya dasa masa mashi azuciyarsa, dakyar ya'iya mikewa tsaye yaja kafarsa yafita a office.
Yana sauka kasa Sadeeq nashigowa,
Ya faka motarsa yafito dasauri yanufeshi ganin halin dayake ciki,kallo d'aya zakayi masa kaga tsantsar damuwa shin fed'e akan fuskarsa,kunsan mutumin da bai saba shiga irin wanna yana yinba idan yasinci kansa aciki tofa akwai masala dankuwa kallo d'aya zakamasa kasan cewa yana cikin tashin hankali.

Sadeeq na isa inda yake yariko hannunsa yana fad'in, "Man so kake kakashi kanka? kaduba irin gudun da kakeyi kamar kana wajen gari to ko awajen garin kk ma ai baza kayi irin wanna kasadan ba,kaidai kawai Allah ne yakawo nan lfy.

Duk abinda Sadeeq yake fad'a shi bama ganewa yakeba,ganin bakin sa yy shiru yadaina motsi.

sai shima yafara magana "Sadeeq kasan itace wacce za'a aura min, kuma bazaurace'ita Amma shine baka fad'amin tuntuniba gashi yanzu Daddy yace bazai janyeba.

Sadeeq yace "Haba MAHFUS akan hakane kad'ai kk son kashe kanka?

Yace "hakanne zakacewa kad'ai?
Wanna fisa rarriyar mara kunyar yarinya wai itace za ahad'a ni da ita,

Sadeeq yace "nidai banga wani ay bon yarin yarna ba,Kuma in kana tunanin abunda ya had'akune awancan lokacin, to ay Kai kafara zaginta, Kuma kasan laifin mune tunda mu muka kusa bigeta Allah yakare,

"Wlh da na auri wanna yarinyar gara na tabbata banyi aureba,har idan kuwa na aureta to Zan ci gaba da rayuwar kunci har karshen rayuwata, Dan zuciyata bazata tab'a jure zama inuwa d'aya da itaba,Zan iya yaki da zuciyata dun dole ba yanda na iya abisa tursa sawar iyaye, in zauna da wata bazaurar Amma ba itaba. Sadeeq bakasan me nake ji acikin zuciya tabane.

Yana kaiwa Nan yajuya zai shiga motarsa Sadeeq yy saurin cewa "kabari nakaika gida kaduba halin da kk ciki tayane zaka iya driving da kanka,bai kulashi yashige motar yafegeta a 70.

Gidansa dake Maitama yanufa, Yana isa jikin get d'in mai gadin yabod'e masa dukda ba kowa acikin gidan Amma akwai maigadi, yabude masa get yashiga ko amsa gaisuwar da mai gadin yake baiyiba ya shige ciki.
Masha Allah gidane mai hawa d'aya,sama nad'auke da 4 bedroom sai katoton parlour Wanda aka kawatashi da kayan more rayuwa kala-kala kamar a turai, sai gefe da parlour wani ketaccen dinning room ne Wanda shi kad'ai ma abun kawuni kana kallon sane,
Sai kiching acikin kiching d'in kwai kofa dazai sadaka da sto.
Kasanma haka tsarinta yake.
d'aya daga cikin bedroom d'in yashiga,


Kai Fan's koda zaku cemin ni bakauyi yace nayarda dankuwa ni ban bab'a ganin ran tsatsen gida irin wanna ba,baki da hanci duka nabud'e ina kallon bedroom d'in.


Yana shiga bedroom d'in yahaye saman bed ko takalmin kafarsa bai cireba Nan yayi kwan ciyarsa ahakan.

