Showing 84001 words to 85666 words out of 85666 words
Chapter 29 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt
a kan ta, da sauri tagyad'a Mata Kai Dan kuwa wani irin bacci ne da batasan da shiba ke fizgarta,
"Karb'i Kisha wanna zakid'anji dad'in bakin ki"
Mommy tafad'a tana bud'e marfin lakasera'n"
Dasauri MAHFUS ya ce "Mommy lakasera Kuma batafaci komai ai sai ya murd'e Mata ciki takuma yin wani a man".
Mommy ta ce "waya fad'a maka ai irin su ire-iren irin wad'an Nan a bubuwa med'an tsami tsamin Nan suke bukata shi yake tai makawa wajen dannen Aman".
JUHAIFAH ko tuni Tamika hannu takarb'i gorar takafa a abikin ta sai da Tasha Rabin gorar kafin tacireshi da ga bakin ta hartana wani lumshe Ido sabida dad'in daya mata.
Mommy tamike takoma kicking MAHFUS yamaso kusa da ita tareda karb'ar gorar ya a je yy Mata matashi da cin yoyinsa yajanye d'an kwalin kanta Yana shafa sumar ta hannunsa guda Kuma yasau kesa saman cikin ta Yana shafawa,yayin da zuciyarsa takasu Kashi biyu kowanne da kalar a bin da take bijiro Masa hankalinsa yafi raja'a ta d'aya barin Wanda take jaddada Masa cewa da yanzu yacuci kansa da yabi na son zuciya da gajen hakuri da kin yadda da kaddara da yanzu Bai mallaki JUHAIFAH ba gashi yanzu tazame Masa alkairi bayan babbar kyautar data mallaka Masa a bu mafi girma da daraja wato budur cinta sai gashi a yau tana d'auke da gudan jininsa a cikinta.
Maida hankalinsa yy kan
D'aya b'ari na zuciyar sa Wanda ke kunshe da d'inbin farin ciki da so da kauran JUHAIFAH yashafe cikin zuciyar tasa gabad'aya.
Itako la mo tayi akan cinyarsa a yanzu bacci kad'ai take da bukatar sa
Jin motsin Mommy na tahowa saitayi saurin Yun kurawa tamike a kan kafarsa Mommy ko murmushi tayi takaraso tadire plt in da ke d'auke a hannunta saman table in da ke gaban su.
Kurawa plt in Ido tayi gwaten alkama ce wacce taji bushashshen kifi da gyad'a da kayan yaji sai ganyen yakuwa da aka yanka manya-manya a ciki sai tashi dawani daddad'an kamshi yake,
Had'iye miyau inda yacika bakinta tayi
"Ci Dan baccin yayi Miki dad'i".
Cewar Mommy Kamar jira take tagyara zaman ta tacire cokalin da ke cikin plt in tasaka hannu tasoma ciki,
Mommy tazauna saman kujerar dake gefen su.
Ido yakura Mata ganin yadda ta dage taketa kwasar girkin hartana wani lumshe Ido.
d'aukar cokalin da ta aje yy yad'ebo a bincin yakai bakin sa tsami had'eda yaji su suka fara yi Masa maraba da sauri ya a je cokalin yad'au ruwa yasha yana Mai cigaba da binta da kallon mamaki duk tulin yaji da tsamin da yaji a cikin a bincin Nan itako a jikin ta babu wani a lama da yanuna Jin d'aya daga cikin wad'annan a bubuwan a gareta.
Saida taci kusan rabi kafin tacire hannun ta Mommy tamike tad'au plt in tamai da shi kicking tafito da robar wanke hannu tabata ta wanke ganin tanata sauke hamma yasa Mommy cewa "jed'aki kikwanta".
Takarashe maganar da nuna Mata d'akin da ta zauna lokacin da take gidan,
JUHAIFAH tamike tashige d'akin tahaye gado cikin sakanni kalilan bacci yy gaba da ita.
A parlour kuwa bayanta sukabi da kallo har tashige d'akin, numfashi MAHFUS yasauke tareda duba a gogon dake makale a hannunsa ganin lokacin sallah yy sai yamike yahaura sama yy alawala yasauko yanufi masallaci.
JUHAIFAH Bata farkaba sai daf magriba MAHFUS yy sintiri a kanta yafi a kirga Dan ma Mommy takan hanashi tace kada ya tasheta yabarta tayi bacci.