Tun bayan fitarsa a office d'in Daddy,Daddy yature duk wasu files din gabansa ya koma dabaya yakwanta jikin sit,tunani iri-iri yarika zuwar masa,lokacinda tunaninsa yazo inda MAHFUS yake fad'in, Daddy nidai wanna yarinyar ce bazan iya auren taba,Allah da gaske bazan jureba zuciyata bazata tab'a jure ba.
Nanata kalmar yarikayi azuciyarsa afili yace" to me yake nufi da hakan lallai akwai dalilin dayasa shi fad'ar wanna kalmar.to menene?saikuma yace "babu wata dalili da lilin kawai shine ciwon dake hanashi auenna itace kesashi fad'ar wanna kalmar,Son dele zakayi aure Dan mutabbatar da lfyrka,idan cutar damuke hasashi akanka ya tabbata to yazama dole mu magan ce maka ita,
Yamike yafita a office in,
Koda Daddy yakomo gida bai sameshiba ya tanbaye Mommy ko yafad'a mata zashi gidan su matar tashi,tace ai ita tun bayan fitarsa daya gama yimata hauka bata kara ganin saba.
Daddy yad'aga waya yakirashi yafi miscall goma bai d'agaba,daga karshedai Daddy text yamishi
Kamar haka,

"Son idan har baka tafi gidan su yarin yarna ba,to ina mai tabbatar maka zakahad'u da mummunar bacin raina Wanda baka tab'a ganin irinsaba tunda kazo duniya.

Yana kwance duk ringing in da wayarsa take yanaji ko kallon inda wayar take baiyiba, harsai lokacin shigowar sakon kafin yajanyo wayar,koda yaduba saiyaga Daddy ne ke Kiran nashi,lokacin daya duba sakon saiyaji han kalinsa yy mugun tashi,tunda yake arayuwarsa bai tab'a Jin kwatan kwacin irin wannan kalmar yafito daga bakin Daddy ba,hasa lima ko kyakyawar tsawa baitab'a shiga sakaninsa da Daddy,kansa yadafe da hanna yensa,afili yafurta "duk ta dalilin ki,Hmmm.

Zunbur yamike yafad'a bathroom yy wanka yafito Nan danan yashirya yad'au makullin motarsa yafito,yashiga motar akuje yanufi,wuse,wato gidan su HAFSAT.............


HHHHH KUDAI BIYONI YANZU AKAFARA WASAN.





Mommyn twins ce🌺 BAZAWARA CE ITA!🌺



بسم الله الرحمن الرحيم

___________________________________


🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________



By✍🏻
Rasheeda S Director




~Free~ ~page~



🅿️4



Koda ya iso gidan
Acan waje yasaya bai shiga cikin gidan ba,yanan zaune acikin mota yahango Aysha zata shiga gidan,yy saurin zuge glass kasa yadanna mata hon, saita juyo ta zo inda motar take,
Kallonshi tayi don son tunano inda tasanshi,cikin sakanni dabasufi uku ba ta tuno inda ta tab'a ganinshi,"tabbas shine." tafurta acikin ranta,shine Wanda suka kusa bige JUHAIFAH lokacinda zamu tafi shopping, ba karya gayen yahado,


katse mata tunani yy dafad'in "Sannun ki."
tace "yauwa,"
yace zakishiga gidannane?."
Tace "Eh."
Yace "yauwa to kice ana Kiran HAFSAT."
tace "Hafsat anan gidan d'in?" Yace "Eh." shiru tad'anyi kana daga bisani tace"ok JUHAIFAH kena to bari nafad'a mata." tajuya tashige gidan,
Nanata sunan dayaji takira yy JUHAIFAH lallai kuwa ya tabbata id'in ce Dan lokacinda suka zo gidan da abokinsa Sadeeq sunan dayaji yayanta yakirata dashi kenan,guntun tsaki yaja tareda komawa jikin sit yakwanta,

Koda Aysha tashiga gidan,part din Ammee tashiga dukda batada tabbacin cewa tana can d'in,a parlour ta tadda Abba da Ammee JUHAIFAH nazaune akasa kusada kafar Abba ta had'a Kai da guiwa sai rusar kuka take.tun nararda tasami labarin anzo niman auren ta,tadaka salle ta dire tace batajiba batagani ba, babu auren da zatayi ranar wuni tayi bataci abinci ba,tarika kuka Abba da Ya Al'ameen ranar sun wuni lallashi Amma fir takiyin shiru har su Ya Mujaheet da Ya Jabeer suka Kira waya suma dakalar nasu lallashin,bashi yasata daina kukan ba haryau Kuma bata fasaba,

tayi sallama tareda karasawa ciki,tarisina tagaida Abba da Ammee,sanna tace "wai ana sallama da JUHAIFAH."
Abba yace "wake sallama da ita?."
tace "wanine awaje yace nayi masa sallama da Hafsat nace masa agidanna yacemin Eh Kuma nasan dai JUHAIFAH ce."
Abba yace "komai akayi manemin auren natane,jeki maza Aysha kice dashi yashigo ciki,sai kikaishi can parlour Mujaheet kice dashi tana zuwa."
ta'amsa da "to." tafita.