Tana tashi bayi tashiga tayi wanka tareda d'auro alawala tafito tagabarat da sallolin da a ke binta sannan tad'aura da magriba da ta isketa bisa kan sallayar.
Mommy tashigo d'akin da sallama ta aje Mata wani a bincin da ta girka Mata wan da tasan zai iya zama a cikin ta batare da tayi a man Saba,
tazauna bakin gado tana zaman jiranta ta idar,
wayarta yafara bada haske a Lamar shigowar Kira Mommy dake kusa da wayar ta Mika hannu tad'au wayar ganin Mai Kiran yasata picking na call in,
"Gani a parking lot Kifito mutafi".
Mommy ta ce "hauka kake da jaririn cikin zaka Rika kwasarta kana yawo da ita a mota to bazai yiwuba Babu in da zata sai cikinnan yayi wayo salon wani abin yafaru da shine kome".
Kafin Yakuma cewa wani a bun Mommy takashe wayar.
Lokacin JUHAIFAH tashafa addu'r da take tamike tsaye Mommy tadubeta da kyau ta ce "a nan Zaki zauna harsai kindad'a Jin karfin jikin ki".
"Tom" JUHAIFAH ta amsa da shi sanna tanimi guri tazauna Mommy Kuma tafita.
Ganin da gaske Mommy take yasa MAHFUS tafiya gida yaje yad'ebo musu kayan su daga ranar suka dawo zaman gidan Mommy,
Da wowarsu kuwa Bai ragesa da komai ba Dan Dazarar Mommy takauce zai shige d'aki wajen matarsa yaje yakwashi rab'a.
JUHAIFAH taga soyayya a gun Wannan family'n kamar wan da ba'a tab'a samin ciki a zuriyar ba labarin cikin JUHAIFAH yakared'e family'n gabaki d'aya
Tarairaya da kauna babu irin Wan da batasamu a gun su,
Farin ciki gun Daddy ma baya misaltuwa yanzu har ware lokaci yake yazauna a gida suta Hira.
Abba da Ammee Ya Al'ameen Ya Mujaheed Ya Jabeer Aunty Rukayya Hassan da Hussain ma duk sunzo ranar da sukazo Rabin wuni sukayi a gidan anata Hira cike da Jin dad'i kafin suka koma.
Mommy ce zaune cikin bedroom inta kare da waya a kunne tanafad'in "ai Hajiya munyi fushi tun da kukazo duba JUHAIFAH sau d'aya Baku Kara zuwaba to ni zan karb'e mijin idan yazo idan Kuma mata ce saina tura Miki ita."
Dariya Ammee dake biye da Kiran tayi ta ce "au niza'a turawa kishiya kenan,to ai Hajiya naga lfyrta lau ai muna kan yimata addu'ar fatan sauka lfy Allah yarabasu lfy Amma dai kirike kishiyar ni a turan mijin idan yazo".
Dariya sukayi gaba d'ayan su daga bisani
sukayi sallama.
_(Nima sallamar nayi musu Dan kuwa na tattara inawa inawa nakoma garinmu nayi niyyar bazan sake komawa Abuja ba Amma sai na kasa yin hakan bayan wani lokaci sainaji inason nakuma leka su naga halin da suke a yau kuwa nanika garina izuwa Abuja ban tsaya ko inaba sai Maitama takofar gidan MAHFUS nabi niyyata nawuce gidan Mommy ganin get in gidan a wangale sai kawai nakusa kaina ciki can nahango MAHFUS nafitowa daga cikin parking lot da alama dai washi a ka bud'ewa get)_
★★★★★★★★★★★★★★★★
Yakara haske harda d'an kiba kallo d'aya zaka Masa kaga zunzurutun kwanciyar hankali a tattare da shi,
Cikin takunnan nasa
Yanufi ciki tundaga bakin kofa yarikajin kuka da sauri yamurd'a handle yatura kofar yashiga da sauri har Yana had'awa da sassarfa
Wani yarone kyakykyawa farin tas zaune cikin parlour'n sai rusar kuka yake cikin hanzari MAHFUS yanufi in da yaron yake yad'agashi cak yaman nashi a kirjinsa yashiga bubbuga bayansa,
yaron kuwa lamo yy a kafad'ar sa sai sauke a jiyar zuciya yake a Lamar yaci kukan yakoshi,
Baki na bud'e kar dai a ce JUHAIFAH harta haihu ni inacan banzo nad'ibo muku rahoton yanda a kayi akayiba🤔
Yana rikeda yaron yanufi wani kofar bedroom sai yanzu na lura da sauyin da gidan yasamu komai nagidan an sauya,
Yatura kofar bedroom in yashiga
JUHAIFAH na zaune gaban mirror daga cikin mirror'n takallesa sau d'aya tajanye idon ta daga kansa tacigaba da shafa man da take,
Ya'isa bakin gado ya a je yaron ai ko Yana a jeshi Yakuma sa kuka Yana kallon JUHAIFAH Yana zamewa a jikin MAHFUS in,
Itako Mai da hankalin ta tayi sosai kan abin da take tayi kamar ma batasan da shigowar wani cikin d'akin ba.