Yana Nan zaune acikin mota tazo tasanar masa da sakon Abba,komai bai ceba,ganin tana tsaye da alama jiran sa take Dan tayi masa jagora zuwa ciki,saiya bude motar yafito, tana gaba Yana biye da ita suka shiga cikin gidan,saida takaishi har cikin parlour Ya Mujaheet, kafin takoma part d'in Ammee,ta sanarwa da Abba yana can parlour Ya Mujaheet.
Abba yadubi JUHAIFAH da tund'azu taketa rusar kuka, yace "Mamana tashi kije ko gaisawa ne kuyi saiki dawo."
Cikin muryar kuka. tace "Abba nifa gaskiya bana son auren."
Abba yace "to Mamana bawani abun naceba cewa nayi kuje kugai sa kawai." yadubi Aysha yace "Aysha jekiyi mata rakiya sugai sa."

Aysha tamike itako tana zaune, dakyar Abba ya lalla b'ata tamike suka fito, har kuma alokacin bata daina sharar kwalla ba,
Abakin kofar parlour Aysha tatsaya tace "kishiga Yana ciki."
Cikin tsiwa had'eda muryar kuka tace "to in anki shigan fa?."
Aysha tace "da dai kinyi hakuri kidai shigan da yafi."
Ido tawato cikin masifa tace "dayafin mun kk ce? to wlh bazan shigaba dan ni bai fimin ba."
Tajuya zata koma Aysha tayi saurin rukota tana fad'in "yi hakuri banface da yafi mikiba,cewa nayi da shidai zai fi mishi."
Fisge hannuta tayi ahannu Aysha ta tura kofar parlourn da karfi,Aysha ko juyawa taji tatafi aranta tana fad'in Allah dai ya shirya JUHAIFAH dai sai gyaran Allah.

Jin karar banko kofar datayi yasashi d'agowa da sauri, can nesa dashi taje tazauna tana cigaba da sheshekar kukanta,
shiru gurin yad'auka bakajin komai sai sautin kukanta,sunkai tsawon 20min ahaka.can saita saida kukan, kamar an zabu reta tamike tsaye tarike kugu tana gir giza,cikin masifa had'e da tsiwa tace "waikai mutum ne ko maye? in banda tsabar maitan ci duk matan dasuke fad'in garinna karasa wacce zakace kana so saini? to bari kaji wlh ina mai tabbatar maka kayi gaggawar cewa kafasa auren nan, idanko ba hakaba wlh sai nasa an b'atar da kai!."

cikin zafin nama da kunar zuciya ya mike tsaye, kan ta ankara ya iso gabanta,sai ji tayi ya angizata saman kujera,yad'aura kafarsa d'aya akan kujerar ya ran kwafo saitin fuskar ta,yafara kad'a d'an ya tsar sa a dai-dai saitin fuskar ta,wani irin mafifaffen tsorone ya lullu b'eta jikinta yakama b'ari,
cikin voice d'insa mai matukar dad'i yafara magana cikin kakkausar lafazi.

"wayace yana son naki?da har zakiyi tunanin kucaka irinki zan zauna nab'ata lokaci na akanki,ni zansa ab'atar min dake domin ke da rayuwarki gara rashinta,domin bakida wani amfani musam man ma aguri na!.yaci gaba,
Kalleni Nan,yanuna cikin idon sa,sanna yace "ko sadaka ake raba zaurawa bazan tab'a kallon hanyar gurin ba,Dan haka kisani ke bakikai wacce zance inasoba,mezan dake bazaura,kefa sauran wani ko ince wasu ne,to mezanyi da sauran dawa su suka rage.


cikin dakiya da juriya take kallon sa dukda maga narsa ya jefata cikin wani hali Amma saita b'oye hakan,
Dan ganin fuskarsa yasata shiga matukar mama ki,nu nashi da yatsa tayi murya narawa tace
"daman Kai.kai. kaine?ina wlh bazai yuwuba."tafad'a tana kokarin mikewa tsaye, kasan cewar yana sun kuye akan tane gakuma kafarsa daya d'aura saman kujerar yato kare ta babu ta inda zata iya mikewa sosai,sai Kawai taji kuka yazo mata,saurin danne kukan tayi tana fad'in "wlh nima da na aureka garana auri mai tsina akan bola,Dan wlh yafiyemin Kai sau dubu."

D'aya kafarsa dake kasa yadagosa yad'aurasa kan kafarta da karfinsa ya mur kushe kafarta,tsanani Jin azaba yasanyata rumtse idanunta da karfe,
Cikin kakkausar murya yafara magana,
"Idan kika kuskura kika shigo cikin gidana ina meyi miki al'bishir tamkar kinshigo kabarin kine,danni banshirya zama da irin kiba sauran wasu, ba'atab'a yin Abu arage sauran nayi amfani dashiba,ke ba komai bace face sauran wasu idan kina tunanin cewa mutane sunayi miki kallon bazaura wacce tatab'a auren namiji d'aya,toni agurina bahaka yakeba bazan tab'a zama inuwa d'aya da kazan taba inafatan kin gane."


Zuwa yanzu magan ganunsa sun kaita makura kalmarsa na yanzu sun dad'a jefata cikin hargitsi,
da iya karfinta ta janye kafarta wacce yaketa murku sheshi yun kurin mikewa tashigayi,
Yace "oh yi zamanki danni bazama yakawoni ba dama sako nazo baki kuma na isar miki Dan haka.
Yaja da baya tareda gyara tsayu warsa yasanya hannu cikin aljuhun wan donsa yazaro bandir d'in yan 1k ya wurga mata, "ga wanna kada kiyi sam manin daga gurina suka fito sakon Daddyna ne idan kina bukatar wasu zaki iya nimansa kamar yanda yanzu kika bukaci hakan."
yajuya haryakai bakin kofa tayi saurin mikewa tad'au kud'in tawur gesa dashi bai samesaba saiya fad'i kasa daf da kafarsa,

tace "ka kalleni ka lalli gidanmu kaga nayi maka kama da masiya ciya?kad'au ka dai ka kaiwa Wanda kasaba wula kan tasu kafin kabasu danni nafi karfin wulakan cin ka wlh."

Girgiza Kai yy batareda yace komai ba yy ficewar sa,
komawa tayi zub'e saman kujera kukan dataketa dannewa d'azu ya sub'uce mata,wanna karo kukan bana shagwab'a bane kukane na bil hakki da gaski,tad'au tsawon lokaci tana kunan kana tashare ha wayenta ta tashi tafito part in Ya Al'ameen tatafi,Yana zaune a parlour shida aunty Rukayya ta isa da gudu tazube bisa goiwo winta tahad'a hannayen ta biyu tace "Ya Al'ameen Dan Allah kada kabari a auramin shi wallah bana son shi Dan Allah kacewa Abba bana son shi." sai tasaki kuka mai tsuma zuciya.
Ya Al'ameen agigice yad'agota Yana fad'in "Shalele meya sameko meya sami idanunki suka kun bura haka?."
"Ya Al'ameen ni bana sonshi Allah idan akamin aurenna guduwa zan kumayi."
Murya narawa yace "kinutsu JUHAIFAH babu Wanda zai sake yimiki dole wanna karon bazamu tab'a yarda akuma mai maita abunda yafaru abaya ba,Zan sami Abba za a janye maganar aurenna,tunda bakiso baza ayi miki dole ba,zo kije ki kwanta kihuta kisa aranki anma fasan."
ya janyo hannunta suka haura sama ya shigar da ita cikin bedroom inta har saida ta kwanta kafin yafito,
Yana fita direct gun Abba yatafi.
A parlour ya sameshi nazaune rikeda jarida ya isa yaxauna kusa dashi tareda gaishe shi,
Abba ya amsa cikeda kulawa ya aje jaridar da ke ahannunsa,yace "har kadawo?."
yace "Eh Abba yanzu shigowata kenan saiga JUHAIFAH tashigo da kuka."
Abba yy murmushi yace "Mamana kenan 'yar rigima to inbanda abunta zata cigaba da zamane da mu batareda yin aureba."
Ya Al'ameen yagyara zamansa yace "Amma Abba tace shine bata son shi, to inaganin bawai aurenne bataso gabad'aya ba, Abba me zai hana abarta tazabi Wanda take so kokuma acan za mata wani,tunda tace bata sonshi inaga barin shiyafi dan gudun Kuma faruwan abunda yafaru abaya."