MAHFUS dayacika har wuya yadubeta daga in da yake zaunen cikin tsare gira ya ce
"Kizokibawa yaro a bincin sa Wannan wani irin zaluncine a kan wani da lilin ki kihana yaro nono".
Mikewa tayi batare da tace da shi kalaba Dan yau kwana uku kenan suke fushi da junan su tazo tawuce shi taje gaban wardrobe tana kokarin bud'ewa taji yafiz gota,kafin tayi wani aune yad'agata cak yad'aurata a kan
gadon,
towel in da ke kirjin ta yakwance yadanne hannayen ta da hannun sa gu da d'aya hannun Kuma yad'ago yaron dashi yagyara Masa kwan ciyarsa a gefen ta ta'in da zai Samu yaci abin cinsa,
Tabud'e Baki zatayi magana yatsereta da rikitattun ida nuwan sa, saurin janye idanunta tayi batare da ta fad'i a bun da takeson fad'an ba,
Yaron kuwa Yana
Kama nonon ba jimawa bacci yad'au keshi ganin yy bacci sai yasaki hannun ta yagyrawa yaron kwan ciya.
Kokarin mikewa take yy saurin maidata da hannu a kunne yarad'a Mata "kin bashi nashi saura nawa yau dai a aje fushun Nan a tai maka nasha rab'a".
Kawar da kanta tayi ta ce "wlh cuta kake sa nabawa yaron Nan".
Sai Kuma tayi rau-rau da Ido saiga hawaye cikin muryar kuka take fad'in
"Yaro watansa 8 ciki wata 3 nikam nashiga uku".
Takarashe tareda Kuma fashewa da wani kukan".
Jan yota yy a jikin sa nan yashiga yimata salon kwantar da han Kali daganan suka Lola duniyar ma'aurata.
MAHFUS zaune a bakin gado Yana tsane gashin kansa da karamar towel ya d'au wayar sa ya danna numbern Mommy bugu biyu tad'aga bayan sun gaisa
Ya ce "Mommy HAFSAT ta tada han kalin ta wai sai dai a yaye Shureem".
Dasauri Mommy tace "ciki gareta?".
Ya ce "E".
"Kai to Masha Allah yanzu ka d'au kosa da kayansa ka kawo mun shi".
"Mommy watansa 8 nefa yanzu Taya za'ayi a yayeshi".
Ta ce "in ban da a binka yaro Mai kuzari ai d'agashi a bakin nonon shi zaisa yakara kuzarin idan Kuma a ka cigaba da barinshi tofa datti zaisa".
Kashe wayar yy yakalli JUHAIFAH saiyaga tayi murmushi yamika hannu yafatad'in "zo Nan harma dad'i kikeji Dan za'a cuci yaro ko".
Zillewa tayi tana ci gaba da dariya.
JUHAIFAH tashiryawa yaron Kaya suka kaishi gidan Mommy daganan suka shige asibiti Dan dai-daita lissafin cikin dake jikinta kwajin farko a kagano 'yan ukune a cikin ta.
Koya Wannan family'n zasu kasance idan sukaji Wannan babban albishir in🤔
TAMMATBIHAMLILLAH👏🏻
*Anan nakawo karshen wannan littafin saidai Ina maiyi muku albishi dacewa Ina tafi muku dawani sabon tittafina Mai suna HAMDAH wanna littafin salonsa daban ne ba irin Wanda nasaba kawo mukushi bane kubiyoni danjin me Wannan labarin yakunsa zakusha mamaki*
Ina kaunarku masoyana🥰
Mommy twins ce