Numfashi Abba yasauke kana yace "da yardar Allah hakan bazata kara faru waba,yazama dole JUHAIFAH tayi aure mukuma mubada goyon baya akan hakan har idan son da muke yimata yakai so, duk wani gata daza mu iyayi mata arayuwa to bai wuce mu aurar da itaba domin kuwa kamarta mace darajar ta mutun cinta gidan auren ta, muci gaba dayi mata addu'a in Sha Allahu abunda zai biyo baya shine alkhairi da yardar Allah,bawai inaso inyi mata auren dole bane a'a saidan inaso rayuwarta ta inganta bamusan yawan alkhairin dake cikin wanna auren ba, Dan haka muzubawa sarautar Allah ido duk abunda yayi damu dai-dai ne Dan shi yafimu sanin kanmu."


Jin jina Kai Ya Al'ameen yy yace "to Amma Abba baka ganin..saurin dakatar dashi Abba yy tahanyar fad'in "kada kace komai,
Kamar yanda nace maka muyi mata addu'a Kawai."
Dun dole Ya Al'ameen yy shuru,yamike Dan lokacin anfara Kiran salla suka fito da Abban suka nufi masallaci.

JUHAIFAH tunda Ya Al'ameen yakaita d'aki takwanta bacci ba ita tafarkaba sai kiran sallar magariba, dakyar ta iya bude idanunta dasuka yimata nauyi ta zuro kafafunta kasa tamike tsaye tanufi bathroom wanka tayi tare da daura alaula tafito tagabatar da sallah tananan kan sallayar har akakira sallar isha tatashi tagabatar tare dayin addu'oi, tamike dakyar jin alamun zazzabi ajikinta tahaura saman bed batare da tacire hijab din dake jikintaba,tana kwanciya sai barci yakuma daukarta, cikin barci taringajin tsuwa nawayanta saita mirgina tare da zaro wayanta da takwanta akansa tamai dashi gefe tacigaba da barcinta, can bayan baccinta yayi nisa takarajin tsuwa nawayan cikin magagin barcin tadau wayan tare picking na call d'in sai tadaurashi kan kunnenta harlokacin idonta arufe daga cikin wayan taji anacewa

"kifara kirga wadannan kwanaki sha hudun dan sune kadai suka rake miki nafarin cikinki kisa aranki daga kansu kindaina rayuwan farin ciki bazaura sauran wasu."
ana kaiwa nan aka kashe wayan, nanfa tanimi baccin dake idonta tarasa tasauko daga saman gadon tanufi kofa tabude, dasauri ta maida kofar tarufe Dan ganin duhu ya mamaye parlour tayi saurin komawa da baya tare da dafe kirjinta dake bugawa dan aduniyar nan ba abunda tafi tsoronsa kamar duhu dasauri taduba agogon dake daure kan durowa taga karfe d'ayan Dare takoma gado ta rakube jikinta na karkarwa dakyar bacci b'arawo yad'au keta.

Washe gari bayan ta idar da sallah tana kokarin ninke sallaya taji alamar shigowar sako awayar ta,asannu ta aje sallayar ta isa bakin bed tazauna tajanyo wayar tabud'e message d'in, asannu tafara karanta sakon

_"ina_ _mai_ _tunatar_ _miki_ _bazaura_ _ko_ _sadaka_ _ce_ _bana_ _so_ _bare_ _ke_ _Wanda_ _kika_ _gama_ _tunkan_ _kizamo_ _bazaurar_."

Dai-dai Nan sakon tatsaya

"Inna lillahi'wa'inna'ilaihirraji'un wanna mutumin waye shi? meyasani game

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login